Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama inuwa ɗaya toh abu na gaba da zai biyo shine nuna mata haramcin duniyancin da take yi wanda ita kuma ba haka take so ba wannan dalili ya sa take nesanta kan ta da ɗiyar ta,toh yau babu ita babu dalilin ta..
  Abu ɗaya ta sani,shine da zarar lokacin cika ƙudirin ta ya kai dole ta saka a mata kiranyen gimbiya Ondrea dan ta ƙarasa cika burin ta a duniya..

★★★★
  _OTTOMAN EMPIRE_
  Wuta ne kawai ke kan kamawa a masarautar Ottoman dan da zarar wannan ƙofar ta buɗe toh wani zai rufe,fitintinu kawai ke ta afkuwa a masarautar Sultan Baal-Hamon wanda ya zuwa wannan lokacin Sultan ya gama sadaukarwa duniyar ta mai juyin masa mai wuyar maidowa kamar da..
  Hakan na nufin kenan tasa ta kusa zuwa ƙarshe duk wasu abubuwan da ya daɗe yana ginawa yana tattalin su zasu rabu da shi dan rantsuwar da yayi ne a shekarun baya ke son bin sa ta baibai,..
  A kullum fitinar dake doso sa daban daban ne daga yayi asarar dawakan sa na alfarma sai yayi rashin mayaƙan sa sai ya tsinci kan sa cikin rashin bacci da kwanciyar hankali..
  Ɗiyar sa ɗaya tilo wato gimbiya Acenath duk ya fi tausayawa dan bata ji ba bata gani ba masifar da ya dasa na son shafar ta,hatta da rayuwar holewar sa da yake yi da Dacey,ya manta rabon da ya laluɓe ta dan masifar da yake ciki kaɗai ta ishe sa komai,ko lokacin matar sa sarauniya Bayarma bai da dama can bai da lokacin nata bare yanzu da yake cikin masifa da jarabta...
  Da yake shi ɗin ɓatacce ne sam bai da ranar canza halayyar sa dan bai shirya ba gani yake kawai kamar mugun aiki ake mai a duhu shi yasa bai gane kan abubuwa amma ya ma kan sa alƙawari duk lokacin da zai gano me mai wannan ɗanyen aikin toh fah ba zai yi sparing nasa ba..
A duk sadda ya kalli gimbiya Acenath sai ya ji tausayin ta ya lulluɓe sa abin na ba sa tausayi kwata kwata baya son abin da zai taɓa ta amma ya san bai da yadda zai yi rana na nan zuwa da dole ya haƙura ya bar nature yayi taking place...


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:57&58*

_ONE MONTH LATER_

_Turkey_
Rayuwa tayi sauƙi a wun su Juda dan ba laifi suna kan koyar abubuwa da dama a fannin addinin su wanda suka aminta da shi kuma abin na masu daɗi,ana mutunta juna sosai ana daraja decision ɗin kowa da opinion nasa babu hantara bare nuna halin ko in kula ga maganar wani ko wata.
A yayin da gimbiya Ondrea ta ke renon cikin ta tana kaf kaf da lafiyar cikin nata duk wani abu na sha'awa da zata ce tana so toh mijin ta is ever ready ya mata hakan na daɗa ƙara danƙon yarda da amincin dake tsakanin su da shi..
Kwata kwata bai wuce kwanaki uku ba da zasu tafi yin binciken su a inda zasu fara da masarautar Ottoman,duk wasu shirye shirye da ya dace ya kamata sun yi sa kawai jiran ranar tafiyar suke yi,already Juda ta matsu ta haɗa idanu da mahaifiyar ta dan tayi kewar ta matuƙa kuma ta matsu ta nuna mata Callee da haɗuwar su ta zamo alkhairi,sannan tana son ganawa da ƙanwar ta dan ya zuwa yanzu,an nuna mata haramcin ɗaukar hukunci a hannu ta an nuna mata ta kai ƙara ga hukuma dan su yanke hukunci daidai laifin wanda ya aikata laifi..
Abu ɗaya ke ɗawainiya da Juda a rayuwar ta,wannan abin ba komai bane illah fargaba,dan sai dai in bata haɗa ido da Cahal ba,muddin ta haɗa ido da shi toh dole ne ranar a suƙuƙu zata wuni bata san dalili ba,sau da dama tana gwada son tunkarar Callee da Berenice da batun amma tana jin wani iri duk tsoro da shakkar hakan na damin ta,a kullum in zata gan sa da matar sa toh sai fah ta ji babu daɗi a ran ta wanda bata san dalili ba..
Bata sani ba,Fianna na ankare da duk moves ɗin ta dan yarinyar akwai lura da saurin ɗago abu,toh da yake tun lokacin da wannan abin kunyar da ya faru tsakanin ta da Balik wato ranar da suka yi clashing da shi yana wanka,toh bata ƙara sake jiki da shi ba abin mamaki har yanzu bata sake sosai ba tana ɗar ɗar da shi bata son zama wuri ɗaya da shi.
Toh ta fara fuskantar wani hali da take tsintar kan ta a ciki a duk sadda suka haɗu wannan abin bata san menene ba haka bata san yaushe abin zai rabu da ita ba,ta so sanar da Callee amma itama haka abin sai ya rinƙa ƙaƙare mata sai ta fasa,toh lokacin da ta fara lura da Juda sai ta saka mata ido sosai dan sanin me ke damin ta,tun daga lokacin take bin diddigi tana saka ma Juda ido dan ganin ina zurfin cikin nata zai kai ta ya tsaya..

Fitowar Agneta kenan daga wanka tana goge jikin ta tana tambayar Callee
"Callee,yaushe wai kika ce an maki dole akan ki aminta a lalata maki rayuwa"!?kallon ta Callee tayi sai ta ɗan yi ƙasa da ido tana faɗin
"When i was sixteen"!!ɗan dakatawa Agneta tayi daga goge jikin ta ta zo ta zauna gab da Callee sai ta kuma tambayar ta
"Kin sanar da yayar ki"?(wato Juda kenan dan tun lokacin da Yaya take referring nata kasancewar duk cikin su ita kaɗai ce ƙarama ƴar kimanin shekaru ashirin da ɗaya)..
Girgiza kai Callee tayi tana faɗin
"Ban sanar da ita ba dan bana son mu kuma aikata jahilcim da muka yi a baya,kawai tunda babu abin da ya faru mu bar shi kawai,let's focus on the future kawai Agneta"gyaɗa kai Agneta tayi tana jimamin dalilin da ya sa ita dai har wa yau bata fara jin wani feelings akan wani ɗa namiji ba sai dai tayi mutunci da su amma batun soyayya kam,babu shi,ba wai dan babu masu nuna interest akan ta bane a'a kawai dai soyayyar ce bata ɗaɗa ta da ƙasa kawai..
Tare suka fito dan yin breakfast a inda su Fianna suka riga su zuwa dan yanzu kamar family suke,a duk sadda Cahal ya tuno abin arziƙin da suka mai a baya na taimakon sa da matar sa sai ya ji wannan kaɗai da yake masu isn't enough,wannan dalili ya sa kawai ya yanke shawarar taimaka masu samo sauƙin rayuwar su duk da ya san matar sa ta kusa haihuwa amma a kullum yana nuna mata farin cikin da zasu yi in suka sami justice da haka ita kan ta gimbiya Ondrea ke sakawa tan ta taimako zata yi kuma lada zata samu..

Da suka kammala cin abincin ne aka fara teasing juna kamar dai yadda suke yi a kullum,sukan tuno rayuwar su ta baya sukan yi alhinin jahilcin da suka tafka,one thing for sure they know is that sun tsallake wannan rayuwar babu maimaitawa kuma Juda ta san tarihin ta dake cikin kundin nan nata,shall always be her family legacy but the delusional illusions,are no where accommodated in her life anymore wanda a rayuwar sauran ma haka ne sun yaye wannan abubuean believes ɗin dan sun fahimci duk sihirin nasu a iya nan yankin nasu ya tsaya kuma an nuna masu hakan na faruwa ne due to meditation da delusional believe da suke yi a duk sadda abin zai faru ko zasu gudanar da wani abu,dan haka suka yi ƙoƙarin share wannan abin a rayuwar su..
Pertaining their horses kam tuntuni Balik ya basu shawarar su sayar da su kawai su yi amfani da kuɗin su kafa wata sana'a,shawarar ya karɓu dan tun asali Juda sana'ar nasu kenan siya da sayarwa toh da wannan shawarar suka kafa sana'ar su ba tare da sun yarda da facts ɗin da Cahal ya rinƙa kawo masu na su bar wani sana'a shi zai na sponsoring nasu ba,da haka suma suka kuma wayewa dan sana'ar da Balik ke yi ya sa ya daɗa wayewa haka su Juda akan ɗan fita tare da su time to time dan yawon buɗe ido saboda duk su cire wannan mentality dake tattare da su,kuma ba laifi a yanzu duk ya tafi dan har waya suka fara riƙewa gimbiya Ondrea ce ke koya masu,abin dai kamar a mafarki rayuwa ta rinƙa sauya masu..
Duk da wannan jin daɗin tunanin su gabaɗaya yakan ta'alaƙa akan komawa gida wun family nasu dan sukan ji kewar families nasu..
Ko da ranakun tafiyar nasu ya matso,sai zumuɗin yayi yawa suka zaƙu su koma gidajen su though hidden facts are still hidden between Juda,Cahal,princess Ondrea,Fianna and Balik...

★★★★
_Back to Oman Empire_

Bayan barin mistress ɗin sarki Malik garin Turkey,tayi nasarar raba sa da ƙasar sai dai duk yadda ta so tursasa sa ya biyo ta su tafi masarautar Ottoman dan aiwatar da abin da mahaifin sa ya saka ta aiwatar wa bai yadda ya bi ta ba haka ta rinƙa dabarun ta amma inaa abin ya ƙi,toh dama tana son sa ta daɗe tana kwaɗayin sa amma bata taɓa samin fuska ba..
Toh sai kawai ta yanke hukuncin threatening nasa akan ko ya yarda su tafi ko ya kwanta da ita,sanin kan ta ne cewa sam ba zai aikata hakan ba,sai ta gwada yin amfani da wannan hanyar..
Ai ko ta sha mamaki dan kuwa ya ce da ita ya aminta sai ta ji farinciki ya lulluɓe ta murna kamar me sai dai ya nunar mata akan su koma ƙasar su in ya so a nan sai duk abin da zai faru ya faru,nan hankalin ta ya tashi dan ta san ko gigi take yi ba zata iya aikatan hakan ba,kenan wasar ƙwaƙwalwa yarima Ziyan ya mata,lallai dole ta san abin yi dan ko ba yarda zata yi ta rasa wannan damar da sarki Malik ya bata ba..
Toh tun daga ranar da wannan conversation ya shiga tsakanin su bata kuma ce mai komai ba,a haka har ta gaji ita da muƙarraban ta suka yanke hukuncin komawa gida kawai in ya so ta mai wani sharrin dan fah ba zata yi biyu babu ba sai dai a ɓata biyu ɗaya ya gyaru..
Daga haka suka bar inda suka yi matattara wato camp ɗin su,suka bar wurin suka ɗau hanyar komawa masarautar Oman da abubuwa daban daban a zuciyoyin su..

Ko da suka koma gida sarki Malik ya ga abu wani iri sannan ya ji labari daban sai da ya ji kamar ya hukunta ɗan sa yarima Ziyan amma ba zai iya ba, dan yana bala'in son sa dan haka ya gayyace sa da ya taho cin abinci tare da shi..
A ranar sai da ran sarki Malik ya ɓaci kamar me dan tsaf yarima Ziyan ya warware mai yadda suka yi da wannan mistress nasa,sai da sarki Malik ya jijjiga masarautar nan dan kuwa sai da ya sa aka fille mata kai dan cewa yayi tana so ta lalata masa ɗa ta kuma ci amanar sa dan so tayi ta haɗa da shi da ɗan sa..
Ko da dare yayi sai da yarima Ziyan ya sa aka haɗa kaf mutanin fadar nan ya sa aka fara bincikar su ko a ina suka tsaya a matakin karatun addinin da ake masu,jin wannan magana sai sarki Malik ya ji gaban sa ya faɗi dan kuwa ya san ya hana aiwatar da wannan addini dama dama na bokon,dan haka sarki Malik yayi yadda zai yi dan ya dakatar da hakan amma inaa ya makaro dan kuwa yarima Ziyan ya gano komai kuma bai tanka ba yayi tafiyar sa ɗakin sa yayi kwanciyar sa..
Da wannan ɗabi'ar tasa ya share tsawon sati guda a masarautar mahaifin sa ba tare da ya kuma ziyartar mahaifin nasa ba,wanda wannan abin bai mai daɗi ba dan ya san silent punishment ɗan nasa ke masa kuma ya jiggatu ya ji a jikin sa,duk da ya san yana son duniya amma dole ya faranta ma ɗan sa dan dai shi nasa zunubin bai kai nauyin na Sultan Baal-Hamon ba dan shi kan sa abubuwan da yake aiwatarwa a nasa masarautar duk under influence ɗin Sultan Baal-Hamon ne toh da yake yana da raunin imani sai abin ya rinjaye sa ya bi ya dulmuya cikin tsaɓo ɗan sa na son fidda sa amma yana ƙi dan rayuwar tsaɓon ya masa daɗi..
Kamar wasa haka gaba ta shiga tsakanin sa da ɗan sa har sai da mahaifiyar sa ta saka baki sannan ya nuna ɓacin ran sa akan ƙin bin maganar sa da aka yi a masarautar da hakan ake son ya zama sarkin when his people aren't respecting his wish..
Toh fah a nan ne mahaifin sa ya shiga nuna mai ya karɓi kuskuren sa kuma zai gyara m,tundaga wannan rana sarki Malik ya tsayu yana gabatar da addini a masarautar sa duk da yana da ɗan ɗison kwaɗayin son mulkar mutani amma ɗan sa ya dage wun nuna masa lallai lallai fah wannan buri bai isa ya cika sa ba mutum ɗaya ke da ikon mulkin duniyar kuma shine Allah subhanahu wata'ala,da haka fah da ƙarfi da fin ƙarfi yarima Ziyan ya saita mahaifin sa wanda ya so ya gana da satauniya Zinaida dan sanar da ita sabon al'amarin da ɗan sa ya kawo masa sai dai yarima Ziyan bai yarda an sami wata ɓaraka ba da zai sa yayi satar fita ya gana da sarauniya Zinaida ba..
A halin da ake ciki a yanzu kusan tsawon shekara kenan dan kaɗan ya rage shekara ta cika a watannin da yarima Ziyan ya ɗauka yana wanke ƙwaƙwalwar mutanin yankin masarautar mahaifin sa ciki har da mahaifin nasa..
Lokacin nan ba ilimin addini kaɗai ake gudanarwa a masarautar ba hatta da na zamani sai da yarima Ziyan ya sa aka kafa sa dan kuwa mahaifin nasa ne bai sani ba amma shi kam ya koyo hanyar da zai gurfanar da mai laifi a gaban hukuma kuma yana fata nan gaba ko da zai kawo hukuma wannan yankin zai zo da sauƙi dan mahaifin sa da masarautar su zata kasance cikin less focused..
Akwai wani zama da sarki Malik ke tuntuɓar yarima Ziyan akan zancen haɗa sa aure da gimbiya Acenath suke son yi shi da aminin sa Sultan Baal-Hamon,ai a nan kuwa yarima Ziyan ya birkice ya nunawa mahaifin nasa Allah ya kashe sa in zai karɓi auren wannan shagwabaɓɓiyar yarinya marar kamun kai sai ra'ayin tsiyar,..
Duk yadda sarki Malik ya so fahimtar da shi akan ya haƙura su rufawa kan su asiri tunda ta ce bata son yariman Cyprus shi take so kuma shi so yake wai ta sanadiyar yarima Ziyan ɗin suma masarautar Ottoman ta gyaru ta karɓi addinin islama kamar yadda aka karɓa a nan ɗin dan shi ya san ko da sama da ƙasa zata haɗe wu guda ne toh fah Sultan Baal-Hamon ba yarda zai yi da wannan addinin ba amma in har ɗiyar sa ta nuna sha'awar ta akan addinin toh wata ƙil ya amince..
Har dai suka rabu shi dai ba gamsuwa yayi da wannan batu ba kawai dai ya bar shi akan zai yi nazari ne in abin ya mai fine in bai mai ba toh sai dai fah a haƙura dan ba zai iya tarayya da wannan yarinya marar tarbiya da kwaɓon ba..
Shi dai sarki Malik addu'a yake akan Allah ya sa ɗan nasa ya yanke hukuncin ya amince dan kar ya ha'inci Sultan because har wannan lokaci yana ji a jikin sa kamar bai kyautawa Sultan Baal-Hamon ba...

A daren da suka gama maganar ne yarima Ziyan ya laluɓi wayar sa ya danna kira dan yana buƙatar samin mafita cikin wannan duhun da yake ciki..
Ba jimawa aka ɗaga daga ɗaya ɓangaren a inda aka yi sallama shima ya amsa sallamar yana mai gaida wanda ya mai sallamar..
Ɗan taƙaittaciyar hira suka yi kana ya ɗora da batun abin da ya sa yayi kiran a ƙarshe ya rufe maganar da
"Friend,ina son sanin ainihin matsalar wannan masarauta ni fah ba gimbiya mr bace a gaba na,bata min ba amma ina son nunawa Sultan Baal-Hamon iyakar sa dan dole fah sai ya karɓi laifin sa da yayi shekaru da dama saboda i want him to bear the cross of what he caused due to his curse"..
Daga ɗaya ɓangaren aka amsa mai da
"Ziyan kenan,kamar ka dai manta ni,ni fah na sanar da kai mai centre of focus ɗi na kenan,in ga downfall ɗin wannan mutumi dan hakan ne ma ya sa ka ga nayi takakkiya na kai kaina masarautar sa,na jure zama da shi a hakan da daɗi da akasin hakan na yarda na maida kaina irin mutanin da yake mulka,wato Ziyan idan na fara fayyace maka wani abin sai ka yi mamaki dan it's too strange,i have alot to tell you but sai ranar da dubu ta cika muka ma wannan mutumin kamu,irin kamun da prosecutor ke ma victim ɗin sa dan ba zan kira wannan mutumi da client ba he is very selfish and confused,but,ka bari ranar ta kusa zuwa zamu gyara duniyar mu yadda ta kamata kuma zamu sami ladar yin hakan kawai kai dai ka cigaba da creating awareness da kake yi a nan wurin ku aboki na dan na sami labarin akwai similar cases a wasu ƙasashe biyu i think the two countries are called Tanzania and Nigeria,though is not that much in these two countries, but still we have to eradicate such act because it is a violence it is a total act of domestic violence and abuse,aboki na sai mun haɗu already Khabeer and Ra'ees na nan na kula da Mughal da kuma Cyprus kuma they are doing good ba laifi"..
Nannauyar ajiyar zuciya yarima Ziyan ya sauke jin an sami cigaba a rayuwa fiye da da da wannan azzalumin Sultan Baal-Hamon ɗin ya tauye duk dan babu wayewar kai da tsoron sa da ya saka a zukatan mutani,amma wannan conjunction da yayi da abokan karatun su da suka kammala tare har suka fara aiki a biranai biyu wato Turkey da Spain kamar dai yadda aka tura su daga makarantar su akan su tafi wuraren da ke da ƙarancin ilimi su wayar da kai toh fah shine shi yarima Ziyan ya zaɓi ƙasar sa yankin sa masarautar su a case of study nasa,dama sa'ar wacce ta tafi ɗauko sa ɗaya,lokacin shima ya koma kai report ne akan ga inda ya samu yake kuma da interest akai sai aka yi sa'a a ranar ta zo ta ɗauke sa wanda bayan hakan ne ya san yadda yayi communicating da sauran team members nasa suka rarraba kan su a wuraren da suke a halin yanzu dan so yayi shi yayi handling abin shi kaɗai saboda su kuma su myi focusing akan inda aka tura su sai dai ganin kamar babu isasshiyar lokaci sai kawai yayi involving nasu..
Dama faɗuwa ce ta zo daidai da zama akwai mai ra'ayin tafiya ƙasar Ottoman sai dai bai san haka jahilci da daƙiƙancin masarautar take ba sai da ya tafi,da haka suka ɗau lokaci suna communicating duk abin da wani ya samu da ya kasance sabo ne toh sai ya sanar da sauran..
A haka suka tara enough facts ba tare da sanin kowa ba all they know shine zasu gyara ƙasashen nan sannan zasu koma su binciko wasu ƙasashen dake da irin wannan ɗabi'ar..

"Toh aboki na,ai na yarda da kai na yarda da fasahar ka,fin hakan ma kana iya yi,lallai ban yi kuskuren saka ka cikin plan ɗi na ba dan kai ɗin jarumi ne,alfarma ɗaya ya rage,shine ka binciko min yarinyar nan mai suna gimbiya Acenath dan ban gamsu da bayanin mahaifi na ba"..
"Baka da matsala da wannan aboki na,consider it done"..daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar sa,.
Har yarima Ziyan ya kwanta da nufin bacci sai kuma ya tashi ya kuma ƙunna wayar ya fara kiran Khabeer suka yi magana ya sami update daga gare sa bayan sun gama ya kira Ra'ees shima ya sami uodate daga gare sa sannan yayi sallama da shi ya kwanta da burin nan da kwanaki huɗu zai yi tafiya zuwa masarautar Ottoman ta Sultan dan fara kawo ƙarshen waɗannan halayyar tasa da kuma jahilcin da yake aiwatarwa a masarautar sa duk da an san tatihin masarautar kamar dai yadda rayuka suka salwanta duk dan dai a dasa addini a ƙasar kuma yana sane amma tsabar son rai da son zuciya ya saka ƙafa ya shure ya kafa jahilci yana rayuwar dabbobi da tumasanci a ƙasar sannan ba shi kaɗai yake zunubin ba hatta da mutanin ƙasar da basu ji ba basu gani ba sai da yayi involving nasu cikin jahilcin sa da duhun kan sa,wannan abin na ƙona ran yarima Ziyan Aman kuma ya rantse sai ya wargaza sa in har yana numfashi because he doesn't believe in those act and he is not ready to centre his believe in them....


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:59&60*

_Babylon_

"Yura,ni kam kin san wani abu kuwa"?tambayar da Hadara mahaifiyar Juda ta ma aminiyar ta kenan..
Kallon ta Yura tayi tana mai maida hankalin ta gabaɗaya ga Hadara sai ta cigaba da
"Ina jin wani iri,kamar dai Juda bata cikin kwanciyar hankali,sai nake ganin kamar nayi son kai da yawa,a ce ɗiya ta ɗaya ƙwal,in bar ta ta tafi wata uwa duniya alhalin ban da tabbacin shin wacce ta tafi nemowar na raye ko a'a,ban ma Juda adalci ba Yura,ina son bin bayan ta"!!
Kallon ta Yura tayi a yayin da ta ida maganar tana mai zubda hawaye dan ta matuƙar yin nadamar rabuwa da ɗiyar ta da tayi duk saboda wani dalili dan daga baya tazauna tayi nazari dan kan ta ta ga rashin dacewar abin da ta yi..
Dafa kafaɗar ta Yura tayi tana bata magana mai sanyi haɗe da bata hope akan any moment soon Juda will be back kuma da positive result zata dawo masu..
Sosai Hadara tayi zaman kaɗaici da zurfin tunani a wannan satin,sharewar shekara kenan babu ɗiyar ta babu labari sannan ga mugayen hannaye da ke burin ganij Juda ta zo gare su,abin dai ita ya zame mata gaba kura baya sayaki..
Duk wasu hanyoyin bauta,Hadara na ƙoƙarin bi dan ta ga ta sami kwanciyar hankali dan ta san in har tayi addu'a toh zai isa wun ɗiyar ta,a kwanakin ta dage da zuwa wurin bauta tana addu'a akan yarinyar ta ta kasance cikin kariya da faɗawa hannu na gari..
Damuwa sosai ke addabar ta,ba kullum take samin ikon fita kasuwa wun siya da siyarwar da take yi,lokuta da dama takan gwammaci zama a gidan ta rinƙa yiwa ɗiyar ta addu'ar nasara da kariya dan ta gane cewa,revenge,never pays instead,it ignites the calm situation into violence..

Ko a yau ɗin nan shiryawa tayi cikin shigar mutunci daidai al'adar su ta can ta nufi wun shiga keken doki dan ya kai ta inda zata tafi bauta,sakamakon mummunar mafarkin da ta rinƙa yi a kwanakin bayan nan,bata gamsu da su ba hankalin ta kaf ya koma ga lafiyar

Please Login or Register in order to submit comment