Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sara tana duba bakin gatari dole ta fita harkar gimbiya Ondrea tunda ta rantse sai ta mallaki kundin nan hakan na nufin ta jurewa duk wasu rigingimun da zasu dumfaro ta..da haka ta saka kai tayi wucewar ta zuwa fadar wankan ta..

  A daren ranar Cahal da gimbiya Ondrea suka saci jiki ta ƙofar kudu suka gudu ƙofar da ba kasafai aka cika amfani da shi ba sai in za'a yi baƙi na musamman daga wasu ƙasashen ake buɗe sa saboda karrama su,ko da sarauniya ta ji wannan labari a washegarin ranar da suka bar gidan ba ƙaramar ranaza ta yi ba sai dai ta baza tsaro akan duk wanda yayi kaciɓis da su ya kawo mata su ko a raye ko a mace,har fuskokin su aka zana a paper aka rarraba a garin har ƙauyukan garin abin nan ya zamowa sarauniya Zinaida wani abin koma baya duba da yadda ta ɗora buri akan gimbiya Ondrea amma duk tsaron da take mata sai da ta watsa mata ƙasa a ido lallai yaran zamani sai dai a bar su..
  Sama da sati biyu babu labarin gimbiya Ondrea da masoyin ta Cahal tun sarauniya Zinaida na ma abin kallon wasa har abin ya girme ma nazarin ta dan har ramewa ta yi sannan ga kundin da aka ce da ita ya kusa zuwar mata har rana mai kamar ta yau shiru baby kundi babu labarin sa ga ɗiyar ta ɗaya tilo ta ƙaurace mata saboda ɗa namiji sannan ga labari da ya riske ta akan masarauta Ottoman ya kuma haɓɓaka dan ta ji ƙishin ƙishin wai kundin ya kusa shiga hannun sarki sultan Baal-Hamon wanda hakan na nufin zata dawo baiwar sa kenan kuma masarautar ta ba zai cigaba da zama ƙarƙashin ikon ta ba sai abin da ya ce sannan zata yi..sam ba zata yarda da wannan zance ba dan haka ta bazama nemar hanyoyin tarwatsa masarautar Ottoman tun kafin damar ta kufce mata.. 

★★★★★

Zaune suke suna cin abinci a wata bukka mai kama da bukkan masu sayar da abincin kasuwa,babbar kasuwa ce mai zagaye da idanun gari sakamakon tsatsaurar tsaro da sarauniyar garin ta saka dan kamo ɓata garin da ke shigo mata ƙasa a duk sabuwar wata dan tafiya da matan da ake yi wanda oda ce daga masarautar Ottoman..

  Gyaran murya tayi tana mai ƙarewa kasuwar kallo kallon mamaki sannan ta ce
"Ni kam Berenice wannan ƙasa taku haka take ne ko me,ban gane ba tsaro ko ta ko ina saboda me ake hakan na lura tun da muka iso garin nan muka rinƙa ganin masu tsaro ba dare ba rana me yasa hakan"?ƴar murmushin gefen baki Berenice tayi sannan ta ba Juda amsar tambayar ta
  "A duk shigowar sabuwar wata,tsaron da ake sakawa na ninkuwa sakamakon ɓata garin da ke shigowa suna garkuwa da mata suna kaiwa ƙasar Ottoman fadar sarki sultan Baal-Hamon wanda hakan ke bala'in ƙonawa sarauniyar wannan ƙasa rai dan haka ta yanke hukuncin duk wanda aka kama yana haka a yanka sa har sai ya daina numfashi sannan a kawo mata kan sa dan ta wulaƙanta sa sannan ta aikawa sarki sultan Baal-Hamon bayan haka kuma duk wanda ya kai mata wannan umarni nata wato yanka ɓata garin,takan mai babbar kyauta yanda yake so dan shi zai faɗi abin da yake so a bashi kuma duk tsaurin abin nan sai ta nemo sa ta ba mutum shi saboda a ranar kwana take cikin farin ciki da annashuwa,kin ji dalilin da ya sa aka yaɗa masu tsaro ta ko ina kenan a garin"!!gyaɗa kai Juda tayi tana auna baƙin hali da son mulkin tsiya irin ta sarki sultan Baal-Hamon,tunani tayi muddin aka aiwatar da hakan toh sarauniya Zinaida na iya yiwa wanda ya aikata hakan kyautar duk abin da yake buƙata dan farincikin da take riskar kan ta a ciki a duk sanda aka kawo mata ɓata garin kamar dai yadda Berenice ta sanar da ita yanzu..
  Saurin ɗago kai Juda tayi tana kallon Berenice dake cin abinci tayi saurin fauce mata abinci tana mai daɗa kallon ta,abin da ya ba Berenice mamaki har ta kasa yin shiru sai da ta furta
   "Juda lafiyar ki kuwa da fauce min abinci"?cikin sauri Juda ta girgiza kai sai Berenice ta mata kallon ko da na ga alama sannan ta girgiza kai ta kuma ɗibar abincin zata kai baki ai kuwa Juda ta kuma fauce sa,a wannan karon a ɗan fusace ta kalle ta zata yi magana sai Juda ta riga ta ta hanyar ce mata
  "Ke ana ta kai kina ta ciki,,wa ya ce maki in ana tsaka mai wuya har wani kwanciya mr hankalin samin cin abinci ake"!!!ina kuma wannan ta dosa?tambayar da Berenice ta ma kan ta kenan cikin zuciyar ta sannan ta kalli Juda ta ce
  "Anya lafiyar ki kuwa Juda?wani tashin hankali kuma muke ciki yanzu"?cigaba da kallon ta Juda tayi kafin ta ce
  "Kin ce in aka kama ɓata gari aka yanka kawunan su aka kaiwa sarauniya Zinaida tana iya cika maka burin ka duk girman sa"?da mamaki Berenice ta gyaɗa mata kai sai ta matso da kan ta kusa da na Berenice tayi ƙasa da kai sannan ta ce
  "Matsalar mu ta zo ƙarshe Berenice"!!abin mamaki sai Berenice ta ce
"Kamar yaya"cikin yin ƙasa da murya tayi tambayar sai Juda ta bata amsa da
  "Ba sai mun saci jiki mun tafi gidan horo mun sato ɗan uwan ki ba,a sauƙaƙe zamu kamo ɓata garin mu aiwatar da abin da ta ce sai mu tara kawunan mu nufi masarautar da su ni zan shiga ciki da su sauran zancen,,ni na san yadda zan mata su ba sai na sanar da ke ba"tsit Berenice tayi hankali da tunanin ta ya gushe mata ta rasa ya aka yi Juda wasu lokutan bata da tunani mai ma'ana in ba haka ba ta yaya zata yi irin wannan wawan tunanin..
  Ja da baya tayi haɗe da ɗan ɗaga murya ta ce
  "Amma baki san abin da kike faɗa ba Juda"sai ta kawo hannun ta ta taɓa goshin Juda dan jin ko jikin ta ya canza launi ne sai dai ta ji ta daidai dan haka ta ce
  "Halan wa ya ce da ke sarauniya Zinaida shashasha ce da zata yardar maki?a jin ki ita sarauniya Zinaida bata da wayo ne da zata yardar maki?hmm bari ki ji shawarar mu ta fari shi zamu bi in ba haka ba sai dai a canza wata shawarar amma zancen a yi fito na fito bai taso ba"cikin jin mamakin Berenice Juda ta ce
  "Hey,kar fah ki manta,fitowa na yi dan cika buri na na bar gida na na bar mahaifiya ta da ta rage min duk duniya na shigo duniya sai na haɗu da ke sannan na ajiye nawa ƙudirin a gefe na yarda mu fara cika naki ƙudirin,ni na bada shawarar farkon sannan yanzu na kuma kawo wata shawarar da na san zai fiye mana sauƙi na kuma ce da ke ni na san yadda zamu ƙarasa a cikin fadar ba sai kin sani ba sannan ki kalle ni ki ce da ni shawara ta bai da ma'ana?me kike nufi"?shiru Berenice tayi tana ganin rashin dacewar kakaman da ta faɗawa Juda ganin ita kaɗai ce mai iya taimakon ta duk duniyar nan sannan ta baƙanta mata,..
   Saurin riƙo hannun ta tayi sannan ta ce
"Ki yi min afuwa Juda,tsoro ya gama dabaibaiye ni,bana son abin da zai taɓa wanda na yarda da shi a duniyar nan,daga yaya na sai ke,ku kaɗai gare ni a duniyar nan yanzu in na rasa ku ya zan yi,ina gudun azzalumanci irin na sarauniyar nan dan wayo ne da ita kamar wacce rayi rayuwa da mutanin zamanin ƙarnin farko"!!dariya maganar ta na ƙarshe ya ba Juda dan haka ta ɗan dara kafin ta ce
  "Babu abin da zai faru ni dai buri na ki yarda da ni bayan haka bana buƙatar komai daga gare ki"...gyaɗa kai Berenice tayi tana mai jinjinawa ƙarfin hali irin na Juda mace mai zuciyar maza..

Cigaba da cin abincin su suka yi har suka kammala sannan suka tashi suka nufi hanyar cikin gari suna tafe suna hira har suka bar kasuwar suka zo hanyar shiga cikin wani ƙauyen,duk hankalin su ya koma kan hirar da suke yi ta yadda zasu yi garkuwa da ɓata garin da zasu zame masu mabuɗin kwaɗon masarautar Mughal Empire...
  Basu ankara ba suka hango wasu mutani biyu na zaune saman kujerar da aka lulluɓe sa da kara fuskokin su rufe basu buɗe gabaɗaya ba sai Berenice ta ɗan dakatar da Juda tana mai nuna mata su,..
  Juyowa tayi ta zuba masu ido sai ta ga an miƙo masu wasu kofunan katako biyu suka karɓa suka tashi suka bar wurin,a yayin tafiyar nasu ne mayafin ɗaya ya faɗi ƙasa ai kuwa fuskar ta bayyana sai Berenice ta buɗo idanun ta waje tana mai ce da Juda
  "Wancan,,kin san ta"?kallon ta Juda tayi kafin ta ce
  "Ya za'a yi in san ta Berenice"cikin sauri ta ce
  "Gimbiya Ondrea,sunan ta kenan ɗiyar sarauniya Zinaida ce yarinyar da aka kame yaya na saboda ita,me ta fito yi a nan alhalin ko wajen masarautar nan bata taɓa fita ba tun da aka haife ta"!!abin sai ya ɗaurewa Juda kai ta ce
  "Kina nufin wannan ita ce gimbiyar da tayi sanadiyar yin garkuwa da yayan da sarauniya Zinaida ta yi"??gyaɗa mata kai Berenice tayi tana mai jin baƙin ciki da wani irin raɗaɗi na bin hanyoyin jinin jikin ta..
  Ko kafin Berenice ta sani Juda ta bar wurin sai duba ta ta shiga yi amma bata hango ta ba sai da ta yi da gaske sannan ta hango jelar rigar Juda da iska ya kaɗa,da sauri ta biyo bayan ta tana ƙwala mata kira..
  Ko da ta zo sai ta ga takobi riƙe hannun Juda ga gimbiya Ondrea riƙe a hannun ta yayin da shi kuma abokin tafiyar nata na tsaye riƙe da nasa takobin suna masu nunawa juna,gefe guda kuma gimbiya Ondrea kuka take yi kamar ran ta zai fita dan bata taɓa jin damƙa irin wannan ba sannan wacece wannan ɗin bata sani ba gashi tana nunawa masoyin ta takobi ita kuma ta kasa aiwatar da komai..
 
Zuwan Berenice wurin ya sa Juda ta gane amma bata juyo ta kalle ta ba haka itama Berenice ɗin bata ce da ita ƙala ba har sai da ta ji Judan ta furta wata kalma
  "Kika yunƙura da nufin ƙwace kan ki yanzu zaki tsinci kan ki a ƙasa gangar jikin ki a gefe dan haka ba wani abu mai wuya bane a gare ni dan haka ki natsu ki sanar da ni ina mahaifiyar ki ta kai _Balik_ ɗan uwan Berenice"?ta faɗi hakan tana mai juyo da takobin ta zuwa wuyar gimbiya Ondrea wanda hakan ya birkita Berenice da Cahal dake tsaye,hakan ya saka Berenice kiran sunan ta a firgice dan Berenice akwai tsoro ba kaɗan ba kuma ta lura in dai Juda ce toh yanzu zata fille ma gimbiya Ondrea kai saboda sam bata da imani..
  "Judaaaa"!!!juyowa tayi ta kalli Berenice ɗin sannan ta maida duban ta ga Cahal dake tsaye yana jiran ta juya ya shammace ta,murmushi tayi sannan ta ce
  "Ka tsaya a matsayar ka ba da kai nake yi ba dan haka ka daina yunƙurin shammata ta dan zan illata ka"ɗan yanka ta ma gefen wuyar gimbiya Ondrea sai ga jini ai kuwa take Berenice ta ƙaraso da gudu tana mai wurgar da hannun Juda daga wuyar gimbiya Ondrea a lokaci guda Cahal ya nuno mata takobin sa shima haɗe da zaro idanun sa waje sannan ya yaye mayafin da ya rufe fuskar sa da shi fuskar sa ta bayyana sai Juda ta kai hannun ta gefen rigar ta ta fiddo wata takobin,kafin a ce meye wannan tuni suka fara kawowa junan su hari yayin da Berenice kuma tayi garkuwa da gimbiya Ondrea ta kai ta jikin wata ginin ƙasa ta ɗaure mata mata hannu da ƙafa da yadin rigar ta da ta yanka sannan ta koma wurin su Juda dan raba yaƙin,ai kuwa tana zuwa ta ga wayam babu su babu dalilin su wannan abin ya ɗaure mata kai where would they possibly be....


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:56] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:25&26*

  Yaƙi ne sosai ya kaure tsakanin Juda da Cahal wanda ya saka su canza wurin damben suka koma ta bayan harabar da suka fara yaƙin,sosai suke dambacewa da takubban su kowa na nuna irin tasa bajintar da fasahar a ɓangaren yaƙi,shi bai gaji ba haka itama Juda bata nuna alamun gajiwa ba dan haka suka rinƙa yaƙar juna har sai da suka iso wata bishiya inda Juda ta kaɓar mai da takobin sa ta haɗa sa da bishiyar,.
  Tana haki ta shiga tambayar sa kamar zata doke sa dan haushi
"Ina Balik yayan Berenice?da wa kuke tare a kasuwar nan"?shima hakin yake yi sannan ya ce da ita
  "Ban sani ba kuma ba zaki taɓa samin amsar tambayar da kika min ba"murmushin gefen baki Juda tayi sai muryar Berenice ta karaɗe wurin tana faɗin
  "Muddin baka faɗa ba toh alhakin ran gimbiya Ondrea zai rataya a kan ka dan saura ƙiris in yanka ta,,sai ka zaɓa,ko ka bayyana inda yake ko a yanka gimbiya Ondrea sannan a ɗora alhakin kisar ta a kan ka,,wanne ka zaɓa"!??kallon Berenice yayi sannan ya kalli Juda dake riƙe da wuyar rigar sa ga takobin ta a wuyar sa sai ya juyar da kai ya shiga narrating masu ainihin abin da ya faru wanda yayi sanadiyar fitowar su har suka zo wannan ƙauye,..
  Ba ƙaramnin mamaki ne ya kama Juda ba sai dai bata nuna a fuskar ta ba dan kar a gane karayar da zuciyar ta tayi.
  Berenice kuwa ihu ta saka tana mai furta
"Shikenan,,,shikenan na rasa yaya na har abada,dama barazana na so yiwa sarauniya Zinaida da ɗiyar ta gimbiya Ondrea idan muka doshi masarautar nan sai dai hakan ba abu mai yiwuwa bane ya zan yi Juda"!!da kuka ta ida maganar wanda ya saka Juda jin ta daɗa karaya da lamarin sai dai faɗin wani,tashin wani dan haka ta daka mata tsawa tana faɗin
  "Kul,,kar in kuma jin haka daga gare ki,iya abin da nake buƙata daga gare ki shine natsuwar ki dan muddin babu natsuwa tattare da ke toh lallai komai namu zai ɓaci dan haka ki daina hawayen nan"...juyowa tayi ta tsurawa Cahal ido tana mai ƙare mai kallo kafin ta mai magana
  "Ka haɗa hannu da mu mu fiddo ɗan uwan Berenice dan kai ma ka sami gimbiyar ka in ko ka ƙi yarda toh yanzu zan iya fille mata kai ban da damuwa da wannan,wanne ka zaɓa"??kallon cikin idon ta yayi,ba dan kwana biyu da yayi babu practice ba da ya san tuni ya gama da shafin Juda dan abin nata na so ya shammace sa amma yanzu da take mai baraza dole ya haƙura da burin sa akan ta dan ceto masoyiyar sa tunda dama can bai da matsala da Balik duk sharrin sarauniya Zinaida ne ya sa ya kasa ceton sa a sa'ilon da ta saka a yi garkuwa da shi...

  Iska mai huci ta huro mai a fuskar sasannan ta ce
  "Amsar ka nake jira"!!kallon ta yayi kafin ya kai duban sa ga Berenice dake tsaye tana kallon abin dake faruwa tsakanin su su biyun..
  Amsa ya bata ta hanyar saka idanun sa cikin nata idanun dake cike da masifa haɗe da tsanar da take yiwa sarauniyar da bata taɓa sanin ta ba..
"Na yarda sai dai ki sani,kuskure ɗaya,,am out"!!ingiza sa tayi sannan ta juya baya tana mai ce da Berenice ta kwance gimbiya Ondrea,komawa Berenice tayi ta kwance ɗaurin da ta mata sannan ta riƙe ta a hannu suka yi nufin tafiya...
Hanyar masarautar suka nufa wanda dama ba wata nisa ne da ita ba daga kasuwar da suka baro zuwa garin,sai dai kasancewar dare ya tsala sai suka raba daren a daji suka kwanta dan yin bacci akan washegari sai su ƙarasa zuwa masarautar...

°°°°°°°°°°°°°°°°°
Cikin baccin ta ta rinƙa jin iska na hurawa fiye da ƙima dan haka ta daɗa haɗe jikin ta wu ɗaya tana naɗe hannuwar ta daga ƙirjin ta zuwa bayan ta haɗe da daɗa naɗe ƙafafun ta tana mai gyara kan ta,sai dai kamar daɗa ƙarfin sanyin ake yi dan haka ta buɗe idanun ta sai dai bata ga sauran cikin yanayin gajiya da sanyin da ake yi ba,hakan sai ya ɗaure mata kai dan haka sai ta shiga tashi a hankali tana mai cigaba da kallon wurin,.
  Wani abu da ta lura da shi shine,yanayin ƙarfin wutan dake kamawa ya canza,dan yin sama yake yi sai yayi ƙasa da sauri wanda a zahirin gaskiya ba haka ya kamata wutar ya rinƙa kamawa ba..
  Wuf ta miƙe tsaye haɗe da fidda takobin ta tana mai nufar wutar da shi sai ta ji kamar an gudu ta bayan ta dan haka da sauri ta juya,kuma jin iskar mutum tayi a bayan ta sai ta kuma juyawa sai dai babu kowa hakan ya hazuƙa ta dan haka ta natsu ta tsaya shiru..
  Wasu abubuwan take yi a zuciyar ta wanda ita kaɗai ta san ko menene wannan abin,kamar ƙiftawar ido ta sari mutum,wanda ƙarar sarewar nan tayi daidai da tashin sauran abokan tafiyar nata..
  Kowa tashi yayi haɗe da fiddo takobin sa yana mai tambayar ko lafiya,gimbiya Ondrea dake maƙale bayan Cahal tana toshe kunnuwar ta dan tsoron da ke ɗibar ta sai ta riƙo rigar Cahal tana mai faɗin
  "Masoyi na ka zo mu gudu,,ni ban yarda da wannan yarinyar ba,hala ita ta haɗa wannan tarkon dan ta kashe mu,ni dai ka zo mu gudu"!!sarai Juda na jin ta sai dai yanzu ba lokacin biyewa shirmen ta bane sai ta yi kamar bata ji abin da gimbiya Ondrea ta faɗi ba ta maida hankalin ta ga son kamo mai yunƙurin kawo mata farmaƙi...

"Me ya faru Juda?wa kika sara"?tambayar da Berenice ta mata kenan sai ta durƙusa ƙasa ta yaye mayafin fuskar wanda ta sarewa hannun,..
  Namiji ne wanda ba za'a kira sa da saurayi ba dan ya ɗan manyanta zai girmewa Cahal a shekaru..
  Maƙure masa wuya Juda tayi tana mai tambayar sa wanda ya aiko sa ai kuwa ya tsaya yi mata gardama ko kafin a sani tuni ta yanke mai kai...
   Ba Berenice ba hatta da Cahal dake jajirtaccen mayaƙi sai da ya ji zuciyar sa ta buga wata irin bugu da bai taɓa ji ba dan bai taɓa ganin kisa ido da ido haka ba kai tsaye sai dai shi yayi a yayin da yake gudanar da yaƙin sa,bayan wannan bai taɓa ganin irin wannan kisar gillar ba sai yanzu kuma wai mace ce tayi wannan kisar...
   Ita kuwa gimbiya Ondrea dake ɓoye bayan Cahal suma tayi da babu wanda ya sani sai da aka ji faɗin mutum ƙasa sannan aka maida duba ga bayan Cahal ɗin wanda a nan hankalin sa ya dawo jikin sa,tuni ya nufe ta yana mai jijjiga ta haɗe da kiran sunan ta yana ji kamar ya je ya shaƙe Juda sai dai yanzu ba ta nata yake ba ta masoyiyar sa yake dan haka ya maida hankalin sa gabaɗaya kan ta yana ta jijjiga ta..
  Wani irin kallon banza Juda ta aikawa Cahal da gimbiya Ondrea dake sume sannan ta yi wani abu mai kama da gugar zana(scoff)wanda ya sanar da su da su take yi sai Berenice ta kalle ta cikin kiɗimuwa tana ɓarin baki dan har yanzu bata saba da halayyar Juda ba,yadda take raban kan mutum da jikin sa,a duk sanda ta yi hakan sai ta tsinci kan ta cikin wani irin mawuyacin hali har ta rinƙa tunanin anya wannan mutum ce ko aljana dan bata da ɗigon imanin ɗan adam a jinin ta...

  "Let's get out of here"haka ta furta kalmar cikin jin haushin gimbiya Ondrea da ta sume saboda samin wuri shi kuwa Cahal kallon Berenice yayi yana faɗin
  "Ba zan iya cigaba da tafiya tare da ku ba dan an firgita min gimbiya ta wanda bata saba ganin hakan ba"wani tsawa da Juda ta daka mai ya saka sa maida idanun sa gare ta
  "Baka da buri a rayuwa ina gani,toh ni ina da shi dan haka ka tashi ka cicciɓe ta mu bar wurin nan tun kafin abin da zai fi ƙarfin mu ya same mu a nan"..
   Bin ta da ido su duka biyun suka yi kafin suka tash,shi Cahal ya rungume gimbiyar sa ita kuma Berenice ta koma bayan sa riƙe da ƙaramar wuƙar ta yayin da Juda ta ƙarasa fille kan ta cire ta riƙe a hannun ta suka fara tafiya..

★★★★★★★★
  Tun da suka fara tafiyar nan basu tsaya sun huta ba har gari ya gama wayewa tangaran,sai a lokacin gimbiya Ondrea ta dawo daidai dan a daren an yayyafa mata ruwa sama da sau huɗu in ta farka sai ta koma ta kuma sumewa da ƙyar Cahal ya haɗa kan sa dai aka cigaba da tafiyar har wayewar gari inda suka yada zango a wata ƙorama mai kyawun kallo...
  Ko da suka isa nan da zuwan su Juda tayi bayan dutsen ƙoramar ta cire kayan ta ta shige cikin ruwan rafin ta hau yin wanka har ta ji ta gamsu sannan ta fito ta canza suturar jikin ta ta saka wani,duk dai bata canza zani ba dan siffar iri ɗaya ce da sauran biyun da ta saka..
  Zama tayi a wurin ta buɗe jakar ta ta fiddo ganyen da mahaifiyar ta ta naɗe mata shi mai ƙunshe da abinci samfurin kayan lambu,warware igiyar tayi ta buɗe ta gan sa tsaf kamar bata shiga ruwa da shi ba,bai lalace ba sai ta kai bakin ta ta gatsa ta lumshe idanun ta tana taunawa,ba komai ke dawo mata ba sai fuskar mahaifiyar ta da halin da ta baro ta a ciki na rashin isasshiyar lafiya ga tsantsar tunani da kewar ɗiyar ta wato ƙanwar Juda da sojojin Ottoman suka ɗauke..
  Tuno abin da ya fito da ita ya sa ta miƙe tsam ta kwashi kayan ta a hannu ta shiga tafiya,bata ankara ba ta ji an harbo arrows har biyu...
  A halin da take ciki na ɓacin rai da alhini sai kawai ta juyo a harzuƙe ai kuwa sai suka yi ido cikin ido da mai harbo arrow ɗin.
Abin mamaki,budurwar rannan ce wato Agneta,wannan abin da ban mamaki yake,hala wannan budurwar mayya ce da take gani har hanjin mutum in ba haka ba ita da tun ranar da suka rabu bata kuma ganin kurwar ta ba amma sai gashi yau ta biyo ta har inda take,duba take yi ne ko kuma mai yi mata duban take yawo tare da shi da yake nuna mata hanyoyi..
  Tana tsaka da tunanin ta sai ta ji muryar Agneta na faɗin
  "We meet again Juda Artemas"!!tsantsar mamaki duk ya gama mamaye Juda dake tsaye jin Agneta ta kira sunan ta cikakken sunan ta ba iya nata kaɗai ba,wannan wace iriyar yarinya ce mai kama da jinnu..
  "Mamaki ko"??ɗago idanu Juda tayi daga kallon suturar jikin Agneta da take yi ta mai da cikin ƙwayar idanun ta sai ta gyaɗa mata kai dan haka ta ce
  "Don't be,ni ɗin ƴar baiwa ce ina haɗa ido da mutum toh komai nasa na gama sani sai dai shi zai yi wuya ya san ko ni ɗin wacece amma abin mamakin shine,,ke,kin yi min shigar wuri dan na sanar da ke sunana kai tsaye,ban san dalili ba kamar kina da wata ɓoyayyiyar sirri a tattare da ke da ke saka mutum yin abin da bai yi niyar yi ba sai ya gama ya dawo yana da ya sani"!!!cigaba da bin ta da ido Juda ta yi har ta kammala zantukar ta sannan ta murmusa kafin ta furta mata

Please Login or Register in order to submit comment