Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka cigaba da tafiya._
  _Aƙalla sun kwashi sati guda suna tafiya suna tsayawa akan hanya suna cin abinci sannan suka bar ƙasar su suka zo wata ƙasar nan kusa da tasu ƙasar wato BABYLON.._
  _A nan suka yada zango tun ba'a san su ba har aka san su har sarkin garin ya san da zaman su wanda babban ɗan Kiara wato Baadi Artemas yake aikin kula da tsaftar dawakan gidan wannan sarki,har da haka bai rasa maƙiya ba dan ganin sarkin ya janyo sa jiki yana a matsayin baƙo da ba'a wani san sa a garin ba amma sarki ya ɗauki yarda da aminci ya basa sai aka fara ƙulla mai sharri duk lokacin da zai fito daga wanke dawakan nan toh sai su tafi su ɓata jikin dawakan washegari sarki ya ji labari ya kirayi Artemas ya gargaɗe sa ya ba sarki haƙuri amma kamar lokacin aka fara abin kullum sai an mai haka tun sarki na gargaɗin sa har wata rana ya sa aka tsare mai Artemas dan ganin yayi kamar raina sa yayi,ranar mahaifiyar sa ta sha kuka har ta gaji ta ma sarki magiya akan sharri ake mai dan yana sanar da ita amma sarki ya share ta har dai Artemas ya ɗauki kwanaki bakwai a tsare wanda ƙannen sa suka zo ganin sa sau uku mahaifiyar sa kuwa sau ɗaya ta taɓa zuwa wanda ta ce bata kuma komawa sai sarki ya sakar mata ɗa._
  _A ranar da ya fito mahaifiyar sa ta ce bata yarda ya cigaba da aiki gidan sarkin ba ita zata rinƙa nemo masu abinci dama garin akwai albarkar kasuwanci zata cigaba da sana'ar ta har dai su sami mafita daga cikin wannan rayuwar da suka tsinci kan su amma sam Artemas ya ƙi ya ce zai cigaba da zuwa dan kar sarki ya ga kamar bai da biyayya,haka dai ta haƙura da sharaɗin muddin aka kuma yi mai sharri makamancin irin na farin  da aka mai toh sai dai ya haƙura amma ba zata kuma barin sa ya koma gidan da nufin aiki ba,ya amince ya cigaba da zuwa aikin sa lafiya ƙalau kamar bai da maƙiya sai kuma mahassadan suka ɓillo mai ta wani hanyar akwai wata rana da sarki ke da wasar doki na sarakai masu kuɗi daga ƙasashe daban daban sarki har alheri ya mai akan ya tabbatar ya wanke dokin nan sannan bayan an gama yi wa dokin ado ya kuma goge sa har zuwa lokacin da zai hau dokin._
  _Wannan alheri da sarki ya wa Artemas ya saka sa jin nishaɗi har yayi alƙawarin a nan zai kwana dan ya kare dokin sarki mahaifiyar sa bata so ba amma saboda shi kaɗai suka dogara da dan shine babba mai ɗaukar nauyin gidan kasancewar yanzu ya kai shekaru ashirin har da huɗu ƙannen sa ma duk sun girma toh sai ta bar shi yayi aikin kwanar,haka yayi aikin sa cikin yarda da aminci ya kwana a gidan har zuwa lokacin da sarki ya zo ya hau doki aka fara gasa dama a tsarin gasar wanda ya zo na ɗaya shine ƙwararre kuma shi zai rinƙa ɗaukar ragamar sauran sarakunan duk masarautar da ke nan kusa da ƙasar sa da kewaye kenan shi zai zamo a gaba sauran sarakunan zasu zamo a ƙarƙarshin ikon sa dan kowani shekara biyu ake gasar dan gwada jarumtar sarkuna toh dama wannan sarki ya kai shekaru takwas yana lashe gasar shi ke yin na farko a kowanne wanda a wannan karon ma yake fatar sake lashe gasar a masarautar sa,ba ƙaramar girma da daraja ake basa ba dan wasu daga cikin mutanin ƙasar har bauta mai suke yi dan ganin jarumtar sa ta daban ce babu wanda ya taɓa yin waɗannan shekaru akan wannan mulki sai shi toh ba ƙaramar shiri ya ma wannan gasar ba.._
  _Ana fara gasa ya kai zagaye na ɗaya,na biyu a na ƙarshen har zai kai gab da madakata kawai dokin ya ƙwace mai ya kasa saisaita dokin da haka ya faɗi ƙasa ya rasa wannan matsayi wanda hakan ya ma sauran sarakunan daidai suka ji daɗi daga haka aka yanke wanda ya zo na farko aka ɗora mai muƙamin zama sarkin da zai rinƙa mulkar sauran sarakunan nan da kewaye aka karɓi duk sauran abubuwan da ke hannun wannan sarki aka ba sabon sarki taro ya ƙare kowa ya koma gida da garin sa.._

  _Wannan rashin nasara an alaƙanta sa ne da sakacin mai kula da dokin sarki wato Artemas ai kuwa aka tsare sa aka rinƙa ba sa horo mai tsanani wanda ya saka Artemas cikin wani yanayi da har ya cire tsammanin zai rayu a doron ƙasa dan an azabtar da shi kamar za'a rasa sa da numfashin sa akan dole ya amince shi ya haddasa rashin nasarar sarki shi kuma ya rinƙa masu bayanin bai san haka ba bai san yadda aka yi aka haukatar da dokin sarki ba amma aka cigaba da azabtar da shi har sai da mahaifiyar sa Kiara da ƙaramar ƙanwar sa Daliyah wacce ta zama budurwa ya zuwa lokacin dan ta kai shekaru goma sha bakwai (17years)har sauraron samari ta fara yi da amincewar yayan ta,su suka tunkari gidan sarki suka rinƙa mai kuka akan a mai ragwami a sassauta mai wahalar da ake bashi dan sun san sa ba laifin sa bane ba zai taɓa aikata hakan ba amma sarki ya sa aka kora su ya ce a hana su zuwa gidan har sai an gama bincike.._

  _Wasa wasa sai da Artemas ya kai tsawon watanni shida a tsare kafin a kammala bincike aka gano waɗanda ke da saka hannu a manaƙisar da aka yi wanda ya hana sarki lashe gasar,ana gano gaskiya aka saki Artemas tare da ɗaure waɗannan bayin da suka yi aikin sarki ya zartar da hukuncin a kashe su kisar wulaƙanci.._
  _Kasancewar jahilci da son zuciya ta buwayi ƙasar da mutanin ƙarnin haka aka hallaka su aka ba Artemas haƙuri jar ma aka ƙara mai matsayi a masarautar dan amincin sa da nagartar sa wanda ya janyo mai so da aminci.._
  _Saboda ya zamo wani mai matsayi a masarautar sarki sai aka fara koya mai yaƙi da takobi dan gab yake da zamowa mai kare sarki da lafiyar sa kuma a iya zan sa bai taɓa sanin yadda ake riƙe takobi da nufin yaƙi ba sai a lokacin da aka fara koyar da shi ɗin..haka har ya ƙware kusan shekara guda aka ɗauka ana koyar da shi yaƙin nan kafin ya ƙware har aka fara fita yaƙi da shi na kare martabar ƙasar. _
  _Zuwa wannan lokaci ƙannen sa biyu Yahaira da Daliyah sun fidda mazajen aure kowacce kuma mazajen daga yankunan yamma suka fito cikin sojojin yaƙin masarautar wata masarauta dake nan kewaye kusa da masarautar Babylon,a tsarin yadda ake gudanar da al'adun ƙasar in za'a yi aure haka aka gudanar da za'a aurar da ƙannen Artemas dan an yi bushasha mai tsayawa cikin kundin tarihi kasancewar yayan amaren babban mai tsaron sarkin ƙasar Babylon ne gabaɗaya,an sha barasa an ci namomin dabbobi kamar bikin gidan ƴaƴan sarki an yi bushasha da mata a duhu an hole rayuwa kafin daga baya aka bada dawakai takwas biyu na amare huɗu na masu tsaron su daga nan Babylon har zuwa ƙasar da za'a kai su aure.._
_Ranar kamar kar su rabu da yayan su da mahaifiyar su wacce girma ya rigada ya fara zuwar mata zuwa lokacin,da yake masarautar gari ɗaya za'a kai su bambancin ƙauyuka ne kawai tsakanin su wanda ba wani mugun nisa ne tsakanin su ɗin ba..._

_Bayan kimanin watanni biyu da bikin ƙannen Artemas wata rana suna zaune suna fadanci saƙo ya iso fadar sarki akan sojijin kewayen Babylon na nan zuwa kawo farmaƙi ma masarautar ƙarƙashin jagorancin mai koyar da yaƙin ƙasar wanda oda ce daga sarkin masarautar,wannan abin ba ƙaramin ɗaga ma sarki hankali yayi ba tsoron sa ɗaya,kar a zo yaƙi a ɗauke ko a ƙwace mai abin da ba zai iya ganin ya rasa sa a rayuwar sa ba,ba wai ba zai iya cin yaƙin bane dan yana da mayaƙa fiye da tsammani amma tsoron sa ɗaya kar su zo yaƙin shi ya yaƙe su amma su sulale su ɗauke mai abin da ya daɗe yana killacewa yana raino yana karewa da ƙarfin sihirce sihircen sa.._
  _Haɗa kayayyakin yaƙi aka fara yi cikin mayaƙan har da Artemas dake kan gaba wun jagorantar yaƙin dan sarki ya gama yarda da shi ya bashi amana,ko da daren yayi an gama shirya masu jiran su ake yi sai aka ji su shiru,hankalin sarki ya kai ƙololuwa wun tashi dan ya fara tsoro kar a biyo ta bayan gida..._
_Suna nan suna kan jira sai kawai sarki ya kira Artemas ya roƙe sa ya kuma nemi alfarmar sa akan ya taimake sa ya taya sa killace wannan abin da ya daɗe yana killacewa dan ya duba ya ga sam babu wanda zai iya riƙe masa wannan ajiyar sama da shi dan amincin sa da nasabar sa..da fari ya yarda zai riƙe masa amanar dan bai san menene wannan amanar ba sai da ya nuna mai tilon ɗiyar sa ɗaya da ya daɗe yana ɓoyewa yana killace ta yana dakon miƙa ta ga wata lafiyayyiyar masarauta mai albarka na alfarma amma a yanzu sai ya ga in ba shi Artemas zai miƙawa ɗiyar nan nasa ba sam babu wanda zai riƙe ta da amana dan sarai ya san shirin masarautar da zasu zo masu yaƙin nan wato so suke su zo su yaƙe sa a ƙasar sa sannan su nuna masa iyakar sa ta hanyar ɗauke masa tilon ɗiyar sa a musayara yaƙin ko ya bada ɗiyar sa ga sarkin ƙasar shi kuma a bar sa da martabar sa da sarautar sa ko a ƙwace masa komai ciki har da ɗiyar tasa sannan a wulaƙanta sa,shi kuwa ba zai iya wannan abin ba a ganin sa gwara a raba sa da komai da a ce ya bada ɗiyar sa ga sarki a aura masa ita ya rinƙa muzanta mata yana cin zarafin ta yadda ran sa ya so..._
  _Wannan abin ya rikitar da Artemas dan yana da labarin babu wanda ya san yanayin kamannin fuskar ɗiyar sarki ko da kuwa muryar ta ne babu wanda zai shaidi hakan tsabar tsauri da tsantsar tsaron da sarki ya saka mata dan ko masu kula da ita haka suke kula da ita amma sam muryar ta ya haramta a gare su wanda ma ya jiyo muryar ta toh kashe sa ake yi dan a tarihin masarautar akan yi amfani da muryar gimbiya a cutar da ita toh da zarar wani ya ji muryar ta yana iya bada misalin sa sai a yi amfani da hakan a cutar da ita shi yasa duk wanda yaji muryar ta ake hallaka sa,sai gashi yanzu shi da iya zaman sa a ƙasar a kuma masarautar sama da shekaru goma sha biyu bai taɓa sanin ya kamannin ɗiyar sarki gimbiya yake ba abin da ya sani shine sunan ta sunan ma a bakin mahaifin ta ya ji sa wanda shima an sanar da shi ne dan kusancin sa da sarki amma bayan shi sam babu wanda ya san sunan gimbiyar masarautar Babylon bayan iyayen ta da shi Artemas ɗin..._
  _Roƙon sarki yayi akan ya rangwama mai shi bai kai matsayin riƙe mai wannan ɓoyayyiyar abin tasa ba matsayin sa yayi ƙasƙanci da yawa ba zai iya ba...,sai gashi sarkin na roƙon Artemas da tausayi haɗe da tsantsar rashin madafa da madogara wanda ya sandarar da Artemas ya amince akan zai karɓi alfarmar da aka nema daga gare sa..._
_A take sarki ya sa aka haɗa mai ƴar ƙanƙanuwar liyafa wanda daga shi sai ma'amintar sa da shi Artemas ɗin zasu halarci liyafar dan kuwa a daren ya haɗa aure tsakanin Artemas da gimbiya ɗiyar sa mai suna Hadara,mahaifiyar Hadara sai ta ga kamar an ƙasƙantar da ɗiyar ta ne ta hanuar bada ita ga bawa sai dai sarki ya nuna mata shi ya fi ta son ɗaukaka Hadara amma bai da yadda zai yi hakan ya faru ne a dole ya mata bayanin dalilin sa wanda ya saka ta ƙwacewa da kuka mai tsanani na tausayin ɗiyar ta gani take kamar Artemas sam ba zai iya kular mata da ɗiyar ta ba.._
  _A daren nan aka yi kaca kaca aka zubar da jini aka yanka mutani kamar dabbobi sannan aka shiga nemar sarki da ahalin sa amma ba'a same su ba dan tun bayan an ɗaura auren Artemas ya saka sarkin barin masarautar shi da matar sa sannan ya ce kar wanda ya biyo su su tafi can gidan iyayen sa su ce da mahaifiyar sa shi ya ce su zo dan kar ta tsaya tambayar su kasancewar ta matsoraciya sannan ya ce a kawo mai matar sa amaryar sa Hadara wanda a ranar ya fara haɗa ido da ita ya kuma mata kallon ban tsoro kasancewar a tsakiyar yaƙi da fargaba yake bai cikin hayyacin sa..._
  _Toh wannan tsarin aka bi sarki da matar sa Kirjath-Baal suka tsira sannan Artemas ya yaƙi mutanin nan ba tare da sun san gimbiyar masarautar bata nan a muhallin ta ba..,bayan an gama yaƙin sun tafi nemar gimbiya shi kuma ya goya matar sa a baya dan dama a ƙarƙashin dokin ta aka rufe ta cikin ɗakin dawakai da ya taɓa aiki a baya,,ta hanyar can baya bayan gidan masarautar ya bi da amaryar sa ya rinƙa raɓewa har ya dawo gidan su inda ya ga duk sun tsaya cirko cirko ana jiran sa..._
  _Kuka mahaifiyar sa ta saka akan sam ita bata yarda su cigaba da zama a nan ba dan ana iya biyo su a far masu,wannan shawara ta mahaifiyar Artemas tayi tasiri dan kuwa a daren suka bar gidan suka yanki daji suka bar yankin ƙasar Babylon a hanya ne mahaifiyar Hadara sarauniya Kirjath-Baal ta yanki jiki ta faɗi dan bata saba da wahala ba ko kafin su sani ta bar duniyar haka gimbiya na kuka kamar ta bi mahaifiyar ta shima sarki jikin sa duk yayi laƙwas a nan dai aka binne ta bisa ga al'adar sa ta masarautar sa sannan suka cigaba da tafiya har gari ya fara wayewa ita kuwa gimbiya na goye a bayan mijin ta Artemas in sun yi tafiya sun gaji sai su zauna su huta...._
  _A haka dai har suka bar ƙasar suka iso wata ƙasar inda a nan suka yada zango cikin daji,a hankali suka fara sabawa da rayuwar dajin har suka faɗaɗa mazaunin su wanda suka sami mazauni ɗai ɗai har uku da na sarki da na mahaifiyar Artemas sai na Artemas da gimbiya Hadara..._
  _Sannu a hankali aka wayi gari sai ga Hadara da ciki sosai suka yi murnar wannan abin dan sarki ya yarda da Artemas dan ya nuna mai ƙwazon sa da nemar na kan sa ya dage ya kafa sana'ar sa tamkar dai irin sana'ar mahaifin sa kuma da shi yake ɗauke ɗawainiyar iyalin sa gabaɗaya..._
  _Lokaci lokaci Hadara na raka sa zuwa wun sana'ar sa kafin ta yi nauyi dan bayan auren su ta same shi a mutum na uku wanda zata iya fallasawa zuciyar ta ta kuma yarda da shi ta bashi aminci saboda ya nuna mata kulawa matuƙa fiye da misalin ta dan yadda yake nuna mata kula da damuwar sa akan ta abin ya zarta tunanin kowa wannan yasa ta yarda da shi take jin bata iya zama da kowa a rayuwar ta sama da shi..._
  _Ana haka Hadara ta shiga watar haihuwar ta sai dai abin al'ajabi da ya faru da su shine mahaifiyar Artemas ta yanki jiki ta mutu ba tare da an san dalilin mutuwar ta,a ranar sun shiga ƙunci sosai dan suna da burin bata abin da zasu haifa ta cigaba da zama tare da ita tunda su kam fita yin kasuwanci suke yi ba zaman gidan suke yi ba,haka dai suka yi makokin ta har zuwa wani lokaci kafin su cigaba da sabgar su..._
  _A wannan zama da suka yi har lokacin Artemas bai san inda ƙannen sa suke ba iya abin da ya sani shine watan watarana dole zai fita neman su dan su kaɗai suka rage mai sai cikin dake jikin matar sa Hadara dan har lokacin yana mata kallon gimbiya ce ɗiyar sarkin sa ba wacce ta zamo nasa ba har abada dan ƙima da darajar ta da yake gani shi kan sa bai san dalilin da ya sa ya kasa yarda ita ɗin ta zamo nasa ba harda ma takan nuna mai sun zama ɗaya lokuta da dama.._

_A ranar da Hadara zata haihu ranar Artemas kasa taɓuka komai yayi dan tun cikin dare da ya tafi ya kirawo ungozama a nan kusa da inda yake kasuwancin sa ta zo ya kasa zama haka mahaifin Hadara sarki shima ya shiga damuwa ganin ɗiyar sa cikin wani irin yanayi gashi babu abin da zai iya aiwatarwa dan ƙarfin sa bai kai nan ba kusan kwana Hadara tayi tana naƙuda mai tsanani kafin washegari ta haifi ɗiyar ta mace wacce ta kasance fara tas saɓanin mahaifiyar ta da bata cika haske ba kenan mahaifin ta Artemas ta kwaso..._

_Wannan yarinya tun ranar da aka haife ta kakan ta sarki ya saka mata suna sannan ya ce kar wanda ya kira ta da wani suna akasin wannan sunan,su kam iyayen murmushi suka yi suka mai alƙawarin bin umarnin sa,da sunan ta suke kiran ta duk da da fari abin na masu nauyi kasanceear sunan na da girma da ƙima a tarihin rayuwar masarautar Babylon amma tunda mahaifin Hadara ya ce haka yake so a rinƙa kiran ta..._
  _JUDA shine sunan ta yarinya mai kazar kazar tun yarintar ta dan ko fita iyayen ta zasu yi tare suke barin ta da kakan ta sarki wanda ya zuwa lokacin ta gane sa sarai kuma in ba iyayen ta ko shi kakan ta ba sam bata yarda da kowa dan akwai ƙiwa bayan wannan rayuwa mai daɗi suke yi da ƴanci...._

*_IS SIYAIBRAHIM_*
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:7&8*

 
  _Rayuwar ƴanci da jin daɗi suke gudanarwa haka Juda ta fara wayo har ta kai shekaru uku iyayen ta na bata kulawa daidai gatan su basu hana mata komai duk nisa da tsananin abu muddin ta ce tana so haka zasu nemo mata shi,kakan ta sarki kam yana bata wata irin kula da kariya kamar yadda ya ba ɗiyar sa mahaifiyar Juda a shekarun baya da take ƙarƙashin ikon sa.._
  _Juda na da shekaru uku a duniya Hadara ta kuma samin wani cikin da ya zo ma ahalin da sabon yanayi dan tun da ta sami cikin nan babu daren da zai zo ya wuce ba tare da tayi mummunar mafarki game da abin da ke cikin ta ba abin nan na ɗaga mata hankali tun bata bari a sani har ta kasa riƙema kan ta ta sanar da mijin ta Artemas daga bisani suka sanar da mahaifin Hadara wato sarki._
  _Jin haka sai sarki yayi wata doguwar tafiya ya tafi dan nemo masu mafita wanda yayi dace dan an ba shi sihiri mai ƙarfi da zai kare abin da ke cikin Hadara duk da dai abin ba wai mai ɗorewa bane amma yin hakan shi ya fiye masu alkhairi dan kuskure guda ɗaya aka samu toh cikin nan na iya ɓarewa,.._
  _Shan magungunar sihire sihiren tayi sannan ta bi ƙa'idojin da aka ce ta rinƙa  bi toh da haka dai ta sami sauƙi sai dai fah tun sun iya ɓoyewa har watarana aka kawo masu farmaƙi da hari ɓakatatan daga masarautar Ottoman ƙarƙashin odar sarkin masarautar Ottoman wato Baal-Hamon dan ya daɗe yana biɗar wannan abin mamaki ya daɗe yana bibiyar rayuwar masu ɗauke da juna biyu dake ƙasar sa kaf amma sam bai sami abin da yake biɗar ba sai kawai watarana ya saka mallamin sihirin sa Aberald (The great Wizard)dake zaune nan cikin masarautar tun zamanin kakanni da kakannin sarkin dake kan mulki yanzu da haka,shi ya haɗa siddabarun sa ya bankaɗo ƙasar Babylon inda a nan aka san cewa abin da sarki Baal-Hamon ya daɗe yana yunwar samu yana nan a ƙasar kuma babu nisa dan haka ana iya samin abin ko ta halin yaya,toh ranar da aka kawowa ahalin Artemas wannan hari suna kan hanyar su ta zuwa kasuwancin su cikin babbar kasuwar ƙauyen kawai sai suka ga mutani fuskokin su rufe da baƙaƙen ƙyalle ko kafin su yi wata yunƙurin har sun riƙo hannun Hadara kafin Artemas yayi wani abin sun ɓace ɓat da ita aka neme ta aka rasa..._
  _A ranar cikin baƙin ciki suka ƙarasa ranar dan ko ta ko'ina an bincika ba'a same ta kaf ƙauyen nan babu Hadara babu labarin ta wannan abin ya ɗaga hankalin mahaifin ta sarki da ɗiyar ta Juda wacce take faman tambayar inda aka kai mata mamar ta ita a dawo mata da mamar ta,haka dai ta rinƙa ƙiriniya tana kuka har bacci ya ɗauke ta sai mahaifin ta ya saɓa ta a kafaɗa ya kama hanyar dajin da zai sada sa da hanyar kasuwar da aka ɗauke Hadara a nan ne ya shimfiɗa Juda a tsakar kasuwar ya rinƙa bin ta da wasu irin ruwa masu sanyi ƙalau haka ya zagaye ta tas sau huɗu yana yayyafa mata ruwan nan kuma bata farka ba sai ma jan numfashin da ta yi ta cigaba da baccin ta,ko da ya gama zagaye ta sai ya ja gefe ya tsaya kimanin sakanni sai wani irin hadarin hayaƙi ya fara tashi daga jikin ta hakan ya saka sa miƙewa tsaye da kyau yana mai ware idanun sa dan son ganin eh abin da mahaifiyar sa ta bar mai yana hawa kan hanya..._
  _A haka har hayaƙin ya ɗauke wurin ya washe kamar babu abin da ya faru a wurin sai ya cicciɓe ta ya tsaya tsaye ya rinƙa wasu waƙe waƙe(incantations)babu jimawa sai ya ga an ingizo Hadara daga inda babu tsammani sai ya janyo ta ya rungume ta yana kiran sunan ta,a rikice take sanar da shi abin da ta gani wanda hakan ya ɗaga mai hankali har suka dawo gida sannan ya sanar da sarki abin da ya faru wanda wannan shine dalilin sarki na kuma zuwa can kudu maso yamma ya kuma karɓo wasu siddabarun dan ya rantse maƙiyan sa ba zasu ga bayan sa ba dan dama tun shekarun baya akwai babbar al'amari tsakanin masarautar Ottoman da ta Babylon kuma a ganin sarki,ana so a yi amfani da cikin Hadara ne a rama duk wata ƙurar da ya ɗan lafa bayan ya tashi a shekarun bayan nan...._

  _Sai da cikin Hadara ya kai watanni takwas sannan suka daina samin farmaƙi suka fara yin rayuwar ƴanci kamar kowa dan har hana ta fita Artemas yayi yana zuwa kasuwancin sa shi da ɗiyar sa Juda haka bai yi ƙasa a gwiwa ba wun koyar da ita yadda zata sarrafa takobi da wuƙaƙe dan fansa ne mai mugu mugun yawa zata ɗaukar masu daga ɓangaren sa shi mahaifin ta da ɓangaren mahaifiyar ta da duk ya fi ɗaukar babbar kaso dan kasancewar ta daga gidan sarauta ta fito masu harin ta ita da mahaifin ta kakan Juda yawa ne da su dan haka ko a kasuwar ana iya shedar ta da wannan ɗani'a dan ko shi mahaifin nata bai da niyar koyar da ita takan tasa sa gaba saboda abin ya dawo ya zame mata kamar ɗaukar darasi ne dan fah bata da abokanan wasa kaf ƙauyen nan tana nata ne iya abin da ke haɗa ta da mutani shine sayar da abu in aka zo siya a rumfar su dan sun zamo manya masu sayar da abunuwa daban daban kamar dai dangin busassun kurkur,tafarnuwa,cinnamon,curry,busassun tufa,pumpkin da dai sauran kayan lambu da itatuwa da ba kasafai ƴan ƙasashen ƙetare da ƙasar Babylon ke samu a nasu ƙasar ba.._
  _Cigaba ne wannan sanayyar da aka ma Artemas da ahalin shi sai dai har lokacin babu wanda ya

Please Login or Register in order to submit comment