Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barin ɗumbin abin mamaki a masarautar Sultan...

★★★★

Duk wani shiri da ya zammana dole an yi sa an tara jami'an tsaro haka zalika an tara masu kwasar rahoto da ɗumi ɗumin sa,duk wasu masu kare haƙƙin ɗan adam sun haɗu kama daga human right archivist da women,children and society advocators..
Gefe guda kuma,ayarin su Cahal ne da abokan sa(su Juda da abokan tafiyar ta)..
Matuƙa Cahal ya so a ce gimbiya Ondrea ta haihu kafin su bar wannan ƙasa,sai dai abin ya ci tura,haihuwar bata zo mata ba,a haka a wannan rana suma suka tattara ya nasu ya nasu suka bar ƙasar Turkey suka nufi hanyar ƙasar Ottoman dan aiwatar da binciken su da gano gaskiyar lamarin..
Motoci ne manya na kwasar kaya daga ƙasa zuwa ƙasa,suka cike ta tam suka nufi hanya da addu'ar samin nasara..
Duk da Juda na murnar ganin abu ya zo ƙarshe,a wani fanni na zuciyar ta tana jin kamar ko komai ya lafa,toh da wuya ƙanwar ta na raye cikin ƙoshin lafiya...

★★★
Sharewar kwanaki kafin su iso wannan yanki na ƙasar Sultan Baal-Hamon wanda yayi daidai da zuwar su yarima Ziyan Aman dan suma kam bayan wucewar su shi da iyayen sa,ya ɗau kwanaki sannan ya haɗa nasa ayarin suka taho wannan ƙasa duk dan a tona asirin wannan azzalumi mai ɗaukar doka a hannun sa..
Da albarkar iyayen sa ya baro ƙasar sa dan a nasa ƙasar komai yayi daidai kuma alhamdulilah sun karɓi addinin da hannu bibbiyu kuma suna kiyaye duk wani abin ƙi da addinin ya haramta..
A yayin da suka haɗa gungun su,a masarautar Mughal ta sarauniya Zinaida ma an gama haɗa mata tarko kuma ta faɗa kasancewar ta mace mai tsananin son maza kamar ran ta sai kawai abokin yarima Ziyan dake nan ya rinƙa ruɗin ta amma fah bai yarda wani alaƙa ta shiga tsakanin su ba dan bai yarda ya bayar da kan sa ba ganin ya zo ne dan ida nufin sa na kawo ta ƙasa,toh dama tun fari da sigar mai faɗakarwa ya zo sannan yayi amfani da kyawun sa ya ruɗe ta har ta amince ya rinƙa yaɗa addinin da ta ce ta tsana ta ƙi jini a rayuwar ta,da haka ne fah har suka saba ya zamana har tana ji kamar zata aure sa sai dai bata bayyana masa ba tana jiran ta aiwatar da ƙudirin ta tukunna..

Duk tare suka haɗa plan ɗin su akan su haɗu su kawo ƙarshen jahilci da azzalumanci da waɗannan sarakai ke yi a yankunan su na sarauta,hatta da wanda ke aiki a masarautar Jordan duk sun tanadi rahoto mai zafi da zasu iya defending kawunan su da al'umar dake cikin azabar mutanin nan..
Abin dai yayi daɗi dan kamar rigimar da ya daɗe yana tashi yana kwanciya bayan wasu shekaru ya kuma tashi toh zai zo ƙarshe dan youth are ready to fight the old folks da aƙidar su sannan su kafa tarihi mai wuyar mantuwa..
Ana haka ne saƙo ya iso masarautar sarauniya Zinaida akan ga fah abin da ya faru a ranar da aka yi taron baikon ɗiyar sa da yarima Ziyan wato ɗan aminin sa sarki Malik..
Ranar da ta ji wannan saƙo ba ƙaramin daɗi ta ji ba kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha,haka ta rinƙa ji,a ranar murnar ta ta kasa ɓoyuwa a fili ta nuna sa..
Ganin haka sai ta rinƙa baza mulkin ta fiye da yadda take yi a da a baya sai abin ya girmama jin daɗi kamar yau ta fara samin labari mai daɗi a rayuwar ta..
Duk da gefe guda,takan yi tunani akan ɗiyar ta ta kusa dawo mata amma ta san in har ta dawo toh da wuya in zata iya zuba mata ido ta kalle ta ba tare da ta yi abin da ta daɗe tana mararin son yi ba..
Shi kuwa matsafin ta mai yi mata duba ya daɗe da sanin cewa kashin su ya kusa bushewa dan ana faɗin mai laya ya kiyayi mai zamani kuma wannan lokacin ya rigada ya zo kawai jira yake ranar ta zo dan haka ya rinƙa shirya kan sa dan tsera da mutuncin sa domin kuwa ya san ya kauce hanya sai dai bai yi zaton nan kusa sakayyar zai dawo masa ba ya zata sai a wata rayuwar dan haka ya rinƙa tanadar gamsasshiyar amsoshi ga tambayoyin sarauniya Zinaida..
A yayin da duniya ta zamowa sarauniya Zinaida sabuwa haka duniyar ta ma Sultan baƙi ƙirin dan har wata rashin lafiya yayi na tsawon sati ɗaya baya sanin wadanda ke kan sa haka Dacey ta rinƙa tsoro da fargaba tana shakkar rasa sa dan shi kaɗai ne gatan ta haka shi kaɗai yake iya daukar jinginar ta dan bayan shi bata da kowa,dama rashin mutuncin da take yi a masarautar ya sa bata da farin jini a wun kowa sai dai a wun shi,shi da take zaman sa kuma gasho yanzu kamar barin duniyar zai yi..
Ba komai ya haddasa mai wannan rashin lafiya mai zafi da barazanar ba face tsoron rasa mulkin sa da zai yi sannan ga tozarci da zai fuskanta dan har ya fara fuskanta already daga wun sarauniya Zinaida da yarima Ziyan Aman..
Matar sa haka hankalin ta ya tashi sosai dan ita dai Allah ya kuɓutar da ita ta tserata daga wannan fitinar zaman rashin sanin addini da bautawa ubangijin,a haka a kullum take salloli tana mai addu'ar samin lafiya dan bata cire ran zai sami rabo ba duk da ta san irin mugun halayyar da yayi a baya dan ya bar baya da ƙura amma bata cire tsammanin zai sami rahamar ubangiji..
A fannin ɗiyar sa gimbiya Acenath kuwa abin ba sauƙi dan tun barin yarima Ziyan ta sakawa kan ta damuwa tun gimbiya Adriel na rarrashin ta da lallamin ta har abin ya fusata ta ta fita harkar ta ta wuce masarautar su dan ita kan ta ta fara gane cewa iyayen nasu na gudanar da gurɓataccen aƙida marar ɓillewa...
Ko da ta koma masarautar su sai ta ga canje canje da ta nemi sanin dalili sai ta ji wai ai masarautar ce ke gudanar da addinin da Sultan ya hana su gudanarwa, min nutshell da tayi viewing abin a perspective sai ta gano ashe dai Sultan ne kaɗai ke aiwatar da wannan aƙidar gargajiyar dan ta sami labarin cewa masarautar Mughal ma ana nan ana yin wannan aƙida kuma ta gano sirrin da ya sa sarauniya Zinaida yarda a aiwatar da wannan addini haka ma ta sami labarin a ƙasar Cyprus ana nan ana yin addinin duk da ba gabaɗayan su ba dan wasu sun yi imani da Sultan Baal-Hamon kuma suna ganin shine zai masu komai amma ba ubangijin da ya halicce su ha,hakan ba ƙaramin ɓata ran abokin yarima Ziyan yayi ba da yake aiki a ƙasar kuma shi kan sa ya rantse sai ya ga bayan wannan banzar aƙida da Sultan ya dasa sa..
Though an gama yi masu tarko,karaf suke jira su kama Sultan Baal-Hamon dan shi kaɗai ne zai warware ɓakin believe da ya saka a rayukan ɗumbin al'uma da suka yarda da shi ɗari bisa ɗari...

★★★★
A yau da su Juda suka diro masarautar Ottoman a yau ɗin ne kuma su yarima Ziyan Aman suka iso su ma da nasu tarkon,toh da gimbiya Acenath ta ji hakan sai tayi tunanin hala wun ta ya zo ko ya dawo ne ya gyara alaƙar sa da ita dan ya aure ta sai dai jin wai ba shi kaɗai ya zo ba har da wasu gungun jama'a sai ta ji hankalin ta ya tashi duk ta ji tsoro ya shige ta..
Cikin saurin ta ta nufi sashen mahaifin ta da yanzu ya dan fara samin lafiya har yake iya yin magana a gane,.
Da zuwan ta ta zauna kusa da shi tana mayar mai da zance cikin tsanani firgici da kuka da ya saka mahaifin nata gane cewa eh fah lallai ɗiyar sa ta gama kamuwa da so da ƙaunar yarima Ziyan ya gama mata mugun kamu shi kuma bai so hakan ba amma ya zai yi,dik da ya san wani kalar tozarci shi yariman ya zo mai da shi amma dole ya karɓe sa dan bai sani ba hala ya yarda ya karɓi soyayyar ɗiyar tasa a ƙarshen raahin mutuncin nasa..
Rarrashin ta yayi akan ta kwantar da hankalin ta zai aura mata yarima Ziyan Aman..
Ita kan ta ta san faɗi yake dan ta ga yadda yarima Ziyan ya mai rashin kunya kuma ya kasa aiwatar da komai toh yanzu ne zai ce yana iya yin wani abin,sai dai ta san ba zai iya cigaba da ganin ta cikin halin damuwa ba dan haka ta saka hope ɗin ta akan sa si dai still ta nufi mahaifiyar ta da zancen kuma haka sarauniya Bayarma ta mata alƙawarin akan zata tsaya mata dan ta sami abin da take so..
Tsugune ne bai ƙare ba ganin kashi kashi na mutani har biyar a masarautar Sultan,abin da ya ba mutanin masarautar mamaki kenan kuma wai duk zuwar ta Sultan Baal-Hamon ne,matuƙa mai dubar sa wato Aberald,ya girgiza dan kuwa babu wani sassauci a tare da mutanin,duk da ya gane yarima Ziyan amma bai san dalilin da ya sa yayi masu irin wannan dirar miƙiyar ba sannan ga wasu mutanin daban duk wai wun Sultan Baal-Hamon suka zo,lallai yau dubun su ya cika dan mai hana su hukunta Sultan da masarautar sa sai dai wani nufin dan da ganin mutanin ka ga mutanin da suka fito daga wurare daban daban haka zaka iya gano _Bambancin kasashen_ da suka fito dan kuwa siffar su daban daban take kuma a hakan ma wai su yarima Ziyan basu san da zaman su Juda ba dan haka kowa dai facing abin da ya kawo sa yayi duk dai a ga ƙarshen aƙida da al'adar gargajiyar da Sultan ke yi da kuma mutanin da ya ɓatar ya shagalar akan wannan dabi'a ta sa..
Calva dai wannan rana ta zame mata rana mafi alkhairi da bigewa dan ta san ko ta ko ina ta gama cinna ma Sultan Baal-Hamon wutar gasa kan sa kuma ta san a yau ba a gobe ba sai an ruguza sa,da iya wannan kaɗai ta san zata sami sukunin da ta daɗe bata samu ba..
Ziyartar wannan bursinar tayi ta sa aka tado mata wannan yarinyar ta saka aka mata wanka aka gyara ta sannan ta sa aka fito da ita zuwa sashen bayi,..
A zuciyar ta ta ƙudiri abin yi da wannan yarinya dan ta daɗe tana saƙawa a ran ta akan yau kam dubun Sultan Baal-Hamon ya cika kuma sai ta taya Irad durƙusar da Sultan kamar yadda ya halaka mata ahali ya durƙusar mata da kasuwancin ta da mahaifin ta ya daɗe da wuya da azaba yana tarawa duk dan su more sa amma Sultan ya bata mata komai ya wulaƙanta mata iyaye..toh yau kuwa tana son ganin bayan sa ido da ido kuma ta shirya mai,ƙiris ya rage ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan ta ga mutani da yawa na nan na fakon sa dan ga su sun taho kuma tsaf zata haɗa kai da su su danƙwafar da Sultan.....



*_SIYAIBRAHIM_*
[3/30, 14:19] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:63&64*
  Sanar da Sultan Baal-Hamon aka yi akan ga fah baƙi sun zo kuma ga abin da ya kawo su,sai da ƙirjin sa ya buga dan dama ya san haka kawai yarima Ziyan ba zai kawo mai ziyarar wofi ba toh shi kam ya ya san zai yi da ɗan zamani,..
  Ya dai yi alƙawari akan duk runtse ba zai yarda ya rasa mulki da ikon sa ba sai dai su ƙaraci rigimar su su tafi..
  Da wannan tunani ya lallaɓa ya fito falon sa n karɓar baƙi ya hakimce bisa kujerar mulkin sa yana mai bada izinin a taho masa da baƙin..
  Jim kaɗan sai ga su yarima Ziyan sun shigo,fuskar yarima Ziyan kaɗai da ya kalle sai da ya ji gaban sa ya faɗi,bai san dalili ba amma yana ji a jikin sa babu alkhairi a wannan ziyarar..
  Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da su Juda suka shigo da nasu jama'ar sannan ya gane kamar fah ƙullaliya aka mai,amma ya dai dake yana jiran jin ko da me suke tafe..

  Bayan zaman su ne haɗe da ƴan jaridun da suka zo tare,Sultan ya sa aka kawo masu kayan motsa baki haɗe da abubuwan kore ƙishi..
  Da yake dai su ba wannan ya kawo su ba,sai basu tsaya taɓa abin ba suka mai bayanin abin dake tafe da su kamar haka
  "Sultan ba tare da mun ɓatawa kan mu lokaci ba ko mun ɓata maka naka lokacin ba,abu ne mai muhimmanci ke tafe da mu kuma kamar yadda idanunwar ka suka gani,jama'ane da suka ga ya kamata su shiga wannan abubuwa da ake tuhumar ka da shi,kuma ana so cikin daɗin rai a yi komai a gama ba tare da an yi hayaniya ba,amma in ka ƙi ka ɗaga mana murya,toh fah Sultan ka sani,wannan hukuma ce mai zaman kan ta da zata iya hukunta ka yadda ta so kuma daidai laifin ka,dan haka ka bamu haɗin kai mu yi abin nan cikin jin daɗi mu rabu lafiya dan ba zuwa muka yi da nufin kwana a masarautar ka ba"..wannan jawabi ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin media and press members da yarima Ziyan ya zo da su.
  Tun da ya fara jawabin sa Sultan Baal-Hamon ya rinƙa kallon sa ganin ƙeƙe da ƙeƙe fah so ake a mai ɗibar albarka a masarautar sa,toh amma kuma ya rarrashi zuciyar sa akan ya ƙara haƙuri har ya gama ganin iya gudun ruwan su..
  Amsa su yayi cikin gadara da hucin zazzaɓi da ya taso sa gaba
  "Ina sauraron ku,da me kuke tafe"?abin ya ɗan ba yarima Ziyan dariya ganin rashin kunyar sa a fili haka,madaɗin yayi laƙwas amma sai ya rinƙa wani cin magani shi a dole sarki kuma mai burin mallakar duniya...

  Ko kafin ɗaya daga cikin press members da yarima Ziyan ya zo da su yayi magan,tuni yarima Ziyan ɗin ya riga su yin maganar ta hanyar ce da Sultan
  "Amma Sultan ai ka san ba mu kaɗai bane a nan ɗin,ga wasu nan da suka zo kuma alama ya nuna,tattare suke da zantuka da in bata zo daidai da tamu ba,toh ba zai rasa nasaba da tuhumar ka ba,baka son sanin ko da me suka zo ne"?wannan tambaya a wun Sultan Baal-Hamon daidai yake da irin tambayar rainin wayon nan da rainin hankali haɗe da rashin kunya,sai dai bai ce ƙala ba ya fuskanci su Cahal da ya mai kamar ya taɓa sanin sa a wani wuri sai dai ba zai iya cewa ga takamammen inda ya san sa ba..
  Kallon sa shima Cahal yayi yana baƙin cikin abin da ya mai ya kuma yi wa iyayen sa,dan kuwa Sultan ya zamo azzalumin sarki da bai da tausayi bai da imani dan yawan mutanin da ya raba da ahalain su bai ƙirguwa..
"Sultan abu ɗaya ya kawo mu,mu da waɗannan mutani kuma justice,shi muke nema daga gare ka da sauran al'umar dake sauraro da kallon mu a wannan wuri,ba zuwa muka yi dan yin kace na ce ba,kai tsaye zaka amsa mana tuhumar mu"!!mamaki ne ya gama sandarar da Sultan a wurin ganin shi ne fah mai yanke hukunci mai yin isa da nuna isa a yadda ya so amma yau waɗansu ne suka shigo mai yanki har da nuna mai basu buƙatar ɓacin lokaci dan a uzurce suke..
  Lallai yayi sake ɗan zaki ya girma a gaban sa sai dai in sun san wata,ai basu san wata ba...

  Jinjina kai yayi cikin takaicin ama mai rashin mutuncin gaban al'umar sa,ga ɗiyar sa da ta kasa samin matsuwa ta kasa ta tsare ita dai burin ta ta sami yarima Ziyan ko zata ji sanyi.
  Fanni guda kuma,gimbiya Ondrea ce zaune ta ɗan jingina da jikin mijin ta jin kamar zazzaɓi na nemar rufe ta,ga su Juda da tun da suka shigo,babu uhm bare uhmuhm,shiru suka yi tunowa da irin darun da suka sha a baya a lokacin da suka ci burin shigar masarautar sai dai duk hakan bai yiwu ba sannan da yake lokacin shigar nasu bai kai ba,haka suka shiga ba tare da sun tsinto komai ba suka fito,ashe jinkirin alkhairi ne a gare su dan gashi sun shiga wata duniyar wacce take daban da sauran duniyar da suka fito kuma basu yin da na sanin tafiya wannan duniyar dan gashi sun sami abokan taimakon su kuma sun gano ashe ba su kaɗai bane ke farautar Sultan Baal-Hamon ba ga sauran al'uma da dama dake farautar sa,su kam nasu buƙatar bai wuce ya fito ma Juda da ƙanwar ta ba sannan ya ga sakamakon mugayen halayyar sa da ya daɗe yana yi...

  Kallon Agneta Callee tayi tana ɗan taɓa ta haɗe da faɗin
  "Kina ganin Sultan ɗin nan zai mana yadda muke so kuwa,ko sai an haɗa mai da na ƙarfi ne"?take Berenice ta juyo a yayin da Balik ma ya juyo suka kalli Callee dan gasganta maganar da ta faɗi,sai kuwa suka ga ta kuma maimaita maganar..
  Fianna ce ta ɗan girgiza kai tana riƙo hannun Callee ta ce
  "Ki kwantar da hankalin ki ƙanwar mu,ba sai an haɗa mai da ƙarfi ba dan wannan zamanin ya wuce kuma duk nan ai kin ga masu kare haƙƙin al'uma nan da ba sai mun gwada wani irin abnormal attitude ba kin gane"?gyaɗa kai Callee tayi tana mai da duban ta ga Sultan Baal-Hamon dake zaune yana baza mulki kamar ba mai laifi ba..
  Ganin kamar ƙarfin tuhumar su Cahal ya fi na su yarima Ziyan sai yarima Ziyan ya bada umarnin su Cahal su fara nasu tuhumar kafin su suyi nasu..
  Ba tare da ɓata lokaci ba Cahal ya ma ɗan jaridar alama da ya fara watso tambayoyin sa..
  Cikin kwantar da murya da son samin masalaha ya fara aiko mai da tambayoyi kamar haka
  "Sultan,ni sunana Qarib Theodor ni kuma ɗaya ne daga cikin manyan ƴan jaridu masu kare rajin ɗan adam da basu haƙƙokin su,ni da abokan aiki na mun zo ne dan tuhumar ka akan wasu abubuwan da suka faru a lokuta masu dama da kuma abin da ka aiwatar da bai dace ba,cikin mutuntaka da sauƙin lamari muke fatar ka haɗa kai da mu mu yi binciken nan cikin kwanciyar hankali"!!kallon sa Sultan yayi a tankaɗe kafin ya sauke ajiyar zuciya..
  "Sultan Baal-Hamon,an daɗe ana zargin ka da aikata laifi,ba ma laifi kaɗai ba,laifuka da dama tun bayan hawan ka kan mulki sama da shekaru talatin,babu abin alheri dake gudana a masarautar ka sama da zalunci da son duniya haɗe da son zuciya da kake amfani da su wun tafiyantar da mulkin ka,toh yanzu abin da muke son sani shine,shin kana iya sanar da mu yawan rayukan da ka hallaka duk ta sanadiyar son cigaba da gudanar da mulkin ka"?wannan tambayar sai da ya fusata Sultan Baal-Hamon...  
  Cikin ɓacin rai Sultan ya kalli Qarib yana faɗin
  "Ni kake wa wannan tambayar rainin hankalin da rashin kunyar"?wani kallon mamaki Qarib ya bi sa da shi kafin ya amsa mai da
  "Eh,da kai nake yi Sultan"?girgiza kai Sultan yayi cikin jimami yana ta kaɗa kai dan ganin kamar total disrespect ne wannan amma da yake shima yana da tanadin da ya masu sai ya ce
  "Ban sani ba,dan wannan ba hurumin ka bane"!!gyaɗa kai duk suka yi ganin Sultan zai yi ja da su kawai sai Qarib ya ce
  "Kenan wannan wani abu ne dake a ɓoye kuma baka shirya bayyana sa nan kusa ba sai bayan ka sami duniyar da ka ce kana son samu"!!wani ras gaban Sultan ya bayar kafin ya ce
  "Kana min cin fuska kuma ba zan iya ɗauka ba dan haka bana son jin komai daga gare zan saka a hukunta min kai daidai laifin ka"!!wannan furuci ya matuƙar gjrgiza al'umar wannan wuri ganin abin da suka ji ya zamo gaskiya..
  Qarib bai wani damu ba ya jefo mai wata tambayar
  "Ko kana iya sanar da mu yawan adadin mutanin da kayi garkuwa da su ka saka a bursinar ka"?ɗagowa yayi ya kalle sa yana zazzaro idanun sa waje dan kuwa babu wanda ya san da zaman wannan labari sai shi da ahalin sa da kuma masu gadin bursinar..
Ɗan hayaniya ne ya fara kaurewa a fadar sai daga bisani Sultan Baal-Hamon ya ce
  "Wa ya ce da ku hakan"?abin dariya abin haushi sai kawai Qarib ya ce
  "Ba matsala bane wannan dan ka ga muna tare da masu kare rajin al'uma,muna da masu hukunta masu laifi,bamu zo kai tsaye masarautar ka ba,sai da muka yi bincike mai zurfi game da kai da kuma masarautar ka dan haka ka ga ba sai mun tsaya yi maka bayani ba manufar mu kawai,ka amsa wannan tambaya"zufa ce ta fara ketowa Sultan dan ya ga abin da bai yi zato ba..
  Kasa amsa masu yayi sai ya ce
  "Ku kame min wannan mutumi,yana son ci min zarafi yana wulaƙanta ni"!!tsit ya ga wurin babu wanda ya tashi sai ya zama wani iri yana kalle kalle ganin babu wanda ya motsa..
  Ƙara ɗage murya yayi yana faɗin
  "Shin baku jin abin da nake faɗi ne"??sai ya ga masu tsaron suka yi ƙasa da kawunan su sai abin ya fara ba shi tsoro..
  Kallon sa Qarib yayi da murmushi a fuskar yana faɗin
  "Ka gani ko Sultan!!babu wanda yayi saura a mabiyan ka dan kowa ya san gaskiya kuma kowa ya san abin da kake yi marar tsari kuma basu tare da kai Sultan dan haka ka amsa mana tambayoyin mu mu yi abin da zai yiwu"!!

  Cahal ne ya dubi Sultan cikin ɓacin rai ya ce
  "Sultan Baal-Hamon ka amsa mana tambayoyin mu tun kafin rai na ya ɓaci dan yanzu dai ka sani ba wani daraja da ya saura gare ka,babu wani mai zaman karƙashin ka a yanzu kowa ya san gaskiya dama kallon ka ake dan haka ka amsa mu"!!ran Cahal ya matuƙar ɓaci sai dai bai ce komai ba bayan wannan furuci da yayi..
  Abin mamaki duk sauran jama'ar wurin sai da suka yi mamakin Cahal ganin irin zafin rai imda yake da shi sannan ga yanayin yadda yake maganar kamar dai ba zai yi hakan ba..
  Kallon sa Sultan yayi cikin mamaki sai ya kasa ce da shi komai haka bai amsa tambayar ba sai da abin ya harzuƙa Callee ta miƙe tsaye,ko kafin a sani har ta diro gaban sa da takobin da ba'a san daga ina ta same sa ba..
  Tsoro ne ya kama mutanin wurin har shi kan sa yarima Ziyan da bai san ashe su Juda suma sun iya yin wannan abin..
  Takobin ne ta saka daidai wuyar Sultan dan dama ita haushin sa take ji tuntuni wannan tambayoyi gani take kamar ana ɓata mata lokaci..
  Cikin zafin rai ta ce
  "Sultan..,ka shiga hankalin ka tun kafin rai na ya ɓaci,ni na gaji ba zan cigaba da sauraron wannan shirme ba,ni da kai na zan ɗau mataki kuma kar wanda ya zo kusa da ni"..
Tsoro ne ya shigi su yarima Ziyan da ya ga abin mamaki dan bai san za'a iya samin wani makami mai lahani ga mutum ba a wun su sai ga wata da takobi

Please Login or Register in order to submit comment