Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wacce ke son fiddo wasu kurakurai akan fuskokin su,lokaci ta ɗauka tana ƙare masu kallo kafin daga bisani ta yi gyaran murya,a lokaci ɗaya suka ɗago suna mai kallon ta suna jiran jin me zata furta masu..
  Magana ta fara yi cikin isa akan a kawo ƙarar farko wanda ya kasance ƙara ne akan wani miji dake baɗala da matar wani yana barin matar sa a gida sannan ya hana ta ƴancin ta na fita zuwa yin kasuwancin ta da ta saba,toh ita kuwa wannan sarauniya mai amsa sunar sarki a ƙa'idar ta in har namiji na iya yin baɗala da wasu matan a waje toh hukuncin sa ɗaya ne cikin biyun imma ya dawo gidan sa ya gyara gudan sa da zamantakewar sa da matar sa ko kuma itama a bata ƴancin sheƙe ayar ta da wasu mazajen,..
  A nasa laifin kuwa ya rasa damar sa ta fari wato damar ya koma ya gyara gidan sa dan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ana kawo mai gargaɗi kuma ya ƙi dan haka a take bayan an fito da shi ta sanar da shi hukuncin sa sannan ta bada umarni akan in aka kama sa yana ƙoƙarin hana matar sa sheƙe ayar ta toh a kawo mata rahoto dan ta fito mai a ɗaya zahirin ta da ba kowa ya san da hakan ba sai waɗanda suka yi mata laifi mai tsauri..

  A haka ta cigaba da bada hukunce hukunce ga masu laifi sannan ta miƙe ta juya rigar ta tayi tafiyar ta daga haka fada ya cigaba da gudanar da abubuwan yau da kullum masu zaman a bamu mu kai baka na nan na jira masu tafiya sun tafi..

  Shigar ta wani yanki cikin masarautar nata ta hango wani ɗan saurayi da ta daɗe tana kwaɗayin sa dan tun lokacin da yayan Berenice ya ƙi amince mata ta hangon yaron saboda kasancewar abin kamar abin kunya sai Berenice ta sakaya maganar ta ƙi sanar da Juda cewa har ƙaramar yaƙi aka yi tsakanin yayan ta da sarauniya Zinaida akan ya ƙi yarda ya kula ta kuma ya amsa gayyatar ta wanda hakan ya daɗa tunzira ta ta mai sharri sannan ta kame sa,,..
  Shi wannan saurayi ya kasance babba cikin sojojin masarautar ta dan shine mai kula da koyar da yaƙin sauran sojojin masarautar dan ya kasance amintaccen shugaba tun lokacin marigayi sarki mijin sarauniya Zinaida na da rai,babu ruwan sa da shiga harkar da ba'a saka sa ba dan ko za'a yanka mutum a ɓoye wuƙa a gaban sa ko uhum ba zai ce ba bare ya kai ga tura ƙara zuwa ga wani har a gano masu laifin,sam bai da damuwa dan a halin da ake ciki ma,wannan saurayin a ƙarƙashin tursasawar wannan sarauniya yake abubuwan da basu dace ba saboda sau da dama yakan zauna ya rinƙa tuno yawan rayukan da yake kashewa duk wayewar safiya zuwa duhun dare,a ƙalla rayuka ɗai ɗai har zuwa ɗari yakan kashe a rana kafin dare ya tsala wanda hakan kuwa ba nufin sa bane ƙarfin asiri ne irin ta sarauniya Zinaida dan ta rantse sai ta haɗa shimfiɗa da wannan saurayi kasancewar ta gama kwaɗaituwa da shi tuntuni amma bata fito da maitar nata sarari ba,lokaci kawai take jira..
  A yanzu da take tafe ta hango sa babu riga a jikin sa daga shi sai wandon dake jikin sa da takobi a gefen wandon sai wani dake riƙe a hannun sa yana gwada ma sauran waɗanda yake koyawa yaƙin yadda zasu yaƙi maƙiya cikin sabon salo ba kamar yadda suka saba koya a baya ba..
  Wannan ƙwazo da hazaƙa haɗe da basira ta wannan saurayi ya sa sarauniya Zinaida ke bala'in jin sa har cikin jinin ta burin ta kawai ta keɓe da shi wanda take saka ran nan ba da jimawa ba anjima zata gabatar mai da ƙudirin ta duk mai afkuwa ta afku..

Tafiyar ta tayi tana mai ƙudurta yadda zata sarrafa wannan saurayin dan ta gama kwaɗaituwa da shi kuma ita duk namijin da ta ga ya biya mata a rai toh tilas sai ta sarrafa sa dama can ko da mijin ta ke da rai lokuta da dama in har zasu yi kwanciya da shi toh akwai masu tayar masu da hankali daga ita har shi a nan ne in namiji mai tayar mata da hankalin ya shiga ran ta sai ta fasa kwanciyar da mijin ta sai ta kwanta da shi namijin haka shima a nasa ɓangaren,toh ana iya ce ma hakan mummunar sabo wanda ya zamo mata masifa in ta ga namiji ko bai neme ta ba ita zata neme sa kuma dole ya amince..
  Lokuta da dama ɗiyar ta gimbiya Ondrea kan kama ta kamun turmi da taɓarya ita da wanda take tare da shi sai dai ta girgiza kai tayi wucewar ta dan mahaifiyar ta ta zama babba sai dai ta bi ta da ido,sau da dama takan kwaɗaitu da abin da mahaifiyar ta kan yi sai dai takan tuna kalmar mahaifin ta kafin ya mutu da ya ce da ita ta mayar da hankalin ta akan karatun da ake koyar da ita a ɓoye ba tare da sanin mahaifiyar ta ba dan baya so ta cigaba da rayuwa a nan irin tasu rayuwar yana so ta mori rayuwar da ake gudanarwa a ƙasashen da ba tasu ba rayuwar ƴancin kai dan daga shi har ita are compelled and under the control of sarauniya Zinaida saboda hamshaƙiyar matsafiya ce ba kaɗan ba..

Tana zaune tana saƙa da warwara tana tanadin abin da zata ba wannan ɗan saurayi sai ta ji shigowar ɗiyar ta ɗakin dan ƙamshin ta kaɗai ke tabbatarwa mutum da ta shigo wuri tun kafin ta buɗi baki ta nemi izinin shigowa..
  Ƙarasawa tayi zuwa bakin gadon ta zauna tana kallon mahaifiyar nata dake ɗan kishingiɗe bisa gadon ta na alfarma da ya sha gyara kamar mai rumfa,ɗan tashi tayi ta haɗa ido da gimbiya Ondrea na wasu seconds sannan ta buɗe baki tana mai ce da ita
  "Kina da damuwa ne gimbiya"?natsuwa tayi tana sauraron mahaifiyar nata har ta rufe baki sannan ta numfasa kafin ta ce wani abin
  "My king,,ina da damuwa ban san da wa zan yi shawarar damuwa ta ba"..kallon bazata sarauniya Zinaida ta aika mata da shi tana tunanin wani irin damuwa gare ta da har ya saka ta ramewa dan sai yanzu ta lura da yadda ta rage ƙiba kasancewar ta ƴar madaidaiciya a jiki,ta san dai duk wasu abubuwan jin daɗin rayuwa da more rayuwa daidai gwargwado ta wadata ta da su toh meye kuma damuwar ta..
A ɗan dame ta riƙo hannun gimbiya Ondrea tana mai yi mata kallon so da ƙauna sannan ta ce
  "Gimbiya menene wannan damuwar da ke damin ki har ya saka ki ramewa a ƴan kwanakin nan"?shiru gimbiya Ondrea tayi kafin ta ce
  "Mama na kar ki yi fushi da batun da zan kawo maki amma mama na na ga wani abu na shirin faruwa a gidan nan wanda na san da zarar ya faru yana iya zamo maki abin kunya dan mulkin ki ya wuci gaban hakan ta faru a masarautar ki"!!!shiru tayi yayin da sarauniya Zinaida ta shiga duhu kan ta ya ƙulle ta rasa inda zantukar ɗiyar ta suka dosa sai dai zata yi shiru dan cin ribar zancen..
Cigaba da magana gimbiya Ondrea tayi
"My king,i am deeply in love with _CAHAL_ kuma rashin sa yana daidai da rashi na na maki alƙawari muddin na rasa sa toh nima za'a rasa ni,i swear"...wani irin fincike hannu sarauniya Zinaida tayi daga riƙon da da ta ma hannun gimbiya Ondrea ta miƙe tsaye tana haki haɗe da watso mata zagayayyun idanun ta tana kallon ta kallon tsantsar mamaki haɗe da tsoro..
  Lamarin na son kacame mata sai dai dole ta yiwa tufkar hanci dan ba zata juri wannan shashancin ba ta yaya gimbiya Ondrea zata zo mata da wannan shirmen lallai tayi sake da yawa..
Kallon ta Ondrea tayi tana ganin yadda fuskar ta ya canza launi bala'i kawai ke ruruwa a cikin ta dan haka sai ta tari numfashin ta ta hanyar miƙewa tsaye itama cikin gaskiya da gaskiya ta ce
  "My king,babu fashi a zance na,na maki rantsuwa da marigayi mahaifi na sarki Adha Bait Akbar ana hana ni Cahal ina kashe kai na dan ina son sa fiye da yadda nake son kai na Mama na"!!..wani irin azababen zufa ke karyo wa sarauniya Zinaida ta inda bata tsammani dan ta tsorata ba kaɗan ba da kalaman bakin ɗiyar ta gimbiya Ondrea,me hakan ke nufi kenan?tayi sake ɗan zaki ya girma a gaban ta?ko kuwa wani salo ne na firgitarwa gimbiya Ondrea ta zo mata da shi?saurin ɗago idanun ta tayi ta kalli ƙwayar idanun gimbiya Ondrea kafin ta ce
  "Ondrea me ke shirin faruwa da ke  e halan?kin rasa tunanin ki shikenan kuma sai ki rasa hankalin ki?kin fita daga duniyar mu ne da har zaki yi tunanin ni,,ni,,ni isasshiya sarauniya Zinaida mai mulkin masarautar Mughal Empire zan amince maki da ku ƙulla alaƙa mai girma da tsauri tsakanin ki da wannan bawan da bai da ranar samin ƴancin kan sa ne?ki amsa min Ondrea tun kafin fushi na ya illata ki"!!.
  Hawaye ne ya hau saukowa gimbiya Ondrea daga idanun ta zuwa saman kumatun ta sai ta juya baya ta shiga magana
  "Mama na ba zan bijire maki ba in kin ce ba zaki yarda alaƙa mai tsauri ta shiga tsakani na da mutumin da kike wa kallon bawa ne a fadar ki kuma bai da ranar samin ƴancin kan sa,sai dai ki sani na maki rantsuwa da ƙarfin mulkin wannan masarauta mai ɗumbin tarihi,ni gimbiya Ondrea Adha Bait Akbar zan bar maki masarautar ki in shiga duniya dan cigaba da rayuwa ta kamar yadda kowa ke rayuwar ƴanci sannan ki sani ko bana gidan nan kika yarda alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakanin ki da Cahal,,,,..humm bana jin zan yafe maki My king"..tana kaiwa nan tayi tafiyar ta yayin da mahaifiyar ta sarauniya Zinaida ta ji kamar ta tsala Ihu ko zata sami sassauci a zuciyar ta dan ɗiyar ta ta gama ɗaure ta da jijiyoyin jikin ta kuma ta gama da ita dan yarinyar ce kaɗai gare ta saboda wataran abin da take gudu zai iso kuma hakan na dai dai da rasa mulkin ta kafin lokaci take son yin amfani da gimbiya Ondrea wurin samin nasarar ta a rayuwa dan ita kaɗai ce jinin ta a kaf duniya dole sirrin ta sirrin gimbiya Ondrea ne sai dai kuma bata jin zata iya barin gimbiya Ondrea ta cigaba da rura wutar tsanar dake son ƙunnuwa tsakanin su..

  Tsaf ta miƙe tsaye ta janyo rigar ta ta sama ta saka takalmin ta ta tako har waje ta nifi hanyar ɗakin gimbiya Ondrea ko zata yi karo da ita sai dai bata gan ta ba,bincike ta shiga yi tana duba ɗakin amma bata hango ta ba sai hankalin ta ya bi ya tashi ta rasa ina zata kuma duba gimbiya Ondrea..
  Tsoron ta ba dai guduwa tayi ba kamar yadda ta mata iƙirarin barin gidan dan shiga duniya ba,in ko haka ne toh tabbas ya kamata ta sa a tsare mata ƙofofin shigi da ficin masarautar har sai ta yi nasarar gano inda gimbiya Ondrea take sannan za'a buɗe  ƙofofin...

Fita tayi cikin azama tana mai ƙwala kiran masu kula da shigi ficin gidan haɗe da bada dokar a rufe ƙofofin gidan kar a buɗe sai ta kammala binciken ta tsaf,kamar yadda ta ce haka aka yi aka bi duk ƙofofin gidan aka rufe su kaf haɗe da daɗa jaddada ma sauran masu kula da ƙofofin akan kar a buɗe ƙofar sai sarauniya ta bada izini..
  Rai a ɓace ta kama hanyar komawa cikin gidan tana tafe tana wasi wasin inda zuciyar ta ke hasaso mata gimbiya Ondrea zata iya kasancewa..

★★★★★
  Da zafi zafi suke abubuwa babu ƙaƙƙautawa ba su suka saitu ba sai da suka sami kan su,kwanciya yayi ita ma ta bi sa ta kwanta bisa kafaɗar sa,numfashi suke saukewa yayin da ya kawo hannun sa ya rungumo ta yana mai sumbatar goshin ta haɗe da faɗin
  "Gimbiya ta idan mahaifiyar ki ta gano inda kika zo fah me zamu ce da ita"??daɗa yin lamo tayi a jikin sa sannan ta ce
  "Masoyi na ka manta da mahaifiya ta dan sai da na gargaɗe ta akan abubuwan da ke iya faruwa wanda zasu janyo mata ƙasƙanci amma ta rufe ido haɗe da toshe kunnuwar ta akan magana ta,dan haka kar ka damu duk abin da zai biyo baya alhaki na kan ta masoyi na"...ɗan shiru yayi sannan ya ce
  "Gimbiya ta ina tsoron kar wata ran abu mai ƙarfi ya shiga tsakanin mu ba tare da mun mallaki juna ba,idan hakan ya faru bana tunanin sarki zai yafe min a duk inda yake"..shiru tayi tana tuno mahaifin ta kafin ta ce
  "Kar ka damu masoyi na,,babu wata alaƙa da zata shiga tsakanin mu ba tare da aure ba da ta wuce wannan,dan haka ka daina damuwa ka ji"??gyaɗa mata kai yayi yana mai sauraron numfashin ta kafin daga bisani ya tambaye ta
  "Ya karatun ki gimbiya ta"?ɗan murmushi ne ya kufce mata ta ɗan ɗau lokaci tana murmusa sannan ta bashi amsa da
  "Masoyi na,an ce da ni baka da ranar samin ƴancin kan ka dan haka tarayya ta da kai ta haramta,sai dai kuma wanda ya faɗi hakan ya tafka kuskure dan ƴancin ka na gab da samuwa ko da amincewa ko babu amincewa zan ƙwatar mana ƴancin mu bayan na gama shirya abin da nake kan shiryawa"...murmusawa yayi sannan ya ce da ita
  "Ina maki fatar samin nasara gimbiya ta"..musayar murmushi suka wa junan su dan su suka gane ma'anar kalaman su ta ƙarshen nan..
 
  Tana tafe tana jin faɗuwar gaba na riskar ta kamar dai kar ta nufi ɗakin sai dai dole ta tafi dan tantance gaskiyar lamarin,tana tafe tana kalle kalle har ta kawo daidai bakin tagar ɗakin,wucewa tayi sai hankalin ta ya ba ƙwaƙwalwar ta saƙon da ta dawo baya da sauri,dan haka da saurin ta dawo da baya ta natsu tana ƙare ma ɗakin kallo..
  Ɗiyar ta ce kwance haihuwar ta babu sutura ko ɗaya a jikin ta kwance saman kafaɗar ɗa namiji da shi kan sa bai da sutura a jikin sa sannan babu wani mahaluƙin da zai kalle su ya ce babu abin da ya shiga tsakanin su duba da irin yanayin da suke..

Bata san lokacin da ta ƙwala ihun kiran sunan ɗiyar tata ba dan jikin ta kyarma ya shiga yi ta rinƙa jin wani ɗaci ɗaci a ran ta zuciyar ta na tafarfasa sam ganin ta ya gushe bata gani sosai..
  "Ondrea"!!!!!!a mugun firgice gimbiya Ondrea ta tashi daga jikin sa sai suka yi ido huɗu da mahaifiyar ta da itama zaro idanun tayi tana mata kallon tsoro,sake kiran ta tayi
  "Ondrea"!!!hankali tashe gimbiya Ondrea ta daɗa buɗe idanun ta tana kallon mahaifiyar ta da ta kama su kamun turmi da taɓarya cikin wannan halin...


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:56] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:23&24*

A firgice sarauniya Zinaida ta koma ta ƙofar ɗakin haɗe da hankaɗa shi tana mai fidda numfashi mai nuna tsantsar ɓacin ran ta haɗe da fusatar ta,..
Tana shiga ta nufi kan gadon haɗe riƙo hannun gimbiya Ondrea ta janyo ta ta sauko daga saman gadon sannan ta bi wannan saurayi da ƙazantaccen kallo tana mai tofar da yawu kafin ta fuskanci gimbiya Ondrea cikin ɓacin rai ta shiga yi mata magana
  "Kin haukace ne Ondrea??ina tambayar ki ki bani amsa baki da lafiya ne?ki rasa da wa zaki haɗa jiki sai da wannan bawan?tukunna ma yaushe kika yi girman haɗa jiki da ɗa namiji?cikin masarauta na kike wannan abin?asiri ya maki ne?iyee?ki amsa min"?cikin ɗagin murya ta mata tambayar ƙarshen tana mai yi kamar zakanya dan saura kaɗan ta ɗauke ta da mari..
  Hawaye ne ke bin fuskar gimbiya Ondrea tana mai yin tir da halin mahaifiyar ta a ce uwa na haɗa shimfiɗa da wasu mazajen da bata san asalin su ba sannan ita dan ta yi hakan da wanda kowa ya san sa ya san tarihin sa shine zata tada hankalin ta akai in ba dai manufar ta take son isarwa akan sa ba me zai sa hankalin ta ya tashi sannan ta razana haka..
  Tana tunanin ne yayin da shi kuma wannan saurayin ya nemi wandon sa ya suturta jikin sa yana mai yunƙurin saka rigar sa ta leda mai gauraye da fata,ai kuwa fauce rigar sarauniya Zinaida tayi ta ɗaga hannun ta ta yanke mai maruka har biyu tsabar takaici da baƙin ciki,..
  Gimbiya Ondrea bata san lokacin da tayi tsalle ta faɗa jikin saurayin nan ba ta fashe da kuka tana mai yi wa mahaifiyar ta wasu irin maganganu masu razanarwa.
  "Na rantse maki in kika kuma ɗaga hannun ki akan masoyi na zan manta cewa ke kika haife ni in yanke hukuncin da ya zo min rai na sannan in baki sani ba yau ki sani ni da Cahal mun zama ɗaya a yau ɗin nan ɗazu ɗazun nan ba da jimawa ba saboda haka ki cire idanun ki daga gare mu in ba haka ba zan ɓace maki ɓacewa ta har abada"!..da kuka ta ida maganar wanda ya birkita sarauniya Zinaida ta kasa haɗa kan ta wu ɗaya dan haka ta kalli saurayin da gimbiya Ondrea ta kira da Cahal tana mai wani irin mugun kallo mai ɗauke da harara
  "Ka yarda ka san ɗiya ta?ka yarda ka haɗa jiki da ita?toh bara na sanar da kai ka tafka babbar kuskure a rayuwar ka wanda ya janyo maka yin rayuwa gidan horo rayuwa ta har abada"!!sai ta juya ga ɗiyar ta tana kallon ta sannan ta ce
  "Ke kuma mu zuba ni da ke cikin masarautar nan tunda kin kwaɗaitawa kan ki abin da ya fi ƙarfin ki"tana kaiwa nan ta fita fuuu tana tafe kamar tayi fiffike ta miƙe sama ta tsinci kan ta a ɗakin ta,..
A yayin tafiyar ta mutani sama da takwas sun amshi maruka daga gare ta sannan mutani biyar sun sami hukuncin shekaru biyar gidan horon ta..
  Tana shiga ɗakin ta bata tsaya ko ina ba sai cikin ɗakin ta mai tsananin duhun gaske,tana shiga ta hankaɗa labulen wani gefen ɗakin ta shige ciki sai gata tsaye gaban wani irin kyakyawar gunki da aka ajiye shi kamar an zana da hannu,tana zuwa ta faɗi gaban gunkin nan ta hau faɗe faɗe tana iface iface kafim ta dawo ta faɗi ƙasa warwas ta shiga shesheƙa tana tambayar gunkin kamar haka
"Kai ka ce min duk abin da nake buƙata kuma na gan sa a gaba na in yi yadda nake so da shi,me ya sa yau na buƙaci haɗa shimfiɗa da wannan bawa amma ɗiya ta ta min shigar sauri bayan ta sanar da ni tana son sa na hana ta yin wata alaƙa da shi sai ta yi mai gabaɗaya ta haɗa jiki da shi sannan bata ji shakka ta ba?me ya sa hakan ya kasance?me hakan ke nufi"?wani guguwa ne ya taso ya lulluɓe ta kafin murya ya biyo baya cikin isa aka fara yi bata amsar tambayoyin ta
  "Dalilin faruwar hakan shine kundin da kike buƙata na nan zuwar maki dan a halin yanzu kundin na nan ƙasar ki kuma nan ba da jimawa ba zai shigo masarautar ki amma kar ki manta na sanar da ke muddin kika riƙe wannan kundi a hannun ki,,kaf asirin da kika ma ahalin masarautar ki ciki har da ɗiyar ki zai warware sai kin ɗora wata sabuwa ta yadda zaki mulki duniyar baki ɗayan ta saboda ki sani kina iya fuskantar abubuwan al'ajabi iri daban daban wannan kaɗan ne daga irin abubuwan al'ajabi da ban mamaki da zaki fuskanta kafin kundin nan ya shigo hannun ki,dan haka ki sani baki da ikon haɗa shimfiɗa da wannan saurayi dan ƴar ki ta gama amincewa da shi a zuciyar ta saboda ta mallaka mai jikin ta da tunanin ta kuma matuƙar kika tsananta akan sai ta rabu da shi toh zaki rasa ta rasawa ta har abada,ki tuna rasa gimbiya Ondrea na daidai da rasa komai naki a duniyar nan,rasa ta na daidai da rugujewar gwamnatin ki ko da kin mallaki kundin nan dan haka ki yi azamar gyara tunanin ta kafin ta ƙubce maki"!!!ana gama faɗin haka guguwar ya ɗauke sai ta miƙe wuf ta fito ta koma kan gadon ta tayi kwanciyar ta tana mai baƙin cikin hana ta kusantar wannan saurayi da ta gama ƙudirin kasancewa da shi a ɓangare ɗaya kuma tana murna da farinciki kundin da zai shigo hannun ta kenan mayaƙiya Berenice bata mutu ba ta tsaya tsayin daka dan ta kawo mata kundin nan saboda ta sakar mata ɗan uwa,lallai akwai shaƙuwa ta musamman tsakanin Berenice da ɗan uwan ta...

★★★★★

Tun bayan fitar sarauniya Zinaida gimbiya Ondrea ke rusa kuka tana mai rarrashin sa haɗe da alƙawarta mai cewa yau ba gobe ba zasu bar masarautar kuma bata son ta ji komai daga gare sa,yayi yayi ta fahimci mahaifiyar ta su haƙura da juna amma wani irin bijirewa umarnin mahaifiyar nata ne ya rinƙa fizgar ta har dai ta ji in ba barin gidan suka yi ba irin haushin mahaifiyar nata da take ji na iya saka ta aikata abin da ba shi kenan ba,dan haka ta hana sa wani kafar da zai ƙi amincewa da shawarar ta dan ta gama ƙullawa a ran ta yau zata bar gidan ta bar masarautar ita da masoyin ta in ya so sai su cigaba da rayuwar su a wajen masarautar ba tare da an san su ba..
  Rarrashin sa ta yi sannan ta saka sa shirya kayan sa dan a tsakiyar daren zasu bar masarautar saboda sam bata son ta kwana a gidan.. 

  Fitowar ta kenan tana tafe tana tunani marin da mahaifiyar ta ta ma masoyin ta babu gaira babu dalili duk dan saboda ita mulki da iko su ne ƙashin bayan ta a wannan masarauta amma ita duk waɗannan basu ɗaɗa ta da ƙasa ba hasalima ta tsani tsari irin ta masarautar dan a baya mahaifin ta na tafiyar da komai yadda ya kamata amma yanzu da mahaifiyar ta ce ke gudanar da al'amuran masarautar sai masarautar ta gundire ta ta ji ta gaji da zaman masarautar gabaɗaya..
  Bata ankara ba har ta zo zata wuce ƙofar mahaifiyar ta sai ta dawo da baya ta shige ɗakin ta hangi mahaifiyar nata na shirin tafiya fadar wankar ta dan sanye take da rigar wankar a jikin ta..
Tana hango ta sai tayi saurin nufo ta haɗe da riƙo hannun ta tana kallon ƙwayar idanun ta cikin sanyin jiki da nuna tsantsar nadama ta shiga murza hannun gimbiya Ondrea tana faɗin
  "Ɗiya ta,,,ina so ki gafarce ni da yi maki shisshigi cikin al'amuran ki amma ina so ki sani ɗiya ta,,mun _BAMBANTA_ da wasu mutanin,ina so ki gane akwai _BAMBANCIN ƘASA_ cikin jinsi jinsin mutani,akwai _BAMBANCIN_ al'adu tsakanin mu da wasu mutanin,Ondrea ɗiya ta,,ba son ƙuntata maki nake yi ba a'a,so nake in tseratar dake daga faɗawa halakar da zaki faɗa dan sakamakon _BAMBANCIN ƘASAR_ dake tsakanin mu da ƙasar wannan mutumin da kike son haɗa alaƙa da shi mun fuskanci abubuwa da yawa sannan zamu fuskanta muddin kika cigaba akan ƙudirin ki dan haka ki fahimce ni,ki raba kan ki da wannan bawa kin ji ɗiyata"?wani kallo gimbiya Ondrea ta aika mata da shi dan ta sami amsar da take buƙata sai kawai ta fizge hannun ta tayi tafiyar ta tana jin muryar mahaifiyar nata na kiran ta amma ta mata banza tayi gaba..
  Wannan ɗabi'a ta gimbiya Ondrea ya matuƙar harzuƙa sarauniya Zinaida sai dai tana

Please Login or Register in order to submit comment