Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗar sarki Sultan dan aiwatar da abin da zai iya yiwuwa saboda ayi a wuce wurin,da wannan shawarar suka rabu suka kama hanyar zuwa kasuwar dawakai..
Kowa ya sami nasa daidai ɗaukar sa kuma sun ɗana dawakan kafin su tafi da su bayan Fianna ta biya kuɗin dawakan dan ita ce ta fito da kuɗaɗe saboda sai da sarki Malik ya sa aka cika mata jakar tafiyar ta da kuɗaɗe dan yanayin tsaro na kan hanya..

Tafiyar su babu jimawa Baccus ya zauna yana nazarin abu guda da ya ɓoyewa su Juda dangane da wannan tafiyar tasu da zasu yi dan ya san da wuya ayi wannan tafiya rayuka shida har da shi na bakwai ba tare da an sami mishkilar rasa rai ɗaya ƙwaƙwara ba kuma wannan dole ne ba wai wai bane dan hakan yana faruwa kuma ko a yanzu ma zai iya faruwan sai dai yana fata in suka aiwatar da abin da zai kai su suyi nasara ko da za'a rasa rai ya kasance ran ba a yi rashin iska ba..

★★★
Rayuwa na nan na masu daɗi kuma suna daɗa fahimtar junan su da sanin halayyar junan su haka yarda na daɗa shiga tsakanin su kuma suna kan ƙirga kwanakin da ya rage masu su dumfari masarautar Sultan...
Da yammaci ne haka suna zaune suna hira sai ga wasu manyan manyan bulls suna fitowa daga dajin dake daga bayan su ko kafin su sani su ankara har sun ga an mamaye su kamar haɗin baki aka saka su a tsakiya aka bar su da raba idanu gashi basu da komai na kare kan su a wurin daga su sai su...


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:00] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:43&44*

Wani irin zagaye su aka yi da sai da suka tsorata dan kuwa dandazon mutani ne ba kaɗan ba a wurin abin ban mamakin kuma bai wuce ta yadda suka gano inda su Juda suke ba da har aka masu dirar miƙiya..
Kallon kallo suka aikawa junan su tunani kowa ke yi a ransa ta yaya zai yi galaba akan waɗannan mutani ba tare da an mai rauni ba..
Duk tunanin su ƙafewa yayi a wuri ɗaya sakamakon rashin madafa amna sun san ko ya nene dole su samo mafita ɗaya..
Duk wannan tunane tunanen a seconds aka aiwatar da shi duba da yanayin mutanin babu wani wargi ko wasa a tattare da su sai kawai masu baiwar sihiri suka yanke hukuncin yaƙar su da sihirin su kafin marasa shi su ɗauko abubuwan yaƙin su dan dai suyi distracting waɗannan mutani..
Kamar haɗin baki hukuncin da suka yanke da zuciyoyin su kenan amma kamar a zahiri suka yi sa..
Kallon hadarin kaji biyu daga cikik mutanin da suka yi dandazon suka aikawa su Juda kafin ɗayan ya tofar da yawu yana masu kallon ƙyama da ƙasƙanci sai da abin ya harzuƙa Agneta tayi kamar zata tunkare su dan tsabar wulaƙanci tsakanin su wa ya kamata ya karɓi kallon ƙasƙanci da ƙyama sama da su da suke yi,hana ta motsaywa Berenice tayi tana mai girgiza mata kai akan ta ƙara tsumayen su kafin su faɗi abin da ya ɗare su dan su yi faɗa da hujja..

Takowa ɗaya daga cikin su ya fara yi yana ƙare ma Fianna kallo dan duk ta fi su girman jiki,daga ita sai Berenice a girman jiki dan haka ana iya kiran ta mai girman halitta a cikin su su biyar ɗin..
Yana zuwa ya tsaya daidai ibda take tsaye ya rinƙa ƙare mata kallo yana bin ta da kallon zalama da kwaɗayi sai dai ta daure bata ce komai ba jira kawai take ya kawo hannun sa jikin ta ita kuma ta yanke dan takaicin ƙazamin duk ya ishe ta ga ƙazantaccen bulls da suka taho da su masu warin aladu duk sun cika mata hanci..
Bai taɓa ta ba amma haka ya rinƙa zaga ta kamar zai taɓa ta kamar zai lashe ta dan zalama..
Sai da ya shafe lokaci mai tsayi kafin ya dawo ta gaban ta ya kafe ta da ita,duk babu wanda ya tanka mai a cikin su sai bin sa da kallo da suke yi sai kuma kamar an tsungule sa ya fara dariyar tantirai marasa jin magana..
Duk a nanma babu wanda ya tanka mai sai da ya ji dariyar ta mai sannan ya tsagaita ya buɗe baki yana magana kamar dai yadda bulls ɗin nan ke gurnani babu daɗin ji haka shima muryar sa kamar ganga ta fashe ya fara magana
"Wai ke da ku duk masu iya riƙe razanar su ko?gani kuke dan kun ɓoye razanar ku ni zan wani yarda ne har in bar ku haka nan koh?wai shin ya aka yi ma ban iya yi maki komai ba ke mai farin rigar nan(wato Fianna dan kalar kayan jikin ta fari ne kuma da shi ta fito tun daga masarautar su),?uhum?kema baki sani ba ko?toh sai na taɓa ki dan na kwaɗaitu da ke duk da duban gari muka zo yi daga masarautar Sultan ba zan bari garaɓasa babba haka ya tsallake ni ba sai na lasa"..haka ya rinƙa magana kuma maganar na ta shiga kunnen Fianna ga wani haushin sa da take ji..
Sai kawai dariya ta kaure tsakanin mutanin da ya zo tare da su..
Wani juyawa yayi da alfahari ya kalle su yana faɗin
"Ku ma lu zo ku zaɓi naku dan ni dai wannan ita ce zaɓi na yarinyar akwai kyau,duk mace ɗaya maza biyar su huta da ita ni na baku wannan odar"!!sam bai lura cewa akwai namiji a wurin ba kasancewar Balik haka yake da fuskar mata ga yanayin da yayinda sumar sa kamar yadda mata ke ɗaurewa su naɗe sai wannan mutumi ya rinƙa masu kallon duka mata ne babu namiji a cikin su..

Daɗa matso Fianna wannan mutumi yayi yayin da sauran garorin dake tare da shi suka matso suma da zumar ɗaukar ko waceace ɗaya,ga wani wari warin da suke yi ga lashe bakim da suke yi kamar wasu karnuka sannan su su Juda tsoron su kar suyi wani ƙwaƙwaran motsi waɗannan bulls su haukace amma hakan ba yana nufin zasu yi ta tsayuwa bane dole su aiwatar da wani abin..
A daidai lokacin da wannan mutumi ya kawo hannu zai sauke saman ƙirjin Fianna sai kawai ya ji kamar hannun baya a jikin sa,dan haka ya ɗauke wuta ya tsaya cak na wasu mintuna,duka ƙasa da zai yi sai ya ga gunduwar hannun a ƙasa ga dungun a jikin sa,..
Waro idanu waje yayi yana kallon hannun sa a ƙasa yana kallon su Juda dake tsaye ga sauran da suka ɗebi jiki wai zasu tunkari su Juda..
Ai babu shiri ya sake wani razanannen ƙara da ya karaɗe dajin har ya saka bulls ɗin matsawa baya suna nemar mafaka dan sun tsorata..
Su kan su mutanin sai da suka ji kamar su gudu tsabar kaifin ihun sai ya fara magana cikin azaba
"Ku yanke su matan nan mayu ne sun cire min hannu na ku yanyanke suuu"!!!da ƙarfi ya ida maganar ƙarshe..
Toh dama Agneta ta gaji da halin da yake ta nuna masu sai kawai ta yanke hukuncin amfani da sihirin ta akan sa ta fara da shi kafin ta koma kan sauran..
Ai kuwa mutanin nan na nufo su wani irin guguwa ya taso ƙasa ya rufe masu idanun su ko da guguwar ta lafa sai suka ga su Berenice da takubba a hannayen su dama guguwar dan yayi distracting nasu ne kar su yunƙura su biyo su Juda har sai bayan sun ɗauko takubban su...
Wani irin mummunar yaƙi ne ya kaure a tsakanin su shi dai da aka guntilewa hannu yana can gefe yana faman kallon hannun dan yana tsoron kar ya fuskance su a kuma raba sa da hannu ɗayan in suka mai hakan sun gama da shi..
Faɗa ba na wasa ba five of them against the little crowd da zasu kai talatin da wani abu,babu wasa haka aka rinƙa kaiwa ana komowa..
Babu ƙarar abin da ke tashi a wurin nan sama da ƙaran takubban su da numfarfashin su dake ta tashi a wurin kwata kwata babu sauƙi faɗan,..
Lokaci mai tsayi suka ɗauka suna yaƙin nan har sai da aka yi jina jina aka zubar da jini faca faca kamar an yanka dabbobi..
Ko da abin ya lafa Callee ta sami rauni a hannun ta na dama ta sama sannan Juda ta sami yankewa a laps ɗin ta bayan su babu wanda yayi rauni sai gajiya da suka yi amma kaf jama'ar mutumim nan an ƙarar da su saboda nuna mai ƙasƙanci ma har kawunan wasu Juda da Berenice suka yankewa su wurgowa uban gidan nasu da ya basu odar yin abin da suka yi..

Juyawa yayi ya ga ko ina an gama da mutanin sa da ya taho da su sai ya fara rarrafen miƙewa zai nemi hanyar gudu,ashe dama ƙaryar iskanci yake yi yana da tsoro.
Dubawa yayi ya ga kamar hankalin su baya wun sa sai kawai ya tashi tsaye ya arta a guje sai dai yana tsaka da gudun ne kuma yaji an halbo sa da wani wuƙa daidai tsakiyar bayan sa..
Faɗi yayi a wurin yana shure shuren mutuwa,cikin sauri Callee ta ƙaraso ta cakumo shi tana tambayar sa
"Ina Sultan yake?in suke ajiye mutanin da suka yi garkuwa da su"?kallon ta yayi ya ga desperation a fuskar ta da muryar ta sai kawai yayi wani dariya mai tafe da ciwo da azaba ya ce da ita
"Ba zan bayyana ba kuma ku sani ba kun yi yaƙi da mu da ni ni Khalais kun tsira lafiya ba?toh gagarumin yaƙi na nan dumfaro ku ku tsaya ku gani sai zaman dajin nan ya maku wahala"!!!...tun kafin yayi nazarin furta wani abin ta yanke sa a wuya sai numfashin sa ya tsaya cak,alamar dai mutuwa yayi daga haka ta take sa ta wuce sai ga Juda cikin hasala ta zo ta ƙarasa raba kan da jikin sa ta aje gefe..

★★★★★★

Cikin dare suna zaune suna cin namar da suka gasa an yi sashi sashi mutum bibbiyu Callee da Agneta,Balik da Fianna Juda da Berenice ana cin nama ana hira ana ba'a da raha..
A nan suka kwanta suka yi bacci har wayewar gari inda Agneta da Callee suka tafi nemo abinci,Balik kuma ya tafi wanka Juda da Berenice na kan wasa takobin su Fianna kuma na zaune tana meditating a can gefe da su..

Bayan Fianna ta gama meditation ɗin ta tashi ta nufi hanyar rafin nan da nufin yin wanka,Juda ta so hana ta dan Balik na wurin amma kasancewar bata ba abin muhimmanci ba sai kawai ta share ta bar Fianna ta tafi su kuma suka cigaba da hirar su suna wasa takubban su..
Tana tafe tana kalle kalle har ta ƙaraso rafin ta fara cire kayan jikin ta,tsugunnawa tayi tana cire maɗaurin takalmin ta har ta gama ta cire takalmin duka ƙafa biyu..
Miƙewar da zata yi dan cire rigar cikin sai tayi karo da Balik da yanzu ya ɗago sama daga nutsewar da yayi ɗazu dan nishaɗin sa,wani irin razanannen ƙara ta saki tana janyo rigar ta dan ta mayar ai shi kuwa Balik me zai yi in ba dariya ba sam bai kai hankalin sa inda take tunanin nan ya kai ba sai abin ya bata haushi ya kalle ta sannan yana dariya..

Wankar da Fianna bata yi ba kenan a ranar haka ta koma wurin su Juda hankalin ta tashe tana ta tunanin ko ya gan ta gabaɗaya ko a'a,joining su Juda tayi suka ƙarasa wasa takubban..
Ko da Balik ya dawo sam Fianna bata yarda sun haɗa ido ba dan shakkar sa take ji bata san dalili ba..

A yammacin ranar suka hau dawakan su suka nufi hanyar kasuwa dan haɗuwa da Baccus saboda a yau ɗin ya kamata su kammala duk wata shiri nasu na tunkarar masarautar Sultan Baal-Hamon..

★★★

Tana gaban abin bautan ne amma sam hankalin ta baya jikin ta gani take gagarumin wahala da tashin hankali ne zai riske ɗiyar ta amma dole ta tsaya ta dage ta mata addu'ar nasara..
Aminan nata ne suka ɗan taɓa ta ta dawo daidai daga haka suka cigaba da addu'ar har aka kammala sannan suka fito..
Tambayar duniyar nan sun mata akan meke damin ta da bata saki jiki tayi bauta da kyau ba amma bata sanar da su komai ta barwa kan ta da haka suka rabu suka kama hanyar gidajen su ita kuma ta nufi hanyar komawa gidan ta..

Bata yi tafiya mai tsayi ta haɗu da wani mai keken doki ta tare sa ta shiga ta mai kwatancen inda zai kai ta,har gidan ta ya kai ta ya sauke ta ta bashi kuɗin sa ya ce da ita bai da canji ta ce ya riƙe sai dai yayi mamaki ganin ta damƙa mai kuɗi mai yawa wanda ba kasafai mutum ya cika bada su haka nan ba tare da ya amshi canjin sa ba..
Godiya ya mata ya wuce ita kuma ta shige gidan ta haɗe da rufe ƙofar..
Tun a farfajiyar gidan ta zauna ta rage gajiya duk ma tunani ya addabe ta tana son komawa kasuwa dan ƙarasa siyar da kayayyakin ta da suka rage sati mai zuwa zata tafi siyo wasu kayayyakin amma tunanin ɗiyar ta ya tasa ta gaba..
Har sai da duhun dare ya tsala sannan ta shige cikin gidan ta nemi abinci ta ci sannan ta kwanta tana ta tunani..

Kaman da awanni bayan kwanciyar ta ta ji ana ta bubbuga mata ƙofar gida,tashi tayi ta fito waje tana tunanin cikin daren nan wa zai zo mata kuma ta san ba kowa ya san da gidan ba dan an asirce sa in har ba amintaccen baƙo bane toh ba lallai bane ka ga gidan ba sai dai ka ga fili ko tekun ruwa amma sai gashi ana buga mata ƙofa..
Wani tunani tayi sai tayi saurin ƙarasawa ta buɗe ƙofar dan ganin ko waye wannan baƙon dare..
Tana buɗe ƙofar sai ta ga an nufo ta da wuƙaƙe fuska a rurrufe ana tambayar ta ina kuɗaɗe suke ta je ta kwaso..
Abin sai ya ɗaure mata kai dan har barazana ake mata akan ta je ta kawo koh a kashe ta..
Kamar dai ta ƙyale su sai kawai ta ga ta gaji da ire iren ziyarun da ake kawo mata na bazatta..
A zuciye ta bige ɗaya daga cikin su ta ƙwace wuƙar hannun sa ta riƙe wannan a wuya tana masu barazana sai suka dage suma akan lallai fah sai ta tafi ta ɗauko masu kuɗi ita kuma ta dage akan suna taɓa ta zata yanke wanda ta riƙe ɗin nan..
Sai da suka ga da gaske zata aikata abin da ta faɗin sannan suka sauke wuƙaƙen ita kuma ta buɗe fuskar mutanin dan ganin ko waye..
Ga mamakin ta sai ta ga wannan same mutumi da ta ba kuɗi ɗazu wato mai keken doki..
Tsabar takaicin yankar bayan da ya so yi mata sai kawai ta ɗaba mai wuƙar nan a wuya ta yanke sa sannan ta kalli sauran..
Da mugun hanzari suka kwasa a guje suka fita ai tun kafin su ƙarasa bakin ƙofar suka tsinci kan su a waje da gawar mutumin da ya masu alƙawarin kuɗaɗe masu tsoka in ya sami abin da yake so,dama basu san sa ba sai a wannan dalili dan haka gudu suka yi dan tsira da mutuncin su...

A nan cikin gidan kuma kasa bacci Hadara tayi sai tunanin abubuwan da suke ta faruwa da ita da suka gama tsorata ta da rikita ta..a haka ta cigaba da zama tana tunanin mijin ta,mahaifin ta da ƴaƴan ta..
Ta ma kan ta alƙawari in Juda ta dawo da ƙanwar ta toh tattara kan su zasu yi su koma wani garin dan zaman nan babu amfani...

★★★
"Kun san na ce da ku an lulluɓe masarautar nan da baƙin sihiri ko"?duk suka gyaɗa kawu nan su sai ya cigaba
"Toh akwai makarin wannan sihiri cikin kundin Juda sunan ki kenan ko"?yayi maganar yana kallon Juda sai ta gyaɗa mai kai alamar eh sunan kenan..
"Kawo kundin nan ina son duba wani shafi ciki dan a nan ne kaɗai zamu sami makarin wannan sihirin in ba a nan ba toh sai a wurin sarkin"..
Miƙo mai kundin Juda tayi tana jin faɗuwar gaba lokuta da dama takan zauna ta ƙurawa Callee ido tana fata da ma Callee ta zamo ita ce missing sister ɗin ta amma ta san ba abu mai yiwuwa bane dan Sultan Baal-Hamon ya saka aka ɗauke ta ita kuma wannan daga can Babylon ta fito kenan kawai shaƙuwa ce ba ta jini ba tsakanin ta da Callee amma ƙanwar ta na nan ƙarƙashin wannan azzalumin dan haka dole tayi komai dan taimakon ƙanwar ta daga ƙangin wannan azzalumin..

Ƴan dube dube Baccus yayi kafin ya ce da Juda
"Makarin ya kasu kashi daban daban kuma babu yadda za'a haɗa su dole sai an gwada ko wanne a ranaku daban daban hakan na daidai da zuwa masarautar nan sau biyar cikin ko wani dare dan samin nasara"..hankulan su ya tashi suna tunanin ta yaya hakan zai kaaance su da kw son ayi a wuce wurin dan abubuwan dake gaban su yawa ne da su..
Kasa haƙuri Agneta tayi ta ce wani abin
"Yanzu dole sai an yi daban daban kafin a sami biyan buƙata?ba za'a iya haɗa biyu a kwana ɗaya ayi ba"?kallon ta Baccus yayi yana faɗin
"Ba zai yiwu ba dan hakan na daidai da rasa abu mafi martaba da ƙima a wannan masarauta kin ga dan Sultan Baal-Hamon bai kamata a wulaƙanta kyawun sunan da ƙasar nan ke da shi sama da shekaru ɗari biyar da suka wuce ba"..
Gyaɗa kai suka yi baki ɗayan su sai Baccus ya cigaba..
"Amma ku zauna a nan kawai ku kwana har zuwa washegari da zan samo ainihin mafita mafi sauƙi a gare mu sannan kamar yadda mutumim nan ya faɗa maku gagarumin yaƙi na nan kusanto ku toh babu shakka za'a kawo maku hari matuƙar ba'a ga dawowar su gida ba..
Shiru suka yi dukkan su kafin su amince zasu kwana a nan ɗin amma da sharaɗin ba zasu yi bacci ba dan ba wai gama yarda da shi suka yi ba musamman Juda da take ganin kamar tana tsallake sharaɗin kakan ta na kar ta yarda da kowa dan mutani basu da amana..
Nuna masu ɗakunan su yayi suka shige suka zazzauna ɗakunan su na kusa da na juna amma bayan tafiyar Baccus sai suka dawo suka haɗe a ɗaki ɗaya suka yi zaman jiran sakamako dan kar abin ya juya..

★★★
Wuraren safe bacci ya ɗauke su sakamakon hana kawunan su bacci da suka yi a jiya,a can ɓangaren Baccus kuwa bai runtsa ba dan har kamar ya fi Juda son ɗaukar fansar abin da Sultan ya mai dan ƙarar mai da family yayi kaf bai bar sa da kowa ba..

Ko da ya koma ya duba su sai ya ga suna bacci dan haka ya bar su saboda ya san bacci ne basu samu ba a jiyan shi ya haifar masu da wannan baccin safen..
Basu tashi ba sai da rana ya ɗaga sannan suka fito suka nufi hanyar ɗakin da Baccus ya saba kasancewa..
Bayan gaisuwa sai ya fara yi masu bayani akan abin da ya gano a binciken nasa na jiya..
"Na gama duk wasu binciken da ya kamata in yi kuma na gano mafita ɗaya cikin wannan binciken nawa,wato na gano wani addini da wannan sarki ya kamata ya ɗabbaƙa a masarautar nan nasa amma ya hana ya kuma hana wasu ƙasashen dake ƙarƙashin ikon sa yin wannan adinni,a bincike na na gano cikin kundin ki akan an so faɗaɗa wannan adinni sama da shekaru arba'in da suka wuce amma sakamakon hawan wannan sarki mulki sai komai ya lalace ya ruguje aka ti fatali da batun addinin nan sai dai a binciken an kuma faɗin wannan addinin ce kaɗai zata wargaza wannan sihiri nasa,wannan addini ce kaɗai zata ƙasƙanta sa dan shima ya ƙasƙanta wannan addini tun ba yau ba kuma wannan ne kaɗai hanya mafi sauƙi da za'a bi a wargaza komai da ya mallaka da wanda yake da burin mallaka kamar dai wannan kundi naki dan haka kamar sai an samo masani a wannan ɓangare wanda ya fi mu sanin ma'anar wannan addini wato islam kamar dai yadda na gani a cikin kundin ta haka ne kaɗai za mu iya shigar masarautar nan dan nemo masani yayi ya saka sa ya tsaface masa masarautar da sihiri kashi uku wanda duk an harhaɗa ilimin addinai uku ne daban daban a wannan sihiri.,me kuka gani dangane da wannan shawara"??..

Duk ajiyar zuciya suka sauke kafin Juda ta ce wani abin
"Me za'a iya yi bayan wannan shawarar dan lokaci ne zai yi ta tafiya ba tare da mun san madogarar mu ba"!ɗam murmushi Baccus yayi hanin uneasiness a kan fuskar Juda
"Akwai wata hanya amma tana da hatsari dan kuna iya shiga amma fitowar ku ce ba tilast ku fito da lafiyar ku garau ba me kuka gani"?kallon kallo suka ma junan su sai Balik ya kuma tambayar Baccus
"Ina dai babu wanda zai rasa ran sa dan an bi wannan shawarar"?ɗan kasaƙe Baccus yayi kafin ya ce
"A'a"daga haka bai kuma furta komai ba sai da Juda ta yi magana
"Toh mun amince ka bamu sirrin wannan hanya dan abubuwa ne da yawa a gaban mu"!!gyaɗa kai yayi sannan ya ce da su
"Kun ci abinci ne dan na ga kamar baku ci komai ba tun jiya"!!hankulan su a tashe yake dan haka amsa mai kawai suka yi akan zasu ci abincin ba dan suna buƙata ba..

★★★
_SOME MINUTES LATER_
Suna zaune gaban the great bear seller Baccus suna sauraron bayanan sa da yake masu na hanyar da zasu bi su shiga maaarautar..
Kaf bayan ya gama yi masu bayani suka miƙe suka mai sallama sai ya dakatar da su akan su jira sa zai biyo su da haka shima yayi shirin sa na yaƙi da bai taɓa yi ba..
Tare suka fito duk da nufin a yau su tunkari masarautar Ottoman su yaƙi Sultan dan mugayen abubuwan da yake yi yayi yawa ko me ma zai faru ya faru a wuce wurin tunda dama ba a samin abin da ake so sai an yi asarar rayuka..

Fitowa suka yi suka hau dawakan su suka fito daga yankin kasuwa suka wuce ta hanyar gabas da ƙudirin sauke dawakan su a ƙofar masarautar Sultan Baal-Hamon..


*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 09:01] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:45&46*
Babu inda suka dakata tun

Please Login or Register in order to submit comment