Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin suma suka amsa mata da ido..
Rage ƙarfin yaƙin su suka yi suka rinƙa kaiwa iska hari suna faɗa yayin da su Fianna da Callee suka dage suna yaƙar ta.
Sai da abin yayi tsamari sai ta yar da jakar ta take abubuwan ciki suka fita.
Idanun Fianna ne ya kai kan kundin Juda ai tun kafin ma Callee ta ankara tuni Fianna ta kai hannun ta ta ɗau kundin nan jiki na ɓari ta kalli sauran tana mai nuna masu takobin hannun ta haɗe da faɗin
"Kar ku kuskura ku biyo ni dan zan iya kashe ku musamman wacce ta matsu da son sai ta ƙwace wannan kundin dan haka ku raba kan ku da ni".abin mamaki sai ga Fianna ta murzawa idanun ta toka sam ta manta tare suke da Callee kuma ga abokan tafiyar su da suka samu sai ta ba kowa mamaki hatta da Callee da ta kasance abokiyar tafiyar ta sai da abin ya ɗaure mata kai shin dama Fianna bata da amana dama!?..
Daga haka act ɗin ya dakata duk suka dare dama already Callee ta sake da lamarin Fianna dan haka tsaye take a gefe tana kallon Fianna dake ƙoƙarin barin wurin tana saka kundin cikin jakar tafiyar ta,.
Matsowa Agneta tayi kusa da Fianna tana ƙare mata kallo ko da bata san ainihin dalilin su Juda na yin wannan abin ba ta gano wani abu dake ɓoye a yanzun ɗin dan haka tana nufo ta ta miƙo hannu sai Fianna cikin tsaurin ido ta fiddo takobin ta tana son kawowa Agneta hari.
Kamar ƙiftawar ido Agneta ta ɗauke ta da mari ta kuma sauke mata wani haɗe da fincike takobin ta wurgar sannan ta ingiza ta ta faɗi ƙasa haɗe da ɗauke jakar da ta saka kundin a ciki tana numfashi da sauri da sauri dan abin cikin seconds tayi sa shi yasa ta ji nunfashin ta na ɗan sama sama.
"Ke zalamammiya ko?wato muna yawo da zalamammiya marar amana da aminci ko?mu zauna muyi magana da ke mu yarda akan matsaya ɗaya amma ki mana yankan baya?toh bara ki ji in sanar da ke wani abu kin ga Juda nan"?ta faɗi tana nuna Juda da yatsa sannan ta maido da duban ta ga Fianna ta cigaba
"Toh ta fi ki daraja da sanin abin da ta saka kan ta akai,dalilin ta na gano tuntuni ina cikin duhu da ɓacewar basira,haɗuwa da ita na gano matsala ta dan haka ke baki isa ki janyo mana koma baya cikin wahalar da muka daɗe muna yi ba dan ina da tabbacin da saka hannun ki cikin kasa gano wannan mutumin tukunna ma daga wace ƙasar kika fito"!!?cikin hargagi da ɗagin murya Agneta ta mata tambayar wanda abin ya ba dukkan su mamaki dan sun rasa ya aka yi tayi switching cikin blink of an eye..
Kallon ta Fianna tayi tana son ɓoye mata sunan ƙasar da ta fito sai dai mugun banzan kallon da Agneta take kai mata ya sa ta furta cikin ɗaukewar tunani
"Oman"!!sai gaban Agneta ya buga bugun da sai da yayi sanadiyar ɗaukewar ganin ta dan daina gani tayi.
A take tunane tunane suka rinƙa yawo mata a kai ba dai turo ta sarki Malik yayi ba dan ta cika mai burin sa da ita ta kasa cika mai ba?.
Tambayar da ta ma kan ta kenan sai ta tashi tsaye tana kallon Fianna ta ja da baya ta haɗa bayan ta da jikin wani bishiya.
Juda da su Berenice sun gano sanyin da Agneta tayi dan sun san labarin ta dan haka sun san tunowa tayi da ƙasar da ta fito da kuma azabar da ta sha cikin rashin sani..
Berenice ce tayo kan Agneta ta kwanto da ita jikin ta sai ga Agneta na ruwan hawaye tana kuka sosai ita kuma tana rarrashin ta sai Fianna ta saku tana kallon Agneta daga bisani ta maida idanun ta ga suturun jikin Agneta sai a nan ta tuno siffar Agneta da sarki Malik ya fasalta mata dan har irin yadda yake holewar sa da ita sai da ya fasaltawa Fianna sannan ya suffanta mata ita akan ko da wataran a tarihi zata ga Agneta ita kuma bata taɓa tunanin nan kusa zata haɗu da Agneta..
Tashi tayi ta miƙe tsaye ai ko Juda bata bar ta ta numfasa ba ta fara gasa mata maganganu akan tarihin Agneta a masarautar Oman kaf babu abin da ta rage sai wanda ba'a rasa ba haka abin ya ɗaurewa Callee da Fianna kai sai da Callee ta ji a jikin ta dan ita kam abin da ya fito da ita daban ba kundin nan bane amma kasancewar ta haɗu da Fianna sai ta ƙi zayyane mata ainihin gaskiyar lamarin ta barwa kan ta amma kuwa wani abin ne daban ya fito da ita daga inda ta fito sannan ta lura duk sun girme ta sai ta natsu dan ta ƙaru da wayon su da faaahar su dan ta sami abin da ya fito da ita.
Amma wannan abin da Fianna ta mata ta kuma yi wa sauran ya sa ta ji kawai ta faɗi inda ta fito ƙila itama ayi nasarar samin wanda ya fito daga ƙasar da ta fito dan haka ta yi ƙasa da kai ta ce
"Ku ji mana"!!sai aka maida hankali kan ta ana kallon ta,sai da ta ɗan ɗau lokaci sannan ta ce
"Ban sani ba ko ya zaku ji abin nan amma daga ƙasar _Babylon_ na fito kuma ni ba kundin nan ya fito da ni ba wano abin ne daban ya fiddo ni amma ganin Fianna ya sa na ce nima abin da ya fito da ita ya fito da ni sannan haɗuwar mu da ku sai na ɓoye maku ƙasar da na fito dan in ƙaru da ilimin ku amma bayan hakan ba komai mai kama da kundi ya fito da ni ba ku yarda da ni"..!
Tun da Callee ta fara maganar nan Juda ta sake sakamakon jin sunan ƙasar da tace ta fito dan haka zuciyar ta ya fara raya mata abubuwa daban daban kan ta ya fara ƙullewa ta kasa cewa komai.
Fara takawa tayi tana nufar Callee jikin ta na ɗan rawa idanun ta na son hasko mata wani abu..
Tana zuwa ta riƙo hannun ta ta buɗe baki cikin sanyin jiki tana faɗin...


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:00] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:41&42*
"Kin ce daga Babylon kika fito Callee"?gyaɗa mata kai Callee tayi tana mai jin nadamar ɓoye asalin ta da tayi tun fari sai Juda ta ɗan ji faɗuwar gaba kafin ta ce
"Ni ma..daga Babylon na fito sai dai yankin mu daban da naku dan ƴan yankin mu ba haka suke shiga ba"!cikin ɗar ɗar Callee ta ɗago idanun ta ta ɗora su bisa fuskar Juda sannan ta amsa mata da
"Eh,yankin da na fito ya yanka hanya ya shiga ta kudancin ainihin ƙasar Babylon kuma mu mutanin yankin mu da yawan su ƴan gudun hijira ne amma akwai ɗaiɗaiku da suke ainihin ƴan yankin"!!kallo ne ya dawo kan su,duk sai suka maida hankali kan su Juda da son gano wani abu game da Callee..
Ɗan kasaƙe Juda tayi kafin ta dubi Callee ta fara yi mata wasu tambayoyi
"Dama ke ƴar gidan mayaƙa ne ko kuma tsinto ki aka ui aka koya maki yaƙin sannan menene ainihin abin da ya fito da ke daga yankin ku zuwa nan Ottoman"?ɗan shiru Callee tayi kafin ta amsa tambayoyin Juda
"Eh,ni ƴar gidan mayaƙa me dan mahaifi na a yawon yaƙin sa ne ya haɗu da mahaifiya ta ya aure ta ya baro ta da yankin ta da ƴan uwan ta sannan abin da ya fito da ni daga yankin mu zuwa wannan yanki na Ottoman ba komai bane face fansa da ramuwar abin da sarkin wannan masarauta ya min dan ya cutar da ni da ahali na fiye da tunanin mutum"!muryar ta ne ya fara sarƙewa yayin da take maganar dan haka tayi shiru kawai ta bar maganar dan in ta cigaba toh tabbasa da kuka zata ƙarasa maganar haɗe da ɓacin zuciya..
Babu wanda bai fahimci shirun Callee ba dan kowa has a story to say amma na wani ya fi na wani shi yasa babu wanda ya takura mata akan sai ta kai ƙarshen batun ta dama iya tambayoyin da Juda ta mata kenan dan haka ta amsa su ko da ba cikakken amsa bane..
Ɗan share hawayenm tayi tana jan hanci ta cigaba da magana kamar haka
"Ban yi zaton sarki Sultan Baal-Hamon ya ƙwarai a zalunci da ƙeta har haka ba sai da na shirya fitowa farautar sa inda a nan na haɗu da wasu mutani biyu,mace da namiji..shi namijin ya taɓa taimaka min a wata rana da nayi dare na rasa wurin kwana sannan bana jin wani ƙarfi a jiki na sai da na tsaya a hanya na rage gajiya sannan wannan mutumin ya zo wucewa sai ya gan ni,a nan ya tambaye ni ko ɓatar hanya nayi na ce da shi a'a sai na mai bayanin abin da ya fito da ni,da fari kamar ba zai taimaka min ba sai kuma ya taimake ni har ya kai ni gidan sa sai na ga wata budurwa,a cewar sa ita ce matar da zai aura,a nan gidan na kwana sai a washegari ya rako ni hanya mafi sauƙin kawowa wannan masarauta sannan ya sanar da ni cewa duk wanda na gani a wannan hanyar toh in san da cewa gidan masarauta zai tafi kuma masarautar sarki Sultan Baal-Hamon dan haka in bin shi mu tara hanya amma kar in yarda in bayyana abin da zai kai ni masarautar illa in an tambaye ni in ce ai abin da zai kai mutumin shi zai kai ni".
"Ya ce da ni in yi wayo a tafiya ta sannan in yi abin da ya kamata dan shima yana nan a hanyar zuwa wannan masarauta domin ɗaukar fansar abin da aka mai shi da ahalin sa,abin da ya bani mamaki kenan na ga ba ni kaɗai wannan sarki ya zalunta ba kenan ashe har da wasu".
"Mun rabu bamu san sunan junan mu ba zan wuce na ɗaga murya na tambaye sa sunan sa sai ya amsa min da_'Cah'_ daga haka ban ƙarasa jin sunan ba sakamakon bige ni a kai da na ji an yi wanda ba kowa bane illa Fianna".tana kaiwa nan aka maido ido ga Fianna dake tsaye tana bin su da ido kamar marar gaskiya..
Cigaba da magana Callee tayi
"Ko da na buɗe ido na sai na gan ta a kai na tana tambaya na ina ma fito kuma ina zan tafi sai na rasa amsar bata sai na kawar da kai na.toh da yake ta girme ni kuma ta fini girman jiki sai tayi nasara akai na ta yaƙe ni,abin bai zo mana da sauƙi ba sai da muka yi sosai sannan na ce da ita masarautar Ottoman zan tafi sannan na ga ta ja baya,a ƙalla kwanakin mu uku tare a wannan jejin da na farka na tsinci kan mu a ciki,sai a rana na huɗu ne muka cigaba da tafiya sama sama mukan ɗan yi magana wanda a cikin maganan ne nake daɗa tantance baƙin hali irin na Sultan Baal-Hamon kuma a tare da ita na daɗa gano amfanin sirri dan Fianna bata da sirri komai faɗa min take yi ni ban san dalili ba".
"Wata rana mun yi dare sai muka dakata a wata mashaya dan rage gajiya sai muka sa aka kirawo mana mai mashayar dan mu mai bayanin saboda ya bar mu mu kwana a nan wurin,bayan an kirawo sa ne sai muka gan sa da shirin mayaƙa abin ya bamu mamaki muka rinƙa kallon sa sai ya ce da mu kar mu yi mamakin ganin sa a wannan suffar dan shi haka yake kullum cikin shirin ta kwana dan jiraye yake da mutanin masarauta Ottoman yana iya yiwuwa da haɗin bakin mu aka turo mu dan mu zo mu yaƙe sa ko mu kawo masa hari"
"Bayanin komai muka masa dangane da abin da muma ya kawo mu nan ɗin sai shima ya fara bamu labarin kan sa inda a nan yake nuna mana ai yanzu ba zamu taɓa samin galabar shiga masarautar ba dan an tsaface sa da baƙin sihiri babu mai iya shigar sa kai tsaye sai amintaccen ɗan gidan amma mu bari nan da kwanaki ashirin mu dawo gare sa zai taimaka mana mu shiga da sharaɗin muma zamu taimaka masa"
"Ko da muka kwana muka bar wurin ni da Fianna a nan muka bar mai shawarar sa dan gani muke surutu kawai yake yi saboda shekarun sa sun fara ja,a daren muka nufi masarautar sai abin da ya ce da mu ya faru muka gani da idanun mu,sai a sannan muka yarda da batun sa amma Fianna na ta ƙoƙarin goge min abin a kai na ni kuma na nuna mata mu koma gare sa dan sanin menene sihirin"
"Da muka koma bamu gan sa ba sai da dare dan haka muka mai bayanin komai sai ya mana dariya ya ce ai ya faɗa mana muka ƙi yarda ya ce da mu shekarun sa sama da ashirin da biyu yana harin masarautar nan amma bai taɓa yin galaba akan sa ba a cewar sa shi ɗin daga ƙasar Cyprus ya fito kuma abu mai muhimmanci ya fito da shi amma sakamakon rashin nasarar da yake ta samin sa dole ya haƙura ya kafa sansanin sa a nan Ottoman ya kuma kafa kasuwancin sa inda har baki ɗaya yankin Ottoman suka san sa da wannan sana'a tasa wato na saida giya(popular bear seller)ya kuma sanar da mu sunan sa wato Baccus".
"Alƙawari ya mana akan akwai abin da yake jira ya iso hannun sa dan ya shigo garin ko amma bai kamo hanyar zuwa gare sa ba amma yana shigowa zai warware wannan sihiri kuma komai zai zo ƙarshe dan haka muka yi da shi akan zamu rinƙa ziyartar sa lokaci zuwa lokaci dan jin ina aka kwana"..
"Tun bayan barin mu wurin sa bamu kuma komawa ba amma muka shirya cikin dare muka zo masarautar da kan mu a ranar ne muka haɗu da ku kuma ko a kwanakin da muka yi da ku muna fita nemo masanin sirrin sihirin nan duk muna sane kuma muna ankare akan cewa akwai mai taimakon mu amma ban san dalilin Fianna na hanawa mu je mu same sa ba"..

A nan ta dasa aya wanda ya bar su Agneta da Berenice cikin duhu da tunanin wai halan Fianna wace irin mutum ce ita..
Balik ne yayi ƙarfin halin tambayar Fianna dalilin ta na yin hakan ita kuma bata ɓoye masu ba ta amsa mai
"Ban da wata dalili da ta wuce na son samo komai da kai na dan alƙawari sarki Malik ya min akan in har na iya sarrafa duk wata matsalar da zata tunkare ni da kai na ba tare da taimakon kowa ba toh zai naɗa ni a mulkin da bai taɓa naɗa kowa ba sannan yace da ni zai ɗaukaka daraja ta fiye da na matar sa ni kuma na ɗau wannan alƙawari nasa a kai na na bar wa kaina sirrin komai akan bayan maganar nemar mai sanin sirrin sihirin ya lafa sai in saci jiki in koma gare sa in mai bayanin komai in ya so sai ya bani sirrin,toh sai kuma na ga abin da ya faru ɗazu na ga kundin da sarki Malik ke ta kwatanta min da kuma siffanta min sai na ɗauke a nufi na in koma wun wannan mai siyar da giyar in nuna mai in ya so sai ya warware min ban san akwai ɓoyayyiya a ƙasa ba sai yanzu"!!ajiyar zuciya Juda ta sauke tana mamakin Fianna da rashin wayon ta da take ma kallon wayo ne ita ya ta san ko da gaske shi mai siyar da giyar ba cutan ta zai yi ba ya ƙwace kundin ya gudu ba sannan ita ya bar ta a tutan babu..

Cigaba da kallon ta suka yi sai Berenice ta jefo mata tambaya babu alamar wasa a tattare da ita
"Wannan sirrin da kika ce sarki Malik ya baki ke kaɗai ɗin nan fah?ina ainihin labarin sa yake"?ɗagowa tayi suka yi ido huɗu da Berenice ta ga babu alamar wasa a tattare da ita sai ta ce
"Babu wani sirrin da ya bani kawai hikima ta ce ta in na koma wun wannan mutumi Baccus in ya sanar da ni sirrin sihirin sai in dawo in ce da ku mu tafi in muka tafi dama ai na nuna maku ni kaɗai ke da izinin amfana da sihirin toh a nawa in muka tafi ni kaɗai in shiga in aiwatar da abin da ya kawo ni in fito kun ga ni kaɗai nayi komai in na koma masarautar mu in sanar da sarkin mu sai ya cika min alƙawarin da ya ɗaukar min"..a yadda take bayani mutum zai yi tsammanin da gaske abin ba wahala kuma in aka yi nazari za'a tantance tsantsar shirme cikin zantuka da tunanin Fianna..

Still dai Balik bai bar ta ba ya kuma tambayar ta
"Toh dama tun asali me ya fito da ke daga masarautar ku"?ɗan natsuwa tayi dan tana gudun aikata shirme a karo na biyu a rayuwar ta sai ta amsa mai da
"Aiko ni sarki Malik yayi akan in shigo in nemi karuwar sarki Sultan Baal-Hamon in yi garkuwa da ita,ya ce min sunan ta Dacey kuma duk ya fi ji da ita a masarautar fiye da matar sa a wasu lolutan ma har ɗiyar sa gimbiya Acenath,ya ce da ni in nayi garkuwa da ita sai in saka ta aikawa a kirawo sarki Sultan toh a lokacin ne ni kuma zan aiwatar da abin da ya kawo ni masarautar"!daga nan tayi shiru..
Duk kallon ta ake yi ta ƙarasa zancen dan har wa yau bata ƙarasa faɗin abin da aka tambaye ta ba.
Da ɗan ɗagin murya Agneta ta ce
"Tambayar ki aka yi meye ainihin abin da ya fito dake daga masarautar ku sannan kin ma mutani shiru"!!amsa Fianna ta bayar da
"Cewa yayi in kashe sarki Sultan sannan in dawo mai da kan sarkin"!!kallon haushi da takaici ne Agneta ta bi ta da shi sannan ta ɗan kawar da fuskar ta tana tambayar ta
"Ya sanar da ke yadda zaki fita daga masarautar ba tare da an gane ke kika fille masa kai ba kuma da tabbacin cikin ƙoshin lafiyar ki zaki bar masarautar"?shiru Fianna tayi tana nazarain kalaman Agneta wanda babu ƙarya ciki sai gaskiya dan da zata yi tunani da kan ta toh tabbas sarki Malik bai fah sanar da ita hanyar mafita daga wannan aikin da ya saka ta ba..
Lallai saura ƙiris daƙiƙancin ta da son abin duniyar ta ya kai ta ya baro toh da ta tafi ta sami nasarar shiga fah sai ta fito yaya?..
Babu wanda ya ce da ita ƙala akaata shiru sai ta fara jin wani iri a jikin ta kamar bata kyauta masu ba dan ita kaɗai ce ta yi wauta ga Callee nan bata masu zamba ba sai ita kaɗai anya son kan ta bai yi yawa ba duba da alƙawarin da suka masu ita da Callee akan zasu taimake su su cika abin da ya fito da su amma ita kaɗai ce ƴar wayo da dabara da ta tsame kan ta ta fitar tana abu dan kan ta ba dan cigaban su su duka ba..
Muryar Callee ne ya dakatar mata da tunanin ta da ta faɗa tana yi
"Toh yanzu ai sai ki tafi ke kaɗai,,ki yi tafiyar ki kawai ba sai kin biyo mu ba dan ke ɗin mai son kan ki ne da yawa"..kallon ta Fianna tayi tana girgiza kai kafin ta ce
"A'ah babu inda zan tafi ina nan tare da ku nima ina buƙatar agajin ku kar ku ce in tafi kun ji"!kowa kallon ta yake yi dan gasgata zancen nata..
Da mamaki a ce har tayi saurin karaya nan kusa dan haka suka ɗan nuna rashin yardar su akan maganar nata sai da ta nuna da gaske take akan tayi nadamar abin da tayi sannan suka aminta da ita..
A taƙaice dai a wannan rana suka kuma sabunta alaƙar su baki ɗaya aka ajiye magana akan mai purpose da target goal nasu shine su ga faɗuwar sarki Sultan Baal-Hamon ƙasa warwas su ƙasƙanta sa ta yadda sai ya kunyata sannan su ga ƙarshen sa kafin kowa ya koma inda ya fito tunda duk target ɗin kowa cikin su shine wannan Sultan..
Daga ranar suke shawara tare komai tare ideas da thoughts nasu duk iri ɗaya suke sharing sannan sun yarda amana da yarda ta shiga tsakanin su dan abin ya masu daɗin tafiya..

★★★★
A yau ne kuma suka yanke hukuncin tafiya ganin wannan mai siyar da giyar kuma daga wurin sa su tafi kasuwar dawakai dan siyowa kan su dawakan saboda su sami sauƙin tafiyar da suke yi a ƙafa a kullum..
Bayan sun kammala shirin su me suka nufi hanyar kasuwar mashaya ta garin Ottoman dan ganin wannan mutumi mai suna Baccus dan shawartawa tare da shi akan abubuwan da ya dace..
Sun ɗan shafa tafiya kafin su kawo wun mutumin wanda tashin farko ya gano Callee da Fianna sai dai su Juda da ya kasa shaidawa sakamakon rashin sanin da ya maau..
Bayani Fianna ta mai daki daki akan komai da kuma zamowar su team members duk dan niya da ƙudirin su ta ta'alaƙa ne akan wannan azzalumin sarki wato Sultan..
A haka ne ma Juda ta mai bayanin abin da ta gani cikin kundin ta shi kuma ya fassara mata haɗe da ƙara jaddada mata kar ta yarda ta bari kundin ya kufce mata duk da ya san an ce kundin ya sami adana mai kyau da wuya ya ɓace nan kusa..
A nan ne Juda ta gane zalamar waɗannan sarakuna wato so suke su karance kundin tas sannan su laƙanci duk wani sihirin dake cikin ko wani shafi wanda dama dole sai mutum ya san wannan tarihi a kan sa babu gargada ko harhaɗa da cakuɗa labarai da tarihin sannan sirrin sihirurruka na nan a kan sa babu gargada toh a sannan ne zai zamo sarkin da zai amsa sunan sarki da zai mulki duniyar baki ɗayan sa..
In nutshell wato kowa so yake ya ƙarawa kan sa ƙarfi bayan wanda yake da shi kowa na son duniya haka kowa na kwaɗayin abin dake cikin ta wannan son duniya ina zata kai mutani..
Ita mammalakiyar kundin kan ta so take ta tsira da masoyan ta wato ƙanwar ta mahaifiyar ta da ƙannin mahaifin ta in ta haɗu da su lafiya ba ta hangen nesa amma ashe mutani da dama hararar duniyar suke..
Sannan tana fata ta sami damar barin wannan duniyar tasu ta tafi duniyar da aka ce mata komai na duniyar ya bambanta da wanda ta taso ciki bata fatan cigaba da zama a wannan duniyar bayan ta cika burin ta sam bata son cigaba da zama a duniyar nan..
Shirya komai suka yi akan nan da kwanaki tara zaau haɗu a hanyar

Please Login or Register in order to submit comment