Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana dakatawa tana shan ruwa har ta kawo wani madakata inda ta nemi wata bishiya ta zauna ta fiddo kundin dake cikin jakar ta ta buɗe ta ƙara kallon shafin da ta kalla jiya sai ta ji dariya ya taso mata ai kuwa ta shiga darawa tana yi babu ƙaƙƙautawa har sai da ta ji dariya ta ishe ta sannan ta daina ta dawo cikin hayyacin ta ta maida hankali ga shafi na gaba da ta buɗe sai ta ga suna kamar haka
  *_THE HERO OF OUR TIME:QUEEN BOUDICCA_*..

   Fara bin shafin tayi tun daga matakin farko(Paragraph)tana karantawa,natsuwa tayi tana bin karatun hankalim ta suka ya karkarta ga wannan labari wanda yake kamar haka..
  _BOUDICCA ta kasance sarauniya mata ga sarkin yankin Celtic cikin al'adar yaren Iceni,ta kasance amintacciyar sarauniya da ta tsinci kan ta dumu dumu cikin takabar rashin mijin ta wanda tun daga lokacin ta zamo mayaƙiya(warrior)wacce tarihin ta ya shiga kundi kundin tarihi kala kala.._
  _Marigayi mijin ta Prasutagus ya rigada ya bar ajiyayyen magana tun yana raye kafin ya mutu ya ce idan har ya faɗi ya mutu karagar mulkin sa zai dawo hannun ƴaƴan sa mata ne su biyu da makusantar sa amintacce dake a masarautar Romania(Roman Emperor wanda tunda aka kafa tarihin masarautar ba'a taɓa yin mulkin mace ba bare ma ya kai ga mata har biyu su ja ragamar mulkin masarauta.._
  _Duk da a ƙasar Romania(Rome)basu yarda da mulkin mata sai maza dan su ke da gadon tafiyar da masarauta ba mata ba.._
  _Toh bayan mutuwar Prasutagus sarki mijin Boudicca sai ƴan ƙasar Romania(Rome)waɗanda marigayi sarki Prasutagus ya fi yarda da su suka shigo ƙasar marigayi sarkin Celtic suka azabtar da matar sarkin eato sarauniya Boudicca sannan suka ma ƴaƴan ta mata fyaɗe waɗanda sarki ya bar ajiyayyen magana akan su akan in ya mutu su zasu hau ragamar mulkin su jagoranci mulkin masarautar,kaca kaca suka ma ƴaƴan suka azabtar da mahaifiyar su ta hanya daban daban wannan abin ba kaɗan ba yake tsayawa sarauniya Boudicca a rai.._

  _Wuraren shekara ta 60 A.D., sai sarauniya Boudicca ta ga ya kamta ya kuma cancanta su san abin yi da waɗannan mutanin da suka taso su gaba dan ba iya masarautar ta suka tsaya suka ma rashin imani ba hatta da jama'ar garin sun taso su gaba,dan haka sai ta nemi mutanin yankin dake yare ɗaya da ita dan a samo masalaha su sami sauƙi,ta sanar da su manufar ta akan son da take na su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yaƙi al'umar ƙasar Romania(Rome)su kore su su fitar da su daga ƙasar su baki ɗaya ta hanyar harhaɗa sojoji(Assassins)dubu ɗari(100,000)wanda zasu kasance daga masarautar ta zasu fito kenan ita zata basu oda ta haɗa kawunan su a matsayin nata gudunmawar.._
  _Sun yaƙi waɗannan mutanin kuma sun yi nasara wanda har ita kan ta Boudicca ta wurgar da matattun jikin ƴan Romanian cikin wurin bautar ƙasar Romania dake nan kusa da Burtaniya(Britain)..._
  _Sosai Boudicca ta yaɗa maganganu wanda ya bi ƙasashe waɗanda duk gargaɗi ne akan kar wanda ya kuma shigo mata ƙasar ta ba tare da amincewar ta ba,maganganun ta ya yaɗa wurare kamar Londinium(London)da Verulamium(St.Albans),ta dage ta yaƙi duk wasu masu yi mata kutse cikin al'amurun ƙasar ta ta tsaya kai da fata ta yaƙe su dan sai da ta feɗe mutani kusan dubu saba'in(70,000)zuwa dubu casa'in(80,000)duk ita kaɗai wanda wannan namijin ƙoƙari nata da ta yi da nasara nata ya saka Sarkin Burtaniya wato sarki Nero,ji kamar ya bar ƙasar sa dan mace ta zo ƙasar sa ta yaƙi masu son ganin bayan ƙasar ta shi kuma yana kan karagar mulki a matsayin sa na namiji bai iya aiwatar da wani abu ba,sha'awa ta bashi haɗe da birge sa ba kaɗan ba.._
_Duk da ma ƴan ƙasar Romania sun kuma dawowa sun yi yaƙi da sarauniya Boudicca har sun cinye yaƙin sun yaƙe ta abin ya zame mata kamar abin Allah ya kiyaye ne dan daga baya ma gasa abin ya dawo ita tayi ta cinye gasar haka suma su zo su yi wani lokacin su lashe yaƙin,haka ne ma ya sa ake tunani da tsammanin ta mutu ne akan dalilai biyu ko rashin lafiya sakamakon baƙin cikin da gasar ta haifar mata ko ta kashe kan ta da kan ta sakamakon baƙin ciki da mayaƙan ƙasar Romania suka ƙunsa mata.._
  _Duk da wannan rashin mutuncin da mayaƙan suka mata bata yi ƙasa a gwiwa ba ta dage sai da tayi aikin ta ta jajirce ta gyara ƙasar wanda hakan ya janyo mata martaba da ƙima a ƙasar Londinium(London).._
  _Har a gobe ana tuna ta da irin ƙoƙarin ta da jajircewar ta a ƙasar London da wasu ƙasashen da tarihin ta ya zaga dan ta zame zakaran gwajin dafi tun a zamin Victoria(Victoria era)._
  _A shekara ta alif ɗubu ɗaya da ɗari tara da biyu(1902)an ƙirƙiri wani mutum mutumi da aka rubuta Boadicea da ƴaƴan ta(Boadicea and her daughters) (Bronze Statue)dake nan wurin wani gada da ake zuwa kallo dake wurin Westminster bridge,  a ƙirƙirarren mutum mutumin an saka wata mayaƙiya na jan wani doki mai haɗe da kurar da ake maƙala dokin sarauta da shi tana nufar fagen yaƙi da wasu dawakai har biyu a gefen dama da hagun ta sannan a kan dawakan nan biyu akwai ƴaƴan ta mata da mayaƙan Romania suka ma fyaɗe suna ɗan giciye yayin da ita kuma ta ɗaga hannun ta sama tana mai nuna takobin ta ma iskar dake kaɗawa a sama.._
  _A saman gunkin aka saka Boadicea,Boudicca sarauniyar Iceni da ta mutu a shekara ta AD 61 bayan ta yaƙi ƴan kutsen mayaƙan ƙasar Romania..._

  Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Juda ta sauke da ta iso ƙarshen labarin wannan mace mai kama da mazan da ta bar tarihin da bata taɓa cin karo da shi ba ko a lokacin da kakan ta ke da rai wanda shi ke bata tarihi iri kala daban daban na mayaƙa duk dan ya kwaɗaita mata yaƙin kuma yayi nasarar kwaɗaita mata shi a ran ta musamman tanzu da ta karanta irin tarihin mace mai kamar maza ko ma mace da ta fi maza wun kare martabar ƙasar ta da ahalin ta duk dan ta samar ma mutanin ta zaman lafiya,gashi dai a yaƙin ta rasa ran ta amma ba'a manta da jarumtar ta ba lallai wannan ita ce mace da ta amsa sunan ta cikakkiyar mayaƙiya dan kasancewar ta sarauniya da aka san da zaman ta bai saka ta jin izza ko ganin ita ɗin ƴar sarauta bace ko sarauniya matar sarki ba da zata ƙi fitowa ta tsaya ma mutanin ta ba..
  Ta so ta san matar nan amma ta san lokacin da aka yi yayin ta a doron ƙasar nan ko kakannin kakannin(Ancestors)ta ba'a kawo su  duniyar ba wannan ma tarihi ne da ya rinƙa zagayowa yana yawo har ya kai kan mahaifin kakan ta da shi ne ɗan zamani da har ya zauna ya tsara wannan tarihi da ma sauran tarihin dake tattare cikin wannan kundin..
  Duk da ta san ba komai zata fahimta ba a yanzu in ta karanta kundin ba sai nan gaba in ta yi katari da matakin da ya kamata ta gan sa ido da ido  amma tana ji a jikin ta in har tarihin sarauniya Boudicca bai maimaita kan sa ba toh kaɗan zai rage ba'a kuma yin siffar yaƙin da ta yi ba dan kuwa duk alamu sun nuna sarkin ƙasar ottoman baya nimar sun wanue lafiya da shi dan kuwa shine misabbabin duk wasu matsalolin su wanda take saka ran in har tayi ido huɗu da shi mai ƙwartar shi daga hannun ta sai wani ƙarfin iko dan irin tsanar da ta mai ita kaɗai zata iya ƙiyasta shi...

  Rufe kundin tayi dan ta ji ran ta ya sosu so tayi ta kuma karanta wani shafin amma ta haƙura har sai ta sami wani lokacin dan yanzu tana da buƙatar ƙara yin gwaji saboda ta ga yaƙin dake gaban ta ba kaɗan bane babba ne..
  Fiddo da ganyen da ta rage abinci da taci jiya da dare tayi ta buɗe ta fara ci,bata bar wurin ba sai da tayi nak sannan ta miƙe ta cigaba da tafiyar ta tana tafe tana nazarin tarihin dake cikin kundin nan haɗe da son sanin ko me sarkin masarautar ottoman ke nufi da ya saka masu ido akan dole sai ya mallaki wannan kundin.wani ɓangare na zuciyar ta ne ya amsa mata da hala wani ƙulalliyar ke ciki kuma yana da buƙatar abin shi yasa..
  Ƙwafa tayi tana mai girgiza kai kafin ta kuma ɗorawa da wata tambayar kamar haka wanda a fili ta yi  shi
"Toh so yake ya mulki duniyar"?sai ta ce"hmm ko ma dai menene ya guji haɗuwar sa da ni"..
 
  Daga haka ta cigaba da tafiyar ta ita kaɗai har ta kawo wata daji da ta ji kamar ta tsaya a nan ta fara gwajin ta(training)tana yi tana kuma jin tsanar wannan sarko da bata taɓa ganin sa ba amma sunan sa da tarihin sa a rayuwar ra ya zame mata ruwan sha,abincin ci har ma da kuzarin ta na son yin abu ko da bata shirya ko ta yi niya ba.. 

  Sai da duhu ya fara mamayar wurin sannan ta ɗau jakar ta ta cigaba da tafiyar ta har ta kawo wani ƙauye dake da hasken wuta da alama dai wurin kamar mashaya ne(Bar) sai ta je can bayan mashayar ta kafa tantin ta ta shige ko wankar ma bata nemi wurin yin ta ba dan bata buƙatar sa..

  Kwanciya tayi ta gefe ɗaya tana sauke ajiyar zuciya har dai daga bisani ta rufe idanun ta bacci yayi awon gaba da ita..
  Can cikin baccin ta ji kamar ana tsaye kan ta ana ƙare mata kallo a lokaci ɗaya kuma ana kallon jakar ta da tayi matashi da shi,babu tsammani ta buɗe idanun ta kafin wani ƙwaƙwarar motsi har ta tashi tsaye riƙe da takobin ta..
  Fita aka yi daga tantin nata da gudu itama sai ta saɓa jakar nata a baya ta fito a guje tana bin wanda ya bar ɗakin ba tare da ta tsaya naɗe tantin ba,da iya ƙarfin ta take gudun kamar zata tashi sama,akwai ƴar tazara tsakanin ta da wanda take bin amma tsabar zuciya sai da ta tako wanda take bin da zuwan ta bata tsaya yin wani abin ba ta take rigar wanda take bin sai santsi ya kwashi wanda ake bin sai ga mutum a ƙasa tim..
  Da azamar ta da ƙarfin ta ta kai hannu tana ƙoƙarin yaye abin da aka rufe fuska da shi tana son sanin wanene wannan ɗin dake bin ta har ma yake hararar jakar ta hala ma daga cikin mutanin sarki Baal-Hamon ne,in ko haka ne toh sai ta lahanta wannan mutanin..
  Ganin za'a kware marufin fuskar  wanda aka biyon, kawai sai aka watso ma Juda ƙasa a fuska abin da ya harzuƙa ta ta kawo takobin ta gab wuyar wanda take bin haɗe da faɗin
"How about this move huhh"!?ɗif wanda ake bin yayi sai kawai Juda ta ga an saka hannu an yaye mayafin fuskar...  
  Baya ta ja da sauri tana mai buɗo idanun ta cikin tsantsar mamakin ganin wanda ke biye da ita...

*_ SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:38] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:11&12*

  Wata kyakyawar budurwa ce wacce ba zata yi ƙasa da shekaru ashirin da iku zuwa da huɗu ba kusan dai tsarar Juda sai dai kyawun wannam ƴar budurwar na daban ne dan har wani walwal take yi tsabar kyau da hasken ta ga wani irin naɗi da ke kan ta kamar sarauniya a masarautar farauta sai dai fuskar ta tamau take babu alamar wasa a tattare da ita wanda ya sa in ba kallon tsain ka mata ba baka gane cewa kyawun ta na iya ruɗar da maza..

Miƙar da hannun ta tayi da nufin tashi zaune sakamakon ganin irin kallon da Juda ke bin ta da shi wanda ya saka ta a duhu ta kasa tantance kallon tsoro Juda ke bin ta da shi ko kuma kallon farautar ta take yi.,
  Tana yunƙurawa zata tashi ta ji an kuma mai da ta ƙasa da matuƙar ƙarfi,jiyo nishi tayi gab da hancin ta wanda ya tsorata ta sai ta buɗe baki cikin masifa ta fara faɗa
  "Wannan wani irin rayuwa ne,ina zaman zama na ki shigo min rayuwa kina nemar yi min lahani akan me"?wani irin mugun kallo Juda ta bi ta da shi.
Lallai wannan ƴar rainin wayo ce da tunani,ta biyo ta har tantin ta tana nemar sace mata gadon ta sannan yanzu ta buɗi baki tana faɗin ita ce ta shigo mata rayuwa,ah lallai da alama wannan yarinyar bata san wacece ita ba sai ta gwada mata..
  Babu wani magana da ta bari ya shiga tsakanin ta da wannan budurwar,zaro takobin ta tayi wanda lokacin da ta tashi ta ɗan mayar gefen rigar ta,daidai saitin cikin ta ta kawo takobin da alamar daɓa mata shi take son yi..
  Ai kusmwa wannan budurwar na gani haka ta yi wani kukan kura ta hankaɗa Juda ta miƙe tsaye tare da zaro nata makamin mai ji kamar ƙahon dabba sai kaifi da haske,ta daidai wun ƙahon ta murza wani abu nan da nan ƙahon ya canza ya dawo takobi mai matsakaicin tsawo dan ya fi wuƙa tsayi sosai,kayan jikin ta ya dawo kamar jikin dodon koɗi(snail shell)zanen siffar dodon koɗin duk ya mamaye jikin ta sai ta nunawa Juda takobin tana haki tana kallon ƙwayar idanun Judan bakin ta na marmarin furta wata kalma amma ta kasa sakamakon fargabar da take ji..

  Ita kuwa Juda kallon iko take ta yi wa wannan budurwar ganin siddabarun(Magic)da tayi a gaban idon ta babu tsoro bare shakkar kar ta mata wani illah,kenan wannan ba da mugun nufi ta biyo ta ba dole wata dalili ko manufa tata ne ta kawo ta nan ɗin..
  Yin wannan tunani ya sa Juda maida takobin ta ma'adanar sa ta fuskanci budurwar ta ƙura mata ido tana ƙare mata kallo har sai da budurwar ta tsargu da kallon da Judan ke bin ta da shi
  "Why are you giving me that silent look"??cewar budurwar sai Juda ta girgiza mata kai tana mai cigaba da kallon ta kafin daga bisani ta buɗi baki ta ce
"Who send you here and why are you following me"?ɗan murmushin gefen baki tayi kafin ta bata amsa da
  "Am not out for your search"sai ta ɗan girgiza kai kafin ta cigaba"am out for a different purpose so i guess you are bluffing"!!!..murmushi ne ya kuɓcewa Juda dan budurwar ta bata dariya sai dai ita kuma dariya ba abin yin ta bane a gaban maƙiyin ta sai dai ta murmusa dan haka ta murmusan ta ƙure ta da ido sannan ta ce
  "Na ga alamar tsoro da fargaba da ɗawainiya da ke dan sam baki da wani ƙwarin gwiwa a yayin da kije magana da ni har kike musayar yawu da ni,,faɗa min,shin...daga ina kuma wacece ke dan na ga kamar you are lost"!!!banzan kallon budurwar ta ma Juda tana mata ƙasƙantacciyar duba mai kama da zanar guga kawai furtawar ce bata yi ba...
  Abin mamaki ita Juda dake  nemar masalaha da budurwar sai ga budurwar na nemar ɗaukar wata hanyar ta daban dan kuwa tsakanin ta kan gaskiya da gaskiya ta saka takobin ta saman wuyar Juda da nufin yaƙar ta..
  Da fari abin ya ɗan firgita Juda kafin daga bisani ta ce da budurwar
"Kar ki sake jini na ya fito ya sauka kan takobin nan naki in ba haka ba har mutuwar ki cikin jini zaki cigaba da kasancewa ban nufe ki da wata manufa ba dan haka tun kafin in rasa haƙuri na akan ki kiyi gaggawar rabar jiki na da takobin ki"!!!cikin hargagiya da hargowa budurwar ta ce
  "You are bluffing lady,,..sam ba zan cire ba sai kin sanar da ni me ke cikin wannan littafin da kike ɓoyewa,,yi sauri ki sanar da ni abin da ke ciki n shi"!!!...
  Shiru Juda tayi tana kallon ta ita ba tsoro budurwar ta bata ba mamakin ta take yi ganin irin rashin ta idon da take da shi ne ke ɗaure mata kai a ce wai da zafin ta da fushin ta ta sassautawa wannan budurwar amma ita kuma abin da zata saka mata da shi kenan..
  A zuciye Juda ta ingiza ta kafin wani abin ta nufo ta da takobin ta ta fara ƙoƙarin yaƙar ta ai kuwa faɗa ta kacame a tsakanin su yi suke yi kamar dama can da manufar faɗar suka zo dajin..
Abin yayi tsamari ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba faɗa sosai suka yi su da takubban su basu tsagaita ba sai da ɗaya ta kayar da takobin ɗaya sannan suka tsagaita inda cikin haki Juda ta fara magana
"Na nufe ki da lallami kar ki bari in ƙara tunzira in hukunta ki fiye da haka ina jin tausayin ki in ba dan haka ba da sai na kar ki...wacece ke sannan wa ya aiko ki gare ni"??kamar ƙiftawar ido wannan budurwar ta ture Juda daga saman ta ta cigaba da faɗa da ita suka sake komawa filin faɗar a karo na biyu wanda a wannan karon ba ƙaramin dambatuwa suka yi dan dukkan su sun ji a jikin su babu ciwo ko yanka ko ɗaya a jikin su amma kam jikin su ya amsa,share lokaci suka yi suna dambaruwa..
  Dan kan su suka dakata haɗe da wurgar da takubban su a gefen su suka tsaya kallon kallo ita dai Juda so take ta san wa ya aiko wannan budurwar dan bata gamsu da cewa nan ne ƙurewar ta ba,dan sun gwada yaƙi su biyu har suka kusa isa magajiyar juna hakan bai wani gamsar da ita ba haka bai birge ta ba...
  Ido cikin ido budurwar ke kallon Juda ganin tunda ta fito yawon farautar ta bata taɓa haɗuwa da mace ɗaya mai jin kan ta kamar doki sannan tana dambe kamar maza babu alamar gajiya tattare da ita ba kamar wannan budurwar dan haka take ganin me zai hana ta saukar da kai ta mata ladabin ƙarya dan ta ƙaru da ita dan ta lura zata matuƙar amfanar da ita dan cinma manufar ta in lokaci yayi. 
  Yanke wannan hukuncin tayi bayan ta gama shawartawa da zuciyar ta haɗe da yin na'am da wannan shawara tata..
  Idanun ta na cikin na Juda ta canza murya daga na ƴan farauta ta sassauta shi ta salamta shi zuwa na mutani masu galihu ta fara rero kalamai da zuciyar ta ta shimfiɗa mata kamar haka.
  "Na san kina da tambayoyi kala kala a zuciyar ki game da ni,wacece ni me kuma ya haɗa ni da ke da har nake kalle miki littafin da kika ɓoye cikin jakar ki,,.toh ni dai abu na fari da nake so da ke shine ki bani hankalin ki ki kuma yi ƙoƙarin fahimta ta in ya so bayan na gama baki labari na sai kiyi abin da kika ga ya dace zaɓi zai rage naki ba nawa ba"..

  Shiru Juda tayi tana bin ta da ido tana nazarin ta tunani take ta yarda da ita ne ko kuwa ta ja bata ne,take ta tuno da huɗubar kakan ta na kar ta yarda da kowa dan kowa maƙiyin ta ne ana iya amfani da kasawar ta da yanayin amincin ta a cuce ta in tayi wasa..,
Har ta yanke hukuncin tunkarar budurwa ta shafe tarihin ta sainkuma zuciyar ta ta fara gargaɗin ta akan kul Juda ko ba komai ki bata kunnuwar ki ki ji da ne ta zo dan ki san ta yadda zaki fuskanci al'amarin dan yana iya yiwuwa ta zame maki hanyar samin nasarar ki kuma ko ba dan haka ba da gani kin san wannan budurwar abu ne ya fitar da it,toh me zai hana ki mata ladabin kura ki nuna mata kina tare da ita dan ki gano me ke tafe da ita na ainihin dan alamu kaf sun nuna wannan budurwa ƙarya take shirin shirya mata sam babu ƙamshin gaskiya cikin lafuzan ta na shimfiɗa...
 
  Gyara tsayuwa Juda tayi tana mai saka fuskar yarda da budurwar ta ɗan gyaɗa kai haɗe da faɗin
  "Ina jin ki"!!cike da ɗumbin mamaki ta kalli Juda,tayi tunanin hala abin da zai faru tsakanin ta da Juda dambe ne sai ta ga akasin haka lallai tsuntsu daga sama gashasshe ya faɗo mata lallai ta amsa sunan ta na sarauniyar mafarauta tunda har ta iya farautar zuciyar wannan mace mai kamar mazan ba tare da ta wahala ba cikin salama ai ita tayi dace ba kaɗan ba ashe ma duk muzuran na kan fuska ne cikin zuciyar nata a karye yake..
  Wani gigitaccen kallo budurwar ta bita da shi mai kama da kallon a tausaya min ni da rayuwa ta,bude baki tayi ta fara magana.
  "Ni sunana Berenice,na fito ne daga masarautar Mughal a inda na kasance mace ɗaya cikin ahali na dan dukkan mu ƴaƴan mahaifin mu ni kaɗai ce mace cikin jerin mazaje ɗaiɗai har takwas,mahaifi na ya kasance shahararren ɗan farauta da yayi ƙaurin suna kaf Mughal da kewaye kuma kowa ya san shi dan dagewar sa da jajircewar sa akan farauta sai daomi in bai saka kan sa akan yin farauta ba amma yana ɗora idanun sa akan abu toh baya barin abin nan sai ya farauce shi,toh duk cikin yayye na babu wanda yayi gadon sa sai ni ni ɗaya wanda hakan ya sa ya fi ji dani har yake min kirari da sarauniyar mafarauta har dai sunan ya bi ni ko ina ana kira na da sarauniya.."
"Wata rana an mana kira ni da mahaifi na zuwa ga masarautar Mughal(Mughal empire)a inda sarkin masarautar ya nunawa mahaifi na da ko ya bar batun faraurtar da yake mai a ƙasa kokuma ya saka masu tsaron ƙasar su kora mu mu bar mai ƙasa,sai mahaifi na ya ce sam ba zai iya yarda ya bar farauta ba dan farauta ta mai rana har da ma dai ta mai illah dan sanadiyar farauta ya rasa matar sa mahaifiyar mu dan haka ba zai amince da wannan shawarar ta sarki ba dan shima ɗin sarkin kan sa ne a tasa masarautar.."
  "Abu kamar wasa bayan mun koma gida sai muka ji sammaci a kotun masarauta inda aka ɗauke mu ɗungurgun aka kai mu can inda muka fuskanci matsi mai tsanani akan ko mahaifi na ya ja baya kokuma a kora mu mu bar ƙasar,a nan mahaifi na ya nuna masu ya amince aka sake mu muka dawo gida sai ya ɗan kwana biyu bai fita farautar ba kwatsam sai kawai aka kawo mana hari aka kashe min kaf ahali na dukkan simu ni kaina da ƙyar na gudu na nufi wani sansani daga haka na fara nemar hanyar da zan tsira da lafiya ta da haka na rinƙa farautar sojojin da suka kawo mana hari ɗaya bayan ɗaya har nayi nasarar hallaka su kaf ba tare da an san wanda ke kashe su.."
  "Toh ɗazu da yamma ina zaune a inda nake rayuwa ta sai aka kawo min farmaƙi aka kusa raba ni da rayuwa ta da ƙyar na ƙwaci kai na na gudo na zo nan wurin kusa da mashayar nan sai na ga kamar har lokacin nema na ake yi sai na fito a ɓoye ina nemar mafaka,hango tanti nayi sai na shiga ciki ba tare da nayi la'akarin akwai mutum a ciki ba.."
  "Tsoro ne ke tattare da ni wanda ya saka ni kasa zama na tsaya ina kallon ki har kika farka kika gan ni dan duk hanyar da zan rufe fuska ta kar a gane ni ina bi amma ke kuma sai kika gan ni a zahiri,da fari na so kashe ki ne

Please Login or Register in order to submit comment