Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan kar ki tona min asiri amma sai na ga kin min rangwami cikin ƴar ƙaramar yaƙin da muka yi da ke wanda hakan ya nuna min cewa ke ɗin mai tausayi ce kuma ina iya yarda da ke nake ga kamar in na sanar da ke tarihi na kina iya taimako na in sami ƴancin kai na a ƙasa ta sannan ki taya ni rama cin amanar da sarkin masarautar Mughal ya min ni da ahali na"..da hawaye ta ida zancen nata wanda ko kaɗan bai wani ɗaɗa Juda ba dan ta san duk zancen ƙarya ne in ba ƙarya bane me ya sa bata sanar da ita illar mahaifin ta ba da ya sarkin Mughal ya taso su gaba ba akan ko su daina farauta ko ya kora su wajen ƙasar sa,sannan bata sanar da ita ta yadda ta baro ƙasar ta ba har ta tsinci kan ta nan kusa da ƙasar Babylon ba,bayan wannan ya tayi rayuwa tun lokacin har kawo yanzu da suka haɗu sannan bayan wannan ma tun yaushe wannan abin ya faru da ita tsayin wani lokaci ta ɗauka tana rayuwa ita kaɗai,ya kuma aka yi ta ga ta gamsu da ita har take fayyace mata sirrin ta haka nan daga haɗuwar yau ɗazu ɗazun nan lallai akwai tambaya da bincike cikin zantukar wannan budurwa da ta ce sunan ta Berenice ne hala har sunan ma ba nata bane dan wannan ta shahara a fagen tsara ƙarya fuskar ta kaɗai ya isa ya nuna ma mutum hakan kyawun ta ne kaɗai ke iya ruɗa mutum har ya ji ya kasa tambayar ta ta faɗa mai gamshasshiyar magana amma ita kam sam ba zata yarda da Berenice ba bare tayi gigin sanar da ita abin da take son ji dangane da it..
  Amma kafin nan dole itama ta saka mata tausayin ta na ƙarya dan dama an ce in baka iya kama ɓarwo ba toh shi zai kama ka..
  "Na tausaya maki matuƙa Berenice kuma ki sani ni na amince da ke haka na yarda da ke kuma zan taya ki karɓo haƙƙin ki daga wun azzalumin sarkin masarautar ku"!!!..
  Bambaraƙwai Berenice ta ji abin wai anya kuwa ita ta kamo wacce ya kamata ta kamo kuwa?ta yaya tana ta shan kwana sannan wannan budurwa bata son bin hanyar kwanar ne wai?ta mata ƙarya ta nuna mata ta yarda da ita ta so ta ji sunan ta amma bata sanar da ita ba sannan ta so jin tarihin ta aa budurwa ta ƙi yarda ta sanar da ita anya wannan mace ba aljana bace?lallai in tayi wargi hannun ta ba zai taɓa hawa kan wannan littafin da ta daɗe tana mafarkin taɓawa ba...

  Ajiyar zuciya ta sauke haɗe da nufo Juda da nufin rungune ta sai dai hakan bai yiwu ba dan kuwa takobinm Juda ta saka a tsakankanin su tana mai nuna wurin da ya fi kaifi ga cikin Berenice tana girgiza mata kai haɗe da faɗin
"Kar ki kuskura,,kawai ki tsaya a haka na fahimce ki na kuma san murnar ki na samin wacce ta yarda da ke,,dan haka ki riƙe annashuwar ki har sai mun taya ki cinma burin ki ina fatar kin fahimta"?ta ida maganar tana mai ɗage mata gira ɗaya sama wanda ya kaɗa Berenice dan ta ɗauka ta haɗu da wawiya ce marar wayo sai dai a yanzu ta fara ganin kamar ita ce marar wayo lallai tsugune bata ƙare ba...
"Nagode da wannan tarbar da kika min cikin zuciyar ki duba da cewa baki san ni ba amma kin yi na'am da ni cikin zuciyar ki wannan kaɗai na san zai bada wata babbar yarda taki cikin idanu na kuma na maki alƙawarin duk abin da kike nema zan taya ki ki same shi kawai ki yarda da ni"!!murmushin wautar Berenice Juda tayi dan ɓaro ɓaro ta ga rashin wayon ta amma ba zata taɓa fitowa ta nuna mata ta san ƙarya take ba dan in ta nuna mata zata  fi ta zamowa wawiya dan haka kawai ta bar wa kan ta sanin matakin gaba da zata ɗauka akan Berenice...

"Kar ma ki damu dan in nice sam ban da wata damuwa"abin nan ya ɗaurewa Berenice kai ba kaɗan ba sai dai ta yarda da kalmar a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe..
Murmushin ƙarfin hali tayi kawai ta gyaɗa kan ta sai Juda ta maida takobin haɗe da kallon Berenice tana mai ce da ita
"Ni na tafi dan ina da saurin bacci yanzu sai mi ga na fara bacci a nan tsayen da nake"da sauri Berenice ta kallo Juda tana nazarin zancen ta kenan in har ta ce tana da saurin bacci cuta ne da ita na baccin irin na litattafai da baban ta ke bata labari,ai kuwa ta gode dan tana iya amfani da kasawar ta ta fannin baccin nan ta ɗauke littafin tayi wucewar ta..
Ƴar dariya tayi sannan ta ce
  "Mu tafi in bi ki dan nima ban da mafaka a kowani lokaci waɗannan mutanin na iya biyo ni su ɗau rai na"..kallon ta Juda tayi sai ta ce
"Ba matsala mu tafi"daga haka suka fara tafiya suna nufar hanyar da ta kafa tantin ta da bata naɗe ba har suka ƙaraso ita dai Berenice tayi jiran tayi jiran har ta gaji tana ta son jin sunan Juda amma sam Juda bata bata fuska ba ainihi ma nunawa tayi kamar ta fara magagin bacci wanda ya saka Berenice cikin farin ciki...
  Suna isowa tantin Juda ta ja ta tsaya ta ce da Berenice
   "Shiga mana"sai ta saka kai ta shiga tana ɗan ɗari ɗari sai Juda ta ɗan yi murmushi tana kallon ta ita wannan ma bata san meye duniya ba kawai ɗan ƙanƙanuwar basirar da aka dasa mata ne take amfani da shi bata da nata wayon,in ko har ta gano Berenice cutar ta tazo yi toh dole ta kashe ta dan zama da mugu babbar kuskure na a rayuwa...

  Lafiya ƙalau suka zauna yayin da Berenice ta dangana da Kwanciya tana mai faɗi mata sai da safe itama Juda ta mata sai da safe ta kwanta ta rufe idanun ta kamar baccin ne ke fizgar ta..
Bayan wasu lokuta Juda na nan kwance ta ajiye jakar ta carelessly kamar bata damu da shi yayin da Berenice ta daɗe da kaiwa jakar hari jira kawai take Juda ta juya sai ta warci jakar tayi gaba..
  Kamar Juda ta san abin da take hasashe sai ta juya ta bata baya ai kuwa Berenice ta yi wuf ta kaiwa jakar damƙa ta tashi zata fita sai ta ji ƙafar ta ya sarƙe kafin ta sani ta tsinci kan ta a ƙasa..
  Babu wani tantama Juda ta kai mata yanka a hannun ta daidai damtsen ta ta yage mata hannun rigar ta tana mai ce da ita
  "Wannan kike nema ko"??haɗe da nuna mata littafin kundin sai Berenice ta zaro idanun ta tana daɗa girman su cikin jimami da wayon rashin wayon ta da ta yi zaton wayo ne dama haka take da wayo har haka ita bata sani ba

"Dama ban yarda da ke ba tun karon fari,haɗuwa ta da ke na san maƙaryaciya ce ke sam zamtukar ki sun nuna min ƙaryar ki ƙarara dan haka ki hanzarta ki sanar da ni wa ya turo ki hare ni kafin in rasa haƙuri na akan ki Berenice"!!!da ɗan hargowa ta ida maganar wanda ya firgita Berenice sai kawai ta fashe da matsananncin kuka iya gaskiyar ta amma Juda bata nuna mata alamar ma kukan ya taɓa ta ba dan ta gama mata kallon shahararriyar maƙaryaciya ko tuntuni..

  "Ki yafe ni kumi tsaya ki saurare ni na maki alƙawari a wannan karon gaskiya zan faɗa maki babu ƙarya cikin zantuka na kuma ina da dalilin yin duk abin da nake yi saboda fansa ce ta fito da ni daga gidan mu zuwa gare ki amma in har na gama baki ainihin tarihi na kika ji baki yarda da ni ba kina iya ɗaukar mataki akai na na baki wannan damar"!!cikin ƙosawa da lamarin Juda ta ce
  "Start talking".....

*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 08:38] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:13&14*

Cikin ƙaraje Berenice ta fara magana kamar haka
  _"Kamar dai yadda na sanar da ke ainihin sunana Berenice sai dai ban faɗa maki sunan mahaifi na ba wanda sunan shi Habaccus ne kuma ya zamanto babban mayaƙi ne ba mai farauta ba kamar yadda na sanar da ke a baya ba,mahaifi na mu biyu kaɗai ya hafa ni da yaya na Habilah wanda ya ke nan ɗaure yanzu da haka sakamakon kama shi da aka yi yana hira da ɗiyar sarki gimbiya Ondrea wanda aka ce tsageranci ne kawai yake nunawa in ba haka ba ina shi ina gimbiya hakan ya sa aka kame shi mahaifin mu kuma dama yana ɗaya daga cikin jigajigan masu kula da masarautar Mughal(Mughal empire) wanda hakan ne ma ya sa ba'a yankewa yaya na hukunci ba dan girman mahaifin mu da ake gani,toh wannan abin ne ya sa mahaifin mu kasa riƙe baƙin cikin har ya faɗi ya mutu ba tare da an sani ba dama mahaifiyar mu ta daɗe da barin doron ƙasar nan mahaifin mu ne ke kula da mu shi ya koya mana yaƙi ya kuma sanya min sunan sarauniya".._
   _"Kafin ya mutu ne ya saka ni ɗaukar mai wata babbar alƙawari akan duk runtsi kar in yarda in bar yaya na ya mutu cikin wannan kangon azabtarwar dan dama saboda yana raye ake rangwama mai yanzu da ya kusa barin duniyar dole komai ya dawo hannu na in zamewa yaya na komai in cika ma mahaifin mu burin sa".._
  _"Sarauniyar farauta shi ya saka min,ya ce min in farauci masarautar Mughal in kuma cika mai burin sa dan sarkin masarautar Mughal ya cutar da shi cuta marar misali kafin ya bar duniya,matar shi sarauniya Zinaida da ke mulkar ƙasar ma ta cutar da shi dan tana sane ta tura ɗiyar ta gimbiya Ondrea tayi zance da yaya na dan a kame sa dama tsanar da take ma mahaifin mu ba kaɗan bane dan bai cika yarda da ƙudirin ta ba da zarar ta ɓullo mai ta nan sai ya kauce har so tayi ta kwanta da shi duk dan ya yarda da ƙudirin ta amma ya ƙi wannan dalilin ne ya janyo mai tsana ƙararar a idanun ta wanda ya zamo har take mai kirarin ko ya yarda da ita ko ɗan sa ya cigaba da zaman bursina"._
_"Wannan dalilin ne ya haddasawa mahaifi na baƙin cikin zuciya ya faɗi ya mutu ni kuma na nufi masarautar dan nemawa yaya na rangwami daga wun sarauniya Zinaida sai ta nuna min in na yarda na cika mata ƙudirin ta toh tabbas zata sakar min yaya na,toh ni ban san abin da take nema ba sai na nuna mata na yarda zan yi abin da take so".._
   _"Ce min tayi zata nemo min hanya mafi sauƙi zuwa yankin Babylon dan in zo in yaƙi duk wasu abubuwan da suka hana a kawo mata wani littafin kundi zata min abin da nake so muddin na ɗauko mata wannan ɓoyayyen kundin wanda ta ce da ni ta gama tsara abubuwa ta kuma binciko inda kundin yake da kuma wanda kundin ke hannun shi nawa aikin kawai shine in zo in fuskanci duk wasu matsalolin da zan fuskanta in ɗauko mata kundin,a cewar ta muddin na mata wannan aiki toh zata sakar min yaya na mu bar ƙasar ta mu tafi mu cigaba da rayuwar mu ba tare da tsoro ba".._
  _"A cikin ƴan kwanakin da suka gabata wanda yayi daidai da kwanaki aahirin da ɗaya da mutuwar mahaifin mu na amince da aikin da ta saka ni akan zan yi in ya so bayan na dawo sai in gudu da yaya na amma ni na san ba abu mai sauƙi bane in sato wannan littafin kundin ba dan na sha jin labarai akan wannan kundin da kuma tarihin duk wanda yayi yunƙurin ɗauke shi rasa rayuwar sa yake yi,dan haka amsa mata nayi da na amince ba dan na san zan koma da rai ba sai dan na san in ta ga haka tana iya rangwama wa yaya na amma na san in na fito mutuwa zan yi".._

_"Yaya na na sanarwa da wannan batu sai ya nuna min in haƙura kawai dan kar a yi rashi biyu shi ya mutu nima in mutu amma na nuna mai a'a ina son in fanshe shi da ya ga na dage sai ya bani shawara haɗe da nuna min hanyoyin da zan bi in tsira ba tare da an sami matsala ba,shi ya koya min abin da na zo na yi da ke duk labarun da na shimfiɗa maki shi ya koya min".._
  _"Komawa nayi ga sarauniya Zinaida na nuna mata ina shirye in nufi inda ta tura ni,cikin farin cikin ta ta tura ni wani ɗakin ta mai duhu ta furta wasu kalmomi babu jimawa na tsinci kai na a nan ɗakin wanda tsoron abin ne ya saka ni tsayawa ina kallon ki da kike kwance ina kuma kallon littafin kundin dake gefen ki ina tunanin in ɗauka ko a'a sakamakon mugun sihirin da aka ce littafin na mamaye da shi".._
  _"Da kika tashi kika gan ni na tsorata matuƙa sai na yanke hukuncin in gudu kar ki ga fuska ta amma sai kika nuna min jarumta duk da ƙaryar da na shimfiɗa maki kin gane cewa ni ɗin maƙaryaciya ce ba gaskiya na faɗa maki ba".._
  _"A yanzu buri na bai fi in fanshi ɗan uwa na ba yaya na wanda shi kaɗai ya rage min a duniyar nan ba in ya so daga baya sai mu koma ni da shi mu ɗau fansar mahaifin mu,amma kin rigada kin kama ni kin san sirri na bana jin zan ɓoye maki wani abin,turo ni aka yi in zo gare ki in sace wannan kundin naki ni kuma duk abin da zai sa sarauniya Zinaida ta sakar min ɗanuwa shi zan yi dan shi kaɗai gare ni kuma wannan shine iya gaskiya ta in kuma baki yarda da ni ba...,,ki min hukunci daidai da laifin da na maki amma ki sani bayan wannan ban da wata ɓoyayyiyar abu".._

  Nannauyar ajiyar zuciya Juda ta sauke kafin ta ce
  "Kin tabbata wannan kaɗai ne dalilin da ya kawo ki ko kuma kina ɓoye min wani abin ne"??kallon mamaki Berenice ta jefi Juda shi sai juda ta kaɗa mata kai alamu eh abin da take nufi kenan sai ta share hawayen ta ta fara magana
  "Iya gaskiya ta kenan na rantse maki da _Jaleesh_ bayan wannan maganar babu wata maganar kuma"kallon ban fahimce ki bq Juda ta aika mata da shi sai tayi saurin fahimtar abin da Juda ke nufi dan haka tayi saurin ce da ita
  "Na rantse maki da abin bauta ta Jaleesh ban da wata ɓoyayyiyar abu bayan wannan da na sanar da ke"!!..
 
  Shiru ta mata tana kallon ta cike da alhinin zantukan ta,shin ta aminta da ita ne ko kuwa ta bijire ma zantukar nata ne,ƙilla duk shiri ne irin nata na son ganin ta cinma burin ta akan ta..
  Tambayoyi da yawa ke running a zuciyar ta dan ta shiga halin ɓacewar basira da tunanin mafitar zatunkar Berenice amma abu ɗaya da ta sani shine Berenice ta ɓace kuma tana buƙatar taimakon wanda zai cec rayuwar ta ya dawo mata da farincikin ta..
Ɗan kallon sauri ta yiwa Berenice kafin ta ce wani abin
"Na yarda da ke Berenice,sai dai ki sani,ni,ba saurin sabo ne da ni ba dan na yarda da ke ba hakan na nufin zan saba da ke bane,,taimako ɗaya da zan iya yi maki shine,duk runtsi zan taya ki cikin wannan murɗaɗɗiyar hali da kika shiga dan in ga kin sami ɗan uwan ki ya dawo gare ki,.baya da wannan kuma,,,babu abin da zai haɗa ni da ke,saboda ki san iya matsayar ki ki kuma yi ƙoƙarin kawar da idanun ki akan lamurar rayuwa ta,haka ne kaɗai in kika yi zaki ci ribar tarayya da ni"..
  Kallon ta Berenice tayi cikin samin sauƙin zuciya sannan ta ce
  "Ko da a kullum zamu na raba hanya mu rinƙa haɗuwa a mahaɗa ne da ke,na amince zan bi dul wasu sharuɗɗa da kika gindaya min matuƙar zai samo min hanya mai ɓillewa yaya na ya dawo gare ni"..gyaɗa kai Juda tayi tana daɗa bin ta da kallo kafin ta ce
  "Mu koma tanti na,ki kwana a waje dan ban gama yin na'am da ke ba a zuciya ta har yanzu"ba yabo ba fallasa Berenice ta ce da Juda
   "Ban da damuwa da hakan in dai ke kin lamunta da shi"..babu wani abin da ya kuma gittawa tsakanin su na kalmar baki illah fita daga tantin da Berenice tayi ta raƙube bayan tantin tana share hawayen fuskar ta ita kuma Juda ta koma ta kwanta haɗe da yin matashi da jakar ta tana mai riƙe sa gam gam gudun kar Berenice ta sulale ta sace mata jakar..

  A taƙaice dai babu wacce tayi baccin kirki a cikin su su biyun dan kuwa ita Berenice kwanan tsaye tayi tana kai kawo a tsakankanin tantin Juda da kewayen mashayar nan dan bata so wani abin ya gitta da zai saka Juda nesanta kan ta da ita,yayin da ita kuma Juda ta kasa baccin ne dan zuciyar ta sam bai aminta da shawarar ta yi baccin ba,gani take matuƙar ta runtsa toh fah Berenice na iya yi mata zamba cikin aminci ta hanyar zagayowa ta ɗauke jakar ta gudu wanda ita kuma ba zata so hakan ba dan tana ji kamar bayan iyayen ta da kakan ta da ta yarda da su toh kamar ita wannan ma tana iya aminta da ita amma dole sai ta tsallake gwaje gwajen da zata mata dan ita bata yi wayo da wani wanda suka zo tsara ɗaya ba dan haka bata wani san daɗin zama da wani a matsayin abokin shawara ba...

  Har gari yayi haske Berenice bata natsu ba toh ashe dama Juda na ankare da kai kawon da take faman yi tana kallon ta tana nazarin ta amma bata nuna mata idanun ta biyu ba har yanzu da take ƙare mata kallo tana tunanin dalilin da ya sa sarauniya Zinaida ta jefo ta wun ta,wai ma shin,,,menene a cikin wannan kundi da ake ta kawo mai hari har ya raba ta da iyayen ta da ƙanwar ta sannan ga wasu ma suna hararar sa ba mutum ɗaya ko biyu ba..
   Tunani tayi sai ta miƙe ta nufi Berenice tana mai ce da ita
  "Sunana Juda Artemas kuma fitowa nayi dan mufar masarautar Ottoman saboda ƙwato ƙanwa ta dake nan ƙarƙashin ikon mulkin sarkin ƙasar wato sarki Baal-Hamon dan haka ina ganin tafiyar mu zata zo ɗaya in har kina da hikima da basira"..
  Kallon ta Berenice take yi tana nazarin ilimi da fasaha irin ta Juda wacce ba zata wuce ta a shekaru ba amma hikimar ta ya wuce shekarun ta..
  "Baki da damuwa ta wannan kuma ina miki fatar samin ƴar uwar ki kamar yadda nake fatar samin ɗanuwa na ya dawo gare ni ba tare da an ɗau lokaci ba"..cikin gamsuwa Juda ta gyaɗa kan ta sannan ta ce da Berenice
   "Kina son tafiya nemo abinci cikin daji ne"??girgiza kai Berenice tayi tana mai faɗin
  "A'a bana jin akwai buƙatar hakan"!!gyaɗa kai Juda tayi kafin ta miƙe tsaye tana mai ɗaukar jakar ta da nufin fita
  "Ni zan tafi nemo kayan itatuwa daga nan zan nufi rafi mafi kusa da nan dan in yi wanka,in kin ga na daɗe ban dawo ba kina iya cigaba da tafiyar ki in ya so zuwa duhun dare sai mu haɗu saboda tsaro"...
  Gyaɗa kai Berenice tayi tana mai ɗagawa Juda hannu ita kuma Juda ta juya ta cigaba da tafiya yayin da Berenice ke bin ta da ido har ta ɓacewa ganin ta ita kuma ta koma cikin tantin Juda ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta,ta kuwa yi bacci sosai kafin ta farka ta kalli gefen ta bata ga kowa ba sai ta saka a Juda bata dawo ba kenan dan haka fitowa tayi ta hau naɗe tantin har ta gama gabaɗaya ta saka a gefen rigar ta sannan ta fara tafiya tana tafe tana tunane tunane kala kala a zuciyar ta game da mafitar ta...

**************

Zaune take bakin wani teku tana kallon littafin dake hannun ta tana nazarin sunan dake rubuce saman shafin,tana tunanin ko wani rikitaccen labari zata tsinta cikin wannan shafi...

  *THE LEGEND OF NAKANO TAKEKO OF JAPAN*

  Ta kasance mace ɗaya da aka fi sani da _Onna-Bugeshia_a tarihin ƙasar jafan,.Takeko ta sami ilimin ta na fasaha da zane zanen hannu wato (Literary and marital art)kafin ta ware kan ta ta koma cikin fagen yaƙi inda ta kasance cikin mayaƙan Boshin..
   Yaƙin ƙasar jafan(japanese)ɗin ya ɗau tsayin lokaci tun daga  uku ga watar junairu(3rd January) shekara ta alif dubu ɗaya da casa'in da sittin da takwas(1868)har zuwa sha takwas(18th may) ga watar mayu shekara ta dubu ɗaya da casa'in da sittin da tara(1869)kuma wannan yaƙin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin ma yakan zamani da ake kira da civil war army...

  A yaƙin Aizu da ya kasance cikin shekara ta alif dubu ɗaya da casa'in da sittin da takwas(1868)Nakano da sauran matan da suka haɗa kai suka tsunduma cikin yaƙin suka jajirce dan  ganin an cinma matsaya,ba'a ɗauke su da muhimmanci ba hasalima,numawa aka yi ba'a san su ba kuma ba'a san da zaman su ba a matsayin tantanttatun mayaƙan zamani na Aizu(official Aizu army)..

  Wannan rashin shaidar da aka mata ita da sauran matan da suka jajirce a yaƙin sai ya saka ta harzuƙa ta raba kan ta da kafatanin jerin mayaƙan zamanin ta kafa nata gangun yaƙin na mata ita da waɗanda suka amince zasu goya mata baya dan su yaƙi rashin adalci a ƙasar wanda gidauniyar nata ta mai inkiya ne da _"MAYAƘA MATA"_wato(Women's army)..

  Abin da take amfani da shi a yaƙin wanda shi ta zaɓa dan ra'ayin ta ya kasance wani maki ne mai suna  Naginta_wanda yake taimaka mata tana yaƙin kuma tana nasara a sa'ilin sai dai hakan bai kai ta ga samin nasara har zuwa ƙarshen yaƙin ba..

  Takeko ta sami wani hari da yayi sanadiyar mutuwar ta bayan duk jarumtar ta dan an harbe ta ne a ƙirji a sa'ilin da take tsaka da yaƙar Imperial japanese army dake ƙarƙashin ikon Ogaki..
  A lokacin da aka kawo mata wannan harin ta matuƙar tsorata ba kaɗan ba dan tana tsoro da shakkar kar mayaƙan su ɗauke gawar jikin ta su adana a wun adanar su dake ƙarƙashin ikon mulkin su dan kamar yin hakan izgilanci ne da cin zarafi a gare ta ko da kuwa bata raye sai ta yanke hukunci da zuciyar ta akan ƙanwar ta ta mata gata,dan haka cikin filin yaƙin ta kirayi ƙanwar ta kafin ran ta ya bar jikin ta ta umarce ta da ta yanke kan ta ta tafi da shi ta saka a ma'adanar kundin tarihin jajirtattun mayaƙar ƙasar su sannan ta kai jikin ta ta binne shi,wannan shine maganar ta na ƙarshe da ƴaruwar ta kafin ta daina numfashi..
   A hankali ƴar uwar ta ta cika mata burin ta dan ta kai kan ta ta binne a ƙarƙashin wani bishiya dake can wun bauta a Hōkai-ji wanda yake a Fukushima..
  A yau,tarihin ta da aka adana wanda ba'a iya mantawa da shi ya zamo wurin da yara mata ke kaiwa ziyara a duk shekara saboda su bata girma da darajar ta a lokacin da ta kafan reshen sansanin gidauniyar ta na mata mayaƙa(Women's Army),suka tafi ne a ko wani shekara daidai ranar da ake bikin mayaƙan Aizu dan tunawa da wannan shahararriyar

Please Login or Register in order to submit comment