Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tafi ta nemo nata haka ma in dai Agneta ce ta nemo abinci toh fah Berenice ba ci zata yi ba sai dai ta nemo nata har ta kai ta kawo wasu lokutan har gori Agneta ke wa Berenice akan babu abin da ta sani sa da sato abinci bata iya yin zuciyar nemo nata na kan ta ba..
A duk sadda Agneta zata wa Berenice gorin ɓarauniyar abincin nan toh sai hakan ya ƙona mata rai dan har tuno mata tayi da ranar da suka tafi fadar Mughal ta sarauniya Zinaida da suka sami sarari ta ɗebo abinci mai yawa ta ɓoye a cikin rigar ta ta gudu da shi,wannan tunatarwar da Agneta ke wa Berenice kullum in zata goranta mata yakan ɓata mata rai sai dai ta koma gefe ta keɓe kan ta ta sha kukan ta har ta ji sanyi a ran ta sannan ta dawo cikin su ba tare da ta nuna masu wani abu ya faru ba..

Cikin tsakiyar dare suna tsaka da baccin su cikin tantin da ya zamo masu nasu na dole dan Juda tayi accommodating nasu gabaɗaya zuwa cikin tantin in zasu yada zango duk da a ɗan takure suke dan girman tantin bai kai na ya karɓi mutani sama da mutani uku ba amma sai gashi har su huɗu dan haka a ɗan takure suke sai dai da babu gwara a kwai ko da ƙanƙani ne..
Ƙarar jemage ne ya karaɗe wurin dan haka sai Agneta tayi firgigit ta farka,bata tsaya jiran komai ba tayi hanyar waje jikin ta na rawa,.
Ai ko tana fitowa ta yi karo da eagle ɗin ta kwance cikin mawuyacin hali kamar zai bar numfashi dan haka ta isa gare shi tana faman kiran sunan sa kamar dai yadda ta laƙaba masa
"Januu!!!Januu ka tashi,ka tashi mana me kake son yi min ne haka,,ka tashi mana kar ka rufe idanun ka me kake shirin aikatawa kan ka ne haka ina aka maka hakan faɗa min"!!da kukan ta sharɓe sharɓe take maganganun sai dai wannan jemage dai baya cikin halin amsa mata a sigar da ya saba amsa mata dan haka sai ya gyara kwanciya..
Gyara kwanciyar sa kuma wata alama ce da ke nuni da akwai wata a ƙasa dan haka yana kwantawa sai ko ta hango wata wasiƙa naɗe da igiya mai kalar ruwar ƙasa,saurin ɗaukowa tayi ta warware ta shiga karantawa kamar haka
_"Kina wasa da wuta zuma na,sai da na ce maki ido na na yawo a duk faɗin inda zaki tafi amma wautar ki ta sa kika lamunta kika cigaba da bin yarinyar nan da mabiyan ta dan kina ganin kamar wata wayo ce da ke da zaki iya kauce min toh wannan gargaɗi ne dan ki sani,januu ɗin ki ya tare maki ya kuma karɓi hukuncin da ya kamata a maki dan shine kaɗai mai son ki toh a tarawar mu ta biyu abin ba zai yi daɗi ba dan ki sani ina iya zuwar maki a wano yanayin dan in hukunta ki,,daga mai ƙaruwa daga gare ki sarki Malik Bairaj"_..
Kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata sai yi take tana tunanin ita haka rayuwar ta zata cigaba da tafiya,ta sami waɗannan mutani da suke nuna mata kamar suna son ta in aka cire Berenice mai son ganin bayan ta,ta fara sabawa da su sannan yanzu kuma kwatsam sai ya zo ya ɗaga mata hankali me yake nufar ta da shi ne toh wai..

Kukan nata ne ya tayar da sauran dan wani irin bacci ne mai daɗin gaske ya ɗebe su gabaɗaya sakamakon gajiyar da suka yi dan yau tafiyar kwana biyu suka cika dan sun matsu su isa ga Ottoman Empire..
Berenice ce ta fara fitowa dan haka ita ta fara ankara da abin da ya faru duk da bata san me ke cikin wasiƙar dake hannun Agneta ba amma ta san takarda irin wannan toh ba takardar alheri bane dole ko gargaɗi ko kuma sanarwa akan mutuwar wani ko wata ko kuma mutuwar shi mai karanta wasiƙar..
Mantawa tayi akan suna faɗa kuma basu jituwa sai ta nufe ta tana faɗin
"Agneta me ya faru da ke kuma me ya sami jemagen ki"?itama Agneta haka ta sami shafewar basira alan faɗa suke da Berenice sai ta shiga labarta mata abin da ya faru a ƙarshe ta ɗora da
"Daga ya tafi nemo mana abincin safe shine fah wannan azzalumin ya saka aka illata sa shi da bai san komai ba yanzu in ya mutu ina zan saka kai na wa zai rinƙa min hira a lokacin da na shiga wani halin sannan wa zai cigaba da nemo mana abinci"!?kuka take yi har ta faɗa jikin Berenice bata sani ba.
Kaf wannan labari a nunnen su Juda da Balik da suka ɗan jima da fitowa sai da suka tasuaya ma Agneta musamman Berenice da ta san zafin rashin wani naka dan ta ɗanɗani azaba ko kafin mahaifin su ya bar duniyar sarkin ƙasar su mijin sarauniya Zinaida ya kasance mutum mai kirki a zahiri amma a baɗini kuwa ita zata fayyace azabar sa dan azaba iya azaba ta sha sa a hannun wannan sarki wanda hakan ya sa tayi farinciki da mutuwar sa bata ko ji ɗar ba dan ya kasance mugu azzalumi mai tursasa ta yin abin da bata yi niyar yi ba kuma a matsayin ta na ɗiyar mai bada shawara bata da ƴancin kaucewa umarnin sa..
Sannan cikin maganar Agneta Berenice ta gane wato dama ba ita ke fita nemo abincin da take dawowa da shi ba a duk lokacin da ta fita nemowa ashe dama aikar wannan eagle nata take yi sai ta maida su wawaye akan ita ke fita nemowa kenan in nutshell dukkan su ɓarayin ne daga ita har Agnetan..
Murmushi tayi kafin ta ɗago kai ta kalli Juda tana mata alamar ta zo ta riƙe Agneta dan tana son taimakawa wannan eagle in da sauran ran sa a gaba kenan..
Zuwa Juda tayi ta rungume Agneta a jikin ta sai Berenice ta ɗan juya zuwa ga wannan eagle ta mai kallon tsaf sannan ta fara ƴar dabarun ta da ba za'a rasa ba na sihiri,..
Abin dai kamar ba zai yi tasiri ba sai can bayan kowa ya cire rai sai wannan eagle ya tashi da ɗan kuzarin sa..
Ai Agneta na ganin haka bata san lokacin da ta fincike daga jikin Juda ba tayi kan januu ɗin ta tana faɗin
"Januu sarki ko?shi ya maka wannan?shi ya so raba ka da ni?kayi haƙuri jannu zan rama maka ni da kai na zan tafi in rama maka abin da sarki ya maka ka ki"?ɗan karkaɗa kan sa yayi sannan ya kaɗa bindin sa haɗe da tashi tsaye daga haka kuma bai tsaya ba ya miƙr fukafukan sa yayi sama sai Agneta ta bi sa da kallo..
Bata san ya zata rayu babu wannan eagle ba ita ta san mutuwa zata yi,sai dai su kam su Juda abin ya ɗaure masu kai dabbar da yake ji kamar zai bar numfashi aka farkar da shi amma har ya tashi yayi gaba toh ina ya dosa kuma?..
Tambayar dake zukatan su kenan har ita kan ta wacce ta farkar da shi dan haka Balik ya tambaye ta
"Ina kuma januu ɗin naki ya tafi"?bata jira komai ba ta amsa mai
"Abincin gobe na safe ya tafi nemo mana"abin ya ɗaure masu kai sai suka yi suƙuƙu suna kallon ta suna mamaki dama shi ke nemo mata abincin da gaske kamar yadda suka ji ta faɗa ɗazu suka yi tsammanin ko gigin abin da ya riske ta ne ya sa take faɗe faɗe ashe gaske ne..
Berenice kuwa dariya tayi dan dama ita ta daɗe da gano inda maganar Agneta ya dosa..
Kallo ne ya koma wun Berenice ana mamakin dariyar me take yi sai Agneta ta ce
"Me ya faru kike dariya"?kamar jiran ta take sai ta bata amsa da
"A kwanaki uku zuwa huɗu da suka wuce a kullum kikan kira ni da ɓarauniyar abinci har ma ki ce da ni ban da zuciyar nemar na kai na haka zalika kullum sai kin tuno min da ranar da na kwaso abinci daga gidan sarauniya Zinaida da muka tafi kin gama saka ni jin kai na ni ɗin ɓarauniyar ce sai dai yanzu na gano a sanadiyar satar da kike saka eagle ɗin ki na yi a kullum har ya kusa haɗuwa da ajalin sa,yanzu mun zama daidai Agneta ni da ke duk ɓarayin abinci ne Balik da Juda ne kaɗai masu nemar na kan su"!!wani kunya ne ya lulluɓe Agneta dan bata yi tsammanin za'a cire wannan maganar cikin maganganun ta da tayi ba sai dai Berenice smart ce ta gano komai cikin seconds lallai sun zama daidai kuwa..

Suma Juda haka dai suka tsinci kan su suna murmusawa bisa ga abin da ke faruwa tsakanin Agneta da Berenice dan haka komawa ciki suka yi yayin da Berenice da Agneta kuma na wurin sai daga baya Berenice ta tashi ta shige ciki sai dai tun ana jiran shigowar Agneta har aka gano kunya ce ke damin ta wanda ya hana ta komawa cikin tantin dan haka sai suka bar ta suka yi pretending bacci suke yi sai daga baya Berenice ta gaji ta tashi ta fito sai ta ga Agneta zaune ta haɗa kai da gwiwar ta..
Tana zuwa ta ja ta,a bazata abin ya zo ma Agneta sai ta tashi ta biyo bayan Berenice amma she isn't comfortable but da hakan dai suka kwana...

★★★
Washegari da safe haka januu ya kawowa Agneta abinci ta tafi ta karɓo a inda ta saba zuwa sai dai tayi tsammanin ko Berenice zata yi teasing nata sai dai hakan bai faru ba rather da hannu bibbiyu suka karɓe ta suna haba haba da haka ta sake da su har suka ci abincin suka ɗora tafiyar su..

Sai da suka kuma samin kwanaki biyu suna tafiya sannan suka fara hango tsayin ganin masarautar Ottoman ta sarki Sultan Baal-Hamon mai ikon mulki masarauta mai ɗumbin tarihi..
A ranar kamar Juda ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta rinƙa ji dan gani take wahalar ta ya zo ƙarshe saboda zata gano ƴar uwar ta kuma zata ɗauke ta ta raba ta da wannan azabtacciyar masarauta ta wannan mugun sarki kuma ta yiwa kan ta alƙawarin ba ita kaɗai zata bar gidan ba sai ta bar gidan da mafi soyuwar wannan sarki wato gimbiya Acenath dan kawai ta ɗanɗana mai azabar rashin ɗan ka a tare da kai,babu wanda ta sanarwa da wannan sirri nata ta bar wa kan ta...

Ko da sauran abokan tafiyar nata ke baccin ban gajiya ita kam bata yi sa ba saboda zumuɗi duk da takan yi tunanin in ta shiga masarautar ta ina zata fara dan an ce da ita babbar masarauta ce mai girman ban mamaki sannan kakan ta ya ce da ita akwai sirrika da yawa ƙunshe cikin wannan kundi sai dai ta rasa har sai yaushe waɗannan sirrika zasu bayyana kan su dan ta damu matuƙa ta fara ganij sirrikan sihirin nan amma ba komai ta san in har ta tunkari gidan toh zata sami mafita ta rigada tayi mai wuyar wato zuwa masarautar...

Tana nan zaune wajen masarautar nan tana kalle kalle sai ta hango wasu mutani biyu sun wuce lulluɓe sai ta kawar da kan ta ta maida ga kallon da take yi,sai dai kamar ana tsungulin ta akan ta tashi sai ta tashin ta fara bin hanyar da ta ga giftawar mutanin nan sai dai tana zuwa suma suka dawo sai suka yi kiciɓis a hanya..
Suna haɗuwa sai ɗaya daga cikin mutani biyun ya yaye mayafin sa yana faɗin
"Ki taimaka min matata zata mutu tun jiya bata hayyacin ta ki taimake ni m"!!a birkice yake amma hakan bai hana ta recalling fuskar ba sai ta buɗe baki tana faɗin
"You"??sai a sannan ya mata kallon tsanaki sannan shima ya tuno ta sai ya girgiza mata kai ita kuwa Juda tsaya tayi tana kallon sa tana mai kallon mamaki shin fatar ta ne ta kasance ko kuwa wata shafin ƙaddarar ce zata kuma tunkarar ta kamar na da..
Maganar sa ce ta kuma karaɗe kunnuwar Juda da ta ɗan bar duniyar ta faɗa duniyar tunani,kai duban ta tayi ga abin da taji kamar ya faɗi a ƙasa sai ta kuma kallon fuskar da kyau ta ga eh wannan fuskar ce abin ta sai ta fara ja baya tana jujjuya kai har ta kai kusa da tantin su tana girgiza mai kai alamar dai ba zata taimaka ɗin ba...


*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 08:59] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:37&38*

Cikin sauri Agneta ta riƙo ta daga bayan da ta kusa faɗi tana faɗin
  "Ya haka me ke damin ki Juda"?faɗi tayi warwas a jikin Agneta daga haka bata san inda kan ta yake ba har sai bayan shafewar lokaci sannan ta dawo daidai..
  Buɗe idon ta yayi daidai da juyowar wanda ya firgita ta dan haka ta maida idanun ta ta rufe sai dai babu jimawa ta kuma buɗe su ta sauke kan wannan mutumi kafin daga bisani ta taahi ta zauna tana ƙarema ɗaukacin ƴan wurin kallo..
  Cikin sauri Berenice ta matso ta tana faɗin
  "Thank goodness kin farka na ji tsoro dan na rasa menene abin nan da ya firgita ki meke faruwa dake"!!
  Kasa cewa komai Juda tayi sai ma kallon mutumin nan da tayi tana son yin magana kuma ɗaukacin mutanin wurin sun gane tana son yin magana ne
"Me ya kawo ka nan kuma me kake yi a nan ina mun gama da shafin ku tun ba yau ba"?abin sai ya basu mamaki sai Berenice ta ɗan rufe mata baki tana faɗin
  "Juda meye kuma haka baki ga halin da suke ciki bane shi da matar sa"!?ƙyale ta Juda tayi tana cigaba da kallon su sannan daga baya ta ce
  "Ban ji amsar ka ba me ya kawo ku kusa da mu ko aiko ku aka yi ku zo kuyi garkuwa da mu"?har Agneta zata yi magana sai yayi saurin tsayar da numfashin ta ta hanyar fara yin magana
  "Ba komai abin da ya faru shine a jiya aka ɗaura aure na da na mata ta amma tun bayan ɗaurin auren nan babu kwanciyar hankali sai kawai ta rikiɗe min duk kuma mutanin dake wurin suka guje mu da fari nayi zaton abin zai sassauta amma sai gani nayi abin yayi yawa,ɗaukar ta nayi muka koma gida saidai ko da muka shiga gidar sai na rasa ya aka yi kawai buɗe idon da zan yi sai na tsinci kai na a nan ki yarda da ni ban san ya aka yi na zo nan ba dan hasalima a tsarin da muka yi ni da matata mun yi ne akan bayan auren mu sai mu koma ga masarautar su mu nemi afuwar mahaifiyar ta ta yafe mana in ya so sai muyi rayuwa irin ta kowa amma sai abin ya girmewa tunanin mu,..a nan na tsinci kan mu sai kuma na haɗu dake na kuma tuna na san ki a watannin baya shi yasa na zo nemar taimakon ki amma sai na ga kina gudun taimaka mana amma mun gode dan yanzu ta dawo daidai dan gashi har ta iya zama da kan ta kuma godiya gare ki da abokan tafiyar ki dan su suka taimaka mana"!..
  Wani irin mugun takaici ne ya kama Juda da jin wai su Berenice ne suka taimaka ma waɗannan mutanin abin ya kawo mata har wuya kamar ta shaƙe su dan takaici amma ta haƙura har sai sun keɓe dan ta ji haushi ba kaɗan ba..

  Bata amsa masu ba dan haka sai su Berenice da Agneta suka zamo masu maganan while Juda ta ƙyale su sai ma tashi tayi tayi shigewar ta cikin tantin ta ta kwanta..
  In za'a saka mata wuƙa ko takobi a wuya toh ba zata iya faɗin abin da ya sa take jin takaicin taimakon da su Berenice suka ma Cahal da gimbiya Ondrea ba ita dai ta san bata ji daɗi ba kuma ran ta ya ɓaci matuƙa..
  Har bacci ya ɗauke ta bata sani ba amma tsabar zullumi da ƙwallafawa ran ta abin sai da tayi mafarkin abin da ya faru ɗazu a baccin ta dan haka tun kafin gari waye ta shirya ta fita ta nufi hanyar rafin dake dajin dan yin wanka..
  Haka suke neme ta suka rasa da suka farka kaaancwwar ba addini ne da su ba sai kowa ya kama gaban sa har sai bayan rana ya ɗaga sannan suka dawo matattarar su suka zauna zaman jiran Juda yayin da Cahal ya tafi nemowa matar sa abinci dan ta sami ƙarfin tafiya saboda a jiyan bata wani samin baccin natsuwa ba duk a hargitse tayi sa sai daga baya ta yi baccin natsuwa amma duk ya kasa kwantar da hankalin sa dan bata saba da wannan halin ba..
  Iya tunani yayi yayi linking matsalar da ta same su da kiranyen sarauniya Zinaida sai kuma daga baya ya natsu ya zauna yayi nazari mai zurfi sai gano kamar ahalin sa ne ke mai wannan abin dan ya san shi dai rabon sa da gida da ahalin sa sama da shekara ashirin kenan kuma tun bayan barin sa gida bai kuma marmarin komawa ba sai a daren jiya da abin ya bijiro mai bayan doguwar tunani da nazarin da yayi..
  Baya so ya tuno past life event nasa dan ba mai kyau da daɗin ji bane amma ya san koma dai menene,a nan ƙasar aka haife sa a nan ƙasar ya bar iyayen sa da kuma abokan sa amma ba zai iya tuna ga takamammen inda suke residing ba sakamakon shafewar tunanin da ya riske sa tun bayan rabo sa da gida da aka yi...

  Kwance take cikin tantin tana nazarin rayuwar ta,tun bayan barowar ta gida bata kuma tsintar kan ta cikin kwanciyar hankali da jin daɗi ba sai dai ba zata ce tayi zaman rayuwar ƙinci da baƙin ciki ba dan Cahal da a yanzu yake a matsayin mijin ta yana iya ƙoƙarin sa wurin ganin ya faranta mata dan bai rage ta da komai ba na jin daɗin rayuwa sai dai abin da ya zamo a jinin ta yake wato sarauta,sai takan ji wani iri wasu lokutan amma ta san abin zai masu sauƙi wuyar ta su sami abin komawa gida a ciki..
  Duk yadda zata yi zata yi dan ta shawo kan mahaifiyar ta ta fahimce su kuma ta yafe masu dan ta aminta da zaman su a gidan in ba haka ba toh zafin zai mata yawa amma kafin nan in Cahal ya shigo zata tunkare sa da maganar..
  Bata gama tunanin nata ba sai ta ji shigowar sa dan haka tayi wuf ta nufe sa ta rungume sa tana mai fashewa da kuka haɗe da furta
  "Ko dai curse ɗin mahaifiya ta ce ke bin mu dan ka ga tun jiya bamu sami kwanciyar hankali ba masoyi na ni dai ka zo mu koma gida ko zamu sami sauƙin lamarin nan ka ji masoyi na"?shi dai abim wami iri ya mai yafi so su nemi iyayen sa a nan ɗin sai su fara zama da su in ya so daga baya sai su koma masarautar Mughal amma abin kamar gaba kura baya sayaki sannan bai so ya sanar da ita gaskiyar lamarin wato kiranyen da nasa ahalin suka mai dan yana gudun kar ta guje sa..
  Rungume ta yayi yana faɗin
  "Kar ki damu gimbiya ta komai zai mana daidai dan akwai abin da nake so mu kammala a nan ɗin kafin mu tafi nemar yafiyar sarauniya"!!daɗa kwanciya tayi a jikin sa tana faɗin
  "Kayi alƙawari"?gyaɗa mata kai yayi sannan ya janyo hannun ta ya zaunar da ita yana mai bata abincin da ya siyo masu a baki,sai da ta ji ta gamsu da abinci sannan ta ɗan canza fuska alamun shima ya ci abinci dan haka shima ya ci sauran abinci daga haka suka fito dan tafiya..
  Gabaɗayan su dake wajen suka bi su da idanu suna kallon su sai daga bisani Agneta ta tambaye su
  "Ina zaku tafi kuma"?da ɗan fara'ar sa ya amsa mata da
  "Zamu fara nemar hanyar mu ta zuwa gida dan kafin dare yayi muyi rabin tafiya"!!.
  Gyaɗa kai suka masu sannan suka masu fatar alheri a kan hanyar tasu daga nan suka yi sallama da su bayan ɗumbin godiyar da suka masu..
  Har sun ɗan fara nesa da su Berenice Cahal ya tsaya haɗe da juyowa ya ɗan ɗaga muryar sa sama yana tambayar ina Juda take..
  Amsa Agneta ta bashi da
"Tun safe bamu gan fmta ba ina kyautata zaton wanka ta tafi yi"!gyaɗa kai yayi kafin ya bar mata saƙo
"In ta dawo ku sanar da ita nayi godiya ta ban girma dan haɗuwar mu ta fari alheri ne sannan haɗuwar mu ta biyu a jiya alheri ni ina fatar haɗuwar mu a wataran ta zamo alheri sai wani haɗuwar"ya ƙarasa maganar yana ɗaga masu hannu suma suka ɗaga mai hannu daga nan suka yi yafiyar su ta yamma su kuma Berenice suka tsaya gyara kayan su dan a yau duk sun yi wanka sai dai ba tekun da Juda tayi ba hakan ne ya sa basu haɗu ba amma sun san tana wurin wanka dan a nan kaɗai take ɗaukar lokaci wanda mafi yawan lokutan zama take yi ta rinƙa tunanin rayuwar ta a baya da kuma yanzu wasu lokutan tayi kuka wasu lokutan tayi annashuwa musamman daga jiya zuwa yau da ta ga gata ga tsayin tower na gidan sarautar ƙasar Ottoman abin sai ya rinƙa yi mata kamar mafarki kokuma tunani...

  Ba Juda ta dawo ba sai da rana tayi sanyi zuwa lokacin kuma duk sun gaji da jiran ta sun ƙosa ta dawo su tafi dan komai ya wakana amma shiru suke ta ji har sai da ta dawo a yanzu ɗin..
  Da fari basu wani gane ta ba dan canza shiga tayi tun daga kan ta har ƙasan ta wato takalmin ta da ke ƙafar ta dan ta daɗe tana son saka kayan nan amma in ta tuna akwai sauran tafiya a gaban ta sai ta haƙura but zaman da tayi a tekun da tayi wanka yau sai ta ga ya kamata ta saka kayan nan dan lokacin saka su yayi...
  Kayan nan da ta saka kuma ba kawai bane dan kaya ne na ancestors ɗin su da aka ajiye sa dan tarihi da tunawa da ranar da kayan suka yi ga mammalakiyar kayan wato mahaifiyar kakan Juda marigayiya _"Tulsia Aron"_..
  Ɗaure sumar kan ta tayi da maɗaurin dake haɗe da kayan sannan ta saka rigar da yake kamar rigar leda kuma kamar na fata,sai ta saka wandon rigar ta janyo sa ya rufe rigar kamar dai tayi tucking,wata ƙarfe ce mai ɗauke da ramuka da yawa ta naɗe tun daga gaban wandon har zuwa bayan ta sannan ta ɗaure maɗaurin ƙarfen da ya rufe rabin cikin ta sannan ya kai ƙugun ta,takalmin da ta saka takalmi ne dogo kamar dai irin takalmin makiyaya mai tsayi tun daga tafin ƙafa har zuwa gwiwar ƙafa,yana ɗauke da igiyoyi dan haka ta ɗaure igiyoyin dan takalmin bai da tsini ko kaɗan sumul yake,hannun ta sanye yake cikin wani safa mai launin kayan jikin ta sai face mask da ta saka a fuskar ta

Please Login or Register in order to submit comment