Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka ɗauko tafiyar nan sai a masarautar Sultan mai mulki da isa,haka duk suka diddiro daga dawakan su suka ja akalar su zuwa wani hanyar daban ta yadda babu wanda zai yi la'akari da su dan su sami damar shigar masarautar cikin kwanciyar hankali..
Baccus ne a gaba yayin da su kuma matan ke tsakiyan su sai Balik a bayan su dan gudun abin da ka kai dawo..
Tun da suka doshi babbar ƙofar masarautar da ya sha ado da kwalliyar zinari da azurfa gaban Juda ya rinƙa faɗi bata san dalili ba amma ta san ta tsinci kan ta awani yanayi da bata san dalili ba haka bata san mafarin sa ba..

Wani irin shararriyar tafiya suka rinƙa yi kamar dai ba wannan ƙofar da suke hanga zasu dosa ba dan kuwa tafiyar ya basu mamaki saboda a zahiri dai ga su ne ga ƙofar amma tafiyar sai ta ɗare yadda suka yi zato..
A haka sai da suka ɗan jigatu kafin su nufo ƙofar sai dai tsaro da sihirin da aka ma ƙofar duk ya saka su ruɗu in aka cire Baccus da zuciyar sa ta bushe sam baya ma jin wani shakka ko ɗar dan ya san dole wani rai ya bar jikin mammalakin sa toh yanzu shi a shirye yake ko nasa ran ne zai rasa ya aminta ya rasa in dai zai ga bayan wannan mugun Sultan..
Kallon su yayi yana tausaya masu dan dole wani a cikin su ya rasa rayuwar sa sai dai sanin wanda zai rasa rayuwar ne bai yi ba amma ya san da wuya su shiga dukkan su sannan su fito ƙalau da rayukan su babu wanda ya rasa..
Ɗan hasashe yayi sannan ya kalli Balik ya ce da shi
"Kai ne babba duk a cikin su haka kaine wanda ya fi cancanta ka fara shigewa gaba dan ganin komai ya tafi bisa tsari amma kasancewar na gano baka da wannan ɓoyayyen sihirin ƙanwar ka ce kaɗai mai ita toh ita zata jagoranci shigar yayin da Agneta kuma zata rufe shigar ita zata kasance a bayan mu mu duka"..ɗan shiru yayi kafin ya cigaba
"Sai dai kamar yadda na faɗa maku ne a baya ba dole yadda kuka shiga da rayukan ku ku fito duka da rayukan ku ba dole ayi asarar wani dan a ceto wani wannan ƙa'ida ce da haka take ko a da tun zamanin mayaƙan mu da mazan fama saboda kuna da damar yi wa kan ku bankwanan ƙarshe dan baku san ya yaƙin zai kasance ba"..
Wannan ƴar tunatarwar da ya masu ya jijjiga su haka ya sanya su jin shakkar fuskantar masarautar amma da yake Agneta akwai zuciya dan ta fi ita kanta jagoran yaƙin zuciya(Juda)sai ta basar da shakkun nata kawai ta ce
"Kawu Baccus kar ka damu kar ka yi shakka in dai zamu sami abin da muke buƙata mu kuma ƙasƙantar da wannan azzalumin Sultan,,,toh gare mu ko da rayuka sama da ɗaya zasu salwanta,,ba damuwa ba ce dan biyan buƙata ya fi dogon buri"..
Gyaɗa kai kawai suka rinƙa yi dan confidence ɗin ta da iya tsara maganar ta ya sa suka sami ƙwarin gwiwa akan duk wani tsanani na tare da sauƙi..

Gaba Baccus yayi yana mai riƙo hannun Berenice yayin da sauran suka biyo sa a baya,shi yayi leading suna hango masu tsaron ya rinƙa karanto wasu abunuwa yana umartar Berenice da ta nanata haka ta rinƙa nanatawa sai can ya janye ya koma baya ita kuma ta matso gaba..
Waɗannan kalamai ta rinƙa nanatawa sai kamar a mafarki ƙofar ta ɗan buɗu suka zazzaro idanun su waje sai Berenice ta shige Baccus ya biyo ta sai sauran ma suka biyo a ƙarshe Balik ne ke gaban Agneta wacce ita ce ta rufe shigar da wasu siddabarun ta..

Abin mamaki babu wanda yayi la'akari da shigar su wannan masarautar sai su abin su dan ba pure natural entry suka yi ba an yi ne ta burga da sihiri..
Tun da suka shiga wannan masarautar Fianna ke bin sa da kallo a haka ma wai basu ƙarasa cikin masarautar ba kenan nan a bakin hanya ce da ta raba masarautar kashi kashi dan haka ba lallai bane su gano ainihin hanyar sashin Dacey wato karuwar Sultan Baal-Hamon..
Wata dabara ce ta faɗowa Callee akan me zai hana su raba jiki tunda suna da yawa sai kowa ya nufi sashi daban daban dan rage yawan lokacin da zasu ɗauka a bincike mai dogon zango..
Duk sun yi na'am da wamnan shawara nata sai dai Baccus na tausaya masu dan za'a rasa rai amma bai nuna masu tsaurin abin ba..
Da haka ne suka rarraba kawunan su suka bazama shiga cikin wannan babbar masarautar suna bincike wanda babu wani a cikin wannan masarautar da yayi la'akari da su dan sam babu mai ganin su sakamakon ɓace ma ganin mutum da Baccus yayi amfani da shi dan ganin sun yi nasara a abin da ya kawo su..

★★★
_THE OTTOMAN EMPIRE_

Fitowar gimbiya Acenath kenan daga wani sashi na masarautar tana tafe tare da gimbiya Adriel suna tattaunawa dan daga dukkan alamu daga wun karatu suka fito duba da yadda suke ɗan musu tsakanin su game da karatun da aka koya masu..
Agneta ce ke wannan sashin dan haka ita ta hango su sai ta ji kamar ta kame su su duka amma bata yi hakan ba sai kawai ta ƙyale su har suka gitta ta basu gan ta ba sai kuma tayi wani tunani toh in ita Dacey ɗin na cikin su fah..
Cikin sauri da azama ta nufe su suna zuwa ta gaban ta sai kawai hannun ta ya kai jikin Acenath wacce ke tsaka da yin dariyar shirmen Adriel.
Ji kawai tayi an riƙo ta riƙo mai zafi wanda ta san ba'a taɓa yi mata irin sa ba ko mahaifiyar ta da suke samin saɓani sakamakon _BAMBANCIN_ dake tsakanin su da saɓanin ra'ayoyin su bata taɓa yi mata riƙo irin hakan ba...
Firgita tayi tana dube dube dan babu wani mai tsaron lafiya dake tare da su bare ta ce ko shine ya mata irin wannan riƙon haka babu kowa tare da su daga ita sai Adriel toh wa zai mata hakan..
"Adriel meke faruwa da ni ne halan ji nake kamar ana takura ni"!!canza fuska Adriel tayi tana kallon gimbiya Acenath da ta ga idanun ta ya cicciko da hawaye ta ce
"Me kike nufi haka ƴaruwa ta"?hawayen ne ya sauko daga idanun gimbiya Acenath sai abin ya ruɗar da gimbiya Adriel dan haka ta fara rabe raben ido.
Ko kafin tayi yunƙurin ƙwala kiran agaji ta nemi gimbiya Acenath ta rasa..
Babban tashim hankalin da basu taɓa zato b sai kuwa gimbiya Adriel ta yanka a guje ta nufi hanyar sashen mahaifiyar gimbiya Acenath wato sarauniya Bayarma..
Da ihun ta ta ƙarasa sashin inda ta tarar ana wanke ma sarauniyar ƙafafu da ruwan ɗumi da kayan adon ƙafa..
Jiki na ɓari ta yanko a guje tana faɗin
"Mai girma maman mu,Acenath,,gimbiya Acenath,,,Acenath,,babu...babu..."maganar da bata ƙarasa ba kenan sakamakon yanke jiki da tayi ta faɗi a ƙasa sumammiya..
A firgice sarauniya Bayarma ta tashi tsaye tana mai sake dogon rigar ta da ta kai mata har ƙasa tana share ƙasar,gyara lulluɓin mayafin ta tayi tana mai saka takalmin ta haɗe da bada umarni hankali tashe
"Ku kula da gimbiya Adriel zan fita in ga me ke faruwa"..cikin sauri tayi hanyar waje sai masu tsaron ta suka dakatar da ita ta hanyar cewa
"Ranki ya daɗe ki koma ciki wannan ba aikin ki bane aikin mu ne mu zamu gano menene matsalar"!!wani ƙululun baƙin ciki ne ya taso mata dan haka ta ɗauke shi mai maganar da mari tana mai rufe sa da faɗa
"Kai ɗin waye,kai ɗin banza kai ɗin wofi,,kana ina aka taɓa lafiyar ɗiya ta?ba nan kuke ba?kana gani aka taɓa ta baka iya yin komai ko aiwatar da komai ba sai yanzu zaka zo kana nemar yi min katanga tsakani na da ɗiya ta dan ka zama sakarai wawa wanda bai san zafin haihuwa ba,gafara ka bani wuri kafin rai na ya ɓaci da kai shashasha kawai"!!
Saurin matsawa yayi gefe yana bata haƙuri ita kuma ta nufi hanyar sashin Sultan tana jin ɓacin rai dan tun a hanya ta saka aka fara shekalar ɓacewar gimbiya Acenath haɗe da bada oda akan kar wanda ya tsallake dokar ta kar a bar kowa ya fita duk wanda ya fita a sare sa..

Mantawa tayi da yana tare da wata a daidai wannan lokacin dan haka ta hangame ƙofar ɗakin nasa mai kama da masarauta mai zaman kan sa ta fara kiran sa
"Sultam...Sultan kana ina..Sultannn"!!!hankali tashe dan haka a firgice ya tashi haɗe da raba jikin sa da na Dacey yana share zufar fuskar sa yana mai umartar Dacey da ta miƙo mai rigar sa..
Miƙo mai tayi tana mai ɓata fuska tana saukowa daga gadon zata nufi hanyar bayin gidan ɗakin a zuciye rai ɓace..
SauriSaurin riƙo hannun ta yayi yana mai kaɗa kan sa yana nazarin ta
"Ina kuma zaki tafi rai ɓace Dacey na"!?abin haushi sai ta mai kallon wofi sannan ta ce
"Ai matar ka ke kiran ka dan haka sai ka tafi"!girgiza mata kai yayi yana faɗin
"Sanin kan ki ne,darajar ki gare ni ya fi darajar sarauniya Bayarma dan haka ki daina ƙunci dan kin ji muryar ta tana kira na kin dai fi kowa sanin halin sarauniya Bayarma da nacin fitina"yayi maganar ne yayin da yake janyo ta jikin sa suka faɗa tare forgetting that muryar matar sa ya ji..

Ran ta ya kai ƙololuwar ɓaci dan ta san wannan fitinanniyar matar na tare da shi haka take mai kamar ita ce matar ita kuma mistress ɗin sa,a ko da yaushe in tana nemar sa bata taɓa ganij sa kai tsaye sai dai in a kirawo sa daga sashen Dacey ko a ce yana tare da Dacey dan dole haka take haƙura dan ta tsira da lafiyar ta da mutuncin ta saboda ba ƙaramin aikin sa bane ya wulaƙanta ta ko a gaban waye in dai magana akan Dacey ne..
Sai dai yanzu dole ta ratsa ta shigar masu dan wannan issue ɗin na ɗiyar su ne,ɗiyar sa ɗaya Acenath..

Bangaje labulen gadon tayi da ya sha ado,sai ta gan su kwance maƙake da juna,sam ran ta bai ɓaci ba dan in da sabo toh ta saba da ganin hakan amma yanzu matsalar ta ya fito a nemo mata ƴar ta..
Ganin kamar haske yayi yawa sai ya ɗan ɗago kan sa a hasale zai sauke kwandon bala'i amma sai ta riga sa ta hanyar tarar numfashin sa
"Gimbiya Acenath ta ɓace ba'a gan ta ba ka fito a duba ta"!!ai hankalin sa in yayi million ya ɓaci dan kuwa baya ƙaunar jin wani abin ya sami ɗiyar sa shi yasa yake tsaurara mata tsaro..
Hankali tashe ya ɗaga daga jikin Dacey ya diro ƙasa yana faman juye juyen duba inda zai ga rigar sa dan ya saka ya fita..
Miƙo mai Dacey tayi tana hararar sarauniya Bayarma dake tsaye tana jiran sa ya gama kimtsawa dan su fita tare..
Fuu ya fita ita kuma sarauniya Bayarma ta mara mai baya sai da Dacey ta tabbatar da ya bar ɗakin sannan muryar ta yayi amo a kunnen sarauniya Bayarma tana faɗin.
"Tunda kika ce ba zaki bar ni in huta ba toh kema kuwa babu ke babu kwanciyar hankali miji dai naki ne amma hankalin sa da natsuwar sa,,nawa ne mu zuba mu gani"!!kamar dai yadda kishiyoyi ke yi in suna kishin mijin su toh haka a kullum Dacey ke ma sarauniya Bayarma kamar itama auro ta yayi..
Ta tafasa sauke sarauniya Bayarma bata ce da ita ba ta sa kai ta fice dan ita ba wannan ne a gaban ta ba tana buƙatar sanin inda ɗiyar ta take in ya so daga baya sai ta dawo ta amsa mata..
Wurgi da abubuwan adon gadon Dacey ta shiga yi dan so tayi sarauniya Bayarma ta amsa mata dan su sami abin faɗa a ce suna canza kalaman baki kamar wasu yara..

★★★
Bayan kamar shafewar awa faɗar masarautar Ottoman ya cika maƙil da jama'a dan duk inda ake tsammanin ɓacin ran sarki Sultan Baal-Hamon ya kai toh ya wuce gaban hakan dan a wannan lokaci ne yake aiwatar da sihire sihiren sa dan gabatowar wata shekarar hakan ya sa yake tsaface masarautar sa da sihiri kala daban daban amma abin mamakin shine ya aka yi wasu bare suka yi penetrating mai masarauta kuma har suka ɗauke mai ɗiyar sa..
Duk masu alhakin kula da ita an saka an ɗaure su haɗe da masu azaba mai tsanani har na tsawon awanni ko kwanakin da za'a gan ta,abin ba sauƙi..
Kuka sosai sarauniya Bayarma ke yi gefe guda ga shahararriyar annamimiyar nan Calva tana sharce hawaye amma inside her hakan ya mata daɗi dan ta san ta wannan hanyar ce kaɗai za'a azabtar da Sultan haɗe da tunkuɗe sa daga karagar da yake kai..
Duk wanda ya kalli Calva ƙarya ne ma ya ce ba tausayawa gimbiya Acenath take da iyayen ta ba dan har kukan ya taɓa zuciyar Sultan..
Shigowar mai duban sa ne ya katse koke koken da ake yi tsakankanin matayen dake aiki a masarautar da annamimiya Calva da Sarauniya Bayarma..
Buzu buzu ya shigo hankali tashe yana mai zama gefen kujerar mulkin Sultan..
Sultan Baal-Hamon bai bar Aberald ya numfasa ba ya fara jefo mai tambayoyi da sai da ya ɗan rikita tsohin dan da zafi zafi Sultan ke mai tambayoyin kamar shi yayi sanadiyar ɓacewar gimbiya Acenath ɗin..
"Mai girma ran ka ya daɗe wato gimbiya Acenath dai bata bar masarautar nan ba dan na ƙure ilimi na da dabaru ne wurin gano inda aka ɓoye gimbiya Acenath kuma na gano shine bata bar masarautar nan ba amma gaskiya samo ta da binciko ta inda take ba abu ne mai sauƙi ba dole sai an bi wasu abubuwa ciki har da tarihin da ya shuɗe dan gyara fitinar da ake ciki"..
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Sultan ya sauke yana mai duba Aberald kafin ya nutsa duniyar tunani sai ma yayi kamar ba a cikin masarautar yake ba haka kawai abubuwan da suka faru suka hau dawo mai wato duk yadda ya so binne wannan abin sai da ya bankaɗo sai da aka mai shigo shigo ba zurfi..
Kiran sa Aberald yayi yana jimami kamar yana shakkar sa sai dai ya zama dole ya sanar da shi gaskiya
"Sultan akwai fah gagarumin matsala dan wasu mayaƙa ne suka bankaɗo cikin masarautar ka kuma sam babu wanda zai iya shaida su dan a siffar boge suka shigo mana sam bana iya shaida su ko siffar su dan akwai jigajigan matsafa da suka shigo kuma a cikin su ne aka sami wanda yayi tsaurin idon ɗauke gimbiya Acenath dan haka yanzu dai suna nan a cikin masarautar nan kuma na san kafin a gano su sai an warware wannan sihirin da aka yi wa masarautar nan"..kasancewar babu wani sirri a masarautar sai duk mutanin fadar suka bubbuɗe idanu cikin alajabi da jimami suna ƙiyasta batun..
Kuka ne ya kuma ƙwacewa sarauniya Bayarma jin ɗiyar ta na gidan amma an rasa ya za'a gano ta wannan masifar da me zata fasalta shi..

Tashi Sultan yayi fuu yana faɗin
"Kowa ya koma bakin aikin sa ni zan san yadda zan shawo kan matsalar bana son ƙara jin komai sannan a cigaba da tsare masarautar nan kaf kar wanda ya shiga bare fita har sai an gano min ɗiya ta"..!!

Daga haka kowa ya koma bakin aikin sa shi kuma yayi gaba yana baza rigar sa abin na ƙona masa rai ba kaɗan ba bai yi zaton nan kusa abin nan zai zo ba amma bai cire rai ba hala wasa ake mai da tunani ba abin bane ya zo..
★★★★

"Agneta me na ce da ke kafin mu rabu?ina na hana ki saurin fushin nan ga shi nan yarinyar nan ta kasa tashi bare tayi ta bamu abin da muke nema dan na san izuwa yanzu kam an karaɗe masarautar nan kaf da nemo mu dan haka in da yadda za'a yi a farfaɗo ta toh ayi dan mu ƙarasa aikin mu"..
Cikin zafin nama Berenice ta ɗauke gimbiya Acenath da wani irin razanannen mari da sai da ya farkar da ita daga sumar da ta yi cikin kiɗima gimbiya Acenath ta farka tana ihu ai sai Berenice ta yi gaggawar rufe mata baki tana girgiza kai alamar tayi shiru amma kamar an ƙunna ta haka ta shiga ihun dan gani take ta wannan ihun ne kaɗai za'a gano ta a kawo mata agaji..
Ganin lallai fah gimbiya Acenath na iya fallasa su sai kawai Baccus ya maida ta baccin dole dan ya san ba basu haɗin kai zata yi ba sai dai ta lalata masu shiri..
Abin ya ɗan basu mamaki sai dai ya nuna masu ga dalilin yin hakan,dan dole suka yi shiru suka tsaya nemar wata mafitar..
Sun daɗe kafin Fianna ta kawo wata shawarar akan me zai hana su koma su kuma binciko gidan hala su yi katari da wani sai su kuma ɗauke su dan ya nuna masu inda ake ajiye waɗanda aka yi garkuwa da su in an raba su da gidajen su da ƙasashen su..

★★★
Durƙushe yake yana faman share zufa yana kallon sashen da aka mai kwalliyar ɗaukar ido,duk ya rasa me keai daɗi,ba dan zai iya gasgata batun amintaccen mai duban sa ba wato Aberald,toh da sai ya ce lallai wanda ke mai duban nan shahararren maƙaryaci ne sai dai ya yarda da Aberald bai taɓa mai ƙarya ba kuma tunda ya ce sai an koma ga tarihi toh hakan ne dole ya koma ya fuskanci abin da ya binne dan gyara yanzun sa,..
Taɓa sashen da aka ma adon yayi yana ƙare ma sashen kallo tunani yake yi idan aka ce sai ya ƙaryata duk wani ikon sa da yake yi dan rufe ƙofar gurɓacewar da ta nufo sa ya zai yi?shin dole ya rufen?ko ko canza taku zai yi?..
Kan sa ya ƙulle dan haka tashi yayi ya nufi hanyar waje yana kiran masinjar sa da shi ke da alhakin kaiwa da dawowar saƙonnin ciki da wajen masarautar Ottoman...
Komawa sashen sa yayi sai ya ga babu Dacey dan haka ya kwanta da baya ragwaf yana tunanin wanene wannan mai dakon sa da ya haɗa mai gadar zare da yake gaf da faɗawa ciki..
Jim kaɗan masinjar ya taho yana mai kirari da fadanci,bai ce da shi hum ba bare uhnuhn yana sauraron sa har ya ida sannan ya ɗora da tambayar sa
"Ran sarki Sultan jinin Sultan jikan Sultan da fatar ban yi laifi ba dan tsayawa yi maka kirarin da ya zamo tambari ne naka kai kaɗai ba"?ƙare masa kallo yayi kafin ya ce
"A je a rubuta wasiƙa ya isa masarautar Mughal,masarautar Jordan,masarautar cyprus,masarautar Babylon da masarautar Oman a sanar da su ina son ganin su da gaggawa bana buƙatar jin uzirin kowa wannan oda ce kuma doka ce duk wanda ya saka ƙafa ya tsallake zai fuskanci ɓacin rai na,,ka tafi ka aika yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba kuma ka turo min Dacey"!!jiki na kyarma masinja ya miƙe yana kuma yi mai kirari har ya fita yayin da shi kuma Sultan ya koma ya kwanta yana nazarin abubuwan da suka rinƙa faruwa da waɗanda ke nufo sa shi kam sam bai shirya sadaukarwa ba sai ya mulki duniyar nan ko da hakan na nufin ya ɓadda matar sa ce wato sarauniya Bayarma dan ya shirya yaƙar ko ma waye wannan ɗan tsugudidin da yake nemar tona masa asiri sam ba zai yarda damar nan ta suɓce masa ba..
Yana cikin tunanin ne sai ga Aberald ya shigo masarautar sashin Sultan ya wuce cikin makwancin sa yana mai kirari..
Shi Sultan ɗin ma ya ɗauka Dacey ce dan ita kaɗai ce zata iya kwantar mai da hankali a yanzu ɗin sai dai yana juyowa ya ga daban..
Kamar zai yi masifa sai kuma yayi shiru yana rarrashin kan sa dan kar ya rasa information mai muhimmanci daga wun Aberald..
Sai da Aberald ɗin ya ga hankalin Sultan ɗin ya dawo gare sa yana jiran ji daga gare sa sai ya ce
"Sarki na ina shakka,ina tsoro,ina gudun fah kamar kwaɗon da muka daɗe muna wa kallo ne a bakin ruwa zai mana ƙafa,ina fargabar sanar da kai lokacin ya zo,lokacin da na daɗe ina sanar da kai ina tunatar da kai,lokacin ne ya zo fah Sultan!!babu makawa daga wannan abin da aka yi maka shi kenan mabuɗin komai zai buɗu dan haka da ayi asarar biyu ɗaya bai samu ba kawai mu koma tarihi a gyara da in ko ba haka ba kana ji kana gani zaka rasa wahalar da ka kai shekara da shekaru kana yi dan ganin komai ya tafi maka daidai,na bar ka lafiya Sultan sarki na ina jiran ji daga gare ka Sultan"..daga haka Aberald ya fita ya bar Sultan Baal-Hamon cikin tsantsar tunani da mafitar bala'in da ya nufo sa farat ɗaya...


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:47&48*
_THE OMAN EMPIRE_
 
  Idan hankalin sarki Malik yayi million toh ya tashi shi ba wai fargabar kar ya sami ragamar mulkar duniyar ce tsoron sa ba shi tsoron sa kar dai a ce wani abin ne ya ya tafi ba daidai ba ganin tun sama da satittaka ya tura mayaƙiya Fianna zuwa masarautar Ottoman amma har wa yau babu ita babu sakamakon aiken da ya mata toh hakan yana ɗaga mai hankali har yake jin anya yana iya haƙura kuwa ko dai ya aika ne a ɗauko mai ɗan sa dan ya je ya aiwatar mai da komai tunda da bare gwamma naka duk ɓacin sa duk da ya san dai abin da kamar wuya yarima Ziyan ya amincewa wannan labarin nasa amma zai gwada..

  Fita yayi daga inda ake mai tausa da gyaran fata ya rufe jikin sa da rigar sa yana tafe yana tunani barkatai game da amincewa da yarjewar ɗan sa bisa ga wannan al'amari kasancewar yana ji a jikin sa kamar abubuwa na nemar ƙwace mai dan fah gagarumin abu ne ya rinƙa faruwa da shi amma a cikin duhu babu wanda ya sani hatta da matar sa bata san da zaman uƙubar da yake ciki ba tun wucewar wancan satin..
  Ɗakin hutun sa ya nufa yana mai gyara zaman sa jim kaɗan aka shigo dan yi mai al'adar sa da aka saba yi mai na yau da kullum sai dai yanayin sa ya sa mai ɗebe mai kewar ta fasa cire rigar ta ta mayar tana kallon sa dan gano matsalar sa..
  Ƙala bai ce da ita ba har sai da ta gaji ta taho gare sa tana mai yin ƙasa da murya ta ce
  "My king,halan me ke damin ka ne wai duk ka susuce kamar ba kai ba kamar

Please Login or Register in order to submit comment