Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ƙafa na ɓari ta bar sashen nasa ta nufi nata sashen leaving him all alone standing like an idol cike da mamakin Calva,lallai dole ya san na yi da Calva in ba haka ba toh sirrin sa zai gama fallasuwa...
Fita yayi ya iso babbar falonsa na karɓar baƙi ya zauna yana huci rai a ɓace ya aika aka kirawo mai masu kula da shigi ficin sashen sa..
In less than four minutes suka jeru a gaban sa suna mai kirari..
Kuma aikawa yayi ya ce a kirawo mai mai kular mai da kayan yaƙin sa dan yau hukunci mai tsauri zai yi..
Jin haka sai da gaban su ya faɗi sai dai suka waske suna danne fargabar su dan kar laifin nasu ya ƙaru(laifin da basu san ko menene ba)..
Nan ma ba'a jima ba aka taho mai da wani irin jibgegen wuƙa,wuƙar da yake amfani da ita duk shekara in za'a tafi gasar yaƙin sarakai,har wa yau babu wanda ya san sirrin dake cikin wuƙar nan sai shi abin sa dan sau da dama in har ya kai ma mutum hari da shi,toh fah sai dai wani ba wannan ba,ya bar numfashi kenan..
Cikin tsoro da firgici suka hau Kallon junan su suna haɗiyar yawu dan basu san laifin su ba sai dai sun san a yau sun yi bankwana da duniyar..
Tashi tsaye yayi yana mai gyara riƙon wuƙar nasa a lokaci ɗaya yana jujjuya wuƙar,dan bai cika ɓata lokaci wurin yanke hukunci ba,take yake aiwatarwa..
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya yana kallon reaction ɗin su na tsoro tsantsa sai yayi wata muguwar murmushi sannan ya soƙi na farin da wuƙar,..
Faɗi ƙasa wanwas yayi yana zubar da jini,haka ya rinƙa bin su ɗaya bayan ɗaya yana soƙin su da wuƙar nan har sai da ya ƙarar da su a na ƙarshen ne ya ɗan ja lokaci dan ya sanar da shi laifin su sai ya fara ba Sultan haƙuri amma ina shima ya soƙa mai wuƙar, dukkan su kwance suke a ƙasa matattu,sai sannan ya aika aka kirawo masa Calva..

Jin kiran nasa me ya saka ta jin faɗuwar gaba amma haka ta tashi ta biyo ɗan aiken dan kar ta aikata wani laifin..
Ko da suka iso ɗakin saukar baƙin Sultan,sai da Calva ta ji faɗuwar gaba amma ta ɗan kama kan ta ta matso Sultan tana mai yin ƙasa da kan ta haɗe da faɗin
"Ga ni na zo gaban ka Sultan,me kake buƙata daga gare ni"!!?ɗibar ta yayi ya zubar sannan ya ce
"Darasi da ishara na kirawo ki ki gani kuma na tabbatar ya zuwa yanzu kin san ma'anar wannan isharar da nayi"?sarai ta gane inda ya dosa dan haka ta jijjiga kai tana mai ce da shi
"Idan na fallasa ko siffar murmushin ka ne Sultan,ka raba min kai na da jiki na"..
Kallon ta yayi sannan ya bata damar tafiya sai dai fah a ran sa ya san duk kusancin sa da Calva dole alaƙar su ta yanke dan ta gano wani sirri nasa wanda bai kamata ta gano ba..

★★★
A fannin Calva kuwa da yanzu take ida shigewa saahen ta,babu abin da take yi face dariya,dariyar nasara dan ko ba komai ta gano wani babban abu dangane da rayuwar Sultan Baal-Hamon,haka zalika ta san ita ce kaɗai zai iya laying plain facts nasa akan ta dan ta san sirrin sa bai isa ya mata barazana ba..
"A yau ni,Calva fatehi,na gano sirrin ka,na gano sirrin ka mai wuyar fassaruwa ga al'umma Sultan,baka da abin da zaka ce da ni sai dai ka cigaba da lallaɓa ni kana bi na da lallami,abin mamakin shine,yadda taku ɗaya kacal ya saka ka bayyana abin da bai kamata ka bayyanawa kowa ba,hmm wata miyar,sai a maƙota,,da ni kake Sultan,yanzu aka fara,ni da kai wanda ya gaji ya fasa"..
Tana zaune ta miƙe tsaye tana mai gyara naɗin mayafin ta ta saka kai ta fito tana nufar hanyar sashen ɗakin mazan masarautar..
Ko da ta tafi sai ta kuma janyo mayafin ya rufe mata fuska dan kar a gano ta d wuri..
Daidai ɗaki mai tambari ja ta dakata tana kallon ɗakin,cikin sauri ta hau bubbuga ƙofar ɗakin kafin daga bisani aka leƙo aka miƙo hannu..
Nata hannun ta saka ta janyo sa waje tana faɗin
"Fitowa zaka yi akwai magana mai muhimmanci da zamu yi da kai yanzu zaka dawo"..fitowa yayi suka nufi hanyar baya suna sauri har suka kai daidai sashen da ake ajiye masu laifi wato bursunar Sultan..
Suna zuwa wurin suka ja suka tsaya nan ma buga ƙofar wurin tayi aka buɗe masu ta miƙowa wanda ya buɗen wani abu cikin leda,ya saka hannu ya karɓa sai ya ja baya suka shige sannan ya rufe ƙofar..
Tafiya suka yi mai tsawon zango har dai suka taho wata ƙofar da aka kuma buɗe masu suka shige,a nan ne suka buɗe ƙofar ƙarshe suka shige.
Mata ne zalla cikin wannan ɗaki kama daga yara har manya da tsoffi,gabaɗaya basu da kyawun gani duk sun sauya kamanni kamar ba mutani ba tsabar wahala azaba da takurawa..
Ƙasa Calva tayi da muryar ta tana magana da wanda suka shigo taren
"Ka gani,duk nan,mutani ne mata ne kuma kowa da ahalin sa amma Sultan ya saka aka rabo su da su akya zo ya sa aka jibge su a nan kamar marasa galihu,tun barowar su da asalin su babu wanda ya kuma gani ko sanin yanayin waje dan a nan aka zuba su kuma a nan ake ɗanɗana masu azaba,idan na cikin masarautar sun aikata laifi sai a zo nan a kwashi wasu a gyare su a kai su cikin masarautar a zuba su,kuma a hakan akan turo ƙartin mazaje su zo su lalata matayen nan har yaran a wasu lokutan ma..".
Takawa tayi shima ya biyo ta a baya sai ta tsaya daidai wani ƙofa tana kallon wata yarinya dake kwance ƙudindine tayi sai ta kawar da fuskar ta gefe tana faɗin
"Tun da suke wannan abubuwan,basu taɓa fuskantar ta da nufin yi mata komai ba dan bana barin su,a kullum nakan ba su kuɗaɗe da yawa dan su nesance ta kuma ba laifi,tun da ta shigo wurin nan kusan shekara ashirin kenan,babu wanda ya taɓa keta mata haddi hakazalik babu ƙuntatawa a tattare da ita ina ƙoƙari na wurin ganin na inganta rayuwar ta dan tana da ɓoyayyen labari a tare da ita wanda ba zan iya faɗa maka ba sai nan gaba"..
Ajiyar zuciya suka yi su biyun sannan ya kalle ta ya ce
"Nagode Calva,haƙiƙa kin cancanci kyauta dan kin min abu babba da Sultan ya daɗe yana ɓoye min,na maki alƙawari,da hannun ki,zaki raba kan Sultan da jikin sa dan ke kika dace da yin hakan,duba da irin gudunmawar da kika bayar a wannan aiki nawa cikin masarautar nan,nagode Calva zaki ga sakamako"!!gyaɗa kai tayi tana share ƙwalla tana jan hanci sannan suka fito..
Sai da suka kusa fitowa sannan ta ja ta tsaya ta mayar mai da abin da ya faru ɗazu tsakanin ta da Sultan..
"Satar hanya nayi na shige sashen Sultan,na ɓoye cikin labulen sa na goga turaren wannan mayyar mistress ɗin nasa Dacey,toh shigowar sa kenan sai nayi sa'a bai gan ni ba shine na rinƙa mai tausa ina danna bayan sa da fatar ya faɗi wani abin da zan amfana da shi shine ya furta abin da sai da na girgiza,duk da na so jin gabaɗaya zancen amma hakan bai faru ba dan ya gano ba Dacey bace ni ce"!!..
Harɗe hannuwan sa yayi a ƙirjin sa yana faɗin
"Ki kwantar da hankalin ki Calva,ni Irad Al-Riaz na maki alƙawari kamar yadda kika taimake ni zan cika maki burin ki dan abin da ya taho da ni ƙasar nan kenan in ga ragwajewar Sultan Baal-Hamon in nuna mai iyakar sa dan yadda ya ƙasƙantar da musulunci a ƙasar sa da ƙasashen dake ƙarƙashin ikon sa toh haka nima zan wulaƙanta sa dan sai addinin gaskiya,addinin musulunci ya ɗaukaka a ƙasar nan da ƙasashen nan da yake mulka dan wannan ɗin,Legacy ne da mahaifi na ya bar min,da karatu na da wayewa na da sanin duniya na amma na bar shi na taho wannan ƙasa mai cike da duhu da rashin wayewar kai,toh na rantse da mahalicci na Allah,ba zan bar masarautar nan ba tare da na ladaftar da Sultan ba haka sai na ɗaukaka addinin musulunci ya zaga ko wani lungu da saƙo na ƙasashen nan"!!gyaɗa kai Calva tayi tana mai fatar nasara da alkhairi dan ta san yana iya aikatawa duk da ba ita ta kawo sa masarautar ba Sultan ya saka aka nemo sa aka zo da shi amma sai da ta san yadda tayi ta hargitsa mai yarda da amincin da yake da shi a kan Sultan Baal-Hamon ta hargitsa komai ta rinƙa fallasa asirin Sultan ga Irad tana cusa mai tsanar Sultan duk da ta san dama ya tsane sa..

Fitowa suka yi suka yi sallama kowa ya nufi sashen sa da abubuwa daban daban..

★★★★★★

Tafiyar kwanaki goma sha tara su Juda suka yi akan dawakan su kafin su iso ainihin ƙasar Turkey inda a nan yarima Ziyan ke karatu,sai dai rashin sa'ar su ya riga su isa ƙasar,dan bayan tafiyar ƙasar sai da suka haɗu da abubuwan ban haushi haka aka rinƙa kallon su kamar wasu aliens da suka zo daga wani planet..
Duk sun fuskanci hantara dan gudun su yara suka rinƙa yi,da fari ma yaran ɗauka suka yi irin masu wasar nan ne a Disney suka zo cikin gari sai daga baya suka ga eh da gaske ne waɗannan ba ƴan Disney bane sai suka fara ihu suna gudun su,..
Akwai wani mutumi ɗaya dake zaune a gefe yana kallon duk abin dake gudana toh shine yayi magana da su cikin harshen Turkey amma basu fahimta ba sai ya shiga yi masu da hannu irin alama ɗin nan har dai Agneta ta ɗan fahimce sa akan tambayar su yake yi..
Rasa hanyar yi mai bayani suka yi sai kawai suka wuce sa suna kalle kalle ta ina zasu ga gini mai siffar makaranta dan sun san a nan zasu yi katari da yarima Ziyan..
Da haka suka rinƙa zaga yankin nan sai can basira ta faɗowa Fianna ta furta sunan makarantar dan ta taɓa jin sarki Malik na faɗa,toh fah wannan ne ya sa suka sami sassauci da sauƙin wahalar da suka fara sha a ƙasar Turkey..
Wata mata ce ta yi amfani da wayar hannub ta tayi kira jim kaɗan sai ga ƴan sanda sun taho da yawan su wai sun zo zasu tafi da su dan babu jimawa wata ta zo da mutanin ta suka fasa makarantar suka ɗauke masu ɗalibin su ɗaya kuma daga dukkan alamu wuri ɗaya suka fito da su Juda dan shigar su da yanayin su kusan iri ɗaya ne..
Toh dama suna nemar irin su dan su yi garkuwa da su su yanke masu hukunci..
Su dai su Juda suna ta kallon iko dan basu san me matar nan ta riƙe a hannun ta ba sannan yanayin shigar ta ya Bambanta da irin nasu shigar kamar dai ba daga duniya ɗaya suke ba.
Basu ankara ba suka ga an nufo su sai ko Berenice ta yunƙura da nufin kare su da sihirin ta amma me?sai abu ya ƙi,tayi tayi ya ƙi,haka Agneta itama ta gwada nata amma abu ya ƙi,hankalin su ne ya tashi matuƙa har suka kasa natsuwa dan hatta takubban su kasa iya riƙe sa suka yi dan wani irin kasala ce ta sauko masu,suna ji suna gani aka yi gaba da su sai cikin motar ƴan sanda ga masu kwasar su video na yi ga masu yi masu hotuna suna yaɗawa akan yau sun ga aliens ido da ido,abin sai ya rinƙa janyo ra'ayoyin mutani da dama suka ji suna son zuwa cikin wannan birni dan ganema idanun su shin da gaske ne aliens ɗin ne ko kuma shirme ne kawai irin na mutani..

A taƙaice daga wurin nan aka yi hanyar station da su Juda aka rinƙa iza kawunan su gaba akan wai za'a shige da su cikin cell dan a ji dalilin su na dawowa ƙasar bayan sun rigada sun bar ƙasar da mugun asarar kayayyaki da rayukan mutani,..
Su dai ba sanin abin da suka yi aka kawo su nan suka yi ba amma sun san koma menene toh hakan na nufin laifi ne kuma mai girma tunda har aka kawo su nan cell,bugu da ƙari ba da yaren da suke ji ake maganar ba sam basu saka turanci ciki wanda kaf cikin su Juda da sauran babu wanda bai fahimtar yaren turanci duba da cewa universal language ne kuma a haka suka taso suka ji ana yin sa ko da kuwa basu iya tantance ya ake rubuta sa amma sun san yadda ake furta sa..
Dukkan su aka haɗa aka ƙulle har ma wani kallon banza wanda ya ƙulle su ɗin yake masu irin an kama ɓarayin ɓoyen nan...


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:53&54*

Sai da su Juda suka share kwanaki biyu cikin gidan kaso kana aka fito da su bayan doguwar bincike da aka yi aka gano ainihin tarihin wacce ta taho ta ɗauke yarima Ziyan sannan aka bincika aka ga cewa su waɗannan ɗin,wasu matafiya ne da basu san komai ba yawon su kaɗai suke yi a duniya daga wani ƙauye suke..
  A ranar da aka fito da su sai da Callee ta bige wani ɗan sanda cikin fushi da ɓacin rai ta haɗa sa da bango tana faɗin sai sun dawo mai a karo na biyu dan yanzu ba shi suka ma zuwar ba..
  Jan ta ƴan uwan ta suka yi akan tayi haƙuri ta zo su tafi,..
  Halayyar nasu ma tsorata mutanin wurin yake haka duk yadda suka motsa dai an bi su da kallon ƙasƙanci,duk suna sane amma da yake abin da ya fito da su daban sai suka ƙyale akan kawai su koma ga Baccus su haɗa kai da shi su tunkari masarautar Ottoman duk ko ma me zai fanjama ya fanjama amma wannan tafiyar wahalar ta ishe su..

  Kamo hanya suka yi suka nufi inda aka ajiye masu dawakan su duk rai ɓace suna ji suna gani sun yi asarar kwanaki da dama ga tsarabar rashin nasara da ta same su abin dai bai masu daɗi..
  Yadda ake masu kallon aliens suma haka suke kallon mutanin a matsayin aliens abin tsoro dan tunda suke a rayuwar su da suka taso basu taɓa ganin bindiga ba haka motocin da suka gani basu taɓa ganin sa ba dama dama Agneta da Fianna suna iya shaidawa dan fah yarima Ziyan ya dage sai da ya kawo masu jajayen kunnuwa yankin kuma a motar su suke kwana haka zalika shi kan sa wasu zuwan nasa yakan taho da motar toh shi kaɗai suka sani mai mota bayan shi basu san komai mai kama da motar ba..

  Suna kan tafiyar su zasu nufi hanyar da suka fito sai Balik yayi wani magana da ya saka su reasoning da shi
  "Ni kam ban san me ke cikin wannan gari ba da duk aka gwada amfani da sihiri amma bai yi ba sannan muka yunƙura mu kare kawunan mu da makaman mu amma duk basu mana aiki ba sannan in fah kun lura,kaf mutanin ƙasar nan shigar su ba irin tamu bane sannan ɗabi'un su ya Bambanta da irin tamu ɗabi'un wannan shi ake kira da _Bambancin Ƙasar_"??..
  Kasaƙe Berenice tayi sannan ta gyaɗa kai tana faɗin
  "Yaya na kana da tunani sosai,ka san abin nan ya daɗe yana dami na a kai na amma furtawa ne kaɗai ban yi ba sai gashi kai ka furta a zahiri,nima ina ganin kamar wannan ake kira _Bambancin Ƙasar_"..
  Karɓe maganar Fianna tayi tana faɗin
  "Yanzu abin yi kawai shine,me zai hana mu canza ɗabi'un mu zuwa irin nasu,a gani na fah,dan kun ga ai ba iya mu ke cutuwa ba a cikin yaƙin nan,mutanin dake zaune a ƙasar nan ta Sultan da abokanan sa duk suna cutuwa,duba da yadda Juda ta mana narrating ainihin labarin addini har ta ce islam na da sharuɗa da dama sannan an yi ƙiyastin al'adu da addinai sun sami ra'ayoyi iri ɗaya dan haka mutum ke iya haɗa biyun yana rayuwa da su,sai nake ganin kamar in muka zauna tare da mutanin nan muna iya zamowa sanadiyar fallasuwar Sultan Baal-Hamon,kun dai san ba wai ba'a kai ilimi ƙasar bane,a'ah,shine dai ya canza komai hawar sa kujerar mulkin nan,shi ya lalata komai dan an ce ba dan shi ba toh da ba haka muke rayuwa ba kuma tunda kuka ga mun yi amfani da sihirin mu amma bai amfanar da mu ba toh ina ga kawai mu zauna tare da mutanin nan mu saba da su mu sanar da su gaskiyar lamarin nan in ya so sai su biyo mu mu tafi tarekun ga in sun tafi suma ai ba lallai bane sihirin Sultan yayi aiki a kan su ba tunda su ɗin wasu irin mutani ne,ya kuka gani"?..
  Nannauyar ajiyar zuciya Juda ta sauke sannan ta gyaɗa kan ta tana faɗin
  "Fianna,kina da kaifin tunani sai dai matsalar,,,"sai tayi shiru sai duk suka sauko daga kan dawakan nasu suka nufo ta itama ta sauko ta tsaya haɗe da ɗora hannun ta a waist ɗin ta tana mai hurar da iska waje kafin ta cigaba
  "Ina tsoro,,hala ma Sultan ya rigada ya gama da tarihin ƙanwata,kun ga duk ku,naku matsalar ƙanƙani ne akan nawa matsalar,mahaifiyar mu na can na mana fatar kariya,tana fatar ganin na koma gida tare da ƙanwa ta,and here i am,leaving in the bondage of the Sultan,ya zan yi da rayuwa ta?i have to go and search for my aunts,my two aunts,i have to create peace in my own land,Babylon,i have so much to balance but i am unable because of this strange Sultan,ya zan yi da rayuwa ta"??..
  Wato tunda Juda ta fara zayyano kalaman ta sai Callee tayi shiru ta natsu tana sauraron ta dan tun da sule tare da Juda bata taɓa faɗa masu sirrin ta ba sai yau,wato tana da tarihi ne kusan irin nata dan itama tana son nemo families ɗin mahaifiyar ta kamar dai yadda Juda ta faɗin ne..
  Kamar an mare ta sai ta ɗago idanun ta ta saka cikin na Juda da yanzu ta juyo dan ganin me Callee ke yi..
  "Ya sunan aunts ɗin naki Juda"?da mamaki duk suka kalle ta sai ta amsa mata da
  "Aunt Daliyah da aunt Yahaira,sunayen su kenan kuma su suka rabu da mu suka rabu da ahalin mu sakamakon aure da ya ɗauke su tun lokacin bamu kuma ji daga wurin su tun mahaifi na na neman su gashi yanzu ya mutu sai ni alhakin nemar su ke kai na dalilin haka ma ya sa kuka ga duk na damu in ga komai ya faru ya wuce"!!cikin hanzari Callee ta tari numfashin Juda
   "Ban san ki ba ban kuma san ya aka yi sunan mahaifiya ta ya zo daidai da na aunt ɗin ki ba da ƴar uwar ta dan nima sunan yar uwar mahaifiya ta Yahaira kuma suma aure ne ya rabo su da ahalin su basu kuma jin labarin su ba sai daga baya da suka tafi inda suka taso a nan suka ci karo da zancen barin du yankin sakamakon yaƙin da Sultan Baal-Hamon ya aika a yi a wurin sannan da saka hannun mutanin masarautar Babylon ɗin"!!da sauri itama Juda ta kalli Callee ta ce
  "Ya sunan waɗannan ahali na mahaifiyar ki"?gaban ta na faɗi tayi tambayar sai Callee ta amsa mata da
  "Mahaifiya ta tace sunan mahaifin su Artegal Ted,sunan babbar yayan su kuma Baadi Artemas iya abin da na sani kenan"!!ai a wani irin mugun kiɗimewa Juda ta janyo hannun Callee tana ƙoƙarin shafa fuskar ta..
  Sai suka zamo abin kallo ga su Fianna da abin ya ɗaure masu kai ganin kamar jini ne ke son bayyana kan sa sai dai suka natsu dan jin inda labarin zai kai..
  Hannun Juda na ɓari ta shafo fuskar Callee tana faɗin
  "Callee...ni...ni..ni ce,.ni ce ɗiyar Baadi Artemas kuma shine babban wa ga ƙannin sa biyu,Yahaira da Daliyah ban sani ba ko daga ahali ɗaya suka fito ba amma suma sunayen su kenan sai dai ban sani ba ko jini ɗaya na fito tare da ke"!!?..
  "Kallon ta itama Callee tayi tana nazarin kalaman ta sai wata dabara ta faɗo mata sai ta tambayi Juda
  "Shin,mahaifin ki ya taɓa shiga matsala a masarautar Babylon har aka saka sa a bursinar koyar da hankali na tsawon satittuka"??saurin gyaɗa mata kai Juda tayi sai ta kuma tambayar ta
  "Shin ya taɓa tsaron sarkin Babylon har ya aka mai sharrin cewa ya haukata dokin yaƙin sarki wanda yayi sanadiyar ɗaure sa da aka yi"??baki na ɓari ta gyaɗa ma Callee kai tana faɗin
  "An yi haka Callee an yi haka wanda sanadiyar sa ne ma ya sa mahaifi na ya sami damar auren mahaifiya ta"!!!tun kafin ta ida maganar Callee ta kuma tarar ta da
  "Sunan ta gimbiya Hadara"??da mamaki Juda ta gyaɗa mata kai tana faɗin
  "Ya aka yi kika san haka Callee"?.ajiyar zuciya kawai Callee tayi tana jin daɗin haɗuwa da wani ɓangare na rayuwar ta kuma jinin ta..
Rungume Juda tayi tana faɗin
"Bambancin jini da bare kenan Juda,wani abin mamaki shine tunda muke tare da ke tsawon kwanaki bamu taɓa sani ba amma sai gashi yanzu out of the blue mun gane cewa mu ɗin jinin juna ne,am happy"!!sai da sauran suka ji kamar su taya su kukan farin cikin da suke yi..
Sai da abin ya lafa sannan suka tsaya dan tsayar da magana ɗaya dangane da batun abin,tunda ko ba komai abin ya zo ma Juda da sauƙi dan yanzu ta gano ƴar uwar ta ta san kaso sittin ya ragu cikin kaso ɗari na matsalar ta..

Shawara suka yanke akan su nemi masana su sanar da su matsalar su in ya so sai su sami mafita mai sauƙi da taimakon mutani..
Wannan shawar ta karɓu a gare su sai dai basu san yadda zasu fara tunkarar rayuwar nan ɗin ba sannan tunanin Baccus na ran su basu san ya zasu yi ba in ya gano cewa sun baro wurin kuma basu sanar da shi ba..
Dawakan nasu suka riƙe ma akala suna tafiya suna tunanin inda zasu nufa dan ajiye dawakan..
Suna tsaka da tafiyar ne idanun su ya kai wani wuri inda ake adana dabbobi dan nishaɗin nutani da yara,sai suka yi tunanin su kai nan a ajiye masu har su kammala abin da suke da nufin yi..
Da fari ƙin yarda mai kula da wurin yayi sai daga baya da ya ga irin ƙadarorin da Fianna ta nuna mai kuma ya san zai amfana da su sai ya karɓi ajiyar dawakan har ma da masu tayin su zo ya kai su masauki sai dai suka ƙi yarda suka nuna basu so..
Bai tsananta masu ba haka suka kama hanya suna tafe suna kalle kalle siffar dai ƙauyawa da basu taɓa ganin big city ba sai town ɗin da suka taso ciki..
Haka kawai sai Juda ta

Please Login or Register in order to submit comment