Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin da ya bata mamaki
  "Na san abin da ya kawo ki kuma ina mai yi maki albishir da yau ba sai gobe ba zan baki shi dan gashi nan a hannu na"ta faɗi hakan tana mai fiddo kundin wanda ya saka Agneta waro idanun ta waje cikin mamaki da walwala wanda ya saka Juda gane tsaurin ido ne kawai gare ta amma akwai yarinta a ƙwaƙwalwar ta dan haka zata iya juya ta son ran ta..
  Kawo hannu Agneta tayi zata karɓi kundin sai Juda ta maida hannun ta baya hakan ya saka Agneta yi mata kallon ban gane ba sai reaction ɗin nata ya ba Juda dariya,darawan tayi sannan ta ce
  "Agneta ni ba wawiya ba ce da zan baki wannan kundin kai tsaye ba,kema kiyi tunani da kan ki in yana aiki kenan,kin taɓa ganin inda aka jefa dutse a wuta aka fitar da shi ba tare da ya canza launi ba"??
  "Me kuma wannan magana taki take nufi"!!?tambayar da Agneta ta ma Juda kenan wanda ya bata dariya ta kuma darawa kafin ta bata amsa da
  "Abin da nake nufi a nan shine,,ba'a yin nasara kai tsaye sai an sha gwagwarmayar rayuwa haɗe da ƙalubalen rayuwa kala kala,zan baki kundin nan amma sai kin min wani aiki dan na lura,,you are brave"!!!ta faɗi haɗe da ɗage gira ɗaya sama..
   Take Agneta ta gano inda zancen Juda ya nufa dan haka sai ta rage muryar ta ƙasa haɗe da faɗin
  "Me kike so"?murmushi Juda tayi ganin zalamar Agneta ƙarara a sarari sai ta hau zagayeta tana faɗin
  "Smart,i see,ba wani aiki mai wahala zaki min ba,so nake mu tafi da ke fadar sarauniya Zinaida ki fiddo min da wani bawan da aka yi garkuwa da shi mai suna Balik,idan kika yi nasarar fiddo min shi ni kuma na alƙawarta maki kyautar wannan kundi kyauta na har abada"!!....

  Jikin Agneta gabaɗaya ya yi sanyi jin sharaɗin da aka bata dan mallaka mata wannan kundi kuma bata jin tana iya haƙura da wannan dama saboda alƙawarin da sarkin ƙasar su ya mata na bata matsayi mai girma haɗe da bata kyauta mai tsoka da muhimmanci in har ta koma mai da kundin nan,dan haka ba zata yarda ta rasa wannan damar ba ko da kuwa hakan na nufin tayi kisa ne dan cika burin sarkin ta gashi tana da cikakken labarin tsana dake tsakanin sarkin ta da sarauniyar wannan ƙasa harda ma sarkin Ottoman kowa dai na da ɓoyayyen sirrin sa a cikin sa tsakanin waɗannan masu mulkin masarauta uku...
  Muryar Juda ne ya daki kunnen Agneta sai tayi firgigit ta dawo hayyacin ta haɗe da faɗin
  "Na yarda da ko ma menene muddin zaki mallaka min kundin"!!tafi Juda tayi ta ce
  "Zamu tafi mu haɗu da abokan tafiya ta in gabatar maki da su suma in gabatar masu da ke da amfanin ki cikin mu"!!gyaɗa kai Agneta tayi sannan ta biyo bayan Juda suka tafi..

  Ba wata tafiya mai tazara suka yi ba suka isa inda su Berenice suke suna jiran dawowar Juda,sai dai abin da ya saka su a duhu shine ta yaya tayi gamo da wannan matar sannan ina ta samo ta,amma amsar tambayar tasu na gare ta dole ita zata basu amsar tambayar...
   Suna nufo su babu wani nuƙu nuƙu Juda ta gabatar da ita sannan ta gabatar da su suma haɗe da fassara masu manufar sako Agneta cikin shirin su,abin da ya ɗaure masu kai kenan dan haka Berenice ta riƙo hannun ta suka ja gefe haɗe da tambayar Juda
  "Are you crazy?how can you involve this stranger in our plan,how could you"??..murmushi Juda tayi sannan ta riƙo kafaɗun Berenice tana mai yin ƙasa da muryar ta ta ce
  "Yarinyar da na ce da ke ta zo min rannan akan in bata kundin nan"!!!gyaɗa kai Berenice tayi sai ta jijjiga kai tana mai cigaba 
  "Ita ce wannan"!!zaro idanu Berenice tayi tana faɗin
  "Juda baki da lafiya ne"?maido fuskar gaske Juda tayi tana faɗin
  "Kina ji na yarinyar nan na da wauta ba kaɗan ba tsabar zalamar ta ce ta saka ni gano tsantsar rashin wayon ta dan haka she is willing to do anything in exchange for this prophecy,dan haka ita zata yi mana jagora a daren yau da zamu nufi masarautar Mughal,zata tafi tare da yin garkuwa da ɗiyar sarauniya Zinaida a matsayin ta kamo ta ni kuma zan shigo da kan mayaƙin nan,yayin da Agneta zata gabatar da gimbiya Ondrea haɗe da yi mata alƙawarin kundin nan ni kuma zan kawo mata kan sannan in buƙaci ƴanta bawa Balik kin ga kenan jiki na rawa zata bani izinin tafiya da ɗan uwan ki tunda abin da take buƙata ya zo hannun ta ga ɗiyar ta ta dawo mata sai dai inda za'a sami matsalar shine,in na buƙaci ta bani da lallami ta nuna min isa da iko toh a nan zan harzuƙa in nuna mata nawa ikon nima"!!jijjiga kai Berenice tayi cikin gamsuwa da shawarar da Juda ta bayar sai dai akwai matsala ɗaya dan haka bata yi nauyin baki ba ta tambaye ta
  "Amma ina fatar kina sane da cewa gimbiya Ondrea da soja Cahal sun gudo ne ba dan suna fatar sake komawa masarautar nan ba sai dan su tserewa sarauniya Zinaida,toh ta yaya zaki maida gimbiya Ondrea ga mahaifiyar ta alhalin bata son komawa"??gyaɗa kai Juda tayi tana faɗin
  "Wannan abu mai sauƙi ne Agneta zata kula da wannan saboda kar ki damu"shiru kawai Berenice tayi ba dan ta gamsu da kalaman Juda na ƙarshe ba..

  Komawa suka yi inda suka bar Agneta da su Cahal a tsaye a nan Berenice ta masu bayanin komai kamar dai yadda Juda ta mata bayani,tuni idanun gimbiya Ondrea suka tara ruwa ta shiga risgar kuka ita sam ba zata koma masarautar su ba sai da abin ya fusata Juda ta ji kamar ta hamɓare ta sai kawai ta share ta ta wuce tana mai faɗin
  "Ni dai ku san yadda zaku yi dan babu fashi daren yau zamu aiwatar da shirin mu in kun ga kukan shi zai kawo maku mafita sai ku cigaba da sauraron ta"...
  Babbar magana an ma mai dami ɗaya sata,yanzu ya zata yi ta yaya ma wannan matar zata ce zata maida ta gida kawai dan ta aiwatar da nata ƙudirin..abin da ke ta bijiro wa gimbiya Ondrea a zuciya kenan sai kawai ta kalli Cahal ta ce da shi
  "Masoyi na,ka zo mu gudu,daga gani wannan yarinyar bata da kirki,ƙila aiko ta my king tayi dan ta zo ta wargaza mu kar ka yarda da ita"..girgiza mata kai Cahal yayi yana faɗin
  "No,we won't dear,dole akwai wata mafita da zasu samar mana gimbiya ta kar ki damu ki kwantar da hankalin ki"..iya ruɗewa gimbiya Ondrea ta ruɗe tayi ƙoƙarin fahimtar da shi amma ya ƙi ya dage akan dole su bi shirin su Juda dan su wanye lafiya,ba dan ran ta ya so ba haka ta haƙura ta ƙyale sa da burin samin mafitar kamar yadda ya ce ɗin...

★★★★★
  _THE NIGHT AT KING ZINAIDA'S PALACE_

  can cikin yammar dare suka kamo hanyar masarautar sarauniya Zinaida cikin shirin su ta kamala kamar wasu mutanin ƙwarai sakamakon shawarar da gimbiya Ondrea ta ba su na in suka tafi a haka da suturun jikin su toh sarauniya Zinaida na iya ɓullo masu ta bayan gidan tunda ba imani ne da ita ba,wannan shawarar tayi tasiri a zukatan su wanda ya saka Agneta samar masu suturun ta hanyar tafiya wun wani mai siya da sayarwa ta bashi wani ƙarfen da ta mallaka a yayin yaƙin ta wanda ƙarfen ya kasance ƙarfe ne mai ɗauke da tarihin dogon lokaci kenan kamar ƙadara ce,akan ya ara mata suturun ya riƙe ƙarfen in sun dawo da su sai ya maida mata ƙarfen,ya kuwa amince sai abin yayi armashi dan sun fara tunanin ta yaya zasu samo wasu suturun..
  Abin daɗin ma shine yadda suka taho cikin keken doki kamar dai daga wata masarautar suka fito duk cikin kayan aron ne,babu gayyata ko sanarwa amma haba haba aka tarbe su ganin shigar su ya saka masu kula da masarautar ganin kamar masu matsayi ne dan haka jiki na ɓari mai sanar da sarauniya saƙo ta ƙarasa turakar ta da take hutawa da maza abokan hutawar ta..
  Da fari kamar zata haɗiye mai kawo saƙon dan masifa sai daga baya da ta ji yanayin baƙin
  "Ta ƙofar ina suka shigo"amsa mai saƙon ta bata da
"Ta ƙofar kudu"!!wuf ta miƙe ta nufi hanyar bayin gidan ta tana faɗin
  "Ki tabbatar sun sami tarbar da ba'a taɓa ba ko wani baƙo ba"!!.gyaɗa kai tayi sannan ta fita ita kuma ta shige bayin dan kimtsa kan ta haɗe da sallamar saurayin..

  Dabarar da suka yi shine an naɗe fuskar gimbiya Ondrea haɗe da saka mata wata arab indian niƙaf da ya sauko ya rufe mata fuskar ta ta yadda sai dai ita ta ga na waje amma na waje ba zai gan ta ba yayin da Cahal kuma yayi shigar larabawa haɗe da naɗe makawiya(turban)a kan sa da ya juyo zuwa fuskar sa ya rufe ta yadda ƙwayar idanun sa kaɗai ke bayyane,Berenice da Agneta kam shigar gimbiyoyi suka yi kayan jikin su kusan iri ɗaya sai dai Berenice ta saka wani irin hula ne babba da ya rufe kusan fuskar ta dan girma da faɗin sa ta yadda ba za'a gane fuskar ta ba, ita kuma Juda doguwar buɗaɗɗiyar riga ta saka ruwan madara ta naɗe sumar kan ta kamar dai yadda sauran suka yi da na su sumar..

  Suna zaune aka shiga yi masu hidima har dai aka cike gaban su da abinci kala kala da abubuwan shan iri iri,suna cikin taɓa abincin ne suka ga ƙofar fadar ta buɗu sai duk suka mai da hankalin su da idanun su ga ƙofar dan ganin ko wa zai fito...

*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:56] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:27&28*

  Ƙamshi da sanyin da ya doki hancunan su ne ya saka su daɗa maida hankalin su ga ƙofar dan son ganin mai fitowar,da fari wasu bayi ne biyu suka fito kafin su hango riga mai jan ƙasa  a buɗe,takun ta na tafiya daidai da saukar rigar ta matakala,ɗaya bayan ɗaya a tsanake take takun nata har ta ƙarasa saukowa inda suka shagala suna kallon ta har ta iso kan kujerar ta na mulki da isa kuma na ganin baƙi..
 Zaman ta yayi daidai da bugun ƙirjin gimbiya Ondrea dan gani take mahaifiyar ta na iya gane ta,hakan ya sa ta daɗa shigewa jikin Cahal wanda duka tsarguwar ta a idanun Juda dan tana ankare da duk wani motsin ta sai dai tayi kamar bata gani dan kar shirin su ya lalace..

  Cikin ƙasaita ta masu maraba haɗe da tambayar su ko abubuwan da aka kawo masu yayi ko kuma a ƙaro wasu suka amsa mata da yayi kuma jun daɗin su ne tarbar da ta masu,wannan abin ya daɗaɗa zuciyar sarauniya Zinaida dan ta yi farinciki.
Juda ce ta jagoranci jawabin kamar haka
  _"Sarauniya Zinaida,ni sunana gimbiya Zarine amma zan fi jin daɗi in kika kira ni da Zarina sakamakon sunan da mahaifi na ya bani kenan,wannan"ta faɗi tana mai nuna Berenice kafin ta cigaba"sunan ta Alyna,ƙanwata ce daga masarauta ɗaya muka fito kuma babbar abu ya kawo mu masarautar ki da fatan zamu yi komai cikin aminci"_..
   Gyaɗa kai sarauniya Zinaida tayi jin sigar maganar Juda da bata da maraba da ta gidan sarauta sai ta tuno da yanayin da ɗiyar ta ke magana dan haka ta ce da Juda
  "Na ji daɗin wannan gabatarwar taku sai kika tuno min da ɗiya ta da ta ɓace kimanin sati biyu da suka wuce sakamakon shigo min masarauta da mutanin sarki Sultan Baal-Hamon suka yi,sun kwashe min bayi sannan suka ɗauke min ɗiya ta,my princess"tayi maganar ƙarshe da alamar disappointment ƙarara irin an zalince ta ɗin nan..
Riƙo hannun gimbiya Ondrea Agneta tayi ganin zata fallasa su tun basu taka kashi kwata cikin shirin nasu ba sai ta daɗa yin lamo jikin Cahal tana mai runtse idanun ta har dai ta sami natsuwa..
  Ajiyar zuciya Juda tayi cikin ƙasaita tana mai girgiza kai alamun tausayawa ga sarauniya Zinaida kafin ta yi magana
  "Am sorry and i apology for making you to recall the hard past two weeks"saurin girgiza kai sarauniya Zinaida tayi tana faɗin
  "Kar ki damu dama haka rayuwa take"sai suka gyaɗa kai gabaɗayan su sai Juda ta tambaye ta
  "Toh yanzu ya ake ciki da batun nemo ɗiyar taki"?ɗan murmushin yaƙe tayi kafin ta amsa mata da
  "Babu,,.na bar ta dan na san ganin ta yanzu zai min wahala gashi ban iya rashin adalci ba,ba zan iya farma sarki Baal-Hamon ba da na rama abin da ya min sai dai na saka addu'a a gaba na akan wataran,ɗiya ta ta dawo min"..
  Lallai wannan mata hatsabibiyar kan ta ne ta iya shirya zance,wannan tunani ne da ya faru a zukatan mutani uku wato Berenice gimbiya Ondrea da Cahal yayin da Juda kuwa ta jinjina wa tsari irin nata..

  "Na ji sunan ki da ta ƴar uwar ki amma ban san sauran ba ko su waye"!!ɗan zabura Juda tayi alamar mantuwa tana faɗin
  "I beg your pardon king,zasu gabatar maki da kan su"murmushi sarauniya Zinaida tayi sannan ta maida duban ta ga Agneta dake nan kamar wata babin roba a zaune saboda yanayin jikin ta da suturan dake jikin ta
  "Ni suna na Aarah,ni gimbiya ce amma a masarautar sarkin farauta wannan kuma yaya na ne sunan sa Salman da matar sa mai suna Reedhah duk masarauta ɗaya muka fito,a tafiyar mu ta kawo maki abin alkhairi muka haɗu da waɗannan gimbiyoyi biyu wato gimbiya Zarine da gimbiya Alyna waɗanda suka nuna mana nan suka nufa sai muka haɗa hanya dan kawo maki ziyara haɗe da godiyar gudunmawar da kike bawa al'umar ki da ta wasu ƙasashen"..
  Daɗi sosai sarauniya Zinaida taji jin wai an zo yaba ma mulkin ta sai ta ji kamar ta gama mallakar kundin ne a hannun ta sai ta sake jiki ta rinƙa hira da su ba tare da hankalin ta ya kai ga cewa gimbiya Ondrea da Cahal haɗe da Berenice basu furta kalmar 'a' ba bare ya kai ga su buɗe fuskokin su ta gan su dan sanayya ba,tsara ta da zancen da su Juda da Agneta ke yi ya sa ta manta ta sha'afa da waɗannan abu biyu..
  Suna lura da lokacin su har zuwa gaɓar da suke buƙata sannan suka sako zancen su cikin hirar tasu
  "Zaki ji mamaki idan na ce da ke ga kundin sihirin sirrin mallakar duniya kyauta"!!?maganar sai ya doki kunnen sarauniya Zinaida ya zo mata kamar tambaya kuma kamar magana cikin zance wanda ke iya zamowa kamar armashin zance..
  Kallon Agneta tayi wacce ta fiddo zancen daga bakin ta tana mai yi kamar ba wata gagarumar magana ta faɗi ba.
"Gimbiya Aarah ban fahimce ki ba"?murmushin nasara Juda tayi yayin da Agneta ta yi nata murmushin a zuciyar ta sannan ta ce
  "Na san zaki yi mamaki sarauniya Zinaida amma ba abin mamaki bane,dama mallakin ki ne tun asali kuma yanzu nemar ki ta zo ƙarshe dan a yau ba gobe ba zan mallaka maki kundin nan saboda jin daɗin hukuncin da kike ma mutanin Ottoman masu yin katsalandar a harkokin ki"da murmushi ta yi maganar tana mai zuba idanun ta kyar cikin idanun sarauniya Zinaida wacce zuwa lokacin ta ruɗe da kalaman bakin Agneta da take amsa sunan Aarah a wannan wurin..
  Kasa riƙe mamakin ta sarauniya Zinaida tayi sai da ta furta
"Kina nufin da gaske,kin taho min da kundin nan"?saurin amsa mata Agneta tayi ta hanyar girgiza mata kai tana faɗin
  "Kar ki sami shakka akan zantuka na,ki yarda da ni hum"?kallon ta sarauniya Zinaida tayi tana tunanin anya gaske ne ko wasa
  "Kar ki damu,zan baki ai kin cancanci fiye da hakan ma"jiki na rawa sarauniya Zinaida ta shiga tambayar shin ya aka yi ta samo sa..
  Ƙarya ta shirga mata da ya saka ta zamowa convince akan zantukar Agneta sai kuma Juda tayi ƙasa da muryar ta ta matso kusa da kunnen sarauniya Zinaida tana mai faɗin
  "Na taho maki da tsarabar da zai sanya ki farinciki fiye da zaton ki"..juowa tayi tana kallon Juda sai ta ce
  "Me ke nan gimbiya Zarina"?.murmusawa Juda tayi tana faɗin
  "Yanzu kuwa zaki gan sa"daga haka ta miƙe ta nufi hanyar waje tana faɗin
"Reedhah,taho mu je"dama a hannu take dan haka tana jin haka ta miƙe wuf ta bi bayan Juda jikin ta na kyarma suna fita ta yaye mayafin fuskar ta ta shiga zazzaro idanu tana magana cikin fargaba
  "Ju....juuuu...Judaaa...na gaji..na gaji...ina son barin gidan nan yanzun nan,,ki zo ki fitar da ni"!!riƙo kafaɗun ta Juda tayi tana girgiza ta tana mata magana
  "Relax,ki natsu ki saurare ni,babu inda zaki tafi abin da nake so da ke shi ne ki cigaba da kama kan ki har mu bar wurin nan cikin kwanciyar hankali"janye jiki gimbiya Ondrea tayi daga tiƙon da Juda ta mata tana faɗin
  "Baki ji bane?sharrin da mahaifiya ta tayi yana nufin dama ba son gaskiya take min ba dole akwai abin da take so da ni ki min rai in bar wurin nan ni da masoyi na"juya kai Juda ta shiga yi tana faɗin
  "A'ah kar mu yi haka da ke in ba haka ba zata zargi wani abu kawai ki cigaba da kame kan ki ni na maki alƙawari muna gama yin abin da ya kawo mu zan bar ki ki huta ke da masoyin ki"ba dan ta so ba haka ta share hawayen ta ta maida mayafin fuskar ta rufe fuskar luf daga haka suka buɗe bayan keken dokin da suka taho da shi inda a nan Juda ta ciro kan mutumin da ta yanka wanda ta naɗe sa cikin wani ƙaramar buhu ta yi gaba yayin da gimbiya Ondrea ta biyo bayan ta suka koma ciki..

  Shigowar su ya sa hankalin su gabaɗaya dawowa ga su Juda da suka dawo,murmushi ne shimfiɗe saman fuskar ta suka zauna,gabaɗaya hankulan su ya dawo ga buhun dake hannun Juda kamar dai irin basu san me take riƙe da shi ba..
  Kasa natsuwa sarauniya Zinaida tayi dan haka ta shiga tambayar Juda
  "Am eager,na matsu gimbiya Zarina,ki nuna min" ɗan dariyar gefen baki Juda tayi tana faɗin
"Yanzu kuwa"tana gama faɗin haka ta hau buɗe buhun sai hankalin sarauniya Zinaida ya koma kan buhun ta matsu ta ga me ke cikin buhun..
  Ba'a ɗau lokaci ba sai Juda ta gama buɗe buhun tana mai kallon ƙwayar idanun sarauniya Zinaida tana tunanin yadda zata yi reacting in ta ga kan..
  "Kin shirya ganin tsaraba ta"?da sauri ta gyaɗa kai,wurgo mata kan tayi ya gungura ya dakata a daidai gaban sarauniya Zinaida saman rigar ta mai kala ja sai kawai sarauniya Zinaida ta waro idanun ta haɗe da miƙewa tsaye kamar ta ga wuta a gaban ta ai sai Juda ta faɗaɗa murmushin ta ta miƙe tsaye tana faɗin
  "Surprise king Zinaida"ɗago idanu sarauniya Zinaida tayi tana ma Juda kallon mamaki ya aka yi haka ta yaya.
  Kamar dai Juda ta karanta zuciyar sarauniya Zinaida dan haka ta furta shi a zahiri sai ta gyaɗa kai sai Juda ta ce
  "Da kyau,kin san ni buri na shine in farantawa mai faranta min ko da ba'a san da ni ba bare ke,da na san ki dan haka wannan ita ce kyauta ta a gare ki na san kin san ma'anar kyautar nan da kuma inda ta fito"? ..
  Ta kiɗima iya kiɗimewa sai dai farinciki bibbiyu ne ya kawo mata ziyara ga kyautar kundi ga albishir da aka kawo mata..
  "Gimbiya Zarina wannan irin kyauta da kika kawo min,,!me zan baki dan in nuna yabawa ta gare ki da wannan kyautar da kika kawo min"?an zo wurin in ji mai tsoron wanka a cewar Juda cikin zuciyar ta
  "Bana buƙatar komai sai abu ɗaya"!cikin farinciki sarauniya Zinaida ta ce
"Menene wannan abin da kike so"?a tsanake Juda ta bata amsa da
"Bawan ki Balik da aka yi garkuwa da shi kwanakin baya"!kamar dirar miƙiya haka ta ji request ɗin Juda a kunnen ta sai ta tambaye ta
  "Ta ya aka yi kika san sa"?murmushi tayi ta bata amsa da
  "Mahaifin sa marigayi ya kasance amintaccen bawan mahaifin mu sarki Fa'il kuma babu abu na shi da bai sani ba,sai dai matsala ɗaya da aka samu shine,,ya munafurci mahaifin mu ya ma ƙarya sannan ya ƙi bayyana mai inda ya ɓoye mai sirrin sa da ya sace har ya mutu,.toh mun sami labarin akwai ɗan sa da aka yi garkuwa da shi a nan ƙarƙashin ikon ki kuma yana gidan nan,abin da nake so shine ki bani shi na wasu mintuna in mai tambayoyi in na gama sai a maida sa dan ba zai amfane ni da komai ba sai baƙin ciki dan haka ki miƙo min shi in gama abin da zan yi sai a maida sa"ɗan jim sarauniya Zinaida tayi sai dai ba ta so a zarge ta kamar dai yadda ta nuna cewa ita ɗin saliha ce amma bata jin zata gama yarda da su Juda gabaɗaya dan haka sai ta saka fake smile haɗe da faɗin
  "Abin da kike so yanzu zan maki,ai ni a gare ni kun zame min alheri dan ban san da me zan saka maku ba"murmushin gamsuwa suka yi su biyun.
  A baɗini kaf abokan tafiyar Juda sun yi mamakin wannan hikima nata dan basu yi tsammanin basira da kaifin fasahar ta ya kai har nan ba,sai a yanzu Berenice ta ƙara gasgata maganar da Juda ta gaya mata a haɗuwar su ta farko wato kalmar_Ban yarda da kowa ba kuma ba zan taɓa yarda da kowa ba_ wannan kalma ya maimaita kan sa a nan dan gashi dai sun gama tsarin su kafin du shigo masarautar sai dai yanzu ta sauya komai kaf babu plan nasu ko ɗaya da ta sako cikin wannan ziyara tasu lallai Juda ta san duniya..

Ƙwala kiran wani gursumin namiji tayi sai ga shi ya zo fuskar sa a ɗaure gashi nan dai dan kyakyawa amma ya haɗe fuska,da zuwan sa sai yayi ƙasa da kan sa.
  Buɗan bakin sarauniya Zinaida sai ta juya harshe tayi magana da harshen da su baƙin basu sani ba abin da ya ɗan razana su kenan amma suka kame,.
Tana gama bada umarnin ta ɗago kai kamar ta ƙwarai ta kuma yi masu godiya haɗe da sanar da su an ba su masaukin da zasu kwana zuwa washegari da zasu kama hanyar komawa haɗe da tambayar Agneta shin da yaushe zata bata kundin sai ta amsa mata da safiyar gobe dan dole ta kwance sihirin da aka lulluɓe kundin da shi,hakan ya gamsar da sarauniya Zinaida dan ta san abin da ta shirya masu,kowa dai murmushin yaƙe yayi amma na ciki na ciki kowa ya barwa kan sa
  "Ga shi nan shi zai kai ki ga bawa Balik"gyaɗa kai Juda tayi sai sarauniya Zinaida ta sallame su akan sai da safe zata tafi ta kwanta,daga haka suka yi sallama shi kuma gursumin ya tsare su da idanu kamar waɗanda suka aikata laifi sai Agneta ta ce da shi
  "Can you excuse us before leaving for Balik asylum"?ɗan gyaɗa kai yayi sannan ya juya masu baya dan wai ya basu sararin yin sirri.
  Abin bai ma Agneta ba dan haka ta ɗan ɗaga mai murya tana faɗin
  "Are we behemoths here "?girgiza kai yayi daga bayan da ya juya masu sannan ya fita bakin fadar ya rufo masu ƙofa.
  Gimbiya Ondrea na ganin fitar sa ta yaye mayafin fuskar ta ta shiga magana a ruɗe tana ɓarin jiki
  "Juda,sarauniya sakawa tayi a kashe ki sannan ayi garkuwa

Please Login or Register in order to submit comment