Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga wani kamar ta san shi dan haka ta fara bin hanyar da yake bi,ba tare da sanin sa ba ta rinƙa bin sa a baya tana fatar ganin eh wanda take tunanin ne..
A daidai wani kwana ya tsaya ya saka hannu ya buɗe ƙofar wurin ya shige sai ta tsaya a wurin dan ganin ko zai kuma leƙowa sai dai sharewar lokaci bai dawo ba abin da ya ɗan ɓata mata rai kenan har ta kasa haƙura ta hau bubbuga ƙofar..
Ba'a buɗe ba sai da ta buga kusan sau huɗu sannan aka buɗe ana mai leƙowa dan ganin mai buga ƙofar..
"Wa nene"?tambayar da aka yi kenan sai Juda ta ɗan dawo ta gaban gidan tana kallon fuskar mai tambayar..
Kamar dai ta so shaida fuskar amma kasancewar wacce ta sani ba a nan take ba kuma ta san babu abin da zai kawo ta nan sai ta kawar da tunanin tana faɗin
"Na ga wani ne yayi nan toh ya min kama da wanda na sani ne shi yasa na biyo sa amma kiyi haƙuri,sai anjima"!!tana gama faɗin hakan ta juya da nufin tafiya sai ta jiyo muryar sa yana faɗin
"Gimbiya ta waye wannan"?ko a bacci ta san sigar maganar sa haka ta san salon da yake amfani da shi wurin magana sai tayi saurin Juyowa tana addu'ar ganin fuskar nasa..
Muryar Callee ta jiyo tana faɗin
"Hala wani hanyar ta bi daban dan kun ga bata nan fah kuma ɗazu muna tare"muryar Agneta ta jiyo tana faɗin
"Ai ni na ga ta nan ta bi dan ina ta kiran ta amma ban san inda hankalin ta ya tafi ba bata saurare ni ba"..
Juyawa tayi gare su tana kallon su sai ta rasa wani direction zata juya ta kalla,shin ta juya wancan direction ɗin ne ko ta juya ta gefen su Agneta ne bata sani ba..
Idanun Fianna ne ya sauko kan ta da take tsaya ta ɗan juya masu baya kaɗan sai ta ce
"Ga ta can,ko ba Juda bace wancan"?a tare suka juyo suka gan ta tsaye sai suka ƙaraso gare ta duk Berenice ta fi damuwa dan sun saba sosai ita tunani ma tayi hala dan abubuwa sun mata yawa ne ya sa ta tafi wani wurin sai yanzu da suka gan ta ne ta tabbatar bata tafi ko ina ba dole wani abin ne ya kawo ta nan..
"Shin me ya kawo ki nan ne Juda mu muna can muna ta nemar ki"?tambayar da Berenice ta mata kenan sai ta girgiza mata kai tana faɗin
"Babu,kawai dama wani ne na hanga kamar wanda na sani sai na zo biyo sa toh sai ya shige nan sannan na buga ƙofar wata ƴar gayu da ta min kama da wata da ma sani ta buɗe ƙofar,sannan yanzu ma na kuma jin muryar wanda na sani amma muryoyin ku ya sa na kasa tantancen muryar wannan da na sanin"..
Duk mamakin ta ya gama kama su sai kawai Berenice ta tambaye ta kai tsaye
"Halan wanene wannan ɗin"??ƙasa tayi da kan ta tana yunƙurin basu amsa sai ta kuma jiyo muryar na amo a kunnen ta dan haka tayi saurin maida dubar ta nan gefen.
Buɗe idanun ta tayi ganin shi ɗin be dai abin sa wato wanda ta biyo ɗin,kenan ba fah mafarkin rana take yi ba da gaske waɗanda ta sanin ne waɗannan..
Muryar Callee ne ya riga nasu fitowa inda take faɗin
"Wannan ai na san shi,shi ne fah wanda na ce maku ya taimaka min har na kwana wurin sa a washegari da zan wuce na tambayi sunan sa sai dai ban kai ga gama ji ba Fianna ta bige ni"!!gabaɗayan su sai abin ya basu mamaki musamman su huɗun wato Juda,Berenice,Balik da Agneta dan sun san shi gashi kuma yanzu Callee na faɗin itama ta san shi.

Shi da tun ɗazu yake tsaye yana ƙare masu kallo sai ya ƙarasa nufo su yana mai yi masu sallama dan gasgata ko waɗanda shima yake tunani da tsammani ne
"Assalamu alaikum"!!banbaraƙwai suka ji abin dan haka sai suka zuba mai idanu kawai dan su fah duk ɗaukar su wani gagarumin yare ya masu da basu san shi ba..
Dama yayi tunanin hakan sai kawai ya ɗan murmusa yana mai kiran sunayen waɗanda ya sani cikin su
"Juda,Balik,Berenice and Agneta ko ba haka bane"?suma tabbatarwa suka yi da eh wanda suka sanin ne dan haka suka gyaɗa mai kai sai ya murmusa yana mai nuna Callee ya ce
"Kema mun taɓa haɗuwa da ke a yankin marabar Ottoman"?gyaɗa mai kai tayi tana murmushi..
Yayi mamakin ganin su a nan dan bai san ya aka yi suka gano nan ɗin ba bare ma har su shigo ko wa ya nuna masu hanya dan kamar nasu labarin,sun ɗan wahala shi da matar sa kafin su taho nan ɗin..
But bai tsaya yi masu wannan tambayoyin ba sai kawai ya masu jagorjagora akan su zo su tafi gidan sa basu musanta mai ba suka biyo sa ya masu jagora har ciki yana mai kiran matar sa da ta kawo masu abin sha..
Ita dai tsoron su take ji dan bata manta rayuwar da tayi tare da mutani irin su a lokacin baya..
Lura da yanayin ta sai mijin nata ya ɗan riƙo hannun ta yana mai yin ƙasa da murya haɗe da furta
"Me ya faru halan duk kin rasa natsuwar ki ko baki gane su bane?sune fah suka taimake mu a lokacin bayan nan da na ce maki ki birkice ranar auren mu kin tuna su?tare muka tafi masarautar ku inda aka fiddo wannan"!!ya faɗa yana mai nuna Balik..
Sarai ta tuno su sai ta ɗan ɓata fuska tana faɗin
"Masoyi na na tuno su amma ni bana son su a nan gidan bana jin zan cigaba da samin kwanciyar hankali dan ina tsoron su"..yaren da tayi amfani da shi wurin yin maganar Berenice ta ji sarai dan haka cikin fushi ta ce
"Juda ku tashi mu tafi ku tashi mu koma inda muka fi wayo inda ake son mu dan bana jin nan ana maraba da mu"!!saurin tarar numfashin ta yayi yana faɗin
"No,ba haka bane,bani gane bane,tana da tsoro ne ba nufin ta ba kenan ku zauna mana"..ran ta a ɓace ta ce
"No Cahal,stay with your wife and please her mu kuma zamu wuce dama abu ya kawo mu kuma bamu yi nasara ba but ba komai zamu tafi"!!kalmar ta na ƙarshe ya janyo hankalin sa ya ce
"Kika ce abu ne ya fito da ku kuma baku yi nasara ba"?gyaɗa kai tayi tana kallon matar nasa sai ya ce
"In ba zaku damu ba,can i know what that mission is"?kallon kallo suka yi exchanging sai Berenice ta labarta mai komai tana mai jinjina irin cin mutuncin da suka fuskanta a nan ɗin..
Shi kan sa Cahal ɗin ya jinjina hakan a ran sa dan kusan similar issue suka samu a lokacin da suka tsinci kan su a nan garin suma,godiyar su ɗaya Gimbiya Ondrea matar sa na da wayewa ita ta tafiyar da abubuwan har aka gano cewa ba mugaye bane daga nan aka yarje masu da taimakon wani mutum suka sami matsuguni a nan ɗin tun lokacin har kawo yanzu..

Numfasawa yayi yana jaddada irin tarin gajiyar dake tattare da su
"Lallai abin ba mai sauƙi bane,kun ga ni,ko lokacin da na tsinci kai na anan ni da mata ta,rayuwa bata mana sauƙi ba,taimakon mu ɗaya ta iya tafiyar da al'adun su dan an koyar da ita,a nan ɗin ne dai muka kuma ba addinin da sarauniya Zinaida ta daƙushe a masarautar ta muhimmanci dan a nan aka nuna mana yawa yawan mutanin wannan ƙasa musulmai ne kuma addinin islam suke bi,bamu da zaɓin da ya wuce mu yarje ma addinin dama mata ta tana da ɗan sani a wannan fannin toh da taimakon ta da taimakon wannan mutumi muma muka zamo musulmai kamar dai irin mutanin ƙasar nan kun fahimce ni"?duk da ido suka bi sa wato dai basu yi tafiyar wofi ba kenan basu dai sami yadda suka so ba amma ga wata mafita ta iso su..
Babu wani nauyin baki Fianna ta ce da shi
"Akwai wani labari tafe da mu bayan wannan"nan fah ta zage ta labarta mai komai tana mai fatar samin yardar sa akan zai taimaka masu..
Matuƙa yayi mamaki dan shi a yanzu bai da wani burin da ya wuce ya zauna a nan ya faranta ran matar sa amma ba ya koma wannan dajij ba dan akwai wani labarin da ya gano bayan tafiyar sa nemo iyaten sa sai dai bai ce da su Juda ƙala ba ya ƙyale su yana faɗin
"Toh ba komai in dai wannan ne amma me zai hana ku zauma a nan ku huce gajiyar hanya in ya so sai gobe muyi maganar da zamu yi dan akwai abin da ya kamata ku sani kafin komai amma in kun yarda kenan"!!basu da wani zaɓin haka suka yi na'am da shawarar sa sai ya ma matar sa magana akan ta kai su ɗakin baƙi su kwana har washegari..
Ba dai a son ran ta ba ta tarbe su ta nuna masu hanya har ɗakin nasu sannan ta dawo tayi serving nasu abincin da zasu ci ta kai masu,daga baya ta sanar da su inda zasu yi wanka in suna buƙatar yin hakan, dama Balik a wani ɗaki yayi masauki nan kusa da na su Juda..
A fannin Cahal kuwa da ita matar nasa faɗa ce ta so kaurewa dan fah ita ta ce bata ga dalilin da zai sa yayi accommodating su Juda a gidan su ba da ƙyar dai ya rarrashe ta suka kwanta..


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:55&56*

  Cikin daren nan Juda da Callee basu runtsa ba duk da gajiyar dake tattare da su amma suka zauna hirar zumunci da hanyar cigaban su ko da sun yi accomplishing goal nasu,su dai sauran sun yi bacci dan bayan sun yi wankan sun sauya kayan da gimbiya Ondrea ta kawo masu duk sai suka hau baccin gajiya..
  A ƙarshe ma Callee ce ta kwanta tayi bacci amma banda Juda,dan ita dai ta san bata jin kan ta daidai kuma bata san me ya sa hakan ke faruwa da ita ba da tun da ta haɗa ido da Cahal haɗuwar farko ta ji kamar akwai wani abu da zai faru a tsakanin su ga halin da suke ciki yanzu na zaman inuwa ɗaya,duk ta ƙagu washegari yayi dan jin me zai sanar da su ko zata sami easiness a tare da ita..
  A ƙarshe dai zama tayi bakin gadon tana ƙare ma sauran kallo tana tunani kala kala a ran ta har dai ta ji ya kamata itama ta kwanta baccin dan haka ta kwanta..
 
★★★
  Wayewar gari ne da hasken da ya haskaka ko ina ya sa suka farka daga baccin dukkan su,as usual yadda host ke ma guest ɗin sa haka aka masu a gidan nan matuƙa gimbiya Ondrea ta lafa ta mutunta su sosai har abin ya fara basu mamaki ganin yadda a jiya ta  nuna masu halin ko in kula sannan yanzu tana nuna masu so..

  Haba haba aka yi breakfast ranar ana ta raha da tuno abubuwan da suka faru a kwanakin baya kafin zuwan su nan ɗin wani bin suyi dariya wani bin su ɗan yi jimami,har suka kammala breakfast ɗin Cahal bai ɗauko masu batun komai ba ya ƙyale su dan kae yayi interrupting masu moment ɗin su..
Sai da suka kammala cin abincin sannan suka dawo inda ake hutawa suka zazzauna inda a nan suke ƙare ma kan su kallo dan ganin yadda suka wani canza dan suturun jikin su ya bambanta da waɗanda suka saba gani suna sakawa sai abin ya masu wani iri kamar ba su ba..
  Bayan duk sun natsu ne Cahal ya daɗa gabatar masu da matar sa da kuma ɗan taƙaitaccen labarin su da yadda suka yi gwagwarmayar rayuwa har suka iso nan,kaf labarin rayuwar su a nan ɗin ya bayar sannan ya ɗora da cewa
  "Na san zaku yi mamaki amma ba abin mamaki bane in kuka yi duba da yadda rayuwa ta zo mana a lokacin baya da bamu san kowa ba sai kan mu mu kaɗai,toh bayana wannan na gano cewa mun daɗe muna rayuwar dabbobi da jakuna,rayuwar da babu alfanu a cikin ta,rayuwar da in ba wani ikon Allah ba,har ka mutu ba zaka taɓa samin sararin bautawa mahaliccin ka ba,a baya na ɗora yarda na da amincewa ta ne akan mutum,na yarda mutum shi ke bani abin da nake buƙata,na yarda in kashe kai na akan wannan mutumin dan na bashi yarda da aminci,na kashe rayuka ba adadi duk akan mutum ɗaya da nakewa kallon shine abin bautawa na,sai dai zuwa na nan ƙasar na gano ba haka bane,na gano cewa akwai wani daban da ake bautawa wanda muhimmanci da ƙimar sa sun ɗare na bil adama wanda shima halittar wannan ubangiji ne,da haka aka rinƙa karantar da ni da taimakon mata ta gimbiya ta wacce dama tun fari ta fara bin hanyar sai dai mahaifiyar ta ta hana ta saboda tsantsar tsaurin ta,but a yanzu ban da abin faɗi sai godiya dan rayuwa ta ta ingantu fiye da da ina jin daɗin mu'ammala ta da mutani dan yanzu bana marmarin komawa dajin nan dan duk wani abu dake gudana a dajin nan,tsantsar jahilci ne da duhun kai wanda nake fata in har komai ya min daidai zan koma wannan dajin sai dai ba ni kaɗai ba,zan tafi ne da masana da zasu iya ƙiyaste girman laifin wannan sarakai su hukunta su amma ba zan yarda in ɗau hukunci a hannu na ba dan a baya nayi ban sani ba yanzu kuma bana fatar sake maimaita wannan kuskuren dan har yanzu ina kan nemar yafiyar mahalicci na wanda zan so ku ma ku tuba ku koma gare sa dan yanzu kuke da dama"..
  Numfasawa yayi yana kallon su dan jin ra'ayin su yayin da su kuma suka zurfafa suna faman tunanin wannan labari da ya basu da ingancin sa dan ga ƙamshin gaskiya nan a labarin sai dai basu san ya zasu yi ba..
  Natsuwa Juda tayi ta basu labarin da Baccus ya bata game da addinai sannan ta ɗora da
  "Ban san ya addinin nan take ba amma ina ji a jiki na kamar zata zamo min garkuwa a rayuwa ta ban san ya sauran ƴan uwa na suka ɗauki addinin ba amma ni dai ina jin wani abu game da shi ban san menene ba"!gyaɗa kai Cahal yayi yana nazarin maganar ta sai ya ce
  "A nawa tunanin kamar dai ku aminta da wannan addini dan kun ga fah,dama can rashin sani ne ya sa kuke rayuwa haka nan amma tunda yanzu kun sani me zai hana ku biyo ni ni da mata ta mu koyar da ku irin addinin mu addinin gaskiya addinin da ya kamata da ko wani ɗan adam muddin yayi imani da shi"!!shiru suka yi su dukkan su suna tunanin yiwuwar abin sai daga ƙarshe Juda ta mai tambaya kamar haka
  "Toh ni dake da abin yi a can masarautar Ottoman fah?ya zan yi?ƙanwa ta na can garƙame a bursinar Sultan yana azabtar da ita,ya zan yi da ita?ga mahaifiya ta dake gida tana jiran komawa ta,ya zan yi da ita Cahal"??duk sai da suka ji tausayin ta amma basu yi ƙasa a gwiwa ba dan basu bari hawayen su ya zubo ba suka riƙe..
  Tasowa Berenice tayi ta nufo ta tana faɗin
  "Ki yi shiru duk zamu magance matsalar Juda,kar ki sakawa kan ki damuwa tunda dai kika ji Cahal da kan sa ya ce in komai ya daidaita mai,toh zai koma dajin nan,ni a nawa sai nake ganin kamar ki saki ran ki ba zamu rasa mafita ba tunda nan duniyar ta Bambanta da tamu duniyar akwai _Bambancin Ƙasar_ a tsakanin mu hala sakamakon wannan _Bambancin ƙasar_ sai ki ga komai ya zo mana da sauƙi har mu sami hanya mafi sauƙi wurin fiddo ƙanwar ki,beside kin ga yadda rayuwar mutanin nan yake ya sha bamban da irin rayuwar mu ta can toh tabbas ba za'a rasa hanyar da za a hukunta Sultan Baal-Hamon"!!..
  Kallon ta Juda tayi tana jinjina lamarin kafin ta maida duban ta ga Cahal tana mai tambayar sa
  "Wai haka ne"?da sauri ya gyaɗa mata kai yana amsa mata
"Tabbas haka ne,dan kin ga a nan akwai jirgi akwai mota,kin ga jirgi wani abu ne dake tashi sama ana tafiya a cikin sa ne ana kuma sauƙaƙa wahalar tafiya da shi sannan mota ma duk abin tafiya ne amma shi a kan hanya yake tafiya duk waɗannan abubuwa abu ne masu sauƙaƙa rayuwa,dan in har kika yarda toh wataran nan kusa zamu yi amfani da motar nan mu tafi masarautar Ottoman dan bai da nisa da nan kin ga in zamu koma sai mu koma tare da waɗanda suka san hukuma suka kuma iya hukunci dan su hukunta Sultan da hujja ko ya kika gani"?shiru tayi sai daga baya ta gyaɗa kai tana kallon sauran waɗanda suma ita suke kallo..
  "Toh su Fianna fah?ya zamu yi da su dan har yanzu akwai wani abu a jikin Agneta da sarki Malik yayi casting mata,bai bar ta ba har yanzu"! ɗan shiru ne ya ratsa wurin kafin daga bisani gimbiya Ondrea ta saka baki cikin maganar dan tun da suka fara bata ce komai ba.
  "In dai akan batun komawar ku masarautar nan ne kar ku damu,miji na zai taimaka maku dan shima nan ne asalin sa kuma ya fuskanci mummunar tarihi a wannan masarautar duk sakamakon wannan sarki wato Sultan dan haka shi kan sa yana da revenge da yake son ɗauka a can hakan na nufin zai koma masarautar sai dai ba shi kaɗai bane,tare da ƴan tsaro zamu koma dan duk masaratun nan da ake abubuwan nan da tauye haƙƙin ɗan adam a tono asirin su duniya ta san da su duniya ta san ha'incin su da suka daɗe suna yi,har yanzu yana kan tara bayanai da nemo masu taimako da zasu tunkari wannan masarautar dan haka ku kwantar da hankalin ku saboda a lokacin da za'a gano hakan,kaf mutanin da aka tsare za'a basu ƴancin su kana a hukunta Sultan da masu bin ra'ayin sa"..
  Ɗan shiru tayi dan tuno da rayuwar mahaifiyar ta a masarautar ta,mahaifiyar ta tayi nisa ba lallai bane ta jiyo kiran su,dan duk wani saɓo da Allah ya hana ya haramta shi take yi toh ta yaya zasu fahimtar da ita..
  Ɗan janyo ta jiki mijin ta yayi yana rarrashin ta dan ya san tunowa tayi da mahaifiyar ta..
  "Is okey mun aminta zamu bi yadda kuka ce dan samin abin da zai amfanar da mu"!abin da Juda ta ce kenan wanda ya ɗan kwantar masu da hankali dan ko a halin da suke basu buƙatar wani ɗayan biyu in dai mafita zata zo masu toh fah basu da damuwa...
 
  Tun daga wannan rana aka natsu ana koyar da su Juda addini da halacci da haramcin abubuwa wanda sai yanzu suke ƙara bambance illolin rashin ilimi da addini da suka tafka a baya sakamakon rashin sanin addinin..
  Aƙalla sun share watanni shida suna kan koyarwar addinin islama ƙarƙashin jagoranci Cahal da matar sa gimbiya Ondrea kuma ba laifi abubuwa da dama sun sauya a rayuwar su kamar dai yadda Cahal kan fita ya tafi wun aiki haka Balik ke bin sa su tafi tare dan ya taimaka masa da rage nauyin wanda in da ta Cahal ne,toh baya buƙatar hakan..
  A nan gida kuma suma matan kan taimakawa gimbiya Ondrea da aikace aikace a gida kuma suna jin daɗin zaman su tare duk da sai a hankali ta saki jiki da su gabaɗaya suna abubuwa tare.
  Ga cikin ta da ya girma dan ta kai watanni kusan takwas tana gab da shiga watar haihuwar ta kuma a wannan lokacin ne aka tara enough facts da za'a yi amfani da shi against Sultan Baal-Hamon da sauran sarakan masarautar dan an binciko an gano manya manyan biranai ma basu da masaniya akan wannan badaƙalar dake faruwa a waɗannan masarautu sai da aka nemi wasu suka tafi suka yi spying masarautun sannan aka gano gaskiyar lamarin har aka yarda aka ɗau case ɗin a matsayin babbar issue da za'a yi exploring very soon..
  Ƙungiyoyi da dama sun nuna interest ɗin su akan wannan case dan tun da aka shigo wannan century a wannan global world ɗin basu taɓa witnessing gagarumin abu kamar wannan ba sai dai su ji a tarihi da kuma movies da ake yi..
★★★★
  An ajiye ajiyayyun rana da watar da za'a ziyarci masarautun nan dan so ake a fara da masarautar Ottoman ta Sultan Baal-Hamon dan shine babba mai laifi kafin a juya zuwa ga sauran masarautun dan dole a yi demolishing irin wannan cultural acts ɗin dan su sun yi considering wannan abun a matsayin wani mummunar ɗabi'a ta gargajiya mai cutar da rayuwar ɗan adam dan haka ana so ayi vanishing wannan act ɗin a waɗannan yankunan dan a sami ingantaccen ƙasa da rayuwa mai kyau da tsafta..

★★★
_THE MUGHAL EMPIRE_

  Tun bayan barin sarauniya Zinaida masarautar Ottoman bata yarda wani abu ya kuma giftawa tsakanin ta da masarautar ba dan bata fata kuma bata muradi..
  Abu ɗaya ta sani,shine ita dai nan ba da jimawa ba zata mulki duniyar nan gabaɗayan ta kuma sai ta ga bayan Sultan dan ya kawo ta har maƙura..
  Akwai wani ziyara da sarkin Oman ya kawowa sarauniya Zinaida dan sanyaya mata rai a bisa ga abubuwan da ya faru tsakanin su da Sultan..
  A ziyarar tasa ne yake nuna mata ai shima ra'ayin su ɗaya sai dai bai fito ya nuna ba saboda kar a yi saurin gano sa dan haka itama ta sakawa ranta ruwan sanyi har dai ya kammala shirin sa ta yadda zasu haɗu su kada Sultan akan mulkin nasa in ya so sai su su mulki duniyar su biyun su..
  Wannan shawarar ta ma sarauniya Zinaida daidai dan har wani irin shagali aka yi a masarautar nata..
  Shawara ɗaya suka ajiye wato na su haɗa kai su yaƙi Sultan su su mulki duniyar,yayin da sauran sarakan kamar sarakan Jordan da Cyprus aka bar su a duhu basu cikin waɗanda aka yi shawarar tare da..
  Lokuta da dama,sarauniya Zinaida kan zauna tayi tunani tayi kewar ɗiyar ta tana mai fatar ganin ta nan ba da jimawa sai dai ganin kusan shekara guda babu ita babu labarin ta sai jikin ta yayi sanyi,tabbas tana son duniya amma tana buƙatar ɗiyar ta,ita da zata dawo ma toh ba zata hana ta auren muradin nata ba ko da hakan na nufin ƙasƙanci ne a gare ta a matsayin ta na sarauniya..
  Ta san abu ne mai wuya ta tsinci labarin gimbiya Ondrea dan ko ta ko ina ta baza tsaro akan a nemo mata su amma amsar ɗaya ce dai wato babu su babu takun su..
  Ta yarda da abin da ake kira da _Komai Lokaci ne_,dan gashi ta gani gar da gar,a baya tana lura da ɗiyar ta tana saka mata tsaro tana ganin ta a kullum but bata taɓa appreciating nata da presence ɗin ta ba a kullum takan hana ta kusantar ta dan ta san suna

Please Login or Register in order to submit comment