Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san sarki ne surukin Artemas dan sam jahar da suke ma babu wanda ya san ya kamannin sarkin yake sun dai san ana zana sa a hoto amma hoton ma ba mai tarr bane dan haka ba wani cika shaida sa ake yi ba..._
  _Buɗi sosai Artemas ya samu da ɗaukaka wanda a nan ma an so a maimaita baya kamar yadda aka ma mahaifin sa,shi kuma sanin haka ya sa ya dage yana koyar da ɗiyar sa yadda zata yaƙi mahassada da maƙiyan ta na ɓoye da na sarari dan ya san a ko wani lokaci suna iya kawo masu farmaƙi kuma dan su yi awon gaba da ita kan ta Judar ba wani abin damuwa bane a gare su amma in har suka zo kuma suka ga mu'ujuzan ta na yaƙi suna iya rangwama mata su fafata da ita amma baya da haka sam suna iya cutar da ita asarar ta masu yawa a fi ƙarfin su sannan a fi ƙarfin ɗiyar sa wacce yake fata da burin ta maye gurbin sa in baya nan..._

_A ranar da Hadara zata haihu abin bai zo masu da sauƙi ba dan har sun gama yarda wannan cikin na ɗa namiji ne dan alamu duk sun nuna dan kuwa hatta da shi sarkin ottoman da ya taso su gaba,tunanin sa namiji ne a jikin Hadara sai dai ranar haihuwa bayan doguwar naƙuda Hadara ta haifo ƙatuwar ɗiya mace wacce ta ninka Juda a jiki ko lokacin da aka haife ta haka ta fi ta haske da saurin shiga rai dan kakan ta sarki har kasa ɓoye abin yayi a gaban kowa nuna mata so yake sai dai yana iya ƙoƙarin sa na ganin yana saka Juda jin itama har lokacin yana son ta in ma ta ɓata fuska akan an fi son sabuwar yarinyar maman ta sai kakan ta ya nuna mata kawai ɗoki ne ba wani abin ba watarana abim zai daina in aka kuma haifo wata sabuwar ɗiyar,da haka aka kashe wutar ƙiyayyar da ya so ginuwa a zuciyar Juda dangane da ƙanwar ta sai ta dawo tana son yarinyar.._
  _Ba'a rigada an ba yarinyar suna ba sojojin masarautar Ottoman suka far masu aka rinƙa fitina Artemas ne yayi ƙarfin halin ɗauke jaririyar ya gudu da ita zuwa wani daji wanda ake ma laƙabi da dajin "al'ajabi"dan in har mitum ya shiga dajin nan toh ba fah dole ne ya fito da lafiyar sa ƙalau ba kasancewar ɗumbin sihirin dake tattare a wannan dajin..._
  _Ko da Artemas ya bar gidan Hadara kuka ta saka dan ta san nata ya ƙare an gama da ita ko ba'a hallaka ta ba an gama da mutani biyu mafi soyuwa a rayuwar ta ɗiyar ta da mijin ta,mahaifin ta ya dage ya kare ta ya yaƙi maƙiyan dan sun gane cewa Artemas wayo ya masu ya gudu da abin da suka zo ɗauka,sosai aka tada ƙura kafin sojojin(Assassins) ɗin su bar gidan Artemas su nufi dajin wanda a nan ma basu sha da kyau ba a ƙalla sun kai ɗari da arba'in da takwas amma sojoji talatin suka tsira da rayukan sau bayan sun goga sun karta artabu da Artemas sun ƙwace ɗiyar da ke saɓe a kafaɗar sa,kamar zasu wuce sai suka fasa suka juyo suka mai wulaƙantacce kisa dan ya daɗe yana tare masu hanya tun ranar da aka haifi ƙanwar Juda suka so zuwa ɗauke ta sai dai ya hana ya yi bake bake a yanzu da suka sami abin da suke nema kuwa sai suka kar shi dan kar ma yayi mafarkin kuma nemo su kamar yadda yayi a watannin baya da Hadara ke ɗauke da jinjirin cikin ƙanwar Juda dan kuwa basu sha da sauki ba kasancewar ya shimfiɗa masu sharuɗɗa masu tsauri da ya saka su yin ƙasa da kawunan su akan wataran zasu rama abin da ya masu dan kam shugaban su ya fi ƙarfin musayar yawu da Artemas sai dai yayi da su..._

  _Washegarin ranar da aka yi harin ne sarki ya tafi wun matsafin sa da yake duba masa lamuran sa kafin ya aiwatar da su,.nan ya tafi aka bashi sihirin kariya daga sharri da kaidin wannan dajin dan suna son shiga dan sanin halin da Artemas ke ciki.._
  _Miƙo ma Hadara ruwan sihirin yayi ta shafe jikin ta sannan ta shafe ma Juda a jikin ta sannan suka ranƙaya zuwa dajin wanda shigar su ta fari Juda ta tsinci wasu fure biyu a suman kan ta ko da kakan ta ya kai hannu da nufin cire mata shi sai ya ji wani irin nannauyar abu kamar dutse a hannun sa da ya hana sa ƙarasa kai hannun sa zuwa ga kan Judar haka mahaifiyar ta ma amma duk irin nare dan haka sai suka gane lallai dajin yana mai maraba da Juda saɓanin su da ƙarfin sihiri ne ya saka dajin amincewa da su ba dan dajin ya so haka ba sai dan an fi ƙarfin sa.._
   _A taƙaice dai haka su Hadara suka dawo gida da gawar Artemas ranar kuka ta rinƙa yi kamar zata mutu har take roƙon mutuwar ta ta matso kusa in tana jin ta ta zo ta ɗauke ta dan ta tafi ta haɗe da mijin ta,abin gwanin tausayi a haka aka masa abim da ya dace,kusan wata ɗaya Hadara bata dawo daidai ba sai da ɗiyar ta ta sarƙafi hanyar dajin nan wato dajin ak'ajabi sannan ta dawo hayyacin ta tana ƙoƙarin yi mata ƙulle a gida har ma dai aka samo masu kula da ita yayin da ita Hadara ke tafiya kasuwa tana mai cigaba da yin sana'ar mijin ta tana nema masu abin rufin asirin su a lokaci ɗaya kuma kakan Juda na cigaba da gina ginin da Artemas amintaccen mai tsaron sa sirikin sa bai ƙarasa ginawa ba wato cigaba da koyar da Juda yadda zata riƙe takobi tana sarrafa shi..a da Hadara ta ji tsoron kar Juda ta taso kamar namiji bata iya komai na mata ba sai na maza ta zo ta rasa mijin aure amma sai mahaifin ta ya nuna mata babu abin da zai hana ta samin miji amma koyar yaƙi kam yanzu ta fara har sai ta ji ta ƙoshi ta gundira da yaƙin dan kan ta ta bar sa saboda wannan ɗin burin mahaifin ta ne haka dai Hadara ta zuba ma Juda da mahaifin ta sarki ido a kullum sukan yi gwaji sau goma a rana wasu ranakun ma har fiye da goma..._
  _Suna a haka rayuwa na tafiyar masu da daɗi babu daɗi har dai Juda ta kai shekara goma sha biyar ta ginu akan yaƙi da sarrafa takobi ta ko wani siga,a wannan shekaru da tayi kuwa basu taɓa samin wata hayagaga daga ko ina ba amma hakan bai saka sarki daina koyar da ita yaƙin ba dan ya san tilas akwai ranar da tarihi zai maimaita kan sa akan ahalin sa dan wasu lokutan har tausaya ma Juda yake yi dan yaƙin da ke gaban ta ba abin tsayawa fallasa mata bane amma yayi ƙoƙarin dasa mata sam duniyar bata da ragowar yarda kowa maƙiyin ta ne kuma ta ɗau fansa akan koma waye sannan kar ta kuskura ta yarda da kowa rayuwar duniyar tata ce ita kaɗai duk yadda zata kare kan ta cikin wannan faffaɗar duniyar ta tabbatar ta yi ta kare kan ta dan duniyar muguwar wuri ce tunda har ta ɗauke mata kakannin ta da suka haifi mahaifin ta sannan ta ɗauke mata kakar ta mahaifiyar maman ta ta kuma ɗauke mata mahaifin ta da ƙanwar ta da ke jinjira bata ma san su ba.._
_Sosai waɗannan abubuwa suka shigi Juda ta hau ta zauna har ya kai in har ta saci jiki ta tafi dajin al'ajabin nan takan dage tayi gwajin yaƙi(practice/training)ita kaɗai har ta fara haɗuwa da maƙiya dake zuwa wurin ta fara yaƙar su tana tsiratar da mutani wanda hakan ya janyo mata ɗaukaka sai dai mahaifiyar ta sam bata so hakan ba dan wannan daji ya bar mata mummunar tambari cikin shafukan rayuwar birnin zuciyar ta tsyi tayi ta ma Juda ƙulle a gida amma kakan ta ya hana ya ce ai mu'ujizar ta ne ke bayyana dan haka ta haƙura ta bar ta tana zuwa amna ba wai dan zuciyar ta yayi na'am da wannan zancen ba.._
  _Sosai fah Juda ta zama tauraruwa a ƙauyen nan dan ita dainin shiga dajin nan ne toh bata da damu kai tsaye take shiga wanda a tarihi kuwa ba haka bane an san duk wanda ya shiga bai fitowa da rai sai dai labari ya sha bamban dan ita Juda takan shiga tayi sha'anin ta ta fito in ya kama tayi taimako ne sai tayi babu abin da zai sami waɗanda ta taimakan wannan jarumta nata ya sa aka saka marmta sunar *"Sarauniya"*dan da shi ta fi cancanta a wun jama'ar ƙauyen..._

  _Sau babu adadi aka fara kawo masu hari daga dai wannan masarautar ta ottoman duk dan akwai sauran mahaɗin sihirin da sarkin ƙasar ke nema kuma a nan gidan mahaɗin yake,wannan abin ya fara harzuƙa Juda da ta zamo ƴar budurwa dan ta kai shekaru ashirin har da ɗaya a wannan harin ne aka hallaka mata kakan ta mafi kusanci da ita wanda ya saka ta ɗaukar ƙudirin ko ma waye wannan sarkin sai ta ga bayan sa dan shi ya watsar mata da ahalin ta kaf..._
  _Yaƙi sosai tayi da su ta halaka sojojin(Assassins) kusan ɗari uku duk cikin dajin nan haka kamar ƙara mata ƙaimi ake yi ta rinƙa yaƙar su har sai da wasu suka gudu sannan ta dawo gida ta tarar da masu kula da ita duk suna zazzaune suna rarrashin mahaifiyar ta da ke nan kamar matacciya dan ta ga duniya kuma duniyar ta fara bata tsoro..._
_Wannan danuwar da mahaifiyar ta ta shiga ya saka ta jin tana son tafiya wannan ƙasar basaraken wato ƙasar ottoman ita burin ta kawai ta ga bayan sa ko zata huta sai dai dole kamar yadda marigayin kakan ta ke sanar da ita akan babu yadda zata iya tafiya ƙasar ottoman sai da mabuɗin hanya mabuɗin tafiya da zai kare ta ya kuma nuna mata hanya kuma sai ta kai shekarun riƙe wannan mabuɗin wato shekaru ashirin da uku wanda a nashi ƙiyastin so yayi tana cika ashirin da uku ya bata komai da kan sa sannan ya raka ta zuwa rabin gari ya asirce ta ta yadda babu wanda zai mata komai har ta tafi ƙasar sai dai kafin burin sa ya cika an ɗauke sa daga duniyar..._
  _A haka Hadara ta rinƙa tafiya yankin boda tana karɓo siddabaru iri kala daban daban ta rinƙa luuɓe gidan ta da ƴar ta ta yadda duk ƙwaƙwar mutum in har mugu ne ba dole bane ya gane akwai mutani da ke rayuwa a cikin gidan ba hasalima ba lallai bane a san akwai gida a wurin ba dan ta mai ne yadda da an zo sai dai a wuce ba za'a ga gida ba sai dai fili..._
  _A wata fitar satar ƙafar da Juda tayi ne mai kula da ita ta tafi nemar ta a dajin da ta mayar gidan ta masarautar ta matar ta faɗi ta mutu sakamakon harbin ta da aka yi da kwari da baka da aka yi(bow&arrow)duk dan ana son kama Juda,ai kuwa tana ganin haka ta ƙarar da mutanin nan tas sannan ta dawo gida ta sanar da mahaifiyar ta abin da ya faru ita kuwa ta fara yiwa Juda ƙulle sannan ta ƙwace takobin da ke hannun ta ta hana ta fita sai dai kamar abin gwaninta tana ganin mahaifiyar nata bata kusa sai ta saci hanya ta nufi dajin nan dan ita ji take kawai ta tsinci kan ta gaban sarkin ottoman dan kawai ta kai shi inda ba'a dawowa kamar yadda ya kai mata ahalin ta..._
  _Tun Hadara bata ganewa har ta fara gane cewa Juda na satar fita kuma takobin ta da take ƙwacewa ba da shi take fita ba da sabbi take fita abin na ɗaure mata kai a ina Juda ke samo takuba dan in ta ƙwace mata su zata gan ta da wasu daban ba irin waɗanda ta ƙwace ba sai daga baya ta gane mutanin garin ne ke ƙera mata shi dan ta zame masu kamar mai gadin ƙauyen,wani irin ƙima da ƙwarjini ne da ita muddin ta haɗa ido da maƙiyin ta toh duk bakin sa na sai ya ga bayan ta sai ya tsinci kan sa da jin nauyin ta da fargabar ta ita kuma da haka ta ke yaƙar su son ranta har dai ta kai shekaru ashirin da uku a inda ta addabi mahaifiyar ta da ta ba ta damar tafiya amma ita kuma tsoro take ji gashi Judan ba zata iya tafiya gaba gaɗi ba sai da wannan mabuɗin wato wannan kundin da kakan ta ya tsaface sa ta ko ina..._
  _Tun Hadara na fargaba har abin ya ishe ta ta sadaƙar komai ta fanjama fanjam ƙwara ta sadauƙar da Juda ko zata sami sauƙi da sukuni dan akwai tabbacin ɗiyar ta da aka sace tun tana jaririya da ita kan ta Judar da zata tafi nemo ta zasu dawo cikin ƙoshin lafiya da haka ta ba Juda wannan littafin da mahaifin ta ya daɗe yana killacewa kaf tarihi da abubuwan al'ajabi sun ƙunsu cikin wannan kundin dan ranar da Juda ta mata wata tambaya sai da ta ji ina ma zata iya fallasawa Juda zuciyar ta da sam bata mata wannan tambayar ba dan ta fi Judar zaƙuwar a kawo ƙarshen wannan abin dan akwai babannin ta ƙannen mahaifin ta Yahaira da Daliyah da har yanzu ba'a san ta ina za'a fara nemar su ba kuma an ce wanda ya riƙe wannan kundin a ƙarshe shi zai samo mafitar duk rigingimun da ya daɗe yana tashi yana lafawa har kawo ƙarshen sa..._
  _Sosai ta tsaface ɗiyar ta kafin ta damƙa mata wannan kundin dan daga ita sai Juda sai wannan kundin da aka saka ma ido daga wurare daban daban wanda sanadiyar sa kakan Juda ya mutu dan sarkin ottoman ne ya aiko a ɗau kundin sannan a kashe Juda sai dai kashh,,,har ranar da Juda ta bar gidan su da nufin shiga duniya mai faɗin da ta fi nasu dan nemo ƙanwar ta jinin ta sannan ta magance matsalolin da suka daɗe suna yawo,babu mutum guda da ya taɓa iya tsayawa ya daki ƙirji ya yaƙe ta dan tayi ƙaurin sunan da jin ta ya fi ganin ta saboda a jiki kam ba wata babba bace haka a shekaru,kwata kwata ita ɗin kenan ashirin da uku bata fi haka ba amma kowani azzalumi in ya ji sunan ta sai ya girgiza bare ya gan ta,toh mai ƙwatar sa wani iko ne mai girma amma kam sai ta tabbatar ta shafe tarihin mutum dan kakan ta ya nuna mata kowa maƙiyi ne kar ta rangwama mai bare ya dawo ya mata yankar baya.._

*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:37] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:9&10*

  *PRESENT CONTINUOUS*

 
A tsanake take tafiyar ta tana yi tana waiwayen baya saboda tsaro dan komai na iya faruwa sakamakon maƙiya da ta tara a ko ina musamman masarautar ottoman,.
  Tafiya take babu tsayawa har sai da ta ga duhu ya fara mamaye ta ta ga ta daina gani sosai sai ta ja layi ta tsaya a madakata ta kafa tantin ta dake naɗe cikin jakar fatar ta da mahaifiyar ta ta saka mata saboda dalili irin haka..
  Bayan ta gama kafa tantin nata ne ta shige ciki ta buɗe jakar ta ta ɗauko guzirin ta da mahaifiyar ta ta mata,buɗe nannaɗaɗɗen ganyen ta yi ta buɗe shi gaba ɗaya ta kai hannun ta ta fara ɗebar ganyayyakin da ke tsume cikin babbar ganye ta fara kaiwa bakin ta tana taunawa,sai lumshe idanun ta take yi tana cigaba da cin ganyayyakin har ta ji ta ƙoshi ta naɗe sauran ta mayar cikin jakar ta..
  Fitowa wajen tantin tayi ta kalli gabas,kudu,yamma da arewa ta ga daga ita sai ita cikin dajin babu kowa babu komai har haske bata ganin ƙurƙushin sa illah hasken aci balbal da ta ƙunna da audigar dake cikin wani kwalba dake nan cikin tantin nata...
  Takawa ta fara yi tana son samin mazubin ruwa dan ta manto ta yo guzirin sa sai da ta yi nisa a tafiyar tata sannan ta tuno kuma babu halin komawa gida,..
  A ƙalla tayi tafiyar kwatar awa mintuna goma sha biyar kenan sannan ta yi katari da wata kwararrafar da ke fidda ruwa kuma kamar daga kogo(cafe)ruwar ke fitowa,da saurin ta ta ƙarasa ta kafa baki ta sha ta ƙoshi har ta tashi zata juya sai ta fasa ta juyo ta hau cire suturar jikin ta,sai da tayi zir sannan ta tsunduma cikin ruwan ta fara wanka babu sabulu babu soda haka ta gama facalcala ruwar nan sannan ta fito ta ɗau kayan ta rigar ma a hanya ta ida saka shi sauran kayayyakin kuma ta riƙo su a hannu ta cigaba da tafiyar ta har ta dawo tantin ta..
  Shigewa tayi ta ajiye sauran kayan a gefe ta janyo jakar ta ta buɗe ta ɗauko kumdin da mahaifiyar ta ta bata ta tasa a gaban ta,tunani take yi ta buɗe shi ne ko kar ta buɗe,lokaci ta ɗauka tana wannan tunanin kafin daga bisani ta yanke hukuncin buɗewa ta duba ko da kallon sa zata yi ba tare da ta fahimci abin dake ciki ba dan ta daɗe tana marara sauke idanun ta cikin wannan littafi...

  Buɗe littafin tayi wanda ke nan rufe da mahaɗar sa kamar botirin riga mai maƙalewa in an haɗa,tana buɗe sa hankalin ta na hanyar waje tana duba ƙofar tantin dan kar wani ya ga sirrin nasu,daga bisani ta buɗe littafin gabaɗaya haɗe da mayar da idanun ta kan shafin farkon da ta fara buɗewa..
  *_"HISTORIES OF OUR LEGENDS"_*..
  Dariya ne ya ƙwace mata kafin ta tambayi kan ta
"Me kuma ruwa na da wannan tarihin?uhum grandpa kenan wato wannan shine dalilin sa na hana a bani littafin nan tuntuni kenan?lallai mutanin da ba'a gane al'amarin su"..ta tambayi kan ta tana mai cigaba da darawa..
  Iya inda ta iya sauke idanun ta kenan sai ta rufe littafin ta mayar cikin jakar ta janyo jakar ta ajiye daidai inda kan ta zai isa in ta kwanta,kwanciya tayi haɗe da ɗora kan ta bisa jakar nata sannan ta rufe idanun ta sai bacci ya kawo mata ziyara ta ko amsa ta fara bacci dan gajiyar da ta kwaso daga ƙauyen su zuwa nan ɗin ba kaɗan bane..

  ••••••••••••••••••••
Misalin awowi goma da fara baccin ta sai ta ji kamar hayaniya ana ta sakin hayaƙi haɗe da sakin kwari da baka(bow&arrow),firgigit ta tashi dan abin ya girme ma tunanin ta tana tashi ta ɗau takobin ta ta janyo jakar ta ta rataya a bayan ta ta fito riƙe da aci balbal ɗin nata a hannu tayi saurin kashewa ta fara naɗe tantin nata ta tana yi tana kallon hanya har ta gama ta saka cikin jakar ta ta ɗau aci balbal ɗin ta saka cikin jakar ta ta mayar ta rufe ta fara yankar daji tana bi ta baya baya..
  A zahiri so take ta kare kan ta daga shiga ko faɗawa cikin yaƙin da ake yi dan mahaifiyar ta ta gargaɗe ta sai dai can ciki cikin zuciyar ta ba haka bane,abin da ta saba ne dan haka a yanzu ɗin ma mararin faɗawa tsakiyar mayaƙan take dan kawai ta ba takobin ta abinci amma da ta tuno da maganar mahaifiyar ta akan gargaɗin ta da ta rinƙa yi akan in har ba dake ake hayaniya ba kar ki kuskura ki kutsa kan ki...

A haka ta rinƙa bi ta baya tana kallon yadda suke zabga yaƙi ana ta barazana da takobi a tsakiyar dajin sai dai bata yi gigin shiga ba ta zaga ta bar wurin ba tare da an lura da ita ba..
  Tana tafe ne kamar wacce ake ingizawa dan matuƙa ran ta ya soso ta so ta taya waɗanda ake kaiwa wuƙaƙen nan jiki sai dai hakan bai faru ba..
Tana tafen nan ta nemi madakata ta laɓe a bayan wata bishiya tana jiran waɗannan mutanin dan tana jin ran ta na daɗa ɓaci sakamakon rashin amfani da takobin da bata yi ba akan waɗannan mutanin.
Ai ko kamar ta saita lokacin dawowar su bata daɗe da laɓewar ba ta fara jiyo hayaniyar su suna tafe suna dariyar nasara suna kalaman da bai kamata ta akan yau kam su da mata ko uban gidan su ba zai nuna masu yadda ake holewa da matan ba..
  Basu ankara ba ta faɗo gaban su ta tsaye kane kane tana masu kallon uku saura sai suka natsu suna bin ta da ido kamar sun ga wani abin mamaki ita kuma sai da ta ƙare masu kallo kaf daga sama zuwa ƙasa ta tabbatar lallai fin ƙarfin waɗanda suka yaƙa suka yi if not babu yadda za'a yi su yaƙe su su wuce haka nan..
  Muryar ta a harzuƙe ta fara masu magana rai a ɓace
  "Wato ku har kun kai matsayin zuwa ku yaƙi waɗanda kuka san kun fi ƙarfin su ku cutar da su sannan ku yi wucewar ku dan kun ga basu da waɗanda zasu tsaya masu ko"?wani irin kallon wofi suka mata sannan suka fashe da wata muguwar dariya da sai da dajin ta amsa..
  Mayar da duba babban cikin su yayi zuwa ga Juda dake tsaye riƙe da takobin tana jiram jin ta in zai ɓullo dan yunwa takobin hannun ta take ji..
  "Ke,,ke kuma daga ina aka wurgo ki da har zaki zo nan dajin dake mallakin mu ki tsaya kina tsageranci kina mace ba namiji ba,,iyee"?girgiza kai ta shiga yi tana murmushi kafim ta ɗago ta sauke idanun ta kan wanda ya mata tambayar ta ce da shi
  "Ni sunana Juda sarauniya ɗiya ga gimbiyar masarautar Babylon jika ga sarkin ƙasar Babylon gabaɗaya kuma ɗiya ga babban ɗan kasuwa mai tsaron lafiyar sarkin masarautar Babylon kafin a taso su gaba,ai na san ka gane ko ba haka ba"??zubo mata idanu suka yi daga shi babban nasu har zuwa sauran da basu kai sa matsayi ba,kallon tsoro suke mata dan suna da labarin cewa wannan yarinyar aljana ce duba da yadda mayaƙa ke tunkaro ta kuma take tsayawa ta jajirce ta yaƙe su ita ita ɗaya ba tare da taimakon kowa ba..
  Kallon junan su suka yi basu buƙatar hukuncin da take zartarwa akan sauran mayaƙa suma ya zo kan su wato hukuncin kisar da take yi ma mutani in tayi gamdakatar da su,..
  Kamar ƙiftawar ido ta neme su ta rasa wani irin haushi da takaici ne ya taso mata ta rinƙa jin kamar ta tsinci kan ta a inda suka ɓace suka tafi..
  Wurgi tayi da takobin tana haki haɗe da buga ƙafar ta da bishiyar dake gaban ta,ba ƙaramin haushi ta ji ba..
  Tsugunnawa tayi a wurin tana jin kamar ta fashe da kuka abin da bata taɓa yi ba kenan a rayuwar ta duk inda ran ta ya kai da ɓaci bata kuka sai dai ta tafi dajin al'ajabi tana shiga kuwa hawayen ta zai ɗauke daga niyar tsiyayowar da yayi niyar yi..

  Ta daɗe a haka kafin ta miƙe ta ɗau takobin ta ta fara takawa tana tafiya tana tunanin abubuwan da ta rinƙa cin karo da su a hanyar ta tun daga barin ta gidan su har zuwa yanzu wasu abubuwan ita kan ta ta san ƙarfin tsaface ta da mahaifiyar ta tayi ne ya sa basu tasiri akan ta in ba haka ba ta san da yau ta dakata da wannan tafiyar biɗar da ta fito yi wato*_{Battle to reach}_*...

  A tafe ta ƙarasa daren ranar tana tafe

Please Login or Register in order to submit comment