Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fingers d’in ta, ba ta lura da shigowar shi ba sai takun tafiyar shi da taji a kusa da ita.

D’agowa tayi ta kalle shi tare da lura da yanayin da yake ciki kamar yana cikin damuwa amma ba halin tambaya dan yanzu sai ya hau ta da fad’a.

"Yaya sannu da zuwa" Anisa ta fad’a.

Wani kallo da ya ma ta sai da gaban ta ya fad’i saboda tasan ruwa ba ya tsami banza.


D’akin ya d’au shiru na ‘yan mintina kana yaya Faruk ya fara magana cikin fushi tare da cewa "Anisa bi ki ji san da nayi sallama ba ne ko ke ma za ki nuna min kin kawo k’arfin kan ki ne?

Cikin sanyi murya tace ‘sorry yaya Faruk ban ji bane".

D’akko min copies d’in hotunan da kuka yi ranar graduation d’in ku!

Cikin mamaki tace "yana gurin Fatimah saboda d’azun ta kira ni tace friend d’in mu ta kawo mana".

Ci gaba yayi da cewa "kuna ganin ku kun girma ko da har zaku d’auki hotuna da maza ko? har wani dancing step kuka yi saboda kuna tashen girma, bari in fad’a miki kiji, duk san da na gan ku da saurayi ko kuna zance, hmmm a ranar sunan ku sorry dan sai na kai ku kwata kun kamo kifin oga, ban da sauran purnishment da zan baku iri iri saboda kun ga ina k’yale ku shine kuke yin abin da kuke so".

Ya ci gaba da cewa "yanzu ma saboda tsabar iskanci kina ji nayi sallama amma bi ki amsa min ba, wato ga d’an isa ko? ya kalle ta yana jiran amsa.
Anisa ko da ta fad’a cikin tunani sabida a tunanin ta ba ta san me ya ‘bata mai rai da zai zo ya huce a kan ta kuma ya aka yi yasan sunyi hoto da ‘yan class d’in su? Ko dai ya je gidan su Fatimah ne!

To in ban da abin yaya Faruq menene laifi dan sun d’au hoto da ‘yan class d’in su? Abin da ake yin shi na rana d’aya saboda tarihi.

Tsawar da ya daka mata ita tasa ta yanke tunanin da take yi.

"Kayi hak’uri yaya Faruk ban ji sallamar ka bane shi yasa" Anisa ta fad'a.

Wani gajeran tsaki ya ja ba tare da yayi Magana ba, ya nufi side d’in shi.

Tun tafiyar yaya Faruk d’aki, Anisa ke mamakin shi saboda ita dai a iya sanin ta ba ya shaye-shaye bare tace ko a buge yake, ita ko taba bata ga yana sha ba.
To ko dai allurar sojan ce ta motsa? Wannan ne ba ta da amsar shi.

Wani sa’in in ya zauna yana d’an jan ta da hira ba k’aramin dad’i take ji ba, saboda d’an uwa rabin jiki ne, hasali ma shi kad’ai ne wanda iyayen su suka haifa.

Addu’ar ta shine Allah yasa yayi aure ko ya rage fad’an da yake yi.


Yaya Faruk kuwa yana shiga d’aki ya fara kaiwa da komowa kamar wanda yake training.

Sak’a da warwara yake yi duk akan mafita da yake nemar wa kan sa don in har bai d’au mataki ba yana ganin zai iya fad’a wa a cikin rami..

Marin da ya min ne yake mishi gizo a idanun shi kamar a time d’in ne ya mare ta.
Hannun shi yakai ma naushi kamar shine ya mishi laifi.

Zuciyar shi ce ta fara raya mishi akan cewa me yasa ya mare ta? hakan ba zai jawo ta k’ara jin haushin shi ba, tun da ita a tunanin ta yana matsa mata ne?.

A fili yake fad’in "why? me yasa na mare ta? me yasa ban yi controlling d’in temper d’ina ba? duk wannan tambayoyi ne yake yi wa kanshi wanda ba su da amsa.

Hannun shi ya d’aura a kanshi wanda yake faman yi mishi ciwo.

Zuciyar shi ce yaji tana bashi command akan cewa yaje ya ba ta hak’uri ko ya samu sauk’in rad’ad’in da take mishi.

Wata kuma zuciyar na ingiza shi akan cewa kar yaje, saboda hakan zai iya jawo wa ta raina shi wanda shi kuma ba ya fatan hakan ta kasance a gare shi saboda in akwai abin da ya tsana bai wuce raini da wulak’anci ba.

Ganin bai samu mafita ba yasa ya tashi ya shiga wanka ko ya samu relief akan abin da yake damun shi.

Bayan ya fito wanka ne ya d’akko t-shirt da jeans yasa, ya d’auki kwalin exotic a fridge kasancewar shine favourite drinks d’in shi dan haka ba ya rabo dashi a fridge, ya nufi garden d’in gidan.

Sipping d’in exotic d’in yake yi a lokaci d’aya yana danna wayar dake hannun shi.

Tunanin d’azun ne ya k’ara dawo mishi a karo na biyu akan cewa yaje ya ba Fatimah hak’uri ko da yana ganin hakan na nufin girman shi zai zube a gurin ta saboda yanayin rawar kanta da yaga tana fama dashi.

*(Hmm to nima dai na k’osa in samo amsar a gurin yaya Faruk saboda zargi ne kala- kala a raina*
*Amma dai bari in bishi sannu a hankali saboda nasan amsar na nan tafe)*


Ganin tunanin bai da wani amfani a gare shi illah wani damuwar da zai k’ara mai, shi yasa ya tashi ya nufi side d’in Momi wacce ke zaune a 2-sitter rik’e da littafi da biro a hannun ta, da alama wani abu mai mahimmanci take yi.

Yaya Faruk ne yayi sallama yazo ya zauna kusa da ita yana lumshe ido kamar wanda yake jin bacci.

Amsa masa sallamar tayi kana ta maida hankalin ta gare shi.

"Faruk! ta kira sunan shi.

Cikin husky voice d’in shi ya amsa mata da "na'am Momi, Sannu da hutawa".

Momi ce ta nazarce shi a cikin ‘yan mintuna sannan tace "Faruk! what is wrong with you".

Amsa ma ta yayi da cewa "ba komai Momi, kawai dai ina jin stress ne ya min yawa".

Murmushi Momi tayi kana tace "Faruk! yanda na lura akwai abin da yake damun ka, but it seems like you don’t want to tell me, any way bazan matsa maka ba tun da kana ganin ‘boyewar shine mafita a gare ka".

"believe me Momi, i don’t have any problem, kawai dai ba na jin dad’in jiki na ne".

Kallon shi kawai tayi saboda ba ta yarda da maganar shi ba amma bari ta bi dashi a hakan.

Kasha magani ne? ta tambaye shi.

"Eh na sha" ya ba ta amsa.

Canza hirar yayi da cewa "Momi kayan sun k’araso ne?

"Sun iso, yanzu ma lissafin da nake yi kenan saboda wasu za su kai garuruwa ne, na ga ma wannan karan an fi son less, next time sun zan sa a kawo min da yawa, dan ina ganin wannan zasu yi saurin k’arewa".

Ci gaba suka yi da zancen business kana yaya Faruk ya mik’e da niyyar tafiya yana cewa "Momi bari in je in d’an kwanta".

"Ka ci abinci ne? Momi ta tambaye shi.

"No Momi i don’t feel like eating" ya amsa mata.

"Daurewa za kayi kaci, saboda zama da yunwa ba dad’i, zan sa Anisa takai ma abincin side d’in ka" Momi ta fad’a.

"Ok Mom" ya amsa mata sannan ya juya ya fita daga d’akin.

Momi ce ta kira Anisa akan taje takai ma yaya Faruk abinci.

Kitchen ta nufa ta d’akko abicin ta nufi d’akin.

Samun shi tayi a kwance akan rest chair da alama akwai tunanin da yake yi, sabida ko sallamar da tayi bai amsa ba saoda yana cikin duniyar tunani.

Ajiye food flask d’in tayi akan center table, ta nufi fridge ta d’akko mai swan water ta ajiye.

Ganin duk wannan kai kawon da take yi a d’akin bai mata magana ba wanda ke nuni da yayi nisa a cikin tunani.

Har ta juya da niyar barin d’akin, in yaso in ya gama tunanin ya ci abincin.

Yanayin damuwar da taga yake ciki tun lokacin da ya shigo gidan yasa ta kasa samun peace of mind, dan haka ta matsa kusa dashi ta kira sunan sa a hankali amma bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta rik’e mishi hannu.

Da sauri ya d’ago kamar wanda ya tashi daga bacci yana kallon ta.

Ganin haka ne yasa tace "yaya ga abincin nan in ji Momi wai kaci".

"Ok" ya ba ta amsa a gajarce.

Ta juya da nufin tafiya ta d’ago ta kalle shi kamar da abin da take son cewa.

Kamar ya lura da yanayin ta ne yasa ya kira sunan ta.
"Anisa zo nan".

takowa tayi ta zauna a bakin gado.

"Come close to me Anisa" abin da yace da ita kenan.

Cikin sanyinta ta zauna kusa dashi.

Hannun ta ya rik’e yana cewa "Anisa tell me what is in your mind, don’t be afraid, nasan akwai magana a bakin ki, so feel free".

Kame-kame ta fara yi sannan tace "ba komai yaya, dama naga kamar akwai abin da yake damun ka ne, shi yasa na damu".

Lallausan murmushi yayi ya ce "don’t worry my Sister, ba abin da yake damu na, but still i need your prayer because there is something that i want to archieve"

Kallon shi kawai tayi ta gane he is serious of his word, dan haka tace "yaya i wish you success on what you want to archieve".

Dad’in kalamenta yaji saboda yasan ko ba komai ya samu sauk’i a tunanin da yake yi.

Haka ya dinga jan ta da hira wanda hakan ba k’aramin dad’i yayi wa Anisa ba, dan ta manta raban da ya zauna ya nuna mata caring d’in shi.

Sallama ta mai ta tashi ta tafi tana mai fatan hakan ya dawwama a tsakanin su.
[3/23, 13:03] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Wannan shafin naku ne*.

*Mrs Makama* (Hijira)

*Mom Hanan* (Mijin Aurenah)

*Ummien Fauzan* (Tsananin Rabo)

*Ummu Fatima* (Dija Qaya)

*Khairaty* (Ya Sheikh)

*Napheesa Isah Shehu* (Sanadin Maraici)


*'yar mutan Paki na mik’a gaisuwar ta gare ku tare da yi muku fatan alkhairi*.



*NA YABA MUKU*

*Xarah Auwal*

*Meeynarh*

*Da sauran Wanda ban samu ambatar sunan su ba*

*Kune ku ka bada amsar question of the day daidai*.

*Allah ya k’ara ilimi mai amfani*.
*Sunan wanda manzon Allah (s.a.w) ya ambata a lokacin da aka tambaye shi a cikin maza wa yafi so? Shine ya ba da amsar da cewa *‘sayyidina Abubakar radiyal lahu anhu shi yafi so a cikin maza’*.





*Tunatarwa*

Ka da ka damu da hassadar da mutum zai yi maka/ki, saboda wata ni’ima da Allah yayi maka/ki, idan ya baka/ki, babu mai k’wacewa.
Wannan nasiha ce.

Ka/ki ji tsoron yi ma mutane mummunan zato, ko da zaton naka/ki gaskiya ne, don zato shine mafi k’aryar a cikin zance.
Wannan hadisi ne.





25&26

Bayan fitar Anisa daga d’akin, yaji ya samu relief a ranshi, ko ba komai ya ji dad’in addu’ar da ta mishi, yana yabawa da natsuwar ta.

Abincin da Anisa ta kawo mai yaci, kana ya kunna tv yayin da ya kunna tauraron d’an adam, channel d’in Aljazeera yasa inda yake sauraran labarum da ke faruwa a k’asa daban-daban.

Yanda ake faman fad’a a wasu k’asashen ne ya d'au hankalin shi, yayin da wasu k’asar suke fama da kashe-kashen da ake yi musu na kashe musu ‘yan uwa, mazajensu, matayen su ko ‘yaya ba tare da wani dalili ba.

nuno wasu mutane aka yi suna kuka na yadda suke fama da yunwa da rashin muhalli duk a dalilin rashin zaman lafiya na k’asar.

Hamdala yayi wa Allah da a k’asar mu ba a fama da irin wannan fad’ace-fad’acen, sai matsalar da ba za a rasa ba, na fama da matsalar (kidnapping) garkuwa da mutane da yanzu ya addabe k’asar tamu.

Addu’a yayi akan Allah ya kawo mafita ya kuma zaunar da k’asar mu lafiya da sauran k’asashe baki d’aya.

Kiran sallar la’asar ne yasa ya mik’e ya nufi masallaci, ko da ya dawo daga salllah bai shiga cikin gidan ba illah motar shi da ya shiga ya nufi haleems dan ya huta.

Ko da ya isa gurin, ke’bantaccen guri ya samu ya zauna, yana kallon mutane da ke harkokin su.

A wani ‘bangaren kuma, abokai zaka ga suna hutawa, wasu kuma masoya ne ke hutawa.

Ido ya tsura ma wani saurayi da budurwa, kai daga gani masoyan gaskiya ne, in kai duba da yadda suke hirar su cikin nishad’i alamar ba abin da yake damun su.

Yadda suke caring d’in junan su yasa yaji sun burge shi wanda shima yana fatan nan gaba ya samu irin haka ko ma fiye da haka.

"Sai yaushe kenan? yaushe ne zai fito ya bayyana sirrin zuciyar shi da yake faman adana shi wanda yake ganin akwai lokacin da zai samu furta abin da ke ranshi? tambayar da yayi wa kansa kenan da yake buk’atar amsar a karan kanshi.


(HMM YAYA FARUK KAR KAYI SAKE…. SAI KACE BA SOJA BA?)

Yana cikin karanta wasik’ar jaki ne wata kyakkyawar yarinya tazo ta zauna a kusa dashi, ganin ko alamar kallon ta bai yi ba bare aje ga zai tanka ta.
Ganin idan ta biye mai bai san da wata hallita a gurin ba, dan haka ta mishi sallama.

Sanin darajar sallama yasa ya amsa mata, ya d’auke kan shi yana mai ci gaba da kallan wannan saurayi da budurwar.

Lura da tayi bai san da zaman ta ba yasa tace "handsome naga kana zaune kai kad’ai ne shine naga ya dace in zo in taya ka hira".

Yanda taga bai da alamar amsawa yasa tace "in ba damuwa zan iya samun numban ka".

Wani malalacin kallo ya mata na alamar gargad’i amma hakan bai sa ta ji d’ar ba illah k’ara cewa da tayi "suna na Fatima amma ana kira na da Binafa, zan iya sanin sunan ka? ".

Jin sunan da ta ambata yasa ya d’ago ya kalleta amma bai ce mata komai ba sai ma alamar tafiya da yayi saboda yadda yarinyar ta takura mai, gashi ya fito ne dan ya huta amma da alamar yarinyar ba za ta ba shi damar yin hakan ba.

Mik’ewa ya yi da niyyar tafiya, saboda ya k’osa ya bar gurin duba da yadda yarinya ta takura mai.

Cikin sauri ta k’araso gurin shi tana pleading d’in shi cikin shagwa’ba tare da cewa "plss handsome ba ka fad’a min sunan ka ba? idan ba damuwa can i have your phone number".

Ganin yadda yarinyar ke da rawar kai, da alama irin sangartacciya ce yasa yace "I by name Bregadier Umar, but you can call me Faruk" ya juya da niyar ci gaba da tafiya.

Motar shi ya shiga ya hango ta a glass d’in motar shi tana kallon shi, ya rufe motar da niyar tafiya yaga tana nokin d’in k’ofar motar, kamar kar ya kula ta sai yaga gwara su rabu lafiya da ita.

Bu’de glass d’in motar yayi yana cewa "do you need my help?

Karkatar da kai tayi alamar shagwa’ba tana cewa "pls Umar help me with your phone number, i want us to be friend!

Tak’aitaccen murmushi yayi saboda yadda tayi Magana.
numban ya d’auka ya ba ta ya ja motar a guje.

Waving d’in hannu yaga tana mai da murmushi a fuskar ta.

Direct gidan su Fatima ya wuce saboda yadda yaji zuciyar shi na azalzalar shi akan yaje.

Parking d’in motar shi yayi ya nufi cikin gidan.
Ko da ya shiga falon ba kowa a ciki, dan haka ya nufi side d’in Yaya Khalil.

Samun shi yayi yana operating d’in laptop da wanda ke nuni da wani aikin yake yi.

Sallama yayi ya nemi kusa dashi yana cewa "Bros ana aiki ne?"

Amsa masa sallama yayi yana fad’ad’a fara’ar shi "sannu da zuwa yaya Faruk, ina wani research ne saboda akwai wani presentation da zamu yi a school" cewar yaya Khalil.

"that is good, karatu sai an yi hak’uri sannan za a ci ribar abun bare in karatu yazo k’arshe sai a hankali" yaya Faruk ya fad’a.

Yaya Khalil ne ya amsa mai da cewa "Gaskiya kam, system d’in karatu ya canza, ga lecturers d’in ba kowannan su bane masu tausaya wa student".

"Allah ya kawo mana mafita kawai" cewar yaya Faruk.

Amsa mai yayi da cewa "Amin".

Zancen makaranta suka ci gaba dayi na yadda karatu ya koma a yanzu da matsalolin da ake fuskanta.


Suna cikin hirar ne ya kalli yaya Khalil yace "ina Teemah ne? naje main parlour ban gan ta ba, ko har yanzu fushi take yi ne? Nasan ta fad’a maka yadda muka yi da ita, tun da kaine friend d’in su".

Murmushi yaya Khalil yayi ba tare da yace komai ba.

"Je ka kira min ita, kace ta same ni a garden" yaya Faruk yayi commanding d’in shi.

Fita yayi daga d’akin ya nufi garden yana mai jiran zuwan ta.

Ko da yaya Khalil ya je side d’in ta bai tarar da ita ba, dan haka ya nufi side d’in Ummu.

Samun ta yayi kwance a jikin Ummu suna hira, da fara’ar shi ya k’arasa d’akin yana cewa "Assalamu alaikum in shigo ko in koma? Dan yau naga Ummu ta ware Khalil d’in ta tana gurin Autan ta".

Ummu ce ta amsa sallamar tana cewa "kai ma kasan auta dangware shalele ce, ta gaban goshi ce, sai kayi kamu k’afa a gurin ta ka samu fada" cewar Ummu.

Ni kuwa dake faman yamutsa fuska saboda nasan yaya Khalil yau da tsokana yazo.

Kallo na yayi da alamar tsokana yace "Fatima ki tashi kije garden, yaya Faruk ne yazo yake neman ki".

D’aure fuska nayi kamar ba dani ake maganar ba saboda har yanzu wani irin haushin yaya Faruk nake ji.

Ganin ban da alamar tashi yasa ya kalle ni yana cewa "Sister ba ki ji abin da nace bane!

Turo baki nayi kana nace "gaskiya yaya Khalil am sorry amma ba za ni ba, neman me yake min da har zai ce in same shi a garden banda marin da yamin bai ishe shi ba shine zai k’ara dawo wa ya d’aura a inda ya tsaya"ido na fal da hawaye.

Duk wannan tak’addamar da muka fara yi da yaya Khalil, Ummu ba tace komai ba sai yanzu ta kalle ni tace "Fatima ki tashi kije tun kan in ‘bata miki rai, tun da ke ba kya jin magana"

Cikin ‘bacin rai na mik’e na fita saboda yadda naji raina ya k’ara ‘baci na yadda ake ji da yaya Faruk a family, shi yasa yake yin duk yadda yaso ba tare da shakka ba, haka zalika ba a ganin laifin shi.

A raina na k’udurta cewa yau duk abin da yazo dashi ina dai dai dashi saboda yadda naga ya takura min, beside kowa yana bin bayan shi, ba mai ganin laifin shi.

Garden na nufa inda na same shi zaune akan kujera yana facing d’in wanda yake shigowa.

Ko da na k’arasa ciki-ciki na masa sallama na nemi guri na zauna ba tare da k’ara cewa uffan ba.

Motsin da bakin shi yayi ne ya tabbatar min da cewa sallamar ya amsa.

Ta’be baki na nayi a raina ina cewa "miskili Kenan, kafi mahaukaci ban haushi, nima zan nuna maka gidan ka tarar".

Jin shirun yayi yawa yasa raina ya k’ara ‘baci fiye da d’azun saboda ni a gani na duk salon wani cin fuska ne da kuma hanyar da zai ‘kara sa min wani ‘bacin rai, in ma hakan yake nufi bazan bashi fuskar ganin hakan a tare da ni ba bare ya samu wata damar na min yadda yake so.






(HMM READERS NASAN KUMA ZAKU SO KUJI DALILIN DA YASA YAYA FARUK YA KIRA FATIMAH, TO NIMA HAKAN TAKE A GURI NA.
KU BI NI SANNU A HANKALI DAN JIN SAURAN LABARIN)

[3/24, 22:28] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀

*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Na sadaukar da wannan shafin gareki ‘yar mutan Nijar* (Dr Maimuna Matar Abdoulaye)
*Marubuciyar* (Latifa)

*Ki yi yadda kike so da shafin*.

*Allah ya k’ara baki k’arfin gwiwa na taimakon al’umma*




*Question of the day*

Wace mata ce ta tara (9) a cikin matan manzon Allah (s.a.w)? menene asalin sunan ta da nick name d’in ta?





27&28

Cikin tattausan lafazi da jan hankali ya kira suna na "Fatimah"

"Na’am" na amsa mai a tak’aice da kuma d’aure fuska saboda yadda na k’osa na bar gurin dan ni ban ga amfanin kiran da yayi min ba.

"Fatima! Kina jin haushin marin da na miki ko? a tunanin ki kamar na tsane ki ko?

"Dago wa nayi na kalle shi dan kamar yasan abin da ke cikin zuciya ta kenan amma ban da halin furta hakan.

Kallo na yayi yaci gaba da cewa "Nasan kina ganin kamar ina takura miki ko? kuma ina interfere a personal life d’in ki wanda tuntuni na gane ba kya son hakan daga gare ni, duk a tunanin ki na samun liberty da human right da yake rud’arki".

Fatima! Ina yi miki haka ne saboda future d’in ki as i take you like my blood sister, d’aya kuke da Anisa a guri na, ba zan ba ku freedom nayin socialization a matsayin ku na mata ba, any social life da kike gani da bature ya fito da tsarin fundamental human right yana da disadvantage, saboda a ciki akwai inda aka yi stating d’in cewa ‘you have the right to participate in any social activities you like’
kin ga kenan akwai illah babba a ce an ba d’an adam damar yin duk abin da ya ga dama ba tare da an tsawatar mai ba wanda a addinin mu, Annabin mu, Muhammas (s.a.w) ya fad’akar damu da cewa " idan baka jin kunya, ka aikata abin da kake so", na d’auke ki ne kamar Anisa da zan iya hukunta wa ba tare da fargaba ba, hakan yasa nake d’aukan action a kan ku, so i will not give you the opportunity to do what you like".

A ‘bangare na kuwa wannan dogon bayanin da yake yi ne ya ishe ni, ji nake yi kamar in tashi in bar mai gurin.

Cikin cool voice ya ce "Fatima am sorry da na mare ki, nima ba da san raina na miki shi ba, ke ki ka jawo hakan saboda yadda kika min magana ne ya ‘bata min rai, da kika tambaye ni dalilin da yasa na yaga miki hoto"

'Wonder shall never end" na furta hakan a raina, ko a mafarki ban ta’ba tunanin yaya Faruk zai furta wata kalma mai suna ‘Sorry’ a bakin shi ba, bare ni da yake d’auka na teenager.

Gaskiya ne da hausawa ke cewa "in da ranka zaka sha kallo".

Dad’i naji a raina yau yaya Faruk ya k’ask’antar da kanshi a kaina yana neman yafiya ta, da nayi tunanin ko wani salon ya canza da zai musguna min ko akwai wani shiri da yake yi a kaina yasa na magantu akan dad’in da naji nay a nemi yafiya ta.

Ci gaba yayi da cewa "Fatima! Zan iya jurar komai amma ban da raini da wulak’anci, da fatan zaki kiyaye saboda as from now, ina so ki d’auke ni kamar Khalil da zaki iya fad’a wa damuwar ki da kuma neman shawara a gurin shi".

Rasa a wace duniyar nake, wai yaya Faruk ne yake min Magana in a polite way da kuma neman mu shirya.

Wani tunani ne yazo min akan cewa akwai dalilin da yasa yake neman mu shirya dan ruwa ba ya tsami banza.

"Teemah" ya kira suna na da sanyin murya.

Ban samu damar amsawa ba saboda yau mamaki ne ya cika ni, bin shi kawai nake yi da kallo dan ina so in tabbatar da cewa a buge yake ko a hankalin shi yake fad’an maganganun nan, duk da ban ga wata alama na yasha wani abu ba, yana fad’ar maganganun nan ne da gaske.

Kallon da yaga ina bin shi dashi ne yasa yayi tak’aitaccen murmushi yana cewa "are you surprise? ki cire mamakin da kike yi dan na nemi yafiyar ki".

Zuciya ta ce ke ingiza ni akan kar in yadda da dad’in bakin da zai min, saboda yana da dalilin yin hakan.

Ganin ba zan ce mai komai ba yasa yace "Teemah! ba ki ce komai ba, ko ba ki yafe min ba?

Satar kallon shi nayi na yadda yake magana yana wani lumshe ido kamar yana magana da budurwar shi.

Duba da yadda nake son in bar gurin, hakan yasa nace "na yafe maka yaya Faruk kuma ni b aka min laifi ba".

Wani murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya bayyana a fuskar shi.

Lura da nayi da bai da alamar bani damar tafiya yasa na k’ara d’aure fuska kamar zan yi kuka saboda yadda na gaji da zama a gurin, kuma ni har yau ba wai na huce da abin da ya min bane.

Tambaya na yayi akan wane course na yi applying kuma wani school nayi za’ba?

A tak’aice na bashi amsa da cewa "computer science nayi applying kuma kaduna Polythecnic ne first choice d’in da na sa".

K’arfin gwiwa ya dinga bani akan harkar karatu kasancewar sa mai son muyi karatu.

Alamar

Please Login or Register in order to submit comment