Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lumshe idon shi saboda wahalar da yake sha.


Meema Wanda tun dawowar Dr taji shigowar shi side d'in shi.


Tashi tayi ta nufi side d'in shi saboda yau bai wuni a gida ba tun da ya fita aiki.


Tana shiga taga Dr a halin da yake ciki.


Da gudu ta k'arasa gurin shi ta rik'o shi.
Kuka Meema ta fara tana tausaya ma Dr halin da yake shiga.


Ta rasa abin da yasa sai ya fita ya dawo yake shiga wannan halin.


Dr Wanda hankalin shi ya fara barin jikin shi bai san me Meema ke ciki ba.


Lokaci d'aya numfashin Dr ya d'auke.
[10/23, 07:40] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



Facebook: Kainuwa Writers Association


www.maryamahmadpaki.blogspot.com






_ALHAMDULILLAH_


_Kamar yanda na fad’a a cikin littafin nan cewa a last page d’in novel d’in nan zan fad’i wanda suka zo na 1-3 a cikin shirin Question of the day_.


_Sannan kamar yanda na alk’arwanta cewa akwai kyauta ga wanda suka zamo 1-3 a cikin shirin_.


_Ba abin da zan ce wa duk wanda suka ba da gudunmuwar su wajen ba da amsa tambayoyin question of the day sai dai in musu fatan alkhairi da addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi ya kuma sa jannatul fidausi ta samo makoma a gare mu baki d'aya_.



*Meeynah* _(Princess of question of the day 1st position)_


*Xarah Auwal* _(Ass queen of question of the day 2nd position)_


*Aisha Autar Mama* _(Queen of the question of the day 3rd position)_


_Sauran wanda su ma suka ba da gudunmawar su a cikin shirin sun had’a da_:

_Hajarah Isah_

_Fadyla Ingawa_

_Ummu Fadlu_

_Ameenatou_

_Salmah

_Maman Walida_

_Sakina Ilyas_

_Ramlah_

_Fadeelah_

_Br Teemah_

_Jazakumul lahu khairan bikum_.




⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇


LAST PAGE




Jikin Meema ba in da ba ya rawa lokacin da ta lura Dr ba ya numfashi.


Da k'yar ta samu ta kwantar da Dr akan pillow kana ta d'auki wayar ta cikin kuka ta kira Momi ta fad'a mata halin da ake ciki.

Ba a d'au wani lokaci ba Momi ta tawo da Hanan suka zo gidan.


Gaba d'ayan su kuka suka sa ganin halin da yake ciki saboda duk Wanda ya ga Dr a lokacin dole ne ya zaci ya mutu.


D'aukan Dr suka yi suka sa shi a mota suka nufi Kangiwa hospital dashi.


Sai da likitoci suka had'u akan Dr kafin su samu numfashin shi ya dawo kana aka jona ma Dr abin taimakawa numfashi(oxygen).


Sai da Dr ya kwashe awa kusan uku sannan Dr ya dawo normal aka kai shi special room.


An ba su Momi damar su shiga su duba shi amma su kiyaye yin hayaniya ko wata magana da za ta sa Dr ya koma cikin wani halin.


Duk Wanda ya shiga ya duba Dr sai ya tausaya masa.


Dr sai da ya kwashe kwana kusan 4 a kwance a asibiti.


Sai dai tun san da Dr ya fara jin sauk'i yake ambatar suna na.


Hakan yasa Momi ta fahimci akaina ya shiga wannan halin da yake ciki.


Meema kuwa ranta ne ya b'aci da ain da Dr ya ke yi, gani take yi kamar wani salon cin fuska ne yake mata, hakan yasa ta rage zaman asibiti.



Yau Momi ce da Dr a asibiti take tambayar shi abin da yasa shi cikin wannan halin.


Hawaye ne ya fara zubowa Dr kana cikin sanyin murya Dr ya ce "Momi ke da Dadi nasan ba za ku so ku dinga gani na a cikin wannan halin da nake ciki ba, so Momi if you want to see my happiness ki je gun Zarah ki rok'ar min ita ta amince dani, ni nasan tana so na Momi, sai dai abin da na mata ne yasa take min haka, I love her Momi, nasan alhakin ta ne ya kama ni shi yasa Allah ya k'ara min sonta fiye da a lokacin baya, ni kaina nasan ban ma Zarah halacci ba, ban saka mata da irin sadaukar da ta min na soyayya ba, pls Mom pls help me, ina son ganin ta kusa dani".


Jikin Momi ne yayi wani irin sanyi had'e da tausayin Dr.


A shirye take taje ta rok'e ni in amince in auri Dr ko dan ceto rayuwar shi sannan ita kanta ta yaba min dan tasan ba ni da matsala hasalima Meeman da taso ya aura ita kanta yanzu ta fara dawowa daga rakiyar Meema saboda halayen ta.


Rik'o hannun shi tayi ta sakar mishi murmushi ta ce " ka kwantar da hankalin ka Sadik, in dai Fatima rabon ka ce sai ka aure ta yardar Allah, yanzu a shirye nake na je na rok'eta ta amince ta aure ka, ni kaina yabawa da halin ta, ka sa ma ranka za ka samu Fatima in dai Allah ya nufa, ina da tabbacin har yanzu tana son ka za kuma ta amince, sai dai Sadik ba na so ina ganin ka a wannan halin, kasan ciwon da ke damun ka ba ya son damuwa, ka dinga kiyayewa dan samun ci gabanlafiyar ka, insha Allah zan je gidan su".


Murmushi ne ya bayyana a fuskar Dr kana ya k'ara rik'o hannun Momi.


A hankali ya ce "Momi na gode, Allah ya saka da alkhairi".


Ita ma murmushin ta mayar mishi kana ta ce "you deserve more than that my Son".


Haka Momi ta ci gaba da lallashin Dr ya kwantar da hankalin shi, suna cikin haka ne Dadin Dr ya shigo.


shima dai kwantar mishi da hankali ya dinga yi.


Haka suka dinga ririta Dr kamar wani k'aramin yaro.




Yau Yaya Faruk ne ya tawo Kaduna dan ya gaishe da su Momi.


Gidan su ya fara zuwa kana ya wuce gidan Yaya Aminu dan sun yi waya yana gida.


Momin Dr da kanta tayi driving tazo gidan mu.


Ina d'aki a kwance ina sauraran wa'azin Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa.


Ina kwance na jiyo magana a main parlour amma ban maida hankali na gurin sanin wacce tazo ba.


Ummu ce ta shigo ta kira ni.


Tun da na shiga falon na yi tozali da Momin Dr.


Mamakin zuwan ta nayi da tambayar kaina kar dai Dr ne ya turo ta.


Murmushin Momin ne ya k'aru ganin na k'araso.


A sanyaye na tsuguna na gaishe ta kana na nemi guri na zauna.


Ummu ce ta kalle ni ta ce "Fatima ga Momin Abubakar nan, ta ce gurin ki tazo".

Juyawa tayi gurin Momi ta ce "Hajiya bari in shiga ciki in Baku guri, in kun gama maganar Fatima ta kira ni".


Momi ce ta ce "Haba ba zai kin je ko ina ba, ni nafi so ma in yi maganar a gaban ki" .


Murmushi Ummu tayi ba ta ce komai ba.


"Zarah alfarma nake nema a gurin ki, ina so ki yafe ma Sadik abubuwan da ya miki a baya duk da ban San mai ya miki ba, duk wanda kiga an nemi yafiyar shi to shi aka cuta, ina so ki yafe mishi saboda girman Allah da kuma darajata da na tako na zo dan na nemi yafiyar ki" Momi ta fad'a.


Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da zoben hannuna na ce "Momi ni Dr bai min komai ba, wanda ya min a baya ma na riga na yafe mishi".


Fara'ar Momi ce ta k'ara linkuwa ganin yanda tayi saurin shawo kaina dan haka ta ce "Alfarma ta biyu da nake so ki min ina so ki amince ma Sadik ki aure shi, Sadik ya shiga wani hali a dalilin k'in amince mishi da kika yi, yanzu haka yana kwance a asibiti, ba Wanda yake ambata sai sunan ki, wannan alfarmar nake so ki min".


Shiru nayi kamar bazan yi magana ba har sai da Ummu ta min magana.


D'ago kaina nayi na kalli Momi kana na sunkuyar da kaina.


Yanayin Momi ya sa jiki na yayi sanyi yanda take rok'o na, da alama halin da Dr yake ciki yayi tsanani.


Zuciya ta ce na ji tana son yin rauni, saurin kau da hakan nayi a zuciya ta.


"Fatima ina jin ki, ki fad'a min ra'ayin ka akan Dr d'in" Momi ta katse ni.


"Momi ki ba wa Dr hak'uri, ni a yanzu ba na ra'ayin k'ara auren shi, akwai wanda nake so in aura, Allah yasa hakan yafi zama mana alkhairi" na fad'a.


Momi cikin lallashi ta dinga rok'o na in tausaya ma Dr saboda gudun halin da zai shiga saboda rashin amincewa ta amma hakan bai sa na canza shawara ta ba.


Ummu kuwa tun da muka fara maganar da Momi ba tasa bakin ta ba.


Momi ganin ba ta samu nasarar shawo kaina ba yasa ta juya gurin Ummu.


Hawaye ne ya fara zubowa a fuskar Momi ta ce ma Ummu "Hajiya ki taimaka ki sa baki Fatima ta tausaya ma Sadik, yanzu in ki ka ga halin da yake ciki sai kin tausaya mishi, ban san me zan fad'a mishi ba" Momi ta k'arasa maganar da fashewa da kuka.


Tausayin Momi ne ya cika Ummu ganin babbar mace na kuka.


Cikin tausayawa ta ce "Hajiya insha Allah komai zai zo da sauk'i, sai dai a yanzu ba zan matsa wa Fatima akan ta amince ta auri Sadik dan ban san dalilin da yasa tak'i amincewa dashi ba bayan a baya ita ita ta kawo shi a matsayin wanda za ta aura, in Fatima rabon Sadik ce, sai ki ga komai yazo da sauk'i ta aure shi, shi kuma Sadik Allah ya bashi lafiya, Allah ya daidaita lamarin".


Hawaye ne ya ci gaba da zubowa a idon Momi tare da jinjina yanda za ta fuskanci Dr da wannan bayanin.


A na cikin haka Yaya Faruk yayi sallama ya shigo.


Gaishe da su Ummu da Momiyayi kana ya nemi guri ya zauna.


Gaishe shi nayi ya amsa min a dak'ile.


Sallama nayi ma Momi na koma d'aki na.


Addu'a nake yi Allah yasa zuwan da yaya Faruk yasa yazo ne ya fad'a min ya amince da magana ta, da ban San farin cikin da zan yi ba.


Bayan tafiya na Ummu taci gaba da fad'a ma Momi kalamai masu kwantar da hankali, har lokacin hawaye bai daina zubowa a fuskar ta ba.


Duk maganganun nan da suke yi Yaya Faruk yana jin su.


Momi ganin babu alamun samun nasara a zuwan ta yasa tayi musu sallama ta tafi.


Bayan tafiyar ta ne Ummu ta mishi bayanin zuwan Momi gidan.


"Allah ya zab'a abin da yafi alkhairi" Yaya Faruk ya fad'a.


Sun d'an tab'a hira da Ummu kana ya mik'e ya shigo d'aki na.


Mamakin ganin shi nayi domin ban yi zaton shigowar shi a lokacin ba.


Hannun shi ya hard'e ya jingina da bangon d'akin yana kallo na.


Sunkuyar da kaina nayi saboda tsoron hukuncin da zai min na ke yi na kiran shi da nayi a waya.


"Fatima" ya kira suna na.


A hankali na amsa mishi.


Murmushi yayi ganin yanayi na da ya nuna a tsorace na ke kana ya ce "Fatima maganar da na ke so muyi ina so ki d'auke ta da mahimmanci, Fatima ke ce wacce na fara so kuma akan ki nasan dad'in soyayya da illar yin ta, Na so a ce tun farko ni kika fara aura ba wani ba amma sai Allah bai yi na hakan ma yasa na hak'ura da ke, Fatima na sha fad'a miki ina da kishin abin da na ke so, shi yasa ma ba na jin zan amince in aure ki dan nasan kin riga kin mallaka ma wani zuciyar ki da jikin ki ba ni ba, ko a yanzu da kike ik'irarin kina so na zan iya yarda da cewa wani abu nayi ya burge ki kike tunanin so na kike yi kuma nasan kina k'ok'arin ganin kin goge laifin da kika min a baya amma tsantsar so yana gurin tsohon mijin ki, shi kike ma wa, Fatima a yanzu bazan aure ki ba saboda ban yi ma Khadijah adalci ba wacce ta amince ta aure ni a lokacin da nake buk'atar wanda zai maye min gurbin ki, sannan na riga na sa ma zuciya ta hak'uri dake saboda misali ko na aure ki zuciyar ki na ga wani, saboda haka Fatima ki ajiye maganar soyayya da aure a tsakanin mu, ni kaina ba zan so a fara k'irga miki mazan da kika aura ba, gwara mu ci gaba da zama a matsayin y'an uwantaka kamar yanda kika nema a baya, sannan ina so ki tunkare ni da neman shawara in hakan ta taso ni kuma zan tsaya in saurare ki, A k'arshe ina so ki yi hak'uri ki koma gidan tsohon mijin ki tun da shima yana son ki, sannan ki tausaya ma halin da yake ciki da kuma rok'on da mahaifiyar shi tazo ta miki, ina fatan za ki d'auki shawarar da na baki".


D'agowa nayi na kalle shi yayin da hawaye yake zuba a idanu na.


Shi kenan na rasa Namiji d'aya tamkar da goma.


Na rasa jajurtaccen namiji, mai kyawawan halaye da dad'in zama.


Dole in hak'ura da Yaya Faruk tun da ya min wannan bayanin.


Cikin rawar murya na ce "Na gode Yaya Faruk, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a tsakanin mu, ba abin da zan ce maka sai godiya".


Murmushi yayi ya ce "Yawwa Fatima haka na ke son ji, yanzu ina so ki taso in kai ki asibitin ki fad'a ma shi Dr d'in kin amince za ki aure shi".


Saurin d'agowa nayi na kalle shi na fara mutsu-mutsu da baki.


Fahimtar da Yaya Faruk yayi ban son zuwa yasa ya ce "Fatima ba na son musu, ki taso mu tafi".


Ba yanda na iya, haka na tashi nasa hijab muka fito a tare.


Sai da muka je gun Ummu, Yaya Faruk ya fad'a mata za mu unguwa kana muka shiga mota muka tafi.


Sai da muka fara tafiya ne Yaya Faruk ya tambaye ni wani asibiti a ka kwantar da Dr d'in.


Duk da ban da tabbacin in da aka kwantar dashi, nasan ba zai wuce asibitin da yake aiki ba, hakan yasa na fad'a ma Yaya Faruk asibitin.


Ko da muka shiga asibitin ba mu sha wahalar gane in da aka kwantar dashi ba kasancewar shi sanannen Dr a asibitin.


A tare muka shiga room d'in da Yaya Faruk.


Tun da muka had'a ido da Dr ya fara k'ok'arin sakkowa daga kan gadon.


Wani irin tausayin shi ne ya kama ni ganin yanda ya canza a y'an kwanaki duk a sanadi na.


Na k'ara tabbatar da cewa Dr ba k'aramin so yake min ba tun da ya shiga wannan halin.


A yanzu nasan cewa soyayyar da Dr yake min tafi wacce na mishi a baya.


Momi kuwa murna ce ta kama ta kamar ta tashi ta taka rawa.


Meema kuwa dake can gefe tana danna waya ta d'ago ta zuba min wulak'antaccen kallo kana ta mik'e ta bar d'akin.


Yaya Faruk ne ya tambayi jikin Dr kana ya mishi fatan samun sauk'i.


Sallama ya musu kana ya sanar dani yana jira na a mota.


Momi ma fita tayi daga d'akin ta barni daga ni sai Dr.


Alamu ya dinga min akan in zo kusa dashi.


Hakan yasa na k'arasa gefen gadon na zauna.


"Fatima Zarah" Dr ya kira suna na cikin muryar rashin lafiya.


Ban amsa kiran da ya min ba sai kallon shi da nayi.


"Fatima ke na ke gani a gaba na kin zo duba ni, Zarah ban San wani irin farin ciki nake ciki ba na ganin ki da nayi a wannan lokacin, San da Momi ta dawo ta sanar dani kin k'i amincewa dani sai da likitoci suka taru akaina saboda numfashi na da ya d'auke, da k'yar aka samu numfashi na ya daidaita, ki tausaya min Zarah, ke ce farin ciki na kuma sanyin idaniya ta".


A yanzu ina ganin ba abin da ya wuce da in amince da Dr tun da Yaya Faruk ya ce in hak'ura dashi na kuma fahimci hujjar shi nayin haka".


Dr ne ya katse min tunanin da na fara da cewa " Kin amince Zarah za ki aure ni mu ci gaba da gudanar da soyayyar mu a rayuwar auren mu".


"Na amince Sadik, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gare mu" na fad'a.


Cikin murna Dr ya dinga min godiya.


Cikin y'an mintuna sai ga Dr a zaune yana hira dani kamar ba shi ne a kwance ba.


Sanin Yaya Faruk ba ya son jira yasa na ma Dr sallama na fito.


Dr ya so ya raka ni na hana shi kasancewar na lura jikin shi bai dawo normal ba.


A waje na had'u da Momi na mata sallama.


In da Yaya Faruk ya yi parking d'in motar shi na je na shiga muka tafi.


A hanyar mu ta komawa gida ne Yaya Faruk ya kalle ni cikin tsokana ya ce "Ashe k'anwar tawa har yanzu tana son Dr d'in ta, gashi daga kai ki duba shi kin barni a zaune kuna can kuna hirar soyayya".


Rufe fuska ta nayi ina dariya na ce " Yaya Faruk ba fa hirar soyayya muka yi ba fa".


Murmushi yayi ya ci gaba da tuk'in shi yana jana da hira jefi-jefi.


Ko da muka koma gida a Main parlour muka zauna muna ci gaba da hira dashi.


Tun ban sake dashi ba har na sake muka ci gaba da hira.


Ummu San da ta shigo falon ta ganmu da Yaya Faruk muna ba k'aramin jin dad'i ba ne ya bayyana a fuskarta ba.


Haka Ummu ta zauna muka ci gaba da hirar da ita.


Yaya Faruk ya jima a gidan mu kana ya mana sallama ya tafi saboda ya ce a yau yake son komawa Abuja.



B’angaren Dr kuwa an samu ci gaba wajen samun lafiyar shi tun san da na je duba shi a asibiti.


Hakan yasa ganin ya samu lafiya aka sallame shi tare da k’ara bashi hutun kwana biyu.


Yanzu Dr hankalin shi ya kwanta ganin na amince zan aure shi.


Kulawar da yake nuna min da gudun b’acin raina da yake yi yasa na ji na k’ara samun natsuwa da auren shi.


Matsa min da Dr yake yi akan yana so ya turo gidan mu ayi maganar aure yasa na fara tunanin yanda zan tunkari Ummu da Abbu da maganar dan ban san yanda za su k’arb’i maganar ba.


Ummu na fara sa ma na fad’a mata halin da ake ciki kana na d’aura mata da yanda muka yi da yaya Faruk.


Ummu tayi mamakin maganar da na fad’a mata game da yanda muka yi da yaya Faruk, ba ta ji haushin yaya Faruk dan ya k’i aure na, tasan cewa ni na b’ata rawa ta da tsalle sannan ba kowa ba ne zai laminci abin da nayi daga baya ya amince ya aure ni ba, tun farko taso a ce shi na Aura amma Allah bai nufa ba, yanzun ma tasan Allah bai nufa zan zamo matar shi ba, fatan alkhairi ta min akan maganar mu da Dr kana ta ce za ta sanar da Abbu halin da ake ciki.


San da Abbu ya dawo gida ne Ummu ta zayyane mishi halin da ake ciki.


Shi kan shi yaso a ce karo na biyu yaya Faruk ne ya same ni a matsayin mata amma tun da yaya Faruk ya kawo dalilin na k’in aure na yana ganin bai kamata ya mishi magana akan ya aure ni ba tun da yanzu ba ya ra’ayi na yasan Allah ne bai nufa zan zamo matar shi ba.


Fatan Allah yasa shi Dr d’in ya zamo wannan karan shine mijin da zan aura baa tare da wata matsala ta k’ara shiga tsakanin mu ba har ta kai ga rabuwa.


Ummu yasa ta kira ni ya min nasiha tare da addu’ar Allah ya tabbatar mana alkhairi a tsakani na da Dr kana ya d’aura da cewa in fad’a ma Dr d’in ya turo.


Ina fad’a ma Dr yanda muka yi da Abbu akan ya turo ya dinga murna.


Ba a d’au wani lokaci ba Dr ya turo magabatan shi aka tsayar da biki nan da wata uku.


Wannan karan na samu na samu natsuwa a alak’a ta da Dr ganin su Ummu da Abbu sun nuna amincewar su sannan su yaya Khalil da yaya Aminu da Anisa ma sun nuna amincewar su.


San da Anty Jiddarh tazo na ke fad’a mata yanda muka yi da yaya Faruk da kuma halin da ake ciki tsakani na da Dr ita ma fatan alkhairi ta min.


Meema kuwa tun san da taji aure na Dr ta tada hankalin ta da shi kanshi Dr d’in akan cewa ba ta amince ba.


Tun Dr yana bin ta a hankali har tazo ya biye mata suna sa’in’sa da ita amma duk da haka Meema ba ta da alamar hak’ura.


Dr da farko ya d’auka cewa za ta hak’ura ta daina ta da hankalin ta akan aure na da zai yi amma abin ya ci tura.


Ganin yanda kullum suke cikin rikici da ita yasa ya je ya fad’a ma Momin ta, ita kanta Momin Meeman fad’a ta fara mishi akan aure na da zai yi.


Ganin nan ma ba nasara yasa ya je ya fad’a ma Momin shi matsalar da su ke fuskan ta da Meema.


Hak’uri Momi ta bashi tare da k’ara nuna mai ribbar hak’uri da yanda zai lallashi Meema d’in.


Ta fad’a mishi in ta samu free time san da ba ta da aiki za ta zo gidan ta lallashi Meema d’in.


Yaji dad’in yanda Momi ta bashi shawarwari kana ya mata sallama ya tafi.


Ko da ya koma gida haka Meema ta dinga zuba mishi rashin mutunci wanda ta kai ya kasa controlling d’in zuciyar shi ya mare ta.


Haka Meema ta dinga kuka tana fad’an duk maganar da tazo daga bakin ta.


Jin yanda zuciyar shi ke mishi wani irin zafi da maganganun da Meema ke fad’a mishi yasa ya nufi side d’in shi dan yasan tsayuwar shi a gurin zai sa ya mata mummunan hukunci.




Yau Momi ce ta zo gidan Dr.


Side d’in Meema ta fara zuwa ta tarar da ba kowa a falon sai mai aiki.


Mai aikin ce ta gaishe ta kana Momi ta ce ta kira matai ta.


Sai da aka d’au lokaci kafin Meema ta fito.


Tun da taga Momi ce ke kiranta ta k’ara d’aure fuska saboda yanzu haushin Momi take ji saboda tana ganin ta had’in bakin ta Dr zai aure ni.


Sai da ta nemi guri ta zauna kana ta gaishe da Momi a dak’ile.


Duk da Momi taji haushin yananyin yanda Meema ta gaishe ta amma sai ba ta nuna ba ta amsa mata da fara’a a fuskar ta.


Nasiha da lallashin ta Momi ta dinga yi amma duk wannan mganar da Momi take yi kamar ba da ita take yi ba.


Momi ce tasa Meema ta kira mata Dr kasancewar yana gida.


Nasiha ta dinga musu gaba d’aya da nusar da su hak’uri da juna da kuma zaman lafiya a tsakanin su.


Meema wacce ranta ya b’aci da wannan nasihar da Momi take musu ta ce
"Momi ni fa in dai ba cewa kika yi yaya Sadik ya fasa auren nan ba to ina ganin no need of this advice, nasan kema son auran nan da yaya Sadik zai yi kike yi saboda kina son farin cikin d’an ki amma ni ba kya son nawa, ke kan ki Momi kin san irin son da yaya yake ma Zarah amma shine kike so ya auro ta ya had’a mu saboda in ta kwasar bak’in ciki, to ni dai bazan zauna da wata kishiya ba tun da gidan mu ma ban taso na ga kishiya ba saboda haka sai dai Dr ya hak’ura da wannan k’addararren auren da yake son yi"




Momi da mamakin abin da Meema ta yi ya kama ta yasa ta kasa yin magana sai bin ta da tayi da kallon mamaki.


Dr kuwa wanda ran shi ya gama b’aci da maganganun da Meema take fad’a ma Momin shi yasa ya daka mata tsawa ya ce "Ya ishe ki Meema, zan iya jurar komai amma ba zan lamunci ki fad’a wa Momi magana ba, ko da yake tarbiyya ba isan ki tayi ba".


Wani banzan kallo ta watsa mishi kana ta ce "Ina fa tarbiyyar za ta ishe ni tun da ban je gidan ku an koya min ba, k’arya nayi ba da Momin aka had’a wannan munafuncin auren da za kayi bad an ta ga ni ba y’ar ta ba ce, in da Hanan ce ko Farida ai ba za ta bari a k’ara musu kishiya ba shine ni take so a min, in dai ana son kwanciyar hankali a gidan nan dole ne ka fasa auran nan in ba haka ba kuwa ka dinga gamuwa da b’acin rai, ko dan ka ga ina son ka shine za ka dinga wulak’anta ni, kai kan ka kasan ni y’ar gat ace gaba da baya saboda haka ba zan tsaya in ga za a yi disgracing d’ina ba".


Dr saboda b’acin rai jikin shi har rawa yake yi

Please Login or Register in order to submit comment