Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kokarin shigo da wata, nasan duk yadda Dr yake da tsarin turawa wataran zai ajiye wannan raayin ya bukaci haihuwa, idan ni kuma har lokacin ban samu haihuwa ba na san zai bukaci haihuwa daga gurin Meema, a lokacin ni kuma zan zama y'ar kallo.


Da kyar na iya samu na tashi daga gurin na koma cikin daki na.


Washe gari ko da na hada breakfast da kyar na iya daurewa na kai ruwan shayi baki na saboda yadda na ji baki na yana min daci, bacin rai ne kawai a tattare dani da haushin Dr da nake ji.


A gefe guda kuma tsanar Meema ce ta ke yawo a raina saboda yadda take so ta yi ma rayuwa ta karan tsaye ta hanyar auren Dr.


Da yamma sai ga Dr ya dawo daga aiki da faraar shi ya tare ni.


Daurewa nayi na ari murmushi na tarbe shi duk da yadda nake jin zuciya ta na min zafi.


Ba na son in yi saurin yanke hukunci sai na samu hujjar da zan gabatar mishi da ita, nasan yanzu in na mishi maganar zai iya musa min akan cewa ni ce nake zargin haka.


Haka na daure na mishi duk abin da ya kamata, amma shi kanshi ya fahimci akwai abin da yake damuna da har sai da ya tambaye ni.


Nunar mishi nayi da ba abin da yake damu na, kawai dai ina ji na so weak ne.


Ranar na taki sa'a Dr bai fita ba, sai da ya d'auki kusan two weeks bai fita da daddare ba.



Wata Ranar Talata Dr ya dawo aiki da wuri, ranar na ji sun yi waya da Momi, ban san dai maganar da suke yi ba, na ji dai yana ce mata bai samun lokaci ne amma in ya samu lokaci zai je.


Da daddare wani irin bak'in ciki ne ya kama ni da wani irin kishin Dr da hakan ya nuna a fuska ta, tuni fuskata ta canza zuwa b'acin rai.


Yau na shirya ma tunkarar Dr mu yi wacce za muyi dashi, ba zan juri d'aukar rainin hankalin da yake min.


Kusa dani ya zo ya zauna, in ban da k'amshi ba abin da ke tashi.


Jin zuciya ta nake tana tafarfasa, yanzu duk wannan kwalliya da wannan k'amshin duk Meema yayi ms wa.


"Zarah ba ri in je gidan su Mema mu gaisa da su Dad, kwana biyu ban samu time na je ba" cewar Dr.


Lallai yau na tabbatar da Dr ya maida ni k'aramar Yarinya mara wayau wacce ba tasan me duniya ke ciki, amma zan nuna mishi na wuce a raina min hankali, nasan me Duniya ke ciki.


Cikin d'aura fuska na ce " Za ka gaida su Dadi ko za ka ga Meema".


Murmushi yayi kana ya ce "In ban da abin ki Zarah, tun da gidan su zani kin san dole mu had'u da Meema".


Mik'e wa yayi had'e da fad'in " Sai na dawo, i will not take long time".


Ya kusa kai wa bakin k'ofa nayi saurin mik'ewa na sha gaban shi, fuskar nan tawa ba fara'a a cikin ta.


Mamaki ne ya kama Dr ganin yanda na zo na tsaya a gaban shi ya ce "ya aka yi ne Zarah, zan fita kin zo kin tare min hanya".


" Dr ban yarda da fitar nan da za ka yi ba, saboda haka ka fasa fitar nan da za kayi" na fad'a cikin d'aure fuska.


"What do you mean Zarah da za ki ce in fasa fita?" Dr ya tambaye ni.


"Yanda ka ji na fad'a haka nake nufi Dr" na fad'a.


"Saboda me ba zan fita ba?" Dr ya sake tambaya ta.


Kai na tsaye na ce "Saboda na gaji da yawo da hankalin da kake min da kuma mayar dani yarinya da kake yi wacce ba tasan abin da duniyar ke ciki ba".


Ran Dr ne ya fara b'aci da yanda na ke mishi magana, dan haka shima cikin fad'a ya ce " Look Zarah, i don't want any trouble, bani hanya in wuce".


Ni ce na ce na ce "Dr I mean what i said, yau ina son gane matsayina a gurin ka".


Dr ne ya ce " Zarah wai me ya faru ne kike irin wannan maganar, pls ki ajiye wannan maganar da kike yi, ki bari in na je na dawo sai ki fad'a min me yake faruwa".


"Ka na d'auka maganar da nake yi da wasa nake yi, wlh Dr fitar ka gidan nan na nufin neman rashin zaman lafiya a gidan nan, ko kana sha ban san abin da yake faruwa tsakanin ka da Meema kamar yadda a kullum kake son b'oye min me ke tsakanin ku, a duk lokacin da na maka tambaya akan Meema amsa d'aya ka ke bani cewa ba soyayya a tsakanin ku, ka d'auke ta ne a matsayin k'anwa, duk abin da aka yi shi a rashin gaskiya duk daren dad'ewa sai ya bayyana, na gano cewa fitar daren da kake yi gurin Meema kake zuwa a matsayin unguwa da ka ce min kana zuwa, ni kuma ka bar ni in maka jiran gida, to Dr in ba son Meema ka ke yi ba amma ai kana shirin auren ta ko?" Na k'arasa maganar da tambayar Dr.


Mamaki ne ya kama Dr da har hakan ya nuna a fuskar shi.


Bi na kawai yake da kallo saboda mamakin jin maganganun da na fad'a mishi.


Jin bai bani amsa ta Ba yasa nayi murmushin takaici na ce "Me yasa kayi shiru Dr? kasan duk abin da na fad'a gaskiya ne, shi yasa ka kasa bud'e bakinka ka kare kan ka, Dr zan iya maka uzuri ko yafiya a duk abin da za ka min amma ba zan maka wannan alfarmar ba gurin yi min kishiya ba, kishiyar ma Meema wacce kasan ba ma shiri da ita".


Nasan yau Dr yayi mamakin maganganun da na fad'a mishi, saboda a ko yaushe yana ganin zan iya hak'uri a duk abin da ya min.


Cikin lallashi Dr ya ce " Zarah dole ki d'auki k'addara a yanda tazo domin auren Meema zan yi, abin da yasa ban fad'a mi ki ba saboda ba na so in d'aga miki hankali, amma tun da kin gano auren ta zan yi kin ga no need in k'ara b'oye mi ki".


Meema nasan kina so na, dole ne kuma ki yi kishi na, wannan auren zan yi shi ne dan tausayin Meema da kuma umarnin da Momi ta bani akan in auri Meema, pls Zarah am sorry".


Duk wannan maganganun da Dr yake yi kamar yana sa mashi yana caccaka min a cikin zuciya ta haka nake ji, wani irin b'acin rai na ke ji yana ziyarta ta a lokacin, wai ni Dr zai kalli ido na ya ce min zai auri Meema ne dan tausaya mata da yake yi da kuma umarni da Momin shi ta bashi akan ya auri Meema.


Wasu hawaye ne suka fara zubo min ba tsayawa.


Baki na ne ya kama rawa saboda kukan da yake son tawo min.


Kallon takaici nayi ma Dr kana na ce "Me...kake...nufi...da...wannan maganar...da...ka...fad'a...min..cewa...za...ka...auri Meema...saboda...tausayin...ta...da...umarnin...Mom...".


" Wannan Dalilin da na fad'a miki haka yake Zarah, apart from that ban da wani dalili da zai sa in auri Meema" Cewar Dr.


"Kenan yanzu Dr auran Meema za kayi kenan..." Na k'arasa maganar da fashewa da kuka.


"Ya zaman min dole in aure ta Zarah saboda umarni Mom ta bani" Dr ya fad'a.


"Dr dama can kayi niyar auren ta, da kake cewa saboda Mom za ka aure ta, idan ba ka yi niyya ba Momi za ta maka dole ne" na fad'a cikin shashshek'ar kuka.


Dr ne ya ce "Zarah ba zan iya musa wa Mom duk abin da ta buk'ace ni da nayi ba, shi yasa zan auri Meema".


Dr ba ka isa ka auri Meemba, in kuma ka ce sai ka aure ta sai dai ka zab'a ko ni ko Meema".


Tak'aitaccen murmushi Dr yayi ya ce " Zarah ke zab'i na ce, Meema kuma zabdamuwam ce, kin ga kenan dukkan ku zan zab'a".


Dr daman akwai ranar da za ta zo ka min irin wannan sakayyar, duk irin soyayyar da na nuna maka da halaccin da na maka amma sakayyar da za ka min kenan, a dalilin kishin ka da son da na ke maka yasa zan Shiga wani hali idan ka auri Meema amma shine Dr kake fad'a min dukkan mu za ka za'ba, Dr kana kallon yadda tun kafin auren ka na samu matsala da iyaye na da y'an uwa na akan auran ka da nake son yi duk da d'an uwa na da yake matuk'ar so na amma na zab'e ka na k'i auren shi, a dalilin auren ka na shiga damuwa duk na jure saboda ina tunanin in na aure ka za ka maye min gurbi da farin cikin da na rasa a lokacin za ka kuma rik'e ni amana da yarda, ashe ni ce nake nawa wautar ban sani ba, sai gashi ka nuna min duk ba zan sami hakan a wajen ka ba" na k'arasa maganar da k'ara sautin kuka na.


Zarah ba zan biye miki ba saboda ina son ki sai in k'i yi ma Momi biyayya?, da kike cewa kin zab'e ni akan d'an uwan ki ina ce saboda son da kike min ne, Zarah ni ban ce kar ki yi ma iyayen ki biyayya a kaina ba, nasan dai na ce ki nemar mana mafita akan yadda za mu mallaki junan mu, nasan tabbas Zarah kin nuna min so da ba kowace mace ba ce za ta iya nuna min ba tun da har kika zab'i farin ciki na akan ki bi umarnin iyayen ki, tabbas duk wacce tayi haka ta zama jaruma a soyayya, shi yasa nima ba zan yi irin kuskuren ki ba Zarah, dan haka ne ma yasa zan ma Momi biyayya in auri Meema domin yi wa iyaye biyayya nasa mutum ya samu farin ciki a rayuwar sa da ci gaban sa".


Ji nayi kukan da na ke yi ya tsaya cak sakamakon maganganun da Dr ya fad'a min.


jijiyoyin jiki na ke na ji sun daina aiki, jiki na yayi wani irin sanyi wanda ba na jin zan iya wani k'wak'k'waran motsi a gurin, ko idona na kasa motsa shi.


Wani abu ne na ji ya tokare min makoshi.


Yau ni Dr yake wa jirwaye mai kamar wanka akan k'in bin umarnin su Abbu da ban da ban yi ba duk da a dalilin shi yasa na k'i auran Yaya Faruk d'in da kuma shawarar shi da na bi dan in ga na mallake shi a matsayin miji, sai gashi wai yau ni Dr yake goranta mawa akan ban yi ma su Abbu biyayya ba, ban tab'a zaton Dr zai min wannan maganar ba, sai gashi yau a dalilin auren Meema Dr ya goranta min, ta yaya zanyi farin ciki da wannan auren da zai yi?


Ko ina a jiki na rawa yake yi, durk'ushewa nayi a gurin na fashe da wani matsanancin kuka.


Cikin kuka na ce "Dr na gode da tunasar dani abin da na manta a baya, wannan maganar da ka min ta sa na d'auki wani darasi na rayuwa, hakan da ka fad'a min yasa na gane kuskuren da nayi a baya, nasan ba komai ya ja min haka ba illah Makauniyar Soyayya da na nuna maka wanda daman irin ta take jawo wa mutum danasani, yau ni Dr kake goranta ma wa akan son da na nuna maka, na gode Dr..." Na k'arasa maganar cikin shak'ewar murya sakamakon kukan da ya tokare min a mak'oshi".


Da k'yar na iya tashi na ja k'afa ta saboda nauyin da k'afa ta tayi min.


Ina shiga d'aki na zauna a k'asan rug na saki wani kuka mai ban tausayi.


Jin kaina nake yi kamar zai tsage saboda ciwon da yake min.


Ban San tsawon lokacin da na d'auka ba a zaune ina kuka.


Maganganun da Dr ya fad'a min su suke min yawo a k'wak'walwata.


Sai a yanzu na gano kuskuren da nayi a baya wanda a da ban tab'a hango zai zaman min k'alubale ba, sai a yanzu na gano kuskuren da na tafka a baya da ban bi abin da su Ummu da Abbu da sauran mutane suke hango min ba.


"Me ya hana ni yi musu biyayya in auri yaya Faruk ko sa da k'in shi zai iya ajalina?".


"Me yasa ban faranta musu ransu ba a lokacin da suka buk'aci in musu abin da suke so duk da nasan ba za su tab'a zab'a min abin da zai cutar dani".


"Me yasa duk son da iyaye na suka nuna min nima ban yi k'ok'ari na faranta musu da abin da suke so ba?".


Duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan ba ni da buk'atar amsan su dan nayi wannan tunanin ne a lokacin da yake neman k'ure min.


Nasan duk wannan misunderstanding din da muke samu da Dr har da rashin d'aukar magar su Abbu ya jawo min da hakk'in Yaya Faruk da ya nuna min soyayya ta gaskiya amma na k'i auren shi.


Gashi yanzu ina fuskantar k'alubale a zamantakewar mu da Dr, ya kuma zaman min dole in yi hak'uri da duk abin da zai min ko zai fad'a min tun da ni na ce na ji na gani.


Wannan abin da Dr ya min ya dasa jin haushin shi, na kuma sa ma raina a shirye nake da fuskantar duk wani hukunci sa da zai yanke min in dai akan maganar auren Meema ne, ba zan bari ya auri Meema ba, in kuwa har ya ce sai ya aure ta to hakan na nufin zaman lafiya a tsakanin mu ya k'are.


Dole gobe Dr ya tsaya mu tsayar da mafita a tsakanin mu.


Ranar nayi kukan da na dad'e ban yi irin shi ba.


Ko sa da na kwanta ban yi baccin dad'i ba.


Washegari da ciwon kai na tashi, gashi ba ni da magani a side d'ina, first aid box yana side d'in Dr.


A yadda nake jin zuciya ta game da Dr ba na jin zan iya zuwa side d'in shi in d'auki magani in sha.


Haka na ci gaba da kwanciya duk da ba bacci nake yi ba.


Sai da na d'auki lokaci a kwance kana na tashi naje na dama kunun gyad'a na sha.


Wanka na shiga nayi na nemi simple dress na sa, ko mai ban tsaya shafawa ba na koma na kwanta.


Sallah kawai nake tashi na ke yi kana in koma in kwanta.


Sai wajen yamma na ji kaina ya min sauk'i, tashi na yi na gyara gidan sannan na je na d'aura simple food.


Ko da na gama girkin na ci, d'aki na koma na ci gaba tunani.


Gaba d'aya na rasa abin da yake min dad'i a raina.


Har zuwa dare ban k'ara fita falo ba.


Dr ne yayi sallama ya shigo d'akin.


Tun da ya shigo na zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake yi kamar a yanzu ne yake fad'a min zafafan kalamen da ya fad'a min a jiya.


Wasu hawaye ne naji suna k'ok'arin zubo min, saurin maida su nayi.


Kusa dani ya zo ya zauna yana kallo na.


Kau da kaina nayi na juya wani b'angaren saboda yadda naji raina na k'ara min zafi.


Shiru ne ya ratsa d'akin kafin Dr yayi k'ok'arin kau da shirun da cewa "Zarah am sorry".


Murmushin yak'e nayi na ce " Sorry for what Dr".


Cikin sanyin murya Dr ya ce "Zarah I know i have hurt you, is a mistake".


" Dr ni ba ka min komai ba, abin da ka fad'a min kamata yayi in gode maka saboda ka tunasar dani abin da na manta ne, saboda haka kar ka da mu" na fad'a.


Duk yadda Dr yaso in tsaya mu fahimci juna ban saurare shi ba, haka ya gaji da zama ya tashi ya tafi side d'in shi.


Tun daga wannan ranar muka fara samin sab'ani da Dr.


Sai da muka kai kwana goma a haka kullum sab'anin mu gaba yake yi, duk yadda na nuna b'acin raina akan Dr ya janye maganar auran Meema amma Dr ban ga alamar janyewar shi ba, hakan yasa zaman mu yak'i dad'i.


Duk na bi na canza kamar ba ni ba, ga rama da nayi a y'an kwanakin saboda rashin kwanciyar hankali.



Yau ranar ta kasance ranar weekend, Dr na gida bai je aiki ba, a yau na shirya ma fuskantar Dr dan nima na gaji da irin zaman da muke yi.


A side d'in shi na same shi yana danna waya.


Can nesa dashi na zauna ina fuskantar shi.


"Dr ina so in yi magana da kai ne" na fad'a kai tsaye.


"Ina jin ki" ya ba ni amsa a tak'aice.


Ni ce na ce "Ina so ka fad'a min me ka yayanke akan maganar da muka yi da kai akan Meema".


Tsayar da danna wayar yayi kana ya d'ago ya kalle ni.


"Amsar ba ta canza ba Zarah, zan auri Meema" cewar Dr.


Cikin b'acin rai na ce "Dr wai dole ne sai ka auri Meema? to sai dai ka zab'i zama da Meema ko ni dan ni ba zan tab'a zama da ita ba, ba ma Meema ba, ba na jin zan yarda ka auri wata ka kawo min ita a matsayin kishiya bayan ni ka gama cuta ta, tun da ka bani pills d'in abortion da family planning da kasa nayi, gashi nan har yanzu ban sake samun ciki ba, ka na sha ban da hankali ne zan k'yale ka kayi aure alhalin ni ka nakasta min rayuwa dan a yanzu ban da tabbacin zan haihu ko ba zan haihu ba, nufin ka kayi aure nan gaba ka bukaci haihuwa amaryar ka ta haifa maka yara ni ina nan a zaune, impossible! dole mu ci gaba da zama ni da kai a haka, maganar wai za kayi wa Momi biyayya ka ajiye ta a gefe dan nima kai ka ja min na k'i yi wa iyaye na abin da suke so akan in auri Yaya Faruk na k'i bin maganar su, saboda son da nake maka yasa nayi haka".


Shi ma cikin fad'a Dr ya ce " Zarah ni kike fad'a ma wannan maganar".


A lokacin ina jin zan iya fad'a ma Dr duk maganar da ta fito daga baki na saboda yadda nake cikin b'acin rai.


Ba tare da tsoro ko shakka ba na ce "Kai na ke fad'a ma wa Dr, a abin da na fad'a maka ka fad'a min wanda ba gaskiya ba".


Wani banzan Kallo Dr ya jefo min kana ya ce " Tun da kin ce ni na jawo kika k'i yi ma iyayen ki biyayya ko in kawo miki hanya mafi sauk'i ne da za ki je ki auri d'an uwanki dan ki yi musu biyayya".


Kai tsaye na ce "Za ka iya yin hakan Dr dan nima a yanzu zan so in share ma iyaye na hawayen da ban share musu a baya ba, nima zan so in gyara kuskuren da nayi a baya dan sa iyaye na farin ciki da ban sa su a baya ba da kuma guje ma gorin da ka min".


Wani murmushi ya yi iya leb'e da na rasa ma'anar murmushi sannan ya ce " Zarah kar ki yi saurin cewa haka, nasan duk hukuncin da zan yanke ke za ki fi shiga wani hali dan son da kike min ba na wasa ba ne, kar ki zo daga baya kina danasani akan haka ".


Murmushi mai cin rai nayi kana na ce " Dr duk hukuncin da za ka yanke min zan jura tun da dai nasan ba zan rasa raina ba" na fad'a.


"Haka ki ka fad'a ko?" Dr ya watso min tambaya.


Ba tare da nazari ko tunanin wani hukunci Dr zai yanke min ba na ce "of course haka na ce".


"Ki je Zarah na sake ki saki d'aya..." Dr ya fad'a.


Wani irin fad'uwar gaba ne na ji ya ziyarce ni a lokacin, k'irji na ne ke faman harba wa kamar zai fito, tun da Dr ya fad'a min kalmar saki na rasa a wace duniyar yake, ban tab'a tunanin wannan hukuncin Dr zai yanke min ba, a yanzu ina ganin lokaci yayi da zan hak'ura da Dr ko da shine autan maza, a yanzu na sa ma kaina juriya da hak'uri da Dr tun da zaman mu ya k'are dashi, yanzu babu wani sauran wata alak'a a tsakanin mu.


Da k'yar na had'o kalmomi na fad'a ma Dr saboda juwar da ke naman d'auka ta.


"Na gode da hallacin ka Dr, sakamakon *Makauniyar soyayyar* da na nuna maka ne ya jawo min haka da rashin d'aukar magana iyaye na ya jawo min, nasan na cancanci fiye da haka, mutane sun sha fad'a min illar makauniyar soyayyar da nake maka amma ban ji shawarar du ba saboda a lokacin ido na ya rufe da soyayyar ka sai a yanzu na gano illar son da na nuna maka dan shi ya sa ni a halin da nake ciki a yau, a yau na d'auki babban darasi a gurin ka na rayuwa, kuskuren da na aikata ba zan sake maimaita irin shi ba, sai dai kafin in tafi zan fad'a maka wata magana, duk wanda ya zalunci wani a zamantakewar mu Allah ya saka mishi".


Ina gama fad'ar haka naje na fara had'a kaya na a trolik, sai a lokacin kuka yazo min mai k'arfi.


dressing Mirrow na zauna na ci kuka na ba mai rarrashi na.


Da k'yar na samu nayi controlling d'in kuka na ya tsaya saboda ba na fatan ci gaba da zama a gidan Dr, yanzu ganin gidan nake yi yamin bak'i, ji nake kamar a kan k'aya nake.



Jiki a sanyaye na tashi na d'auki hijab na saka kana na jawo trolik d'in na fito.


Ina fitowa wasu hawaye suka zubo min, saurin goge hawaye na nayi na nufi hanyar fita.


Sai a lokacin na lura da Dr da yake zaune a falon.


Saurin fita nayi daga falon na fita daga gidan.


Ko motar da Dr ya siya min ban tsaya d'auka ba dan ba ta da amfani a gurin na.


Kasancewar unguwar ta masu kud'i ce yasa ba wasu mutane a layin sai d'aid'aiku dake wuce a motar su, ga kuma yamma da tayi.


K'arasowa bakin titi nayi na tsaya ko zan yi sa'a na samu abin hawa.


Sai a lokacin sharad'in Abbu ya fad'a min a rai akan duk matsalar da za ta fad'a ni da Dr kar in tunkaro shi da maganar.


Yanzu ina zani? Na tambayi kaina.


Sai a yanzu na k'ara jin danasani ya k'ara shiga ta.


"Wayyo Allah! Na ga ta kaina".


Na d'an jima a tsaye kafin wata bak'ar mota ta tsaya a gaba na.


Bud'e motar a kayi kana ya sakko da k'afafuwan shi waje sannan ya fito daga motar.


Wanda na gani ya fito a motar ne yasa na ji kamar in ruga da gudu.






_To ni kaina 'yar mutan paki zan so sanin waye a cikin motar dan ban da wannan amsar_.

*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



www.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa writers Association






_Masu kira na a waya ina Godiva, ba ni da abin ce muku sai dai fatan alkhairi, Sumayya Bala kema ina Godiva da yabawar ki gare ni_.

_Wannan shafin na Baku shi kyauta ku yi yadda kuke so dashi_.





91-92


Yaya Faruk ne cikin wani tsadadden sky blue d’in yadi, daga ganin yadin kasan mai tsada ne.


Gani nayi ya k’ara haske da k’iba, kana kallon shi kasan yana cikin kwanciyar hankali.


Rabo na da ganin shi tun ran bud’ar kan su Anisa da muka had’u dashi a gidan mu, tun daga wannan had’uwar ba mu sake had’uwa dashi ba, sai yau da muka sake had’uwa dashi.


Jikin motar shi ya jingina ya hard’e hannun shi.


Ji nake yi kamar k’asa ta tsage in shige dan ban san me zan ce ma yaya Faruk idan ya tambaye ni inda zani da akwati.


A takure nake da tsayuwar yaya Faruk a gurin.


Nasan in ba ni na mishi magana ba bazai min ba dan haka na ce "Ina wuni yaya Faruk".


"Lafiya" ya amsa min a tak’aice.


Shiru yaya Faruk yayi kamar ba zai k’ara min magana ba kana ya ce min "Fatima ina zaki da yamman nan da akwati a hannun ki, na zo wucewa ce na ganki a tsaye, daga gidan Aminu nake".


Sunkuyar da kaina nayi na rasa amsar da zan bashi dan gani nake yi ban da amsar tambayar da ya min.


"Yanzu ina zan ce ma yaya Faruk zani bayan ni kaina ban san in da zani ba?" na

Please Login or Register in order to submit comment