Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momi ta tambaye shi aiki kana suka ci gaba da hira.


Cikin hirar ne Momi ta canza hirar da cewa "Sadik wai b aka da lafiya ne?".


Amsa mata yayi da cewa "Me kika gani Momi".


Cikin kulawa Momi ta ce "Sadik na ga ka canza ne ka rame, sai ka ce wanda yayi jinya, in da abin da yake damunka ka fad’a min".


Murmushi yayi kana ya ce "Momi ba abin da yake damu na, in ma dai akwai abin da yake damu na bai wuce matsala ta da Meema ba, har yanzu zaman mu ya k’i zama normal da ita, sai tayi kamar ta canza sai ta dawo da halayen ta, gaskiya Momi na gaji da halayen Meema, sai a yanzu na ke k’ara danasanin rabuwa ta da Zarah dan ita ba haka take min ba, tana k’ok’arin duk abin da tasan zai sa ni farin ciki da kiyaye abin da ba na so sab’anin Meema da ban isa da ita ba, kullum ita tana nuna min tana da right na kan ta".


Nisawa Momi tayi bayan ta gama jin bayanin Dr kana ta d’aura da cewa "Ka ci gaba da hak’uri Sadik, nasan Meema ba ta kyauta maka akan wasu abubuwa da take yi, amma idan ka ci gaba da hak’uri da ita da nusar da ita nasan za ta gyara tun da tana son ka, idan ba ta gyara ba zan tsawatar mata, mace sai da lallab’awa da lallashi ka ji ko Sadik".


"To Momi zan yi yanda kike so amma in ta kai ni k’arshe zan ba ta mamaki" Dr ya fad’a.


Shiru Momi ta yi ba ta k’ara cewa komai ba dan ita kanta ta gaji da k’arar da Dr yake kawowa akan Meema.


Ci gaba da lallashin shi Momi tayi tare da nusar dashi akan kar yasa damuwa akan shi.


Ya ji dad’in shawarwarin da Momi ta bashi dan ya samu relief akan damuwar da Meema take sa mai.


Sai da ya ci abinci a gidan kana ya tafi dan yasan ba lallai ba ne in Meema tayi girki dan sai ta gadama take yi.


Ko san da ya koma gida samun ta yayi a side d’inta tana hakimce yayin da music ke tashi a home theatre dake jone a wajen Tv d’in.


Tun da ya shigo da sallama ta amsa mishi ciki-ciki kana ta d’auke kanta daga gurin shi ta ci gaba da bin wak’ar da ake yi.


Mamaki ne ya cika shi na irin halin Meema yanda ba tasan ta tarbi miji in ya dawo ba ko ta amsar masa jaka ko wani abu in yana rik’e dashi a lokacin da ya dawo, sai dai in taso ne za tayi hugging d’in shin a welcoming d’in shi.


Ganin ba kula shi za tayi ba yasa ya ce "Meema ba ki ganni ba ne".


Juyowa tayi kana ta ce "Ni ko na gan ka yaya Sadik tun da ga ka a zaune kusa da ni".


"Amma dan iskanci kin fi k’arfin ki min sannu da zuwa ko ki tarbe ni" cewar Dr.


"Sorry yaya Sadik tun da ni ba wuya na yi laifi" Meema ta fad’a a yatsine.


Jan tsaki Dr yayi ya mik’e ya bar gurin ba tare da ya k’ara cewa komai ba dan in da sabo ya saba da halin Meema.


Bin shi tayi da kallo ta ja kana k’aramin tsaki kana ta ci gaba da bin wak’ar ba tare da wata damuwa ba.


Washe gari ba laifi san da Dr ya dawo daga aiki ya samu tarba da kulawa a gurin Meema.


Sai da ta raka shi har d’akin shi kana ta had’a mishi ruwan wanka sannan ta fito falo ta kunna wata wak’ar indian tana tik’ar rawa kamar a k’asar indian take.


Bayan ya fito daga wanka ne ya nemi simple dress ya sa kana ya fito falo.


Tsayawa yayi kawai yayi yana kallon ta ganin yanda take tafiyar da rawar kamar dan ita aka yi wak’ar.


Ya kai kusan minti biyar a tsaye ba tare da Meema tasan da tsayuwar Dr a gurin ba.


Extension wire ya je ya kashe kana cikin d’aurewar fuska y ace "Wai ke Meema wannan rawar da wak’e-wak’en da kike yi ba ya isar ki ne, atleast ya kamata a ce komai yana da time d’in shi".


Turo baki tayi kana ta ce "Haba yaya Sadik ya ina cikin rawa na za ka zo ka kashe min, kasan I have the right to make myself entertain, so ni ban ga aibu ba a abin da nayi da kake complain".


Yasan in ya ci gaba da biye ma Meema ranshi ne zai b’aci dan Meema tayi nisa a koyi da rayuwar turawa dan haka ya ce "Ni Meema ba na ce kin yi laifi ba ne amma ya kamata ki rage jin wak’e-wak’en nan dan ba abin da yake jawowa sai shaid’anu a cikin gida, ina fatan kin fahimce ni".


Kusa dashi ta zo ta zauna ta ce "Na fahimta".


Amma a cikin ran ta ba k’aramin haushin kashe mata wakar da take ji tayi ba.


"Meema ina abinci na yunwa na ke ji" Dr ya fad’a.


D’aure fuska tayi dan tasan yanzu nan za su sami matsala da Dr a rashin girkin da ba tayi ba ta ce "Ban yi girki ba yaya Sadik".


"Saboda me yasa ba ki yi girkin ba" Dr ya tambaye ta.


Meema ta amsa masa da cewa "Ina sha za ka biya gidan Momi ka ci ko restaurant ka ci shi yasa ban dafa ba, infact kasan ni girki ba favourite d’ina ba ne".


Cikin b’acin rai ya ce "Wannan shine reason d’in ki da ba ki yi girki ba, kullum ni kuma sai in tafi gurin Momi ko restaurant in ci abinci alhalin ina da mata, impossible! Meema ina d’aga miki k’afa amma ba ki sani ba, sau nawa nake miki magana akan rashin yin girkin ki amma kin k’i canza wa, sai dai in na dawo in nemi drinks ko tea in sha idan ba ki yi girki ba saboda wata cutar ta kama ni, in ke ba ki damu da lafiyar ki ba ni na damu da tawa, Meema you better Know what you a doing beffer I show you the other side of me".


Yana gama fad’ar haka ya mik’e ya shiga d’aki ya d’akko key d’in motar shi ya bar gidan.


Ita kuwa Meema ba abin da ya dame ta akan fushin da Dr yayi dan tasa ma ranta cewa Dr ba zai matsa mata ba akan girki ba, ta aure shi ne dan tana son shi ba wai dan tazo ta maida kan ta baiwa a cikin gidan ba.


Haka dai zaman gidan Dr ya ci gaba da gudana yau fari gobe tsumma.




A b’ngare na kuwa ba ni da wata sauran damuwa dan ina k’ok’arin ganin na kiyaye duk wani tunani da zai dame ni.


Cikin d’an lokaci sai gashi na canza na yi fresh ga kuma aiki na da nake zuwa.


Haka lokaci ya ci gaba da tafiya.
A cikin haka ne Nana ta haifi d’iyar ta mace.


Tun da na ji labarin haihuwar Nana na k’ara tausaya ma kaina dan ni ban san lokacin da zan mallaki d’an kaina ba tun da yanzu ban a tare da Dr ga kuma planning d’in da nayi wanda ban san ko ta dalilin haka na sami matsala ba.


A na gobe suna su Ummu da Anty Jidderh za su tafi Abuja dan haka nima na nemi excuse gurin aiki na muka tafi tare.


Ita Anisa ta riga mu tafiya dan ita kwanan ta biyu da tafiya kenan.


Tun da muka isa Abuja nayi arba da yarinyar na ji yarinya ta shiga raina.


Ji na ke yi kamar ni na haife ta saboda son ta da ya shigar min rai.


Yanzu duk wata haihuwar da za a yi a family sai na ji ina ma ni ce aka zo yi min murnar haihuwa.


Nasan wannan tunanin da nake yi yana da alak’a da son ganin d’an kaina ganin yanda lokaci ke tafiya.


Nasan yanzu yanda nake nemn kusan shekara da rabuwa ta da Dr ba zai yiwu in ci gaba da zama a haka ba, Abbu da Ummu nasan sun zuba min ido su ga iya gudun ruwa na.


Ni kaina yanzu na ajiye maganar Dr a gefe tun da gashi ina neman shekara d'aya ba tare da yazo yayi biko na ba akan in koma gidan shi ni ma kuma ban damu da hakan ba dan nasan na fuskanci k’alubale a zaman mu.


Fata na yanzu shine Allah ya zab’a min abin da yafi zama alkhairi a gare nib a wai son raina ba dan nag a illar Makauniyar Soyayya.


Tun da muka zo na tare a d’akin Nana rik’e da babyn da aka haifa, sai dai in an zo barka ko za a ba babyn nono zan ba da ita.


Su Anisa da Anry Jidderh sai tsokana ta suke yi wai in yi aure tun da baby nake so.


Murmushi kawai nayi kawai nayi ba tare da nayi magana bad an ni a yanzu ban san wanda zan tsayar a matsayin miji na ba.


Ranar Suna yarinya taci sunan Momi Rukaiyya ana kiran ta da Khairat.


An yi k’ayatacciyar walima tare da kayan rabo na alfarma.


Haka taron sunan ya watse sai dai mu ce Allah ya raya Khairat.


Washe gari ta kasance ranar Asabar, a ranar ne su Ummu da Anty Jidderh da Anisa suka koma Kaduna.


Ni kuma na ce sai ran litinin zan koma dan excuse d’in da na nema har da ranar litinin na nemi excuse.


Yanda yaya Faruk na ga yana kula da Nana da khairat hakan ya k’ara burge ni, ko yana gurin aiki haka zai dinga kiran ta a waya yana tambayar ta ko akwai abin da take so ko in zai fita aikin.


Idan yana gida kuwa baby na hannun shi.


A kwana biyun da nayi wani tunani ne ya d’arsun min a zuciya ta wanda nasan ba abu ne mai yuwuwa ba.


Tunanin da na fara sa ma raina shine ina ma yaya Faruk zai aure ni ya ajiye abin da na mi shi.


Sai a yanzu nasan yaya Faruk shine irin mijin da ya dace in aura wanda zan samu dukkan kulawa kamar yanda yake ba Nana kulawa.


Nasan in har na auri yaya Faruk nayi dace sannan nasan zan samu soyayyar shi kamar yanda ya nuna min a farko.


Ni kaina a yanzu zan iya cewa ina jin yaya Faruk a raina tare da tunanin shi wanda ni kaina zan iya cewa son yaya Faruk ne ya fara shiga na a lokacin da ban yi tsammani ba.


Sai dai yanzu abin da ya fi damuna shine yanda har yanzu yaya Faruk ya k’i sakar min fuskan shi bare mu zaun mu yi hira da shi irin na ya da k’anwar shi.


Ran litinin na baro Abuja na dawo Kaduna tare da kewar Khairat a raina.




Shi kuwa Dr damuwar da ya sa ma kan shi ya sa jinin shi yau, ko da yayi ma kan shi gwaji ya tabbatar da BP d’in shi ya hau amma hakan bai sa ya rage tunanin da yake yi ba.


Yanzu tunanin da Dr yake yi shine yanda zai iya tunkara ta ya bani hak’uri in amince dashi ga wani irin so na da yake d’awainiya dashi wanda bai tab’a min irin shi ba sai a yanzu. yanzu lamarin Meema ya fara isar shi dan haka ba ko wane abu ba ne yake biye mata sai dai ya zuba ma ta ido ya ga iya gudun ruwan ta, sai dai in ta kai shi k’arshe ne yake tsawatar mata.


Yanzu damuwar da yake ciki ta shafi har b’angaren aikin shi domin yawan patient d’in da yake duba wa a da a yanzu ba ya duba mutane da yawa, har gurin aikin abokan aikin shi sun san Dr ya canza a yanayin aikin shi saboda yanda a ka san shi da jajircewa da nuna k’ok’arin shi ta b’angaren aiki.



Yau Meema ce zaune a falo tana kallon wani American film a lokaci d’aya tana pressing d’in wayar ta.


Knocking d’in da aka yi bai sa ta tashi ta bud’e k’ofar ba sai ma ci gaba da kallon ta da take yi.


Sai da aka yi knocking kusan uku sannan Meema ta tashi ta je ta bud’e k’ofar.


Ganin su Hanan ne da Farida yasa ta d’an saki fuskarta ta ba su guri suka shigo.


Bayan sun zauna ne Farida ta gaishe da Meema ta amsa ba yabo ba fallasa yayin da Hanan ta kau da kan ta ba tare da sun gaisa da Meema ba dan yanzu ba wani shiri su ke yi da Meeman ba.


Sun kai minti goma a zaune ba tare da Meema ta kula su ba ko ta tashi ta d'akko musu abin motsa baki.


Hanan Wanda ran ta ya fara b'aci da shariyar da Meema ta musu ta ce "Meema yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan".


Juyo da kallon ta tayi ga Hanan kana ta watsa mata harara ta ce " Me nayi da za ki ce na kyauta".


Hanan ce ta ce "Yanzu mu zo gurin ki amma ki yi banza da mu kamar ba ki san da zaman mu a gurin ba, ina ganin ko da ba ki san mu ba muka zo gidan ki bai kamata ki mana irin wannan tarbar ba".


Cikin fad'a Meema ta ce "Me kike so in muku Hanan, mun gaisa da Farida ke ko darajar gaisuwa ban samu a gurin ki ba amma kin fara k'orafi, Goya ku kike so in yi dan in nuna nayi farin cikin ganin ku ko me kike so in yi".


Hanan ita ma cikin b'acin rai ta ce "Ban buk'aci Hakan a gare ki ba amma ki sani ba zan juri wulak'anci ba dan ke kan ki shaida ce akan haka".


" To ki d'auki mataki mana Hanan ina ganin ai zai fi akan wannan surutun da kike yi, kin san dai ban son hayaniya" cewar Meema.


"Ba yanzu zan d'auki mataki ba sai lokacin d'aukan matakin yayi" Hanan ta fad'a.


Duk wannan maganganun da su Meema ke yi Farida ba ta tsoma bakin ta ba sai ma tab'e bakin ta da tayi ta ci gaba da danna wayar ta.


Tasan a cikin su ba Wanda za ta ba wa hak'uri ya hak'ura hasalima sun fi kusa tun da k'awaye ne.


Sai da ta ga hayaniyar su na ci gaba sannan ta sa baki.


Da k'yar ta samu suka yi shiru.


Haka falon ya d'auki shiru kamar ba mutane a ciki.


Sun kai kusan minti sha biyar a zaune ba tare da Meema ta tashi ta d'akko musu abin sha ba, hakan yasa Farida ta tashi ta d'akko musu drinks a fridge.

Ko kallon in da suke Meema ba ta sake yi ba.


Sun kai kusan awa d'aya a zaune amma Meema ba ta da niyyar tashi ta kawo musu abinci dan haka cikin wasa Farida ta ce "Anty Meema yunwa fa na ke ji, me zan samu ne".


"kitchen d'in ai ba bak'on ki ba ne, za ki iya tashi ki dafa, a yanzu ba Wanda ya isa ya tashe ni in je in muku girki dan ni ba baiwa ba ce, na ga kuma a gidan ba son yin girkin ku ke yi ba" Meema ta fad'a kai tsaye.


Cikin Mamaki da amsar da Meema ta ba su ta ce "Anty Meema me ya kawo wannan maganar, daga wasa sai ki fad'a min wannan maganar, Allah ya baki hak'uri".


Hanan ce ta k'arb'i maganar da cewa "For what reason za ki ba ta hak'uri bayan ita yakamata ta baki hak'uri akan maganganun da ta fad'a, da kike cewa ba ma girki amma ai ke kan ki kin san mun fi ki dan ba abincin da ba za mu iya dafawa ba, kin ga kenan mun fi ki".


Nan Meema da Hanan suka ci gaba da musayar yawu.


Da k'yar Farida ta samu Hanan ta tashi suka tafi gida.


Ko da su ka koma gida Hanan ta fad'a ma Momi abin da ta musu.


Ran Momi ya b'aci jin wulak'ancin da Meema ta ma su Hanan sai dai tayi k'ok'arin danne fushin ta dan ba ta son ta sa bakin ta tun da tsakanin su da su Hanan ne.


Ita kan ta Momi sai yanzu ta gano abin da yasa Momi ke kauce ma auran Meema lokacin da ta ce ya aure ta.


Yanzu ga shi nan sai matsaloli ke kunno kai.


Fatan ta dai komai ya daidaita ya dawo normal.


Ni kuwa ta b'angarena na shiga tsaka mai wuya a tunanin da na d'aura ma kaina wanda na ke ganin kamar iska ce ke wahalar da mai kayan kara dan nasan abu ne mai wahala Yaya Faruk ya dawo da ni rayuwar shi dan ni kaina nasan ban kyauta mishi ba da kuma kunya in iya tunkarar shi in ce yanzu Ina son shi ya aure ni.


Wani lokacin ji nake yi kamar In kira shi in fad'a mishi Sirrin Zuciya ta ko da ba zai yi marhabin da magana ta ba.


Nasan fad'an maganar zai sa in samu sauk'i a halin da na tsinci kaina a ciki.


Wannan shine tunanin da a yanzu ya fi tsaya min a rai.



Yau ranar ta kasance ranar lahadi ba ni da aiki.


Zaune na ke a falo Ina kallon wani Nigerian series mai suna my kids & I.


Muryar Wanda na ji yayi sallama yasa nayi saurin d'agowa dan ko a ina na ke muryar ba za ta b'ace min ba.


Yaya Faruk ne cikin wani tsadadden yadi kalar sararin samaniya.


Amsa mi shi nayi kana na k'ara yalwata fuska ta da murmushi.


Nesa da ni ya nemi guri ya zauna.


Gaishe shi nayi ya amsa min ba yabo ba fallasa.


Tambayar shi nayi ya Nana da Khairat ya amsa min da su na nan lafiya.


A raina na ce ko yaushe Yaya Faruk ya shigo Kaduna?


Gaba na ne na ji yana fad'uwa saboda na sa ma raina cewa yau zan tunkari Yaya Faruk da maganar in ji ra'ayin shi a kaina.


Wani b'angare na zuciya ta kuwa kwab'a ta take yi akan in bar maganar a raina dan zan iya fuskantar b'acin rai a gurin Yaya Faruk ko ya wofintar da buk'ata ta a gurin shi.


Katse min tunani na yayi da cewa "Fatima ina Ummu".


" Tana d'akin ta" na fad'a.


Mik'ewa tsaye yayi ya nufi d'akin Ummu yayin da na bi shi da kallo.


Tashi nayi na fita na tsaya in da Yaya Faruk yayi parking d'in motar shi dan in jira fitowar shi.


Saman motar na hau ina ci gaba da tattauna yanda zan tunkari Yaya Faruk da wannan maganar kai tsaye.


Na d'an jima a zaune kana Yaya Faruk ya fito ya nufi in da yayi parking d'in motar shi.


Da sauri na sakko na tsaya ina jiran k'arasowar shi.


Kallo ya bi ni dashi gani na a tsaye a gurin motar shi.


"Lafiya Fatima na ga kin tsaya a nan, ko akwai abin da kike buk'ata ne" yaya Faruk ya fad'a.


"Lafiya lau Yaya Faruk" na amsa mi shi.


Bai k'ara ce min komai ba ya bud'e motar shi.


Ganin tafiya zai yi yasa nayi saurin cewa "Yaya Faruk dan Allah ka ban 10 min ina son mu yi magana ne".


D'aure fuskar shi yayi kana ya rufe motar ya zuba min ido yana kallo na.


" Ina jin ki, amma ki tabbata maganar da za ki fad'a min ba zai wuce lokacin da ki ka d'iba ba saboda ina da abin yi".


Sunkuyar da kaina nayi na rasa ta in da zan fara maganar.


Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin Yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "That means kenan ba ki da abin cewa tun da kika yi shiru".


Cikin kame-kame na ce " Yaya Faruk daman ina so in k'ara ba ka hak'uri akan abin da ya faru a baya, nasan ban kyauta maka ba, amma a yanzu na gano kuskure na, dan Allah Yaya Faruk ka yafe min".


Kallon mamaki ya bi ni dashi kana ya ce "Fatima in dai akan wannan maganar ce ta riga ta wuce a gurina tun da na ce na yafe miki sannan ni na ki min laifi ba tun da kin zab'i abin da zuciyar ki take so ne, in ma laifi ne bai wuce yanda tun farko ba ki fito kin fad'a min gaskiyar abin da ke zuciyar ki game da ni kika dinga b'ata min lokaci kina yaudara ta, beside ni komai ya wuce a guri na".


" Na gode Yaya Faruk" na fad'a cikin sunkuyar da kai.


"Za ki iya koma wa cikin" Yaya Faruk ya fad'a.


Ganin in dai na bar nan gurin ba tare da na fallasa ma Yaya Faruk abin da ke damuna ba dan haka na ce "Yaya Faruk...daman... so na ke yi...in nemi...alfarma...a...gurin ka....".


Yaya Faruk ya ce "Wace alfarma ce Fatima".


Shiru nayi ban ce komai ba ina fargabar fad'a mai.


" Kin yi shiru, wa ce alfarma ce kike nema a guri na, ki fad'a min in ji ko zan iya" cewar Yaya Faruk.



Cikin k'arfin gwiwa na ce "Yaya Faruk ina Neman alfarmar ka aure ni saboda ina son ka.........".






*Hmmmmmm Yau ake yin ta readers tsakanin Yaya Faruk da Fatima*.



*Wannan amsar na gurin Fatima da Yaya Faruk*.



*Ni kaina zan so in ji wni amsa Yaya Faruk zai ba ma Fatima*




*'Yar mutan Paki na mu ku fatan alkhairi*.
[10/8, 21:52] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽


www.maryamahmadpaki.blogspot.com


facebook: Kainuwa Writers Association






*TUNATARWA*:


*KADA MUBI HANYOYIN SHAIƊAN*



_Shaiɗan shine farkon wanda ya fara fifita kansa akan waninsa_.



_🌸Idan kaima ɗabi'arka/ki kenan to lallai kam kana/kina bin sahunsa a cikin mabiyansa_.



_🌸Ya Allah kayi mana tsari da shaiɗan da ayyuka na shaiɗanu kuma ka ƙara tabbatar da zukatanmu akan yi maka biyayya_.






101-102


Wani irin murmushi yaya Faruk yayi da na kasa fassara mai murmushin shi yake nufi.


Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba kana ya ce "Fatima ina so ki maimaita abin da kika fad’a min yanzu".


Kai tsaye na k’ara cewa "Yaya Faruk ina son ka".


Lumshe idon shi yayi ya bud’e kana yayi y’ar dariya ya ce "Yanzu Fatima tun da ki na so na ya za ayi kenan".


Cike da karsashi na ce "yaya Faruk so na ke yi ka amince da tayin soyayyar da na maka wanda na ke fatan ta kai mu ga yin aure, yaya Faruk kai ka dace da ka zama abokin rayuwa ta saboda halayen ka abin so ne ga duk wata y'a mace".


Tun da na ke maganar yaya Faruk murmushi ya k’i b’ace wa a fuskar shi, hakan yasa na d’auka zai amince da ni dan nasan har yanzu yaya Faruk yana so na, abin da na mi shi a baya ne zai sa ya danne so na a cikin zuciyar shi.


Lokaci d’aya yaya Faruk ya d’aure fuskar shi kamar ba shi ba ne ya gama sakin murmushi a yanzu.


"Fatima kin san abin da kike fad’a kuwa, ina tunanin ba kya cikin hankali ko kuma kina tunanin mafarki kike yi, in ma mafarki kike yi ya kamata ki farka daga nannauyar mafarkin da kike yi saboda wanda yake gaban ki a tsaye a yanzu Faruk ne d’an uwan ki a tsaye a gaban ki wanda a da kika guje ma auren shi kika ce ba shi kike so ba".


Jiki na ne ya fara yin sanyi jin maganar da yaya Faruk ya fad’a min amma duk da haka na sa ma kaina dauriya na ce "yaya Faruk nasan kaine a tsaye a gaba na, abin da na fad’a maka da gaske nake yi ba wasa ba, wannan maganar da na fad'a maka har cikin zuciya ta haka yake, yaya Faruk so na ke yi ka amince da ni mu yi aure".


Wata irin tsawa yaya Faruk ya daka min da tasa na firgita kana ya kalle ni ya ce "Fatima enough of this rubbish, lallai yau na tabbatar da ba ki da kunya da har ki ka iya tunkara ta da wannan maganar ba tare da kin ji shakkar fad'a min wannan maganar ba, ko da yake miye abin kunya a gurin ki tun da a da ma kika iya fad’a min ba ni kike so ba kina da wanda ki ke so, ki shiga hankalin ki kafin in dawo da ke hankalin ki".


Hawaye ne ya tarun min a idanu na dan jiki na ya fara ba ni cewa b azan samu nasara ba a gurin yaya Faruk.


Wata Zuciyar ta ce min kar ki yi saurin karaya ki ci gaba da bashi hak’uri har ya amince dake tun da akwai son ki a zuciyar sa.


"Yaya Faruk nasan na maka laifi

Please Login or Register in order to submit comment