Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaya Faruk in ranshi ya ‘baci zai iya yanke kowane hukunci dan samar ma kanshi mafita yasa ya zartar da hukunci, bai duba halin da zai shiga ba, Kalamen da ya yi amfani dasu wajen yi min magana shi ya bi duk sassan jiki na ya katse min kuzari na da nake tare dashi a wannan lokacin.

A lokacin wani irin tausayin yaya Faruk ne ya kama ni wanda ban san lokacin da hawaye ya fara sintiri a idanu na ba.

Ci gaba yayi da cewa "Fatima ina da power da zan iya auran ki in kuma koya miki so na ko da ba kya so, ba wai wannan abin da kika aikata ne yasa naji tsoro na hak’ura da auran ki, sai dan ni ba mai son shiga rayuwar wani ba ne, ina son ba wa mutum right d’in shi ne a matsayin shi na d’an adam, kin fad’a min wannan Dr ki ke so ban d’au hakan a komai ba, sai yanzu da kika d’auki matakin fara guduwa daga gaban iyayen ki, na ji tsoron a matsayin ki na ‘ya mace kar ki je ki aikata wani abin da bai dace ba duk a dalilin aure na da zaki ko bayan anyi aure na da ke ki je ku ci gaba da soyayyar ku kuna cin amana ta, kin ga kenan zan iya d’aukan ko wai mataki da ya zo min idan hakan ta kasance, hakan yasa na fasa auren ki, Fatima nayi niyar nuna miki kuskuren ki na yaudara ta da kika min, da tozarta ni da kika yi niyar yi a lokacin da bikin mu bai kai sati biyu ba kika tawo nan da niyar guje ma aure na, na so in nuna miki ba kowane namiji ne ake yaudarar shi a zauna lafiya ba, sai dai k’udurin da nake dashi na miki hukuncin na fasa dan ke ‘yar uwa tace, hannun ka ba zai ru’be ba ka yanke ka yar, shi yasa zan barki da halin ki".

Maganganun da yaya Faruk yayi amfani dasu wajen yi min magana sun min tsaurin da zuciya ta ba za ta iya amsar su ba, nasan maganganu ne yake fad’a min a k’aik’aice masu isar da sak’onnin da yake son isar wa wanda Hausawa ke cewa "kukan kurciya jawabi ne".

Wani irin kuka na saka a lokacin, in ban da shasshek’ar kuka na da ya cika d’akin ba abin da ke tashi.

Murmushin takaici yayi ya kalle ni ya ce "Fatima ba ki yi wa kan ki adalci ba da kike yin kuka alhalin ni ban miki wani abu ba, ina ganin in akwai wanda ya dace yayi kuka bai wuce ni ba saboda halin da kika sa ni a ciki, Fatima ni kukan zuciya nake yi wanda yafi na fili ciwo, ni a gani na murna ya kamata ki yi yau na cika miki burin kin a barin ki da wanda kike muradi".

Ni dai ba abin da nake yi sai ci gaba da kuka na da nake yi, wannan maganganun da yaya Faruk yake fad’a min zai fi min sauk’i akan yasa bulala ya zane da wannan maganganun da yake fad’a min.

Ganin Hajiyan Wagini kawai muka yi ta shigo cikin d’akin tana cewa "Haba Soja me kuma kayi ma amaryar taka, ko me ta maka ai kamata yayi kayi hak’uri da ita dan nasan dama ita ce da laifi, ni kaina tun da tazo take sa ni magana, dama ina jin haushin ta’ba min waya da tayi".

Ci gaba nayi da kuka na ba tare da na tsagaita ba, hakan yasa Hajiyan Wagini ce ma yaya Faruk "Mai gida na wai me ka mata ne ta cika mana kunne da kuka".

Wani irin banzan kallo ya watsa min kana ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya kukan jin dad’i take yi dan ni ba abin da nayi mata".

Hajiya cikin lallashi ta ce "Wai me aka miki ne ki ke kukan nan".

Cikin kuka na ce "Hajiya dan girman Allah ki ba ma yaya Faruk hak’uri, na mishi laifi ne".

"Me kika mishi?".

Hajiya ta tambaye ni tana kallo na.

Shiru nayi wannan karan ban bata amsa ba, hakan yasa Hajiya fusata ta fara fad’a tana cewa "Ka ga ja’iran yara, kowa sai tambayar shi nake yi me yake faruwa kun k’i fad’a min sai tamaula ku ke yi dani".

Yaya Faruk ne ya rik’o hannun Hajiya ya ce "Hajiya mu je falo zan fad’a miki abin da yake faruwa" yana gama fad’ar haka suka bar d’akin.

Samun guri yayi ya zauna ya zayyane ma Hajiyan Wagini abun da yake faruwa da hukuncin da ya yanke yanzu.

Hajiyan Wagini na gama jin labarin ta sa kuka tana cewa "Yanzu dama abin da Fatima tayi kenan, shi yasa ta tawo nan, ba yadda ban yi ba akan ta fa’da min dalilin zuwan ta tak’i ta kuma d’au waya ta tayi min wani surkullen da ban da damar in kira mutane ko a kira ni, wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce, yaushe soyayyar zamani ta canza Fatima ta koma haka, to wallahi ba ta isa ba sai ta aure ka ko tana so ko ba ta so, anya Fatima tana da rabo kuwa a duiya tun da ta k’i ka, shi yasa ta ke kunna min wak’ar soyayya ni ina sha duk cikin son ka ne ashe wani barbad’ad’d’en take so ba kai ba".

Duk da ranshi ba ya mishi dad’i amma hakan bai hana shi murmusa wa ba jin Hajiya na cewa wai anya Fatima na da rabo a duniya kuwa?

Jin fad’an Hajiya yayi yawa yasa ya ce "Hajiya kar ranki ya ‘baci akan wannan maganar, ni na riga da na hak’ura da Fatima, kin ga kar a zo ayi abin da zumunci zai ‘baci".

Wani kallo ta mai na anya kasan abin da ka ke fad’a kafin taci gaba da cewa "Anya Soja kana cikin hankalin ka kuwa, ko dai shi wannan Dr d’in da ka ce yana son ta ya maka wani surkulen da zaka hak’ura da Fatiman, in ba haka ba ya za ayi bikin ku bai wuce sati biyu ba kace ka hak’ura da ita, ina ganin ka gwarzon namiji ashe ba haka ba ne, ko da yake bazan yi mamaki ba tun da son da kake ma Fatiman ba zai barka ka d’au hukunci akan ta ba, abin kunya yarinyar da ka ga k’uruciyar ta amma wai shakkar ta ka ke yi, to in kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, ba wanda ya isa ya kawo min matsala a cikin iyali na in dai ina raye".

Lallashin ta yaya Faruk ya fara yi amma kamar k’ara zuga ta ake yi, maimakon tayi shiru sai ma mik’e wa da tayi ta nufi d’akin da nake ciki.

Tun san da suka fita suka bar ni na ci gaba da kuka na har na gaji, sai faman ajiyar zuciya na ke yi, ba kalar tunanin da bai zo min a raina ba a wannan lokacin.

Fad’an Hajiya ne ya katse min tunanin da nake yi.

"Sannu Fatima, na ji abin da kika aikata, bari in fad’a miki babu wanda ya isa ya lalata min zumuncin da yara na suka dad’e suna yi, a yadda soja yake fad’a min nima za ki iya fad’a min magana in dai akan wannan Dr ne, to ko ke Laila-Majnun ce k’arewar soyayya sai kin hak’ura da shi wannan shed’anin yaron da yake zuga ki, ke ba ki isa ki kunya ta ‘ya’ya na ba, ke in banda sharrin so ai kin san Soja yafi k’arfin ki a komai ma".

Duk fad’an da Hajiyan Wagini take min kaina a sunkuye yake, nasan Hajiya za ta iya min abin da ya fi haka kasancewar duk cikin familin mu tafi son shi da shak’uwa dashi sannan sunan kakan mu ne wanda ya rasu, shi yasa duk wanda ya ta’ba yaya Faruk sai inda k’arfin ta sai ya k’are.

Yaya Faruk ne ya shigo ya ga fad’an da Hajiyan Wagini ta ke min, magana ya mata a kan ta k’yale ni tun da ya hak’ura, jin hakan ya k’ara tunzura HajiyanWagini ta dawo da fad’an kanshi "Rufe min baki, na ga akan Fatima za ka iya dawowa Sallamame sai yadda tayi dakai, kai in ban da ba ka da zuciya har za ka iya sa bakin ka har ka bani hak’uri duk da abin da ta maka, to in kai kana tsoron ta ni ba tsoron ta nake ji ba".

Duk wannan fad’an da Hajiya ke mai bai ce mata komai ba sai ma wayar shi da ya ciro yana daddanawa.

Ganin wayar da yake dannawa yasa Hajiya ta ce "Yanzu Soja duk wannan fad’an da nake yi akan ka shine za ka bad’a min k’asa a ido, maimakon kaima ka nuna ‘bacin ranka ka taya ni yi mata fad’a sai ma wayar ka da ka d’akko kana dannawa, ai shi kenan" nan Hajiya ta k’ara sa wani kukan.

Sanin rikicin Hajiyan Wagini yasa ya maida wayar shi gaban aljihun shi ya ce "Hajiya ki yi hak’uri, ban cika son d’aura ma kaina damuwa ba, likita ya min gargad’i akan haka saboda kiyaye lafiya ta kuma kin san ni ban cika son hayani ba".

Wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a ne yasa Hajiya yin shiru daga fad’an da yake min.

Hajiya ce ta fara fita a falon, har ya fara tafiya kana ya juyo cikin d’aurewar fuska ya ce min "Ki shirya yau za mu koma Kaduna in kin gadama, in kuma za ki kira wannan Dr d’in ne ya zo ya d’auke ki ku tafi wani gurin, kina da damar yin haka, za’bin ya rage naki" yana gama fad’ar hakan ya bar d’akin.

Samun Hajiya yayi akan zai koma Kaduna dani, Hajiya na jin haka ta ce itama da ita za a tafi a yi komai a gaban ta.

Yaya Faruk bai mata musu ba ya ce ta shirya zuwa anjima za su tafi.

Abinci Hajiya ta shirya ma yaya Faruk wanda na dafa.

Tun da Hajiya ta zubo mishi abincin yaji bai marmarin shi dan yasan ni na dafa, ba yadda Hajiya ba tayi dashi ba akan yaci amma yak’i, sai ma ce mata da yayi bai jin dad’in bakin shi ne, ruwa kawai yasha da dambun naman da Hajiya ta kawo mai wanda ba ta rabo dashi yaci kad’an.

Haka na zauna a d’aki ba tare da na fito ko falo ba, abincin da na dafa ma kasa fitowa nayi na ci, ko sallah a band’akin ciki nayi alwalata, na san in dai na kuskura na fito falo ba abin da zan fuskanta sai ‘bacin rai, fad’an Hajiya kawai ya ishe ni bare a je ga kallon da yaya Faruk yake min a yanzu, A yanzu ina ganin yaya Faruk ya dawo kamar yaya Faruk d’in da na sani a da, yanzu ga wani tsoron shi da ya sake shiga na a karo na biyu.

San da za mu tafi yaya Faruk ne ya shigo d’akin ya ce in fito mu tafi.

Ko da zan shiga motar tunani na fara yi akan gaba zan zauna ko a baya, had’a idon da muka yi da yaya Faruk ne ya watsa min wani banzan kallo yasa ba shiri na bud’e baya na shiga, Hajiya ma baya ta shiga yaya Faruk ya ja mu muka tafi.
[7/8, 21:57] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

www.maryamahmadpaki.blogspot.com
Facebook: Kainuwa Writers Association



*GAISUWAR TAKU CE*

_Noorul-jannarh (Marubuciyar Detective Noor)_

_Maman Usy_

_Faeedaabdullahi1_

_Habiba Rabo_

_Hajiyar Allah_



_Surar da take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junan su, dangantaka bayyananna ko ‘boyayya, kuma zumuntar sun a gudana gwargwadon dangantar su da juna ita ce Suratul Rum_



69-70


Tun da muka d’auki hanya banyi magana ba, Hajiyan Wagini ce ke jan yaya Faruk da hira jefi-jefi, yanayin shi na nuna ba dad’in hirar yake ji ba, kawai dauriya yake yi, alamun shi na nuna kamar bai da lafiya.

A haka muka ci gaba da tafiya, in ban da tunani ba abin da nake yi, Hajiya ita a dole fushi dani take yi shi yasa ba ta ja ni da hira ba.

Muna shiga Kaduna yaya Faruk ya wuce da mu gidan Abbu, in ban da gaba na da yake fad’uwa, ba abin da yake yi, da ina da hali da na ce ma yaya Faruk kar ya kaini gidan mu, ya fara kaini gidan su duk da nasan ba lallai ba ne in samu tarba daga gurin su Momi da Anisa, nasan Dadi ba zai canza min a fuska ba, sai dai ya min fad’a akan abin da na aikata, nasan ko da ba a cikin hayyaci na nake ba, ban isa in nemi wannan alfarmar daga gurin yaya Faruk ba, yanayin fuskar shi kad’ai tsoro yake bani, ga wani kwarjini da min da ban tunanin zan iya mishi magana.

Ina ganin yaya Faruk yayi horn, Malam Musa ne yazo ya bud’e mai gate d’in, nan na ji jiki na ya d’auki rawa, ga wani tsoro da fad’uwar gaba da had’u ya min dabaibayi a zuciya ta, duk wanda ya kalle ni a lokacin yasan ba na cikin natsuwa ta.

Parking yayi a ma’ajiyar adana motoci kana ya bud’e ma Hajiyan Wagini mota ta fito daga ciki.

Tafiya suka fara yi ba tare da sun damu da halin da nake ciki ba.

Cikin rashin k’arfin jiki na bud’e motar na fito, a lokacin na ji wasu zafafan hawaye na zubo min, ni kaina a lokacin ba zan iya fad’ar dalilin hawayen nawa ba.

Tsayawa na yi a jikin motar na kasa tafiya, jiki na ne ya min nauyi wanda ya haddasa min rashin k’arfin motsa k’afa ta.

Yaya Faruk ne ya lura da rashin tawowa ta, hakan yasa ya juyo ya watsa min wani kallo mai isar da gargad’i.

Ganin kallon da ya min yasa na ji tsoro ya k’ara shiga ta, ban san lokacin da na fara taka k’afa ta na fara tafiya ba, duk kuwa da yadda k’afa ta tayi min nauyi.

Sallama su Hajiyan Wagini suka yi suka shiga cikin falo.

Ummu ce ta amsa musu sallamar cikin walwala.

Yaya Khalil ne ya gaishe su kana Ummu ta gaishe da Hajiyan Wagini.

Yaya Faruk sun gaisa da Ummu cikin girmama wa.

Ummu da yaya Khalil ne ta tare da tambayar shi ya k’arfin jikin shi.

Amsa mata yayi da ya ji sauk’i.

Sai a lokacin na tabbatar da zargi na akan rashin lafiyar yaya Faruk saboda yadda yanayin shi ya nuna hakan.

Yaya Khalil ne cikin tsokana ya kalli Hajiyan wagini ya ce "Matar ke ce a garin mu, gwara da Allah ya kawo ki, dan nayi kewar ki".

Cikin dariya Hajiya ta ce "Ja’iri ni matsa can, in da ka yi kewa ta ai da kaje in da nake".

Dariya yayi yace "Hajiya ba lokaci ne shi yasa".

"Ai na ga agogo ma a aiki" Hajiya ta fad’a cikin dariya.
Suna cikin hirar ne Abbu ya fito daga shashen shi ya shigo main parlour.

Murmushi ya saki lokacin da yaga Hajiya.

Cikin farin ciki suka gaisa na irin tsakanin Uwa da d’anta.

"Ina wuni Abbu" yaya Faruk ya furta cikin sanyin murya.

"Lafiya lau Faruk, ya jikin naka".

"Da sauk’i Abbu".

"Allah ya k’ara sauk’i" Abbu ya fad’a cikin kulawa.

"Amin Abbu".

Hajiya ce ta ce "Wai Ibrahim me ya samu Sojan ne na ji kuna ta tambayar shi ya jiki, rashin lafiya yayi kenan sosai ban sani ba?".

Abbu ya amsa mata da cewa "Yayi fama da rashin lafiya ne, amma yanzu da alama jikin da sauk’i".

Juyowa tayi ta kalli yaya Faruk ta ce "Hala ciwon naka ba zai rasa nasaba da abin da Fatima ta maka ba ko, dan nasan har da dalilin ta kayi wannan rashin lafiyar, ai ba ta isa ta bijire ma wannan auren ba ta sa ka a wani hali, sai ta aure ka ko ba ta so, sai dai in mutuwa za tayi k’arewar rashin son ka kenan".

"Hajiya, Allah ne ya d’aura min ciwo ba ruwan Fatima" yaya Faruk ya fad’a cikin sanyin murya.

Cikin Hasala Hajiya ta ce "Ai dama haka za ka ce, tun da kai ba son laifin ta kake yi ba, ka riga ka makance a son ta".

Sai a lokacin Hajiya ta kalli falon ta ga ba na ciki.

Ni kuwa duk wannan abin da yake faruwa ina can jikin k’ofa a ra’be ba tare da na shigo ba, in ba ka lura da gurin ba, ba lallai kasan ina tsaye a gurin ba .

Hajiya ce ta hango ni a tsaye a bakin kofa kana ta ce "Au Fatima can kika tsaya, ai dole ne ki kasa shigowa tun da ba ki da gaskiya" Hajiya ta fad’a.

Duk wanda yake d’akin maida hankalin shi bakin k’ofa yayi jin Hajiya ta ambaci suna na, sai a lokacin suka lura da ni.

Ummu tun da muka had’a ido da ita ta min wani kallo, hakan yasa na k’ara jin jiki na yayi sanyi.

Falon ne ya d’auki shiru kamar ba kowa a ciki.

Abbu ne ya kalli Hajiya, fuskar shi cike da ‘bacin rai ya ce "Hajiya ina kika samo wannan yarinyar".

"Guri na ta tawo, ashe gudun hijira ta yi ta tawo guri tana ganin za ta samu tallafi na, sai da Soja yazo yake fad’a min ai ba a san da zuwan ta ba, Soja ya sanar dani halin da ake ciki, ni kuma na ce ta sha ruwan k’arya ta ce ba za ta auri Soja ba".

Yaya Khalil ne ya mik’e ya tawo in da nake, saboda rashin kuzari a jiki na yasa na kasa motsawa.

Hannu na ya rik’o ya shigo da ni cikin falon.

Guri na samu na zauna a can gefe, ni kaina na tsargu da zama na a falon saboda laifin da nayi.

Ummu wacce takaicin abin da na aikaita wanda dashi take kwana take tashi a ranta yasa ta taso ta fara duka na.

Ba wanda ya hana Ummu duka na saboda haushin abin da na aikata, sai Hajiya ce ta wa Ummu magana akan ta daina duka na, addu’a ce magani ba duka ba.

In ban da shashshek’ar kuka ba abin da nake yi, yau ni kaina nasan na daku a gurin Ummu.

Abbu ko saboda ‘bacin ran dake damun shi kasa magana yayi, sai bi na yake yi da ido kawai.

Kuka na naci gaba da yi ba mai lallashi na, nasan dama ba wanda zai kula ni tun da suna jin haushin abin da na yi, ni kaina nasan ban kyauta ba.

Hajiya ce ta kau da shirun da cewa "Ibrahim ka kira min yayan ka ayi komai a gaban shi, dalilin zuwa na kenan, na ga alamar Fatima so take yi tayi fito na fito da kowa akan wannan maganar".

Waya yayi ma Dadi ya sanar dashi zuwan Hajiyan Wagini da sak’on neman shi da take yi.

Ba a d’au wani lokaci ba sai ga Dadi da Ummu da Anisa sun zo.

Zama suka yi aka gaggaisa kafin Hajiya ta d’aura da cewa "Isuhu".

Dadi cikin ladabi ya amsa "Na’am Hajiya".

Hajiya ta ci gaba da cewa "Abin da yasa Na ce Ibrahim ya kira min kai shine akan maganar Soja da Fatima, naji k’udirin da Fatima take son aiwatarwa akan bijire ma auran, tun da ta na so ta nuna mana ita ‘yar zamani ce ta hanyar bijire maganar da aka riga aka gama ta, lokaci kawai ake jira, rana d’aya ta bad’a wa idon ta k’asa ta nuna bare yafi d’an uwanta, saboda haka na yanke hukunci Fatima ba ta isa ta auri wani ba in ba Soja ba".

Dadi ne ya ce "Amma Hajiya….".

Hajiya tayi saurin kar’ban maganar da cewa "Isuhu bana buk’atar jin wani bayani in dai ba goyon baya za ka bayar ba akan maganar auran".

Falon ya d’auki shiru, kowa da irin tunanin da yake yi a ransa.

Yaya Faruk ne ya nisa kana ya katse shirun da cewa "Hajiya ki yi hak’uri da hukuncin da na yanke kamar yadda na fad’a miki a baya, nasan kina son auran mu da Fatima, amma Allah bai k’addara ba, tun da Fatima ta nuna tana da wanda take so, ba ni take so ba, ina ganin Hajiya gwara a barta ta auri za’bin ranta dan guje ma wata matsalar da ka iya tasowa in aka yi auran, Hajiya bazan iya auran yarinya da ta mallaka ma wani zuciyar ta ba, ina neman afuwar ku, ni na hak’ura da auran Fatima" ya k’arasa maganar a hankali.

Hajiya cikin fad’a ta ce "Wai kai Soja kana da hankali kuwa, akan ka faranta ma Fatima shine kai ka yarda ka sa kan ka a cikin damuwa, ita har ta isa ta ce ba ta son ka, to tayi k’arya dan bantan uban ta, ko kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, dole ne sai an yi wannan auran, sai dai in an yi auran ta d’au wuk’a ta yayyanka naman ka gunduwa-gunduwa saboda k’in ka da take yi".

Abbu duk wannan maganganun da ake yi bai yi magana ba sai a yanzu ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ki kwantar da hankalin ki, ko da a ce kowa ya hak’ura da wannan auran ni sai na d’aura shi, Fatima ta sa min wani bak’in ciki a cikin zuciya ta da banyi zato ba, da nayi niyyar in zuba mata ido tayi duk abin da ta yanke ma kanta saboda yadda ta fifita saurayi akan mu iyayen ta, sai nayi wani tunanin akan in na k’yale ta hakan na nuna kamar ita ta haife mu kenan, saboda haka nima na ce Fatima ba ta da miji in ba Faruk ba in dai na isa da ita".

Ba maganar da ta d’aga min hankali sama da ta Abbu, nasan yanzu ban da wata hanya da zan bi in samu in cimma muradina, hakan na nufin in rabu da Dr kenan.

Hawaye ne ya fara zuba a idanu na, ni kaina na fara tausaya ma kaina halin da zan shiga matuk’ar ban samu Dr ba a matsayin miji.

Yaya Faruk cikin sanyin jiki ya ce "Abbu na gode da kulawar ku gare ni, sai dai ina neman alfarma Abbu kayi hak’uri ku bar Fatima ta auri wanda take so, hakan zai fi wa kowa kwanciyar hankali akan a zo ayi abin da za ayi danasani daga baya".

Ummu da Momi kuwa ba wanda ya samu k’arfin yin magana, kowa da abin da yake kissamawa a ranshi.

Dadi cikin ladabi ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ba wai zan ja da maganar ki ba ne ko hukuncin da kika yanke, sai dai nima ina neman alfarmar ku akan ki duba wannan al’amarin, ku bari Fatima ta auri shi wannan Dr tun da har ta nuna shi take so, ni kaina zanyi farin ciki idan Fatima ta auri Faruk tunda duk d’aya ne a gurin mu, su duka ‘ya’yan mu ne, tun da auren yazo da tangard’a, hak’urin shi yafi".

Haka Daddy yaci gaba da lallashin Hajiya da kawo mata hujjoji akan illar yin auran, da alama jikin Hajiya ya fara yin sanyin da maganganun da Dadi yake fad’a mata.

D’aura zancen yayi da cewa "Hajiya ki yi hak’uri kar ki sa ma kan ki damuwa, mu yadda hakan Allah ya k’adar ta".

Hajiya ce ta ce "Yanzu Isuhu kana nufin kenan dai Soja ya hak’ura da Fatiman, shi kenan tun da kana ganin hakan yafi, Allah shi ma ya kawo mishi ta gari wacce za taso shi" ta k’arasa maganar tare da fashewa da kuka.

"Amin dai Hajiya, ki yi hak’uri Hajiya, mu rok’i Allah yasa hakan yasa shi yafi zama alkairi a gurin su" Dadi ya fad’a cikin sanyin murya.

Da k’yar aka samu aka lallashi Hajiya tayi shiru.

Momi wanda takaicin hukuncin abin da Dadi ya yanke yasa ta kalli Dadi ta ce "Yanzu Alhaji an ma yaron nan adalci kenan, kana ganin halin da ya shiga, shine yanzu za ka yanke wannan hukun…".

Katse ta yayi da cewa "Rukaiyya ba na so ki sa bakin ki a cikin wannan maganar, hukuncin da kika ga na yanke, to ina fatan hakan ya sa yafi zama alkhairi da kuma samun maslaha ba tare da an shiga hakk’in wani ba a cikin su".

Abbu ne ya kalli Dadi cikin taushin harshe ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba wai zan yi jayayya da hukuncin da ka yanke ba ne, sai dai kamar yadda na fad’a a farko ban sauya ba, Fatima ba ta da wani miji sai Faruk".

Cikin d’aure fuska Dadi yayi ya ce "Yanzu na gano hujjar ka Ibrahim, kana so ka nuna min ban da iko akan Fatima

Please Login or Register in order to submit comment