Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samun phone number d’in ki mu dinga gaisawa tun da ba a bani damar nuna kalar soyayya ta gare ki ba, yanzu sai naje na lallashi zuciya ta, na ba ta hak’uri tun da an dasa mata ciwo".

Ganin mafita d’aya ce a gare ni a gurin Haidar shine in bashi numba ta ko na samu ya rabu dani, dan haka na fad’a mishi numba ta.

Kallo na yayi ya rausayar da kai yace "Fatima ki bani aron wayar ki in sa miki numba ta, kar in kira ki dinga ce wa waye? Ban gane mai Magana ba".

Murmushi nayi saboda a yadda na karance shi yana da ban dariya.
Waya ta na mik’a mai ba tare da nace komai ba.

Duk wannan abun da yake faruwa yaya Faruk na kallon mu har zuwa san da na mik’a ma Haidar waya ta.

Takun tafiya naji a kusa da mu, shi yasa ni d’aga kai dan ganin waye.

Ido na ne ya had’u da na yaya Faruk wanda tsantsan ‘bacin rai ne kwance a fuskar shi.

Ni in ba ido na yake min gizo ba, har wani ja na ga fuskar shi tayi, abun ka ga farin mutum, idon nan nashi ya kad’a ya koma kalar ja, jijiyoyin kanshi ko duk sun tashi.
Wani irin rawa jiki na yakama yi da bugawa da k’irji na da yake yi saboda tsoron da ya kama ni a lokaci d’aya.

"Wayyo! Naga ta kaina" na fad’i haka a raina.

Sai faman zare ido nake yi kamar wacce tayi wa sarki k’arya.

Ciikin izza ya amshi waya ta dake hannun Haidar ya maka ta a k’asa.

Tun san da yaya Faruk ya fasa min waya naji wani k’unci ya ziyarce ni da kuma tsanar sa da naji ta ka’ra shiga min a cikin zuciya, in ban da zalunci akan me zai fasa min waya, ko yana tak’amar ba ni da k’arfin rama wa shi yasa ya aikata hakan ko kuma duk cikin k’iyayyar da yake min ce? me nayi wa yaya Faruk da yake min haka? tambayar da nake ta yi wa kaina kenan.

Haidar kuwa bin shi yayi da kallo saboda ganin k’arfin halin wannan mutumin da bai san waye ba.

"Malam akan me za ka amshi waya a hannu na sannan ka fasa ba tare da wani dalili ba, hasalima ni ba sanin ka nayi ba".

Kallon rainin wayau ya mishi sannan yace "ba sai ka san ko ni waye ba da na aikata hakan, na isa ne shi yasa na aikata hakan dan nasan ba abin da zai faru".

Haidar shima ran shi ne ya ‘baci da abin da wannan mutumin ya mai saboda rainin hankali "kai waye? me kake ji dashi da za ka aikata haka sannan kana fad’a wa mutum maganar da ka gadama".

Da ‘bacin rai, yaya Fruk ya fara magana "gentle man you have to control your tongue, if not, you will face da consequences, sanin ni waye ba zai maka amfani ba saboda haka ka kula, lastly abin da zance maka shine ka fita hanyar k’anwa ta dan ba da irin kai ta dace ba saboda kaima naga har yau baka gama mallakar hankalin kan ka ba bare ka iya kula da wata ko ka bata caring irin na lovers, bayan haka ma she is a teenager, bazan bari a ‘bata mata tarbiyya ba, wannan shine gargad’in da zan maka in ka ji kenan".

Wannan maganar da yaya Faruk yayi, shi ya ba Haidar amsar tambayar shi saboda ya gano suna da alak’a da Fatima.

In a cool sound Haidar yace "Am sorry! Ban san cewa k’anwar ka bace kuma ni tsakani da Allah na ji ina son Fatima, kuma ni ba da niyyar cutar da ita nayi ba ko in yadaure ta ba kamar yadda kake nufi, sai anjiman ku".

Bai jira jin amsar da yaya Faruk zai bashi ba ya bar gurin cikin fushi.

Juyowa yayi cikin fushi ya fara Magana.

"Fatima! ki kiyaye ni, kar ki bari in nuna miki true colours d’ina, ba za ki ji dad’i na ba, yanzu abin naki ya wuce na yin chat da hoto da mazan ‘yan class ya koma kin fara kula samari at your small age? Ana so a gina muku future d’in ku amma ke ba kya ganin haka, kina amfani da yadda rayuwa take tafiya wanda hakan matsala ce, let me warn you, duk san da na sake ganin kin kula wani, hmmm zaki fuskanci hukunci mai tsanani a guri na, ki tashi mu tafi gida".

Duk wannan maganar da yake fad’a, kaina a sunkuye yake ina faman zubar da k’walla na takaici da bak’in ciki a lokaci d’aya.

Wata tsawa da ya daka min ita tasa ni tashi ban yi niyya ba saboda har cikin kaina naji ta.

Anisa kuwa dake kwance akan grass carpet can d’an nesa damu tana pressing d’in wayar, tun san da yaya Faruk ya baro gurin da yake ya k’araso gurin mu har san da ya fasa min wayar hankalin ta ya dawo kan mu.

Abin da yake mata yawo a ranta shine "mai yasa yaya Faruk ya fasa ma Fatima waya kuma da alama ranshi ya matuk’ar ‘baci, ko ma dai menene ita a ganin ta wannan bai kai laifin da zai sa ya fasa mata waya duk da ita ma ya ta’ba fasa mata waya akan ya kama ta tana yin chat".

Zuciyar ta ce ta ba ta amsa da cewa "yaya Faruk yayi hakan ne don ba yaso mu fara kula samari a yanzu wanda har yanzu kallon yara yake mana, yana so yaga mun maida hankalin mu a kan karatu".

Jiki a sanyaye na mik’e na fara tafiya kamar mai fama da rashin lafiya saboda yadda a lokaci d’aya naji jiki na ya min duk a sanadin ‘bacin rai.

Anisa da ba ta ji dad’in abin da ya faru ba yasa ta rasa mai za tace dan yadda Fatima ta hau dokin zuciya ba lallai ta saurare ta ba.

A wani bakery ya tsaya ya siyan musu ice cream da snacks.

Ko da muka shiga cikin motar ba wanda yake da k’arfin yin Magana saboda yadda ran mu yake a ‘bace.

Jin shirun yayi yawa ne yasa ya kunna k’ira’ar sheikh Al Gamidi cikin suratul Rahaman, bin surar yake yi yana jin zuciyar shi na sa mun sauk’i.

Gaskiya ne, duk wanda ya rik’e Alk’ur’ani, zai saman masa waraka da mafita a dukkan lamuran shi.

Parking yayi a k’ofar gidan mu ba tare da ya shiga ciki ba.

Fitowa nayi ba tare da nace komai ba, ko Anisa ban yi wa sallama ba, har yanzu abin da yaya Faruk ya min ya tsaya min a rai.

Bayan fita na daga mota ya kalli Anisa wacce ta rasa abin da yake mata dad’i yace "Anisa d’au ledan nan ki kai ma Fatima, ki yi ma Ummu sallama sai ki fito mu tafi".

Jiki a sanyaye ta fito daga motan ta nufi cikin gidan.

Ko da ta shiga cikin main parlour, ba ta same ni a ciki ba, direct d’aki na ta wuce.

Samu na tayi a zaune akan gado ina wani irin kuka mai ban tausayi.

Anisa cikin sanyin jiki ta zo ta zauna kusa dani ta dafa kafad’a ta ta fara da cewa "Fatima! me yasa kike kuka alhalin kin san halin yaya Faruk, ko ni ban ji dad’in yadda ya fasa miki waya ba, though shi a ganin shi wannan ce hanyar da zai yi abiding d’in mu da kar mu kula samari".

Cikin kuka na fara cewa "Anisa na gaji da abin da yaya Faruk yake min, tun ina iya daure wa har takai zuciya ta na ingiza ni akan in yi fito na fito dashi ko na samu freedom".

"why? me yasa yake son takura min? me yasa yake interfere a cikin personal life d’ina? me yasa zai yaga min hoton da na d’auka da ‘yan class d’in mu yanzu gashi ya fasa min waya, me yasa ya takura min a cikin rayuwa ta… na k’arashe maganar.

Anisa tace "wani hoto kuma ya yaga?

"hoton mu ya yaga wanda muka d’auka da mazan class d’in mu".

Anisa kuwa ba kalar tunanin da bai zo ma ta ba a ranta, a k’arshe dai ta dasa alamar tambayoyi akan abin da yasa duk Yaya Faruk yake aikata hakan.

Kuka na ci gaba da yi ina k’ara jin haushin yaya Faruk a raina.

Anisa kuwa in ban da hak’uri ba abin da take bani, k’arshe ma rok’o na tayi akan kar in fad’a ma su Ummu da Abbu, ita za ta fad’a wa Momi abin da ya faru kuma tasan za ta d’auki mataki akai sannan za ta sa yaya Faruk ya siyan min wata sabuwar waya.

Yaya Khalil ne ya shigo cikin d’akin kana yace "Anisa kije yaya Faruk na jiran ki, ina tsarabar outing?

Zaro ido tayi ta mik’e saboda ita ta manta yaya Faruk na jiran ta, yanda yake cikin ‘bacin ran nan, zai iya huce wa akan ta.

Narai-narai tayi da ido alamar za tayi kuka.

Yaya Khalil ne ya kalle ta da mamaki yace "ya akayi ne naga kamar za kiyi kuka?

" tsoro nake ji yaya Khalil kar yaya Faruk ya ta’ba ni, in ya kama ni sai na gane kure na".

Yanda tayi maganar yasa shi darawa, hango Fatima yayi sai faman shasshek’ar kuka take yi.

Kallon Anisa yayi da alamar tambaya yace "Anisa me ya samu auta naga tana faman kuka".

"ita da yaya Faruk ne" ta bashi amsa.

Ta’be baki yayi yace "Auta ta yaya Faruk Kenan, ai fad’a a shirya".

Anisa ce ta kalle ni tace "Plsss Fatima ki daina kuka, yaci ace kin saba da halin shi, ni zan tafi, sai na sake ‘bullo wa".

Ganin ko amsa mata ban yi ba yasa ta gane har yanzu ina kan dokin zuciya, dan haka tayi murmushi ta bar d’akin.

D’akin Ummu ta shiga ta mata sallama ta fito yayin da Yaya Khalil ya raka ta bakin gate, ta nufi inda Yaya Faruk yayi parking d'in mortar shi.

*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Wannan shafin tukwici ne gare ku*
*‘yan Facebook*, *mazan ku da Matan ku*
*Ina yin ku sosai na yadda kuke son wannan novel d’in*.



*KUN YI BAJINTA*

*Meeynah*

*Salmah*

*Autan mama* (Aisha matar Abdul)

*Kune kuka bayar da amsar daidai*.

*Da sauran wad’an da suka yi k’ok’arin amsa tambayar Question of the day amsar da suka bayar akan wace Surah ce a cikin Alkur’ani aka yi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce, amsar itace Suratul Baqara a cikin Ayah ta 282, wasu sunyi k’ok’arin cewa Suratul Baqara*.

*Allah ya albarkaci ilimin mu baki d’aya*.




*K’ORAFI*

*Na samu k’orafin ku da dama, wasu suna k’orafin in k’ara yawan typing, wasu kuma suna k’orafin ban a posting da wuri*.

*Na gode da k’orafin ku kuma insha Allahu zan duba, amma yanayin rashin time yasa hakan ke faruwa da kuma wasu uzuri da za su iya tasowa*.

*Da fatan za a min uzuri*.

*Na gode*.🤝🏽🤝🏽




*TUNATARWA*

Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka iya wa kowa.

Ka/ki zamo me neman na kai, amma ka da yakai ka/ki ga neman haram.

Ka/ki zamo mai son iyalin ka/ki amma kada ka/ki yarda ka/ki shagala.




33&34

Ko da ta shiga motar, tarar da yaya Faruk tayi ya kifa kansa akan sitiyarin mota, sun d’au kusa minti biyar a haka kamar bai san da shigowar ta ba.

Anisa kuwa in ban da addu’a ba abin da take yi saboda tasan me k’watar ta a gurin yaya Faruk sai Allah, tasan tun a gida take ‘bata mishi lokaci gashi yanzu ma yace ta shiga ta kai ma Fatima ledar shopping d’in da ya musu gashi ta da’de.

D’ago kai yayi ya mata wani banzan kallo sannan ya d’aura da cewa

'uban me kika zauna yi a ciki bayan kin san ina jiran ki, ga driver kin samu ko? put in your mind sai kin fuskanci hukunci".

"plsss yaya Faruk kayi hak’uri! Wlh ban je da niyar zama ba, Fatima na gani tana kuka shine na tsaya ba ta hak’uri".

Jikin shi ne yayi sanyi saboda yasan shine silar da yasa Fatima kuka kuma shima yana ji a jikin sa bai kyauta wa Fatima ba amma sai ya dake ya fara Magana cikin fad’a da cewa "amma da kika tsaya ba ta hak’urin ina fatan kin had’a da goya ta, saboda ina ganin za ta fi jin lallashin da kike mata, ni kuma da kika maida d’an iska shine kika shanya ni ko?

Ita dai ba ta k’ara ce mai komai ba illa sauraran fad’an da yake ta jero mata, fatan ta su isa gida ta fad’a wa Momi duk abin da ya faru, dan gaskiya abin ya tsaya mata a rai.

A guje ya ja motar kamar wanda zai bar garin.

parking d’in motar shi yayi a parking space, tsoron fito wa take yi kar yace ba ta jira ya fara fito wa ba.

Tsawar da ya daka mata da cewa "uban me kika tsaya yi a ciki? ko sai na zo na fito dake ne!

saboda rikicewa ba ta tsaya d’aukar ledar ba ta fito ta kwasa da gudu kamar wanda aka biyo ko murfin motar ba ta rufe ba.

Gajeran tsaki yayi a lokacin da ya ga ta bar ledan a motar, ya d’auka ya rufe motar kana ya nufi side d’in shi ta k’ofar baya.

Tana shiga cikin falon ta dinga sauke numfashi, tarad da Momi tayi zaune a falo.

Momi ce ta kalle ta tare da cewa "ke kuma lafiya zaki shigo a guje kamar wanda aka biyo".

Cikin basar da zance ta amsa da "ba komai Momi, sannu da gida".

"yau an sha yawo kenan Anisa" cewar Momi.

Kusa da ita taje ta zauna tana bata labarin gurin da suka je.

Wayar tace tayi k’ara alamar kira ya shigo.

Ganin sunan yaya Faruk yasa ta d’auke wuta kamar ba ita ke ba da labari ba.

"ki same ni a d’aki na" abin da yaya Faruk yace kenan ya katse wayar.

Cikin sanyin jiki ta mik’e tana cewa Momi "bari in je d’akin yaya Faruk ya na kira na".

"Ok" momi ta amsa a gajarce.

Samun shi tayi zaune akan rest chair, yana sanye da vest da three quarter.

Sallama tayi ta shiga d’akin, ta nemi guri ta zauna.

Amsa mata sallamar yayi kamar ba ya so.

Taso wa yayi ya d’au d’an k’aramin cup dake ajiye akan fridge d’in shi ya kama hannun ta ba tare da yayi mata Magana ba.

Bin shi kawai take yi ba tare da tasan in da za su je ba.

K’ofar baya ya bud’e ya nufi wajen flowers d’in dake cikin gidan.

Tambaya take ma kan ta "me za su yi anan da taga ya d’akko kofi ya kawo ta nan".

Kallon ta yayi cikin d’aurewar fuska yace "je ki d’akko waccen bucket d’in na wajen tap d’in can".

"dakko wa tayi tare da cewa "gashi yaya Faruk".

Mik’a mata kofin yayi yace "wannan kofin da na baki shi zaki yi amfani ki cika min wannan bucket d’in, wannan shine purnishment d’in ki for today na ‘bata min time da kika yi".

Saurin kallon k’aton bucket d’in tayi da kuma d’an k’aramin kofin da ke hannun ta, da ratar in da tap d’in yake da wajen bucket d’in.

Tunanin ya za tayi ta cika wannan bucket d’in take yi da d’an k’aramin kofin nan?

"za ki fara ko sai jikin ki ya fad’a miki, ba na son ‘bata lokaci".

Hawaye ne ya fara ambaliya a fuskar ta.

Kallon ta yayi yace "will u wipe your tears & start your work".

Tap d’in ta nufa ta fara tarawa kana tazo ta juye a cikin wannan bucket d’in.

Kujera ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya akan d’aya yana sauraren cool music a wayar shi.

Haka Anisa ta dinga d’iban ruwa a cup tana juyewa a wannan bucket d’in.

Momi kuwa da taji shirun yayi yawa yasa ta mik’e ta nufi side d’in yaya Faruk.

Ko da ta shiga ba ta tarad dasu a ciki ba.

Momi ce ta tambayi kan ta da cewa "ina suka tafi kuma".

Ta glass window ta hango su a gurin flowers.

Ta k’ofar d’akin yaya Faruk ta fito ba tare da ta koma side d’in ta ba.

Anisa wacce saboda jeka ka dawo d’in da take yi yasa taji k’afar ta rik’e mata gashi ko rabin bucket d’in ba ta cika ba.

Hawaye ne ke ta zuba a idon ta amma yaya Faruk bai da alamar tausaya mata, sai ma rausayar da kanshi da yake yi alamar yana jin dad’in music d’in da yasa.

Momi ce ta k’araso da sauri tana cewa

"me zan gani Faruk! me ta maka da zaka ba ta such kind of purnishment irin wannan daga dawowar ta".

Cikin sanyi yayi magana "Sorry Mom, laifi ta min shi yasa".

Anisa kuwa in ban da filling d’in bucket d’in ba abin da take yi, taji dad’i da Allah ya kawo Momi a lokacin, ko ba komai tasan yanzu zai kyale ta.

Momi ta kalli Anisa cikin tausayawa tace "Anisa stop that work!

Anisa da kamar jira take yi tayi saurin ajiye kofin ta tawo gurin Momi.

Juyawa tayi ta kalli yaya Faruk cikin fad’a taci gaba da cewa "Faruk! am warning you amma ba ka ji, ka daina ba su irin wannan purnishment d’in saboda kasancewar su mata amma ka k’i ji, A wani dalilin za ka sa ta cika ruwa a wannan big bucket d’in da ‘dan k’aramin cup d’in, bayan kasan kan ta cika sai ta wahala, to ni ‘ya ta ba ta iya aikin wahala ba, ka kiyaye ni Faruk in ba haka ba zan sa’ba maka".

"Sorry Mom" abin da yace kenan.

A lokaci d’aya yana jin ‘bacin rai na yadda Momi za ta mishi fad’a a gaban k’anwar shi, salon ta raina shi.

Hannun Anisa kawai Momi ta kama suka nufi side d’in su.

A can ‘bangaren Fatima kuwa, yaya Khalil ne ya kalli Fatima wacce ke faman kuka yace "Wai Fatima me yaya Faruk ya miki ne haka da kike faman wannan kukan'.

Fatima cikin shasshek’ar kuka tace "plss yaya Khalil, help me ask yaya Faruk what have i done to him da yake min irin wannan hukuncin?

"tell me abin da ya miki" ya fad’a cikin hasala.

Zayyane masa duk abin da ya faru tayi a outing d’in da suka fita.

Shiru yayi yana kallon ta sannan yace "Fatima ba wai yaya Faruk bai yi laifi bane da ya fasa miki waya, ina so ki sani shi yaya Faruk matuk’ar ka kiyaye dokikin shi za ku zauna lafiya, yana son ci gaban ku na son ku ci gaba da ilimi shi yasa yake lura da takun ku, ku ke ganin kamar ya takura muku ne, tun da ya nuna ba ya son ku fara soyayya, ya kamata ace kin kiyaye dokokin".

Kallon shi nayi da mamaki nace "are my not big da ba zan kula saurayi ba? infact ni ba ni na kira shi ba, after all ni ban yi accepting d’in shi ba, yaya Khalil mai yasa da yazo bai tambaye ni ba, sai ma fasa min waya da yayi".

"Fatima! ya kamata ki d’auki yaya Faruk a matsayin wa a gare ki kamar yadda ni da yaya Aminu muke a gurin ki, duk abin da zai miki ki barshi a matsayin ke k’anwar shi ce kamar Anisa, kin fahimce ni ko?

D’aga mishi kai tayi alamar eh.

'yawwa Auta, share hawayen ki, ni zan siyan miki irin taki ta da".

Goge hawaye na nayi ina murmushi, sai naji na samu relief akan abin da ya faru.

***************************
Momi kuwa direct d’akinta ta tafi da Anisa tana ci gaba da fad’a.

Anisa wacce ta kwanta a jikin Momi sai faman ajiyar zuciya take sauke wa kamar wacce tayi gudu.

"Mtsww" Momi ta ja wani gajeren tsaki.

"Wai me kika mai ne ya baki wannan purnishment d’in?
Momi ta tambaye ta.

"Akan yace in kai wa Fatima ledar shopping d’in da ya mana cikin gida, shine da na shiga sai na tarar da ita tana kuka, ni kuma na tsaya ba ta hakk’uri ban fito da wuri ba, da na shiga mota shine yace sai ya bani purnishment" Anisa ta fad’a cikin shagwa’ba.

"To ita Fatima me aka mata take kuka" Momi ta tambaya.

Nan Anisa ta kwashe duk abin da ya faru ta fad’a wa Momi.

Momi wanda ranta ya gama ‘baci da labarin da Anisa ta gama ba ta tace

'Akan wani dalili zai yaga mata hotuna ya kuma fasa mata waya saboda ta kula saurayi? Ni kaina na gaji da irin wannan abin da Faruk yake yi amma zanyi maganin shi, dole ne ya fito da mata yayi aure saboda ina ganin har da rashin aure yake sa shi yin wannan abubuwan, in ba haka ba zai gamu da ‘bacin rai na".

"ina zuwa" abin da Momi tace wa Anisa kenan ta bar d’akin.


Shi kuwa Faruk tun da ya shiga d’aki ya rasa me ke masa dad’i.

"me yasa ban tsaya ta min bayani ba na fasa ma ta waya? Why? me yasa zuciya ta take ingiza ni akan d’aukan mataki akan ta? bai kamata ina taking action cikin zafin rai ba dan ba abin da zai jawo sai ‘bacin rai".

Yana cikin wannan tunanin Momi ta shigo cikin ‘bacin rai.

Kallon shi tayi ta kira sunan sa

"Faruk"

Saita kansa yayi ya amsa "Na’am Momi".


"Faruk akan wani dalili ka yaga ma su Fatima hotunan graduation alhalin kasan na tarihi ne, hotunan ne suka d’auka bai dace ba ko ganin ra’ayin kanka ne yasa ka yaga? Sannan duk wannan bai ishe ka ba shine sai ka fasa mata waya akan ta had’u da wani a inda kuka je? ina so ka fad’a min dalilin ka na yin haka?.

zuciyar shi ce ke umartar shi da ya fad’a mata dalilin shi nayin hakan amma yana ganin da sauran time, sabida haka yace "Momi kiyi hak’uri, yarinyar ce naga tana da rawar kai".

"kid’an kai take dashi ba rawar kai ba, ka fita hanya ta Faruk, akan irin hukuncin da kake musu zan sa’ba maka, mata kowa yasan lalla’ba su ake yi, ni ba ina nufin kar ka hukunta su ba ne in suka yi laifi, ya zamana akwai lokacin hukunci da kuma wasa".
Ci gaba yayi da cewa
"yanzu abin da nake so dakai shine ka siya mata wata sabuwar wayar ka kai mata, sannan maganar mu ta d’azun akan maganar auren ka ba wai na manta bane, in Dadin ka yaga zai iya zira maka ido akan rashin auren ka to ni a zan iya ba, na baka nan da d’an wani lokaci kafin ka koma aiki in ba haka ba zan baka mamaki in za’ba maka".

Ba ta jira jin cewar shi ba ta fita daga d’akin.

Kan shi ya dafa wanda yake ji ya mishi nauyi.

Kwantawa yayi akan gado yana kallan sama wanda ke nuni da ya fad’a tunani.

"ya zama dole ya samar wa kanshi mafita a ‘bangare biyu, yanzu gashi Momi ta taso shi gaba akan zancen yarinyar da yake so bayan har yau bai furta wa yarinyar yana son ta ba, yanzu ya zai yi?

Ya zamar mishi dole ya d’auki za’bi a d’aya a cikin biyu, ko dai ya fad’a ma yarinyar ko kuma Momi ta za’ba mishi yarinyar da ta mata kamar yadda take furta wa.

Yau kwana biyu kenan rabon yaya Faruk da gidan mu, sai hakan ya min dad’i.


Da yammaci ina zaune a wani ke’battaccen guri da akayi shi dan hutawa, inda aka ajiye kujeru da ta table, yayin da aka yi wata ‘yar bukka a sama.

Pineapple-cocunut drinks ne a gaba na ina sipping a lokaci d’aya ina pressing d’in I-pad d’in yaya Khalil da ke hannu na.

Jin shigowar mota yasa na d’aga kai na kalla dan ganin wanda zai shigo..

Ganin Motar yaya Faruk ce yasa na kau da kaina na ci gaba da abin da nake yi.

Parking d’in motar shi yayi a parking space.

Hango ni yayi a gurin shak’atawa yasa ya nufo gurin.

Guri na naga ya na tawowa rike da wata leda a hannun shi, tamke fuska nayi dan ban san kuma da mai yazo ba.

Sallama ya min ya nemi d’aya daga cikin kujerun ya zauna.

In ban da amsa sallama dole ce da ban ga abin da zai sa ni in amsa mishi sallamar ba.

Ciki-ciki na amsa sallamar kamar ba na so kana na gaishe shi wanda ko ni nasan ba lallai bane in ya ji gaisuwar da na mishi.

Ga mamaki na sai naji ya amsa da "lfy lau Fatima, ya hak’uri da ni?

A raina kuwa cewa nayi "ji wani tambayar rainin wayau da yake min, hak’uri da kai sai dole dan ba yadda mutum zai yi dakai ne, amma da sai na rama abin da kake min".

Sanin ba zan bashi amsa ba yasa yayi murmushi.

"Fatima" ya kira suna na a hankali.

D’ago

Please Login or Register in order to submit comment