Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a waye, sai dai da difference is clear.



Yafi jin dad'in kasancewa da ni akan Meema, yasan ni ta daban ce da baiwar da Allah ya min, yasan zai yi wuya ya samu iri na wajen faranta mi shi yanda yake so.


Tun a nan ya fara missing d'ina, saurin kau da tunani na yayi a ran shi, a yanxu yana ganin bai da buk'atar yin tunani na tun da nuna ban damu dashi ba tun da ban ne me shi ba tun da muka rabu.


A haka zaman su ya ci gaba da kasancewa, ba laifi Dr yana ba ma Meema Kula ita ma Meema tana k'ok'arin yin abin da Dr ya ke so da kauce ma abin da bai so.



Da zama yaci gaba da gudana a tsakanin su ne zaman nasu ya fara canza salo.


Matsalar da suka fara samu shine rashin son yin girki da Meema ba ta son yi saboda ba wani iya different foods tayi ba kasancewar tun tasowar ta ba ta shiga kitchen da niyyar yin girki har tafiyar ta turai karatu, ko a can tafi gane ma yin take away, sai in taso ne za ta yi simple food, ko da ta dawo gida Nigeria bai sa ta maida hankalin ta wajen koyan girki ba, abin da ta fi maida hankali shine dafa indomie da kuskus da dai irin simple food , sai dai ta ce ma Dr yaje restaurant ya musu take away, hakan ba k'aramin b'ata ma Dr rai yake yi ba kasancewar shi mai k'yank'yami ne, ba ya son cin abinci waje, hakan yasa wani lokacin yake zuwa gidan Momi yana cin abincin, ga fita da take yi without his permission, idan yayi mata magana sai tace mi shi tana da damar zuwa in da ta gadama dan ita ba matar kulle ba ce, ga yin shigar da ta gadama ko za ta fita ne ba tare da tayi la'akari da cewa a yanzu ita matar aure ce, gashi sometimes ba ta yarda dashi in zai yi love making da ita, sai dai in ita ta gadama, a tak'aice dai Meema nayi duk abin da ranta yake so.


Kasancewar shima Dr d'an Human right ne da koyi da rayuwar turawa yasa bai cika damuwa da sa mata ido akan al'amuran ta ba, daga baya ne da yaga abin na ta ba na k'are ba ne yasa suka fara kai ruwa a tsakanin su.


Wani lokacin in ya mata fad'a takan d'auka saboda son da take mi shi amma da an kwana biyu za ta dawo yin abin da ta gadama.


Tun Dr na mata fad'a akan abin da take yi har ta kai ga yanzu tana maida mi shi magana dan ita a ganin ta ba za ta iya rayuwar takura ba.


Wani lokacin in ya ma Momi complain akan halin Meema sai dai ta ba shi hak'uri dan tana ganin kamar yanakawo k'arar Meema ne dan ba choice d'in shi ba ce, daga baya da ta gano gaskiyar maganar da Dr yake fad'a mata akan Meema yasa ta ci gaba da bashi hak'uri had'e da kwantar mi shi da hankali.


Dr ya fara shiga damuwa akan irin wannan zaman da suke yi da Meema.


A lokacin ne ya fara danasanin rabuwa da yayi da ni, ga kewa ta dake addabar shi, hakan yasa damuwar ta mi shi yawa.


Shi kan shi in ka ga Dr kasan ya canza in kayi duba da ramewar da yayi.




Yau ranar ta kasance ranar lahadi, Dr yana gida yana hutawa yayin da Meema ke cikin d'aki.


Meema ce ta fito cikin wani irin material mai tsada transparent kalar pink yayin da yafa d'an k'aramin veil a kan ta.


Cikin takun k'asaita take tawowa, ba abin da kake ji sai k'arar takalmin ta, hakan yasa Dr ya d'ago ya kalle ta.


Cikin murmushi ta zo ta zauna kusa dashi.


D'aure fuska yayi yana ci gaba da kallon ta.


"Ina za ki ne Meema na ga kin yi shirin fita?".


Meema ta amsa mishi da cewa " Yau birthday d'in Leema, shine nake so in je".


Da mamaki Dr ya kalle ta ya ce "At this tym za ki birthday, yanzu fa aka yi sallar magrib, shine kike shirin fita, wai da izinin wa za ki fita".


"Haka aka yi fixing din tym d'in sannan kasan dai yanda mu ke da Leema, kasan ya kamata in halarci birthday d'in ta" Meema ta fad'a kai tsaye.


" Ba za ki ba" Dr ya fad'a.


Da sauri ta kalle shi ta ce "Because of what yaya Sadik za ka ce ba za ni ba".


Dr ne ya ce " Saboda ni ke da iko da ke tun da ina matsayin mijin ki".


"Amma Yaya Sadik kasan dai Leema ba za taji dad'i ba in ban yi attending ba saboda kasan she is my close friend" Meema ta fad'a cikin marairaicewa.


"That's your business not mine" Dr ya fad'a cikin ko in kula.


Wayar shi ya fara pressing ba tare da ya k'ara kula ta ba.


Mik'ewa tsaye tayi cikin b'acin rai ta ce " Am sorry Dr, but i must attend that birthday, akan nayi aure sai ka ce ba zan dinga fita ba, am social yaya Sadik, so gaskiya ba zan juri takura ba, sai na dawo Yaya Sadik".


Tana gama fad'ar haka ta nufi bakin k'ofa.


Bin ta yayi da kallo har ta fita daga d'akin.


Dafe kan shi yayi saboda a yanzu ba ya jin zai iya jurar abin da Meema ke mi shi.


Nadamar rabuwa da ni ne ya fara d'awainiya dashi.


A yanzu ya rasa mafitar da zai Samar wa kan shi.


Tashi yayi ya d'auki key d'in motar shi ya bar gidan.


A can b'angare na kuwa gashi ina Neman fin wata a Abuja amma har yanzu babu alamar komawa ta Kaduna.


Tun san da Yaya Faruk ya fad'a min magana san da na mi shi magana ya fad'a min magana na k'ara shayin in k'ara tunkarar shi da maganar.


Abbu ya kira yaya Faruk ya mi shi magana akan ya dawo dani Kaduna.


Yau ina zaune a d'aki Nana ta shigo ta sanar da ni yaya Faruk na kira na.


Bayan ta fita ne na biyo ta a baya.


D'aya daga cikin kujerun na nemi guri na zauna.


"Yaya Faruk sannu da hutawa" na fad'a.


"Yawwa" ya fad'a a tak'aice.


Ni ce na ce "Gani yaya Faruk".


"A satin nan in na samu free time zan maida ke Kaduna, Abbu mun yi waya dashi ya ce in dawo da ke".


" To yaya Faruk " na fad'a cikin sanyin murya.


Shiru ne ya ratsa kafin yaya Faruk ya d'aura da cewa "Za ki iya tafiya".


Tashi nayi na koma d'akin.


Abubuwa biyu ne suka had'un min a lokacin, farin cikin komawa ta Kaduna da kuma fargabar had'uwa ta da Abbu.


A satin yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki.


Ran da za mu tafi sai da na ji wani iri a raina saboda yanda muka saba da Nana.


Naji dad'in zama da ita saboda yanda ta ke sakar min fuska duk da tasan alak'ar soyayya ta tab'a had'a ni da mijin ta, halayen Nana sun burge ni saboda yanda ba ruwan ta da shiga harkar abin da ba ruwan ta, gashi magana ba ta dame ta ba.


Da za mu tafi haka ta had'o ni da tsaraba.


Har gurin mota ta raka mu, sai da ta ga fitar mu sannan ta koma cikin gida.


Tun da muka d'auki hanya ba Wanda ya kula d'an uwan shi har muka kawo Kaduna.


K'ira'ar Sheikh Shureim kad'ai ke tashi a motar.


Wannan tafiyar ba ta min dad'i ba saboda yanda shirun ya min yawa, shi yaya Faruk nasan daman magana ba damun shi tayi ba.


Tun da muka doshi gidan mu gaba na ke fad'uwa har mu ka k'arasa cikin gida.


Ko da muka isa parking space yaya Faruk ya riga ni fitowa.


Jiki a sanyaye na fito na bi shi.


San da na shiga samun yaya Faruk nayi suna gaisawa da Ummu.


Sallama nayi Ummu ta amsa min.


Tun da na shigo Ummu ta ke bi na da kallo.


A lokacin ba abin da nake buk'ata da ya wuce in ji ni jikin Ummu.


Jikin Ummu na fad'a na fashe da kuka.


Ummu cikin lallashi ta fara shafa baya na tana cewa "Miye abin kuka".


" Ummu am sorry, ki yafe min" na fad'a cikin kuka.


"Ya isa haka Auta, ai na ce na yafe miki, ki je d'aki anjima za muyi maganar".


Had'a ido muka yi dashi yayi saurin kau da fuskar shi.


Tashi nayi na tafi d'aki na, d'akin da na d'auki shekaru ba na kwana a cikin shi sai gashi a yanzu na dawo da niyyar zama a cikin shi.


Haka naci gaba da kuka na har bacci yayi awon gaba dani.


Bayan tafiya ta d'aki ne Ummu ta dinga yi ma yaya Faruk godiya a bisa rik'e ni da yayi.


Sun jima suna hira kafin ya mata sallama akan da daddare zai zo su gaisa da Abbu.


Da daddare tun da naji dawowar Abbu na rasa sukuni.


Ummu ce ta shigo ta min magana akan in fito in gaida Abbu.


Jiki a sanyaye na fito daga d'akin na tsugunna nesa da Abbu.


San da na gaishe da Abbu ba laifi ya amsa min ba yabo ba fallasa.


Abbu ne ya d'aura da cewa "Fatima, a yanzu nasan kin fahimci mecece rayuwa da yanda rayuwa ka iya canzawa a kowane lokaci, nasan a yanzu ki d'auki darasi ko akan abin da shi Sadik d'in ya miki, Ni da Ummun ki wani irin so da kulawa da so ne ba mu nuna miki ba amma saboda soyayya kika zab'i faranta ran ki akan namu farin cikin, a gaban mutane Fatima nasa miki sharad'i dan ki janye k'udurin ki amma ba ki duba hakan ba kika ce kin amince da sharad'in da na sa miki, ko a lokacin raina ya b'aci da abin da kika yi amma saboda fushi na illah ne a gare ki yasa nayi saurin yafe miki a lokacin, yanzu kin ga sakayayyar da Makauniyar soyayya ta jawo miki, shi yasa San da Faruk ya zo min da maganar ki na ce mi shi kar ya kawo min ke tun da ke da kan ki kika yarda da sharad'in da na sa miki, ko a yanzu na ji ciwon rabuwar da kika yi da shi Sadik d'in".


Maganganun Abbu ba k'aramin tab'a min zuciya yayi ba, nasan ban kyauta ma su Abbu ba.


Kusa da Abbu na zo na tsugunna ina cewa " Abbu ka yafe min, na gano kuskure na, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da nayi ba..." Na k'arasa maganar da fashewa da kuka.


Sunkuyar da kan shi Abbu yayi kana ya d'ago ya kalle ni ya ce " Na yafe miki Fatima".


"Na gode Abbu" na fad'a cikin kuka.


Ummu ce ta d'aura da cewa " Fatima ita Makauniyar soyayya da kike gani ba ta da amfani, ba abin da take jawowa fa ce danasani, duk soyayyar da idon ka zai rufe ba ka ji ba ka gani sannan ba ka duba me nan gaba za ta haifar maka sannan ba za ka ji shawarar da mutane suke ba ka akan ta ba, to wannan soyayya ba alkhairi ba ce, ina fatan kamar yanda kika fad'a cewa kin gano kuskuren ki hakan yake har cikin zuciyar ki, ina fatan kin d'auki maganar da ni da Abbun ki muka mi ki".


"Na d'auka Ummu, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da na yi a baya ba" na fad'a.


Haka Abbu da Ummu suka ci gaba da min fad'a da nasiha kafin daga bisani Abbu yace in tafi in kwanta.


Tun daga wannan lokacin na samu sukuni a raina had'e da walwala saboda yanda na samu yafiyar iyaye na.


Cikin ikon Allah sai gashi Allah ya cire min k'ulafuncin Dr a raina.


Na cire ma raina tunanin shi dan guje ma kaina wata matsalar.


A haka na ci gaba da zama a gidan mu.


Lokacin da muka yi waya da Aisha take cewa za tazo gida na nake fad'a mata rabuwar da muka yi da Dr.


Ta jajanta min kana ta ce min za tazo.


Ba a d'au wasu lokaci ba sai gashi tazo.


A hirar da muka yi da ita ne take fad'a min taji labarin Dr ya yi aure.


San da ta fad'a min ban nuna damuwa ta ba duk da a lokacin sai da na ji b'acin rai a zuciya ta.


Mun dad'e da ita muna hira kafin ta min sallama ta tafi.


A haka lokaci ya dinga tafiya, sai gashi har na gama iddah ta, har lokacin Dr bai maida ni d'aki na ba.


Hakan yasa Abbu yasa aka je gidan Dr aka d'ibo min kaya na.


Tun bayan tawowa ta daga Abuja muna waya da Nana muna gaisawa da ita, San da ta kira ni ne take fad'a min sun rubuta final exam d'in su, ta had'a Degree d'in ta, na taya ta murna kana muka yi sallama.


Yanzu ma Anisa tana final class d'in ta na Degree.



Yau muna zaune da Abbu da Ummu muna hira da daddare bayan tafiyar su Yaya Aminu da Yaya Khalil.


Bayan mun gama hirar ne Abbu ya kalle ni ya ce "Fatima tun da kin gama iddar ki, ina ganin ya kamata ki shirya ki je can Wagini gurin Hajiya, ina so in Neman miki aiki saboda ki rage zaman kad'aici, in an sami aikin zan sa Khalil ko Aminu su je so d'akko ki".


Jin tafiya ta Wagini yasa jiki na ya k'ara sanyi, a yanda na fahimta in na tafi Wagini ban San ranar dawowa ta ba tun da Abbu yace sai ya Samar min aiki, babban fargabata shine yanda in naje Hajiya za ta tasa ni gaba akan rabuwa ta da Dr dan tun lokacin da ban auri yaya Faruk ba tasa ni a gaba, nasan in dai naje Wagini sai nayi hak'uri da Hajiya, a yanzu ban da kuma damar cewa Abbu ba na son zuwa Waginin ko dan kar in b'ata ma Abbu rai.


" Allah ya kaimu Abbu" abin da na iya fad'a kenan.


"Amin Fatima" cewar Abbu.


Jiki a sanyaye na tashi na tafi d'aki.
[10/2, 20:56] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



www.maryamahmadpaki.blogspot.com


facebook: Kainuwa Writers Association





_Ina mik’a sak’on gaisuwa ta da fatan alkhairi ga wanda suka kira ni a waya, da wanda suka min magana ta pc da groups akan rashin lafiyar da na yi_.


_Ba abin da zan ce muku sai dai in muku godiya a bisa yadda ku ka nuna kulawar ku gare ni_.


_Allah ya bar zumunci ya saka muku da mafificin alkhairi_.


_Allah na ke rok’o gaba d’aya ya biya mana buk’atun mu na alkhairi ya kuma yaye mana damuwar mu_.


_Allah ka zab’a mana abin da yafi zama alkhairi a gare mu_.




*TUNATARWA*: *JAN HANKALI*



*IDAN KA/KI AIKATA ABUBUWA UKU IMANIN KA/KI ZAI K’ARU:*


1. *Tilawar Alk’ur’ani*.


2. *K’iyamul- laili*.


3. *Azkar*



*Za ka/ki fuskanci matsala a kabarin ka/ki idan ka/kika mutu da abu uku:*


*Hakk’in wani*


*Dabi’ar Annamimanci*


*Hassada*



*Abubuwa uku su na kau da Fushin Allah akan bayin sa*


*Istigfari*


*Tausaya ma wani*


*Sadaka*


*Ya Allah ka bamu ikon kiyayewa*🙏🏽





99-100


Tun da na koma d’aki nake tunanin tafiyar da za mu yi wagini, tunanin da ya tsaya min a rai shine yadda zaman mu zai kasan da Hajiyan wagini idan na je Waginin dan na san dole ne sai na toshe kunne na a duk abin da za ta fad’a min min, matsala ta ita ce ban san tsawon lokacin da zan d’auka a can ba, abin da na sa ma raina shine in yi hak’uri da duk abin da zan fuskanta a gurin Hajiyan wagini, da wannan tunanin na samu na ajiye tuanin tafiya ta Wagini.


A na gobe za mu tafi Abbu ya kira ni ya sanar dani in had’a kaya na gobe za muyi tafiyar in had’a kaya na.


Amsa mishi na yi da Allah ya kaimu kana na tashi na koma d’aki.


Ummu ce ta shigo d’akin ta same ni bayan na koma.


A yanayi na da ta kalla tasan ina cikin damuwa akan wannan tafiyar da za mu yi, ita kan ta na lura kamar Ummu tafi son in zauna kusa da ita, sai dai ba yanda za tayi ne.


Ummu ce ta kira suna na "Fatima".


Amsa mata nayi da cewa "Na’am Ummu".


Ummu ce ta ce "Fatima ba na so ki sa damuwa akan wannan tafiyar da za ki yi, da nan da Wagini duk d’aya ne, ni kaina zan fi so ki zauna a nan d’in amma tun da Abbun ki ya ce za ki zauna a can ne Kafin ya sama mi ki aiki, nasan ko da aikin bai samu da wuri ba zai iya cewa ki dawo, ina so ki natsu Fatima dan ke ba yarinya ba ce, duk abin da kika ga ya samu bawa rubutacce ne daga gurin ubangiji, ba na so ki ci gaba da sa damuwa a ranki akan abin da ya faru da ke, idan kin je Waginin ba na so ki yi abin da Hajiyan Wagini za ta ce kin manta ko ki nuna b’acin ran ki akan wata magana da za ta fad’a miki, duk abin da Hajiyan wagini za ta fad’a mi ki ke kika ja ma kan ki tun da a farko kin k’i jikan ta, dole ne taji haushi, kowa yasan Hajiyan wagini mutuniyar ki ce a baya, tun kan abin da ya faru take fushi dake, ni ma kuma ban ga laifin ta ba, nasan idan ta huce za ku shirya ne, ita kan ta Hajiyan nasan in ta ji abin da ya same ki za ta sakko daga fushin da take yi, nasan daman tunanin zuwan ki wagini da kike yi kenan da kike yi kenan".


"Insha Allah Ummu babu wata matsala" na fad’a.


Murmushi Ummu tayi kana ta ce "yawwa Auta ta".


Nima murmushin nayi.


Da haka muka canza wata hirar.


Washegari ni da Abbu muka d’auki hanyar Wagini.


Wajen la’asar muka isa Wagini.


Da zuwan mu Hajiya tarbe mu da abinci kala-kala kasancewar Abbu ya fad’a mata zuwan mu.


Bayan mun huta ne Ummu ta kalle ni ta ce "Laila-Majnun ashe har da ke aka zo, ina kika bar Majnun d’in naki".


Sunkuyar da kaina nayi ba tare da nayi magana ba.


Maida kallon ta tayi gurin Abbu kana ta ce "Ibrahim ina fatan dai lafiya ko, tun da ka ce min kana nan zuwa da Fatima na ke ta tunanin Allah yasa lafiya".


Abbu ne ya amsa mata da "Lafiya lau Hajiya, daman Fatima na kawo za ta zauna a nan ta kwana biyu kafin ta koma Kaduna".


Hajiya ce ta amshi maganar da cewa "Ibrahim ban son shiririta, me ya faru da za ta zauna a nan, ina ta bar mijin na ta, ko shi mijin ne ya ce ta zo tayi hutu a nan".


"Ko d’aya Hajiya, sun rabu da mijin ne, yau sama da wata uku kenan, shine na ce bari in kawo ta nan kan in samar mata aiki ta fara zuwa" cewar Abbu.


Da sauri Hajiya ta ce "Yau na ji abin da ya fi k’arfi na, kana nufin wai shi mijin na ta ya sake ta, yanzu sakayyar da yaron nan zai mana kenan shi ne zai maida min jika k’aramar bazawara, duk irin son da yarinyar nan ta nuna mishi amma shine zai mata haka, soyayyar da Fatima ta nuna mishi ni ina jin in ba a irin wasan indian nan da nake jin labari ba na dad’e ban ga irin soyayyar haka ba, saboda shi tambad’ad’d’en yaro ne shine zai mata sakayya da butulci, amma wannan yaro ko watsatstse, yanzu da d’an uwan Soja ki kika aura ai da ba ki fuskanci haka ba amma ki ka na ce sai wannan Likitan, yanzu ba ga irin sakayar da ya saka mi ki da ita ba kenan, kema ai da laifin ki da kika na ce sai shi kika nuna mi shi makauniyar soyayya shi yasa zai mi ki sakayya da haka dan jakar uban ki, oh ni na ga abin da zan gani".


Hajiya na gama maganar ta fashe da kuka.


Da lallashi da k’yar Abbu ya samu tayi shiru.


Ganin hakan yasa na tashi na shiga cikin d’akin Hajiyan Wagini dan nasan ci gaba da zama na a falon zai sa Hajiya ta ci gaba da min mitar ta.


Wajejen k’arfe biyar Abbu ya d’auki hanyar komawa Kaduna.


Ranar na sha mita a gurin Hajiyan wagini, ganin duk maganar da za ta min da ta danganci akan Dr ne ba na kula ta yasa ta gaji tayi shiru.


Haka zama na ya ci gaba da gudana a Wagini tun ban saba da zaman garin ba har na zo na saba.


Sai da na d’auki kusan Wata biyu a can kana Abbu ya turo yaya Khalil ya zo ya d’auke ni.


Ran da zan tafi haka Hajiyan Wagini ta dinga kuka wai zan tafi in bar ta bayan ta saba zama dani.


Ni kaina sai da nayi hawaye dan nima zaman garin ya min dad’i.


Da haka muka yi sallama da Hajiya muka tafi.


A hanya haka muka dinga hira da yaya Khalil a cikin mota har muka k’arasa Kaduna.


Sati na d’aya da dawowa Abbu ya kai ni in da ya samar min aiki a Bureau of Statistics.


Sai da suka min intetrview suka ce za su neme ni.


Bayan kwana biyu da yin interview d’ina suka turo min message a Gmail d’ina sun d’auke ni aiki.


Na yi murna da wannan aikin da na samu dan nasan zai d’ebe min kewa da tunani.


Haka na fara suwa aiki na cikin kwanciyar hankali.


Ban wani dad’e ba na saba da ma’aikatar gurin sannan ta b’angare na ina jin dad’in aikin.


Cikin haka ita ma Anisa ta had’a Degree d’in ta.


A yanzu baa bin da na sa a gaba na da ya wuce aikin da nake yi dan a yanzu ina ganin soyayya ta koya min darasi.





A b’angaren Dr kuwa kullum zaman shi da Meema abin yak’i daidaituwa yayin da damuwar shi ke ci gaba da danasanin rabuwa da ni da yayi da kuma matsanancin so na da ke addabar shi.



Yau ranar ta kasance ranar lahadi.


Dr ne a zaune a gurin hutawa da aka k’eb’e a gidan.


A kan table d’in drinks ne kusan kala uku a ajiye da d’an k’aramin kofi a ajiye.


Wayar shi da ke hannu shi yake kallon wani pix d’ina da ke gallery d’in shi.


Bai ji tafiyar Meema ba sai ganin ta yayi a gaban shi.


Wani dogon tsaki ta ja kana ta d’aura da cewa "iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu kai yaya Sadik ba ka da aiki da ya wuce ka tasa hoton tsohuwar matar ka a gaba kayi ta kallo, kasan kana son ta ka rabu da ita, in ban da abin ka yaya Sadik ga ni ka samu mai za kayi da wata banza wacce ba ta fi ni da komai ba, in son da take nuna maka ne ina ganin ai nafi ta son ka".


Daman a cike yake da Meema ga kuma maganar da take fad’a mishi ba tare da ta tauna harshen ta ba dan haka tashi yayi ya tsinka mata mari wanda ya girgiza ta.


Kuka ta fashe dashi tare da rik’e kuncin ta.


Cikin kuka ta ce "Yaya Sadik you slap me".


"Yes na mare ki ko za ki rama ne" Dr ya fad’a cikin hassala.


Meema ce ta ce "Dan na fad’i gaskiya shine za ka mare ni, to yanzu na sa k’afar fad’a maka gaskiya, dan ba zan juri ganin kana kallon hoton wata y’ar iska ba a cikin gidan nan".


Yanda Dr yake jin ran shi a b’ace yana ganin zai iya ma Meema hukuncin da bai kamata ba dan haka cikin tsawa ya ce "Meema you better leave this place or else I will teach you a lesson sannan da kike maganar Zarah in dai a waje na ne ta fi ki komai a guri na, son da na ke mata ba zan tab’a miki irin shi ba, son ta daban yake a cikin zuciya ta, ke in ban da darajar Momi da kika ci da kuma tausayin ki da nake yi da zan aure ki ne har za ki samu damar yi min rashin kunya".


Ci gaba yayi da cewa "Meema ba ki san ni ba ne, k’yale ki kawai nake yi".


Ganin yanda ran shi ya ke a b’ace yasa ya bar gurin dan yasan ci gaba da tsayuwar shi a gurin zai iya sa ya yanke ma Meema mummunan hukunci.


Tun da ya bar gurin Meema ta bi shi da kallon mamaki.


Washe gari Dr bayan ya dawo aiki ya wuce gidan Momi.


Bayan sun gaisa ne

Please Login or Register in order to submit comment