Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai gyaran jiki ta musamman dan ta min gyara na musamman.

Yanzu ba laifi su Abbu ma suna zama mu d’an yi hira, hakan ya rage min damuwar da na ke ciki.

Yaya Khalil ma yana tambaya na ko akwai abin da na ke buk’ata.

Yaya Aminu ma yana kawo Anty Jiddah ta wuni, ita ma haka ta kawo min tsarabar magunguna na sha, har da turarurruka na tsugunnawa ta kawo min, sannan tana zaunar dani ta fad’a min dabarun zamantakewar aure, ina jin dad’in yadda Anty Jiddah take ba ni kulawar ta, hakan yasa na ke k’ara ganin girman ta da mutuncin ta.

Momi da ita ake gudanar da shirye-shiryen bikin, yanzu ta rage fushin da take yi dani, in na gaishe ta cikin fara’a take amsa min.

Anisa ma ta na zuwa a gudanar da shirye-shiryen bikin, sai dai ba ta sakin jikin ta wajen gudanar da shirye-shiryen.

Hajiyan Wagini ce har yanzu ba ta huce ba, hakan yasa nima naji dad’in zaman ta a gidan su Anisa, sai dai idan tazo ne nake kauce ma had’uwar mu, dan in dai muka had’u sai tasan yadda tayi ta fad’a min maganar da ta ‘bata min rai.

Aisha ma tun san da taji abin da ya faru na fasa aure na da yaya Faruk, ta nuna rashin jin dad’in ta.

Gidan mu ya fara cika da ‘yan uwa da abokan arziki.


Yau ne ya kasance za mu yi Bridal shower, shigar cot less nayi fari na doguwar riga, yayin da aka rubuta min *BRIDE TO BE* da farin rubutu wanda aka yi min crossing d’in shi akan rigar, nad’in da aka min na head kalar light silver aka min, takalmi ma kalar light silver na saka.

Kwalliyar da nayi ba k’aramin amsa ta tayi ba.

K’awaye na kuma shigar tommy skirt da polo suka yi.

A farfajiyar gidan mu muka yi event d’in.

Music kala-kala aka dinga playing a Bridal shower d’in.

K’awaye na sun cashe a wannan ranar.

Gaskiya Bridal shower d’in ya k’ayatar.

A ranar ne dangin Dr Sadik suka zo suka sa ni a lalle tare da ba da kud’i mai yawa na sa lalle.


Washegari ran juma’a ya kasance ranar d’aurin aure na, a ranar ne kuma zan yi walima.

Da misalin k’arfe biyu na rana aka d’aura aure na ni Fatima Ibrahim Wagini da Dr Abubuakar Sadik Muhammad a k’ofar gidan mu.

D’aurin auren da ya samu halartar manyan mutane daban- daban.

Ina jin sanarwar an d’aura aure na samu kaina da wani irin fad’uwar gaba, yayin da hawaye suka zubo min a lokacin.

Ni kaina ban san hawayen me nake yi ba, amma na alak’anta hakan da hawayen farin ciki ne nake yi ganin na auri wanda nake so da kuma k’alubalen da na fuskanta Kafin auren, nasan komai yazo k’arshe tun da Allah ya nufa na kasance matar Dr Sadik.

Tsintar kaina nayi cikin farin ciki, damuwar da nake tare da ita na tsawon lokuta duk na ji ba bu ita a lokacin.

Yau Allah ya cika min burin a da ya nufa na samu Dr a matsayin miji.

Haka na ci gaba da gudanar da taron biki na cikin walwala, kowa ya ganni a lokacin yasan ina cikin farin ciki.

Walima ma a farfajiyar gidan mu nayi, Malama Khadija Muhammad ce ta gabatar da muhadara mai taken _Zamantakewar aure a Musulunci_
Malamar tayi bayani akan yadda zaman aure ya kamata ya gudana a tsakanin miji da mata ta fuskar musulunci, malamar ta jawo hankalin mata yadda za su gudanar da rayuwar su a gidan aure.

Haka dai Walimar ta k’ayatar kana aka tashi daga Walimar.

Dr Sadik yazo da abokan shi mun d’auki hotuna, haka muka sha hotuna da su Anisa da Aisha da Halima da k’awaye na, yaya Khalil ma yazo mun yi hotuna dashi, wani mun d’auka ni dashi, wasu hotunan kuma mun d’auka har da Anisa a ciki.

Yaya Faruk ya ba da gift da kyautar kud’i ya ba ma Momi ta kawo min, a ranar na samu labarin tun bayan d’aura auran mu ya tafi Abuja, na so mu had’u dashi in mishi godiya ko da ba zai amsa min ba.

Hak’ik’a nasan yaya Faruk daban ne da har ya iya min kyauta ba tare da ya duba abin da ya faru a tsakanin mu ba.

Hankali na bai tashi ba sai da naji an ce ga motoci can a waje na d’aukar amaryar sun zo, nan nemi farin cikin da nake ciki na rasa.

Kuka na dinga yi san da aka kai ni gurin Abbu in mishi sallama, shi kanshi Abbu a lokacin na bashi tausayi, nasiha ya min akan zamantakewar aure tare da min fatan samun zaman lafiya a d’aki na.

Nasan Abbu ya nuna min gata da so, in ban da matsalar aurena da yazo da matsala har Abbu yayi fushi dani, in ban da wannan matsalar Abbu bai cika nuna fushin shi gare ni ba.

D’akin Ummu aka kai ni, muna shiga na fad’a jikin ta na ci gaba da kukan da na ke yi, ita kanta Ummu duk fushin da take yi dani, sai ta neme shi ta rasa, ganin irin kukan da nake yi ne yasa ita ma hawaye ya fara zuba a idon ta.

"Fatima yau Allah ya nuna min ranar auren ki, ba abin da zan ce sai dai in ma Allah godiya da ya nuna min wannan ranar, Fatima aure ba abin wasa ba ne, kar ki dan kin auri wanda kike so ki yi zaton ko ba za ku samu sa’bani ba, aure zaman hak’uri ne, kowa da kike gani shi yake yi a d’akin shi, a yanzu ne da zama ya had’a ku za ki k’ara sanin halin shi yasan naki, dole ne ki kiyaye duk abin da ba yaso, yi nayi bari na bari, ki yi hak’uri da ‘yan uwanshi da iyayen shi, ki kyautata musu kamar yadda za ki kyauta mana, ki koyi hak’uri, juriya, kawaici, shi zai kai ki matakin samun zaman lafiya a d’akin ki, ki kula da tsafta, kissa, kwalliya, girki, wannan abubuwan da na lissafo miki da na ce ki kula suna da fad’i, shi yasa na baki su a dunk’ule, su ne za su k’ara miki daraja a gurin mijin ki, Auta ki yi hak’uri da duk halin da za ki tsinci kan ki a d’akin mijin ki, kin ga dai ke ki ka za’be shi a matsayin miji, saboda haka ki yi hak’uri kin ji Auta, Allah ya baku zaman lafiya".

"Ummu ki yafe min duk laifin da na miki" Na fad’a cikin shashshek’ar kuka.

"Na yafe miki Auta, tashi ki tafi kin ga ana jiran ki".

K’ara shigewa jikin ta nayi na ci gaba da kuka na yayin da Ummu taci gaba da lallashi na.

Da k’yar aka samu aka cire ni daga jikin Ummu ina kuka aka fita dani daga d’akin.

San da muka fito farfajiyar gidan ne na hango yaya Khalil zaune a saman motar shi.

Gurin yaya Khalil na wuce na kwanta a jikin shi ina ci gaba da kuka, shi kanshi daga gani dauriya kawai yake yin a tafiyar da zanyi.

D’ago ni yayi yana girgiza min kai alamar in daina kukan, a lokaci d’aya kuma yana goge min hawaye.
"Ki daina kuka kin ji Auta, ki zauna lafiya da Dr, in an kwana biyu zan zo in duba ki ko ba kya so" ya fad’a a hankali.

Cikin kuka na ce "Ina so yaya Khalil".

"Yawwa Fatima, yanzu ki tafi kin ga ana jiran ki, zan kira ki a waya".

Maimakon in tafi sai ma sake fashewa nayi da wani kukan, hakan yasa ya rik’e min hannu, gurin Anty Zainab (k’anwar Ummu) ya kai ni ta rik’e min hannu.

Juyawa yayi ya wuce side d’in shi, dan a yadda yake ji ba zai juri ganin tafiya ta ba.

Allah Sarki yaya Khalil, duk a cikin gidan mu na fi shak’uwa dashi, abokin shawara na, mu yi fad’a mu yi wasa haka muke dashi, yau gashi a dalilin aure zan yi nesa dashi, sai kuma na zo gida ko shi ya kawo min ziyara.

Kinkinau aka kai ni, nan Dr Sadik ya gina gidan shi.

Gida ne mai matuk’ar burgewa ga duk wanda ya kalla, filawowin da aka zuba ne a gidan ya k’ara k’awata gidan.

San da muka fito daga motan ne Anty Zainab ta fad’a min in zan shiga in shiga da k’afar dama.

Lokacin da na zo shiga ban manta da abin da Anty Zainab ta fad’a min ba, haka ne yasa na k’ara da addu’a a raina na neman zaman lafiya a tsakani na da Dr Sadik.

Falo biyu ne a had’e wanda za a iya shiga ta gaban gidan da kuma ta ta cikin gida, falo na biyu aka kai ni inda aka jera min kaya na..
Falon da aka kai ni ba k’aramun tsaruwa yayi ba, nan na k’ara ganin kayan alatun da Abbu ya zuba min.
Bedroom aka wuce dani, nan ma ba k’aramin tsaruwa yayi ba.

Ba abin da zan ce ma Abbu da Ummu sai godiya.

Momi da Anty Zainab ce suka ci gaba da min nasiha akan zaman aure wanda yasa jiki na yayi sanyi.

Sadik ne ya kira ni akan in shirya yanzu za a wuce Dinner, ga motoci nan ya kawo.

Anty Zainab ce ta shirya ni cikin wani white gown d’in nan ce mai jan kasa, tana da adon silver a jikin flower d’in, a jikin rigar akwai duwatsu masu shining, head d’in da Anty Zainab ta d’aura min kalar golden, jakar da na rik’e irin wacce amarya ke rik’e wa ita ma kalar golden, haka ma takalmin da na saka, bayan na shirya ne ta sa min gyalen wanda yake zuwa had’e da kayan shima yana jan k’asa.

Dr Kamal ne ya d’auke ni da Dr Sadik ya kai mu inda za a yi Dinner d’in.

Hall d’in ya cika da ‘yan uwa na da da ‘yan uwan Dr Sadik.

Bayan mun zauna a grin da aka ware mana na zaman Ango da Amarya kana aka fara gabatar da program of event.

Mc ya umarci da mu fito fili mu taka rawa, abokan Dr Sadik da k’annen shi haka suka dinga mana lik'in kud'i, a ‘bangare na ma su Anisa da su Halima haka su ma suka dinga min lik'in kud'i.

An ci an sha a gurin Dinner d’in, da haka taron ya tashi.

Dr Kamal ne ya tsaya a gurin sai da kaji ya siya sannan ya tsaya ya siya Drinks kana ya wuce damu gida.

Ina zuwa gida na wuce toilet na watsa ruwa saboda gajiyar da nayi kana na d’auro alwala.

Wata had’ad’d’iyar night gown na sa na shafa humra kana na d’aura hijab na yi shafa’i da wuturi kasancewar sai da nayi sallar isha’i kafin mu tafi Dinner d’in.

Bayan na idar ne na kwanta akan gado saboda wani irin barci da nake ji.

Barci har ya fara d’auka na naji shigowar Dr Sadik d’akin.

"Zarah ba dai har kin kwanta ba, ko abincin baki ci ba?" Dr ya fad’a a hankali.

Cikin muryar barci na ce "Na gaji ne Dr, ga wani irin barci da nake ji shi yasa na kwanta".

Wani irin kallo ya watsa min mai kashe sassan jiki ya ce " Ki sakko ki ci wani abun, kin san yunwar dare tana illah, in ban da abin ki ma Zarah ai yau ba ki da barci".

Fahimtar in da maganar shi ta nufa yasa ta ce cikin shagwa’ba "Haba Dr, Allah kuwa bacci nake ji".

Hannun shi ya mik’o min ya ce "Common, tashi ki ci wani abun, in ba haka ba sai in miki allura".

Hannuna na mik’a mishi ya rik’e muka wuce side d’in shi.

‘Bangaren Dr ma ya had’u, yanda aka shirya side d’in kamar na wata amaryar duk da ba a zuba tarkace da yawa a falon ba, hakan bai hana falon tsaruwa ba, cikin bedroom d’in ma ya k’ayatar.

Plate yasa na d’akko da cup, naman kazan yasa na zuba a plate.

Saboda baccin da nake ji yasa ban wani ci naman sosai ba ga kuma rashin sabo, hakan yasa Dr ya dinga bani da kanshi, shagwa’be min yayi akan nima sai na bashi, haka na d’auka ina bashi yana ci, bayan mun gama ci ne ya tsiyaya min drinks d’in cup yana ba ni, ragowar naman na d’auka na kai frij na saka a ciki.

Bayan mun gama cin naman ne yaje ya d’auro alwala, yana fitowa yasa ni naje na d’auro alwala.

Sallah muka yi raka’a biyu kana ya kama kaina ya dinga jero addu’o’i akan Allah ya bamu zaman lafiya.

Tashi nayi da niyar in koma side d’ina saboda baccin da nake ji kamar zan fad’i.

Dr ne ya kalle ni ya ce Ina zaki ne Zarah".

Amsa mishi nayi da cewa "Side d’ina zan koma in kwanta".

Murmushi yayi ya ce "Ai baki da gurin kwanciya da ya wuci nan d’akin a kuma jikin mijin ki".

Sunkuyar da kaina nayi ganin yadda Dr yake son sa ni jin kunya.
"Zo mu je ki kwanta kin ji Zarah ta" ya fad’i hakan yana rik’e min hannu.

Bin shi nayi na hau can k’arshen gado na kwanta.

Murmushi kawai yayi ganin in da na kwanta a k’arshen gadon, gadon ya kwanta.

Duk da baccin da nake ji kasa baccin nayi saboda Dr da ya hau gadon.

"Zarah" Dr ya kira suna na.

Shiru nayi kamar mai bacci, dan yau a tsorace nake da Dr.

"Zarah nasan idon ki biyu ba ki yi baccin ba, pls come close to me" Dr ya fad’a a hankali.

Saboda tsoron da nake ji yasa na kasa matsa wa kusa dashi, hakan yasa ya matso kusa dani ya kwantar dani a jikin shi.

Lumshe ido nayi saboda yadda jiki na da na Dr suka had’u, ga kuma rashin sabo.

A hankali ya fara magana da cewa "Alhamdulillah, All praise be to Allah, yau Zarah ke ce a matsayin mata ta, ban san yadda zan fasalta farin cikin da nake ciki ba, nasan ba wayau na ko dubarata ba ce yasa na mallake ki a matsayin mata ta, sai dai in ma Allah godiya akan ni’imar da ya min da ya bani ke a matsayin mata ta, ke fa Zarah wani farin ciki kike ciki akan wannan ranar".

A hankali na bud’e ido na da na lumshe na ce "Dr farin cikin da nake ciki baki na ba zai iya furta wa ba, Dr ina maka so wanda ni kaina ban san lokacin da ya min wannan kamun ba, sai dai in gode ma Allah da ya cika min burina na same ka amatsayin miji, alfarmar da zan nema a gurin ka shine Dr ka so ni kamar yadda nake son ka, ka rik’e ni amana, yanzu kaine gata na".

Murmushi yayi ya fara cire min hijabin da ke jiki na, yayin da ya fara shafa min kaina da yasha retouching.

"Kar ki damu Zarah, am yours, u a mine".

Haka muka ci gaba da musayar kalamai masu kwantar da hankali.

A hankali Dr ya canza hirar da salon soyayyar shi, sak’onni yake aika ma ko wani sassa na jiki na.

Dr ya nuna min tsantar so mai wuyar fasaltuwa had’e da kulawa a wannan daren.

Ranar na k’ara tabbatar da babu abin da yafi dad’i fiye da kasancewa da wan da kake so.

Haka muka raya wannan daren irin yadda masoya ke kasancewa a daren su na farko.

Haka muka tsarkake jikin mu muka koma muka kwanta.

Da asuba Dr ne ya tashi ya d’auro alwala ya tafi masallaci yayi sallah.

Sai da ya dawo daga masallacin sannan ya zo yana hura min iska a kunne.

A hankali na fara bud’e ido na, dan har yanzu bacci ne a cikin ido na.

Muna had’a ido nayi sauri na rufe ido na saboda wata irin kunyar shi da nake ji a yanzu.

Murmushi yayi ya ce "Kunya ta kike ji, Sorry princess Zarah na tashe ki, sallah za ki tashi ki yi, in kika yi sallar sai ki zo mu kwanta, nasan jiya ban barki kin kwanta da wuri ba".

A hankali na tashi saboda yadda na ji kasala da ciwon jiki ya kama ni, ga zazza’bi da yake so ya rufe ni.

Tashi nayi na shiga toilet na d’auro alwala na fito na ta da sallah.

Bayan na idar ne na yi addu’o’i na dawo na kwanta.

Dr ne ya janyo ni jikin shi, zafin da yaji jiki na yayi ne yasa ya ce "Oh God, Zarah ni na yi causing d’in wannan fever ko, sorry me yasa ba ki fad’a min ba".

Lamo nayi a jikin shi ban ce mai komai ba.

Kwantar da ni yayi ya je ya had’o ruwan allura, da k’yar na tsaya ya min saboda yadda ba na son allura.

Koma wa bacci muka yi ni da Dr, ba mu tashi ba sai wajen k’arfe takwas na dare.

Side d’ina na koma na yi wanka na saka atamfa super Holland d’inkin riga da skirt, simple make-up nayi.

Momin su Dr ce ta aiko mana da breakfast, Farida ce ta kawo breakfast d’in, mun gaisa cikin mutunci, ba yadda banyi da ita ta zauna mu yi breakfast ta ce min sauri take yi tana da lectures d’in safe, alamun ta na nuna ba ta da hayaniya.

Ragowar naman kazan da muka rage na je na yi warming d’in shi a Oven, dashi muka had’a muka yi breakfast.

Bayan mun gama breakfast ne ya bani magani na pain relief na sha.

Dr ne ya sanar dani zai je gidan su Momi ya gaishe ta.

Bayan tafiyar shi ne na tashi na wanke kayan da muka yi breakfast kana na je na gyara side d’in Dr.

Ranar haka na dinga bak’i daga ‘yan uwana da ‘yan uwan Dr, Anisa ma da Halima da Aisha sun zo, da yamma Aisha da Halima suka min sallama suka tafi.

Su Momi da Anty Zainab sun k’ara gyara gidan.

An kai ni gidan su Dr an gabatar dani a matsayin matar Dr, an nuna ni gurin ‘yan uwan Dr.

Gidan su Dr ba k’aramin had’uwa yayi ba, kai da gani kasan kud’i ya zauna a gidan.

San da za mu tafi ne Momi ta ba da kud’i masu yawa a ba ni.

Muna dawowa na shiga wanka na canza shiga ta cikin wani tsadadden less.

Gidan ya rage daga ni sai Anisa, itama rok’on ta nayi akan ta bari Dr ya dawo sai ta tafi.

Dr na dawowa Anisa ta kira Driver yazo ya d’auke ta.

Da za ta tafi ne naje na d’akko mata turare da wani material da kayan make-up a cikin akwati na, sai da na nuna ‘bacin raina sannan ta amsa.

Raka ta nayi bakin k’ofa inda na ce mata "Anisa pls ki dinga zuwa kin ji, ki gaishe min da yaya Khalil".

Ganin yadda na marairaice ne yasa ta ce min "In ina free zan dinga lek’o wa, zan Isar da sak'on ki ga Yaya Kalil".

Da haka muka yi sallama da ita na koma ciki.

Yau ma haka muka kasance cikin nuna ma junan mu zallar so da k’auna.

Sai da muka d’auki sati d’aya ba inda Dr yake zuwa kasancewar an bashi hutu a gurin d’aki, ko ya fita ba ya dad’e wa yake dawowa.

Hanan da Farida sun zo sun wuni, ganin Hanan ba ta wani sake jikin ta mun yi hira ba yasa muka dinga hira da Farida.

Yau da daddare da za mu kwanta ne Dr ya d’akko ruwa a cup da wani pills ya mik’o min.

Bin shi nayi da kallo nayi ina jiran k’arin bayani.

Cikin shagwa’ba na ce "Dr ai yanzu ba in da yake min ciwo".

Kallon da yake sa ni a cikin wani shauk’i ya min kana ya ce "Wannan ba pain relief ba ne, na family planning ne".

Da sauri na kalle shi dan gasgata maganar shi, ya za ayi sati na d’aya a d’aki na ya ce in fara shan pills na family planning.

"Ban gane ba Dr, ni me zan yi da pills d’in family planning da za ka bani na sha" Na tambaye shi.

"Ina so ki fara shan pills d’in ne saboda ina so ki huta kafin ki d’auki ciki, ba na so ki sha wahala wajen laulayin nan, kin ga kuma ina so ki koma School ki had’a HND d’in ki, kin ga yanzu ki na samun ciki za ki haihu, hakan zai sa ki raba hankalin ki gida biyu wajen rainon baby da karatun ki, ki bari in kika yi nisa a karatun ki sai ki daina shan pills d’in".

Kallon Dr kawai nake yi san da yake min wannan bayanin, ni a gani na ban ga dalilin da zan sha wani pills ba, hasalima ni tsoro nake ji yadda ake samun matsala wajen yin family planning.

"Dr ina ganin ba sai mun yi family planning ba, ka ga wani lokacin yana zuwa da matsala, kuma ni ina ganin baby ba zai hana ni karatu ba, ina ganin a bar zancen family planning d’in nan, Sai ka ga ma Allah bai kawo cikin da wuri ba ko da ba ayi family planning d’in ba".

Dr haka ya ci gaba da fahimtar dani akan in yi hak’uri in sha pills d’in amma na k’i, hakan yasa ranshi ya ‘baci ya ce in tashi in koma side d’ina.
[7/24, 22:37] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



www.maryamahmadpaki.blogspot.com

Facebook: Kainuwa Writers Association





*QUESTION OF THE DAY*

_Wace surah ce take karantar da wajibcin tsare hakk’ok’in mutane, tsakaninsu, a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa_.





75-76

Ina fita daga side d’in Dr na wuce side d’ina na zauna a kan gado.

Tunani na ci gaba dayi akan pills d’in da Dr yake so in sha daga yin auren mu da sati d’aya, duk da hujjojin da ya bani bai gamsar dani ba da zai sa in fara shan maganin tsarin iyali ba tare da na jira na ga tsarin da Allah ya tsara min ba.

Nasan Dr k’wararre ne a ‘bangaren aikin shi, ba zai bani pills d’in da zai zamar min illah ba amma ni a nawa ganin kamar yayi wuri in fara shan pills d’in family planning.

Abin da yafi min yawo a raina shine akan wannan matsalar muka samu matsala da Dr, ban yi tunanin wannan matsalar zai sa Dr yayi fushi dani har yace in koma side d’ina.

Ni ina da nawa dalilin na k’in ba Dr had’in kai wajen bijire ma shan pills d’in da yake so in sha in nayi duba da ko wata ban yi ba da yin aure amma yake so in sha pills, na sha samun labarin yadda wasu suke samun matsala a yayin da suka yi family planning, wasu ma dalilin daina haihuwar su kenan a yayin da suke so Allah ya basu yaran da sauran matsalolin da suke biyo baya a dalilin yin family planning d'in.

Hujjar da Dr ya bani na cewa yana so in yi karatu na ba tare da matsala ba da kuma tausaya min laulayin ciki da zan yi idan na samu ciki shine hujjar shi akan in sha pills bai ishe ni hujjar da zan yi dogaro da ita wajen amince ma buk'atun shi.

Haka na ci gaba sak’a da warwara akan samo mana mafita tsakani na Dr, dan ba na so wannan matsalar ta zama hanyar rusa mana farin cikin mu da muka fara gina wa a rayuwar auren mu.

Zuciya ta ce ta dinga ba ni shawarar akan in amince da buk’atar da Dr yazo min dan nasan ba zai cutar dani ba.

Da wannan na yanke shawarar akan gobe in Allah ya kaimu zan shaida ma Dr na amince da buk’atar shi.

Haka na kwana cikin kad’aci saboda yadda na saba kwanciya a jikin Dr, ya min sabo da jikin shi.

Washegari haka na tashi na had’a mana breakfast na jera a dinning table.

D’akin Dr na wuce inda na same shi har yayi shirin shi na tafiya aiki kasancewa ranar zai koma aiki yana sa socks.

Kallon-kallo muka yi ni dashi kana Dr ya kau da fuskar shi ya ci gaba da sa socks d’in shi.

Murmushi na yi na k’arasa kusa dashi na zauna.

"Good morning Dr" na fad’a.

"Morning Zarah".

"Dr fushi kake yi dani?" na fad’a cikin shagwa’ba.

Tsadadden murmushin shi ya min kana ya shafa fuska ta ya ce "Me kika gani Zarah, ni ba fushi nake yi dake ba".

Kwantawa nayi a kafad’ar shi yayin da na fara magana a hankali na ce "Dr kayi hak’uri akan abin da ya faru jiya da daddare, ba wai na k’i amincewa da buk’atar ka bane saboda nasan ba za ka ban abin da zai cutar dani ba, sai dai ina ganin kamar in na fara shan pills a yanzu yayi wuri sannan ina ganin

Please Login or Register in order to submit comment