Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan tun da har zan zartar da hukunci akanta ka nuna k’in amincewar ka".

Abbu cikin kwantar da murya ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba haka nake nufi ba, Fatima ‘yar ka ce duniya da lahira, ka isa ka zartar da kowane hukunci akan ta, sai dai in aka yi haka ba a kyauta ma Faruk ba duk da shi ya ce ya hak’ura".

Dadi k’ara tamke fuska yayi ya ce "Indai har na isa in yanke ma Fatima hukunci, na ba ta damar kawo shi wannan Dr da take so in d’aura musu aure".

Abbu wanda bak’in ciki ya taru ya mishi dabaibayi a ranshi yasa ya kasa yi ma Dadi musu, shi kad’ai yasan halin da yake ciki a yanzu.

Dadi ne ya ce "Ka bani wannan damar Ibrahim" ya k’arasa maganar da tambayar sa.

Cikin takaici Abbu ya ce "Duk hukuncin da ka yanke daidai ne yaya".

Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatimah!".

"Na’am Dadi" na amsa a hankali.

"D’ago ki kalle ni kin ji Fatimah".

Kasa bin Umarnin shi nayi, wata kunyar Dadi ce ta kama ni, duk wannan abun da yake yi akai na dan ya samar min farin ciki ne, amma shine ni na bad’a ma ido na k’asa ta hanyar bijire ma auran d’anshi, ai da kunya in iya had’a ido dashi.

Bai damu da d’agowa ta ba yaci gaba da cewa "Fatima, za mu baki za’bin ki na auran shi wannan Dr ba wai dan guduwar da kika yi yasa za muyi haka ba, za mu baki za’bin ki ne saboda ke ‘ya mace ce, bazan so a tauye miki hakk’in ki ba, saboda haka ki turo min shi Dr d’in mu yi magana dashi, sannan zan yi bincike akan shi".

Wani irin dad’i ne mara fasaltuwa ya saukar min a lokacin jin cewa Dadi ya amince, nasan komai zai zo da sauk’i, sai dai a halin da nake ciki ba zai bani damar nuna farin ciki na a fili ba, sannan nasan duk wani bincike da zai yi akan Dr ba zai samu wani aibun shi ba, dan haka ban damu da binciken da zai yi akan shi ba.

Ci gaba yayi da cewa ‘Fatima kin yi kuskure, ba ki kyauta ba akan abin da kika yi, ke mace ce, bai kamata akan d’a namiji ki bar gidan ku ki tafi wani gurin ba duk da gurin Hajiyar mu kika je, saboda ita mace abu kad’an ne yake zubar mata da mutunci a idanun mutane ba, kin ga hakan da kika yi kin sa iyayen ki da duk wani makusancin ki a cikin halin damuwa na rashin sanin in da kika tafi, da ni kika zo ki ka sama ki ka min bayani zan fahimce ki, bai kamata ki d’au zugar zuciyar ki ba ki aiwatar da k’udirin ki, yin hakan babban kuskure ne, kar ki sake makamancin haka kin ji Fatima".


Kalamen da Dadi yayi amfani dasu wajen yi min nasiha ne yasa jiki na yayi sanyi, hak’ik’a Dadi mutum ne mai karamci, ba kowa ba ne zai iya nuna dattakun da yayi ba, k’aunar Dadi ce ta k’ara shiga raina na yadda ya d’auke ni kamar ‘yar shi, nima bazan gaji da d’aukar shi a matsayin mahaifi ba.

Wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya a idanu na.

"Abbu na gode, insha Allah ba zan sake ba".

"Yawwa Fatima haka ake so".

Abbu da Ummu na kalla wanda yanayin su kad’ai ya nuna ba su ji dad’in hukuncin da Dadi ya yanke ba, ba yadda za suyi ne.

A hankali na furta "Ummu da Abbu kuyi hak’uri akan abin da nayi, bazan sake ba".

Cikin su ba wanda ya min magana, da alama har yau ba su sauka daga fushin da suke yi da ni ba.

Sai a yanzu muka had’a ido da yaya Khalil, wani irin kallo yake watsa min mai nuna ‘bacin ran da yake ciki da takaici na da ya cika shi.

Anisa ma kallo na kawai take yi na mamakin abin da nayi da kuma haushin abin da nayi.

Abbu ne ya ce "Yaya na amince da wannan maganar saboda ka riga kasa baki, sai dai nima akwai wani sharad’i da zan gindaya ma Fatima, ina rok’on ka yaya da kar ka hana ni".

Dadi ne kalle shi ya ce "Wani sharad’i ne wannan Ibrahim".

Abbu ya juyo da kallon shi gare ni ya ce "Fatima kin ce dai Dr ki ke so ko?" ya k’arasa maganar yana jiran jin amsa ta.

Shiru na yin a kasa bashi amsar tambayar da ya min.

Tsawa ya daka min wacce ta razana ni ya ce "Ba dake nake yi ba kika min shiru".

Cikin rawar murya na ce "Eh…Abbu".

Takaici ne ya k’ara kama Abbun jin yadda ta amsa da ta amince amma sai bai nuna ba.

Shiru yayi yana mamakin wai Fatima ce a gaban shi take son yin jayayya dashi saboda soyayya.

"Good tun da kin ce Eh, ni ma na amince sai dai a bisa sharad’in duk wata matsala da za ta taso tsakanin ki da shi Dr d’in kar ki tunkaro nan gidan ko wajen ‘yan uwa na da sunan za ki kawo mana matsalar ki, idan kin amince shi kenan, kamar yadda aka sa lokacin bikin ba za a d’aga ba".

Kowa a d’akin ni ya zuba ma ido dan jin amsar da zan bayar.

Nima kaina wannan maganar ta min tsauri a guri na, yanzu za’bi ya rage gare ni.

Abbu ne ya katse min tunani na da cewa "Ke na ke jira Fatima".

"Na amince Abbu" na furta a hankali.

Ido muka had’a da yaya Faruk, wani irin kallo ya watsa min da na fassara shi da kallon tsana yake min, idanun shi sun kad’a sun yi ja alamar ‘bacin rai, kallon ya ci gaba da jefo min dashi, hakan yasa na kasa jure kallon na sunkuyar da kaina.

Hajiya ce ta fashe da kuka tace "Fatima ke wace irin shed’aniyar yarinya ce, yanzu mahaifin ki ya fad’a miki wannan maganar, amma saboda ke kin isa da kan ki, so ya riga ya rufe miki idanu, shine kika amince da sharad’in da ya fad’a miki, yanzu akan d’a namiji kika za’bi ki ‘ba ta wa mahaifin ki rai, Fatima ki gyara kuskuren ki tun kan ki zo ki fara nadama a lokacin da ba za tayi miki amfani ba".

Abbu ne ya kalli Hajiyan Wagini ya ce "Hajiya ki k’yale ta tun da ta ga wannan hukuncin ya mata ai shi kenan".

Yaya Faruk tashi yayi ya bar falon, a yadda yake jin zuciyar shi na k’issima mishi abubuwa marasa kyau akai na, yana ganin barin shi d’akin shi yafi, ko da yake cewa ya hak’ura da ni k’arfin hali kawai yake yi, ba wai dan zuciyar shi ta lafa da ciwon da take mai akan so na, sai dai ya k’udurta a ranshi ya hak’ura dani kamar yadda ya furta, zai ci gaba da rok’on Allah akan ya bashi juriyar hak’uri da ni.

Zazza’bi ne yaji yana niyar kama shi, hakan yasa ya shiga motar shi ya tafi gida.

Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatima sai ki fad’a ma Dr ina jiran shi".

"To Dadi zan fad’a mai".

Abbu ne ya kalle ni cike da ‘bacin rai ya ce "Zaman me ki ke yi tun da an miki abin da kike so, ina ganin sai ki tashi ki bamu guri ko".

Jiki a sanyaye na tashi na tafi d’aki na.

Yaya Khalil ma tashi yayi ya bar falon ya tafi shashin shi.
Anisa ma bin shi tayi a baya ta nufi d’aki na.

Su Dadi ne suka ci gaba da tattaunawa akan maganar, Dadi ne yaci gaba da ba kowa hak’uri akan hukuncin da ya yanke da kuma dalilin shi da yasa shi yin hakan, ba laifi su Abbu sun samu sauk’i akan halin da suke ciki.


San da na shiga d’aki na nemi guri na zauna, na rasa abin da yake min dad’i a rayuwa ta, yau gashi an amince min in auri Dr, sai dai hanyar da aka bi gurin amince min ne yazo da akasi, hakan ya hana ni jin farin ciki a raina.

Duk yadda nake so muyi aure da Dr, zan so da amincewar iyaye na, sai gashi da alama Ummu da Abbu ba su nuna farin cikin su da hakan ba, a yadda na lura ma a family d’in ba wanda yake bani goyon baya akan aure na da Dr.

Zan so a ce na samu wanda ya fahimce ni akan son da nake ma Dr ba yana nufin ina k’in yaya Faruk ba ne, ina mishi so ne irin na ‘yan uwantaka, amma nasan hakan ba zai samu ba.

Hawayen tausayin kaina ne ya zubo min a ido na masu zafi, yanzu nasan sai nayi hak’uri da abin da zan dinga gani a family akan za’ben Dr da nayi.

Tuno da kallon da yaya Faruk yake min na ji na k’ara tausaya ma kaina, ban ga laifin shi ba dan ya nuna ‘bacin ranshi akan abin da na mai, da zai bani dama da na bashi hak’uri akan ya yafe min, dan nasan yana min kallo a matsayin wacce ta ci amanar shi, sai dai kash! Na san ba zan samu wannan damar a gurin shi ba.

Hawaye ne ya ci gaba da zubowa a ido na, saboda halin da nake ciki ban damu da in goge su ba.

Anisa ce ta yi sallama ta shigo d’akin, in b aka lura da motsin bakin ta ba baza kace magana tayi ba.
Amsa mata sallamar nayi na sunkuyar da kaina, dan na san ba lallai ba ne ta min magana saboda haushi na da take ji.

Kallo na take yi kamar wacce take son gano wani abu.

Ido muka had’a ta watsa min harara, ban damu da hararar da ta min ba dan nasan tayi hakan ne cikin ‘bacin rai.

"Fatima kenan, ina ganin zubar da hawaye ba naki ba ne a yanzu, ina ganin da tanadar hawayen kika yi ki ka ajiye dan akwai lokacin da zaki zubar da hawaye a lokacin da hakan ba zai miki amfani ba, yau kamata ya yi ya zama ranar farin ciki a gare ki tun da kin samu cikar burin ki, Fatima ba na zo in miki nasiha ba ne dan nasan ba d’auka za ki yi ba tun da kin yi nisa ba kya jin kira, Fatima sai kin yi nadamar abin da kika aikata duk daren dad’e wa, ki rubuta ki ajiye wannan maganar da na fad’a miki"

Tun da ta fad’a min wannan zaffafan maganganun ba ta sake ce min komai ba, sai ma danna wayar ta da taci gaba da yi.

Maganganun da Anisa ta fad’a min sun min zafi a cikin zuciya ta, sai dai ni kaina nayi mamaki da na kasa maida mata martanin maganganun da ta fad’a min, na alak’anta hakan da halin da nake ciki.

Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a cikin, kowa da irin kalar tunanin da yake yi.

K’arshe ma Anisa tashi tayi ta bar d’akin.

Kiran Dr ne ya shigo cikin waya ta.

Cikin sanyi jiki na d’auki wayar, mun d’au tsawon lokaci muna waya dashi kafin na sanar dashi halin da ake ciki da kiran da Dadi yake mai.

Bayan gama tattaunawar su Dadi ne suka yi sallama suka tafi.



A can ‘bangaren Dr kuwa tun san da na sanar dashi amincewar su Abbu yaji farin ciki ya kama shi, bai yi zaton amincewar su Abbu cikin sauk’i haka ba, lallai yarda da irin son da nake mai tun da har na iya jajircewa aka fasa aure na yaya Faruk.

Gida ya wuce dan ya sanar da Dadi da Momi halin da ake ciki.

San da ya shiga falon ne ya tarar da su Hanan da Farida suna kallo.

Sannu da zuwa suka mishi kana ya tambaye su Momi.

Sun sanar da shi tana d’aki.

San da ya shiga d’akin ya same ta hakimce akan kujera.

Guri ya samu ya zauna kana ya mata sannu da gida.

Kallon shi tayi kana ta ce "Yau ba patients ne a asibiti na ga ka dawo gida da wuri".

Murmushi yayi ya ce "lafiya lau Momi, dama mun yi waya da Zarah ne take sanar dani an ce in turo, kuma parent d’in ta sun ce ba za su d’aga bikin ba, shine nace bari in sanar daku".

Momi ce ta ce "Au daman ba ka hak’ura da yarinyar nan, ina ce ka ce da d’an uwan ta za a had’a ta auran".

"Eh Momi, Zaran ce ta nuna ni take so, shine shi d’an uwanta yace ya hak’ura".

Ta’be baki Momi tayi kana ta ce ‘Ni tun farko nafi maka sha’awar Meemat yarinyar Hajiya Suwaiba amma ka na ce sai wannan yarinyar".

Cikin shagwa’ba ya ce "Kai Momi, wannan Meemat d’in da ba ta da tarbiyya za ki ce in aura, ni nafi son Zarah ta".

Momi ce taci gaba da cewa "Yanzu suna nufin a before two weeks suke nufin mu gama shirye-shiryen mu na biki, bayan kai kan ka kasan yadda muke so muyi organizing d’in bikin ka idan yazo, ina ganin sai an k’ara mana time dan ina bikin ka ya zama special…".

Da sauri ya katse ta da cewa "Plss Momi don’t say that, da kyar fa aka shawo kan su suka yarda ita Zaran ta aure ni, yanzu idan aka nemi favour d’in su akan su k’ara mana time zai iya jawowa in rasa ta, tun da dai an fi k’arfin komai ina ganin a bi su a yadda suke so".

‘‘Ai shi kenan tun da ka na ce sai Zaran, in Dadin ku ya dawo zan sanar dashi halin da ake ciki".

"Thanks Momi, bari in je in d’an huta" yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin.


*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*



www.maryamahmadpaki.blogspot.com
Facebook: Kainuwa Writers Association




*SAK'ON GAISUWA*

_Ba zan gaji da Mik’a godiya ta da fatan alkhairi ga masoya wannan Littafin, ban da abin ce muku na yadda ku ke bibiyar wannan labarin, fatana darasin da ke ciki Allah yasa ayi amfani dashi_

_'Yar Mutan Paki na marhabin da duk wanda yake bibiyar littattafai na_




*QUESTION OF THE DAY*

_Ya sunan matar da ta d’auki takobi ta kare Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da mazaje suka guje daga gare shi, akwai san da annabi ya ce mata "Tambaye ni abin da kike so? sai ta ce masa "Ina rok’on ka kasancewa mak’ociyar ka a Aljanna da son ka a duniya da son ka a lahira_




71-72


*WANENE DR ABUBUAKAR SADIK MUHAMMAD?*

Dr Sadik d’a ne ga Arc Alhaji Muhammad, haifaffen d’an garin Kaduna ne, mahaifin su shahararren d’an gwal ne, ya karanci ‘bangaren zane-zane, mahaifiyar su Haj Hauwa lecturer ce a Open University, su hud’u ne a gurin iyayen su.

Dr Sadik suna zaune ne a Unguwar Dosa.

Dr Sadik shi ne babba a gurin iyayen su, daga shi sai Hauwa (Hanan) wacce taci sunan mahaifiyar su, tana karanta Socio-logy, tana 300 level a Kasu, daga ita sai Farida da take 100 level a Open University, daga ita sai autan su Ahmad, yana primary 4 ne a school d’in su.

Dr Sadik yayi karatun shi a ABU Zaria in da ya karanci medicine, yanzu haka yana aiki ne a cikin asibitin Kaduna Polythecnic, sannan yana aiki a wasu asibitocin idan buk’atar hakan ta taso.

Gidan su Sadik wata irin rayuwa ake yi ta ‘yan boko da kuma ‘yanci, babu mai matsa ma wani akan abin da yake so, akwai freedom ta ‘bangaren iyayen, hakan yasa su ma yaren su ka taso da wannan d’abi’ar.

A cikin su Farida ce ba ta cika d’aukan rayuwa da zafi ba, ba ta d’aura ma kanta social life ba, shi yasa su ke samun sa’bani da Hanan akan banbancin ra’ayin su.

Duk da yadda mahiafin su ke basu ‘yancin yin duk abin da suke so, hakan bai hana wani lokacin in sun yi ba daidai ba ya musu fad’a.

Dr mutum ne da bai cika son hayaniya ba sannan shi mai ji da kanshi ne, yana tafiyar da rayuwar shi akan turawa.

Wannan shine tak’aitaccen tarihin Dr Sadik..



San da yaya Faruk ya koma gida, d’akin shi ya wuce ya kwanta, jin zuciyar shi yake yi tana mishi zafi, ga k’irjin shi da yake ji ya mishi nauyi, ya san hakan ba zai rasa nasaba da ciwon rabuwa da ni ba.

Yana k’ok’arin yaga ya cire ni a ranshi, a yadda yake jin son ta a ranshi, yasan hakan ba mai sauk’i ba ne a gurin shi cire ni a lokaci d’aya a cikin zuciyar shi, zai ci gaba da add’u’a akan Allah yasa komai yazo mishi cikin sauk’i.

Haka ya ci gaba da zama a d’akin, ciwon k’irjin na k’ara matsa mai, sai da ya d’auki lokaci kafin yaji k’irjin ya daina mishi ciwo.

Tashi yayi ya watsa ruwa ya canza kayan jikin shi kana ya fito main parlour ya zauna ya kunna Tv dan ya rage ma kan shi tunani.

A haka su Momi su ka dawo suka same shi, sun ji dad’in yadda su ka ganshi yana kallo, duk da idan kayi duba da yanayin shi kasan yana cikin damuwa, dauriya kawai yake yi.

Zama suka yi suka dinga kwantar mishi da hankalali da mishi nasiha akan yarda da k’addara a duk yadda ta zo maka.

Yaji dad’in yadda su Momi suke nuna mishi kulawa, ba sa son ganin cikin damuwa, shi yasa shima yake k’ok’arin ganin ya kwantar da hankalin shi dan kar yasa su cikin damuwa duk da kuwa yanda yake jin rad’ad’in abin da na mishi a zuciyar shi.

Murmushi yayi ya ce "Zan yi amfani da shawarar ku Dadi da Momi, na gode da kulawar ku gare ni, addu’ar ku na ke buk’ata a ko wane lokaci, nasan ita ce nasara ta a dukkan lamura na".

Tausayin yaya Faruk ne ya kama shi, sun san dauriya yake yi a matsayin shi na jarumtaccen namiji, amma abin na mishi ciwo a zuciyar shi.

"Insha Allahu za mu ci gaba da maka addu’a Faruk, kullum kana cikin addu’ar mu, Allah biya maka buk’atun ka na alkhairi, ka dinga rage tunanin da kake yi ka ji Faruk, saboda gudun kamuwa da wata cutar, komai da ka ke gani muk’addari ne daga Allah" Dadi ya fad’a.

"Amin Abbu na gode, zan kiyaye insha Allah".

Momi ta ji dad’in yadda yaya Faruk yadda ya ke k’ok’arin ‘boye damuwar shi, hakan yasa ita ma taji damuwar da take ciki ta ragu.

"Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi Faruk" Momi ta fad’a.

"Amin Momi" ya fad’a a hankali.

Anisa kuwa in ban da murmushi ba abin da take yi ganin yaya Faruk bai sa damuwa akan abin da na mishi ba.

Yaya Faruk ne ya kalli Anisa ya ce "Anisa ya aka yi ne, ko akwai abin da yake damun ki?" yaya Faruk ya tambaye ta.

Murmushi ta mayar masa kana ta ce "Ba komai yaya Faruk".

Haka suka zauna suka ci gaba da hira, wannan hirar da suka zauna suka yi tasa sun samu sauk’i na damuwar da suke ciki.

Tun bayan tafiyar su Dadi na kasa fito wa falo, nasan ko na fito bazan samu tarba ba ta kowane ‘bangare, yaya Khalil ma nasan tun kan matsala ta da yaya Faruk muka rage shiri dashi, daman shi kad’ai wanda a ko wane lokaci nake tunanin samun sauk’i.

Sallah kawai nake iya tashi in shiga band’aki in d’auro alwala in zo in yi sallah, ni kaina zaman ya ishe ni, ga yunwa da take addaba ta.

Haka na wuni a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ba, hakan ya k’ara sa ni cikin damuwa.

Ganin zan cutu yasa nayi k’arfin halin fito wad an samar wa kaina abin da zan ci.

Ina fito wa na tarar da Hajiyan Wagini da Momi da Khalil suna hira, fitowa ta da suka ga nayi ne yasa su ka bi ni da ido.

Kitchen na wuce na d’ebo abinici na dawo d’aki na zauna na fara cin abinci na.

Bayan na gama ci abinci ne na ci gaba da zama na a d’aki, duk kuwa da yadda na takura da zaman d’akin, ina ganin hakan shi yafi min akan fito wa ta.

Ranar haka na zauna ni kad’ai a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ya ga a wani hali nake ciki ba.

Hajiyan Wagini ma nasan ba shigo wa za tayi ba tun da tana fushi dani.

Yaya Aminu ma yazo saboda Abbu ya kira shi ya fad’a mishi na dawo, jin gurin Hajiyan Wagini na je yasa ya ji ya rage matakin da yayi niyar d’auka a kaina, yanda ya tashi a harzuk’e ya nufo d’aki na Abbu yasan har yau ranshi a ‘bace yake da abin da nayi.

Abbu ne ya kira shi ya dawo ya zauna ya fad’a mishi halin da ake ciki, da kuma sharad’in da ya gindaya min na amince.

Abbu ne ya ce ya k’yale ni tun da har na amince, ba buk’atar k’ara d’aukar mataki a kaina tun da na amince da sharad’in shi.


Washegari ina jin su Ummu nayin Breakfast, amma na kasa fitowa, ba kuma wanda ya aiko akan in fito in yi breakfast.

Nasan ‘bacin ran da nasa su ne yasa suka yi watsi da al’amari na, hakan kuwa ba k’aramin sa ni a damuwa zai yi ba.

Ummu kuwa rashin fitowa ta ba k’aramin damun ta yayi ba, tana tsoron kar wani ciwo yazo ya kama ni, sai dai idan ta tuno abin da nayi sai taji takaici na ya kama ta.

Tashi nayi na fito falon dan in gaishe dasu.

Ko da na fito ba wanda ya d’ago ya kalle ni, a hankali na k’arasa inda suke.

"Ina kwana Hajiyan Wagini".

Hajiya wacce haushin abin da nayi bai sake ta ba ta fara fad’a da cewa "Ina ruwan ki da kwana na har da za ki gaishe ni, ni yanzu na yafe gaisuwar ki, na bar ma waccan fitsararren Dr da yake sa ki rashin jin magana duk ki dinga mishi".

Wasu hawaye ne suka fara zubo min a idanuna, yadda Hajiyan Wagini ke min a yanzu kamar waccce ba ta san inda na fito ba, tun san da yaya Faruk ya je can Wagini ya fad’a mata abin da nayi take min fad’a, kamar ba ita ce muke wasa da dariya ba.

Sauri na yi na goge hawayen da suke zubo min, a lokacin muka had’a ido da yaya Khalil yayi saurin kau da idon shi.

A hankali na juya ga su Abbu da Ummu na ce "Barkan ku da Safiya Abbu da Ummu".

A tak’aice suka amsa min da "Lafiya".

Tun daga wannan amsawar da suka yi ba wanda ya sake kula ni.

Jiki na ba k’wari na kalli yaya Khalil na ce "Yaya Khalil ina kwana".

Duk yadda yake jin haushin abin da nayi ba zai iya jurar gani na a cikin wani yanayi ba, gashi a wajen su Ummu da Abbu ma duk fushi suke yi dani.

Sakar fuskar shi yayi kad’an ya amsa min da cewa "Lafiya lau Fatima, ya kike?".

Ganin yadda yaya Khalil ya amsa min yasa na d’an ji dad’i a raina.

"lafiya lau yaya Khalil".

Shima tun daga amsawar da yayi bai sake ce min komai ba, gajiya da zaman da nayi ne a falo ba tare da kowa ya kula ni ba yasa na tashi na koma d’aki.

Hirar su na dinga jiyowa jefi-jefi.

Haka suka gama breakfast kowa ya kama harkar gaban shi, falon shiru alamar ba kowa a ciki.

Tashi na yi na d’akko kayan breakfast nayi kalaci a d’aki na, yayin da na ci gaba da zaman kad’aici.

Ni kaina tunanin halin da na sa su Ummu na ‘bacin rai ya hana ni samun sukuni, dan haka zuciyata ta yi ta nusar dani akan in je in k’ara basu hak’uri ko na samu sassauci.

Da wannan shawarar ta zuciya ta na samu k’arfin gwiwar tunkarar Ummu.

Zuwa na yi na same ta a zaune a d’aki, da alama ita ma tayi zurfi a cikin tunanin da take yi ganin yadda tayi shiru.

Tun da nayi sallama na nemi guri na zauna.

Kallo na tayi ta amsa min sallamar ciki-ciki.

Shiru ne ya ratsa falon kana na kalli Ummu da fuska da ta koma kalar tausayi na ce "Ummu dan Allah ki yi hak’uri ke da Abbu abin da na muku, nasan ban kyauta ba, bazan sake kamanta tafiya wani gurin ba tare da izinin ku ba".

Duk wannan maganar da nayi Ummu bi na take yi da kallo, har yau takaici na ne ke cikin zuciyar ta.

Shirun da na ji Ummu tayi ne ya k’ara sanyayar min da jiki.

Can ta kau da shirun da cewa "Fatima ai ban zaci zaki iya zuwa

Please Login or Register in order to submit comment