Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya gani a fuska ta dake nuna na gaji yasa yace "Teemah za ki iya koma wa ciki, in kin je kya gaishe min da Ummu kice ina sauri ne amma zan shigo gobe mu gaisa".

Ai kamar jira nake yi, nayi saurin mik’ewa ba tare da ce komai ba, na fara tafiya, "ka ji da shi" nace a raina duba da yadda yake ta fito da sabon salo kala-kala wanda shi yasan manufar shi.

Jiki na ne ya bani cewa kamar yaya Faruk kallo na yake yi, juyawa nayi naga kafe ni da ido kamar wanda yaga sabuwar halitta.

Harararshi nayi na d’auke kaina ina mamakin kallon me yaya Faruk yake min?
amsar da ban sani ba kenan.

shi kuwa yaya Faruk yaga san da na harare shi, sai murmushi yayi kawai kamar bai ga abin da nayi ba, yanda na kalle shi ma dariya ma na bashi.

Ko da na shiga main falo, ban nemi kowa ba, na nufi side d’ina.

Gefen gado na samu na zauna ina tunanin da gaske ne yaya Faruk yau ni ya nemi yafiya ta har yana neman mu shirya?

Abu d’aya na yadda dashi shine zamu dinga gaisawa irin ta ‘yan uwan taka ba wai dan ban hak’ura ba, sai dn in ja ma kaina mutunci, tun da shi abu k’adan yake jira ya ‘bata wa mutum.

Yaya Khalil ne ya shigo ya zauna kusa dani yana cewa "Sister ashe kin dawo? ina ta jiran ki a side d’in Ummu".

Ta’be baki nayi nace "yanzu na shigo, shi yaya Faruk d’in nan ya wani tsare ni da wani dogon bayani, sai da ya gama mari na sannan zai lalla’bo wai na yafe mai sannan wai in ina da shawara in zo wajen shi, ni nasan akwai dalilin da yasa ya nemi yafiya ta amma ba wai ra’ayin kan shi bane".

girgiza kai kawai yaya Khalil yayi, ya d’aura da cewa "Fatima! ba ki gama sanin waye yaya Faruk bane shi yasa, he is a simple and nice person ga wanda ya kiyaye dokokin shi, yana da dad’in zama, duk da sometimes miskili ne kuma yana da fad’a amma ba shi da wata matsala, tun da har ya nemi yafiyan ki ya kamata ki yafe mai saboda akwai laifin da muke wa ubangijin mu kuma in mun nemi yafiyar shi ya yafe mana, kar ki zama mai k’ullatar mutum idan ya miki laifi kin ji sister?

D’aga mai kai nayi nace "ni ban k’ullace shi ba, na yafe mai, amma ni ba zan kai mishi damuwata ko in nemi shawarar shi ba".

Dariya yayi yace "is ok Fatima, zo mu tafi side d’ina akwai research d’in da nake yi, kya taya ni hira".

Fita yayi daga d’akin yayin da nake bin shi a baya.



Yaya Faruk kuwa da ya shiga mota, tsintar kanshi yayi cikin farin cikin da bai misaltuwa, lokaci yayi da zai jawo Fatima jikin shi, ta daina mishi kallon mai son kanshi da kuma mulki.

Lokaci-lokaci zaka ga ya saki wani lallausan murmushi.

Ko da ya isa gida, d’akin Anisa ya wuce, samun ta yayi da wani novel tana karanta wa.

Kusa da ita yaje ya zauna yana cewa

"Anisa!

Amsa masa tayi da cewa "sannu da zuwa yaya".

Bai damu da ya amsa mata ba illah cigaba yayi da cewa "gobe in Allah ya kaimu around five p.m ku shirya zan kai ku outing Asaa pramise ku d’an yawata ku ga gari tun da kun ce ina takura muku kamar wasu daddawar d’aka shine naga gara in daina matsa muku" ya k’arasa maganar da wasa.

Ita kanta Anisa abin ya ba ta mamaki wai yau yaya Faruk ke cewa su shirya zai kai su outing".

Ita tun jiya zuwa yau taga ya canza mata, ya dawo so cool wanda ba ta san dalilin canzawar shi ba.

Ita dai fatan ta shine Allah yasa ya d’aure a haka saboda ita ma tana son zama da shi suna hira kamar yadda wa da k’anwar shi suke yi.

Yalwatar murmushin ta tayi dan kar ya gane ko tana mamaki ne tare da cewa "yaya mun gode sosai".

Mik’ewa yayi ba tare da yace komai ba ya bar d’akin, a ranshi kuwa yaji dad’in yadda ta nuna farin cikin ta, shi yasa ma ya d’au alk’awarin zai jawo su jikin shi saboda su sake dashi.

Cikin zak’uwa ta d’au wayar ta, tayi dialling d’in number Fatima.

Daga d’ayan ‘bangaren, Fatima ce tayi receiving tana cewa "Anisa Hi".

‘how a you doing? Anisa ta tambaye ta
"normal Anisa" na ba ta amsa.

Anisa ce ta d’aura da cewa "gobe ki shirya zamu je outing".

Da murna ta nace "da gaske Sister, waye zai kai mu? na tambaye ta.

"Da gaske nake yi, ke dai ki shirya, around five za mu biyo mu d’auke ki, kuma kinsan abin mamaki? Anisa ta tambaye ni.

Amsa mata nayi da cewa "ya za ayi in sani" na ba ta amsa.

"To yaya Faruk ne zai kai mu" Anisa ta fad’a da murnar ta.

D’if nayi kamar an d’auke wutar nefa dan har ga Allah ban so a ce shi zai kai mu ba duk kuwa da yadda nake son fitar, nasan in nace ba zani ba Anisa ba za ta ji dad’i ba amma da ba inda zani.

Shirun da Anisa taji ne yasa tace

"Fatima kina ji na kuwa"

"ok Anisa, Allah ya kaimu sai kun zo" na fad’a da kasalalliyar murya

Sallama muka yi na aje wayar yayin da nake tunanin wai miye dalilin yaya Faruk na canza wa a lokaci d’aya?

Ganin ba mai bani wannan amsar yasa na watsar da tunanin.

Ita kuwa Anisa tana ajiye wayar kiran yaya Khalil ne ya shigo.

Tsadadden murmushi tayi kana ta danna received.

"Assalamu alaikum lovely Sister" yaya Khalil ya fad’a.

Amsa masa tayi da "wa’alaikumus salam yaya Khalil".

"ya kike? Yasu Momi da daddy? ya tambaye ta.

"Su na lafiya" ta bashi amsa a gajarce.

"Anisa kwana biyu ba kya nema na, gashi yaya Faruk ya hana ku yin chat da mun dinga communicating" cewar yaya Khalil.

Cikin shagwa’ba tace "plss yaya Khalil ka sa baki, naga kai na hannun daman shine, may be ya yarda mu fara chat d’in'.

Dariya yayi sannan yaci gaba da cewa "ba ruwa na, so kike yasa ni up & down, in zo ina faman yi wa k’afa ta gashi ko in sa a nemo min mai gyaran targad’e".

Kukan wasa ta fara mai saboda tasan ita yake tsokana.

Hak’uri ya fara ba ta yana dariya kana suka ci gaba da hirar su sannan suka ya mata sallama.
[3/27, 10:16] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*





*EDIT BY*
*MRS MANSOOR*






*Wannan shafin naku na baku shi ne kyauta*


*Aisha* (Auta Mama)

*Maman Walida*

*Fatima Arkilla*

*Fatima Muh’d*

*Maman Baffa*

*Aisa*

*Ina tare daku na yadda kuke bin wannan novel d’in*




*TUKWICI GAREKU*

*Xarah Auwal*

*Aisha* (Auta Mama)

*Ina muku fatan alkhairi na amsar da kuka bayar daidai a Question of the day da wanda suka yi k’ok’arin ba da tasu amsar*.
*Amsar Question of the day shine, Sunan ta Ramlat ‘yar Abu sufyan, nick name d’in ta* (Ummu Habiba) *kuma itace ta tara* (9) *a cikin matan manzon Allah (s.a.w)*.

*Allah ya bamu ikon yin amfani da ilimin mu ta hanyar da ta dace ya kuma*
*k’ara mana ilimi mai amfani*.





*TUNATARWA*:


ka/ki zamo mai hak’uri, amma kar ka/ki yadda hak’urin ya jawo maka raini.


Ka/ki zamo mai kyauta, amma kar ka/ki yadda kyautar ta jawo maka riya.

Ka/ki zamo mai soyayya, amma kada ka/ki so wani daidai soyayyarka/ki ga Allah da Manzon sa.





29&30

Washegari da misalin k’arfe hud’u da rabi, yaya Faruk ne cikin shigar shi na wani lallausan yadi mai kalar sky blue, kayan sun matuk’ar dacewa da kalar jikinsa.

Ta d’akin shi ya shiga side d’in Momi kasancewar akwai k’ofa a d’akin shi da zai iya shiga ba tare da ya fito ba.

Samun ta yayi tana kallon tashar Manara Tv a tauraron d’an adam.

Guri ya samu ya zauna kusa da ita kana ya gaishe ta.

Amsa masa tayi tana mai maida gaba d’aya hankalin ta gareshi.

"Ina za ka ne Faruk? na ga alamar kamar fita za ka yi’ Momi ta tambaye shi.

"Momi za mu d’an fita outing ne dasu Anisa, daga nan zamu biya mu d’auki Fatima" cewar yaya Faruk.

Fara’ar ta ce ta k’aru saboda yau taji dad’in yadda Faruk zai kai su gurin shak’atawa wanda a da ko zama yayi hira dasu bai dame shi ba.

"ko kai fa Faruk, gwara ka dinga jawo k’annen ka a jiki ko sa cire tsoron da suke ma ka"

"ba na jin dad’in yadda suke tsoron ka" cewar Momi.

Murmushi yayi kana ya d’aura da cewa "Momi yaran ne naga suna tashen girma, dole sai ana nuna musu hanya, amma insha Allahu zan yi k’ok’arin jawo su jiki na, nima yanzu ba na jin dad’in yadda ba sa sakewa dani".

"Momi ina Anisa ne? nace ta shirya around this time, amma naga tana so ta ‘bata min lokaci kuma tasan bana son jira"

"Tana ciki bari in kira ta a waya" Momi ta fad’a.

Kiran ta tayi akan tayi sauri yaya Faruk na jiran ta.

Momi ce ta kalli yaya Faruk cike da kulawa ta kira sunan shi.

"Umar"

Saurin d’agowa yayi ya kalle ta saboda yasan duk abin da za ta fad’a mai mahimmanci ne tun da kira shi da Asalin sunan sa.

Da sanyin murya ya amsa da "Na’am Momi".

Sai da tayi shiru kamar ba za ta yi magana ba kana ta d’aura da cewa

"Faruk! cikar mutum ya samu a rayuwa shine ya sami abokiyar zama, abin da nake nufi mata, idan mutm ya samu mace ta gari to ya cika rabin addinin sa".

Kallon ta yayi ganin yadda take maganar yasan abin na damun ta.

Ci gaba tayi da cewa "Faruk duk tak’amar mutum na kud’i, mulki, kyau, ilimi, nasaba da duk wani abu da mutum ya ke tunk’aho da shi, mutane ba sa ganin sa da wannan mutuncin har sai ya samu abokiyar zama sannan duk wa’innan abubuwan da na lissafo kana dasu bare ace baka da halin yin aure ne, babu yarinyar da zaka nema tayi rejecting d’in ka in har ka fad’a mata kana son ta".

"wanccan hutun da ka dawo, ni da Dadin ka mun tuntu’be ka akan maganar aure amma sai wasu excuse kake kawo mana wanda ban gamsu da su ba, idan kana da matsala ne ka fad’a min sai a samu mafita tun da naga kai abun bai damun ka"

"idan kuma idon ka har yau bai gama za’ba maka macen da ta dace dakai ba, ni ka bani za’bi, zan nemo maka a cikin familin ku ko nawa ko a k’awaye na".


Cikin ladabi yaya Faruk ya fara Magana "Momi Plss ku k’ara hak’uri, nima nasan abin na damun ku, insha Allah nan ba dad’e wa ba zan gabatar muku da yarinyar da nake so, matsalar itace har yau ban furta ma yarinyar ina son ta ba dan ba ta dad’e da gama SSCE d’in ta ba shi yasa".

Ranta ne ya fara ‘baci da yadda Faruk yake son raina musu hankali, dan haka ta fara Magana cikin ‘bacin rai "Faruk wai wacece yarinyar nan, da in an maka magana sai kace ba ka fad’a ma ta ba, what do you mean by that, kana nufin muyi ta jiran ka har sai ran da kayi niyya sannan za ka fad’a mata mu kuma muna zuba maka ido, kana nufin ba ka da confidence d’in da zaka tunkari yarinyar ne ka fad’a mata or what?

Zuba mishi ido tayi cikin ‘bacin rai dan tana son jin wace amsa zai ba ta.

"Momi pls take patient, insha Allah everything will be alright" yaya Faruk yayi maganar in a polite way.

Za ta fara mai fad’a ta ga Anisa ta fito daga d’akin ta, dan haka fasa fad’ar abin da za ta ce tayi.

Anisa ce ta tunkaro in da suke cikin shigar wata doguwar riga mai kalar bak’a, ta yafa d’an k’aramin mayafin rigar, takalmin da tasa wani flat shoe ne kalar white yayin da ta rataya side bag a hannun ta kalar white, gaskiya shigar ta amshe ta.

Kusa da Momi ta nemi guri ta zauna yayin da ta d’aura kan ta a jikin kafad’ar Momi.

"my dear you look so cute" Momi ta fad’a.

Anisa kuwa sai murmushi take yi jin Momi tace tayi kyau.

Yaya Faruk kuwa sai watsa mata wani harara yake yin da ta sa shi ya jira ta, dan shi ba abin da ya tsana irin jira.

"za ki tashi mu tafi ko sai kin gama shagwa’bar, since i was waiting for you but you waste my time, instead of you to apologise amma kin zauna za ki fara shagwa’ba".

A ranta kuwa cewa tayi "mai hali ba ya barin halin sa, gwara in bashi hak’uri mu rabu lafiya kar in ja ma kaina wani hukuncin".

A hankali ta furta "sorry yaya Faruk".

Ko sauraren ta bai yi ba illa mik’ewa da yayi yana ce wa "Momi sai mun dawo".

Anisa kuwa waving d’in hannun ta tayi tare da cewa "Momi sai mun dawo, me zan tawo miki dashi?

"Anything that is special" abin da Momi ta ce Kenan tana dariya.

Ko da suka shiga motar, hira suke yi jefi-jefi kasancewar sa ba mai yawan san Magana ba.

Parking yayi a k’ofar gidan su Fatima ba tare da ya shiga da motar ciki ba kasancewar yanzu za su shiga su fito su tafi.

Ko da suka shiga ciki, kallon Anisa yayi akan cewa taje ta ce wa Ftima ta fito su tafi, shi kuma ya nufi d’akin Ummu in yaso sai ta shigo ta gaida Ummu.

Samu na tayi a gaban dressing mirror ina sa jan baki a lip d’ina.

"haba Fatima! ya kamata ace by now kin shirya, kin san yaya Faruk ba ya son jira".

Hararar wasa na mata kana nace "yanzu ai ina jin wasa nake yi".

Dariya tayi tace "koma dai me kike yi kiyi sauri kisa kayan mu tafi".

Mik’ewa nayi na d’akko doguwar riga kalar ta Anisa, sai dai tawa an mata ado da golden colour a jiki na sa, nayi rolling da mayafin rigar, na rataya side bag kalar golden, na d’akko bak’in low past na sa.

"Wow"! gaskiya naga wannan wankan, Fatima ba ki ga kyan da kika yi ba" Anisa ta fad’a.

"Duk kyan da nayi ai ban kai yake ba" na ce da ita.

"hmm haka dai kika ce Fatima, amma ko ki yadda ni dai kin min kyau".

Anisa ce ta kalli Fatima ta ce "Fatima yaya Khalil nan kuwa?

Kallon ta nayi na kya’be baki sannan na fara dariya a lokaci d’aya.

"yana nan, yau ko kin manta hanyar d’akin shi ne in miki jagora".

"to miye abin dariya daga tambaya, ko na fad’i abin da bai dace bane" Anisa ta fad’a tana ta’be baki.

"ba komai Anisa, ke da yayan ki, ai ba zai zama laifi ba dan kin tambaye shi, gani nayi kawai kamar akwai wata a k’asa".

" ke kika sani"cewar Anisa.

Tare muka fito daga d’aki na inda Anisa ta kalle ni tace "bari in lek’a gurin yaya Khalil mu gaisa sai in shigo gun Ummu mu gaisa".

Mamaki ta bani saboda yanzun nan ta gama ce min yaya Faruk na jiran mu amma gashi za ta tafi gurin yaya Khalil.

"ke ma dai kin san sauran in kika dad’e, kya same ni a d’akin Ummu zan je in yi mata sallama" na fad’a.

San da na shiga d’akin, samun ta nayi da yaya Faruk suna hira.

sallama nayi na samu guri a can gefe na zauna na d’ago na kalle shi ganin yadda yayi wani so cool.

"yaya Faruk ina wuni" na fad’a.

Shirun da naji bai amsa ba yasa na yi tunanin ko miskilancin ne ya motsa, d’aga idanun da zan yi naga ya kafe ni da idanun shi alamar yayi nisa a kallo na.

Ummu ce ta kira Sunan sa "Faruk!

Kamar wanda ya tashi daga bacci ya d’ago ya kalli Ummu.

"Ummu Magana kike yi ne" ya tambaya.

"Dama Fatima ce take gaishe ka" ta fad’a.

K’ara kallon ta yayi ya basar kamar bashi bane yake min kallon k’urilla.

"oh! lafiya, ban ji ba ne" ya amsa a gajarce.

Ta'be baki na nayi alamar kai ka Sani.

Mik’ewa yayi kana yace "Momi bari mu tafi sai mun dawo, yamma tayi".

"Sai kun dawo Faruk" Ummu ta fad’a.

Ummu ce ta kalle ni tace "Ki tashi ku tafi ma na kar yayi ta jira, wai ina Anisa ne?

"Tana d’akin Yaya Khalil, ta je su gaisa".

Sallama nayi wa Ummu, na fita daga d’akin.


A can ‘bangaren yaya Khalil kuwa, Anisa ce tayi sallama ta same shi kwance akan gado.

Amsawa yayi kana ya mik’e ya zauna yana murmushi ganin shigar da tayi yadda ta amshe ta.

"yaya Khalil ina wuni, barci kake yi ne halan".

Wani had’ad’d’en murmushi yayi ya kalle ta "Sister sai ina haka, you look so beauty".

"Tanx Bros, zamu d’an fita outing ne da yaya Faruk".

"kai Anisa, shine ba gayyata, lallai kun zama ‘yan gatan yaya Faruk, ya baku purnishment ya Kuma d’auke ku outing, dad’in ya muku yawa" ya fad’a da alamar tsokana.

"kai yaya Khalil, tun da abin ‘yar tsokana ce bari in tafi, dama na shigo ne mu gaisa".

Dariya ya fara yi yana cewa "Sorry Anisa, ni ma in na samu time zan shirya ma na outing amma ni da ke zamu je outing d’in".

Saurin juyowa tayi tace "kaima kasan ba zan iya tafiya ni kad’ai ba sai da Fatima".

" Dama tsokanar ki nake yi, ai tare zan kai ku, muje in taka miki".

""a ka bar shi yaya Khalil, d’akin Ummu zan shiga mu gaisa, ina zuwa direct nan na tawo".

"Muje dai na gaisa da yaya Faruk d’in".

D’akin Ummu ta shiga suka gaisa a gurguje kana ta fito suka jera da yaya Khalil.

Ita kuwa Fatima tun da fito, tsaya wa tayi a gefen motar, yayin da take pressing d’in wayar ta.

Yaya Faruk da ke zaune a mazaunin driver, cool music ya kunna inda sautin ke tashi a hankali.

Ganin Anisa da yaya Khalil sun a tawo wa yasa ya k’ara tamke fuska saboda yadda ta ‘bata mishi rai.

Yaya Khalil ne ya k’arasa ya mik’a masa hannu suka yi musabaha kana ya gaishe shi.

Amsawa yayi ya juya yana watsa wa Anisa banzan kallo.

Cikin ta ne ya kad’a saboda tasan abin da kallon shi yake nufi na zata fuskanci hukunci a gurin shi.

"Anisa kin raina ni ko? a gida haka ki ka ‘bata min time sannan yanzu ma kin k’ara ‘bata min time saboda kin ga na fara sakar miki fuska ko?

Cikin rawar murya ta fara Magana "ya hak’uri, na je mun gaisa da yaya Khalil ne".

"you are stupid! Sai an miki Magana ki fara ba da hak’uri".

Ya juya da kallon shi zuwa ‘bangaren yaya Khalil yana cewa "kai ma har da laifin ka, kasan ba na son jira shine ka ja ta da hira ko?

"Ayi hak’uri babban yaya, mun amsa laifin mu".

Murmushi kawai yayi ya shiga cikin motar ya kunna.

Ni kuwa dake gefe kamar ban san dramar da ake yi ba, sai aikin danna waya kawai nake yi.

Hon d’in da yayi ne yasa muka yi saurin shiga back seat muka zauna.

Wani irin kallo ya watsa mana kana yace "Uban wa kuka mai da driver da za ku zauna a baya".

Anisa ce ke faman ta’ba ni alamar in koma gaba amma nayi biris kamar ba dani take yi ba.

Jin tsawar da ya daka mana ne yasa Anisa ta fito da sauri ta na k’ok’arin bud’e gidan gaba.


Jan motar yayi da k’arfi alamar ranshi a ‘bace yake ya bar layin.
[4/1, 13:38] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Wannan shafin naku ne, masoyan yaya Faruk da Fatima*
*Ina mik’a gaisuwa ta gare ku*.



*Question of the day*

A wace surah ce Allah (s.w.t) yayi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce?



31&32

Tun da muka fara tafiya, na lura da yadda yaya Faruk ya saita madubun gaban shi yake kallo na akai-akai, tun abin ba ya damu na har na fara takura da kallon da yake min.

Shirun da yayi yawa ne a motar yasa na cire tsoron da nake ji na fara jan Anisa da hira saboda bazan iya zaman kurame ba, jefi-jefi yaya Faruk yana sa bakin shi a cikin hirar.

Ko da muka isa gurin, wani ke’bantaccen guri yaya Faruk ya samar mana muka zauna yayin da ya je ya siyo mana ice cream da snacks muka fara ci.

Yadda mutane ke harkar gaban su, ba ruwan kowa da kowa yasa naji gurin ya burge ni.

Wasu suna ciye-ciye, can gefe kuwa gurin hutawa ne da mutane ne ke zaune, yayin da wasu ke wajen swimming pool suna wanka, kowa dai da abin da yake yi.

Kujerar da na zauna tana opposide d’in yaya Faruk, yawan kallon da yake mun ne yasa na fara tsarguwa da kallon saboda ni ban ga dalilin kallon ba.

Tambayar kaina nayi da cewa "ko dai shigar da nayi ne ba ta dace ba? ko kuma ban yi kyau bane? na tambayi kaina, ko ma dai menene shi ya sani saboda tun a mota na lura da yadda ya tsure ni da kallo a mota".

Yaya Faruk ne ya fara da cewa "yau dai gashi na kawo ku outing, kun fita daga cikin layin wanda kuka ce ana takura ma wa ko?

Shiru muka yi ba wanda ya amsa mishi.

Ci gaba yayi da cewa "I know you will enjoy this place shi yasa na kawo ku nan, so in mun gama refreshing za ku iya zagayawa, ba na son hayaniya da mun zagaya ni da ku".

A raina nace "ba ma buk’ata, dan in ka bimu takura mana za kayi".

Mik’ewa muka yi muka fara zagaya gurin kana muka ya da zango a kujerun da aka ajiye da table a wajen swimming pool d’in dan hutawa ko refreshing, a gurin akwai kuma rest chair da aka ajiye musamman dan hutawa kafin ka fara wanka ko in ka gama wanka.

Zama muka yi muna kallon yadda mutane ke wanka a ciki.

Yaya Faruk yana can gefe kwance akan wata kujera ta hutawa yana sipping d’in hollandia, yana kallon duk abin da ke gudana a gurin.

Wani handsome guy ne ya zo ya zauna a d’aya daga cikin kujerun da muke zaune ya mana sallama.

Amsa masa muka yi muka d’auke kan mu.

"Sannun ku da hutawa ‘yan mata" guy d’in ya fad’a.

"yawwa sannun ka"
Anisa ta amsa a tak’aice.

"Suna na Aliyu, plsss in ba damuwa zan iya sanin sunan ku".

Wannan karan ma ban yi Magana ba illah juyawa nayi ina kallon wani side kamar ba da mu yake yi ba.

Anisa ce ta bashi amsa da cewa "ni suna na Anisa, ita kuma sunan ta Fatimah".

"wow! Nice name, Anisa in ba damuwa ina son in yi Magana da Fatima, ina neman alfarmar ki na five min zuwa ten in ba damuwa".

Murmushi tayi tace "ba matsala bari in baku guri".

Mik’ewa tayi tace "Fatima bari in je can grass carpet d’in, kya same ni a can".

Ni kuwa in ban da hararar ta ba abin da nake yi saboda yadda ta wani zauna tana bashi amsa.

"Fatima! kamar yadda na fad’a muku ne, suna na Aliyu amma zaki iya ce min Haidar, tun da na zo gurin nan na ganki na ji na kamu da son ki, ina rok’on alfarma ki ba ni guri a zuciyar ki ko na samu shiga".

Sake d’agowa nayi na kalleshi, ba laifi guy d’in bai da wani aibu amma a loakci d’aya na lura da yanayin shi kamar yana tashen samartaka ne da kud’i.

A estimating ba zai wuce ishirin da takwas ba, a shekarun haihuwa.

Murmushi nayi kana nace "Haidar na gode da son da kake min, but am sorry ni ba yanzu zan fara soyayya ba, karatu zan yi saboda ban dad’e da kammala Secondary school d’ina ba, kuma a gida ma ba za a bar ni ba"

Lokaci d’aya fuskar shi ta nuna ya shiga cikin damuwa da abin da nace mai dan haka yace "duk da kin bani uzurin ki Fatima amma ina ganin wannan ba hujjar da zaki ce ba za kiyi accepting d’ina ba, ni zan iya jiranki ki fara high institution d’in".

A raina kuwa cewa nayi "wannan daga gani zai yi naci, gwara in lalla’ba shi mu rabu lafiya".

"kayi hak’uri Haidar, ba na son in yi deceiving d’in ka, shi yasa na fito na fad’a maka gaskiya, ina maka addu’ar Allah ya baka mai son ka da gaskiya".

Yalwata murmushin shi yayi kana yace "gaskiya Fatima naji dad’in addu’ar da kika min duk da na gane kora da hali kike min, hakan yasa na gane ba k’aramin rashi nayi ba, duk da ba anshi tayin soyayya ta ba saboda na gano akwai wata baiwa da Allah ya miki, in ba damuwa zan iya

Please Login or Register in order to submit comment