Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce ba yaso saboda ba a lokacin ya shirya ma amsar kyautar da Allah ya bashi ba bayan nan gaba bai san ko Allah zai k’ara bashi irin kyautar da ya mishi a farko, ko da yake kai na ga kayi nisa gurin koyi da yahudu, shi yasa ba za ka ga aibun abin da ka aikata ba".


Saukar mari na ji a fuskata da yasa na razana saboda zafin marin da ya shige ni.


Hawaye ne masu zafi suka fara zubo min a idanu na, halin da nake ciki a yanzu ba zai bar ni in goge hawayen ba dan a yanzu nafi buk’atar su ko na samu sassauci a halin da nake ciki.

X
Murmushin takaici nayi na ce "Dr dan ka mare ni ba komai ba ne tun da har ka iya d’aukar magani ka bani a matsayin maganin typhoid ka bani na sha alhalin maganin abortion kake bani nake sha, ashe shi yasa nake zubar da jini da ciwon mara a lokacin da ka bani maganin na sha, sau biyu kana d’aukar maganin kana bani ina sha, ko tausaya min halin da nake shiga idan na sha maganin ba kayi, tun da kake ba ni maganin ban kawo zaka iya d’aukar abin da zai cutar dani ba ka d’auka ka bani saboda yardar da na baka da soyayyar da nake maka, Dr ka riga kayi breaking d’in trust d’in da na maka, ina ganin a yanzu ba wanda ya rage na yardar dashi tun da wanda na yarda dashi ya ha’ince ni, Dr bazan ci gaba da zuba maka ido kana tafiyar min da rayuwa ta yanda kake so saboda tak’amar ka ina son ka".


Kuka na fara yi wanda ke ta’ba zuciyar duk wani mai saurare, na durk’ushe a k’asa ina ci gaba da kukan.


Cikin kukan na ce "Dr ban ta’ba tunanin haka daga gare ka ba, nasan auren soyayya muka yi da kai amma in ka min wani abin sai in yi tunanin ko ba ka so na ne, tun farkon auren mu ka kawo min maganar family planning kuma na yarda da tsarin ka saboda hujjojin da ka bani na cewa zan yi karatu ne kar in wahala shi yasa kake tausaya min, a raina ba na son yi family planning d’in, na biye maka ne saboda ba na son ‘bacin ranka, but why Dr kai ba zaka guji ‘bacin ran nawa ba?".


Cikin shashshek’ar kuka na ci gaba da cewa "Dr ka fad’a min me yasa ba ka shirya mana haihuwa a yanzu ba bayan kasan kullum lokaci wucewa yake yi, Dr ka fad’a min ko ni ce ba ka so ka haihu dani".


"If you succeed in cheating someone, don’t think that person is a fool, Realize that the person trusted you more than you deserve".


Kallon Dr nayi da ido na da ya canza launi na ci gaba da cewa "but do you know what Dr? There will always be a soft spot in my heart for you, even when you’ve done wrong, even when you’ve let me down, even when you couldn’t care less, No any relationship can be survive without trust, but why did you break that trust Dr".


Jikin Dr ne yayi sanyi da irin kukan da nake yi da maganganun da na fad’a mishi.


Takowa yayi yazo gurin da nake durk’ushe ya tsugunna yana kallo na.


"Am sorry my Zarah" Dr ya fad’a a hankali.


"Dr ba na buk’atar wani ban hak’uri da ga gurin ka".


Ina gama fad’ar haka na tashi na bar gurin.

D’akina na tafi na ci gaba da kuka na, na rasa me yake min dad’i a raina.


Ba na so muna samun sa’bani da Dr amma ban san dalilin shi da yake jawo abin da za mu samu sa’bani ba.


Ashe gaskiyar mutane ne da suke cewa duk yadda aka kai ga yin soyayya a waje, idan aka yi aure sai dai a ci gaba da zaman hak’uri saboda hak’urin ne ke jan ragamar soyayya a zamantakewar auren wanda a yanzu nake ganin misali a kaina, a nan ne za ka k’ara sanin halin wanda ka aura wanda ba ka sani ba kafin ku yi aure.


Abin da ban ta’ba zata daga gurin Dr ba shi yake min, abin da yafi damu na shine ba wanda zan iya fad’a wa matsala ta ya bani shawara saboda gudun kar a yi mana dariya in aka yi la’akari da soyayyar da muka yi da Dr kafin aure, Halima ce nake tunanin zan iya fad’a wa matsala ta saboda ita ce take bani shawarar da nake jin dad’i, yanzu in na fad’a mata za ta iya ma Dr wata fassara ko ta ga laifin shi akan abin da ya min, ni kuma ba zan so Halima ta ga laifin shi ba.


Shawarar da na yanke shine in d’auki mataki na da kaina wanda Dr ba zai sake kamanta yi min haka ba, ko a yanzu na lura jikin shi yayi sanyi da abin da ya aikata min, nasan ba zan juri fushi da Dr ba saboda nima zan iya shiga wani hali na damuwa da tunani, sai dai dole ne in tursasa ma zuciya ta hukunta Dr idan ya min abin da bai kamata ba ta hanyar da ta dace.


Haka na wuni a d’aki ni kad’ai, ba irin tunanin da bai zo min ba akan abin da Dr ya min.


Ranar ko abinci ban d’aura ba saboda ba na jin zan iya yin girki a halin da nake ciki.


Da daddare bayan nayi sallah ta ne na tashi na had’a shayi na sha da snacks kana na kwanta.


Lumshe ido na nayi kamar mai bacci, duk wanda ya ganni a lokacin zai iya zaton bacci nake yi amma a zahiri ba bacci nake yi ba.


Mafita kawai nake nenmar wa kaina ni da Dr dan duk son da nake mai ba zan bari ya nakasa min rayuwa ta hanyar bani pills d’in zubar da ciki wanda nan gaba za su iya shafar mahaifa ta, nasan nan gaba in hakan ta faru wata zai iya nemo wa ya aura a lokacin da yake da buk’atar haihuwa, ni kuma ya barni da danasani, shi yasa nake son d’aukar mataki tun yanzu.


Shigowar Dr d’akin ne yasa nayi saurin bud’e ido na saboda ganin shi da nayi a d’aki na.


Mamakin Dr ne ya mamaye sassan jiki na da har yayi jarumtar shigowa in da nake a yanzu.


Lallai yau na tabbatar da namiji bai da kunya, in ban da haka ya za ayi ya ce har ya manta abin da ya had’a ni dashi d’azun.


Ya d’auki magani ya bani na zubar da ciki, sannan in mishi magana maimakon ya lallashe ni sai ma mari na yayi da maganganu masu zafi da ya bi ni dashi, sannan yanzu da daddare ya zo inda nake da sunan zai kwanta dani, ai kuwa zan nuna ma Dr nasan darajar kaina.


Saurin sakkowa nayi daga kan gado na tsaya ina kallon Dr na ce "Dr me ka zo yi a d’aki na?".
Kai tsaye ya ce min " Kwanciya na zo yi tun da na ga yau kin guji side d’ina".


Dr mamaki yake bani yadda yake da full confidence ko da yayi wa mutum laifi ne ba ya jin tunkarar wanda ya yi wa laifin, in ba haka ba ya Dr zai kalli ido na ya ce min ya zo ya kwanta ne kanshi tsaye.


"Amma ba a d’akin nan za ka kwanta ba ko?" na k’arasa maganar da tambayar shi.


"Ba ni da right ne in kwanta a duk in da nake so, ko ke ce kika sa dokar?" Dr ya fad’a.


Ni ce na ce "Kana da damar kwanta wa a duk in da kake so saboda gidan ka ne, sai dai in har za ka kwanta a d’aki nan ni zan bar maka d’akin ka kwana kai d’aya dan ba zan kwanta da kai ba".


Mamaki na ne ya kama Dr da har ya kasa magana sai bi na da ido da yake yi.



Ganin Dr bai da alamar yi min magana yasa na ce " Dr kai nake jira".



Ban san tunanin da yayi ba, fita kawai na ga yayi daga d’akin.



Kulle k’ofa ta nayi na dawo na kwanta, sai da na jima ina tunani da neman mafita kafin bacci ya d’auke ni.



Washe gari ma haka na tashi na had’a ma Dr breakfast d’in shi akan dinning kana na koma d’aki na kwanta.



Sai da na ji fitar shi daga gidan kana na fito nayi aikace-aikace na kana na je na gyara ma Dr side d’in shi.



Ko da Dr ya dawo daga aiki haka na tarbe shi ba yabo ba fallasa, duk yadda Dr yaso ya ga fara’a ta ban bashi wannan damar ba, duk wata hira da zai min sai dai in bi shi da "Eh ko a’ah", hakan ya tabbatar mishi da fushin da nayi dashi babba ne.



Sai da muka yi kwana uku a wannan halin ni da Dr, ina mishi duk abin da ya dace a matsayina na matar shi, sai dai ba na bashi fuskar da za mu zauna mu yi hira dashi dan kar ya ga saurin sauka ta akan laifin da ya min sannan ban k’ara yarda mun kwana a d’aki d’aya ba dan ban ga amfanin kwanciyar mu a tare ba tun da bai shirya ma haihuwa a yanzu ba.



Yau da daddare ina kwance cikin shigar kayan bacci kalar pink wanda ya amshi kalar jiki na.


Dr ne ya shigo d’akin had’e da sallama.


Amsa mishi sallamar nayi kana na d’auke ido na daga kallon shi.


Gefen gado ya zo ya zauna yana kallo na kana ya ce " Zarah ina son mu yi magana ne"


"Ina jin ka Dr" na bashi amsa a tak’aice.


Dr ne ya ce "Zarah, ba na son in mun samu sa’bani mu dinga irin wannan zaman, ba na jin dad’in shi, ina ganin in komai ya wuce bai kamata a dawo dashi baya ba".


Kallon shi nayi kana na ce "Wani abin na maka Dr? ina sauke duk wani hakk’i da ya rataya a kaina a matsayina na matar ka, ko akai wani abu da nake maka wanda ba ka jin dad’in shi?" Na k’arasa maganar da tambayar shi.


"Zarah nasan na miki laifi kuma na baki hak’uri, ya kamata a ce kin yi hak’uri ki yafe min laifin da na miki, insha Allahu hakan ba za ta sake faruwa a tsakanin mu ba".


Cikin lallashi ya ci gaba da cewa "Fatimah Zarah!" Yanda ya kira suna na ne yasa na ji sunan ya ratsa dukkan sassan jiki na saboda yadda sunan ya min dad’i a cikin raina da kuma yadda ya kira ni da cikakken suna na.


Ji nake yi kamar in amsa kiran sunan na da yayi, sai dai yadda nake jin haushin abin da ya min ba zai bar ni damar amsa kiran suna na da yayi ba.


Bai damu da rashin amsawa ta ba ya ci gaba da cewa "Zarah ki yi hak’uri, ni ma nayi realising d’in mistake d’ina, maganin da na baki ba yana nufin zan cutar dake ba ne, a wannan ‘bangaren ne muka samu sa’banin ra’ayi dake, ni ban ce ba zaki haihu ba, na so ne a ce nan gaba idan na samar miki aiki ki ka fara sai ki haihu, amma yanzu da zarar kin fara haihuwa hidima ce za ta k’arun miki na gida, ga hidimar office da na baby, amma tun da kin nuna you are ready to deliver a baby shi kenan, next time in kin samu ciki ba zan baki pills ba".


Ci gaba yayi da cewa "I know how angry you are…& what you must be going through, so I hope, you know how sorry I am, for all that happens between us, please forgive me".


"Sometimes a genuine apology, a simple hear felt " I' m ‘’Sorry’’ can change everything and start to mend the deepest wounds’’ am sorry for what I have done to you Zarah".


Duk da naji dad’in yadda Dr ya bani hak’uri had’e da kalamai masu dad’i da kwantar da zuciya, hakan ba zai sa in yi saurin yarda dashi ba dan ban san ko zai iya ‘bullo min ta wata hanyar ba.


A d'ayan b'angare na zuciya ta ina jin ba zan ci gaba da fushi da Dr ba saboda ni kaina a takure nake da irin zaman da muke yi dashi, ni kaina ba jin dad’in irin zama da muke yi nake yi ba, nayi hakan ne saboda Dr ya gane laifin da ya min mai girma ne a gurin shi yadda ba zai sake ba.



A yanzu na ga alamar nadama a fuskar Dr wanda daman haka nake buk’ata, sai dai ina ganin akai wata hanyar da zan k’ara hukunta Dr cikin sauk’i da zai gane kuskuren shi.


"Kin hak’ura Zarah?" Dr ya katse min tunanin da nake yi.


"Ba komai Dr, komai ya wuce a guri na" na fad’a ina sakar mishi tsadadden kallo na.


Murmushi ya sakar min kana ya ce "Na gode my Zarah".


Nima murmushin na mayar mishi kana na ce "Don’t mind Dr".


Hawa kan gadon yayi hugging d’ina.


A haka Dr ya fara fad’a min tsadaddun kalmomin shi da suke sa ni natsuwa a duk lokacin da na saurare su.


Canza hirar yayi da fara sakar min soft kiss ko ta ina a jiki na, yadda Dr yake min kai kasan yayi missing d’ina, ni kaina nasan nayi missing d’in Dr amma ba zan bashi wannan damar ba saboda ta wannan hanyar ce nake ganin ta rage min da zan k’ara amfani da ita wajen hukunta Dr akan abin da ya min duk da na hak’ura.


Janye jiki na nayi daga jikin Dr na matsa gefe.

Dr ne ya d’ago ya kalle ni a wahalce kana ya fara magana cikin sanyin murya ya ce "Zarah menene haka kike yi".


Duk da na fahimci abin da yake nufi sai na nuna mishi ban fahimta ba na ce "Me nayi Dr".


Dr ne ya ce " Ya za ki bari sai da muka yi nisa da faranta junan mu sannan sai ki janye jikin ki daga gare ni, miye amfanin abin da kika min kenan".


Ni ce na ce "Dr ni ban ga abin da na maka ba, tuno wa nayi da planning d’in da ka tsara ma rayuwar mu, shi yasa ba zan bari ka kasance dani ba".


A halin Dr yake ciki ba zai iya ci gaba da maganar da yake yi ba.


Matsowa yayi ya had’a ni da jikin shi.


Mutsu-mutsu na fara yi dan ganin na k'wace kaina daga rik’on da Dr ya min, amma da yake rik’on namiji daban ne na kasa, hakan yasa na sa mishi kuka na fara cewa " Dr ni ka sake ni, ba zan bari kayi amfani da ni ba sannan in na samu ciki ka ‘barar min, tun da ka ce ba ka shirya ma haihuwa ba ina ganin kasancewar mu a wajen tarayya da junan mu bai da wani amfani, ni zan jira duk lokacin da kake da buk’atar haihuwa sannan sai in baka jiki na amma ban da yanzu".


A hankali ya sake ni ya sakko daga gadon.


Idon shi ne ya canza launi, daga gani yana cikin halin buk’ata ta, ni kaina da na kalli yanayin shi nasan yana cikin wani hali, tausayin shi ne ya kama ni, sai dai ba na jin zan iya bashi wannan damar, nasan wannan hukuncin da na yi ma Dr shi zai kaini ga k’watar ma kaina ‘yanci na a gurin shi.


"Zarah ba na baki hak’uri ba kika ce min kin hak’ura? Sai yanzu da kika ga ina da buk’atar ki shine za ki nuna min ba ki hak’ura ba, ba komai jikin ki ne, ba zan matsa miki ba" yana gama fad’ar haka ya bar d’akin.


Yana fita na fara kuka saboda nima ba a son raina na mishi haka ba, ni kaina ba na son in ga na ‘bata mishi rai, sai dai a yanzu ya zama dole in bi wannan hanyar da in ta za ta kai ni ga samun cin nasara.


Sai da na jima a wannan halin kafin na samu barci ya d’auke ni.


Washe gari da Dr da ‘bacin rai ya tashi, ko da na gaishe shi da k’yar ya amsa min, breakfast d’in da na had’a mishi ko kallon shi bai yi ba ya wuce aiki.


Haka da ya dawo side d’in shi ya wuce, sai da lokacin sallah yayi sannan ya fito ya tafi masallaci.


Ko da na kwanta bacci kasa sukuni na yi saboda yau through out ban ga sakin fuska daga gurin Dr ba.


Yakamata tun da ya gane laifin da ya min in hak’ura, gashi a maimakon mu samu sasanci a tsakanin mu na k’ara damula lamarin tun da jiya ban bashi kaina ba wanda a dalilin haka yake fushi dani.


Tuno hukuncin da duk namijin da ya nemi matar shi ta hana shi nayi, hakan yasa hankali na ya k’ara tashi, nasan Allah ba zai kar’bi uzuri na ba akan hukuncin da nayi ma Dr na hana shi kaina.


Hijab d’ina nasa da wani tsadadden flat shoe d'ina na nufi side d’in shi.


Samun shi nayi a zaune yana danna laptop.


K’arasa shigowa nayi had’e da sallama a baki na.


Motsin da bakin shi yayi ne ya tabbatar min da amsa sallama ta yake yi.


Kusa dashi na zo na zauna.


Shiru ne ya ratsa d’akin kamar ba kowa a ciki.


Dr ne ya kau da shirun da cewa "Ina fatan lafiya ko Zarah na gan ki a d’aki na a wannan lokacin".


Kallon shi nayi jin yadda ya fad’a min maganar, nasan fushin abin da na mishi jiya ne yake so ya huce a yanzu.


Marairaice fuskata na yi kana cikin shagwa’ba na ce " Dan ka gan ni a d’akin ka a wannan lokacin ai ba laifi ba ne Dr tun da d’akin my lovely husband d’ina ne na shigo".


Dr ne ya ce "Laifi ne a guri na tun da jiya da naje d’akin ki kin haramta min kwana, kin ga kenan nima dan na tuhume ki da na ganki a wannan lokacin ai ba laifi ba ne".


" I am sorry to say that sometimes matters of very small importance waste a good deal of precious time, by the long and repeated speeches and chicanery of gentleman who will not wholly throw off the lawyer even in congress, Am sorry Dr for what I have done to you yesterday, i will not repeat my mistake" Na fad’a cikin kwantar da murya da lallashi.


Shiru yayi yana kallo na, da alama maganganun da nayi amfani dashi ya sanyayar masa da jiki akan fushin da yake yi dani.


Hakan da na fahimta yasa na fad’a jikin shi na fara mishi kukan shagwa’ba.


A hankali Dr ya fara lallashi na tare da goge min hawayen da ya fara zuba a idanu na yana cewa "Stop crying my Zarah".


D’ago kaina nayi cikin marairaicewa na ce "Dr ka hak’ura da laifin da na maka jiya?".


Murmushi ya sakar min kana ya ce " Na hak’ura Zarah, ba wanda ya wuce kuskure, but pls stop crying my baby".


Saurin goge hawayena nayi, in a cool voice na ce "Na daina kukan Dr tun da ba ka so".


"Shi yasa nake son ki my Zarah" Dr ya fad’a.


Da wannan dubarar na samu na shawo kan Dr muka shirya.


Haka zaman mu ya dawo normal da Dr kamar ba mu samu sa’bani a baya ba.




Yau yaya Faru k ne suke zaune a falo da Nana suna kallon wani film da ake watsowa a tashar Joy prime na indian series mai suna Jansi Kirani.


Wayar yaya Faruk ce tayi k’ara alamar kira ya shigo wayar shi.


Ganin sunan wacce ke kirar shi yasa ya d’an saki murmushi kana ya d’auka.


"Assalamu alaikum Binafa" yaya Faruk ya fad’a.


Daga can ‘bangaren Binafa ce ta amsa mishi da "Wa alaikumus salam Bregadier Umar".


Binafa ce ta ce "Bregadier ya kwana biyu ya kuma amarya".


Juyawa yayi ya kalli ‘bangaren Nana da idon ta ke kanshi tun san da ya d’auki waya ya ambaci sunan Binafa hankalin ta ya dawo gurin shi.


Had’a idon da suka yi ne yasa ya tayi saurin saukar da idanun ta k’asa.


Murmushi ya sakar mata kana ya dawo kan hankalin shi ga wayar da yake yi da cewa "Lafiya lau Binafa".


"Ai nayi fushi Bregadier tun da ba ka nema na, nayi zaton za ka dinga kira na mu gaisa amma sai ba ka kira ni ba, rabon da muyi waya da kai tun San da na kira ka kace min kayi aure".


"Sorry Binafa ban samun time ne shi yasa, ya su Momy da Dad" yaya Faruk ya fad’a.


Cikin shagwa’ba Binafa ta ce "Daman nasan haka za ka ce ba ka da time, su Mom da Dad suna nan lafiya".


Mik’ewa Nana tayi da niyar barin falon saboda yadda ta fara jin ranta ya ‘baci akan wayar da yaya Faruk yake yi.


Yaya Faruk ne ya sa d’ayan hannun shi ya r’ikota ta fad’a kan jikin shi.


Binafa ce ta ce "Bregadier kasan dalilin kiran ka da nayi".


"No sai kin fad’a" yaya Fruk ya ba ta amsa.


"Na kira ka ne in faad’a maka biki na ya kusa" cewar Binafa.


Yaya Faruk ne ya ce "Congrat Binafa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya a tsakanin ku".


"Na gode Umar da wannan addu’ar taka, my regard to ur groom" Binafa ta fad’a.


"Don’t mind Binafa, a gaishe min da angon" cewar yaya Faruk.


"Zai ji insha Allah" Binafa ta amsa mishi.


"good bye Umar".


"Take care".


Katse wayar yayi ya juyo da kallo shi ga Nana wacce yanayin ta ya canza.


A yadda ya fahimci yanayin ta, yasan kishi ne ke danun ta tun san da Binafa ta kira shi a waya,i dai yasan ba za ta iya mishi magana ba duk da ya ga yanayin ta ya canza.


"Ya aka yi ne Khadija" Yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta.


Cikin sanyinta ta amsa mishi da cewa "Ba komai yaya Faruk".


"Wayar da na amsa ce ta ‘bata miki rai ko?" yaya Faruk ya jefo mata tambaya.


Girgiza mishi kai tayi alamar ba haka ba ne.


Murmushi kawai yayi saboda ya san amsa wayar da yayi ne ya sa mood d’in ta ya canza, yasan ba taso ya fahimci hakan ne.


Wannan halayen na Nana su suke k’ara mata martaba da daraja a idanun shi, shi kan shi a yanzu yasan da cewa ya fad’a tarkon son Nana, sai dai ba ya jin zai yi saurin furta mata Kalmar so a yanzu saboda har yanzu tabon da ke zuciyar shi bai gama warkewa ba.


"Wacce muka yi waya da ita akwai mutunci a tsakani na da ita,, sunan ta Binafa, yanzu haka ta kira ne ta fad’a min za tayi aure, apart from that babu wani abu dake tsakanin mu, na ga k’anwa ta har ta fara kishin Binafan" yaya Faruk ya k’arsa maganar da wasa.



Rufe fuskar ta tayi tana dariya.



Murmushi yaya Faruk yayi ya ce "Ashe gaskiya na fad’a kenan tun da gashi kin rufe fuskar ki".


Da sauri ta bud’e fuskar ta cikin shagwa’ba ta ce " Ni fa ba kishin ta nake yi ba yaya Faruk".


"In ba kishin ta kike yi ba mai yasa mood d’in ki ya canza kuma sannan kika mik’e za ki bar gurin" cewar yaya Faruk.


"Ba komai" Nana ta bashi amsa.


Haka yaci gaba da tsokanar ta ita kuma tana biye mishi, haka suka ci gaba da hirar su cikin annashuwa.




A ‘bangare na komai yana tafiya yadda nake so a zamantakewar mu da Dr, sai dai matsalar da na far fuskanta da Dr shine yadda a yanzu kusancin su yayi yawa da Dr.


Idan na mishi magana sai ya nunar min da babu wani abu dake tsakanin su da ya wuce k’anwar shi ce sannan ga matsalar da ke damuna na rashin samun ciki da ban yi ba wanda har yanzu na lura Dr haka bai dame shi ba, abin ya fara damu na, gashi na rasa wanda zan fad’a ma wa in ji dad’i a raina.


Ga yawan zuwan da Meeman da take yi, wani lokacin takan zo da Hanan ko ta zo ita kad’ai.


A zuwan da take yi ne na fahimci closeness d’in su da Dr yayi yawa, ga waya da suke yi da ita.




Yau ranar ta kasance ranar weekend ne, ina zaune ina kallon pix a wayan Dr yayin da shi yake d’aki yana bacci.


Wasu hotuna ne suka d’auki hankali na a cikin wayar Dr wanda yasa na maida hankali na gurin hoto.


Dr ne da Meema suka

Please Login or Register in order to submit comment