Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali.


Yaya Khalil ne ya kira Anisa ya sanar da ita ya zo gidan yana falo, tare muka fito falon da ita.


Samun su muka yi da yaya Faruk da Nana suna hira.


Tun da na shigo falon yaya Khalil ke bi na da kallo.


Gaishe shi nayi nayi ba tare na k’ara cewa komai ba.


Hira aka ci gaba dayi ba tare da na saka baki na ba, duk hirar da suke yi ina sauraron su.


Bai wani jima ba ya musu sallama ya fita.


Anisa ce ta bi shi ta dawo ta sanar dani yaya Khalili na kira na.


A harabar gidan na same shi yana jingine jikin motar shi.


Jiki a sanyaye na k’arasa kusa dashi.
Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kana na kau da shirun da cewa "yaya Khalil ya su Abbu da Ummu".


"suna nan lafiya kau" yaya Khalil ya amsa min.


Yaya Khalil ne ya ce "Fatima ashe abin da ya faru kenan, san da Ummu ta fad’a min sakin da Dr ya miki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, ban ji dad’in abin da ya faru ba, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tsakanin ku, idan kuma da rabon ki koma sai Allah ya daidaita ku ki koma d’akin ki".


Yaya Khalil ne ya ci gaba da cewa "Amma Fatima me kika mishi ya sake ki?" ya k’arasa maganar yana kallo na.


Sunkuyar da kaina na yi yayin da hawaye ya tarun min a ido na ce "yaya Khalil baa bin da na mishi, kawai dai mun sami misunderstanding da shi ne akan auren da yake son k’arawa wanda a dalilin haka yasa muka rabu".


"Fatima saboda zai k’ara aure ne yasa ki ka d’aga hankalin ki har ta kai kun sami matsala dashi ya sake ki, me yasa ba ki yi hak’uri ba tun da wanda zai aura ba akan ki zai ajiye ta ba, kin san kuma namiji mijin mace hud’u ne, why Sis" cewar yaya Khalil.


"Yaya Khalil ba akan shi kad’ai muka samu matsala ba, Momin shi ce ke son yayi auren, dan na mishi magana shine ya ce min wai zai yi ma Momin shi biyayya, ba zai yi irin mistake d’in da nayi ba da ban ji maganar su Abbu ba…" na k’arasa maganar da fashewa da kuka.


Cikin kukan na ci gaba da cewa "yaya Khalil su Abbu na fushi dani ko? nasan tafiyar nan da za ayi dani Abuja Abbu bai yarda in dawo gida ba ne, yaya Khalil I have ralised my mistake, ina so in nemi yafiyar su Abbu da Ummu, I have learnt a lesson".


Tun da na fara maganar yaya Khalil yake kallo na, da gani yana ji tausayi na ne.


Hannu na ya rik’e yana girgiza min kai.


Jikin shi na fad’a na ci gaba da kukan, bai hana ni yin kukan ba dan yasan a hali da nake ciki a yanzu ina buk’atar yin kukan.


Sai da ya ga nayi shiru ya d’ago ni da ga jikin shi.


Cikin lallashi ya ce "Anisa komi da ya sami bawa rubutacce ne a gurin ubangiji, sai dai kamar yanda kika ce Dr ya ce miki shi zai yi ma Momin shi biyayya ba zai yi mistake d’in da kika yi ba kin ga anan darasi ne babba a gurin ki da ya kamata ki d’auki izinah, Fatima ko da su Abbu suka amince aka yi auren ki da Dr kin san wanda suke so ki aura amma saboda son da ya rufe miki ido yasa ba ki duba hakan ba, akan ki yarda da k’udurin sun a auran yaya Faruk shi yasa Abbu ya sa miki wannan sharad’in amma duk da haka Fatima sai ki ka amince da wannan sharad’in, Fatima ni da yaya Aminu sau nawa muka miki magana akan ki bi abin da su Abbu kike so but you reduce, sau nawa na nuna miki b’acin raina na kuma zaunar dake na miki fad’a akan abin da kike niyyar yi is not wright but still Fatima you did’nt take my advice, yanzu mai gari ya waya tun da shi wanda kika yi domin shi gashi shi yake miki gorin abin da kika yi at the end kuma ya sake ki sannan kuma zai bi umarnin Momi d’in shi ya auri wacce take so yau aura, kin ga ba ki yi gaining d’in komai ba".


Cikin shashshek’ar kuka na ce "yaya Faruk I want to see Abbu & Ummu, ina so su yafe min, ba na so su ci gaba da fushi dani, I miss them".


Yaya Khalil ne ya ce "Ki daina kuka Fatima, Abbu da Ummu ba fushi suke yi da ke ba, sai dai a yanzu dole su shiga damuwa jin abin da ya same ki, Fatima ko wani iyaye dole ya shiga damuwa idan aka yi divorcing d’in y’ar shi, Abbu yana cikin b’acin rai ne, nasan idan ya sauka zai ma yaya Faruk magana ya dawo dake, kar ki damu su Abbu za su yafe miki, ki daina sa ma kan ki damuwa Fatima, komai zai wuce, ban ji dad’in ganin ki haka ba, kowa ya kalle ki yasan ki na cikin damuwa, stop worrying your self kin ji my sis".


"Toh yaya Khalil zan kiyaye" na fad’a cikin sanyin murya.


Murmushi yayi yaya Khalil yayi kana ya ce "that is my Sister, so smile for me".


Ban san lokacin da murmushi ya sakar min a fuska ta ba.


Fuskar yaya Khalil ce ta k’ar yalwatuwa da murmushi ganin na yi murmushi.


Kallon wrist watch d’in shi da ke hannun shi yayi kana ya ce min "Fatima zan koma gurin aiki, excuse na nema na fito, ki kira min Anisa sai in sauke ta a gida".


"yaya Khalil ka gaishe min da su Ummu da Abbu da yaya Aminu da su Anty Jidderh" na fad’a a hankali.


"Za su ji" yaya Khalil ya amsa min.

Falon na koma na sanar da Anisa yaya Khalil na jiran ta.


Sallama ta ma su Nana kana muka jera tana ci gaba da kwantar min da hankali.


Sai da na ga sun shiga motar sun fara tafiya na musu waving d’in hannu na, su ma waving d’in su ka min.


Koma wa nayi cikin d’akin ban sake fito wa ba.


Wajen la’asar yaya Faruk ne ya shigo d’aki na.


Yau ma kamar kullum fuskar nan tashi a d’aure take ya tsaya a gefe.


Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin ya kau da shirun da cewa "Fatima za mu koma Abuja yanzu, ina so in ji saki nawa ya miki saboda akwai sakin da in aka yi shi in har ba kin gama iddah ba kina matsayin matar shi ce in dai ya maida ke a lokacin, za mu tafi dake Abuja ne na d’an wani lokaci.


Ji nayi jiki na yayi wani irin sanyi, nasan tun da yaya Faruk ya ce zan bi su Abuja hakan na nufin cewa Abbu bai hak’ura ba da sharad’in da ya sa min, ji na ke yi kamar in ce ma yaya Faruk ba zan bi su ba, ko a nan d’in ma a takure nake saboda rashin sakewar fuskar yaya Faruk da kuma yanda wani lokacin suke gudanar da soyayya su a gaba na ba tare da jin kunya ba, Nana ce ma wani lokacin take nuna jin kunyar ta idan yaya Faruk yayi mata wani abin a gaba na.


Sai dai nasan ba ni da mafita da ta wuce bin su d’in tun da nasan Abbu bai yarda da dawowa na gida ba tun da har na ji yaya Faruk bai fad’a min yadda suka yi da Abbu ba.


Cikin sanyin jiki na ce "Saki d’aya ya min".


"Kin ga kenan kina matsayin matar shi tun da ba ki gama iddah ba in har yace ya dawo dake, ki shirya kayanki".


Yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin.

Jiki a sanyaye na had’a kayana na zauna jiran su.


San da za mu tafi Abujan ne Nana ta shigo ta min magana in fito mu tafi.


Trolik d’ina na d’auka muka shiga mota muka nufi Abujan.

Wajen magrib muka isa Abuja.


Nana ce ta nuna min d’akin da zan zauna.


Ina shiga d’aki na shiga band’aki na watsa ruwa.


Kaya mara sa nauyi na sa ka.


Ban fito d’akin ba sai da Nana ta zo ta min magana in zo mu ci abinci.


Bayan mun gama cin abincin ne na koma d’akin da aka sauke ni.


Ban jima da shiga d’akin ba na ji waya ta tana kuwwa.


Ganin sunan Ummu da na yi ne yasa jiki na ya k’ara sanyi.

Cikin sanyin murya na d’auka kana na gaishe ta.


Amsa min tayi kana ta d’aura da cewa "Fatima kuna Abujan ne".


"Eh Ummu" na amsa mata.


Ummu ce ta ce "Fatima tun san da Faruk ya zo ya fad’a min mummunan labarin abin da ya same ki hankali na ya gaza kwanciya, na so a ce kina kusa dani a yanzu sai dai ba ni da halin yin haka a dalilin zafin da Abbun ku ya d’auka kuma ba kowa ya jawo hakan ba fa ce ke Fatima da kika yarda da sharad’in shi, yanzu ga avin da kika yi ya jawo miki, ke yanzu abin farin cikin ki ne a ce wannan mummunan k’addarar ta same ki amma ba kya gaban iyayen ki, abin da yasa hankali na ya kwanta shi ne nasan Faruk zai kula dake amma duk da haka ina so ki yi taka tsantsan saboda ba ki gama iddah ba, yanzu saki nawa shi Sadik d’in ya miki" Ummu ta k’arasa maganar da tambaya.


"Saki d’aya ya min" na amsa mata.


"Allah yasa hakan shi yafi miki alkhairi, in kuma da rabon ki koma gidan Dr Allah ya daidaita ku, ki kula Fatima, kin ga har yanzu ba ki fita iddar ki ba, yanzu shi Dr d’in yana cewa ya maida ki kin maidu, sannan ki zauna da Nana lafiya nasan ba ta da matsala, insha Allah ba wani dad’e wa za ki yi a Abujan ba, nasan Dadin ku zai mishi magana, yanzu ma dan yana kan k’udurin shi ne shi yasa bai yadda kin dawo gida ba, ki yi hak’uri kin ji Auta".


Wani irin tausayin kaina da na Ummu ne ya kama ni a lokacin.


Nasan Ummu ma na cikin damuwa akan sakin da Dr ya min, a maganar da ta min na fahimci haka.

Ban san lokacin da na fashe da kuka ba.


Ummu ce ta katse ni cikin tashin hankali ta ce "Yanzu mi ye abin kuka daga magana".


Cikin kuka na ce "Ummu ku yi hak’uri ku yafe min, ki neman min yafiya a gurin Abbu akan laifin da na muka a baya".


"Ki daina kuka Fatima, na yafe miki, idan kika dawo Kadunan za mu yi magana, Abbun ki ma zai yafe miki".


Cikin shashshek’ar kuka na ce "Na… gode…Ummu".


"Ki gaida su Khadijan" Ummu na gama fad’ar haka ta katse wayar.


Kuka na naci gaba wanda ni kaina ban san dalilin yin kuka na ba.





Yau muna zaune a falo ni da Nana kasancewar ta je lectures ta dawo da wuri, yaya Faruk na wajen aiki.


Anty Maryam ce ta shigo rik’e da hannun Asim.


Gaisawa muka yi kana na tashi na d’akko mata drinks da snacks na ajiye mata na rik’e hannun Asim muka wuce d’aki na.


Bayan tafiya ta ne su Nana suka ci gaba da hirar su.


A cikin hirar ne Anty Maryam ta ce "Nana bak’uwa kuka yi ne, kin san tun da kuka dawo Kadunan ban samu shigowa ba, san da kuka shigo gurin mu kuma ba ku shigo da ita ba".


"Fatima ce k’anwar yaya Faruk" na amsa mata.


Da sauri Anty Maryam ta ce "Wai wace Fatiman kike magana?".


Nana ce ta ce "Fatima dai da kika sani y’ar uwar yaya Faruk".


"Tare kuka tawo da ita kenan?" Anty Maryam ta sake watso mata tambaya.


"Eh tare muka tawo da ita" Nana ta fad’a.


"Ina fatan lafiya dai kuka tawo da ita" Anty Maryam ta sake tambayar Nana.


Nana ce ta ce "Sun rabu da mijin ta ne, shine yaya Faruk ya ce Dadin shi ya ce ya tawo da ita".


"Kina nufin nan za taci gaba da zama kenan" cewar Anty Maryam.


"yaya Faruk ya ce ba dad’ewa za tayi ba" Nana ta fad’a.


Nana ta ci gaba da cewa cikin marairaicewa "Anty Maryam tun da yaya Faruk ya ce zai tawo da Fatima na rasa peace of mind d’ina duk ya tabbatar min da yanzu ba wata alak’a ta soyayya da zai k’ara shiga tsakanin su da ita amma hankali na gaza kwanciya, nasan in har yaya Faruk suna zama a guri d’aya da Fatima wataran dole ya ji son ta ya dawo mishi a cikin zuciyar shi ya ji yana sha’awar auren ta, Anty Maryam ke kan ki shaida ce a irin son da yaya Faruk ya ma Fatima, nasan har yanzu ba yanda za ayi ya ce ya rabu da son Fatiman a zuciyar shi, sai dai yana dannewa ne dana bin da ta mishi, kin ga in har yaya Faruk ya dawo da Fatima rayuwar shi ban san yanda zan yi ba in hakan ta kasance" ta k’arasa maganar cikin rawar murya.


Anty Maryam tsura matai do tana kallon ta, ganin hawayen da ya tarun ma Nana a ido yasa tai tausayin ta ya kama ta, tasan Nana tana da hak’uri da kau da kai, tun da ta fito tayi magana abin na damun ta ne.


Cikin lallashi Anty Maryam ta ce "ki yi hak’uri Nana kar ki sa damuwa a ranki, nasan dole hankalin ki ya tashi akan tawowa da Fatima da kuka yi, shawarar da zan baki shine kar ki sa ma zuciyar ki wani tunani daban tsakanin Fatima da Faruk, ina so ki ci gaba da zama da ita Fatiman lafiya, ina so ki yarda da maganar da shi Bregadier ya fad’a miki cewa ba wata alak’a da za ta had’a shi da Fatima, nasan tun da ya fad’a miki wannan maganar to hakan take a ranshi, ki ci gaba da hak’urin da na san ki dashi, kar ki bari shaid’an ya fara sa mi ki wani tunani na daban a ranki, duk abin da kika ga ya samu bawa to rubutacce ne daga wajen ubangiji".


"Na gode Anty Maryam, insha Allah zan yi amfani da shawarar da ki ka ba ni" Nana ta fad’a cikin cool voice d’in ta.


Murmushi Anty Maryam tayi kana ta ce "yawwa Nana, Allah ya k’ara ba ku zaman lafiya da Faruk d’in".


Cikin fara’a ta amsa da "Amin Anty Maryam".


Da haka suka canza hirar da suke yi, sai da Anty Maryam za ta tafi ne sannan Nana ta shigo d’akin da na ke ta amshi Asim a hannu na.


Fitowa nayi muka yi sallama da ita.
[9/23, 19:08] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



www.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa Writers Association






*TUNATARWA*:


HIKIMA ZINARIYA!!!


_Komai a duniya yana da mabud’i_.


_Mabud’in ilimi shine tambaya_.

_Mabud’in nasara hak’uri_.

_Mabud’in arzik’i tsoron Allah_.

_Mabud’in zaman lafiya adalci na gaskiya_.




*Hattara da mabud’ai guda uku*


_Fushi mabud’in azaba_.

_Tsoro mabud’in fitina_.

_Kwad’ayi mabud’in wahala_.






97 & 98


Tun daga wannan lokacin zama na yaci gaba da kasancewa a gidan yaya Faruka a Abuja.


Sai dai zama na a Abuja ba wani ci gaba da na samu na raguwar damuwa ta sai ma k’arin damuwa da na samu saboda yanda zaman kad’aici yake damu na in Nana ta tafi makaranta, ga rashin sakewar fuskar yaya Faruk da ba na gani, in an ga walwala ta wani lokacin bai wuce gurin Nana ba, sai wani lokacin in Nana za ta je block d’in Anty Maryam ta kan nemi rakiyata.


Ba laifi muna waya da yaya Khalil da Anty Jidderh da Ummu, yaya Aminu ma yak an kira ni, Anisa ma da Halima da Aisha muna waya dasu, Dadi da Momi sun kira ni sun jajanta min abin da ya faru, san da Dadii ya kira ni haka ya dinga kwantar min da hankali da min nasihohi masu ratsa zuk’ata, tabbas na ji dad’in maganganun Dadi da ya fad’a min.


Zaman Abuja ya ishe ni, ji nake yi kamar in yi tsuntsuwa in ganni a gaban iyaye na, sai dai abin da yake k’ara sanyayar min da jiki shine duk wayar da muke yi da Ummu ban ji wani labari mai dad’i a gurin ta na cewa Abbu ya hak’ura da fushin da yake yi, nasan in har Abbu ya sauka daga fushin da yake yi zai nemi da in dawo gida.


Duk wanda ya ganni a lokacin sai ya tausaya min, na yi bak’i na rame, da ka kalle ni kasan ina cikin damuwa, Na dawo so silent & cool.


Tun ina mamakin rashin kiran wayar Dr da bai min ba har na daina dan nasa ma raina cewa a yanzu na daina d’aura ma kaina wani tunani a game da soyayyar Dr, nasan a yanzu ba ta ni yake yi ba, ta amaryar da yake shirin yi yake yi, na san cewa dole wataran sai Dr yayi nadamar abin da ya min dan ya ci amanar soyayyar da na mishi ta gaskiya.


Haka na ci gaba da zama a gidan yaya Faruk, gashi a yanzu ina neman wata d’aya a gidan, kullum buri na shine in ji Ummu ta ce Abbu ya ce in dawo gida.


Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk.


Samun shi nayi a falo yana kallon wani American film.


Tun da na gaishe shi ya amsa min ba Wanda ya sake magana a tsakanin mu.


Ganin zaman ya ishe ni gashi ni American film d'in ba wani damu na yayi ba yasa na kau da shirun da cewa " Yaya Faruk in ban takura maka ba ina so muyi magana ne".


"Ina jin ki" ya amsa min ba tare da ya daina kallon da yake yi ba.


Nisawa nayi kana na ce "Yaya Faruk daman na ji shiru ne har yanzu ba ka min maganar komawa ta Kaduna ba kuma Yaya Faruk Sai na ga kamar zama na kamar ina takura mu ku ".


Sai a lokacin ya d'ago ya kalle ni.


Cikin d'aurewar fuska yace " Yanzu me kike so a miki da kika zauna kina min explanation, k'ofa a bud'e take in za ki koma Kadunan ne, in ban da ke stupid ce za ki zo kina ce min wai ko kin takura mana, dan uban ki ni ko Khadija ce muka ce kin takura mana ko kin ga wata alama ta an gaji dake ne?" ya k'arasa maganar yana kallo na.


Hawaye ne ya tarun ma a ido, danasanin tunkarar Yaya Faruk nayi da wannan maganar, ga zagin da ya min ya min ciwo amma ba halin in nuna.


Tsawa ya daka min ya ce "Ba da ke nake magana ba Fatima, ko Sai kin ji a jikin ki".


Girgiza mi shi kai nayi alamar a'ah, dan nasan in na yi magana kula ne zai biyo baya.


Yaya Faruk ya d'aura da cewa " Ke in ban da ba ki da kunya ba, ban yi tunanin za ki iya tunkara ta da maganar cewa wai kin ji shiru akan maganar komawar ki Kaduna, ko da yake tuntuni na fahimci kin canza dabi'un ki, saboda haka ba abin mamaki bane, in kinga kin koma Kaduna to Abbu ne ya ce in dawo da ke, ke in ban da baki da hankali ma Fatima, ni ina sha kin zo ne ki min magana akan in kira Abbu da Ummu in basu hak'uri amma shine za ki zo min da rubbish words d'in ki, in kin San zaman wani guri zai takura ki me yasa tun farko kika yarda da sharad'in Abbu, sai yanzu za ki zo kina min complain, in kika k'ara tunkara ta da wannan maganar sai jikin ki ya fad'a miki, kar kiyi zaton ko yanzu kin girma, a guri na har yanzu ke yarinya ce a guri na, dan haka ki tashi ki ba ni guri".


Wani irin abu ne ya tsaya min a mak'oshi na d'acin maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min, nasan duk maganar da Yaya Faruk ya fad'a min ni na jawo ma kaina.


Gaba d'aya jiki na ba laka haka na tashi na koma d'aki na dasa kukan b'acin ran maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min.


Da na gaji da kukan ne na goge hawaye na.


Ni kaina yanzu nasan kuka ya zama abin ci na dan yanzu abin kuka ba ya min yawa.




Yau Dadi ne ya sami Abbu a office d’in su na Wagini motors.


Bayan sun gaisa ne su ka tattauna akan b’angaren business d’in su, daga nan Dadi ne ya canza hirar da zuwa magana ta.


Dadi ne ya ce "Ibrahim akwai maganar da na ke so mu yi".


Abbu ne ya amsa masa da cewa "To yaya ina jin ka".


"Ibrahim tun san da ka fad’a min an saki Fatima ban k’ara jin kayi maganar ta ba, na ji duk abin da ya faru da ka cewa Faruk wai Fatima ta bar gidan shi sannan kai kuma ba ka ce ta dawo gidan ka ba, abin da yasa ban ce ma Faruk ya kawo ta gida na ba saboda nasan in ta je Abujan za ta samu sauk’in damuwar da take ciki, da ka ce ta tafi to ina kake so ta je? San da ka sa ma Fatima sharad’in na d’auka saboda a lokacin ran ka a b’ace yake shi yasa, ashe kai da gaske ka ke yi, wannan hukuncin da ka yanke sam ba mafita ba ne, nasan Fatima tayi laifi a baya amma kuma ba wanda ya wuce kuskure, duk abin da ka ga ya samu mutum to Allah ya k’addara hakan zai same shi ko yaso ko yak’i, in dai Allah yace (kun) kasance to sai ya kasance, in ita Fatima yarinya ce da k’uruciya kai ai mahaifin ta ne, dole ka mata uzuri a matsayin ta na y’ar da ka haifa, nasan ita kan ta Fatiman sai tayi nadamar abin da ta aikata a baya sannan ba inda za ta ji dad’in zama fiye da gidan iyayen ta, nasan ita ma mahaifiyar ta d’in hankalin ta ba a kwance yake ba akan abin da ya sami Fatiman sannan gashi ba a gaban ta take ba, na zuba maka ido ne dan in ga iya gudun ruwan ka amma na ga kai ba ka da ranar sauka daga fushin da ka yi, hakan da ka yi ya nuna kamar ba ka yarda da k’addarar da za ta iya samun bawa a ko wani lokaci ba, saboda haka ina so Ibrahim ka amince da dawowar Fatima gidan ka sannan ka mata addu’ar Allah ya zab’a mata abin da yafi alkhairi sannan ka yafe mata kuskuren da tayi maka a baya".


Nisawa Abbu yayi kana ya ce "yaya na yafe ma Fatima abin da ta min, na kuma gano kuskuren da nayi na cewa kar ta tunkare ni da matsalar ta in ta sami matsala da mijin ta, zan ma Faruk d’in magana ya dawo da ita".


"yawwa Ibrahim hakan ya kamata ka yi, hak’uri ake yi da yara, Allah ya shirya mana zuri’ar mu baki d’aya" cewar Dadi.


"Amin ya Allah" Abbu ya amsa.


Da haka Dadi ya koma office d’in shi dan ci gaba da aikin shi.


Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk.


Samun shi nayi a falo yana Da




A b’angaren Dr kuwa ya ci gaba da mu’amalar shi da zuwa ayyukan shi cikin kwanciyar hankali.


Wani lokacin in ya ga tunani na zai kama shi sai yayi saurin kau da tunanin.


Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa bikin Dr da Meema.


Wata d'aya kawai aka sa kasancewar ko wani b'angare a shirye su ke.


Meema tun da taji an yi fixing d'in bikin su ta rasa in da za tasa kan ta saboda murna.


Shirye-shirye da event suka dinga shirya ita da Hanan.


A gurin Dr kuwa ba yabo ba fallasa haka game da shirye-shiryen bikin.


Komai aka sa ma rana sai yazo dan a yau ne aka d'aura auren Meema da Dr.


Wani b'angare a gidan Dr ya gyara ma Meema saboda gidan babba ne.


Ko san da aka d'aura auren Dr bai yi wani farin ciki ba, yasan ya amince da auren ne saboda yayi ma Momin shi biyayya da kuma tausaya ma Meema da yake yi.


Ran first night d'in su da ya kasance da Meema yayi mamakin samun ta a virgin da yayi saboda ganin yanda ta ke

Please Login or Register in order to submit comment