Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a baya amma na gane kuskure na, nasan ka na duba abin da na maka a baya ne shi yasa ka ke ganin kamar da wasa na ke yi, yaya Faruk ka manta baya ka amin ce min ka kuma ci gaba da so na kamar yanda a da ka so ni, yaya Faruk nasan har yanzu kana so na, b’acin rai ne yasa ka ke k’ok’arin danne so na a ranka" na fad’a.


Wani irin kallo ya watsa min kana ya ce "Fatima wannan iya tunanin ki kenan, tabbas na so ki a baya, son da ban tab’a tuanin zan ma wata y’a mace a rayuwa ta ba, na shiga wani hali duk a dalilin son ki amma tun lokacin da kika nun aba ni kike so ba na sa ma kaina hak’uri da ke, na fad’a miki wannan maganar san da na je Wagini kika fad’a min kina da wanda kike so, tun a lokacin na fara rok’on Allah akan ya zab’a min abin da yafi zama min alkhairi, cikin yardar Allah sai gashi komai ya zo min cikin sauki ya ba ni ikon hak’ura da ke ya kuma musanya min ke da Nana, ba abin da zan yi sai dai in gode ma Allah da ya bani Khadijah a matsayin matata saboda halayen ta nagari sannan a yanzu ba wanda na ke so sama da Khadijah, to ki sani har yanzu ban canza magana ta ba na cewa na hak’ura da ke, kema kan ki kina yaudarar kan ki ne da kike cewa kina so na, kin fad’i haka ne saboda yanzu kin rasa mijin ki kuma masoyin ki".


Hawaye ne masu zafi suka fara zubo min a idanu na saboda tausayin kaina.


Ban tab’a tunanin yaya Faruk zai k’i amincewa da ni ba saboda son da yake min sai ga shi lokaci d’aya ya nuna min cewa yanzu ba ni ba ce a zuciyar shi.


Har zuciya ta nake son yaya Faruk a cikin raina.


Sai dai abin takaici shi ne har yanzu ina jin son Dr a cikin zuciya ta ga kuma son yaya Faruk da ya shiga zuciya ta a lokaci d’aya.


A raina a yanzu na fi son yaya Faruk ya aure ni ya zama shi ne abokin rayuwa ta saboda halayen shi.


Cikin dauriya nace "Yaya Faruk zan iya auran ka ko da a yanzu ba bu so na a ranka, sannan ko da a ce Dr zai dawo kai zan zab’a saboda a yanzu zuciya ta tafi karkata zuwa gare ka".


"Fatima ina son maganar nan ta tsaya a iya nan tsakani na da ke sannan ina so wannan maganar ta zama ita ce karo na k’arshe da za ki k’ara fad’a min magana makanmaciyar irin wannan maganar domin in dai wannan ita ce alfarmar da kike nema a guri na ba za ki tab’a samun ta ba, ina fatan kin fahimta" cewar yaya Faruk.


D’aga mishi kaina nayi sakamakon yanda na ji kuka yana son zuwa min.


Tun da yaya Faruk na ji ya fad’i cewa ya hak’ura da ni na ji jiki na yayi sanyi.


Nasan yaya Faruk bay a magana biyu, he is a man of one word, maganar da ya fad’a min cewa ya hak’ura da ni nasan har zuciyar shi yake fad’a min maganar.


Lokacin da ya fad’a min cewa ya hak’ura da ni a Wagini ban wani damu ba saboda a lokacin ina cikin mayen son Dr.


Sai a yanzu da ya maimaita min cewa ya hak’ura da


Hawaye ne kawai yake zubo min a idanu na.


Yaya Faruk bai k’ara ce min komai ba ya shiga motar shi ya ja ya tafi ya bar ni a gurin.


Jiki a sanyaye na bar gurin na koma d’aki na.


Kuka na fara yi na rashin amsa tayi na da yaya Faruk yayi.


Ban tab’a tunanin yaya Faruk zai yi watsi da maganar da na zo mishi ba duba da so na da yayi a baya, sai gashi ya ban mamaki gurin bijire ma buk’atata.


"Me yasa yaya Faruk ba zai manta abin da na mishi a baya ba ya amince da tayin soyayyar da na mishi?".


"Why yaya Faruk" na fad’a a fili.


Hawaye ne kawai yake zubo min na rashin madafa dan nasan na rasa yaya Faruk sai dai in wani ikon Allah ne zai sa ya dawo daga baya ya amince min.


Na d’au tsawon lokaci ina zaune a d’aki ba tare da na samar wa kaina mafita ba.


Babbar matsala ta shine yanda a yanzu ba wanda zan iya tunkara da maganar nan dan ban san yanda kowa zai d’auki magana ta ba.


Nasan kowa da yanda zai fassara magana ta da canza min ma’anar magana ta, in akwai wanda ya kamata in fad’a wa maganar nan bai wuce Anisa da yaya Khalil ba ko Anty Jiddah amma nasan ba zan iya ba saboda ni kaina nasan da kunya in iya tunkarar su da cewa ina son yaya Faruk.


Ba lallai ba ne su yarda da maganar da na fad’a musu, saboda haka dole ne in bar maganar nan cikin zuciya ta tare da addu’ar Allah ya kawo min mafita a ciki.


Da wannan tuanin na samu k’arfin gwiwa a cikin zuciya ta.



A can b’angaren Dr kuwa tunanin da yasa ma kanshi kullum gaba yake yi.


Yanzu ba abin da yafi damun shi da ya wuce ya zo guri na ya bani hak’uri akan abin da ya min sannan in amince mishi a karo na biyu.


Tunanin yansa zai tunkare ni yake yi saboda yasan ba lallai in saurare shi ba duba da laifukan da ya min ga kuma matsalar Meema.


Ga wani irin so na da yake k’aruwa a cikin zuciyar shi wanda ko a da bai jin makamancin yanda yake ji a yanzu.
Wannan tunanin su suka hana Dr sukuni.


Shi kan shi Dr yasan yawan tunanin da yake yi zai iya janyo mishi matsaloli dama wanda a yanzu in ya ma kanshi gwajin BP yana hawa, yasan kuma duk tuananin da yake yawan yi ne ya haifar mishi da haka.


Yau Dr ne ya tashi bay a jin dad’in jikin shi, hakan yasa ko shirin zuwa aiki bai yi ba.


Ya jima a kwance ba tare da Meema ta shigo d’akin ba kasancewar in ba tayi niyya ba a side d’in ta take kwana.


Wayar shi da ke kusa dashi ya samu yayi dialling d’in numbar Meema.


Sai da tayi ringing biyu tana katse wa kusan sau uku sannan ta d’auka.
Sanar da ita yayi yana neman ta a side d’in shi.


Meema sai da ta gama jan ajin ta sannan ta nufi side d’in Dr d’in.


Samun shi tayi a kwance yana lullub’e da bargo.


Da sauri ta k’arasa kusa dashi ta yaye bargon da ya lullub’a da shi.


Wuyan shi ta tab’a taji zafi alamar zazzab’i ya kama shi.


Cikin marairaicewa ta ce "Yaya Sadik me ya same ka na ji jikin ka da zafi, ko ba ka da lafiya ne?".


Murmushi yayi kana ya d’aga mata kai alamar eh.


"Ina ne yake maka ciwo" Meema ta tambaye shi.


K’irji na ke min ciwo da kuma zazzab’i da ciwon kai’ Dr ya fad’a.


Hannun shi ta rik’e kana ta ce "Sannu yaya Sadik, Allah ya baka lafiya, ko za mu je asibitin ku ne".


Girgiza mata kai yayi kana ya ce "Kar ki damu Meema, akwai magunguna a guri na, ki je ki had’o min tea sannan sai in sha maganin".


Mik’ewa tayi ta je ta had’o mishi tea ta kawo mi shi.


A baki ta dinga ba shi har ya sha rabin kofi.


Sai da ta ga yasha magani sannan ta fita daga d’akin.


Tun da Meema ta fita daga d’akin ba ta sake koma wa ba sai can da rana, ko tunanin kawo mi shi abinci ba tayi ba.


Da daddare ma sai da ya rok’eta ta dafa mi shi indomie sannan ta kawo mishi.


Ko da ta kawo mishi indomie d’in ba ta dad’e ba kasancewar kiran da k’awar ta tayi yasa ta fita daga d’akin.


San da ta gama wayar ba ta koma ba tayi kwanciyar ta.


Washe gari jikin Dr ya sake rikicewa dan har ciwon yafi na jiya.


Numfashin shi da k’yar yake fita saboda condition d’in da ya shiga.


Yau ko tunanin kiran Meema bai yi ba saboda ba ya jin zai iya d’aga hannun shi ya d’auki wayar ya kira ta, gashi ko Momin shi bai ce Meema ta fad’a ma wa ba yasan da tazo.


K’irjin shi ne yaji yana mishi wani irin ciwo da bai san yanda zai fassalta yanda yake ji ba.


Meema kuwa sai ta gama abin da take yi ta feso wanka tayi shiga na wasu k’ananan kaya ta fesa turare kana ta wuce kitchen ta had’o mishi tea ta wuce side d’in shi.


In ban da k’amshi ba abin da Meema ke yi.


Tana shiga d’akin ta ga halin da Dr yake ciki.


Sakin cup d’in tayi ganin yanda numfashin Dr yake wahalar fita.


Rik’o shi tayi ta fashe da kuka tana girgiza shi.


Dr yana jin kukan Meema amma ba zai iya magana ba saboda matsanancin halin da yake ciki.


Meema cikin kuka kuwa cewa ta ke yi "Dr me ya same ka, ina sha jikin ka yayi sauk’i ashe jikin yayi worst, shi yasa jiya na ce mu tafi asibiti but you refuse, yanzu ji condition d’in da kake ciki".


Da sauri ta fita daga d’akin tayi wa Mai gadi su magana ya taimaka mata suka sa Dr a cikin mota.


Asibitin Kangiwa Hospital in da Dr yake aiki Meema ta kai shi.


Suna zuwa aka k’arb’e shi aka kai shi special room dan ba shi kulawa ta musamman kasancewar Dr babban likita ne a asibitin ana ji dashi.


Meema ta kira gidan su Dr ta fad’a musu halin da Dr yake ciki kana ta kira gidan su ta fad’a musu.


San da Momi suka zo da su Dadi dasu Hanan kuka suka sa ganin halin da Dr yake ciki.


Dadi ne yayi k’arfin halin kwantar musu da hankali.


Ita kanta Meema jikin Mominta ta fad’a tana kuka ganin halin da Dr yake ciki.


Lallashin ta Dadin ta da Momin ta suka dinga yi akan ta kwantar da hankalin ta Dr zai samu lafiya.


Sai da aka kwashe awa d’aya akan Dr kafin aka samu nu numfashin shi ya daidaita.



Ba a bari an shiga gurin shi ba sai da aka yi kusan awa biyu saboda ana so Dr ya huta.


Abokin aikin shi kuma abokin shi Dr Kamal shi ya nemi ganin Dad office d’in shi.


Jin haka yasa Momi ta tashi ta bi shi dan tasan duk wani bayani da Dr zai yi ba zai wuce akan ciwon da ke damun Dr ba.


Bayan sun je office d’in Dr Kamal ne ya sake gaishe su.


Dadi ne ya ce "Wai Me yake damun Sadik d’in ne".


Dr Jamal ne yace "Gaskiya Dadi Dr Sadik yana cikin wani hali, a binciken da muka yi akan Dr mun gane damuwa ce tayi wa Sadik yawa wanda hakan yasa ya kamu da hawan jini, nasan kuma shi kan shi Dr yasan haka kasancewar shi Likita amma bai yi k’ok’arin kiyayewa ba, sannan a binciken da muka yi mun gano cewa Sadik yana fama da Ulcer wanda ta fara mishi cronic, yawan tunanin da yake yi da kuma ulcer da yake tare da ita ya kamu da ciwon zuciya saboda ita kan ta ulcer tana iya janyo heart deasease bare kuma ga tunanin da yake yi yayi worst".


A tare Momi da Dadi suka ce "Ciwon zuciya!".


Dr Kamal ya ce "Ku kwantar da hankalin ku, mun yi nasarar shawo matsalar kasancewar ba sosai ciwon ya tab’a zuciyar shi ba, za mu d’aura shi akan magani sannan in dai ya daina tunanin da yake yi komai zai dawo normal, sai dai yana da kyau ku mishi magana akan ya rage tunanin da yake yi da kuma k’ok’arin cin abinci a lokacin da ya dace".


Momi kuwa kuka ta fara yi tana cewa "Wani irin tunani Sadik yake yi da har ya kamu da ciwon da yake neman barazana da rayuwar shi, yanzu ban da wannan ita ma Meema sai da ta ba da na ta gudunmawar wajen d’aura mishi wata lalurar na kamuwa da ulcer dan nasan rashin shin abincin da ba yayi ne ya sa ya kamu da wannan ulcer".


Dr Kamal ne ya ce "Momi zai iya yiwu bai cin abinci yanda ya kamata ne ko kuma bai cin abincin akan lokaci, ita ulcer da kike gani mutum na iya samun ta ba sai lallai ba ya cin abinci ba, wata cuta ce mai zaman kanta da a yanzu d’aid’aikun mutane ne ba su da ita".


Momi cikin kuka ta ce "Ni nasan Dr abinci bai dame shi ba amma matsalar yanzu ta b’angaren Meema ce, kuma wlh wannan karan ba zan laminta ba dan ba zan bari in rasa d’ana ba".


Dadi ne cikin lallashi ya ce "Take it easy Hajiya, insha Allah Sadik zai samu lafiya, nasan za su bashi kulawarda ta dace, in ma ya samu sauk’i zan mishi visa yaje India ya k’ara ganin likita ta b’angaren cardiologist tun da su na da k’wararru ta wannan b’angaren".


Haka dai suka ci gaba da tattaunawa da Dr Kamal kafin su mishi sallama su baro d’akin.


Momi kuwa ita kad’ai tasan halin da take ciki na tashin hankali game da ciwon Dr sannan a gefe guda ga haushin Meema da take ji, tasan duk abin da ya samu Dr har da na ta contribution din saboda lack of caring d’inta akan Dr d’in.


Wannan karan ta ci alwashi akan cewa ba za ta juri ganin halin da Dr yake ciki ba, dole ne ta d’auki mataki akan Meema d’in.


San da suka koma d’akin Dr ya farka daga baccin da yake yi.


Meema ce kusa dashi ta manne a jikin shi kamar za ta shige jikin shi.


Hanan da Farida suna gefen shi.


Momi ce da Dadi suka k’arasa kusa dashi suna mishi sannu.


Ido kawai yake bin su ba tare da yayi magana ba.


Har yanzu pulse d’in shi da sauri-sauri yake tafiya bai dawo normal ba.


Dr ya sake shigowa ya duba shi kana ya bashi magunguna.


Bai wani jima ba da shan maganin bacci ya sake d’aukan shi.

Ranar dai haka Dr ya kasance cikin wannan halin.


Meema tun bayan sallar la’asar ta musu sallama ta tafi gida.


Sai bayan sallar magrib ta sake zuwa kasancewar ita tayi driving da kan ta.


Ba ta wani jima a asibitin ba ta musu sallama ta tafi.


Dadi ne yaso kwana dashi amma Dr Kamal ya ce ya bar shi shi zai kwana dashi.


Haka su Dadi suka yi ma Dr sallama suka tafi tare da godiya a bisa jajircewar shi da yayi akan Dr.


Washe gari ma haka mutane suka dinga zuwa duba Dr da abokanan Dadi da k’awayen Momi.


Likitocin asibitin ma haka suka dinga shigowa suna gaishe shi.


Sai da Dr yayi kwana uku a asibitin sannan aka sallame shi saboda matsawar da yayi akan a sallame shi.


An bashi hutu a asibiti kasancewar har yanzu jikin na shi bai dawo normal ba.


Yau kusan kwana biyu da dawowar Dr daga asibiti.


Dr ne zaune a falon shi yana kallon news yayin da Meema ke chatting a wayar ta.


Momi ce tayi sallama ta shigo cikin falon.
Meema ce ta amsa mata kana ta ci gaba da danna wayar ta.


Kusa da Dr Momi ta je ta zaune.


Meema tun da ta gaishe da Momi ta tashi ta d’akko mata drinks ta ajiye ta nemi guri ta zauna ta ci gaba da pressing d’in wayar ta, a lokaci d’aya ta manna ear piece a kunnenta tana sauraren music.


Dr ne ya gaishe da Momi kana ya jingina jikin shi a kafad’ar Momi.


Cikin kulawa Momi ta kalle shi ta ce "Ya jikin na ka Sadik?".


"Jiki alhamdullahi, na ji sauk’i Momi" Dr ya amsa mata.


Murmushi tayi kana ta ce "Allah ya k’ara sauk’i, Dad d’in ka ya ce in gaishe ka da daddare zai zo ya duba ka, su Hanan ma suna gaishe ka, sun ce suna nan zuwa".


Murmushi yayi ya ce "Ina amsawa Momi".


Momi ce ta maida kallon ta ga Meema wacce hankalin ta yake kan waya da sauraren wak’ar da ke tashi ta cikin earpiece d’in ta.


Mamakin Meema ne ya cika Momi yanda ta nuna ko in kula da ita.


Momi ce ta kira sunan Meema amma ba ta ji ba saboda earpiece d’in da tasa ta toshe kunnan ta dashi wanda sautin wak’a ne kawai yake fitowa daga ciki.


Sai da Momi tayi mata kira biyu amma still Meema ba taji kiran ba.
Ran Dr ne ya b’aci dan haka cikin tsawa ya kira sunan ta.


Da sauri ta maida hankalin ta gare shi saboda tsawar har cikin kunnen ta taji tare da cire earpiece d’in da ke kunnen ta.


Cikin b’acin rai Dr ya ce "Meema ba ki ji Momi na mi ki magana ba ne".


Cikin marairaicewa da shagwab’a ta ce "Ayya sorry Momi ban ji ba ne, kin san na sa earpiece a kunne na".


Murmushin takaici Momi tayi a ranta tana k’ara mamakin halin Meema.


Sai a yanzu ta k’ara tabbatar da dalilin da yasa Dr yake kushe halin Meeman da guje ma auren ta.


Nisawa Momi tayi kana ta ce "Meema magana na ke so mu yi da ke".


"To Momi ina jin ki" Meema ta fad’a.


Momi ce ta ci gaba da cewa "Nasan kin san halin da Sadik ya shiga na rashin lafiyar da yake fama dashi, Dr Kamal ya mana bayanin cewa hypertension yake damun shi wanda har yaso ya tab’a heart d’in shi sannan bayan nan kuma Dr ya tabbatar mana da cewa yana da ulcer cronic, kin ga kenan lack of caring d’in ki har dashi ya asassa ciwon dake damun Sadik, Meema nasan irin zaman da kuke yi da Dr amma ba na so in sa baki na saboda ba na so in shiga harkar ma’aurata, abin da yasa kika ga na miki magana a yanzu saboda condition d’in da Sadik yake ciki yana buk’atar special caring da kwantar mishi da hankali in ba haka ba ciwon na shi zai iya yin worst fiye da haka, Meema nasan ulcer da ta sami Sadik rashin cin abinci ita ta janyo mishi wannan ciwon dan nasan ba ya samu ya ci abinci yanda ya kamata, kin ga situation d’in da yake ciki a yanzu bay a buk’atar tashin hankali da hayaniya, pls Meema ya kamata ki k’ara effort d’in ki wajen kula da hakk’in da ke kan ki, ni kaina ba na son in ga kuna samun misunderstanding a tsakanin ku, you Know Meema I take you as Hanan ba wai suruka ta ba, shi yasa kika har na zaunar dake na miki magana because I want you to change your behaviors".


Meema tun da ta ji Momi ta fara wannan bayanin ta d’aure fuska.


Sai da ta ba ri Momi ta gama maganar da take yi kana ta tab’e baki ta ce "For God sake Momi, ni miye laifi na akan ciwon yaya Sadik, shi ciwo yana iya samun mutum at any time sannan Momi ni ina ganin har da laifin yaya Sadik gurin samun wannan ciwon dan nasan duk tunanin da yake yi bai wuce akan ex-wife d’in shi ba sannan ni Momi I know I am trying my best wajen kula da yaya Sadik, shine dai ba ya ganin k’ok’ari na sannan wani lokacin in na mishi girki zai nuna min ba shi yake so ya ci ba, kin ga kenan Momi no need in dinga wahalar da kaina wajen yin girkin tun da ni dai wanda na iya shi zan mi shi, ke kan ki Momi kin san ko a gidan mu ba na shiga kitchen in yi girki sai dai in sa house maid ta min but tun da aka yi auren mu da Yaya Sadik nake k'ok'arin shiga kitchen because of his happiness amma Dr bai ganin haka, to kin ga Momi ba ni da laifi in any part".


Momi kuwa bin Meema take yi da kallo da mamakin yanda ta zauna tana jero mata maganganu san ranta ba tare da ta ji kunyar ta ba.


Mik'ewa Meema tayi kana ta kalli ta ce "Momi shi kenan ko zan iya tafiya, bacci nake ji zan je in kwanta"


Murmushin takaici Momi tayi kana ta ce "Shi kenan Meema za ki iya tafiya".


" OK Momi, ki gaida gida" tana gama fad'ar haka ta bar side d'in.


Momi bin ta tayi da kallo har ta bar falon.


Jiki a sanyaye Momi ta juyo da kallon ta ga Dr ta ce "Sadik ka ci gaba da hak'uri da Meema, ka daina tunanin Meema a ranka ko wani tunani na daban a ranka, ka ga dai yanzu ciwon da yake tare da kai ba ya son tunani, kai Likita ne kasan hakan, ka dinga k'ok'ari kana cin abinci yanda ya kamata, in Meeman ba tayi girki ba ka zo gida ka dinga ci ko kira su Hanan su kawo maka, pls Sadik ka dinga kiyayewa ba na son na rasa ka, na fi so in riga ka mutuwa".


Hannun Momi ya rik'e yana murmushi ya ce " Kar ki damu Momi, zan dinga kiyayewa, kin san ita cuta Allah ne ya ke jarrabar bawa da ita a lokacin da ya so, ku ci gaba da taya in addu'a Momi ke da Dadi".


"Za mu taya ka da addu'a Sadik, Allah ya baka lafiya" cewar Momi.


"Amin Mom" Sadik ya fad'a.


Momi ce ta canza maganar da cewa "Sadik ka fad'a min me yake damun ka, tunanin me ka sa a ranka da har ka ke da Bp sannan ga shi ciwon zuciya yana so ya kama ka".


Ji yake yi kamar ya fad'a ma Momin shi tunani na da so na da a kullum yake addabar shi cikin zuciyarshi shi yake damun shi amma a yanzu yana ganin fad'ar mata hakan bai da fa'ida tun da bai riga ya tunkare ni da maganar ba.


Dr ne ya ce "Momi kin San d'an Adam ba a raba shi da tunani sannan ga stress d'in aiki, kawai dai jarrabawa ce".


"Allah ya kawo mafita ya yaye maka wannan ciwon" cewar Momi.


"Amin Momi" Dr ya amsa.


Sun jima da Momi tana ci gaba da kwantar mishi da hankali kana ta ce ya kira mata Meema suyi sallama.


Ko da yaje side d'in Meema samun ta yayi tana bacci.


Duk tashin ta da yayi bai sa ta tashi ba, da han haka ya koma ya sanar da Momi tana bacci.


Raka Momi yayi wajen Motarta ta ja ta kana ya dawo side d'in shi.


Dr sai da ya kwashe kusan two week a gida kafin ya koma aiki.


Kullum burin shi bai wuce yanda zai tunkare ni ba saboda yasan wannan ita ce mafita a gurin shi na samun sauk'in halin da yake ciki.


Sannan yana kasancewa cikin nadamar abin da ya min Wanda a ko yaushe yake ganin rashin kyautatawar shi gare ni.


Matsalar shi a yanzu shine yanda in ya kira numba na ba ya zuwa, tunanin shi ko na daina amfani da numbar ne ko kuma layin ya sami matsala.


Yana ganin in ya same ni a waya komai zai zo mishi da sauk'i wajen fuskanta ta.




Yau ranar ta kasance ranar Juma'a.


Dr ne zaune a bedroom d'in shi yana danna laptop d'in shi.


Wani tunani ne yazo mi shi na cewa yau ya kamata ya tunkare ni mu fahimci juna ni dashi.


Yasan yanda ya b'ata min rai abu ne mai wahala in tsaya in saurare shi a lokaci d'aya.


Shi kan shi yasan ya min butulcin so Wanda a yanzu yake nadama a bisa abubuwan da suka faru a baya.


Zuciyar shi ba abin da take sak'a mai da ya wuce bashi k'arfin gwiwa akan haka.


Kashe laptop d'in yayi kana ya shiga band'aki ya watsa ruwa ya fito.


K'ananun kaya ya sa kana ya feshe jikin shi da turare.


A falon shi ya sami Meema kwance akan 3-sitter tana kallon Action film.


K'amshin turaren Dr da taji ne yasa ta d'ago ta kalle shi.


Kusa da ita yazo ya zauna yana sakar mata murmushi.


Ita ma murmushin ne ya yalwatu a fuskar ta.


Tashi tayi daga kwancen da take tayi matashi da cinyar shi.


"Ki ce kina falo kina kallo kin barni ni kad'ai a bedroom" cewar Dr.


Meema ce ta ce "Jiki na ne na ji shi so weak, na ga kuma aiki ka ke yi shi yasa ba na son takura maka".


" Kin cika son jiki Meema, wani aiki kika yi da za ki ce kin gaji, bayan ga house maid nan na sa an kawo mini" Dr ya fad'a yana shafa fuskan ta.


"Kai yaya Sadik nasan yanzu za ka fara k'orafi daga cewa

Please Login or Register in order to submit comment