Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*TA’AZIYYA*

_Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga family d’in Murjanatu Alhassan wacce Allah ya ma rasuwa a ‘Yar aduwa University a sanadiyar rashin lafiyan da tayi_.

_Allah nake rok’o ya jik’an ki ya gafarta miki, Allah yasa aljanna ce makomar ki_.

_San da naji labarin rasuwar ki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, nasan nayi rashi, ke k’awa ce ta gari da bazan mantaD dake ba_
😭😭😭

_Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga Hussaina wacce Allah yayi wa mijin ta rasuwa_.

_Halima Mk ina k’ara mik’a sak’on ta’aziyyata gare ki na rasa mijin ki da kika yi_.

_Allah nake rok’o ya jik’an su baki d’aya ya kyautata makwancin su, ya sa aljanna ce makomar su, Allah mu ma ka kyautata k’arshen mu_

_Ina rok’on duk wanda ya karanta wannan page d’in yasa su a addu’a_





*QUESTION OF THE DAY*

_Wace surah ce take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junansu, dangantaka bayyananna ko’boyayya, Kuma zumuntarsu na gudana gwargwadon dangantakarsu da juna_





67-68

Su Abbu kuwa ba k’aramin fushi suka yi dani ba, yaya Khalil ma ya fisu shiga damuwa saboda yadda muka fi shak’uwa dashi, ba wani mai walwala a cikin su tun san da na bar gidan mu.

Dadin su Faruk ya bada cigiya ta a kafafen yad’a labarai, sannan ya kai report police station amma har yanzu shiru ba wani bayani a kaina.

Tsakanin Dadi da Abbu an rasa mai k’arfin gwiwar da zai iya tunkarar Hajiyan Wagini akan rashin gani na da ba ayi ba, tunanin fad’an da za tayi da halin da za ta shiga yasa suka ‘boye mata, sun barshi akan sai an ganni za a sanar mata da komai, a cikin su ba wanda tunanin shi ya kawo can zan tafi.

Yau kwana biyu kenan da wayar da yaya Faruk suka yi da Dadi sai gashi a Kaduna.

Tun san da Dadi ya kira shi yake tunanin dalilin kiran da Dadi ya mishi, yasan in akan biki ne zai sanar dashi a waya, ba sai yace yazo ba.

Bayan ya huta ne Dadi ya kira shi side d’in shi.

Samun shi yayi da Momi a zaune, alamun dake fuskar su na nuna kowa da abin dake damun shi.

Sallama ya musu ya nemi guri ya zauna.

Dadi ne yayi k’arfin halin amsa masa sallama.

Cikin ladabi yaya Faruk ya ce "Gani Dadi".

Dadi sai da saki ya gauron numfashi saboda tunanin abin da zai fad’a ma yaya Faruk ba mai dad’in ji ba ne kana ya kira sunan sa "Umar!
Cikin sanyi ya amsa "Na’am Dadi".

A ranshi kuwa jinjina abin da Dadi zai fad’a mishi mai matuk’ar mahimmanci ne tun da ya kira ainihin sunan shi.

Dadi ne ya nisa kafin yaci gaba da cewa "Faruk, dalilin da yasa na ce kazo Kaduna shine akan wata k’addara da ta faru bayan tafiyar ka wanda yake da alak’a da kai, ka ga kenan ‘boye maka bai da wani fa’ida".

Tun kan Dadi ya fad’a mishi maganar da yake son fad’a mai, yaji jikinshi yayi sanyi, yanzu jikin shi ya fara bashi ba abu mai dad’i Dadi zai fad’a mai ba.

"Faruk abin da nake son fad’a maka shine yau kwana hud’u kenan ba a ga Fatima ba, ba a kuma san inda ta tafi ba, hakan kuma na da nasaba ne da auren da za a muku da kuma wanda take so shi wannan Dr d’in, ina son ka d’au hakan a matsayin jarabawar ka, shi Ibrahim saboda ranshi a ‘bace yake ya ce ko da ba ta dawo ba zai d’aura mata aure dakai, kuma ni na fahimci dan ya faranta maka zai yi, ni kaina nasan Ibrahim da Aisha suna nuna maka so kamar d’an da suka haifa,sun kansu yanzu suna cikin damuwa da abin da Fatima ta aikata, maganar a d’aura aure ba a ga Fatima bai taso ba, za a k’ara ‘bata Al’amarin ne, gwara in ta dawo a san yadda za ayi, ba na so ka sa wannan matsalar a ranka dan guje ma kamuwa da wata cutar, kayi hak’uri Faruk, nasan Fatima ba ta kyauta maka ba" ya k’arasa maganar cikin lallashi.

Tun san da lokacin da Dadi ya fara labarta mishi wannan mummunan labarin kan shi yake a sunkuye ba tare da ya d’ago kai ba.

Duk wannan maganganun da Dadi yake ma yaya Faruk ji yake kamar ana watsa mishi tafasasshen ruwan zafi ne a zuciyar shi, ran shi ba k’aramin ‘baci yayi da jin wannan labarin ba, jijiyoyin kanshi duk sun tashi, idanun shi duk sun canza launi zuwa ‘bacin rai, bai ta’ba kawo wa a ranshi wannan mummunan labarin Dadi zai sanar dashi, ji yake ina ma mafarki yake yi ya samu ya farkar daga wannan mummunan mafarkin wanda bai fatan ya k’ara yin irin shi, sai dai kash! Wannan mummunan labarin a zahiri Dadi yake sanar dashi, yau ya k’ara tabbatar da maganar da Hausawa ke cewa idan wani yak’i ka wani sai yaso ka, shi da ‘yan mata ke son shi yana ja musu aji, nan ya tuno da Binafa yadda take mishi magiya akan ya so ta saboda yadda ta kamu da son shi, ya samu ya ba ta hak’uri ta hak’ura da sauran ‘yan matan da suka fad’a mishi suna son shi bai kula su, sai gashi an samu a kanshi na gudu saboda kar na aure shi duk kuwa da irin son da ya nuna min amma ni ban ga hakan ba, na za’bi bare a kanshi, ba abin da yafi tsaya mishi a ranshi shine yadda na dinga mishi yawo da hankalin shi na k’in fitowa a fili na fad’a mishi ba na son shi da wuri, sai daga baya da ya sakankance da cewa ina son shi sannan na nuna mishi da ban yi na’am dashi ba, yanzu ba abin da yake mishi yawo a k’wak’walwar shi shine guduwar da nayi wanda ba a san inda na tafi ba, a yanzu yana ganin ba abin da zai fi mai sauk’i illah ya samar wa kanshi mafita kafin dawowa ta, shi kad’ai yasan matakin da zuciyar shi ke fad’a mishi ya d’auka akan wannan curkud’ad’d’en al’amarin, yana ganin ba wanda yafi cancanta da ya nemo ni dan zartar min da hukuncin da ranshi ke ayyana mishi da ya yanke wanda yake ganin shi kad’ai ne zai kawo k’arshen wannan abun da yake faruwa tsakani na dashi.

Momi da Dadi jikin su ne ya k’ara yin sanyi ganin halin da yaya Faruk ya shiga tun a yanzu wanda ke nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki da kuma ‘bacin rai da ya mishi dabaibayi a lokaci guda.

Falon ne ya d’auki shiru ba tare da kowa ya sake magana ba, kowa da irin tunanin da yake ayyanawa a ransa.

Jin shirun da yayi yawa ne yasa Dadi ya kira sunan yaya Faruk cikin tattausan harshe.

Yaya Faruk ne ya d’ago kan shi wanda yake mishi wani matsanancin ciwo, wani irin nauyi kan yake mishi saboda tsabar ciwon da yake yi mishi.

"Come close to me my son" Dadi ya fad’a cikin lallashi.

Ba abin da yaya Faruk yafi buk’ata a yanzu da ya wuce yaji shi a kwance ko ya samu sauk’in rad’ad’in da yake ji a zuciyar shi da kuma kan shi da yake mishi matsanancin ciwo.

Ba tare da musu ba ya matso ya kwanta a jikin Dadi, a lokacin ne yaji wani irin zazzafan hawaye na fita daga idanun shi, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi kamar wanda yaci kuka ya k’oshi, k’arshe ma runtse idon shi yayi ko ya samu sauk’in halin da yake ciki, sai faman karanta *Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un* da *Allahumma ajirni fih musibatih, wa aklifni khairan minha* wannan addu’o’in su yake ta faman maimaitawa a cikin ranshi, a hankali yaji natsuwa ta fara shigar shi, ‘bacin ran da yake tare dashi ya fara raguwa.

Momi na ganin halin da yaya Faruk ke ciki ita ma ta fara zubar da hawayen tausayin shi, tasan daman hakan za ta faru, yaushe rabon da ta ga hawayen yaya Faruk, amma yau a dalili na yaya Faruk na zubar da hawaye.

Dadi na lura da hawayen da Momi ke yi, yasan dole ta shiga wannan halin in dai ta ga yaya Faruk a cikin wannan halin, shi kanshi kawai dauriya yake yi ba wai dana bun bai dame shi ba, a yanzu ba wanda yafi buk’atar lallashi sama da yaya Faruk.

Dadi ba abin da yake faman yi sai shafa kan yaya Faruk yake yi kamar yadda ake lallashin k’ananun yara, a lokaci d’aya yana fad’a mishi sweet words masu kwantar da hankali.
Jikin shi da yaji ya d’au zafi wanda hakan ke nuna zazza’bi ne ya kama shi mai zafi.

Janyen jikin shi yayi daga jikin Dadi, hannun shi yasa ya rik’e kan shi wanda yake ji kamar zai tsage saboda ciwon da yake mai.

Tashi yayi da niyar tafiya, ya fara tafiya kenan, hannun shi na dafe da kanshi, jirin da yaji yana d’ibar shi, nan ya fara tangad’i zai fad’i, da sauri Dadi ya taso dan ya rik’e shi kafin ya fad’i, ko kan Dadi ya k’arasa yaya Faruk ya fad’i a k’asa.

Momi ce ta taso da gudu tana kuka tazo tana jijjiga yaya Faruk.

Anisa ma wanda shigowar ta yayi daidai da fad’uwar yaya Farud da gudu ita ma ta k’araso gurin yaya Faruk wanda yake kwance a k’asa.

Momi kuwa cikin kuka cewa take yi "Faruk ka tashi, ku kad’ai gare ni, daga kai sai Anisa, ku kad’ai Allah ya ba ni, kar ka mutu saboda ‘ya mace, idan ka mutu ban san halin da zan shi ga ba".

Anisa ma cikin kuka ta kwanta a jikin yaya Faruk tana cewa "yaya Faruk dan girman Allah ka tashi, kai kad’ai ne d’an uwana da nake kalla na ji sanyi a raina, kar ka tafi ka barni da maraicin ka, rashin ka zai sa in shiga cikin wani mawuyacin hali, yaya Faruk kaji tausayin mu ka tashi dan Allah…" nan ta k’ara fashe wa da wani irin kuka.

Cikin Momi da Dadi an rasa mai lallashin wani a cikin su.

Dadi ne ya ta’ba yaya Faruk yaji yana motsi, hakan yasa ya fahimci suma yayi.

Da sauri ya wuce gurin d’an k’aramin fridge d’in shi ya d’akko faro water mai sanyi yazo ya yayyafa mishi a jikin shi.

Saukar ruwan da yaji a jikin shi yasa ya saki wata ajiyar zuciya.

Dadi ne da Momi suka samu suka kama shi suka kai shi side d’in shi.

Wayar shi Dadi ya d’akko ya kira family Dr d’in su ya fad’a mishi halin da yaya Faruk ke ciki.

Ba a d’au wani tsawon lokaci ba sai ga Dr yazo da kayan aikin shi.

Bayan gwaje-gwajen da Dr ya mai ne ya kalli Dadi ya ce "Alhaji a gwaje-gwajen da nayi na gano Faruk yana yawan tunani duba da yanda BP d’in shi ya hau, yawan tunanin da ya fara yi mishi yawa ne ya jawo mishi ciwon kai mai tsanani wanda hakan yasa temperature d’in jikin shi ya canza, ciwon kai da jirin ne ya hadassa mishi suma, sannan Alhaji pls a kiyaye fad’a mishi abin da zai sa ranshi ya ‘baci don kiyaye lafiyar shi, yanzu zan mishi allurar da zai sakko mai da zazza’bin, zan kuma sa mishi drip da yaji k’arfin jikin shi, sannan zan ba da maganin da za a bashi yasha, in da hali a barshi ya huta don a yanzu bai buk’atar hayaniya".

"Za mu kiyaye insha Allah" Momi ta fad’a.

Bayan ya mishi allura ne yasa mishi drip kana ya musu sallama suka fita da Dadi.

Tun da aka sa ma yaya Faruk drip yake ta faman barci kasancewar har da allurar bacci Dr d’in yasa mai.

Momi ce ta koma side d’inta dan dafa wa yaya Faruk abincin da zai ci in ya tashi.

Anisa kuwa zama tayi a kusa dashi tana kallon yadda yaya Faruk ya koma a lokaci guda.

Ba abin da take furta wa sai "Fatima why, me yasa za ki sa yaya Faruk a wannan halin da yake ciki" a lokaci d’aya hawaye na ci gaba da zubowa a idanun ta.

Yaya Faruk sai da ya kwashe fiye da awa uku yana bacci kafin ya tashi daga baccin.

A hankali ya dinga bud’e idon shi, Anisa ya gani a gefen shi tana rik’e da d’ayan hannun shi wanda ba a sa ma drip ba, yayin da hawaye ke zubowa a idanun ta.

Ganin yaya Faruk ya farka yasa ta saki murmushi ta ce "yaya Faruk ka tashi, sannu ya jikin, yanzu ina yake maka ciwo, akwai abin da ka ke so ne, ko in kira Momi ne?".

Jin wannan jerin tambayoyin da Anisa ke jero mishi yasa ya girgiza mata kai.

K’ara rik’e hannun ta yayi yana kallon ta, idanun ta da ya gani ya canza kala ya tabbatar mishi da tayi kuka, hannun shi yasa yana goge mata hawayen.

Kwanciyar da ya ji ya gaji da ita ne yasa a hankali ya tashi ya zauna.

Da sauri Anisa ta kara mishi pillow a bayan shi ya jingina da gadon.

Drip d’in da taga ya k’are ne yasa ta cire mishi ta koma ta zauna.

"Me yasa ki kuka?" yaya Faruk ya tambaye ta.

Kamar jira take yi ta k’ara sa wani kukan, cikin kukan take cewa ‘yaya Faruk dan Allah ka daina sa tunani ni a ranka, likita yace BP d’in ka ya hau kuma duk a dalilin tunani, plss ka cire tunanin Fatima a ranka".

A hankali ya ce "Kar ki damu Anisa, komai ya kusan zuwa k’arshe insha Allahu, ki daina kuka kin ji my lovely sister".

"Na daina yaya Faruk".

Momi ce ta shigo da foodflask a hannun ta da flask.

Ajiye wa tayi a kan centre table ta nufi yaya Faruk cikin fara’a ta ce "Ka tashi Faruk, sannu ya jikin".

"Da sauk’i Momi".

"To Allah ya k’ara sauk’i".

"Amin Momi".

Niyar mik’ewa yayi da niyar tashi amma har yau jikin shi ba k’arfi.

Momi ce ta ce "Ina zaka kuma".

Cikin muryar marasa lafiya ya ce "Ina so in je in watsa ruwa ne, jiki na ne nake jin shi ba k’arfi, ga shi ina so in yi sallah la’asar da ban yi ba".

Cikin tausayawa Momi ta ce "Ka bari kaci abinci zaka ji dad’in jikin ka, in yaso sai ka watsa ruwan kayi sallah".

"Bari in je in yi brush in dawo".

"Ok" Momi ta amsa mishi.

Tashi yayi a hankali yake takawa, da alama har yanzu bai gama jin k’arfin jikin shi ba.

Band’aki ya shiga ya d’auraye fuskar shi kana yayi brush ya fito.

Dawowa yayi ya jingina da gadon.

Momi ce ta kalli Anisa tace "Je ki kan fridge ki d’akko plate da cup a zuba mishi ya ci".

Anisa ce ta had’a mishi kakkauran Tea wanda yaji madara a ciki, d’ayan plate d’in kuma farfesun kayan cikin ne a ciki.

Momi ce ta amshi tea d’in da plate d’in ta matsa kusa da yaya Faruk d’in.

Tea d’in take bashi a baki wanda yake shan shi kamar mad’aci hakan yake jin shi a bakin shi, kad’an yasha tea d’in y ace ya k’oshi, ajiyewa Momi tayi ta fara bashi farfesun, yana shan farfesun ne ba wai dan yana jin taste d’in shi a bakin shi ba, sai don kar ran Momi ya ‘baci yasa yake sha.

Dadi ne ya shigo d’akin yayi don ganin jikin yaya Faruk.

Samun shi da yayi ya farka har yana d’an cin abinci yasa yaji dad’i a ranshi.

A hankali ya k’araso gurin su yana Murmushi ya kalli yaya Faruk ya ce "Jiki yayi sauk’i kenan Faruk, Allah ya k’ara afuwa da sauk’i".

Amsawa yayi da "Amin".

Bayan ya gama cin abincin ne ya mik’e yaje ya watsa ruwa yayi alwala yazo ya rama sallolin da ake bin shi kana ya koma ya kwanta.

Dadi ne ya kira su Abbu ya sanar dasu rashin lafiyar yaya Faruk.

Da daddare sai gasu Abbu, Ummu da yaya Khalil sun zo duba shi.

Jikin Ummu ne yayi sanyi ganin da Momi take amsa musu maganar su kamar ba ta so, tasan hakan bai rasa nasaba da halin da yaya Faruk yake ciki wanda a dalili na hakan ya faru dashi, ko waye aka yi wa d’anta haka dole ne ranta ba zai mata dad’i ba.

Anisa kuwa tun bayan gaishe dasu da tayi ta tashi ta bar d’akin.

Shi kanshi yaya Faruk bai ji dad’in yadda Momi tayi ma su Ummu, da yadda yaga Anisa na share yaya Khalil, yana ganin wannan abin da ya faru tsakanin shi da ni ne, bai kamata su ‘bullo da wannan matsalar ba duk da yasan dan saboda shi suke yin haka, suna jin haushin abin da na mishi.

Yaya Khalil ne ya tashi ya bi ta d’akin ta amma ta k’i sauraren shi, a iya nazarin da yayi yasan ba abin da ya had’a shi da ita bare yace fushi take yi dashi, duk wasu kalamai na lallashi da ya kamata ya fad’a mata ta saurare shi amma tak’i, sai ma kuka da ta sa mishi.

Jikin shi ne yayi sanyi da kukan da yaga Anisa ta na yi, shi kanshi yanzu dauriya ce yake yi irin ta namiji, gashi kuma Anisa na so ta d’aga mishi hankali da kukan ta.

Cikin kukan take cewa "yaya Khalil ina rok’onka ka k’yale ni, ka barni na ji da halin da nake na halin da d’an uwa na yake ciki a yanzu wanda ‘yar uwarka ce silar shi shiga wannan halin, yaya Khalil tun da Fatima ta nuna ba ta son d’an uwa na to nima ina ganin babu wani fa’ida a ci gaba da soyayyar mu, nima ina kishin d’an uwa na kuma ina son sa, yaya Khalil ka fita na ce" ta k’arasa maganar cikin kuka.

Sai yanzu yasan akan abin da yasa Anisa take k’in kula shi, tana mishi haka ne saboda ta rama abin da Fatima ta yi ma d’an uwan ta, yasan ko mai zai fad’a mata ba za ta saurare shi ba, abin da ya fi shine ya bari ta sakko, hakan zai fi sa su fi fahimtar junan su.

Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai ya fita daga d’akin.

Yana fita ta sake fashewa da wani kukan, wannan lokacin akan abu biyu take kukan, na son yaya Khalil da ke d’awainiya da ita a cikin zuciyar da rashin yi mishi adalci na hukunta shi da laifin da ba nashi da kuma tausayin halin da yaya Faruk yake ciki.

Haka su Ummu suka yi sallama da su Momi kowa da abin da yake damun shi a ranshi.

Ranar haka yaya Faruk ya kwana da tunanin in da na tafi.


Washegari jikin yaya Faruk yayi sauk’i dan ya samu ya fito falo ya zauna, ganin yadda kowa ke nuna mishi kulawa yasa ya saki jikin shi duk kuwa da yadda yake jin zafi a cikin zuciyar shi na abin da na mishi.

Yaya Aminu ma yazo da Anty Jiddah sun zo sun duba shi, yaya Aminu haka ya ci gaba da kwantar mishi da hankali, ya nuna mishi shi kanshi halin da yake ciki na abin da na aikata.

Sun d’an jima a gidan kana suka koma gurin Momi suka mata sallama suka tafi.

Yau kwanan yaya Faruk biyu da zuwan shi Kaduna ya shirya zuwa Wagini gaishe ta, kiran ta da yayi a waya haka ma Dadi ya sanar dashi shima bai samun ta a wayar, hakan yasa ya shirya tafiyar.

Fito wa yayi cikin shigar wani yadi mai laushi kalar ash, in ban da k’amshin turare da yake tashi ba abin da falon yake yi.

Sallama yayi ma su Momi akan ya tafi Waginin, may be zai kwana a can ko ya dawo yau.

Fatan a dawo lafiya suka mishi.


Kasancewar ya sa wa motar speed yasa ya isa Wagini a da wuri.

Hajiya na zaune a tsakar gida tana sauraren radio taji shigowar yaya Faruk.

Sallama yayi yazo ya zauna kusa da ita akan tabarmar da take zaune.

Amsa masa sallamar tayi da fara’a a fuskar ta.

Hajiya ce ta ce "Maraba da mai gidana Soja na kaina, sannu da zuwa".

"Yawwa Hajiya, mun same ku lafiya".

"lafiya lau, ya aiki, ya wajen iyayen naka"

"lafiyar su lau, suna gaishe ki".

"Hajiya lafiya wai ba a samun wayar ki, su Dadi suna kiran ki ba sa samu, nima na kira ba ta shiga sai a ce min a kashe take".

Hajiya dama kamar jira take yi ta fara fad’a "Rashin samu na da ake yi ba zai rasa nasaba da wannan ‘yar buhun ubar ba, ba yadda banyi da ita ta gyara min wayar nan amma yarinyar nan tak’i, idan na ce ta kira min ku a wayar sai ta ce ba ta shiga, haka na gaji na k’yale ta".

Murmushi kawai yayi yace "Wai wace yarinyar ce ki ke magana Hajiya".

"Au kai duk bayanin nan da nake yi ba ka gane wacce nake nufi ba, to amaryar ka nake nufi Fatima…".

Da sauri ya katse da cewa "Wace Fatiman wai Hajiya".

Hajiya ce ta mishi dak’uwa tace "Ungo naka, kaji ni da shak’iyin yaro, yau Fatiman ce ba ka gane ba".

"Hajiya kina nufin Fatiman Abbu, dama tana nan ne".

"Yau kwanan ta kusan shida kenan, na ji kana tambayar dama tana nan ne, kana nufin ba a san tana nan ba ne".

"Tana ina ne Hajiya?".

"Tana can cikin d’aki, hala tana can ta kunna kururuwar shed’an tana saurara, yarinya ba ta da aiki sai kunna wak’ok’in soyayya kamar a kanta aka fara".

Bai tsaya sauraren abin jin bayanin da Hajiyan Wagini ta ke mishi ba ya mik’e ya nufi d’akin.

Duk yadda na ‘bata mishi hakan ba zai hana shi jin dad’in tawowa ta nan Wagini ba, kowa tunanin shi bai kawo nan na tawo ba.

Ni kuwa ina kwance akan gado, earpiece ne a kunne na ina sauraren wak’ar Hussaini Danko, sauraron wak’ar na ke yi sannu a hankali kamar ni na raira ta, mai taken _SOYAYYA TA_

Bin wak’ar na fara yi inda mai amshin take cewa _nima soyayya ta zan furta_
_ba a saka ni rana d’aya in yi gudun ka_, _so d’ammara nayi ko za ya saka min hauka_, _ko mutuwa nai zan so a dalilin son ka , _so ajiya nayi ranar shi tazo zan d’auka_, _idan tafiya nayi an ce da gwani amsar ka_, _nace kai na za’ba_, _har zuci bazan canza ba_, _ba kuma zan k’osa ba…_, _ni kaine burina ba a hana ni zuwa gurin ka_, _so ne jagora na shi ya dasa min k’imarka_, _amsar tambihi na je ka rabe min hujjar ka_, _ya zan yi in k’yale ka in ta zama a cikin cuta_, _so so soyay…_

Sauran baitin ne ya tsaya a iya baki na saboda idanuna da suka sauka akan wanda na gani a bakin k’ofa yana kallo na.

A hankali ya tako ya k’araso inda nake ya tsaya yana ci gaba da kallo na, a yanayin shi bazan iya gane halin da yake ciki ba.

Wata irin kunyar yaya Faruk ne ya kama ni da tsoron shi a lokaci guda, daskarewa nayi a zaune ba tare da na iya motsa ko da d’an yatsa na ba.

Wani irin murmushi ya min wanda na kasa fasalta mai murmushin yake nufi a gurin shi.

"Fatima kenan, ashe nan ki ka tawo a na ta neman ki a gida" ya k’arasa maganar yana min wani irin kallo.

A halin da nake ciki na firgici ba zai bani damar in iya bud’e baki na in amsa wa yaya Faruk tambayar shi ba.

A yadda na lura ma bai da buk’atar amsawa ta a yanzu.

Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kike buk’atar in barki da masoyin ki wanda ku ke son junan ku ina ganin lokacin yayi, na yarda ke jaruma ce a soyayya da zaki iya fad’i tashi a kanta, in da kika ban kunya a soyayyar taki shine tsoron da kika sa a ranki har yakai ki ga barin iyayen ki wanda ki ka sa su a cikin halin damuwa, a matsayi kin a ‘ya mace ina ganin ba mutunci ki ba ne barin gari dan ba kowa yasan nan za ki zo ba, hakan da kika yi zai sa mutuncin ki ya zube a idanun mutane, anyway ba dogon zance zanyi dake ba illa in sanar dake *FATIMA NI UMAR FARUK NA HAK’URA DA AURAN KI, FATIMA NA HAK’URA DA SOYAYYAR KI DUK KUWA DA SON DA NA KE MIKI*.

Sauri nayi na d’ago kaina na kalle shi, banyi zaton jin wannan kalamen daga bakin yaya Faruk ba sanin son da yaya Faruk yake min ban yi zaton zai yi saurin yanke hukunci irin wannan ba na hak’ura dani amma sanin halin

Please Login or Register in order to submit comment