Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata magana akan rashin auran yaya Faruk da ban yi ba, yanzu ma kana gani bikin shi za a yi, ina ganin bai kamata ka kawo wannan tunanin a ranka ba".


"Na fahimci kuskure na Zarah, zan kuma kiyaye kin ji my lovely Zarah, so wipe your tears and smile for me" ya fad’a yana sakar min tsadadden murmushi.


Goge hawaye na nayi.


"So smile for me" ya fad’a yana kallo na.


Murmushi na sakar mai kana na kwanta a jikin shi.


A wannan lokacin muka shirya ni da Dr.


Ranar mun sha soyayya mai tsayawa a zuciya.





A ‘bangaren yaya Faruk kuwa sai dai jiran ranar biki kawai yake yi dan ya gama shirye-shiryen shi.


Nana tun ana saura sati d’aya suka fara gabatar da event d’in su kasancewar ta k’ara wasu event saboda yadda k’awayen ta suka matsa mata akan kamu da walima kad’ai sun yi musu kad’an, hakan yasa ta k’ara da Arabian night da bridal shower, yayin da Hajiyar su za tayi mothers day.


Gyara na musamman aka yi ma Nana, wacce tayi mata gyaran ta k’ware a iya gyaran dan ko da yaya Faruk sai da ya ga ta k’ara mishi kyau, sai dai miskilancin sa bai bar shi ya fad’a mata hakan ba.


Ita ma Anisa ta fara gudanar da event d’in ta.


Duk da ina zuwa School hakan bai hana ni halartar duk event d’in da aka tsara ba, na ji dad’in yadda Dr bai hana ni zuwa event d’in ba dan ita ma Anisa sai da ta kwashe kwana biyar ana event na bikin.


Ran Juma’a aka d’aura auran yaya Faruk da Nana Khadijah, bikin da ya samu halartar manya k’usoshi na Nigeria, dan ko ta wani’bangare abin sai san barka, ta ‘bangaren Yaya Faruk abokan shi sojoji da seniors d’in sa sun sami halartar bikin, Dadin shi kuwa manyan ‘yan kasuwa da ma’aikata sun halarci bikin, idan aka je ‘bangaren Dadin Nana kuwa ‘yan siyasa da wanda suka sauka da wanda suke kan mulki sun halarci bikin.


Gaskiya wannan biki ya bar tarihi, dan shagalin da aka gabatar har kawo ranar bikin abin ba zai lissafu ba saboda yadda bikin ya k’ayatar.


Bayan gama d’aurin aure ne aka zarce da Walima.


Daga nan su Dadi suka dawo Kaduna aka d’aura auran yaya Khalil da Anisa.


Taro dai haka ya ci gaba da gudana cikin jin dad’i da annashuwa, kowa ka gani kasan yana farin ciki da wannan ranar, dan biki ne da aka dad’e ba a yi irin shi a familin mu ba.


San da na ga yaya Khalil ne ina ta tsokanar shi ran da yazo gidan su Anisa, da ya ce in kira ta na ce sai ya biya dan a yau Anisa tayi tsada, dariya ya min ya ce ko nawa ne zai iya biyan dan wannan ranar daban ce a gurin shi, sai da na gama ja mishi rai sannan na kira ta.


Haka muka ta d’aukan hotuna, Hajiyan Wagini ma haka ta shigo hoton ana ta d’auka da ita kasancewar yanzu ta rage min fad’a, dan da tazo bikin tasa an kawo ta gida na.


Haka Hajiyan Wagini ta sa kuka wai yau Allah ya nufe ta da ganin auren yaya Khalil da Anisa, ta gode ma Allah da ya nufa suka yi auran zumunci, ni da na k’i gashi Allah ya kawo wanda za su share mata hawaye, da k’yar aka samu Hajiyan Wagini tayi shiru.


Sai da aka yi crossing of the Sword kana aka kawo Nana gidan ta da yaya Umar ya gina a sabon Kawo a Kaduna.


Ban samu zuwa ba saboda ana shirye-shiryen kai Anisa, ina so akai amarya dani, da daddare sai muje dinner da Dr.


Sai da aka kai Anisa gidan ta a unguwar rimi da Abbu ya gina ma yaya Khalil, ban koma gida ba sai da nayi sallar Magrib a gidan.


Da zan tafi haka na dinga tsokanar Anisa, maimakon ta biye min sai kuka da tasa, tun ina mata dariya har sai da tasa nima na zubar da hawaye.


Haka muka rabu da ita muna kewar junan mu, nasan soyayyar mu da Anisa daga Allah ne, ko mun yi fad’a za mu shirya, a tsakanin mu ba wanda yake iya dogon fushi da d’an uwan shi.


Sai bayan isha’i ne muka shirya ni da Dr muka tafi inda za a gabatar da Dinner d’in.


Ko da muka je an riga an fara event d’in.


Hakan yasa muna shiga muka nemi guri muka zauna.


Ana cikin gabatar da program of event d’in ne, MC ya kira ni a matsayin wacce za ta ba da tarihin amarya.


Tashi nayi na je fara ba da tarihin amarya kana na k’ara da fad’an kyawawwan halayen ta, a k’arshe na k’ara da ba ma yaya Khalil amanar rik’e Anisa da amana, a k’arshe na yi ma wanda suka samu halartar dinner d’in fatan alkhairi, daga nan na ba ma Mc micro phone Na koma na zauna kusa da Dr.


Haka aka ci gaba da gudanar da Dinner d’in.


Ganin dare ya fara yi ne yasa muka tashi muka koma gida.


Washe gari ma na je gidan Anisa, anan nake ji jiya bayan kawo amaryar, Momi ta had’a event WELCOME TO THE FAMILY in aka kawo Nana.


Gaskiya Momi ba k’aramin tana ji ta yi ma bikin ba ganin tun da aka fara gudanar da bikin Momi ke ‘barin kud’i.


Ban samu zuwa gidan Momi ba a ranar, hakan yasa ba mu had’u da Nana ba.


Yaya Faruk kuwa yayi farin ciki da ganin wannan ranar mai tarihi, wacce take zuwa mutum sau d’aya a rana, ga kuma wanda Allah ya nufa da samun wannan damar.


Ba abin da zai yi da ya wuce yayi ma Allah godiya na ganin wannan ranar da yayi.


Da ma can Allah ya rubuta Nana ita za ta zama matar shi, hakan yasa wannan matsalar tazo bai aure ni ba duk kuwa da son da ya min.


A yanzu ya sa ma ranshi zai zauna da Khadija a matsayi matar shi da ba ta kulawar da ta dace a matsayin ta na matar shi dan ita Allah ya nufa a matsayin matar shi.


Kasancewar ba ran d’aurin auren zai je gidan shi ba, dan akwai ‘yan uwan Nanan wanda za su kwana, washe gari za su koma.


Kafin yaya Faruk ya tafi gidan shi sai da yaje side d’in Dadi dan ya musu sallama.


Cikin sa’a kuwa ya samu Momi a falon ita da Dadi.


Sallama ya musu ya shigo kana ya zo kusa da Dadi ya zauna a k’asan carpet.


Su biyun suka amsa mishi sallamar da yayi.


"Barkan ku da hutawa" yaya Faruk ya fad’a.


Dadi in ban da murmushi ba abin da yake yi.


Momi kuwa farin ciki ne ya cika ta a ko ina wanda hakan yasa bakin ta ya kasa rufuwa.


"Barka dai Faruk, har an shirya ne za a tafi gurin amarya, shi kenan yau Faruk zai bar mu" Dadi ya fad’a cikin wasa.


Sunkuyar da kanshi yaya Faruk yayi yana murmushi.


Dadi ne ya ce "Alhamdulillah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da ya nuna min wannan rana da ya bani ikon aurar da kai da k’anwar ka Anisa, ban san yadda zan misalta farin cikin da nake ciki ba sai dai in yi ma Allah godiya, Faruk ina so ka rik’e matar ka da amana da gaskiya, ka da ka zalince ta domin Allah yana kallon ka, ita Allah ya za’bar maka a matsayin matar ka, kayi hak’uri da halayen ta, ka zama mai yi mata uzuri, hankalin maza da na mat aba d’aya ba ne, kaine a saman ta, kar ka dinga yawan mata fad’a, hakan zai sa ta dinga jin tsoron ka, Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba".


Shi da Momi ne suka amsa da "Amin".


Dadi ne ya kalli Momi ya ce "Hajiya ko kina da abin cewa".


Momi ce ta ce "Duk abin da zan ce ka riga ka fad’a Alhaji, sai dai in ce Allah ya had’a kansu ya kuma tabbatar musu da zaman lafiya a rayuwar auren su".


Haka yaya Faruk ya musu sallama ya tafi.


Sai da ya biya gurin masu sai da kaji da drinks ya siya kana ya wuce gidan.


San da yaje gidan shiru kasancewar ‘yan uwan ta sun koma Abuja.


Side d’in ta ya shiga ya tarar ba ta falo, hakan ya tabbatar mishi da tana bedroom d’in ta.


Lokacin da ya shiga d’akin, samun ta yayi a zaune akan bedroom ta sha kwalliyar ta.


Sallamar da yayi ne yasa ta d’ago ta kalle shi.


Had’a idon da suka yi ne yasa ta yi saurin sunkuyar da kanta.


Murmushi yayi ya ce "Khadija kun ya ta kike ji ne".


Ba ta bashi amsa ba illah murmushin da take yi.


"Ina wuni" ta fad’a a hankali.


"lafiya lau Khadija, ya taro".


"Alhamdulillah".


Shiru yayi kana ya ce "Kin ci abinci ne".


"Eh Momi ta aiko da abincin".


"Ok in za ki kwanta ki kashe bulb d’in d’akin ki, ni zan tafi in kwanta, ga nama nan ki ci ko ba yawa, nasan ba wani abincin kirki kika ci ga".


"Na gode" ta bashi amsa a tak’aice.


Fita yayi daga d’akin ya wuce side d’in shi.


Jikin ta ne yayi sanyi jin cewa yaya Faruk ba a nan zai kwana ba, ita tsoro take ji dan side d’in ta shiru, sai dai tasan ba za ta iya ce mishi ya kwana a nan ba, dan ba taso ya d’auki maganar da wata manufa ta fad’a mishi.


Wani tunani ne yazo mata akan cewa har yanzu yaya Faruk bai damu da it aba, saboda ba son ta a ranshi, in har da ya damu da ita ba yanda za ayi ya barta ta kwana ita kad’ai alhalin tana sabuwar amarya.


Haka taci gaba da zancen zucin ta, ba ta san iya tsawon lokacin da ta d’auka tana tunani ba, da haka barci ya d’auke ta.


Da asuba yaya Faruk yazo ya tashe ta tayi sallah kana ya wuce masalllaci.


Da gari ya waye Nana ta tashi ta gyara side d’in ta duk da ba wani datti yayi ba, bayan ta gama ne taje ta yi wanka, tana fitowa ta zauna ta tsantsara kwalliyarta ta burgewa kana ta fito ta tafi kitchen ta d’aura musu breakfast.


Tana cikin kitchen ne taji ana Knocking d’in k’ofar side d’in ta, zuwa tayi ta ga Momi ce ta aiko da Driver d’in su da kayan breakfast.


Amsa tayi ta mishi godiya kana ta ce ya gaishe mata da Momi.


Koma wa tayi ta kammala breakfast d’in da ta d’aura, bayan ta gama ne ta juye a food flask ta ajiye a Dinning table.


Ganin har yanzu yaya Faruk bai fito daga side d’in shi ba ya sa ta fara tunanin ko taje ta sanar dashi ta gama had’a musu breakfast.


Tashi tayi ta nufi side d’in shi, ganin k’ofar falon a bud’e yasa ta shiga da sallamar ta.


Samun shi tayi da jallabiya a zaune yana kallo a Tv, hakan yasa ta kasa k’arasowa cikin falon.
Amsa mata sallamar yayi ya maida kallon shi gare ta.


Ganin yadda ta tsaya ta kasa shigowa ciki yasa ya ce "Khadija ki shigo mana ki ka tsaya a nan".


K’arasowa tayi ta zauna nesa dashi kana ta ce "Ina kwana yaya Faruk".


Da Murmushi a fuskar shi ya ce "Lafiya lau Khadija, kin tashi lafiya".


"Lfy lau" ta amsa mishi a tak’aice.


Shiru ne ya ratsa falon, in ban da sautin magana da ke fito wa a falon ba ka jin k’arar komai.


Ganin shirun yayi yawa ne yasa yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "Ya aka yi ne Khadijah".


"Dama na zo in fad’a maka na had’a mana breakfast, Momi ma ta aiko mana da abinci" ta fad’a cikin sanyin murya.


"Sannu da aiki, ki je ki yi breakfast d’in ki, ni sai anjima zan yi nawa in nayi wanka, ban cika yin breakfast da da wuri ba".


"Toh" ta amsa mishi kana ta mik’e ta bar falon.


Zama ta je tayi a dinning d’in, abincin da Momi ta aiko musu ta bud’e, Fankasau ne da vegetable soups wanda yaji naman kaza da naman sa a ciki, d’ayar food flask d’in farfesun kan sa ne a ciki, d’ayan kuma food flask d’in pepper cikin ne a ciki, duk cikin abin da Momi ta aiko musu sai taji ta fi marmarin fankasau, hakan yasa ta d’ebi kad’an taci kana ta had’a shayi a d’an k’aramin kofi tasha.


Bayan ta gama ne breakfast d’in ne ta d’auki kayan da tayi amfani dasu ta je kitchen ta wanke.


Tana gama wa ta ta dawo falo ta kunn Tv tana kallon tashar Joy Prime.


Ba ta wani jima da zama ba sai ga yaya Faruk ya fito cikin shigar wani gezna shadda kalar light brown.


Dinning ya wuce ya zauna, hakan yasa Nana ta mik’e taje ta yi serving d’in shi.


Yadda take komai cikin natsuwa ne yasa yaji ta k’ara burge shi, komai in za tayi tana yin shi ne a natse.


Bayan ya ta gama serving d’in shi ne ta tambaye shi ko akwai abun da yake buk’ata.


Girgiza mata kai yayi alamar babu.
Har za ta tafi ya kira sunan ta "Khadijah".


Juyowa tayi ta kalle shi, tana jiran jin abin da zai fad’a mata.


"Na gode" ya fad’a a hankali.


Murmushi kawai tayi ta koma falon ta zauna taci gaba da kallo.


Bayan ya gama breakfast d’in ne ya dawo ya zauna a falon yana danna wayar shi.


Tashi tayi ta tafi dinning d’in ta d’auke kayan da ya ‘bata ta wanke kana ta dawo ta zauna.


Hira ya fara jan ta jefi-jefi tana bashi amsa.


Ya d’an jima da zama kana ya mik’e ya je side d’in shi ya fito.


Kallon ta yayi ya ce "Khadija bari in je gidan Momi mu gaisa, in na fita sai ki kulle k’ofar, idan na dawo zan bud’e, akwai extra keys a hannu na".


"Sai ka dawo yaya Faruk, ka gaida Momi da Dadi" Nana ta fad’a.


Murmushi yayi ya ce "Za su ji".


"Kar ki d’aura girki, Momi za ta aiko da abinci" cewar yaya Faruk.


"Toh" Nana ta fad’a.


"Me zan tawo miki dashi in zan dawo" yaya Faruk ya tambaye ta.


"Ba komai" ta bashi amsa.


Har ya fara tafiya ta kira sunan shi "yaya Faruk".


Juyowa yayi ya na jiran jin abin da za ta fad’a mai.


"Dama cewa zanyi ko za ka bud’e min side d’in ka in gyara ma".


Yalwataccen murmushi ya sakar mata kana ya ce "Ki barshi Khadijah, bai yi wani datti ba, na riga na gyara, next time sai ki gyara min".


"Toh" Nana ta fad’a.


Fita yayi daga falon ya shiga motar shi, yana mai yabawa da halayen Khadija.


Tashi tayi ta kulle k’ofar kana ta kashe kayan kallo ta tafi bedroom.


Hajiyan su ta kira suka gaisa kana ta kira Anty Maryam suka sha hira, haka Anty Maryam ta ba ma yaya Mus’ab waya suka gaisa.


Bayan ta gama wayar ne ta kwanta, ba a dad’e ba bacci ya d’auke ta.


Sai can da yamma yaya Faruk ya dawo da kayan ciye-ciye da ya siyo, ya bata nata ya nufi side d’in shi.


Sai da aka kira sallar magrib sannan taji alamar fitowar shi ya tafi masallaci, sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo gidan.


Side d’in ta ya shigo ya ganta a zaune a Dinning tana cin abinci.


Kujerar da ke opposite d’in ta ya zauna.


"Sannu da dawowa yaya Faruk" Nana ta fad’a.


"Yawwa Khadija".


"ya su Momi" Nana ta tambaya.


"Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki" cewar yaya Faruk.


Sanyayyen murmushi tayi kana ta ce "Ina amsawa".


"yaya me zan zuba maka" Nana ta tambaye shi.


Lumshe ido yayi kana ya ce "Ki zuba min duk abin da ranki ya miki".


Bayan tayi serving d’in shi ne ta koma ta zauna.


Jefi-jefi yake kallon ta ganin yadda ta kasa sakin jikin ta taci gaba da cin abincin, sai wasa da cokalin take yi.


"Khadija ki ci abincin kar yayi sanyi" yaya Faruk ya fad’a.


"Na k’oshi ne yaya Faruk" cewar Nana.


Kallon abincin yayi ya ga ko rabi ba taci ba amma ta ce ta k’oshi, yasan zaman shi a gurin ne yasa ta takura.


Bayan ya gama cin abincin ne ya ce "Khadija ki ci abincin, na ga ba wani abincin kirki ki ka ci ba".


Yana gama fad’ar haka ya bar gurin ya koma falo ya zauna.


Kwashe plate d’in tayi da cups ta kai kitchen ta wanke kana ta tafi bedroom d’in ta.


Ya d’an jima a falon yana kallon action film kana ya mik’e ya shiga bedroom d’in Nana ya mata sallama ya tafi side d’in shi.


Haka zaman su yaci gaba da gudana, idan yana gidan ya kan zauna su yi hirar duk da ba ma’abota surutu ba ne, zai tambaye ta ko akwai abin da take buk’ata, sannan in tayi girki zai zauna su ci, da daddare ya je ya mata sallama ya tafi side d’in shi.



A ‘bangaren Nana ta rasa dalilin yaya Faruk na k’in kwana a d’akin ta a mastayin ta na sabuwar amarya, duk da yana k’ok’arin ba ta kulawa amma ba ta ganin hakan ya gamsar da ita, tasan ko wani ango wanda aka kawo mishi sabuwar amarya yana k’ok’arin ya ga ba ma amaryar shi lokacin shi wajen gudanar da tsaftatacciyar soyayya da amaryar shi, amma ita mai yasa yaya Faruk bai ba ta irin wannan soyayyar ba, ko hakan na nufin har yanzu ba ita ba ce za’bin shi da ba zai d’auke ta a matsayin amarya ba.


Satin su uku a Kaduna yaya Faruk ya kai Nana gidan su Abbu da yaya Aminu da yaya Khalil suka gaisa kana ya wuce da ita gidan su Momi.


Momi taji dad’in zuwan su, sai nan-nan take yi da Nana, ita kanta Nana taji dad’in yadda Momi ta nuna kulawar ta gare ta.


Sai da daddare suka baro gidan su Momi suka musu sallama za su koma Abuja saboda hutun School d’in su Nana ya k’are wanda aka basu na k’arshen semester, shi ma yaya Faruk zai koma bakin aikin shi.


Washe gari yaya Faruk ya d’auki Nana suka koma Abuja.



Su Anisa da yaya Khalil sai cin amarcin su suke yi, yaya Khalil yana ba ma Anisa duk kulawar da ta dace.


Ya kai ta gidan su Momi kana ya wuce da ita gidan su Abbu, a nan suka wuni, sai da daddare suka dawo gida.


Yanzu kusan watan yaya Faruk d’aya da aure, har yanzu ba wani abu da ya shiga tsanin su na auratayya.


Yau Nana tun da tashi take jin marar ta na mata ciwo, ta tabbatar da period d’in ta ne zai zo.


Yanda take jin ciwo ba ta jin za ta iya tashi ta had’a musu breakfast.


Hawaye ne kawai yake zuba a idon ta saboda yadda marar ta ke mata ciwo.


Yaya Faruk ne ya shigo side d’in ta.


Zama yayi a falon bai ji motsin ta ba.


Idon shi ne yakai kan dining table ya ga ba komai a kai, hakan ya tabbatar mai da Nana ba ta had’a breakfast ba.


Ya d’an jima a zaune amma har yanzu bai ji motsin ta ba.


Tashi yayi ya nufi bedroom d’in ta.
Ganin ta yayi a kan gado ta rik’e marar ta tana hawaye.


Da sauri ya k’arasa gurin ta ya rik’o hannun ta.


Bin ta yayi da ido yana ganin yadda ta ke rintse ido, da alama akwai abin da yake damun ta.


"Khaldijah lafiya kike kuka" yaya Faruk ya tambaye ta cikin kulawa.


"Mara ta ke min ciwo" cewar Nana.


"Sannu, daman kina yin ciwon marar ne" ya sake jefo mata tambaya.


D’aga mishi kai tayi alamar Eh.


"Ki tashi ki yi wanka, bari in je in saman miki abin da zaki ci kafin mu tafi asibiti".


A hankali ta tashi tana dafe da marar ta.


Tausayin ta ne yaji ya kama shi saboda alamun su nuna marar ta matsa mata.


Sai da yaga ta shiga ban d’aki kana ya fita daga d’akin.


Ruwan tea yaje ya d’aura ya juye a flask.


D’akin ya dawo ya ajiye flask d’in kana ya je ya d’akko milo da madara.


Kakkauran Tea ya had’a mata ya mik’a mata.


Kad’an tasha ta ajiye saboda yadda ba ta jin apatite a bakin ta.


Ko breakfast bai yi ba ya ce ta fito su tafi.


Wani private hospital suka je aka duba ta.


Bayan ya gama gwaje-gwajen shi ne ya nemi yaya Faruk ya mishi bayani abin da yake damun Nana.


Dr ne ya fara da cewa "Ba wata matsala ba ce ke damun matar ka illah ciwon mara da yawanci mata ke yi a lokacin da suke mensturation d’in su, ko wace mace da irin yadda ciwon yake mata, wasu suna shan wuya a lokacin da period d’in su ya zo musu, wasu za ka ga ba sa ciwon marar, ya danganta da halittar ta".


Yaya Faruk ne ya k’ar’bi zanen dacewa "Dr akwai wani magani ne da yake tsayar da ciwon".


"Akwai magunguna da allura da ke yi idan mace tana fama da ciwon marar, Wanda yawan shan Magungunan da allurar zai iya jawo wata matsalar in har ta zama addicted to it, za ta iya samun matsala a 'bangaren mahaifar ta ko dai ta wani 'bangaren, sai dai gaskiya abin da yafi magance wannan ciwo da ya wuce alak’a ta auratayya tsakanin miji da mata, in har namiji ya kusanci mace, za ta rabu da wannan matsalar".


Dr ne yaci gaba da cewa "Yanzu zan rubuta magunguna sai ka biya pharmacy ka siya mata magunguna".


"Na gode Dr" yaya Faruk ya fad’a.


Hannu ya bashi suka yi musabaha kana ya je pharmacy ya siya magungunan, Nana ya d’auka suka tafi gida.


Sai da ya tabbatar da tasha maganin ta sannan ya wuce side d’in shi.


Zama yayi ya fara tunanin da likita ya mishi, kenan har da laifin shi wajen ciwon Nana, mai yasa bai sauk’e nauyin shi da Allah ya d’aura mai ba a matsayin shi na miji alhalin ita tana k’ok’arin ta wajen kyautata mishi, rasa abin da yake mishi dad’i yayi san da ya tuno halin da ya ga ta shiga san da take cikin ciwon, shawarar da yanke shine in har ta gama period d’in ta zai sauke nauyin da Allah ya d’aura mai.


Rananr haka ya wuni a d’akin ta yana ba ta kulawa, da yaga ta motsa zai tambayaye ta ko ciwon ne.


Sai da Nana tayi kwana biyar kafin mensturation d’in ta ya d’auke.


Yaya Faruk da ya tabbatar da tayi tsarki yayi niyar kasancewa da Nana a yau.


Da daddare har Nana ta kwanta taji sallamar yaya Faruk.


Tashi tayi ta zauna ganin ya nemi gefen gado ya zauna.


"Ba ki yi bacci ba Nana" yaya Faruk ya tambaye ta.


"Eh ban riga nayi baccin ba" ta bashi amsa.


Shiru yayi kafin ya d’aura da cewa "In ba damuwa ki same ni a side d’ina".


Yana gama fad’ar haka ya tashi ya bar d’akin.


Mamaki ne da tunani ya kama ta a lokaci guda, tambayar kanta ta fara yi mai za ta yi ma yaya Faruk in taje side d’in shi, tasan in abu yake da buk’ata zai fad’a mata, amma kawai ce mata yayi ta same shi a side d’in shi.


Hijab ta d’aura akan sleeping dress d’in ta kana ta nufi side d’in yaya Faruk
[8/11, 23:45] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽


www.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa Writers Association





*Amsar Question of the day ita ce Suratul Bak’ara tana karantar da kira zuwa ga addini da yadda ake ginin sabuwar al’umma daga mutane daban-daban na Jahiliyya*.





*TUNATARWA*:


_Ka/ki zamo mai magana, amma idan za ka/ ki fad’i ka/ki fad’i alkhairi_.


_Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka/kin iya ma kowa_.


_Ka/ki so abin duniya, amma kar hakan yasa ka/ki mance da lahira_.






81-82


San da ta shiga ba ta ganshi a falon shi ba, hakan yasa ta nemi guri ta zauna.


Ya d’an jima a zaune a d’akin bai ji shigowar Nana ba, hakan yasa ya fito da niyyar ya fito falo ya jira ta.


Yana fitowa ya ganta zaune a falo.


"Khadihah ya kika zauna a falo, ki zo mu shiga daga ciki" cewar yaya Faruk.


Tashi tayi ta bi shi ba tare da ta ce komai ba.


Gefen gado ta nemi guri ta zauna tana wasa da hannun ta da ke sanye da azurfa.


Yanayin ta ya nuna a takure take da zaman.


"Khadija ki shiga cikin bayi ki yi alwala" yaya Faruk ya fad’a.


"Toh" ta amsa mishi.


Bayin ta shiga ta d’auro alwala kana ta fito ta zauna.


Tashi yayi suka yi sallar nafila raka’a biyu, bayan sun idar ne ya kama kanta ya dinga jero musu addu’o’i akan Allah ya basu zaman lafiya.


K’aramin frij d’in da ke d’akin ya tashi ya d’akko musu fresh milk.


Mik’a mata fresh milk d’in yayi ta amsa tare da cewa "Na gode".


Murmushi kawai yayi ya nemi guri ya zauna.


A hankali ta dinga sipping d’in

Please Login or Register in order to submit comment