Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya mik’e da niyyar marin Meema amma fahimtar hakan da Momi tayi yasa ta hana shi marin ta.


Cikin b’acin rai Dr ya ce "Meema tun da abin na ki ya wuce kaina ya fara koma wa kan Momi gwara in d’au mataki dan gaba ban san me za ki fad’a wa Momi ba dan haka ki je na sake saki d’aya in kin koyi tarbiyya da ilimin islamiyya may be in iya dawo dake".



Momi ce ta daka mishi tsawa ta ce "Sadik a she ba ka da hankali ban sani ba, a gaba na za ka saki Meema, duk abin da ta fad’a ko tayi ba akan kishin ka da take yi bane yasa ta yi hakan, kai me yasa ba ka iya controlling d’in zuciyar ka ne idan ya b’aci, yanzu wace riba ka samu da ka sake ta".


"Sorry Momi na yi kuskure, raina ne ya b’aci da maganganun da Meema take fad’a, I can’t tolerate it anymore".



Meema kuwa mik’ewa tayi ta ja tsaki ba tare da ta ce komai ba duk da yanda take ji a zuciyar ta na sakin da Dr ya mata.


Kayan ta taje ta had’o a trolik ta zo za ta wuce.


Momi ce ta kira sunan ta amma ko alamar juyowa Meema ba ta da alamar yi.


Tana fita ta shiga motarta ta ja ta bar gidan.


Momi fad’a ta dinga ma Dr akan abin da yayi tare da bashi shawarar in an kwana biyu ya je gidan su Meema ya bata hak’uri ya dawo da ita.


Ita kanta Momi ta dai fad’i hakan ne ganin yanda suke mutunci da amince da ke tsakanin su da gidan amma ba wai dan tana jin dad’in zama da Dr yake yi da Meema ba.


Dr ya amsa mata da zai je gidan su Meema d’in amma ba dan haka yake a zuciyar shi ba.


Haka Momi ta tashi ta tafi tare da mamakin halin Meema a ranta.


Meema kuwa tun da ta je gida take kuka.


Da Mominta ta tambaye ta dalilin kukanta ta fad’a mata gaskiya da k’arya.
Ran Momin ne ya b’aci ta ce Meema ba za ta koma ba tun da Dr ba shi ba ne autan maza.


Lokacin da Dadin ta ya dawo haka Momi ta zauna ta fad’a mishi abin da Meema ta fad’a mata.


Da Dadi ya tambayi Meema ta k’ara tabbatar mishi da maganar.


Dady ya tambayi ra’ayin ta game da komawar ta gidan Dr ta nuna ba ta ra’ayi, hakan yasa Dadi bai takura mata ba ya k’ayale ta.



Lokaci na ta tafiya yayin da bikin mu ya rage saura sati d’aya.


Duk wani shirye-shirye ta b’angare na da Dr komai ya kammala.


Komai sabo Abbu ya min kamar wata budurwa.


Ummu kuwa kayan gyaran jiki ta sa aka had’o min ana min da magunguna na gyara masu tsada ta dinga ba ni ina sha.


Su yaya Aminu da Khalil ma ba a bar su a baya wajen kawo nasu gudunmawar.


Hatta da su Anty Jiddarh da Anisa suma sun yi k’ok’ari ganin sun birge ni a bikin.


Dadin su yaya Faruk ma ba k’aramar gudunmawa ya bayar a biki na ba, ita kanta Momi gudunmawar da ta bayar ba k’arama ba ce da turarurrukan wuta masu tsada.


Hajiyan Wagini ma da tazo ta nuna farin cikin ta na auran da zan yi da Dr, nasan hakan ba ya rasa nasaba da ko yaya Faruk ya mata bayanin shi ya ce ya hak’ura da ni.


Gaskiya ba abin da zan ce sai dai godiya dan na tabbar ni y’ar gata ce gaba da baya.


Wannan karan ma akwatuna masu tsada shak’e da kaya ya min.


Na jinjina irin soyayyar da Dr yake min.


Yaya Faruk mu na yawan waya dashi tare da tambaya ta ko akwai abin da nake buk’ata.


Ta account ya turo min da gudunmawar biki.


Da na fad’a ma su Ummu su ma sun nuna jin dad’in su akan kyautar da yaya Faruk ya min.


Dr yaso mu shirya event amma ban ba shi goyon baya ba ganin wannan ba shi bane auren mu na farko.


Walima kawai da kamu na yarda zan yi.


Tun da aka fara hidimar bikin da Halima da Aisha ake yi duk da sun yi aure haka suke k’ok’arin zuwa.



Rana ba ta k’arya sai dai uwar d’iya ta ji kunya.


Yau dai gashi Allah ya nufa an k’ara aure na da Dr Abubakar Sadik a karo na biyu.


Sai dai in mana fatan Allah ya zaunar da mu lafiya.


Bayan d’aurin auren ne yaya Faruk ya shigo ya min fatan alhkairi.


Mun jima dashi yana min nasiha akan zamantakewar aure tare da kwad’aitar dani akan hak’uri a rayuwar aure.


Ni kam ba abin da zan ce ma yaya Faruk sai dai in ce Allah ya saka mishi da alkhairi.


Duk yanda na so Dr ya bari a d’aga tarewar amma ya k’i.


Haka yasa aka shirya ranar za akai ni.


Yau ma kamar aurena na farko sai da na ci kuka na san da za a tafi kaini na rabuwa da gida.


Su Anty Jiddarh da Anisa sai tsokana ta suke yi.


Lokacin da aka kai ni gidan Dr ne na ga Dr ya canza painting gidan tare da k’awata gidan.


Haka kowa ya watse ya rage sai ni kad’ai.


Ba su jima da tafiya ba Dr ya shigo gidan.


Ranar Dr ya nuna mn wata irin soyayya wanda baki ba zai iya fad’a ba, ya shayar da ni soyayya mai wuyar mantawa, ya nuna min kalar soyayyar da yake min wanda har tausayi ya bani ganin yanda yake zubar da hawayen shi akan irin son da yake min

Na sa ma raina cewa zan yi hak’uri da duk abin da Dr zai min tun da Allah ya nufi daman Dr shi zai zama mji na sannan zan yi iyakar k’ok’ari na ganin zaman mu bai samu wata tangard’a ba.


Sai da muka kwashe sama da sati d’aya Dr yana nuna min kulawa da soyayya.


Tun da na zo gidan na fahimci Meema ba ta gidan, ganin Dr bai min maganar ta ba yasa nima ban mishi maganar ta ba.


Yau da muna zaune ne na ke tambayar shi wai Ina Meema, na ga tun da na zo ban gan ta ba.


Amsa min yayi da tayi tafiya ne.


Tun daga wannan lokacin ban k’ara tambayar shi Meema ba.


Haka zaman mu ya ci gaba da gudana cikin so da zaman lafiya.



Yanzu ban da wata sauran damuwa a zama na da Dr.


Ina zuwa aiki na wanda muka yi da Dr tun kafin mu yi auren dashi akan zan koma aiki ya amince.


Yanzu Hanan ba ni da sauran wata matsala da ita saboda yanda take ba ni matsayina na matar wanta, daman ita Farida ban da matsala da ita.


Momi ma yanzu wata irin kulawa take bani ta musamman wanda da farko har na fara mamaki.


Nima dai ina iyakar k’ok’ari na wajen ganin na kyautata musu.



Yau Dr da yaje gidan Momin shi ne take mai magana akan dawo da Meema, ya amsa mata da zai je.


A ra’ayin Dr ba ya sha’awar dawo da Meema amma ganin yanda Momi shi ke son ya dawo da ita da kuma duba irin son da Meeman ke mishi yasa zai dawo da ita.


Lokacin da Dr ya je gidan su Meema ya shiga falon ba wanda yayi marhabin da zuwa dashi tsakanin Meema da Momin ta.


Maimakon ya samu kalamai masu dad’i a gurin su sai sab’anin haka.


Ba irin maganar da Meema ba ta fa’da mishi ta b’atanci ba.


Haka ya baro gidan ran shi a b’ace.


Ko da ya koma ya fad’a ma Momi yanda suka yi da Meeman ba ta ji dad’in haka ba.


Ta tabbatar mishi da za su je da Dadin shi dan su ba Meeman hak’uri.


Dr yasan zai yi wuya su Momi su shawo kan su Meema amma yafi son su je dan in ya hana ta za ta ga kamar ba ya son dawowa da ita ne.


Momi sun je da Dadi gidan su Meema d’in da daddare.


Dadin ta ya kira Meema ta sake tabbatar musu da cewa ita ba za ta koma gidan Dr ba tun da ya dawo dani, hasalima ta san ba son ta yake yi ba.


Duk yanda Momi da Dadin Dr suka ba wa Meema hak’uri akan ta koma ta ce ba za ta koma ba.


Hakan yasa jiki a sanyaye su ka tashi suka tafi ba tare da sun samu nasarar shawo kan Meema ba.


Ko da Dr yaje gidan Momi ta fad’a msihi yanda suka yi da Meema bai nuna damuwa shi ba.


Ni kuwa duk wannan abin da ke faruwa ban sani ba, sai da su Hanan suka zo suke fad’a min rabuwa suka yi da Dr d’in saboda aure na da zai yi.


Ban ji dad’in abin da ya faru ba saboda ban so ta sanadiyyar aure na yasa suka sami sab’anin ba har suka rabu.
Hakan yasa nima na tuno dalilin rabuwar mu da Dr lokacin da zai k’ara auren Meema ne.


Lokacin da Dr ya dawo na mishi maganar rashin dad’i na akan rabuwa da suka yi da Meema.


B’ata rai yayi ya dinga min fad’a akan in cire baki na akan Meema.


Hakan yasa na sa ma kaina cewa ba zan k’ara mishi magana akan Meema ba tun da ba ya so.


Ganin yanda yanayi na ya canza ne yasa Dr ya dinga ba ni hak’uri.


Nuna mishi nayi ba fushi nayi ba kana ya saki ranshi muka ci gaba da hira.


Yanzu aure na da Dr yana neman wata biyar amma har yanzu ban samu ciki ba.


Hakan yasa hankalin Dr ya fara tashi saboda shi ma ba abin da yafi buk’ata da ya wuce ya ganni da ciki.


Duk wani taimako da ya kamata Dr ya bani a matsayin shi na likita amma ba a samu nasara ba.


Hakan yasa Dr ya fara danasanin family planning d’in da yasa nayi wanda a yanzu yake so in samu ciki amma Allah bai nufa ba.


Ni kaina rashin samun ciki na tun lokacin zaman mu da Dr na farko har zuwa yanzu yana d’aga min hankali.


Ganin yanda Dr yake d’aga hankalin shi ne yasa na ke danne damuwa ta.


Haka Dr ya fara kai ni gurin k’wararrun likitoci suna duba ni.


Sun tabbatar da cewa ba wata matsala da na ke tare da ita, lokaci ne kawai bai yi ba.


Muna na cikin wata na shida ne muka fara gudanar da shirye-shiryen bikin Hanan da za ayi a watan.


Duk wannan shirye-shiryen da ake yi ba jin dad’in jiki na nake yi ba saboda a kwanakin yanda nake fama da rashin lafiya a tsaitsaye.


Yau ban da aiki saboda haka a gidan Momi na wuni saboda bridal shower da za ayi a washegari.


Tun da nake kwanciya saboda zazzab’in da ya rufe ni.


Hakan yasa Momi ta kira Dr ta fad’a mishi ba ni da lafiya.


Ba a d’au lokaci ba sai ga Dr ya zo gidan.


Haka ya shigo hankalin shi a tashe ya nufo kujerar da na ke kwance.


Abokan wasan shi sai tsokanar shi suke yi yana rama wa.


Kujerar da nake kwance ya zo ya zauna ya tab’a wuya na yaji yayi zafi.


Hakan ya tabbatar da zazzab’i ne ya rufe ni.


Zaunar da ni yayi ya nufi d’akin Momi ya d’akko jaka ta da veil d’ina ya dawo ya mik’a min.


Momi ce ta tambaye shi ina za mu kuma bayan yana ganin ban da lafiya.


Amsa mata yayi da gida zamu akwai allurar da zai min kuma bai tawo da ita ba.


Cikin tausayawa aka dinga min sannu.


Haka Dr ya rik’o hannu na muka shiga mota.


Momi har wajen mota ta rako mu tana min sannu.


Sai da taga mun fita daga gidan sannan koma ciki.


Tun a hanya Dr yake tambaya ta in da yake min ciwo ban da fever d’in da ke damu na ce mai ba komai.


Muna zuwa gida na nemi kujera na zauna.


Shayi Dr ya je ya had’o min ya bani na sha.


Ai ban gama shan shayin ba naji amai ya tawo min.


Da gudu na tashi na nufi band’aki na dinga kwarara amai kamar zan amayar da kayan ciki na.


Haka Dr ya rik’e ni sai da na gama aman.


Wanke min fuska yayi ya rik’o ni ya kai ni bedroom ya kwantar dani.


Allura ya min kana ya koma band’akin dan ya gyara.


Ko da ya dawo ya tarar nayi bacci.


Hakan yasa ya zauna a gefe na yana kallo na had’e da tausaya min.


Washe gari ma haka na k’ara tashi da zazzab’in had’e da amai.


Duk wani abu da na ci sai da na dawo dashi.


Hakan yasa Dr ya fara zargin ko abin da muke nema ne ya samu.


Gwada ni Dr yayi ya tabbatar da ina da shigar ciki na tsawon wata d’aya, shine yake wahalar da ni.


Rungume ni Dr yayi cike da murna yana cewa "Zarah mu gode ma Allah, abin da muke nema ne ya samu, Allah ya amshi rok’on mu, you are preganant, am going to become a father, Alhamdulillah".


Ni kaina wani irin farin ciki ne na ji ya kama ni da ban san yanda zan fasalta shi ba.


"Ke ma Zarah kina farin cikin za ki zama Momi ko?" Dr ya tambaye ni.



Hawaye ne ya fara zubo min a idanuna na d’aga mishi kai alamar eh.


Kwantawa nayi a kafad’ar shi yayin da yake shafa min baya na.


Duk yanda na so Dr ya bar ni in je gidan Momi saboda yau Bridal shower Dr ya k’i.


Momi da ta kira shi tambayar shi jiki na da kuma dalilin da yasa ban zo ba.


Shine yake fad’a mata dalilin ciwo na.


Momi ta yi murna da jin wannan labarin na cikin da na samu.


Hakan yasa Momi ta ce in zauna in huta ba sai na zo ba.


Ranar haka Dr ya tare a kaina yana ba ni kulawa.


Motsi kad’an zai tambaye ni abin da yake damu na.


Haka dai aka yi bikin Hanan ina laulayi.


Duk yanda Dr yaso in zauna a gida saboda yanayin jikina na k’i.


An kai Hanan gidan ta da ke Unguwar sarki a Kaduna.


Sai dai mu musu fatan Allah ya zaunar dasu lafiya.



Ciki na yana da wata 9 na haifi d’ana namiji aka sa mishi suna Imran.


Dr ya kashe min kud’i da baby a wannan haihuwar.


Momi haka ta had’o min kaya da na baby a akwati shak’e da kaya.


Dadin Imran kud’i ya aiko dashi ya ce a ba ni.


Hanan ma haka ta kawo ma baby kaya masu tsada.


Ummu da Abbu sun nuna bajintar su a haihuwar da na yi.


Su yaya Aminu ma da yaya Khalil ba a barsu a baya ba.


Yaya Faruk ma ya kawo Nana suna da sha tara ta arzik’i, ranar suka juya Abuja.


Duk yanda Ummu taso in koma gida in yi wanka Dr ya k’i.


Hakan yasa Momin shi ta ce in koma gidan ta nan ma hana wa yayi.


Dole tasa suka ky’ale shi a ka turo wata y’ar uwar Ummu tazo ta zauna da ni.


Haka muka ci gaba da kula da Imran.


Yanda Dr yake nuna ma Imran kulawa yasa naji ya k’ara shiga raina.


Ina da kusan wata biyar da haihuwa yaya Faruk ya tare a sabon gidan shi da ya gina a Abuja shi da abokin shi yaya Mus’ab.



Arzik’in Yaya Faruk ya k’ara yalwata had’e da ci gaba da taimaka wa wajen ceto rayuwar al'umma da basu tsaro yanda ya kamata, hakan yasa ya ke samun lambar yabo da lambar yabo.


Yanzu yaya na maida shi abokin shawara ta,
Ba ni da sauran wata matsala tsakani na dashi.



Wata rana ina zaune Dr ya dawo daga unguwar da ya fita.


Bayan ya huta ne yake sanar da ni daga d’aurin auren Meema yake ta auri wani d’an abokin Dadin ta da yake aiki a NNPC.


Shi ne na ke tambayar shi dalilin da yasa ya k’i dawo da ita yake fad’a min ta ce ba za ta iya zaman kishi da ni ba.


Abin ya ban mamaki ganin irin son da Meema take ma Dr amma ta hak’ura dashi.


Mamakin irin kishin ta nayi da har ta hak’ura da wanda ta ke so saboda kishi.


Dr ne ya tabbatar min da cewa wanda ta aura yana matuk’ar son ta tun kafin shi ya aure ta, hakan yasa ta amince ta aure shi.


Fatan zaman lafiya na musu ita da wanda ta aura.



B’angaren Dr ma abin sai hamdala saboda samun d’aukaka da alkhairi da yake yi wajen taimaka wa al’ummar musulmai.


Hakan yasa a ka k’ara mishi albashi mai tsoka.


Yanzu ban da aikin da Dr yake yi har kasuwanci ya fara yi.


Hakan yasa arzik’in shi kullum sai k’ara hab’b’aka yake yi.


Ba abin da zan ce a zamantakewar auren mu da Dr sai godiya ga Allah subhanahu wata ala.


Imran na da shekara d’aya da rabi na yaye shi.


Na so tun da nayi arba’in mu je Abuja gurin yaya Faruk amma Dr ya hana ya ce sai Imran ya k’ara wayau.


Sai bayan da na yaye shi ne na k’ara msihi maganar ya ce in bari ran weekend sai mu je.


Hakan yasa na kira yaya Faruk na sanar dashi ranar zuwan mu ba.


Ranar lahadi muka shirya muka tafi Abuja.


Sai da muka tsaya a wani gurin siyar da kayan wasan yara muka siya ma Khairat kana muka k’arasa gidan yaya Faruk kasancewar ya fad’a mana sunan unguwar.


Gaskiya gidan da yaya Faruk ya gina abin kallo ne saboda kud’in da aka kashe ma gidan.


Mun samu tarba ta musamman gurin yaya Faruk da Nana.


Khairat ta k’ara wayau sai gudun ta take yi ko ina.


Mun kai kusan yamma kafin mu yi shirin koma wa.


San da za mu tafi ne yaya Faruk ya ce mu shiga gidan yayan Nana mu gaisa da ita.


Kud’i masu yawa yaya Faruk ya ba wa Imran.


Kasancewar na san su lokacin da na yi zaman Abuja yasa san da muka shiga na zauna muka dinga hira.


Dr ne ya ce mu tashi mu tafi kasancewar yamma tayi.


Yaya Mus’ab ma haka ya ba wa Imran kud’i.


Haka suka rako mu muka shiga gidan yaya Faruk muka shiga motar mu.


Sai da suka ga tafiyar mu kana suka daina d’aga mana hannu.


Bayan dawowar mu daga Abuja da kusan wata biyar muka tafi Makkah muka sauke farali kasancewar tun lokacin da na samu ciki yaso ya biya mana, ganin laulayin da nake yi yasa ya d’aga biyan zuwa wata shekarar.


Mun je aikin hajji mun yi ibada kafin lokacin dawowar mu yayi muka dawo.


Y’an sannu da zuwa haka suka dinga yi mana sannu da zuwa.


Yanzu jikin Dr Alhamdulillah da sauk’i sai abin da ba za a rasa ba.


Shi kan shi yasan ya samu sauk’i sosai dan BP d’in shi ya dad’e bai tashi ba da ulcer da yake fama dashi.


Ko da ya je asibitin Barau Dikko b’angaren zuciya likitan ya tabbatar mishi da yana samun sauk’i ya kuma k’ara d’aura shi akan magani.


Dr ya k’san a nemi hutu a gurin aiki kasancewar yana so ayi mishi check up a k’asar India.


Dr ya mana booking d’in jirgin India saboda likitan zuciya (cardiologist) da yake so ya gani sannan za mu wuce k’asar saudiyya muyi Ummarah.


Ana saura kwana biyu tafiyar mu muka je gidan Ummu da yaya Aminu da Momin Faruk muka musu sallama.


Washe gari muka je gidan yaya Khalil da gidan Hanan da gidan Momin shi muka wuni a can
Gurin Momi muka bar Imran saboda a cewar Dr wani bayan duba lafiyar shi da za mu har da honeymoon za mu k’ara yi a can Indian, ba zai so Imran ya takura mishi ba.


Ranar da za mu tafi kasancewar jirgin safe za mu bi yasa Farida ta zo ta kai mu airport.


San da aka kira sunan mu gurin shiga jirgi ne muka mik’e had’e da d’aga ma Farida hannu muka nufi jirgi.


Farida ce ta dinga mana waving d’in hannu muna mata har muka shiga jirgi.


Kujerar kusa dani Dr ya zauna yana rik’e da hannu na.


A hankali Dr ya kalle ni ya sakar min tsadadden murmushi ya fara min magana a hankali.


"Fatima Zarah!" Dr ya ambaci suna na.


"Na am Dadin Imran" na amsa mishi.


"Ina jin dad’in kasancewa da ke a ko da yaushe, duk wuya duk rintsi ina tare da ke, ina miki wani irin so da ban san yanda zan fasalta miki irin shi ba, zan so ki ci gaba da so na har k’arshen rayuwar ki".


Murmushina na fad’ad’a shi na ce "Kar ka damu ni taka ce, nima ina son ka kuma zan ci gaba da son ka a ko wane yanayi".



Rungume ni yayi ya fara min magana a kunne "Na gode Zarah tah! Allah yasa indian nan da za mu ki samo ma Imran k’anwa a can, dan ba k’aramin honeymoon za mu sha a can ba kafin mu tafi Ummarah daga can".


Saurin rufe fuska ta nayi ina dariya.


Wani zazzafan kiss ya kai min a kumatu na wanda yayi daidai da tashin jirgin mu sararin samaniya.





Ni y’ar mutan Paki na ke cewa safe trip.


Alhammdulillah!


Anan na kawo kawo k’arshen wannan littafin mai suna *MAKAUNIYAR SOYAYYA*


Laifukan da na yi Allah ya yafe min.


Abin da na fad’a na alkhairi Allah yasa ya amfani jama’a.


Fata na har kullum Allah yasa labarin da nake rubutawa ya amfani al’umma.


Anan nake cewa sai mun k’ara had’uwa daku a cikin wani sabon littafi na mai suna……

Allah ka sa da mu da alkhairin sa baki d’aya.





*GODIYA GARE KU MARUBUTA*


Memcy Ata (Marubuciyar Ni da yaya Farooq)

Fauxia MB (Marubuciyar Lokaci ne)

Ummien Fauzan (Marubuciyar Bahijjah)

Ummy Abdoul (Marubuciyar Jamaluddeen)

Ina godiya da yanda kuke bin wannan labarin, da fatan da za ku ci gaba da suburbud’o mana labari masu ma’ana.




*ANA TARE*

Mrs Mansoor (Marubuciyar Munafukin miji)

Batul Adam Jatko (Marubuciyar Amfanin soyayya)

Mrs Adam
(Marubuciyar Mamaya)

Hauwa Usman (Marubuciyar Gadar zare)

Noorul Jannerh (Marubuciyar Detective Noor)

Ina jin dad’in yanda kuke nuna kulawar ku gare ni.




*YABON GWANI YA ZAMA DOLE*


Dole ne in jinjina muku marubutan Kainuwa Writers Association, kuna ba da gudunmawar ku wajen fad’akar da al’umma da nishad’antar dasu.




*BA NI DA KAMAR KU*


Y’an Mufy & Maryam A paki fans

Ba wanda ya kai ku yawan comment akan wannan littafin da nuna kulawar Ku akan novel d'in.

Da fatan za ku ci gaba da nuna kulawar ku gare ni.

Nima y’ar mutan paki na tare da ku.

[Mmn Walida, Sakina ilyas, Autar Mama, Fadeela, Hauwa Hussaini, Fadeela, Habiba Rabo, Br Teemah, Hauwa, Maimuna, Hauwaa, Hajara Tijjani, Maryam, Aysha, Safia, Ummie, Najerh, Siddiqa Dahiru, Hauwa j, Lubiee, Maman Aliko, Ramlah Salis Kabir, Maman Umar, ~Hauwa, Harira, Zakiyya, Aysha Umar gogo, Ummu Haneef]




*BAN MANTA DA KU BA*


Y’an Kainuwa Fans whatsapp da facebok
Kuma ba abin da zan ce muku na irin yanda kuke nuna jin dad’in ku akan wannan novel d’in da yin comment d’in ku.

[Xarah Auwal, Meeynarh, Asmau Madugu, Aisha Mahmud, Aisha Madugu, Eesha, Deejahnah, Khadija y’artuwalla, Fatima Arkilla, Rufaatu, Zinatu gatari, Fatima, Binafat, Fatima Ibrahim, Maman Sa’a, Maimunat Abba, Mrs Ahmad, Maryam Bello, Xee virus, Zainab Mas’ud, Maman Faruk, Ummi, Mom Affan, Amina Samaru, Rahma ja’afar, Maman Shahida, Maman Usy, Hajiyar Allah, Atika Bashir, Khadijah Ahmad, Murjanatu Bukhari, Faeedaabdullahi, Aisha Ibrahim, Ameenat Umar Abdulllahi]



*GAISUWAR TA KU CE*


Ina mik’a sak’on gaisuwa ta ga wannan groups d’in whatsapp da facebook yanda kuma ku ke yin comment akan wannan novel d’in.

Tauraruwar Mace group

Ni da yaya Farooq group

Mrs Mansoor novels group

Daily Hausa novels group

Novels Villa group

Da sauran groups d’in da ake posting d’in wannan novel d’i




*DOLE NE IN TUNA DA KU*


Ba ni da bakin godiya gare ku na yadda kuke son novel d'in nan da nuna k'aunar ku gare ni.


Duk irin godiyar da zan nuna muku ina ganin tayi kad'an saboda yanda kuke tare dani.


Fata na Allah ya ci gaba da had'a mu da masoyan mu a ko ina su ke.


Wanda su ka kira ni daga wasu jahohin da Wanda suka min text da masu min magana ta Pc ba abin da zan ce muku sai godiya


Mhiz Tawakkaltu


Nafisa Khaleed (Bintu Khaleed)


Fatima Sunusi Baraya (Unique wife)


Badiyya Kano


Mmm Abdullahi Adnan


Saudat


Hussaina (Facebook)


Hussaina paki


Fannata ta Annabi


Asiya Paki


Zainab Abdullahi (Abuja)


Hussaina Ahmad


Fatima Bintu Kano


Hadiza Murtala


YusraYusra


Da sauran wanda ban samu rubuta sunan su ba saboda yawan ku.


Da fatan za a min uzuri akan haka.




Daga Taskar Marubuciyar

Haka Amincin yake?

Rayuwar Yusra da Afsahan

Silar Kayan Sallah

Makauniyar Soyayya



Taku har kullum Maryam Ahmad paki na ke cewa Bissalam

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke

Please Login or Register in order to submit comment