Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cika d’auka ba sai ya gadama, in ma ya d’auka ba na iya sakewa in mishi magana saboda tsoro, sai dai in ce a gaida Khairat da maman ta.


Tun san da Dr ya zo lokacin da na dawo daga aiki bai kuma zuwa ba, hakan yada nima na manta da batun shi dan ina sha ko ya ji haushin abin da na mishi ne.



Yau ranar ta kasance ranar lahadi ba ni da aiki, hakan yasa na shirya dan in shiga kasuwa in siyo kayan make-up d’ina da suka yi k’asa.


Ummu na je na fad’a ma wa kana na shiga mota ta na bar gidan.


Kasuwa na shiga na yi siyayya ta kana na d’akko hanya na dawo gida.


Tun da na shigo layin na ga motar Dr a gate d’in gidan mu.


K’arasowa na yin a yi parking d’in mota ta a can gefe na fito na nufi hanyar shiga gidan mu.


Da sauri Dr ya fito daga motar ya nufo in da na ke.


Cikin sanyin murya ya min sallama na amsa mi shi.


"Fatima gani na k’ara zuwa, ina fatan yau a free kike dan na ga yau ranar hutu ce, shi yasa na zo a yau".


"Yau ma ka makaro saboda yanzu na dawo daga unguwa, za ka iya dawowa any time da ya maka".


A yanzu Dr ya daina mamaki na saboda shi kan shi yasan sani da yayi a baya ba ni ba ce a yanzu.


Cikin kwantar da murya ya ce "Zarah dan girman Allah ki daure ki saurare ni, nasan duk wannan abin da kike min kora da hali ne amma ba zan yi fushi ba in dai za ki tsaya ki saurare ni".


Jin ya had’a ni da girman Allah yasa na ji jiki na yayi sanyi, dan haka na ce mishi mu shiga cikin gida.


Gurin hutawa da aka keb'e a gidan mu muka zauna.


Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin Dr ya kau da shirun da fara ba ni hak’uri akan abin da ya min a baya kana ya d’aura da cewa "Zarah ina son ki, duk abin da ya faru nasan laifi na ne na kuma amsa, rayuwa ta ba za ta ci gaba da tafiya daidai ba in ba ke, na shiga wani hali duk ta sanadin son ki, yanzu haka ina da hawan jin da kuma heart disease, nasan ba komai ya sa min wannan ciwon ba sai tunanin ki da nake yawan yi, pls Zarah ki manta baya ki yafe min mu koma rayuwar mu irin ta baya ta hayar amince min mu yi aure".


D’agowa nayi na kalle shi jin ciwon da ya ambata yana tare dashi kuma duk ta sanadi na ya samu ciwon.


Tausayin shi ne ya kama ni amma da na tuna halin da na shiga tun da na fara soyayya dashi har san da muka rabu yasa nayi saurin ajiye tausayin shi a gefe na dan a yanzu ba ni da buk’atar ci gaba da zama dashi, na fi buk’atar in auri d’an uwa na da ya nuna min so tun kafin in san miye so.



Cikin d’aurewar fuska na ce "Dr na ji bayanin ka, sai dai a yanzu ba wani taimako da zan iya maka sai dai in ce Allah ya yaye maka lalurar da take damun ka saboda shi ya d’aura maka, maganar in amince maka ma ba ta taso ba saboda a yanzu na yi wa kaina fad’a, ba na so in k’ara maimaita makauniyar soyayyar da nayi a baya wacce tasa ni yin danansani, a yanzu na fi buk’atar in auri yaya Faruk d’an uwa na in dai zai amince da ni kamar yanda ka fad’a min in je in aure shi, Sadik kai kan ka shaida ne a irin son da na nuna maka, na nuna maka so da ba kowace mace ba ce za ta iya nuna maka kwatank’wacin shi, na samu matsala da iyaye na da y’an uwa na duk a dalilin son ka amma wai ni Dr ka ma gori akan ban ma iyaye na biyayya ba sannan ka had’a min da tukwici na saki akan in je in auri d’an uwa na, tun a lokacin na sa ma raina cewa Dr na hak’ura da kai".


Hawaye ne ya zubo min masu zafi na yi saurin goge wa kana na ci gaba da cewa "Dr ka min abubuwa da dama Dr na shanye amma ba wanda ya fi bak’anta min rai irin sakayyar da ka min ta saki sannan ba ka k’ara waiwaiya ta ba sai a yanzu da kayi ra’ayin kan ka saboda kan tak’amar kai ka ke sarrafa zuciya ta yanda ka gadama, in wannan ne tunanin ka Dr ka riga ka makaro saboda Fatiman da ka sani a da ba ita ba ce a yanzu".


Mik’e na kalli Dr wanda jikin shi yayi sanyi ya kasa magana na ce "ka gaida gida".


Ina gama fad’ar haka na bar gurin yayin da Dr ya kifa kan shi akan table d’in da ke gurin.


Da k’yar ya samu ya shiga motar shi ya ja ya tafi.


Tun daga wannan lokacin Dr yake bibiya ta, ko ya zo gidan mu ba ko wane lokaci nake fita ba sai na gadama, kiran waya da text messages har abin ya fara damu na, yanzu ta kai har gurin aiki yana biyo ni yana rok'o na, duk wannan abin da Dr yake yi dai da na ji a raina cewa zan canza ra'ayi na in amince dashi ba dan har yanzu ban daina jin d'acin abin da ya min a baya ba sannan a yanzu na riga na sa ma raina cewa Yaya Faruk shine zab'i na.


Duk da Yaya Faruk bai ba ni goyon baya akan maganar da na zo mishi da ita ba ina sa ma raina cewa zan iya auran shi a haka ko da a yanzu ya daina so na saboda nasan in har mu ka yi auren soyayya ta za ta dawo a gurin shi ba re ina da tabbacin cewa Yaya Faruk har yanzu yana so na sai dai abin da na mishi a baya ne yake k'ok'arin k'aryata zuciyar shi a kaina..


Ni kaina yawan takurawar da Dr yake min yasa hankali na ya fara tashi saboda ba na so wata alak'a ta soyayya ta k'ara had'a ni da Dr.


Hakan yasa nake iyakar k'ok'ari na wajen ganin na ba shi fuskar da zai matsa min akan maganar soyayyar mu.


Ga zawara da a yanzu suke son matsa min a gurin aikin mu ko ma su aikowa gidan mu, su ba na sa su a lissafi saboda bana ganin zan iya tsayar dasu a matsayin Wanda zan aura, hakan yasa na ke basu hak'uri a duk lokacin da d'aya daga cikin su ya tunkare ni da wata Kalmar soyayya.


Babban tashin hankali na shine nasan Abbu na d'aga min k'afa ne kafin ya min maganar tsayar da miji gashi har yanzu ban San a babin da na ke da Yaya Faruk ba tun da babu wata tsayayyar magana da ta shiga a tsakanin mu.


Wannan shine matsalar da na ke fuskanta a yanzu.



Yau da daddare muna zaune a main parlour bayan mun gama cin abinci muna tab'a hira da su Abbu.


Abbu ne ya canza hirar da kiran sunan.
Amsa mishi nayi tare da maida hankali na gurin shi.


Abbu ne ya ce "Fatima rayuwa tana tafiya da k'alubale sannan lokacin mu yana ta tafiya, nasan kin San cewa duk daren dad'ewa za ki sake wani auren tun da yanzu kin fi shekara d'aya a gida, abin da yasa kika ga ban miki maganar aure ba saboda ina so ki samu natsuwa, na zuba miki ido ne ina sha za ki kawo Wanda kika tsayar a matsayin miji Wanda za ki aura amma shiru, ke kan ki kinsan na d'aga mi ki k'afa ban mi ki maganar aure ba, kin San ni da Ummun ki ba za mu so ki ci gaba da zama ba tare da kin yi aure ba, ko wace mace darajar ta aure, A yanzu ke Musulunci ya ba damar ki zab'i wanda kika ga ya dace ya zama abokin rayuwar ki, ina so ki lura gurin zab'an Wanda ya dace da ke dan ba na so ki k'ara kwatanta kuskuren da kika yi a baya duk da k'addara ba Wanda ya isa ya kauce mata, saboda haka na ba ki nan da d'an lokaci ki tsayar da d'aya daga cikin masu nemanki da aure kin ji ko Fatimah".


Gaba na ne kawai yake fad'uwa tun da Abbu ya fara maganar nan.


Ba abin da ya fi d'aga min hankali shine nasan tun da Abbu yayi maganar nan nasan cewa daman irin wannan ranar na zuwa sai dai na so a ce Abbu ya min wannan maganar ne a lokacin da muka tsayar da magana da Yaya Faruk ya amince min.


Nasan Abbu daUmmu za su yi murna da maganar, sai dai a yanzu ba ni da wani abin cewa tun da Yaya Faruk bai ba ni goyon baya akan haka ba gashi Abbu ya ba ni nan da d'an lokaci, hakan na nufin a ko wane lokaci zai iya tunkara ta ya ji wanda na tsayar.


Abbu ne ya katse ni da cewa "Fatima kin ji abin da na ce ko?".


Cikin sanyin murya na ce " Na ji Abbu, zan yi k'ok'ari in tsayar da d'aya daga cikin su".


Murmushi Abbu yayi kana yace "Yawwa autar Ummu, haka nake son ji, Allah ya miki albarka ya zab'a miki wanda yafi zama alkhairi a gare ki".


A hankali na amsa da "Amin Abbu".


Juyawa yayi ya kalli Ummu wacce tun San da Abbu ya fara min magana ba ta ce komai ba ya ce "Aisha ko kina da abin cewa".



"Ba ni da abin cewa dan nima zaman Fatima ya fara damu na, nafi so in ganta a d'akin mijin ta, tun da yanzu ka mata magana nasan za ta maida hankali wajen fitar da miji, Allah ya tabatar da alkhairi ga duk wanda za ta zab'a" cewar Ummu.


Abbu ne ya amsa da "Amin Aisha".


Abbu ne ya kalle ni ya ce " Fatima za ki iya tafiya".


Sallama na musu na nufi d'aki na.


Ina shiga na fad'a kan gado ina tunanin maganar da muka yi da Abbu.


Hawaye ne ya fara zubo min wani na bin wani.


Nasan hawayen da na ke zubarwa ba zai wuce akan rashin mafita da har yanzu ba na kasa samu akan Yaya Faruk ba, gashi Abbu ya k'ara min maganar da ta k'ara d'aga min hankali.


Ganin in dai na zuba wa Yaya Faruk ido ba tare da na k'ara nuna jajurcewa ta akan maganar mu dashi ba wankin hula ne zai kai ni dare.


Shawarar da na yanke shine gobe in Allah ya kaimu zan kira shi a waya da in k'ara tuna mishi maganar duk da gargad'in da ya min dan wannan ne kad'ai mafita a gare ni.


Haka na ci gaba da sak'a da warwara kafin bacci ya d'auke ni.


Washe gari sai da na duba lokacin da Yaya Faruk bai gida kana na kira shi.


Da farko na d'auka cewa ba zai d'auka ba saboda kusan sau 4 wayar na shiga amma bai d'auka ba.


A kira na biyar ne cikin sa'a ya d'auka.
Tun da ya min sallama bai k'ara cewa komai ba.


Bayan na gaishe shi ne na tambayi lafiyar Khairat da Nana ya amsa min a tak'aice.


Shiru ne ya biyo bayan gaisuwar da muka yi.


Hakan Yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "ki gaida su Ummu ina da abin yi dan na ga ke ba ki da abin cewa".


Sanin katse wayar zai yi yasa nayi saurin cewa "Pls Yaya Faruk kayi hak'uri kar ka kashe wayar, magana na ke so muyi in ban takura maka ba" na fad'a.


Shiru yayi kamar ba zai min magana ba kana a dak'ile ya ce "Ina jin ki, amma ki tak'aita abin da za ki fad'a dan ina da aiki a gaba na".


Ni ce na ce Cikin rawar murya na ce " Yaya Faruk... Akan... Maganar mu ta kwanaki ce....na ke so....in tuna maka".


"Wace magana kenan" ya fad'a a tak'aice.


Shiru nayi ina jin tsoron tuna mai saboda gargad'in da ya min akan maganar.


"Ko ba ki ji tambayar da na miki ba ne" cewar Yaya Faruk.


Cikin daburcewa na ce "Akan maganar da na maka...am..uhm...da na ce...ina sonka...uhm....ka....amince...ka ...uhmm...aure....n.....".


Wata irin tsawa Yaya Faruk ya min wacce tasa na had'iye sauran maganar da nayi niyyar k'arasa fad'a.


Cikin fad'a Yaya Faruk ya ce " Fatima kar ki bari mu had'u dan sai na ci ubanki da kyau, na lura har yanzu ba ki yi hankali ba, sai na hukunta ki da irin hukuncin da ya dace dake, kar ki yi tunanin kin girma, har yanzu kallon yarinya na ke miki, ban da tsabar iskanci har ki kira ni ki k'ara fad'a min maganar da na miki gargad'i akai saboda kin raina ni, duk San da kika bari na shigo Kaduna za ki gane kuren ki, ki kiyaye ni".


Duk da na ji haushin maganganun da ya fad'a min sun b'ata min rai amma haka na daure na ci gaba da rok'on shi.


Maganganun da yaci gaba da fad'a min ne yasa raina ya k'ara b'aci amma duk wannan bai sa na ji zan hak'ura da Yaya Faruk ba.


A k'arshe da yaga zan matsa mishi katse wayar yayi.


Kifa kaina nayi na fara kuka mai cin rai.


Da na gaji da kukan ne na share hawaye na.


Tunanin da na ke yi in har Yaya Faruk bai amince min ba wa zan tsayar a matsayin miji gashi Abbu ya bani lokaci ban kuma san lokacin da buk'aci amsa ta ba.


Ba na jin zan iya amincewa da masu zuwa guri na dan ba ma fita nake yi ba bare har in duba wanda ya dace in tsayar.


A zuciya ta ba na jin zan iya auran Dr ba wai dan ba na son shi ba, hasalima har yanzu da soyayyar shi a cikin raina sai dai ina k'ok'arin dannewa saboda guje ma kaina komawa gidan jiya ga yanzu yayi aure, ban san wace matsala kuma zan fuskanta ba.


Fata na shi ne komai ya zo min cikin sauk'i yanda ba zan sami Matsala da Abbu ba.


Ranar haka na wuni a d'aki na rasa abin da yake min dad'i sai da Ummu ta kira ni kana na fito.




A can b'angaren Yaya Faruk kuwa tun da ya katse wayar da yake yi da ni ya ja k'aramin tsaki.


Ran shi ne ya b'aci jin dalilin kiran da na mishi.


B'acin ran da damuwar da ya shiga a baya shine na ke in dawo mishi dashi sabo.


Matakin da zai d'auka a kaina ya fara yi dan ba yaso in dawo mishi da hannun agogo baya.


Yana cikin wannan halin ne Yaya Mus'ab ya shigo cikin office din.


Hannu ya mik'a ma yaya Faruk su ka yi musabaha kana ya nemi d'aya daga cikin kujerun da ke office d'in ya zauna.


Yanayin shi da Yaya Mus'ab ya lura ne yasa ya ce "Faruk lfy kuwa na ga yanayin ka kamar kana cikin damuwa" cewar Yaya Mus'ab.


Nazari ya fara yi akan ya fad'a ma Mus'ab abin da yake damun shi ko ya bar shi.


Wata zuciyar ce ta ke mishi gargad'in kar ya fad'a mishi shi ko dan saboda Khadijah.


Yasan Mus'ab mai fahimta ne amma in dai yaji maganar nan bai San yadda zai d'auki maganar ba saboda a yanzu k'anwar shi yake aure.


Wata zuciyar shi kuwa k'arfafa mishi gwiwa take yi akan ya fad'a mai dan yasan zai bashi shawarar da ta dace.


Mus'ab ne ya katse shi da tunanin da yake yi ya ce "Faruk ka fad'a min me ke damun ka".


Nisawa Yaya Faruk yayi kana ya fad'a mishi abin da yake faruwa tsakani na dashi.


Ga mamakin shi murmushi ya ga Yaya Mus'ab na yi.


" Faruk wannan ba wata matsala ba ce, ina ganin yanzu ne Allah zai cika maka burin ka na samun Fatima cikin ruwan sanyi, tun da ita tayi maka maganar tana so ka aure ta ba matsala ba ce tun da har ta gane kuskuren ta, sannan kaima Allah ya dubi hak'urin da kayi shi yasa Fatima ta tunkare ka da maganar, nasan ba wacce za ka so sama da Fatima, ni dai ina ba ka shawarar ka amince".


Bin shi da Kallo yayi kawai Yaya Faruk yayi har ya gama maganar.


Dariya Yaya Mus'ab yayi ya ce "Ya a ka yi ne Bregadier na ji ka yi shiru, ko shawarar ce ba tayi maka ba".


Tab'e baki Yaya Faruk yayi kana ya ce shawarar da ka fad'a ne naji ban gamsu da ita ba, shi yasa ka ga nayi shiru".


Murmushi yaya Mus'ab yayi ya ce " Nasan za ka d'auki magana ta a shirme, wannan maganar da nake ma ka da gaske nake yi, nasan za ka yi zaton saboda Nana ba zan ba ka goyon ba Saboda tana matsayin k'anwa ta, Faruk zan so ka samu farin cikin da ka rasa a baya, ina so kaima ka d'and'ana gard'in soyayya da masoya suke sha, nasan har yanzu da son Fatima a ran ka, saboda haka feel free, ina da tabbacin Fatima ba za ta ba ka matsala ba".


Murmushi Yaya Faruk yayi ya ce "Mus'ab a rayuwa komai na iya canza wa, a tunanin ka kana tunanin yanzu zan iya dawo da Fatima cikin rayuwa ta, kai kan ka shaida ne a akan abin da Fatima ta min, tun lokacin da ta nuna ba ta ra'ayina na sa ma raina cewa na hak'ura da ita, kasan ni kaifi d'aya ne ba na canza magana, soyayyar Khadijah kad'ai ta ishe ni, ina jin soyayyar ta a dukkan sassan jiki na, ban mata adalci ba idan na auri Fatima bayan halaccin da ta min, ko da zan k'ara aure ba Fatima zan aura ba".


Yasan Yaya Faruk magana d'aya yake yi, yasan yanzu duk shawarar da zai bashi ba zai d'auka ba, gwara ya mishi shiru, yasan nan gaba zai nemi shawarar sa.


Yaya Faruk ne ya canza hirar da maganar aikin su.


Haka suka ci gaba da tattaunawa kana Yaya Mus'ab ya mishi sallama ya tafi.


Yau ina zaune a falo na ji sallamar Anisa.
Cikin murna na amsa mata.
Zama tayi muka gaisa kana ta tafi gurin Ummu.


Ta d'an jima a can gurin Ummu kana ta dawo falo muka ci gaba da hira.


A k'arshe d'aki na muka wuce muka ci gaba da hirar

Ji nake yi kamar in fad'a ma Anisa damuwa ta amma ina Shakkar fad'a mata, nasan Anisa za ta ba ni goyon baya akan maganar amma wata zuciyar na hana ni.


Shawarar da na yanke shine kar in fad'a mata.


Ranar haka mu ka wuni muna hira da Anisa.


Sai da daddare Yaya Khalil yazo suka tafi..


Haka lokaci ya ci gaba da tafiya.



Yau Dr ne da Momi suke hira a d'akin ta.


Cikin hirar ne Momi ta kalle shi cikin kulawa ta ce "Sadik wai me yake damun ka ne, duk ka bi ka canza da yanda na san ka, duk Wanda ya kalle ka yasan kana cikin damuwa, ka kuma san ciwon da kake tare dashi ba ya buk'atar damuwa da tunani dan nasan ka fi ni sanin haka tun da kai Likita ne, ba sai na tsaya fad'a maka illar hakan ba, ina so ka fad'a min matsalar ka Sadik".


Cikin damuwa Dr ya ce " Momi abin da yake damuna bai wuce akan Zarah ba, na je gurin ta time without numbers amma har yanzu ta k'i ta hak'ura, Momi na rasa yanda zanyi dan duk wata hanya da nasan zan bi in ga ta amince dani amma still har yanzu ba canji, a cewar ta d'an uwan ta za ta aura, Momi ina cikin damuwa ".


Tausayin Dr ne ya kama ta, tasan son da yake min ba abu ne mai sauk'i da za ta ce ya hak'ura dani ba, ita kanta tana so d'an ta ya kasance cikin walwala da sukuni, hasalima a zaman da nayi da Dr ba ta ga wata matsala a tare dani ba, sai dai ba taso a kaina ya ci gaba da sa kan shi cikin damuwa.


Cikin lallashi Momi ta ce " Sadik nasan kana son Zarah, ni kaina nasan yarinyar ba ta da matsala, ba na so kana sa ma kanka damuwa akan ta, ni kaina zan yi farin ciki idan ka k'ara auran ta a karo na biyu, amma tun da ta nuna yanzu ba ta da interest akan ka, tafi son d'an uwanta ina ganin ka hak'ura da ita".


Cikin sanyin murya Dr ya ce "Momi bazan iya hak'ura da Zarah ba, ina son ta, zan shiga wani hali in na rasa ta, ki taya ni addu'a Momi".


Jikin Momi ne yayi sanyi jin kalamen Dr, ita kan ta tana tausaya mishi halin da yake ciki, za ta taya shi addu'a Allah ya mallaka mishi ni ko ya samu kwanciyar hankalin da take buk'ata a gurin shi.


Cikin taushin harshe Momi ta ci gaba da kwantar mishi da hankali da bashi k'arfin gwiwa akan zai same ni.


Wannan shi ya k'arfafa ma Dr gwiwa har ya manta da damuwar da yake ciki.


Yau bayan na dawo aiki ne na wuce gidan Anty Jiddah.


Mun sha hira da ita kana nayi niyyar fad'a mata abin da yake damuna dan nasan za ta bani shawarar da ta dace.


Zayyano mata halin da na ke ciki tsakanin Yaya Faruk da kuma takurawar da Dr yake min.


Tun da na fara maganar Anty Jiddarh take kallo na har na k'arasa maganar.


Anty Jiddarh ce ta ce " Fatima a bayanin da kika min ban ga laifin Faruk ba, duk Wanda aka ma irin abun da kika ma Faruk ba kowa ba ne zai yi saurin amincewa dake a lokacin da kika zo da irin buk'atar da kika zo ma Faruk da ita, ni kaina zan yi farin ciki idan Faruk ya aure ki saboda kun dace kuma za ki ji dad'in zama dashi, ta b'angaren Dr ina ganin ki rage abin da kike mi shi tun da ya gane kuskuren shi sannan a tsakanin Faruk da shi Dr d'in ba ki san Wanda Allah zai zab'a miki a matsayin miji ba, shawarar da zan baki ki dage da addu'a akan Allah ya zab'a miki abin da yafi alkhairi".


"Na gode da shawarwarin ki Anty Jiddarh, insha Allah zan dage da addu'a" na fad'a.


shawarwari Anty Jiddarh ta ci gaba da fad'a min Wanda hakan yasa ni farin ciki.


Haka muka ci gaba da hira da ita har Yaya Aminu ya dawo kafin na musu sallama na tafi.



Yau da yamma ina zaune a d'aki ina k'arasa wani aiki da na tawo dashi daga office.


K'arar da waya ta tayi ne ya katse min aikin da na ke yi.


Ganin sunan Dr ne a jikin screen d'in yasa na ja k'aramin tsaki na ci gaba da aikin da na ke yi.


Sai da na ji wayar ta k'ara ringing sannan na d'auka.
Bayan na d'auka ne yake sanar dani gashi a gidan mu yana jira na.


Ko da na gama wayar dashi aikin da nake yi na ci gaba da yi.


Sai da ya k'ara kira nan sannan na tashi na fita.


A jikin motar shi na same shi yana tsaye.


K'arasawa na yi na gaishe shi kana na yi shiru.


Amsa min yayi da murmushi a fuskar shi.


Yau ma dai kamar ko da yaushe rok'o na Dr yayi akan in amince dashi tare da k'ara fad'a min halin da yake ciki akan so na.


Duk da a yanzu ina jin tausayin Dr amma hakan ba zai sa in amince dashi ba dan haka na k'ara fad'a mishi yayi hak'uri ni na hak'ura dashi.


Yanayin shi ne na ga ya canza, alamu sun nuna bai ji dad'in rashin amincewa ta ba duk da ba wannan ba ne karo na farko da na fad'a mishi ya hak'ura dani.


Bai ce min komai ya fara tafiya dan ya shiga mota.


Yanayin yanda na ga yana tafiya na tabbatar da maganar ba k'aramar girgiza shi tayi, yanayin tafiyar shi na nuni da cewa kamar ba yi da lafiya.


Haka da yaja motar da gudu ya danna wa mai gadi horn yazo ya bud'e mishi gate ni kuma na koma cikin gida.


Dr kuwa haka ya dinga Jan motar da gudu har ya k'araso gida.


Side d'in shi ya wuce ya kwanta.


Zuciyar shi ce ke wani irin bugawa yayin da yaji kamar an tokare mishi k'irjin shi.


Numfashi ya fara fitarwa mai wahala yayin da ya

Please Login or Register in order to submit comment