Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yi kamar ita ta rera wak’ar.


Ganin remote a hannun Meema ya tabbatar min da ita ta canza channel d’in da nake kallo.


Raina ne ya ‘baci da abin da Meema ta min amma sai na daure ban nuna hakan a fuska ta ba.


Cikin taushin murya na ce "Meema d’an dawo min da channel d’in da nake kallo, ina son shirin da ake yi ne, na ga ma sun kusa gama wa, in aka gama sai ki dawo da channel d’in da kike kallo".


Wani banzan kallo ta watsa min kana ta ce " Wannan nayi niyyar kallo, dan haka bazan canza ba".


Kallon mamaki na bi ta dashi, ganin yadda take son nuna min mulkin mallaka ni da gida na.


"Amma dai Meema kin san ni nake kallo kafin in bar gurin ko, dan na ce ki maida min channel d’in da nake kallo za ki ce ba za ki canza ba" na fad’a ina k’ok’arin controlling d’in fushi na.


"Ba zan canza ba Zarah" ta fad’a ba tare da wata shakka ba.


Ganin in na tsaya bin Meema a hankali za ta ci gaba da raina min hankali, dan haka na watsa mata harara na ce "Kin san dai gida na kika zo kika same ni, kin ga kenan baki da ikon nuna min isar ki a inda baki da ikon yin haka, dan haka dole ne a canza channel d’in nan dan ba ita nayi niyyar kalla ba".


Kallon mamaki ta bi ni dashi ganin yadda na fad’a mata maganar da ba tayi zaton zan maida mata martanin maganar da na fad’a mata.


Yatsina fuska tayi kana ta ce " Masu gida manya, amma ina jin shi gidan da kike tunk’ahon dashi, kema ba naki ba ne, na yaya Sadik ne, kin ga ina da ikon amfani da abin da yake nashi".


Dariyar tura haushi nayi kana na ce "Ina ganin bakin ki bai fad’a miki gaskiya ba, ki kalli falon nan da kyau, komai da kika gani a falon nan daga gidan iyaye na aka kawo ni dashi, kin ga kenan ba ki da power da kayan nan side d’in, in iko kike so ki nuna min, ki je can side d’in shi Sadik d’in sai ki yi ikon ki a can, in ma side d’in a kulle yake ki zo in baki key d’in side d’in, in nayi niyya ma ko can d’in side d’in Dr d’in, zan iya nuna matsayina na matar gidan ba ke ‘yar d’osano ba".


Kwalliya ta biya kud’in sabulu dan maganar da na maida ma Meema sun k’ona mata rai, in ka kalli fuskar ta zaka ga canzawar da tayi zuwa ‘bacin rai.


"Ke Zarah har kin isa ki min gori dan na zo gidan yaya Sadik, kin san Dad d’ina yana da kud’in da zai iya siyan fiye da kayan da kike cika mana bakin an kawo ki dashi, in banda kin ci darajar yaya Sadik da sai kin yi danasanin maganar da kika fad’a min, da kike tunk’ahon ke matar gida ce, dan dai Allah bai nufa mun yi aure da yaya Sadik ba ne, da ba ki isa ki shigo cikin gidan nan ba" Meema ta fad'a cikin fushi.


Mamakin furucin Meema nayi wai dan Allah bai nufa sun yi aure da Dr ba ne, da ban isa in shigo gidan ba, sai yanzu ne na san alak’ar Meema da Dr ba kamar yadda Dr ya fad’a min cewa yarinyar abokin baban su ce, kenan bayan wannan har da alak’ar soyayya a tsananin su, no wonder shi yasa take min abinda ta gadama, ashe kishi ne ke damun ta da kuma takaicin Dr bai aure ta ba.


"Amma me yasa Dr bai fad’a min alak’ar su ba, dan me zai ‘boye min tsakanin su, me yasa bai aure ta ba?" duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan Dr ne ya kamata ya amsa min.


Duk da kishin da ya turnik’e ni, ban bari Meema ta gani a fuska ta ba.


Murmushin yak’e nayi na ce "wannan matsalar ki ce Meema, ko k’aruna ne Dad d’in ki k’arewar kud’i ba matsala ta ba ce dan ban ta’ba zuwa gidan ku maula ba bare ki goranta min, kuma me shi bay a fad’a sai dai a gani a jikin shi, kin san akwai masu kud’i, akwai muna masu kud’i, kin ga kenan za ki iya banbance a jerin da kuke, maganar alak’ar ki da Dr a da ba damuwa ta bace dan yanzu ni ce a matsayin matar shi, sai nayi niyyar bashi izini sannan zai k’ara, kin ga na zama zarah a cikin taurari, ba irin ki ba da ba ki kai matsayin da za a sa ki a jerin mata ba tun da har kika sa nuna kissar ki irin ta mata Dr ya aure ki".


Tun san da muka fara musayar yawu da Meema, ba wanda yayi magana a cikin su Hanan da Farida, sai wannan karan ne Hanan ta sa bakin ta da cewa "Anty Zarah, bai kamata ki dinga fad’a ma Meema wa’innan maganganun ba, ita ma matsayin k’anwa take a gurin yaya Sadik, Allah ne bai nufa za su yi aure ba, da tana nan a matsayin matar shi".


"Ya ishe ki Hanan, kar ki k’ara sa min bakin a cikin maganar nan, ki bari wacce nake yi dominta ta bani amsa da bakin ta, dan daman nasan bayan ta za ki bi" na fad’a cikin ‘bacin rai.


Yatsina fuska Hanan tayi kanata ce "Dole in fad’i gaskiya in ya zama dole a fad’e ta".


A yanzu ban da lokacin kula Hanan, na fi so in fara maganin Meema dan ita ce take so ta shiga harka ta, so nake in nuna mata nima ba kanwar lasa ba ce.


Da alama na fara samun nasara akan Meema, dan tun da na bata amsar maganar da ta min take huci, a yanayin ta so take yi muyi wacce za muyi, nima kuma a shirye nake da duk wani abin da take ji dashi.


Juyowar da zan yi dan mu ci gaba daga inda muka tsaya da Meema, ba zato naji saukar mari a fuskata.


Meema ce ashe ta taso tazo in da nake lokacin da na juya ina ma Hanan magana.


Cikin huci ta ce "Ke har kin isa ki fad’a min magana in k’yale ki, nawa kike, wanda suka fi ki ma basu isa bare ke, ke ko kallon banza mutum ya min sai yasan ya ta’bo ne bare ke har da zaki bud’e rubbush mouth d’in ki kina fad’a min maganar da tazo bakin ki, ina so in yi warning d’in ki, daga rana mai kamar ta yau, in har kika k’ara bud’ar bakin ki kika fad’a min maganar da ba ta min ba sai kin gane kuren ki, ke ko kallon banza kika min ranar sai kin yi danasani, ki rubuta ki ajiye sai na nuna miki yaya Sadik nawa ne, sai na aure shi….".


Kan ta gama maganar da take yi ni tsinka mata kyawawan mari guda biyu wanda suka fi wanda ta min zafi.


A yadda re-action d’in ta da tayi ya nuna marin ya shige ta dan har dafe kuncin ta tayi.


Hannu ta d’aga da niyyar kai min wani marin, nayi saurin sa hannuna na rik’e hanun ta na watsar.


"Kin yi kuskure Meema da kike tunanin in kika mare ni kamar kin ci bulus, ko a yanzu hannun ki yakai kan fuskata sai na miki mafiyin shi, in kuma kina musu ki gwada ki gani yadda za mu kwashi ‘yan kallo dake, ni da kike gani ba na barin ta kwana, ina k’yale ki ne dan darajar Dr da kuma matsayin kin girme ni, tun da na lura shekarun naki basu da amfani ki da komai ba sai koma baya da ya haifar miki, to ni kuma zan taka girma" na fad'a.


Farida ce ta tashi tana bani hak’uri akan in yi shiru in k’yale Meema.


Ganin yadda Farida ke bani hak’uri ne yasa na yi hanyar kitchen dan ni sai yanzu na tuna da abin da na d’aura.


Ina cikin kitchen d’in ina jiyo maganganun da suke yi.


Wani dogon tsak’i Hanan tayi kana ta ce "Ke dai Farida banza ce, kina kallo ta mari Meema, ban da maganganun da ta fad’a ma ta, shine har da ba ta hak’uri, maimakon ki ba ma ita Meeman hak’uri akan zarafin ta da Anty Zarah taci mata, shine kike ba ma ita Anty Zarah hak’uri dan neman gindin zama".


Meema ce ta k’ar’bi zancen cikin masifa ta ce "Ki k’yale ta Hanan, na lura daman ita Farida tana bayan Zarah ne, sam Farida ba ta kishi na".


Maida kallonta tayi ga Hanan ta ce " Can you imagine Hanan, wai ni yarinyar nan ta d’aga hannu ta mara, sai tayi danasanin marin da ta min, zan koya mata hankali".


Hanan ce ta watsa mata harara ta ce "too late Meema, ai kin bani haushi da kika tsaya ta mare ki har two times ba tare da kin yi d’auki mataki ba, yanzu sai dai ki yi hak’uri kawai dan tayi winning akan ki".


Farida ce ta ce " Abin da kuke yi bai kamata ba, in maganar gaskiya tazo a fad’a, Anty Meema you a the one that start causing this fighting, abin da yasa kika ji haushi dan ta rama abin da kika mata ne, kuma ni ban ga laifin ta ba, dan ko ni aka yi ma haka matakin da zan d’auka kenan".


Gaba d’ayan su suka taso mata wai daman sun san baya na za ta bi.


Meema ce ta ce su taso su tafi gida.


Tashi suka yi suka fita daga falon ba tare da sun min sallama ba.


Farida ce ta shigo kitchen d’in ta min sallama.

[8/24, 22:20] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*



*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽


www.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa Writers Association





*HAPPY EID-EL KABIR*

_Ina ma d’aukacin musulmai da fans d’ina barka da sallah_.

_Allah muke rok’o ya maimata mana, yasa muna da rabon ganin na wata shekarar_.

_‘yar mutan Paki na k’ara muku barka da sallah_.

_Tak’abbalal lahu minna wa minkum_





83-84


Ina jin tashin motar su na ja d’an k’aramin tsaki, takaicin Meema ne ya bi ya dame ni, nasan a yanzu za ta ji shakkar k’ara shiga gona ta tun da muka yi haka da ita.


Jiran Dr kawai nake yi ya zo ya k’ara min bayanin Meema kamar yadda ya ‘boye min alak’ar su a baya, sai a yanzu da nake ji a bakin Hanan da Meema cewa akwai alak'ar soyayya a tsakanin su a da wacce ban san da ita ba.


Shi kanshi haushin Dr d’in nake yi akan yadda ya ‘boye min alak’ar shi da Meema.


Da haka na k’arasa girkin na fito kitchen na wuce d’aki na.


Su Meema kuwa tun a hanyar su ta dawowa gida su da Meema da Hanan suke maganganun su akan abin da ya faru a gida na da suka zo, ita dai Farida kallon su take yi dan tasan in ta sa bakin ta fad’an kan ta zai dawo.


Har suka k’arasa gida ba su daina maganar da suke yi ba a kaina.


Momi suka samu a falo sanye da medicated glass a fuskar ta tana karanta jarida.


Suna shiga falon Meema ta fad’a jikin Momi ta fara kuka.


Hankalin Momi ne ya tashi ganin yadda Meema ke kuka.


Tambayar su tayi me ya sami Meema take kuka.


Hanan ce ta kwashe komai ta fad’a ma Momi abin da ya faru a tsakanin mu da Meema.


Ran Momi ne ya ‘baci jin cewa na mari Meema.


Wayarta ta d’akko ta kira Dr akan in ya tashi daga aiki yazo tana son ganin shi.


Dr yana tashi daga aiki ya wuto gidan su.


Samun su yayi a falo suna kallo, bayan sun gaisa ne ya tamaye su ina Momi.


Fad’a masa suka yi tana d’akin ta.


K’arasa wa d’akin ta yayi ya same ta resting chair, gaban ta kayan marmari ne a ajiye akan d’an k’aramin centre table tana ci.


Sallama yayi ya nemi kusa da ita ya zauna.


"Sannu da hutawa Momi" Dr ya fad’a.


"yawwa" ta amsa mishi a tak’aice.


Ci gaba tayi da cin fruit d’in ta ba tare da tayi magana ba.


Kau da shirun yayi da cewa "Momi gani, naji kin kira ni a waya ki na nema na".


Sai a lokacin ta maida hankalin shi gare ta tace " Magana nake so muyi akan matar ka".


Kallon ta yayi yana jiran jin mai za ta ce a kaina.


"Sadik!" Momi ta kira sunan shi.


"Na’am Momi" ya amsa mata.


Momi ce ta fara da cewa "Sadik tun farko na nuna maka sha’awar auran Meema amma ka ce kai sai Zarah kake so, ka fara kawo wasu hujjoji wanda ban gamsu dasu ba akan Meema da ka bayar, ban sani ba ko ita Zarah tafi saura mata ne da ka dage sai ita oho, let me go straight to the point in fad’a maka dalilin da yasa na kira ka, yau su Meema sun je gidan ka, matar ka ba ta ji kunyar kowa ba ta mari Meema, sannan daga Hanan ta yi mata magana ta fara mata fad’a, so ina so ka ja ma matar kunne akan ta fita harkar Meema, in ban da ka k’i ta da ita za ta zama matar ka, sannan kar ta k’ara kuskuren yi ma yara na fad’a dan ka san ko ni ba na matsa musu".


Tun da Momi ta fara magana yayi shiru yana sauraren ta, dalilin da yasa na mari Meema yake yi, gashi yanzu Momi sai fad’a take yi, shima kan shi bai ji dad’in abin da nayi ba duk da bai san abin da ya had'a ni da Meema ba.


"Amma Momi me ya had’a su da Meemam har ta mare ta" Dr ya tambayi Momi.


Momi ce ta bashi amsa da cewa "Just akan ita Zarah ta kunna Tv tana kallo, so shine Meema ta d’au remote ta canza da ta ga Zarah ta bar falon, shine ita Zarah da ta dawo wai ta fara fad’a musu magana akan canza channel d’in da Meema tayi, har ta nace mata kayan ta ne, in suna so su nuna iko ne su je can side d’in ka, duk wannan bai ishe ta ba har da sa parent d’in Meema a ciki".


Jin bayanin da Momi ta mishi ya k’ara ‘bata mishi rai, for what reason dan k’annen shi sun je gidan shi zan neme su da rigima, ba zai ti tolerating d’in abin da nayi ba.


"Ki yi hak’uri Momi, zan mata magana in na koma, I d’ont expect that a gurin Zarah, zan d’au mataki akai".


"That’s better" Momi ta fad’a.


Canza akalar hirar Dr yayi, dan yasan Momi abu kad’an take jira ta fad’i aibu na tun da Dr ya k’i auran Meema.


A nan Dr ya ci abincin dare, sai da yayi isha’i sannan ya bar gidan.


Ranar Dr bai dawo da wuri ba sai wajejen bayan sallar isha’i sannan ya shigo gidan.


Ina zaune a falo ina pressing d’in waya ta ya shigo da sallama, amsa mishi nayi kana na mishi sannu da zuwa, fuskar shi ba yabo ba fallasa, ya amsa min.


Nima yadda na ke jin haushin shi yasa na k’ara d’aure fuska ta ba tare da na k’ara mishi magana ba.


Side d’in shi ya wuce yayi wanka kana ya canza shigar shi cikin k’ananun kaya ya dawo side d’ina.


Kujerar da ke kallo na ya zo ya zauna yana kallo na ba tare da ya min magana ba.


"Dr ga abincin can a dinning, mu je in yi serving d’in ka, ko in kawo maka nan ne".


"Ki bar shi na ci a gurin Momi" cewar Dr.


Shiru nayi ban ce komai ba, sai ma ci gaba da pressing d’in waya ta da nake yi.


"Zarah! Dr ya kira suna na.


D’agowa nayi na kalle shi jin yanda ya kira suna na nace "Na’am Dr".


Cikin d’aurewar fuska ya ce "Akan wani dalili yasa ki ka mari Meema har ki ka sako parent d’in ta a ciki, sannan dan Hanan ta miki magana ita ma kika had’a da ita, ba ki san Meema ta girme ki ba, ko da a ce ba ta girme ki ba ya kamata a ce ta ci daraja ta ko me ta miki, duk abin da ta miki ba sai ki bari in na dawo ba sai ki fad’a min in d’au mataki amma sai ki zauna ki na fad’a mata bak’ak’en maganganu, Zarah ba na son rigima, ba na so tun yanzu ki fara samun matsala da family na".


Raina ne ya k’ara ‘baci da irin yadda ya je gidan su aka fad’a mishi gaskiya da k’arya kuma ya d’auka ba tare da ya ji ta baki na ba, ya tasa ni a gaba sai fad’a yake min ba tare da ya ji nawa bayanin ba.


Shiru na mishi duk da yadda raina yake a ‘bace na daure ban mishi magana ba har ya gama fad’an shi.


"Zahra kina ji ina miki magana shine kika min shiru, ko ke ba za ki yi laifi a miki fad’a ba" Dr ya fad’a cikin fushi.


Cikin ‘bacin rai na ce "Me kake so in ce Dr, ina ganin duk abin da zan fad’a an riga an fad’a maka shi kuma ka yarda, ka ga kenan bayani na bai da wani amfani a gurin ka, in da hukuncin gaskiya ka ke so ka yanke ai sai nima ka tambaye ni abin da ya had’a ni da Meeman har na mare ta, amma da yake abin son kai ne ka yarda da maganar da k’annen ka suka fad’a maka akan abin da ya had'a ni da Meema".


Wannan karan a hankali ya min magana ya ce "Me ya had’a ku da Meeman?".


Kallon shi nayi na ce "Abin da suka fad’a maka shi ya had’a ni da ita, duk abubuwan da Meema take min ban ta’ba kai k’arar ta gurin ka ba saboda rugudun rigima, yanzu ga shi su sun fad'a maka ka yarda da maganar su, ni da ban da Wanda zai tare min ai sai dai in yi hak'uri da abin da suka fad'a maka".


Ci gaba nayi da cewa " Ni ba ruwa na da girman ta tun da ita Meema ba ta ja girman ta ba..".


Dr ne ya katse ni da cewa "Ya isa haka Zarah, plss ki dinga hak’uri da abin da Meema za ta miki, ba na son hayaniya".


"A kan me zan yi hak’uri da ita ban da wanda nayi a farko, ko da yake ban ga laifin ka ba dan ka ce in yi hak’uri da ita tun da akwai alak’ar soyayya a tsakanin ku a da wanda ba ka fad’a min ba, sai a yau da nake ji a bakin su" Na k’arasa maganar ina jiran jin mai zai ce min.


Shiru yayi bai ce min komai ba, sai ma bi na da ido da yake yi.


Ci gaba nayi da cewa "Dr me yasa ka ‘boye min alak’ar ka da Meema bayan kasan duk daren dad’ewa zan ji mai ke tsakanin ku, shi yasa tun a farko nake tunanin wani irin laifi nayi ma Meema da take nema na da tashin hankali, ashe ni ce ban san abin da yake tafiya ba, soyayya ce a tsakanin ku a da wacce har ta so ta kai ku ga yin aure, Allah ne bai nufa ba, why Dr?".


A wannan lokacin cikin lallashi yayi min magana da cewa "Zarah don’t put that in your mind akan tsakani ni na da Meema, kamar yadda na fad’a miki a baya cewa Meema yarinyar abokin Dad d’in mu ce, akwai aminci tsakanin su, ni ban d’auki Meema a matsayin lover d’i ta ba, na d’auke ta ne a matsayin sister d’ita kamar yadda na d’auki su Hanan, though akwai shak’uwa a tsakanin mu, Meema ita take so na, bai kamata ki ga laifi na ba dan ban fad’a miki wannan maganar ba, dan ni ban d’auke ta mai mahimmanci a guri na ba shi yasa ban fad'a miki ita ba, I hope kin gamsu da bayanin da nayi miki" ya k’arasa maganar yana jefo min shu’umin kallo da yake sanyayar min da jiki.


Wani irin dad’i ne ya ziyarce ni a lokacin jin cewa shi Meema ita take son Dr, ba shi yake son ta ba, amma duk da haka ban gama samun natsuwa a zuciya ta ba in dai har Meema su na tare da Dr, nasan za ta iya yin duk wani dubarar ta taga ta jawo hankalin shi ya yarda ya aure ta, wannan shine babban fargaba ta.


Tunano kalamen ta nayi na d’azun da take ce min Dr na ta ne, sai ta aure shi, ban san me Meema take nufi da wa’innan kalamen ta ba, gashi dai Dr ya min bayanin cewa ita take son shi ba shi yake son ta ba, menene ribar ta in ta aure shi bayan ta san ba son ta yake yi ba?.


In har maganar da Meema ta fad’a akan sai ta auri Dr hakan yake a ranta ban san wani hali zan shiga ba nan gaba.


Ban san lokacin da Dr ya taso ya dawo kusa dani ya zauna ba.


Jin shi nayi ya tallabo fuska ta yana jefa min kallon da ke dawo dani cikin natsuwa ta.


Cikin cool voice d’in shi ya ce "Zarah stop bordering your self, ba na so ki ci gaba da sa tunanin Meema a ranki, daga yanzu in har ta miki wani abun in na dawo ki fad’a min kin ji, ba na so ki na biye mata kuna samun misunderstanding a tsakanin ku, ina fatan kin fahimta".


Murmushi na sakar mishi kana na ce "Na fahimce ka Dr, insha Allahu zan kiyaye".


Shima murmushin ya mayar min ya ce " That’s what i want to hear from you".


Cikin ‘yan mintuna sai gashi na daina jin haushin Dr, daman nasan har da kishi da yake damu na.


A ranar sai da Dr ya koyar dani wani darasi a babin soyayya irin ta ma’aurata da suka damu da junan su.



Tun bayar rigimar da muka yi da Meema, ban k’ara shiga harkar ta ba, duk yadda ta so in biye mata ba na kula ta, ita ma na lura a yanzu tana shakkar nema na da rigima, hakan yasa na k’udurta cewa zan danne duk abin da za ta min, dan ba na so in yi abin da zai ‘bata ma Dr rai.



******************************

A kwana a tashi ba wuya ga mai yawan rai.


Sai gashi har na kammala HND d’ina nayi service.


Har a wannan lokacin ba ni da ciki, a yadda na lura shi Dr hankalin shi bai tashi ba da rashin cikin da ban samu ba.


Ni kuwa hankali na ne ya kasa kwanciya ganin ina neman shekara uku da aure amma har yanzu ban samu ciki ba.


Gashi har Anisa ta haifi yarinyar ta mace wacce ta ci suna Amatur-Rahman.


A ‘yan kwanakin sai na fara jin canje-canje a jiki na, zazza’bi da yawan kasala da ke damu na, ga wani fari da na k’ara yi.




Yau muna kwance ni da Dr a gado, gani nayi ya tashi ya kunna bulb ya dawo ya zauna kusa dani yana kallo na.


Hure mishi ido nayi na ce "Dr lafiya wannan kallon kuwa".


"Ba komai, na ga wasu changes ne a jikin ki, na ga kuma kin k’ara min kyau da fari" Dr ya fad’a yana kanne min ido.


K’ayataccen murmushi na sakar mishi kana na ce "Ni kaina Dr na rasa me yake damu na a ‘yan kwanakin nan, fever da kasala ke damu na, sannan ga haske da da na k’ara yi, ina jink o har da rashin lafiyar da nake yi ne yasa na k’ara haske oho".


Tun da na fara maganar nan Dr ke bi na ido bai ce min komai ba har sai da na gama magana sannan ya d’aura da cewa "Zarah me yasa ba ki fad’a min ba ki da lafiya ba?".


Marairaicewa nayi na kwanta a kafad’ar shi na ce " Yawanci sai ka tafi aiki nake jin zazza’bin da kasala, kan yamma sai ka ga na koma normal, shi yasa ban fad’a maka ba".


"Bayan nan ba in da yake miki ciwo?" Dr ya tambaye ni.


Shiru nayi kamar mai tunani kana na amsa mishi da cewa "Gaskiya babu, sai dai wani lokacin ina yin amai".


Hannu na ya rik’e ya kalla kana ya maida kallon shi gare ni.


"Yaushe rabon ki da ganin period d’in ki" Dr

Please Login or Register in order to submit comment