Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cewa "wai yaya Khalil ban fa gane bane?"

Murmushi yayi yace "da aka yi me sister?"

"To na ga sai hira kuke yi k’asa-k’asa ba ku sa ni a ciki ba"

Anisa ce tace "To ke Fatima tun da kika ga muna Magana a hankali ai ba a so ki ji zancen ne" ta k’arasa maganar tana murmushi.

Cikin shagwa’ba nace "Yaya Khalil na ga so kuke ku had’e min kai da Anisa, in zama ni kad’ai"

"Mu mun isa mu had’e miki kai, ke da kike da babban yaya soja" ya fad’a da alamar tsokana.

Gintse fuska ta nayi saboda nasan yanzu yaya Khalil zai samu hanyar ci gaba da tsokana ta.

Hirar mu muka ci gaba da yi cikin wasa da dariya har muka k’arasa unguwar su Anisa muka sauke ta kana muka nufi gida.

Da daddare ina kwance a d’aki ina chating da friends d’ina naga wata sabuwar number an min Magana da ita.

"Assalamu alaikum" abin da na ga an turo min.

"wa alaikumus salam’ na tura reply.

"Kin gane da wanda kike Magana? aka sake turo min.

Reply na tura da cewa "ban gane ba gaskiya"

Ki na Magana da Bregadier Umar Yusuf, yanzu ina fatan kin gane".

Sai a lokacin na gane yaya Faruk ne, saboda ba da ordinary numban shi yake chat ba.

"Oh yaya Faruk, sai yanzu na gane ka"

"good, ya studies? ya tambaye ni.

Amsa mishi nayi da cewa "karatu lafiya lau, ya aiki?

"Aiki Alhamdulillah, yanzu ma muna shirye shiryen tafiya Adamawa ne wani aiki, a taya mu da addu’a".

"To yaya Allah ya taimaka"

"Amin".

"Bari in bar ki haka ki huta tun da gobe ki na da lectures, ki kashe data d’in ki dare ya fara yi".

Ba a lokacin nayi niyar sauka ba, saboda a group d’in mu na Statistics class rep d’in mu ya turo man da working d’in da function & geometry ya ba mu, ganin yadda yau ya min Magana ba tare da fad’a ba yasa na tura mishi reply
"Ok yaya, yanzu zan sauka".

"that is good, good night & have a sweet dream" abin da ya turo min kenan ya kasha data d’in shi.

Ni ma kashe data na nayi ina mamakin yadda yaya Faruk yau ya zauna yana chating da ni, yanzu kam na yarda yaya Faruk yana so mu fara shiri dashi.

But ban san me yasa na kasa samun peace of mind akan yaya Faruk ba, duk da ko a da d’in ba wai yana min wani abu ne da zai sa in tsane shi ba, sai dai fad’an da purnishment d’in da yake mana ne yasa nake jin haushin shi wanda nake ganin kamar ya tsane ni ne, amma zan yi k’ok’arin in ga na sake dashi a matsayin yaya d’an uwa na kuma yaya na.

Da wannan tunanin na kwanta barci.

A can ‘bangaren yaya Faruk kuwa, tun da ya gama waya da Teeman shi yaji wani farin ciki ya lullu’be shi, yanzu dai gashi ba wata hira suka yi irin ta masoya ba amma ya tsinci kanshi da jin dad’in haka, wai a hakan ma dan bai ji sirrin zuciyar ita Teeman ba, kenan idan ta amice dashi zai tsinci kanshi ne a birnin masoya wand aba kowa ne ke tsintar kanshi a ciki ba sai wanda suka aminta da junan su, in ko haka ne zai ci gaba da addu’ar Allah ya mallaka mishi Fatima saboda ita ce Farin cikin shi.

Zai k’ara ba ta time kan ya tuntu’be ta akan ra’ayin ta game dashi.

Da wannan tunanin barci ya d’auke shi.

Tafiyar su yaya Faruk ta rage yau saura kwana biyu, kiran su aka yi a waya da akwai meeting da su Bregadier General da su Major General za ayi akan tafiyar, ko da suka halarci meeting d’in, an fad’a musu cewar an d’aga tafiyar ne zuwa next week sabida wasu dalilai.

Da wannan damar yaya Faruk ya nemi permission akan yana so yaje Kaduna yayi 2 days.
Sallama yayi Ma Mus’ab ya kamo hanyar zuwa Kaduna.

Yana sauka ya shiga side d’in Momi ya gaishe ta, bayan sun gaisa ne take tambayar sa ba su yi tafiyar bane ta ganshi unexpected.

Sanar da ita yayi an d’aga tafiyar zuwa next week, shi yasa yayi deciding d’in zuwa yayi 2 days a nan.

Momi ta ji dad’in haka saboda tasan yaya Faruk mutum ne mai son iyayen shi da ‘yan uwan shi.

Tashi yayi ya nufi side d’in shi ya watsa ruwa, fito wa yayi ya sami Anisa a falo tana karanta handout d’in ta, a gefen ta wani exercise book ne ta take jotting.

Dad’i ne ya kama Anisa ganin ya kwana biyu bai zo ba, ba ta yi tsammanin ganin shi a wannan lokacin ba tun da Momi ta fad’a mata za su yi tafiya.

Da fara’a tace "yaya sannu da zuwa".

"yawwa Anisa, ya karatu".

"Lfy lau yaya Faruk, amma gaskiya yaya karatun Polythecnic akwai wuya, gashi exam is approaching".

Murmushi yayi yace "Anisa ko wani karatu da kike gani yana da wuyar shi both polythecnic & University, sai dai d’an banbabcin da ba za a rasa ba, ki dage sosai dan ki fito da grade mai kyau".

"zan dage insha Allah".

"yawwa my Sis".

Jefi-jefi suka ci gaba da hirar, a gurin Anisa kuwa tana jin dad’in yadda yanzu yaya Faruk yake jan su a jiki ita da Fatima, ita ma ta na so ta ga yaya Faruk yana jan ta a jiki kamar yadda yaya Khalil ke jan su.

Momi ce ta fito daga side d’inta ta k’araso falon ta zauna.

Hira suka ci gaba da yi irin na happy Family, a ran Momi kuwa dad’i ne ya kama ta ganin yadda yaya Faruk ya fara rage miskilancin sa.

Kasancewar yau ranar asabar, ba mu da lectures, hakan yasa na tashi da marmarin cin samosa da spring roll.

Kitchen na shiga na duba dan in ga ko akwai duka kayan da nake buk’ata, samu nayi da akwai kayan had’in da zan buk’ata.

Iya talatu na kira ta taya ni yanka cabbage da karas, ni kuma na ci gaba da sauran aikin,
Saboda yadda yake da cin time, sai da na d’au lokaci kan na gama, ina gama wa na had’a ginger amma ban cika cittar ba saboda ka da yayi yaji sosai.

Ina fito wa falon na tarar da su Abbu da Ummu da yaya Khalil da kuma yaya Faruk suna hira.

Ja nayi na tsaya kamar wadda aka rik’e a gurin, ban yi zaton zuwan yaya Faruk a wannan lokacin ba.

Yanzu idan ya turke ni akan in fad’a mishi matsayin shi a guri na, me zan ce mai? Ni kaina nasan ban da wannan amsar, da wannan tunanin na k’araso falo na nemi guri na zauna.

Tun da na zauna yaya Faruk ya tsare ni da kallon shi wanda hakan yasa na tsargu.

Gaishe shi nayi na mik’e na shiga kitchen na zubowa kowa a plate da wannan ginger wanda yayi sanyi a fridge.

Ina lura da yaya Faruk da yana cin Samosa har wani lumshe ido yake yi, ko dad’i ya mai ne ban sani ba, ko da yake na lura lumshe ido a gurin shi kamar nature d’in shi ne.

Mik’ewa nayi ganin time d’in zuwa islamiyya ya kusa duk da mun nemi excuse a makarantar ba kullum za mu dinga zuwa ba, saboda yanxu mun fara d’aukar lectures, ran sati da lahadi kad’ai Mu ke zuwa.

Shiryawa nayi cikin Uniform d’ina, ina sa bak'ar socks ne naji waya ta tayi ringing.

Sunan yaya Faruk na gani a jikin screen d’in yana yawo.

Sai da na d’an yi jim kafin na d’auka saboda ban san me zai ce min ba.

Sallama na yi bayan na d’auka, amsa min yayi kana yace "me kike yi ne ban ga kin dawo falo ba?

"Ina shiryawa ne, time d’in makaranta ne yayi".

"Ok har yau dama kuna zuwa ne? ya tambaya.

"Eh muna zuwa, amma ran weekend kad’ai muke zuwa".

"Hakan na da kyau, in kin gama ki fito in kai ki, ina waje".

Amsa mishi na yi da "Toh".

Ba haka na so ba, nasan in dai na shiga motar shi sai ya tambaye ni a inda muka kwana akan tayin soyayya shi wanda har yanzu na rasa me yasa na kasa samun mafita.

Gun Ummu naje na fad’a mata cewa yaya Faruk ne zai kai ni.

Kujera mai zaman banza na zauna, ina wasa da ‘yan yatsu na.

Mun fara tafiya ne ya fara tambaya na game da karatuna, ina bashi amsa.

cikin wasa yace ‘yan k’idaya kenan, kuna fama, dan naji an ce ku lissafin naku har motoci sai a saku ku k’irga sannan ku fitar da data saboda tsananin lissafi, in na samu time zan zo in kai ki barrack d’in mu ki k’irga mun yawan mutanen da ke shiga da fita".

Dariya tayi tace "haba yaya Faruk, ina zan iya tsayawa k’irga motoci sai kace wata injin".

"Gaskiya course d’in ku nasan akwai wuya amma ki dage, course d’in ku yana da amfani a ko ina, infact ku professional ne da ko ba aiki za a neme ku a ko ina, ko wani course da kike gani yana da challenges d’in shi, in ka mai da hankali, sai ki ga kin yi achieving goal d’in ki".

"na gode yaya Faruk da shawarwarin ka".

K’asaitaccen murmurshi yayi yace "Kar ki damu Teemah, you are my sister, it is my responsibility to give you advice at any time".

Har raina naji dad’in shawarar da yaya Faruk ya bani, yanzu na k’ara yadda da zancen yaya Khalil da yake cewa yaya Faruk mutum ne mai dadin zama in ka fahimce shi, gaskiya a kwanakin nan ina jin dad’in yadda yake sake wa da mu.

Ko da mu ka k’arasa gidan su Anisa, cewa yayi in yi sauri in shiga in kira ta, ba ya son jira.

Sanin halin shi yasa ina shiga na tarar da Momi da k’awarta suna duba kayan da Momi ta saro, da fara’ar ta muka gaisa kana na gaishe da k’awar ta, bayan mun gaisa ne nake tambayar ta
"Momi ina Anisa take?".

"Tana d’aki, ina ganin ta shirya, ki shiga ki gani".

D’akin na shiga na sameta ta shirya, ta tsaya sa powder.

Hararar wasa na mata nace "ke matsalar ki cin time a gurin make up".

"kin san Make up na son natsuwa, shi yasa nake tsayawa in yi shi a tsanake".

"yanzu dai ba wannan ba, yau ba yaya Khalil bane ko Driver zai kaimu bare ki ‘bata musu time".

Ci gaba tayi da Make up d’in ta tana cewa "To waye zai kai mu?


"yaya Faruk ne zai kaimu, kin san kuwa ba ya son jira, kuma ke da zaki sa nik’ab, wani make up zaki tsaya yi"

Anisa ba tayi wani mamaki ba, ta san yanzu yaya Faruk is a change person, ba abin mamaki ne dan yace zai kai su Makaranta.

Tasan duk canzawar shi ba zai hana in ka mishi laifi ya zartar maka da hukunci ba, tasan yaya Faruk bai son jira dan ba ta manta da purnishment d’in da y aba ta ba kwanaki na filling d’in ruwa da k’aramin cup ba.

Cikin sauri ta d’aura nik’ab d’in ta fito muka nufi motar shi.

Wannan karan miskilanci ya motsa, tun da muka shiga motar ya kunna wa’azin Sheikh Yahaya Haifan yana saurare, mai taken Tsantseni, gaskiya ko ni da nkae sauraren wa’azin jiki na ne yayi sanyi saboda yadda Malamin ya kawo bayanai akan Tsantseni a rayuwar d’an adam, tambayar da nayi wa kaina a yanzu mutane nawa ne masu Tsantseni a duniyar nan, ko za a samu k’adan ne.
Addu’a kawai nake yi akan Allah yasa mu dace, ya kuma ba mu ikon yin tsantseni akan duniya.

Sauke mu yayi a wajen makaranta ya juya ya tafi.

Ko da aka tashi ga Mamakin mu, shine yazo d’aukan mu.

Lallai mun zama ‘yan gatan yaya Faruk kamar yadda yaya Khalil yake tsokanar mu.

Wannan karan a mota ya ja mu da hira amma ba mai tsawo ba, tun da shi ba ma’abocin surutu bane.

Sai da ya fara sauke Anisa a gida, sannan ya nufi gida da ni.

Kallo na yayi yace "Teemah Samosan da kika yi da Spring roll ya min dad’i, in ba damuwa za ki min gobe in nazo?" ya tambaye ni.

Duk da procedure d’in yin su Samosa da Spring roll yana da wuya, hakan ba zai hana in mishi ba, dan gaskiya nima yanzu na fara jin dad’in zama dashi.

"Ok ba matsala, zuwa gobe insha Allah zan maka".

Murmushi yayi yace "ki barshi wasa nake miki, amma in zan tafi sai ki min".

"Lalacewa zai yi, sai dai in ran da zaka tafi in yi in ajiye a fridge, in yaso in kaje can ka soya"

"Zan ba Maryam ta soya min in na koma, ni ina zan wani iya soya wa"

A raina kuwa tambayar wacece Maryam nake yi, dan ba na tunanin abokiyar aikin shi ce.

Kamar yasan abin da yake raina yace

"Nasan zaki ji nace Maryam, matar aboki na ne Mus’ab, da muke Barrack d’aya"

Shiru nayi ban ce mai komai ba tun da ba tambayar shi nayi ya min bayanin wacece ita ba, sun fi kusa koma wacece.

Da haka muka k’arasa gida, ya ajiye ni a bakin gate ya juya motar shi ya tafi.
[4/16, 12:31] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga duk wanda yake cikin wata jarabta ko cikin wani hali*

*Allah 🙏🏽🙏🏽🙏🏽na yi tawassali da sunayen ka da kyawawan ayukan mu, ka kawo mana mafita a al’amuran mu, ka bamu ikon cin dukkan jarabawar da ka mana*.

*Alllah dan sunayen ka tsarkakakku, ya ubangijin Sammai da k’assai, ya Ubangijin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (s.a.w) Allah ka bi ya mana buk’atun mu na alkhairi*
🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽

_Plsss fans ina barar addu’ar ku akan wasu buk’atu nawa, Allah ya amsa min da sauran ‘yan uwan musulmai baki d’aya_



*Question of the Day*

_A cikin matan manzon Allah s.a.w, wacece ta lurar da manzon Allah (s.a.w) game da wata dabara da zai jawo hankalin sahabban sa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar taci nasara sosai_
_Menene cikakken sunan ta?_




43&44

Bayan na shiga d’aki ne, hirar da muka yi da yaya Faruk a cikin mota da kuma shawarwarin da ya din ga bani game da karatu ya dinga fad’o min a rai.

A yanzu na sa a raina da cewa yaya Faruk ya samu wani matsayi a raina ta ‘bangaren zumunci, wata zuciyar kuma ta na ce min mai zai hana in bashi matsayin da yafi dacewa shine in amince da soyayyar shi, me yasa har yanzu zuciya ta ba ta anshi tayin shi ba?

Wata zuciyar tawa kuwa shawara ta ba ni akan mu ci gaba da zumunci irin na ‘yan uwantaka.

Da wannan sark’ak’en tunanin na tashi na nufi d’akin Ummu.


Washegari ina zaune a falo, ina karanta wani online novel a cikin waya mai suna *Rayuwar yusra da Afshan*, wanda Maryam Ahmad Paki ta rubuta, labarin yayi touching d’ina na yadda soyayya ta canza ma Afshan hali, duk a dalilin soyayyar Muhsin da ta fad’a kuma mijin Yusra wacce ta rik’e ta kamar ‘yar uwarta ta jini, ba ta saka mata da komai ba sai soyayya da Mijin Yusra wanda take son shi kamar ranta, ko yaya labarin zai kasance a k’arshe? Gaskiya na yadda da marubuciyar da tace labarin Soyayya mai rud’ani da tausayi a cikin novel d’in, Shine na k’osa na ji k’arshen labarin.

Sallamar yaya Faruk ne ya katse min karatun da nake yi.

Amsa masa sallamar nayi da sassanyar murmushi na.

Kusa dani yazo ya zauna, yana min kallon gefen ido.

"yaya ina wuni" na gaishe shi.

"lfy amma ba lau". ya amsa min

Kallon shi nayi jin amsar da ya ba ni, a yanayin shi ban ga wani abu da yake damun shi ba.

Shiru na yi ban k’ara cewa komai ba.

Wani tsadadden murmushi yayi kana yace "Teemah ba ki tambaye ni me ya same ni".

"yaya ai ni ban ga alamar ba ka da lafiya ba, na gan ka normal ne".

Kallo na yayi sannan yace "Teemah, ni ko ke rashin lafiya?".

Da sauri nace "Me yake damun ka?" Na fad’a da alamar tausayi.

K’asaitaccen murmushi yayi yace "Ba irin ciwon da kike tunani bane, wannan daban ne, kuma ke ce maganin ciwon nawa".

Gaba na ne ya fad’i, sai yanzu na gane mai yaya Faruk yake nufi, yana so ya d’akko min maganar da muka yi kwanaki ne akan amsar tayin soyayyar shi.

Yanzu in ya tambaye ni mai zan ce mai? Gaskiya bazan iya fito wa direct in ce mai ban yi na’am dashi ba duk da matsayin da na ba shi a guri na.

Katse min zancen zucin da nake yi yace "Teemah!"

nasan kin gane me na ke nufi, ba komai ke damu na ba illah fama da ciwon son ki da ya min dabaibayi a zuciya ta wanda har yanzu ban san matsayi na a gurin ki ba, ina so ki bani amsa ta Teemah, dan zuciyata ta samu peace of mind".

"An zo gurin".abin da na fad’a a raina kenan.

Zuciya ta ce ke kai kawon me zan ce ma yaya Faruk a yanzu da zai yadda da hujja ta, dubara d’aya ce ta fad’o min akan in lalla’ba shi mu rabu lafiya.

"yaya Faruk, kai ma kasa ba zan k’i ka ba, ko dan darajar ‘yan uwantaka dake tsakanin mu, ko a da damu ke samin misunderstanding rashin fahimtar juna ne, amma yanzu na gano kai mutum ne mai dad’in zama da dad’in mu’amala, sai dai ina neman alfarmar ka yaya ka k’ara min time, saboda kasan har yau ban gama sanin mecece soyayya ba"

Tsura min ido yayi kamar yana so ya gano gaskiyar maganar da na fad’a mishi.

Sunkuyar da kai na nayi dan gaskiya ba zan jure kallon da yaya Faruk yake min.

"Fatima!" ya kira ni da wani irin salon maganar shi da ya banbanta da sauran lokuta.

"Na’am yaya"

Sai da yayi shiru kamar ba zai ce min komai ba, can ya d’ago ya kalle ni.

"Teemah, zan iya k’ara ba ki time kamar yadda ki ka buk’ata, ina so duk san da na k’ara tambayar ki ya zama kin samo amsar".

Ci gaba yayi da cewa "Teemah, ina son ki wanda ni kaina ban san adadin son da nake mi ki ba, ni mutum ne da ba na soyayya sai akan ki da na fara, akwai ‘yan mata da suke so na amma ni ke ki ka min, ba na so in yaudari mutum, dan haka Teemah ina rok’on ki kar ki yaudare ni, gwara tun wuri ki fito ki fad’a min abin da ke ranki, zai fi min sauki".

Jiki na ne na ji yayi matuk’ar sanyi da maganganun da yaya Faruk ya fad’a min, yanzu gaskiya ba k’aramin girman yaya Faruk nake gani ba.

"yaya insha Allah ba za ka same ni da aikata haka ba".

Murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya nuna a fuskar shi.

"Teemah, kinga kin sa na koyi surutu duk saboda son ki" ya fad’a da alamar wasa.

Dariya nayi nace "Ni ba ruwa na yaya".

Girgiza kai kawai yayi bai ce min komai ba.

Haka muka ci gaba da zance jefi-jefi, yana k’ara jaddada min irin son da yake min.

Tambaya na fara yi ma kaina "wai yaya Faruk wani irin so yake min haka? ni kaina na san ba ni da amsar amma alamu sun nuna ba k’aramin so yake min ba.

Muna cikin haka ne, yaya Khalil yayi sallama ya shigo falon, ka sa ‘boye mamakin shi yayi ganin mu tare da yaya Faruk a kujera d’aya muna hira.

Hannu ya mik’a mishi suka yi musabaha kana ya nemi guri ya zauna.

Yaya Faruk ne ya kalle shi yace "Ashe ba ka nan, shi yasa ban ga motar ka ba"

"Na d’an fita ne, naje gurin friend d’ina" yaya Khalil ya ba shi amsa.

"Ok" yaya Faruk ya fad’a a gajarce.

Ci gaba yayi da min Magana k’asa-k’asa yana fad’a min gobe zai koma Abuja, kar in manta in mishi Samosa da Spring roll d’in in ba Ummu ta ajiye mai, zai biyo ya amsa.

Sauraren shi kawai nake yi ba tare da n ace komai ba saboda na ga yaya Khalil ya maida hankalin shi gare mu.

Shi kuwa yaya Khalil kallo ya bi mu dashi ganin yadda mu ke Magana k’asa- k’asa, yana so ya tabbatar da zargin da zuciyar shi take yi akan mu.

"Tun yaushe yaya Faruk da Fatima su ka shirya? An yaya babu wata alak’a tsakanin yaya Faruk da Fatima kuwa? Duk wannan tambayar da yake yi ma kanshi yasan ba mai ba shi amsar sai Faruk ko Fatima, shi kanshi yasan ba zai iya tunkarar yaya Faruk da wannan zancen ba, gwara dai ya tambayi Fatima.

Kallan tsadadden wrist watch d’in shi yayi wanda ke d’aure a hannun shi, kallan time yayi ya juyo ya kanne min ido ya ce min cikin murya k’asa-k’asa

"Teemah, zan tafi, nasan gobe in nazo ba zan same ki ba, mai za ki bani wanda zan dinga tuna wa dake" ya tsura min ido yana jiran ji mai zan ce mai, shi ko kunyar yaya Khalil ba ya ji.

Murmushi nayi nace "yaya ni ban san me zan ba ka ba, amma dai zan maka addu’ar Allah ya kai ka lafiya, ya kuma baka nasara a aikin ka".

Lumshe ido yayi saboda yadda yaji dad’in addu’ar da na mishi.

"Na gode Teemah da wannan addu’ar taki, ko ita kad’ai ta wadatar dani".

Had’a ido muka yi da yaya Khalil ya sakar min murmushi, saurin kau da ido na nayi dan nasan yau zan sha tsokana a gurin yaya Khalil.

Mik’ewa yayi yace "Bari in shiga gurin Ummu mu gaisa, sai mun yi waya".

"Ok sai mun yi waya" na ba shi amsa.

Hannu yaje ya ba yaya Khalil suka yi musabaha yace

"Khalil bari in lek’a gurin Ummu, gobe zan koma Abuja, may be ba ka nan, kana school".

"Gaskiya may be ba za ka same ni ba, gobe da wuri nake so in shiga school".

"Don’t mind, sai na dawo daga Abuja kenan".

"Safe journey yaya Faruk"

"Thanks Khalil" ya fad’a ya nufi d’akin Ummu.

Samun ta yayi tana zaune tana muraja’ar Alk’ur’an, sanye da medicated glass a fuskar ta.

Sallama yayi ya nemi k’asan carpet ya zauna kusa da ita.

Amsa masa tayi da murmushi a fuskar ta.

Gaisawa suka yi ta tambaye shi ya su Momi, Daddy da Anisa.
Amsa mata yayi da suna nan lafiya.

Ce wa tayi ya fad’a ma Momi tana nan shigowa wannan sati.

Hira suka ci gaba dayi, a ciki hirar ne yace "Ummu gobe zan koma Abuja"

"Da wuri haka Faruk, ni ina sha zaka yi mana kwanaki a Kaduna".

"Ummu da kwana biyu na nemi permission zanyi saboda prospond d’in tafiyar mu da aka yi".

"Allah dai ya taimaka, gwara da ka fad’a min da wuri, gobe sai in maka dambun naman ka tafi dashi".

Yau tsintar kanshi yayi da kunyar Ummu duk da ba ta san me ke tsakanin shi da Fatima ba, yana mai k’ara ganin girman Ummu na yadda take nuna kulawar ta gare shi.

"Ummu da kin barshi, saboda Fatima za ta min Samosa da Spring roll in tafi dashi, gobe zan biyo in amsa".

Dad’i ne ya kama ta ganin ce wa Fatima ce za ta mishi Snacks ya tafi dashi, hakan na nuna yanzu sun shirya kenan.

"Faruk ai Snacks daban, danbun nama daban, ka biyo gobe sai ka amshi duka".

"Ummu na gode, Allah ya k’ara girma".

"Amin Faruk, amma na sha ce maka in na maka abu ba godiya a tsakanin mu".

"To Ummu bari in k’arasa gida"

"Ka gaishe su"

"Za su ji".

Yana fito wa daga d’akin Ummu, d’aga mana hannu yayi ya fita daga falon.

Yaya Khalil ne ya dawo kusa dani yana kallo na.

Ni kaina kallon da yake min nasan akwai Magana a bakin shi, sai ban nuna mishi ba.

Dariya nayi ganin yadda yake min kallon tuhuma yana murmushi.

"yaya Khalil wai lafiya wannan kallon"

Bai ba ni amsar tambaya ta ba, sai ce min yayi "Sister kun sa ni a confusion"

"Ni da wa?" na tambaye shi.

"Ke da yaya Faruk"

"Da aka yi me?"

Hararar wasa ya min yace "Fatima kinn gane abin da nake nufi, amma tun da kin nuna ba ki fahimta ba, bari in miki filla-filla".

Ci gaba yayi da cewa "Fatima wai yaushe kuka had’e da yaya Faruk ban sani ba? na fara zargin ko akwai wata alak’a a tsakanin ku, sister tell me the truth".

In akwai wanda ya cancanta yasan alak’ar mu da yaya Faruk bai wuce yaya Khalil da Anisa ba, sai dai kash, hakan ba zai yiwu ba, dan muddum yaya Khalil ya ji maganar nan kamar kowa yaji ne a family, hakan na nufin dole in amince da yaya Faruk duk da har yau

Please Login or Register in order to submit comment