Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi aure inda a asibiti aka tabbatar tana d’auke da blood cancer, yanda jenny yake lallashin ta yana kwantar mata da hankali yayin da ita kuma take kuka, wani scene aka k’ara nuna wa suna zauna a k’ark’ashin bishiya inda jenny ke kwance a jikin johnny yana ba ta caring duk saboda blood cancer da take d’auke dashi gashi likita ya tabbatar musu ta kusa mutuwa.A gaskiya film d’in ya d’auki hankali na ga tausayi kamar in yi kuka dan sai da naji k’walla ta tarun min a ido, don haka ne ko motsi ba na so nayi.
Mai da hankali na nayi gun allon tv inda aka nuno jenny ta mutu a jikin johnny yana rungume da ita, hawaye ne yake zubo mai a idanun sa saboda kan ta mutu tace ya mata alk’awarin ba zai yi kuka ba.
Saboda tausayin johnny da ya kama ni ban san lokacin da na fara kuka ba saboda ganin ya rabu da masoyiyar shi ta gaskiya wanda suka sadaukar ma junan su da soyayya tun suna yara har kawo yanzu da suka girma.
Duk da ban san dad’in soyayya ba saboda ba na yin ta amma sai da naji wani feeling a raina saboda wannan shine soyayyar gaskiya, lallai wannan film d’in yaci sunan shi (endless love)
Soyayyar yahudawa kenan ma bare a je ga wadda Annabin mu Muhammad (s.a.w) ya koyar damu.
A raina na ce nima Allah ka bani wanda zai so ni tsakani da Allah da nuna mun caring da soyayya.
K’amshi da ya cika d’akin ne yasa nayi saurin d’ago kaina don ganin wanda yake sanye da wannan turaren.
Yaya Faruk ne cikin kakin shi na soja, fuskar nan a murtuke kamar bai san wata kalma wai ita dariya ba. kallo na yake yi kamar bai t’aba gani na ba, ganin abin nashi ba sauk’i yasa na sunkuyar da kaina k’asa.
"Teemah" naji ya kira suna na.
Cikin sanyin murya na amsa da "na’am yaya Faruk ina wuni"
bai amsa gaisuwar ba illah ce min da yayi "me yasa ki kuka"
shiru nayi saboda ban san amsar da zan bashi ba
tsawa ya daka min mai firgitarwa yace "ba tambayar ki nake yi ba ko sai kin ji a jikin ki"
"ba komai yaya Faruk" na fad’a cikin marairaicewar murya.
Takowa yayi ya zauna kusa dani har muna jin numfashin junan mu, shiru falon ya d’auka kamar ba mutane a ciki, can ya kalle ni yace "Teemah kina soyayya ne?
Tambayar shi ta ban mamaki saboda nasan ba na soyayya amma saboda kar in yi laifi sai na girgiza mishi kai alamar a’ah
Ci gaba yayi da ce min "idan ba kya soyayya mai ya baki tausayi a wannan film d’in har ki ke masa kuka? tun d’azun na shigo amma ba ki lura da ni ba, kinyi concentrating akan film d’in, if you are not in love, why will you worry yourself in this movie at your age?
Shiru na mishi saboda ni dai nasan ba na soyayya kuma nasan Abbu ma bazai bar ni ba har sai na shiga jami’a.
Yaya Faruk kuwa duk da film d’in ya burge shi kuma ya tayar mai da tsohon mikin da ke cikin ranshi amma bai nuna ba illa wani sabon lamari da ya shiga ranshi.ci gaba da nazari yayi a cikin ran sa yana wani tunani na daban, ko da yake nesa ta zo kusa, ba ya son yin sake, yana bin komai ne a sannu.
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Wannan shafin naku ne ‘yan group d’in*

*Tauraruwar Mace*

*Mufy & Maryam A Paki fans*

*Kainuwa Writers fans*

*Khaleesat Haidar hausa novels*

*Home of Hausa Novel*

*Da sauran groups na facebook da whatsapp da ake posting d’in wannan novel d’in*.
*Na gode da kulawar ku*.🤝🏽


*Na ji dad’in yadda wasu suka gwada nasu k’ok’arin na ba da amsar Question of the day, sai dai amsar ba Sayyidina Abubakar bane, amsar ita ce Sayyidina Usman bn Affan, shine wanda ya sadaukar da dukiyar sa da rak’uman sa a lokacin da Annabi Muhammad (s.a.w) yake cewa wa zai ba Allah rance ya biya sa ranar tsayuwa*!

*Ina ba da hakuri*
🙏🙏 *sakamkon ji na shiru da akayi, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzuri da suka taso min*




*TUNATARWA*

*Zamo mai yawan tuna mutuwa, hakan zai sa ka/ki cire kwad’ayin Duniya

*Kar ka/ki raina matsayin wani saboda gaba.

*In ka/kin samu dama kai aikin alkhairi da ita kafin ta kubce maka/ki

*Yi k’ok’ari ka/ki yak’i shaid’an ta hanyar karanta Alkur’ani domin kariya ne a gare mu.

Wannan ‘yar nasiha ce.👌🏼





13&14

Yaya Faruk ne ya d’ago ya kalle ni ganin zancen zucin da yak yi ba zai saman mai mafita ba.
"Fatima" ya kira suna na cikin wata irin muryar da ban san shi da ita ba domin yau yaya Faru ya canza min na yadda yayi sanyi kamar bashi ba.

Ya ci gaba da cewa "yau zan koma Abuja bakin aiki, ina so ki kiyaye da dokoki na da na fad’a miki a baya, yin hakan shi zai ku’butar dake daga hukunci na, idan na dawo naji ance kunyi wani abu ke da Anisa, hmmm ba sai na fad’i sauran ba dan ita ma na ja mata kunne don haka ku kiyaye".

"Insha Allah zamu kiyaye" abin da na ce dashi kenan saboda a gaskiya yaya Faruk na shiga mun lamura na da yawa amma nasan ko na kai k’ara ba wanda zai goya min baya.

d’agowar da zanyi mu ka had’a ido, nayi saurin sunkuyar da ido na saboda yau ni dai ban san me yake damun yaya Faruk ba.

"Teemah" ya kira suna na.
A raina nace ko kai ka rad’a min sunan sai haka, abu kad’an ya kira suna na.
Wannan karan ban amsa kiran da yamin ba saboda duk a takure nake, shima naga alamar bai damu da in amsa kiran ba dan haka yaci gaba da cewa "as from today, ki daina sa irin wannan kayan kina zama dasu saboda kin fara girma kuma za a iya yin bak’i at any time ki na jina koh?.
Kallon mamaki na bishi dashi na kuma kalli jikina saboda ni ban ga aibun shigar da nayi ba, wasu k’ananan kaya nasa doguwa sannan na d’aura top mai transparent wanda aka yi wa d’inkin kimono, lallai yau yaya Faruk da sabon salo yazo min dashi, in ban da haka miye gamin kifi da kaska, shi ba saurayi na ba kuma ba mijina ba bare ace ko kishi ne yake d’awainiya dashi da har zai kafa min wannan dokar ban da takurawar da yake min, ganin ba zan iya bin wannan dokar ba yasa nace "yaya Faruk ni ban ga aibun wannan shigar ba kuma ni ai naga daga ni sai ‘yan uwa na a cikin gidan shi yasa na sa kuma ma ai ban girma ba bare ace hukunci zai hau kaina"
ran shi ne ya soma ‘baci ganin yadda nake so in fad’a mishi Magana a fakaice saboda ya gano Magana na fad’a mai na yadda yake ce mana ba mu girma ba shine yau na samu hanyar maida mai da martini don haka yace "ai daman baza ki ga aibun shigar ba tun da yanzu naga kina tashen rashin kunya sannan ga ci gaban da aka samu na kallon wannan philliphine d’in da kike yi, dan naga kamar sun fara sa ki a kan hanya shi yasa zaki ga baki yi wani laifi ba, da kike cewa baki girma ba ki koma play class nan zan san ke yarinya ce"

a raina nace "kan ka ake ji, dama an ce gwano baya jin warin jikin sa, ya manta lokacin da yake cewa mu ba mu girma da yin chat ba dan yanzu na tuna mishi shine zai zama laifi"

"Ummu na ciki ne? ya tambaye ni
Amsa mishi nayi da ‘eh tana ciki"
"kije ki ce mata nazo" ya fad’a yana danna wayar shi dake hannun shi.

Mik’ewa nayi na nufi side d’in ta don fad’a mata zuwan yaya Faruk, yaya Faruk ne ya bi ni da kallo kana ya ta’be baki.
Tun da na sanar da Ummu zuwan yaya Faruk nayi zama na a d’akin ta saboda nasan in dai na koma falon sai yaya Faruk ya nemi wani laifin ya d’ora min.
Ni har tausaya wa matar da za ta auri yaya Faruk nake yi saboda fad’an shi, ko da yake irin su mata sun fi ladabtar dasu a cikin gida kaga kamar ba su bane suke masifa a waje. Maganar mu daina chat ma bai taso ba don yanzu nasa k’afa don ni ina k’aruwa a social media d’in nan, shi da yake wannan maganar yana nufin bai chat d’in ne ko duk salon takurawa ce.
Haka na ci gaba da zancen yaya Faruk ni kad’ai a raina saboda a gaskiya ni dai tamu ba ta zo d’aya ba.

Ummu ce ta nufo falon da fara’ar ta tana cewa "Faruk har an shirya za a tafi?
Yaya Faruk murmushi yayi yana cewa "ina wuni Ummu, mun same ku lafiya?
"lfy lau Faruk, za a tafi Kenan? Ummu ta fad’a
Ya amsa mata da ‘’eh Ummu zan koma, hutun da aka bani ya k’are ga Ogan mu sai kira na yake yi akwai wani aiki da zamu je a garin Yobe na kwantar da tarzoma sai na samu sauk’in aiki na lek’o kadunan"

"To Allah ya taimaka Faruk, ya baku sa’a a dukkan lamarin da kuka sa a gaba, Allah ya baku nasara, Faruk a ci gaba da rik’o da ibada don shine hanyar da za ta dinga taimakon ka" Ummu ta fad’a.
Hakika yana jin dad’in addu’ar da Ummu ta ke mai kamar ita ta haife shi, shi yasa yake d’aukar ta kamar mahaifiyar shi kuma yake neman shawarar ta a al’amuran shi dan haka yace "Amin Ummu na gode"
Kud’i ya ciro cikin wallet d’in shi ya matso kusa da Ummun ya ajiye yana cewa "Ummu gashi ba yawa a sa mana Albarka"

Ummu tace "Faruk ba ka gajiya? To kaima Allah ya baku masu muku biyayya, Allah ya muku albarka"

Cikin jin dad’i yake amsawa da "Amin Ummu"
Kallon Ummu yayi yana cewa "Ummu pls a dinga lura da takun su Fatimah saboda naga kansu na rawa ga wannan chat d’in da suke yi, a sa ido saboda yanda ake samun ‘bata gari da marasa tarbiya ga mayaudaran samari duk a cikin wannan social media d’in, na dai kafa musu doka akan chat d’in, nasan idan suka ga ba na nan zasu iya ci gaba da yi"

Murmushi Ummu tayi tace "kar ka damu Faruk, zan sa ido akan su"
Nan ya mata sallama ya tafi yayin da Ummu ke mishi addu’ar nasara.


*************************

WACECE FATIMA?

Suna na Fatima, ni ‘ya ce a gurin Alhaji Ibrahim wagini motors, Hajiya Aisha ita ce mahaifiya ta. Asalin iyaye na ‘yan Katsina ne a k’aramar hukumar wagini wanda a yanzu mahaifin su Abbu ya dad’e da rasuwa sai Hajiya, mahifiyar su Abbu ce ke zaune a garin da ‘yan uwa, zama ne ya kawo su garin kaduna, yayi Degree d’in shi a ‘bangaren Business administration inda ya fad’a harkar kasuwanci na import & export na kayayyaki irin su atamfofi da su materials, haka zalika suna da kamfani shi da wan sa na saida motoci da suka bud’e mai suna ‘wagini motors’.
Mu uku ne a gurin iyayen mu, yaya Aminu shine babba a gidan mu inda yayi Degree d’in shi akan information technology a ATBU Bauchi, yanzu haka yana aiki a ma’aikatar sadarwa na MTN dake kaduna, ya na zaune a kinkinau da matar shi da yaran sa guda biyu, Aisha ana ce mata Humaira sai namijin sunan sa Nabil.
Daga yaya Aminu sai yaya Ibrahim wanda ya ci sunan mahaifin mu ake kiran sa Khalil, yanzu haka ya karatu a Kaduna State University, yana karantar pharmacy inda yake 400 level.
Daga nan sai ni Auta inda yanzu na kusa kammala secondary school d’ina a Fenfield int’l scool dake wajen gwamna road.
Ni dai fara ce amma ba can sosai ba, sannan ni tsaka tsaki ce saboda ni dai ba doguwa bace kuma ba gajera ba, ina da d’an manyan ido sannan ina da yalwar gashin gira da na kai, baki na d’an madaidaici, a tak’aice dai ni ina tsaka tsaki a masu kyau.
Na taso cikin gata kasancewa ta ni kad’ai ce mace a gurin iyaye na amma hakan bai hana samun ingantacckenan
tarbiyya ba. ba mu cika shiri da yaya Aminu ba saboda ganin wataran gidan wani zan je kuma ba kowa ne zai d’au shagwa’bar da nake yi ba duk da wani sa’in yana ja na da wasa amma hakan bai hana ni shakkar sa ba.
Mutumina shine yaya Khalil saboda tamu tazo d’aya dashi saboda yadda yake zama muyi hira dashi sannan in yana da wata matsala ko shawara zai tunkare ni da ita ba tare da kowa ya ji ba, shi yasa Ummu da Abbu suka ce ba a jin kan mu, duk da sakewar da yake dani hakan bai sa na raina shi ba saboda Ummu tace ya bani ratar shekara kusan 3.
Mahaifin mu sananne a wajen business d’in shi na siyar da kayayyaki da kuma gurin sai da motoci.
Wannan shine tak’aitaccen tarihi na

Wannan kenan
[3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Ina mika gaisuwa ta ga*
*Miss Marriam novels group*

*Maejeeddarh Othman* (Home of Hausa novels group)

*Ummi*(Kainuwa Writers fans)

*Mhiz Tawerh* (nima ina yin ki sosai)

*Fannata ta Annabi* (zinder)

*Hussaina Paki*(‘yar garin mu)

*Da sauran wanda ban samu damar anbata ba sabida yawan Ku*

*Na gode da son da kuke ma novel d’in nan*🤝🏽

*Allah ina rok’on ka 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 kabar mu da masoyan mu a du inda suke*, *ka nisanta mu da masu mana hassada da bak’in ciki da k’iyayya*



*Wannan karan ban samu wanda suka ba da amsar question of the day na tambayar da nayi na cewa*
*ya sunan bishiyar dake cikin aljanna*?
*Amsar ita ce* *Jannatul kuldi*

*Ina jin dad’in yadda kuke gwada hazak’ar ku*.

*Allah ka k’ara mana ilimi mai amfani*.




*Tunatarwa*

Hak’uri ya kasu kasha uku 🤟🏼

* Hak’uri gurin yi ma Allah biyayya

* Hak’uri saboda kiyaye dokokin Allah da sa'ba mishi

* Hak’uri gurin jarrabawa

Dukkan hak’uri yana tare da nasara, ya Allah ka bamu ikon hak’uri.





17&18

Ko da muka je gidan yaya Aminu, hira muka zauna muka yi da Anty jiddah kasancewar ta ita ma ‘yar hirar gashi tana da jan mutane kamar ba dangin mijin ta ba.

Muna cikin hira da ita ne take ce mana "ina ko Faruk, kwana biyu bai lek’o mu ba, bari in munyi waya dashi zan ce mai kar ya bari azumi yazo bai yi aure ba, in ba haka ba, zamu ba dashi sadaka"

Dariya muka yi gaba d’aya kana Anisa tace "ya koma Abuja, yana can yana fama da fad’an shi"

Ni ce na k’ar’bi zancen da cewa "ai da su Momi za su taimaka su mishi aure saboda ina jin har da rashin auren ne yake sa shi wannan fad’an da yake yi, amma kuma ina tausayawa matar da za ta auri yaya Faruk saboda ba k’aramin hak’uri za ta yi da fad’an shi da miskilancin sa ba"

Murmushi Anty Jiddah tayi kana tace "ni da zai bi shawarata da na za’bar mai kalar type d’in shi saboda ita yarinyar za ta iya dashi"

Zaro ido nayi ina cewa "pls Anty kar ki fara, ki tausayawa ‘yar mutane, ki jik’anta in ba so kike ki sa yarinya ya aure ta, ta fara k’ashin wuya a rasa dalili ba alhalin yaya Faruk ne yake gasa mata gyad’a a hannu"

Anisa ce ta kar’bi zancen da cewa "Anti in dai zai ji shawarar taki, pls ki masa magana saboda yayi auren nan nima in samu sakewa a gida saboda komai a takure nake yi kamar a gidan yari" ta k’arashe zancen kamar za ta yi kuka.

Dariya muka fara yi saboda yadda take maganar, abin har ran ta haka yake.

Haka muka ci gaba da hirar mu kamar wasu k’awaye.

Sai da muka ci abinci sannan muka yi sallar la’asar, ba yadda ba tayi ba akan mu jira yaya Aminu ya dawo ya kaimu amma muka k’i, saboda in har muka jira shi ba lallai ya kaimu gidan k’awar mu ba amma yanzu tun da driver muke, ba mu da wata matsala.

Sallama muka yi mata kana muka nufi gidan Aisha k'awar mu.

Tun da muka je gidan muka dasa hira irin ta k’awaye, muna cikin hirar ne nake sanar dasu yanda muka yi da yaya Faruk ran da zai koma Abuja.

Dariya suka yi gaba d’aya, ganin dariyar tasu kamar da manufa suke yasa na d’aure fuska kamar ba dani ake hirar ba.
Anisa ce ta k’ara kallo na ta fashe da dariya tana cewa "wato Sister a yanzu na samo satar amsa a dramar da kuka yi da yaya Faruk da kuma dalilin da yasa ya hana mu chat da kuma takura mana da yake yi"

Kamar ya? Na tambaye ta.

Wani kallo ta min tana k’unshe dariyar da take bakin ta saboda yadda ta ga na d’aure fuska.

Fatima! Zargi na ya fara hararo min cewa yaya Faruk son ki yake yi! Anisa ta fad’a.

Dam! na ji k’irji na ya buga saboda yadda maganar ta zo min a bazata.

Dariyar rainin hankali nayi sannan na k’ara d’aure fuska.

"Anisa Kenan! ke a ganin ki mun dace da yaya Faruk? let me tell you something, na san yaya Faruk na da duk wani qualities da mace take buk’ata a gurin namiji, but to me, ba na daga cikin su saboda ke shaida ce na yadda tamu ba ta zo d’aya dashi ba, kuma ana yin aure ne idan jinin ku had’u da mutum ko ra’ayin ku amma ni duk a ciki, ba bu ko d’aya, So plss kar k’i k’ara bi na da irin wannan bak’ar fatan though shi yaya Faruk d’in ma bai ce yana so na ba kuma a yanayin girman kan shi, nasan bazai kula ni ba saboda har yau kallon yarinya yake min"

Yanayin fuskar Anisa ce ta canza zuwa ‘bacin rai saboda maganar da na fad’a akan yaya Faruk bai mata dad'i ba kuma in da kara ai bai ci in fad’a mi shi haka ba don haka tace "Fatima ya kamata in zaki fad’i Magana ki tauna, kuma in da ka’ra bai kamata ki fad’i wannan maganar a gaba na ba saboda kar ki manta yaya na ne kuma zan ji zafin duk wanda ya zage shi a gaba na kuma duk wannan abun shi yaya Faruk bai sani ba, ni ce na ce ina zargin haka"

Jiki na ne yayi sanyi saboda ban zata maganar za ta ‘bata mata rai ba don haka nace "Sorry Sister, ban san maganar zata miki zafi ba, but am sorry to say, ba na iya ‘boye abin da ke cikin raina ne"

Duk wannan conversation d’in da muke yi, Aisha ba ta sa mana baki ba sai yanzu ne ta k’ar’bi zancen da cewa

"Sisters ku bar wannan chapter d’in is not useful tun da shi yaya Faruk d’in bai fito ya fad’a ba, so plss dukkan ku kuyi hak’uri"

Dariya muka yi gaba d’ayan mu amma a raina na k’udurta k’ara nisanta duk wani alak’a da za ta had’a ni da yaya Faruk, duk da a yanzu ma ba abin da ke had’a ni dashi sai takurawa da fad’a.

Haka muka ci gaba da hirar mu kana muka canza akalar hirar tamu zuwa ga yadda jarabawar mu ta Waec da Neco take ta matso wa.

Misalin biyar da rabi muka mik’e dan tafiya gida saboda Dadi na hanyar shi ta koma wa gida.

Rako mu Aisha tayi har inda Driver d’in mu yake, sai da taga fitar mu daga gidan su sannan ta daina d’aga mana hannu.

Ko da muka isa gida, toilet na fad’a na watsa ruwa saboda yadda ba na shiri da zafi yayin da Anisa ta fad’a gado tana lumshe ido
San da na fito daga wankan, samun ta nayi tayi nisa a bacci.
Duka na kai mata a jikinta ina hararar ta, a firgice ta mik’e tana murza idanu alamar magagin bacci.
"Ke wai wace irin lazy ce, daga d’an fitar nan da muka yi shine kika wani baje kina bacci a zafin nan, kin wani saki baki sai kace wanda muka tafi a k’afa" nace da ita.

Amsa min tayi da cewa "in ban yi bacci ba me zan yi, kina ganin tun d’azun muka fita, ai dole ka gaji"

Simple English wears na sa, na juya ina kallon ta nace "yi ta barci ni kinga ma na bar maki d’akin" na fad’a ina fita daga d’akin.

Ko da na fito parlour ba kowa, zama nayi a d’aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake k’awata parloun.
Wani film naga ana haskawa a tashar Mbc Bollywood mai suna *Ramaiya vastavaiya*
Hankali na ne ya tafi kan film d’in saboda ina son indian film especially love film din su.

Yanda jarumin film d’in RIYA ya baro garin su ya tawo garin buduwarshi SONA duk da ba wani kud’i gare su ba, hasali ma ba a cikin gari suke zaune ba, ya taso a cikin daula, amma hakan bai dame shi ba illa ma hak’uri da ya dinga ba yayan Sona d’in akan ya barshi ya zauna tare dasu.
Sharad’in da yayan Sons d'in ya gindaya ma jarumin ne ya ban mamaki,
Saboda yayan yace zai ware mai fegi d’aya na gona ya nome hatsi kuma zai dinga wanke shanu amma duk ya yarda.

Hmmm lallai na yarda india sun iya wahala akan so in ba haka ba yaushe zan yarda da wannan sharad’in.

Sai naji jarumin ya burge ni saboda ina so in ga masoya nason junan su tsakani da Allah.

Anisa ce tazo ta zauna kusa dani tana cewa "Fatimah! d’an ban labarin film d’in tun da ba a fara da ni ba’
Yamutsa fuska nayi ina cewa "pls Anisa don’t interrupt me, naga ke baki san yadda nake ji da lovers bane shi yasa zaki ce in baki labari alhalin ba gama film d’in nan aka yi ba".

Ta’be baki tayi tana cewa "ke idan kina kallo sai ki maida film kamar gaske, wai da kike zancen lover’s kina soyayya ne da zaki san mahimmancin so? Anisa ta tambaye ni.
Hararar ta nayi kana nace "in ma ina soyayyar ai kin fi kowa sani"
Murmushi Anisa tayi kana ta ce "irin kune Fatimah in kuna so baku iya son abu kad’an ba"
"Kan ki ake ji" na ba ta amsa a tak’aice.

Ba wanda ya sake Magana a tsakanin mu, muka maida hankalin mu kan allon talabijin d’in muka ci gaba da kallo.
Sai da film d’in ya k’are kana na juyo na kalli Anisa na ce "Sister dan Allah soyayyar Riya da Sona bai burge ki ba"
Kallon mamaki take min sannan tace "sun burge ni, sai aka yi yaya? Ta k’arashe zancen cikin zolaya.

Tsadadden murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba.
Haka muka ci gaba da hirar film d’in, kiran sallar magrib ne yasa muka mik’e muka nufi d’aki don ba da farali.
[3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*QUESTION OF THE DAY*

*Menene sunan bishiyar da take a cikin Aljannah*?





15&16

*Ci gaban labarin*

Dawowar Ummu d’akin shi ya tabbatar min da yaya Faruk ya tafi, harara ta tayi tana cewa "ke wai Fatima wani irin kunnen k’ashi gare ki? Ki na ji yayan kin a min sallama zai koma bakin aiki amma ko ki fito ki masa sallama".

Cikin shagwa’ba na fara cewa ‘ai Ummu gwara da ya tafi! mutum ya bi ya matsa min kamar a kan sa nake zaune, ni dama yayi ta zama a can Abujan da naji dad’i.

Murmushi kawai Ummu tayi kana tace "Allah ya shirye ki auta"

Dariya kawai nayi na mik’e ina cewa ‘amin Ummu, bari inje in k’arasa kallon film d’in da na ke yi wannan masifaffen yaya Faruk yazo ya katse min kallo na.
Film d’in na mayar na ci gaba da kallo na saboda yadda film d’in ya tsaya min a rai.

Scene d’in karshe ne ya fi ba ni tausayi akan na baya, tun mutuwar Jenny, johnny ba ‘kara samun natsuwa ba.

Kamar yadda suka yi wa juna alk’awari na cewa in sun mutu zasu had’u a wata duniyar, a cewar su a nan zasu ci gaba da rayuwar su.

Johnny ne yake tafiya akan keke yana tunanin mutuwar Jenny, unfortunately kawai mota tazo ta bige shi wanda a take anan shima ya fad’i ya mutu.

Lallai wannan soyayyar Johnny da Jenny ta kai a sa ma film d’in endless love.

Ganin film d’in ya k’are yasa na mik’e na nufi d’aki ina raya

Please Login or Register in order to submit comment