Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna kulawar shi gare ta.


Tun daga wannan lokacin yaya Faruk yakan yi k’ok’arin kiran ta ko su had’u a chat, in ya samu lokaci yakan je gurin ta.


Mu’amalar shi da Nana sai ta zamo abin burgewa dan suna ganin mutuncin junan su.


San da yaya Mus’ab ya sanar da Hajiyar su da Dadin su halin da ake ciki sun yi farin ciki da jin wannan labarin, dan sun yaba da halayen yaya Faruk da kyawawan halayen shi, sun san Nana tayi dacen samun gwarzon namiji irin yaya Faruk.



Zaman mu da Dr sai son barka, ba na tare da wata matsala sai wacce ba za a rasa ba tsakanin miji da mata.


Anisa ta kan lek’o ni in tana free kasancewar ta samu D.E a Kasu, sun bata Microbiology.


Abbu da Ummu sun zo da yaya Khalil, ranar haka na wuni cikin farin cikin ganin su da na yi.
Dadin su Dr da Momin shi sun zo gidan mu.


A cikin haka ne Dr ya sai min form na HND, nayi murna san da ya sanar min in kawo credential d’ina zai min applying d’in HND ne.


Ba a wani d’au lokaci ba Admission ya fito na samu gurbin ci gaba da HND d’ina a nan Kaduna Polythecnic.


Karatu na yana tafiya yadda nake so cikin nasara.


Matsalar Meema sai abin da yayi gaba, sai dai ina k’ok’arin danne fushi na idan na ga tana nema na da fitina, a gefe kuma na ga Hanan tafiyar su d’aya da Meema, har yanzu kuma ban fad’a ma Dr abin da yake faruwa ba.



Yau ranar ta kasance ranar weekend, ban dad’e da dawowa daga School ba kasancewar wani lecturer da ya ce mu zo ran sati.


Dawowa ta kenan na kwanta a 3-sitter ina hutawa.


Sallamar su Hanan na ji sun shigo kasacewar a bud’e na bar k’ofar.


Jin sallamar su ne yasa na tashi na zauna ina murmushi.


Farida ce da Hanan suka gaishe ni, Meema kuwa ko kallo ban ishe ta ba.


Tashi nayi na kawo musu drinks.


Meema ce ta ce "Hanan zo mu shiga kitchen in samu soft food in dafa, yau throughout ban ci komai ba".


Hanan ce ta ce "Mu je toh".


Nasan Meema abin da zan tanka mata take nema ba ta samu ba, shi yasa take nema na da fitina.


Basu d’auki lokaci ba suka fito falon.


Soyayyar taliya suka dafa da suka sa mata kayan lambu.


Sun fara cin abincin ne suka kalli Farida suka ce tazo su ci ta ce ba ta ci.


Haka suka gama cin abincin nan ba tare da sun d’auke ko da spoon ba, ni kuma nayi alk’awarin bazan d’auke komai ba, dan na ga abin nasu kullum gaba yake yi.


Dr ne ya shigo falon kasancewar da zan tafi school shi yayi dropping d’ina yace min zai lek’a cikin asibiti akwai patient d’in da zai duba.


Tun da ya shigo falon yaga yadda aka ‘bata shi ya d’aure fuska, ko da su Hanan suka gaishe shi a tak’aice ya amsa musu.


Sannu da zuwa na mishi na kau da fuska ta kamar ban san abin da yake ma fushi ba, nima bai san raina a ‘bace yake ba.


Lokacin da zai shiga side d’in shi ne ya min magana akan in same shi a ciki.


Tashi nayi na bishi dan in ji mai zai ce min.


Bayan tafiya ta ne Farida ta kalli su Hanan ta ce "Ya kamata Anty Hanan ku gyara falon nan, kun san yaya Sadik ba ya son k’azanta".


Harara Meema ta watsa mata ta ce "Ba za a d’auke ba Farida, na ga kamar tsoron Zarah nan kike yi".


Farida ce ta mata wani irin kallo kana ta ce "plss Anty Meema ba da ke nayi magana ba da za ki fara min fad’a, da Anty Hanan nake, da kike cewa ina tsoron Anty Zarah ai ba laifi ba ne, dan matar brother d’ina ce".


Jin yadda Farida ita ma ta bud’e mata wuta ne yasa tayi shiru ba tare da ta k’ara cewa komai ba, in ban da faman hararar Farida ba abin da take yi.


Ita kuwa Hanan danna wayar ta take yi ba tare da ta sa musu baki a maganar ba.


Ina shiga d’akin na same shi yana rage kayan jikin shi.


Kallon shi nayi na ce "Dr me zan dafa maka, ban dad’e da dawo wa daga school ba, ban d’aura komai ba".


Maimakon ya bani amsa sai ce min yayi "Zarah akan me za ki bar falon da datti, kin san ba na son k’azanta, shine za ki bar falon a haka kuma kin san zan yi magana".


"Ai ba ni na ‘bata ba, su Hanan da Meema ne suka ci abincin suka ‘bata gurin" nima na fad’a cikin d’aurewar fuska.


"Da suka ‘bata ba sai ki gyara ba ko ki musu magana su gyara" cewar Dr.


"Ina jin kafin su tafi za su gyara ne shi yasa ban yi musu magana ba" na fad’a.


Bai k’ara ce min komai ba ya fita daga falon yayin da na nemi guri na zauna akan gadon.


Yana zuwa ya daka musu tsawa yace "Shine kuka ci abinci ku ka bar gurin haka, kun san ban son k’azanta, da ku ka bar falon haka wa kuke nufin ya gyara muku, tun kan ranku ya ‘baci ku tashi ku gyara falon nan sannan ku wanke kayan da kuka ‘bata".


Ba shiri su Meema suka mik’e suka fara gyara falon kana suka wanke kayan da suka ‘bata.


Suna gamawa suka shiga mota suka tafi ba tare da sun min sallama ba.




A ‘bangaren yaya Faruk sun fahimci juna da Nana, hakan yasa yaya Faruk ya kira su Dadi ya sanar dasu halin da ake ciki.


Dadi da Momi sun ji dad’in wannan labarin, hakan ne yasa Dadi yace ma yaya Faruk ya sanar da Dadin su Nana d’in suna na zuwan Abujan da a tsayar da maganar bikin.


Anisa ma da Momi take fad’a mata maganar ta ji dad’i da Allah ya musanya ma yaya Faruk da Nana, dan a kwana d’aya da tayi da ita ta fahimci rashin hayaniyar Nanan da natsuwar ta.


Shima Abbu san da Dadi ya sanar da shi maganar yaya Faruk da Nana ya yi farin ciki da jin wannan maganar, hakan yasa suka tsayar da ranar da za su je Abujan.


Ran weekend su Abbu da Dadi da Kawun wagini suka tafi Abuja.


An musu tarba mai kyau da karamci, bayan sun gaisa ne su Abbu suka gabatar da abin da ya kawo su.


Sun ba da kud’in gaisuwar iyaye kana suka tsayar da nan da sati biyu za su dawo a sa rana, haka suka rabu ana wasa da dariya.


Sati biyu na cika su Abbu suka koma Abuja, an tsayar da biki nan da wata uku.


Bayan dawowar su Abuja ne aka yanke shawarar had’a bikin su da su Anisa tun da yanzu yaya Khalil ya fara aiki a wani private Hospital inda suka bashi d'aya daga cikin pharmacist store.


Ko wani ‘bangare shirye-shirye ake yi ba kama hannun yaro.


Yaya Faruk bai samu zuwa Kaduna ba saboda yadda aiki ya tsare shi a Abuja, ya ce in ya samu sauk’in aiki zai zo, dan haka ta waya suke tattauna wa akan maganar bikin.


Momi duk ta fi kowa murnar wannan auran da yaya Faruk zai yi, tana ganin hanyar fitar yaya Faruk ne yazo, ga kuma bikin auta Anisa da yazo a tare da yaya Faruk, dan haka shiri take yi ba na wasa ba.


Sun yi da da Momi akan zai turo kud’i a had’a mishi kayan akwati tun da bashi da time, san da Momi ta sanar dashi akwatin da ya had’a min yana nan, ya sanar da ita a ajiye su, in yazo zai san yanda za ayi da kayan, a had’a wasu tun da wannan sun kwana biyu.




Lokaci na ta tafiya yayin da biki ke ta matsowa.


Yaya Faruk ya tambayi Nana in akwai event d’in da ta tsara ta fad’a mishi, ta nunan mishi da walima da kamu kawai za tayi, yayin da ‘bangaren shi abokan shi suka had’a mishi crossing of the sword.




Yau biki ya rage sati biyu, dan haka ne yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki ya tawo Kaduna.


Momi tayi murnar ganin shi ganin yanzu bai da wata sauran damuwa, duk tasan har yanzu abin da ya faru ba mai sauk’in wuyar fice wa ba ne a rai.


Lokacin da Momi take tambayar shi abubuwan da suka tsara ya sanar da ita, haka Momi ta dinga jero mishi event d’in da ta tsara.



Sai dai yayi murmushi kawai, yasan Momi ta na so yayi aure, ga kuma abin da ya faru tsakani na dashi, dole yanzu ta nuna murnar ta.


Ta nuna mishi akwatunan da ta had’a da wanda ita ma ta siya, shi kanshi yaya Faruk kayan sun burge shi ya kuma yaba.


Yaya Faruk ya je gidan mu, su Abbu da Ummu sun yi murnar ganin shi, sun mishi fatan alkhairi a auran da zai yi tare da sa mishi albarka.


Har kullum yana d’aukar su Abbu kamar iyayen shi, ba sa banbanta shi dasu yaya Aminu.


Yaya Faruk yaje gidan yaya Aminu inda Anty Jiddah ta dinga tsokanar shi, sun tattauna da yaya Aminu akan yadda bikin zai kasance.


Yaya Khalil ma ya had’a akwatuna na burgewa masu kyau da tsada.


Yaya Khalil na yawan kira na yana fad’an min abubuwan da suka dangancin bikin.



Nima na je gida san da muka yi waya da yaya Khalil yake fad’a min an sa biki, haka na kira Anisa ina ta tsokanar ta.


Ba yadda ban yi da Dr akan ya barni in je gidan mu tun da bikin ya matso amma ya k’i yace sai bikin ya kusa.


Haka na k’yale shi ba dan raina ya so ba, ina jiran a shiga satin bikin.

An kai kayan akwati gidan su Nana, da su Ummu aka kai akwatin da su Anty Jiddah da k’anwar Momi Anty Fauziyya sai k’awar Momi.


An basu tukwici na kai kayan da suka yi.


San da su Ummu suka dawo ne ta kira ni a waya ta fad’a min fad’a akan rashin zuwan da ban yi ba, na ba ta hak’uri akan ranar mu na test a makaranta ne duk da ba gaskiya na fad’a mata ba, nasan idan ta ji Dr ne ya hana ni baza ta ji dad’i ba, ta fad’a min lokacin da za a kai kayan yaya Khalil, mun yi da ita akan insha Allahu zan zo ranar.



Lokacin da Dr ya dawo nake fad’a mishi bai ce min komai ba, sai na d’auka ya amince min ne.


Ana gobe za a kai kayan da daddare muna kwance da Dr nake k’ara fad’a mishi gobe zan je gida ba zan je school ba saboda ina son akai kaya dani.


Wannan karan ma bai ce min komai ba, hakan ya ‘bata min rai saboda ban san ma’anar shirun shi ba.


Da safe yana shirin tafiya aiki na ce "Dr jiya na tambaye ka zan je gidan mu ba ka ce min komai ba".


"Ba za ki ba ne Zarah" ya fad’a min a tak’aice.


Wani irin ‘bacin rai na ji ya ziyarce ni, lokaci d’aya na ji wasu hawaye sun tarun min a idanu na, na rasa manufar dalilin Dr na yi min haka, in sha’anin family d’in su ne da na mishi maganar shi zai kai ni ba tare da ya min musu ba, amma in dai abin da ya dangance ni ne sai ya dinga kakkaucewa, ina ganin wannan karan dole ne in k’waci ‘yanci na, ba zai yiwu ya dinga hana ni yin zumunci da ‘yan uwa na ba.


"Akan me zai sa ba zan je ba Dr" na fad’a cikin ‘bacin rai.


"Saboda ina da ikon hana ki zuwa ko ina, shine dalilin" ya bani amsa.


Hawaye ne suka zubo min na share na ce "Dr in ka min haka ba ka min adalci ba, san da za akai akwatin yaya Faruk haka ka hani ni zuwa, yanzu ga na yaya Khalil za akai akwatin shi ka ce ba zani ba, ka kuma san yadda muke, da wani ido kake so in kalli su Ummu da mutane idan ban je ba, Dr ina so ka fad’a min dalilin ka da ba ka yawan bari na in je sha’anin family d’in mu alhalin ka na bari na ina zuwa na family d’in ka".


"Ba sai na fad’a miki dalili ba" ya fad’a min a tak’aice.


Yana gama fad’ar haka ya fita daga falo.


Zama nayi a falon ganin yadda Dr ya min halin ko in kula da damuwa ta, bai damu da abin da hakan zai jawo min idan ban je ba.


Wasu hawaye ne suka dinga zubo min na takaicin Dr.


Zuciya ta ce take bani shawarar akan in shirya in je tun da na tambaye shi ya k’i bari na.


Haka na tashi na shirya na kulle k’ofar na shiga motar da Dr ya siya min, ba ko wane lokaci nake hawa ba saboda hannu na bai gama k’wari ba.


Ina zuwa gidan mu na ga ‘yan uwa, nan wani farin ciki ya ziyarce ni.


Ban wani jima da zuwa ba aka tafi gidan su Anisa dan kai akwatunan.


A raina ina fargabar zuwa saboda so d’aya muka zo da Dr muka gaishe su, ranar Dadi na nan, ban san yadda Momi wani kallo za ta min idan ta ga har dani aka kawo akwatin.


Ga mamaki na san da muka je gidan haka Momi tayi ta nan-nan dani, haka ta dinga ja na a jiki, haka yasa na ji dad’i a raina, na san Momi ni mutuniyar ta ce, tun san da abin da ya faru tsakani na da yaya Faruk take fushi dani, yanzu na tabbatar da ta daina fushi dani.


Haka na shiga d’akin Anisa ina tsokanar ta, zama nayi muka sha hira irin wacce muka kwana biyu ba mu yi irin ta ba.


Sai da muka d’an jima kana muka tafi.


Haka Momi ta ba su Anty tukwici na
kayan akwatin da muka kawo.


Muna koma wa gida na wuce side d’in yaya Khalil, nan na zauna muna ta tsara yadda bikin zai kasance kana muka zarce da hira.


San da zan tafi gida ne muka had’u da yaya Aminu ya zo d’aukan Anty Jiddah, tsayawa nayi muka gaisa.


Sallama na musu kana na shiga mota ta na ja.


Sai da na fara tafiya ne fargaba ta kama ni dan yanzu nasan Dr ya dad’e da dawowa daga aiki, gashi ba yaso in kai yamma idan na fita, yanzu kuma gashi yamma tayi sosai.


Da wannan tunanin na isa gida, ina shiga harabar gidan na ga motar shi a parkin space.


Ganin k’ofar falon a bud’e yasa na shiga da sallama ta.


Samun shi nayi a zaune yana kallon tashar Master Channel.


Ciki-ciki ya amsa min sallamar da na yi mai.


"Sannu da gida Dr".


Bai amsa min ba sai ma tambaya da ya watso min "Daga ina kike?".


Duk da nasan yasan in da naje bai hana ni amsa mishi da cewa "Daga gidan mu nake".


"Good" ya fad’a a tak’aice.


Ci gaba yayi da cewa "Amma ba na ce miki kar ki je ba".


Duk da masan ban da gaskiya tun da na fita ba da izinin shi ba, hakan bazai hana ni in k’watar ma kaina ‘yanci ba.


"Ka ce kar in je, amma na ga zuwa na yana da mahimmanci, shi yasa na je, amma kayi hak’uri fitar da nayi ba tare da izinin ka ba".


Bai ce min komai ba ya tashi ya tafi side d’in shi.


Ganin bai min magana ba yasa jiki na yayi sanyi na nufi d’aki na.


Da daddare na shirya cikin shigar kayan bacci na nufi d’akin Dr.


Samun shi nayi yana danna laptop.


Duk da yaji shigowata amma hakan bai sa ya d’ago kanshi ya kalle ni ba.


Kusa dashi na je na zauna na ce "Dr sannu da aiki".


"Yawwa" ya amsa min a tak’aice.


"Me kika zo yi?" ya tambaye ni.


Tambayar ta ban mamaki da takaici tare da wani irin haushi da tasa na tsaya ina kallon shi, amma sai na danne fushi na ce "wannan wace irin tambaya ce Dr, za ka ce me na zo yi, kwanciya na zo yi".


Cikin d’aurewar fuska ya ce "Ki tafi side d’in ki kije ki kwanta, a yanzu ba ni da buk’atar ki, in ina buk’atar ki zan nemi ki, tun da ni ban isa in baki umarni ki bi ba".


Tsayawa nayi ina al’ajabin Dr tare da mamakin shi, duk da kunne na ya jiyo min abin da Dr ya fad’a min amma na kasa gasgata kunne na.


Ina ganin akan fitar da nayi har ya kai ya zama wani laifi da har Dr zai hukunta ni irin hakan, bayan na bashi hak’uri akan laifin da na mishi duk da nasan akan gaskiya ta na aikata hakan.


"Wai ni yau Dr yake cewa in tashi in bar mishi d’aki bai da buk’ata ta".


Tashi nayi na fita daga d’akin.


Tun kan in k’arasa side d’ina na fashe da wani irin kuka mai cin rai.


Kwanciya nayi akan gado ina ci gaba da kuka, a lokaci d’aya ina mamakin Dr.


Sai yanzu ne Kalmar na da aka fad’a min na cewa aure zaman hak’uri ne ya fad’o min, da ni a gani na in har kuna son junan ku ba wata matsala da ka iya zuwa ta muku dabaibayi a zaman ku, sai gashi tun ba a je ko ina ba na fara ganin dalilin da yasa ake cewa in yi hak’uri.


Da k’yar na samu bacci ya d’auke ni saboda yadda nayi sabo da jikin Dr, ga kuma takaicin abin da ya min a lokaci d’aya.
[8/5, 22:30] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀




*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




www.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa Writers Association





*FATAN ALKHAIRI*


*Khrty* _(Marubuciyar Ya Sheikh)_.


*Maryam Bodinga* _(Maganin Biri, Karen Maguzawa)_.


*Ummien Fauzan* _(Marubuciyar Bahijjah)_.


*Mrs Xerks* _(Marubuciyar Sanadin Talauci)_.


*Ummu Fatima* (Marubuciyar Dijah qaya)_.


*Noorul huderh* _(Marubuciyar Detective Noor)_.


*Mmn Rufaida* _(Marubuciyar Sanin Masoyi sai Allah)_.






*QUESTION OF THE DAY*


_Yi bayanin abin da suratul Bak’ara ta ke karantawar?_.






79-80


Washe gari haka na tashi na had’a mana breakfast, mamakin Dr ne har yanzu a raina.


Ina zaune a dining ina breakfast Dr ya fito cikin shirin shi na tafiya aiki.


Kujerar da ke kusa dani yazo ya zauna.


A tak’aice na gaishe shi ya amsa min saboda har yanxu ban daina jin haushin abin da ya min ba.


Kallo na yayi cikin wasa, ya ce "Zarah yau ba jira".


Mamakin shi ne ya kama ni, kamar ba shi ba ne jiya da daddare ya gama ce min bai da buk’ata ta duk da hak’urin da na bashi, shine har ya manta abin da ya min, yake son ja na da wasa saboda ya d’auke ni a mara wayau.


Ba tare da na d’ago na kalle shi ba na ce "Naga ba a da buk’ata ta shi yasa ban jira ka ba".


Murmushi yayi kawai dan yasan magana na fad’a mishi.


Breakfast na had’a mishi na ajiye a gaban shi.


Lokaci na duba na ga na kusa yin latti, hakan yasa na tashi na je na d’akko jaka ta na fito falon.


Samun shi nayi har gama breakfast d’in.


Tare muka fito, saboda neman tsokana sai cewa yayi "Ki zo in sauke ki, dan na ga har yanzu hannun ki bai gama k’wari ba".


"No ka barshi kawai, zan yi driving da kaina".


Ban saurari mai ze ce min ba, na shiga motar na tafi.



Da daddare ban yi gigin zuwa side d’in shi ba, dan ban manta maganar da ya fad’a min ba.


Kwanciya ta nayi a side d’ina ni kad’ai, duk da tsoron da nake ji.


Bud’e k’ofar da Dr yayi ne yasa na maida hankali na bakin k’ofar.


Bulb d’in d’akin ya kunna.


A kujerar dressing mirrow d’ina ya zauna yana kallo na.


"Zarah ashe baki yi barci ba". cewar Dr.


"Eh" na bashi amsa a tak’aice.


"Na ji ki shiru ba ki zo ba, shi yasa na zo in ga ko lafiya".


Kallon shi kawai na ke yi san da yake jero wannan bayanan, in ban da Dr ya maida ni yarinya, jiya ya gama ce min bai da buk’ata ta sannan yanzu yace min yaji shiru ban je gurin shi ba, saboda ni ban san darajar kaina na ‘ya mace ba da har zan bi shi ya koro ni, nima zan nuna mai ina da nawa matsayin a gurin shi.


"Zarah na ji kin yi shiru" ya fad’a yana kallo na.


"To me zance maka Dr" na fad’a.


Mik’ewa yayi ya ce "Ok tun da ba ki da abin cewa ki tashi mu tafi side d’ina".


Wani kallo na watsa mishi na alamar ka manta abin da ka fad’a min ne kana na ce "yanzu kana da buk’ata ta kenan, gashi ni kuma ba ni da buk’atar ka".


Wani kallo ya watsa min na gargad’i kana ya ce "Zarah mu bar wannan maganar, laifi ni kika yi ma wa, ni ya kamata in yi fushi dake ba ke ya kamata ki ya fushi dani ba, tun da na bar maganar, ya kamata ke ma ki bar maganar, ba na son jan zance, ki zo mu tafi".


Murmushin takaici na yi kana na ce "Tun da ka ce a bar maganar na bar ta, amma ni fa yau ba zan je side d’in ka ba".


Kallo na yayi ya ga fuska ta a d’aure, yasan ba da wasa na fad’i maganar ba, ganin hakan ne yasa ya girgiza kai yayi murmushi.


"Ya zan yi tun da gimbiya Zarah yau ta ja kambun ta, dole in yi yadda take so, bari in kwanta a nan d’in, ai duk d’aya ne" Dr ya fad’a cikin wasa.


A hankali yadda ba zai ji ni ba na ce "Da dai ka koma side d’in ka da yafi, dan nima ban da buk’atar ka".


"Me kika ce" ya tambaye ni.

"Ban ce komai ba" na bashi amsa.


Kwanciya ta nayi ba tare da na k’ara bin ta kanshi ba.


Ina jin shi ya kashe bulba d’in, ya kunna dim light na gefen gadon.


Gadon ya hau ya kwanta, dan neman magana ina jin shi ya matso kusa dani ya kwantar da kanshi a jiki na.


Ina jin shi ya fara ta’be-ta’ben shi a jiki na ban ce mai komai ba.


Sai da na ga ya canza salon da yake min ne yasa na fara k’ok’arin k’wace kaina.


Matsawa nayi can gefe ina maida numfashi.


A hankali Dr ya ce "Zarah me ya faru za ki min wannan hukuncin".


"Ban da buk’atar abin da kake min ne, shi yasa" na fad’a.


Kallo mai alamar tambaya ya watso min kana ya ce "Ban gane ba ki da buk’atar abin da nake miki ba, sai ki na da buk’atar hakan kenan sannan za ki bani hakk’i na".


"Ni ban ce haka ba" na fad’a a tak’aice.


"Kin ga Zarah, in ke baki da buk’ata, ni ina da ita, dole ne ki bani hakk’i na" cewar Dr.


Wannan karan ban ce mai komai ba, sai ma kwanciya ta da nayi.
Haka Dr ya matso ya fara yin yadda yake so yayi dani kasancewar nasan ko zan k’waci kai na wahala zan sha, dan d’azun ma da k’yar na k’waci kaina.


Kuka na saka mishi, hakan yasa ya tsaya da abin da yake yi.


Kallo na yayi ya ce "Zarah kukan me kike yi, dan zan amshi hakk’i na shine za ki sa min kuka, in dai dana bin da nake miki ne ba k’ya so, ni na hak’ura".


Ci gaba da kuka nayi na ce "Dr ba akan wannan abi nda kake min nake kuka ba, duk da ka ce in bar maganar, but i can’t Dr, abin yana damu na a raina, plsss Dr ina so ka fad’a min dalilin da yasa ba ka so in je abin da ya danganci family d’in mu".


Shiru yayi kana ya ce "Zarah, stop crying, i will tell you my reason, ba wai ba na so ki je abin da ya danganci family d’in ku ba ne, sai dan ina ganin kamar in kina yawan zuwa za a iya samun matsala dan na ga famiky d’in ku sun fi so ki auri d’an uwan ki, shi yasa na ke hana ki zuwa".


"Dr wannan ba dalili ne da za ka dinga hana ni zuwa ba, Dr ina so in dinga zumunci da ‘yan uwa na, ina shiga cikin su, rashin zuwa na zai sa su ji haushin ka akan rashin bari na da ba kayi in suka fahimci kai ne ba ka bari na in je, ni kuma ba zan so a familin mu su ga laifin ka ba, bayan na baka trust akan cewa ba za ka bani kunya ba, sannan tunda aka yi auren mu ba wanda ya k’ara ta da

Please Login or Register in order to submit comment