Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta duba ni.

Ganin ba ta ganni ba yasa ta duba cikin band’aki na amma ba ta ganni ba, haka ta dinga duba ko ina a gidan ba ta ganni ba.

Mamaki ne ya kama ta dan ita tasan ba muyi da ita zan fita ba.

Fito wa tayi harabar gidan, sunan wanda yake musu gadi ta dinga kira.

"Malam Musa! "Malam Musa!
Jin kiran da Ummu ke mai ne yasa ya fito daga d’an d’akin shi dake can gefen gate ya tawo da gudu.

"Hajiya gani" Malam Musa ya fad’a cikin ladabi.

Ummu ce ta ce "Daman tambayar ka zanyi, ba ka ga fitar Fatima daga gidan nan ba, na tashi daga bacci ne na ga ban ganta ba".

"Gaskiya ban ga fitar ta ba, ina jin ko lokacin da na shiga band’aki a lokacin ta fita".

"Ba komai Malam Musa, za ka iya tafiya" tana gama fad’ar haka ta juya cikin falo.

D’akko wayar ta tayi ta kira Anty Jiddah ta tambaye ta ko na zo gidan ta, nan Anty Jiddah ke sanar da ita ban zo ba.

Haka Ummu ta kira Anisa ta k’ara tambayar ta ko na zo gidan, ita ma sanar da ita tayi ban zo ba.

Duk inda Ummu take tunanin zanje, ta kira ta tambaya an tabbatar mata da ban zo ba.

Gashi tana ta kiran numba ta ba ta shiga ba, ganin haka yasa Ummu ta kira Abbu ta sanar dashi halin da ake ciki.

Ko minti ishirin ba a d’auka ba sai ga Abbu da yaya Khalil sun shigo a tare.

Abbu ne ya kalli Ummu wanda hankalin ta ya fara tashi ya ce "Hajiya ya aka yi Fatima ta fita ba ki sani ba, kuma ba gidan k’awayenta ta tafi ba?" ya k’arasa maganar da tambayar ta.

Ummu ce ta nisa ta ce "Na tashi daga bacci sai na ji ban ji motsin ta ba, na shiga d’akin ta ma ba ta nan, na kira gidan su Jiddah da Anisa ba taje can ba, har k’awar ta d’in nan Aisha ita ma na kira ta tace min ba ta je can ba, na kuma tambayi Malam Musa yace bai ga fitar ta ba, sai dai Khalil yaje gidan wannan k’awar ta Halima yaga ko can taje".

Abbu ne ya kalli yaya Khalil ya ce "Khalil je ka gidan k’awar Fatiman ka ga ko tana can".

"Toh Abbu, bari inje in gani" yaya Khalil ya amsa kana ya juya ya bar falon.

Abbu ne ya nisa ya ce "Kar ki damu Hajiya, insha Allahu ba nisa tayi ba".

Ummu ta ja gauron numfashi ta ce "Allah dai yasa Alhaji".

"Amin".
ya fad’a a tak’aice.


*************************
Yaya Khalil ya je gidan su Halima ya tambaye ta ko na zo gidan, ita ma ta tabbatar mishi da ban zo ba.

Ganin yanayin yaya Khalil yasa taji tausayin shi, tasan suna cikin wani hali gurin nema na, matsalar da aka samu shine ban fad’a mata inda za ni ba, dama tun farko ita ba ta bada goyon baya na wajen yin tafiyar nan ba, da haka suka yi sallama da yaya Khalil ya dawo gida jiki a sanyaye.

Tun da na shiga d’akin Hajiyan Wagini na ajiye kaya na, cire kaya na nayi na shiga band’aki na watsa ruwa, na nemi kaya marasa nauyi nasa na fito na nufi kitchen na d’ebo abinci da ruwa na dawo falo.

Zama nayi kusa da Hajiyan Wagini na fara cin abinci muna d’an yin hira da ita.

Cikin hirar ne Hajiya ta kalle ni ta ce "Fatima lafiya na ganki a garin nan ke kad’ai alhalin bikin ki ya kusa, mu da muke shirin zuwa biki sai kuma in gan ki kinzo" ta k’arasa maganar tana kallo na.

Ban so Hajiya ta fahimci plan d’ina da wuri, na fiso sai ta tashi tafiya Kaduna in bijire mata in k’i bin ta, zan fito in fad’a mata k’udiri na akan fasa auren yaya Faruk, nasan ba k’aramin rigima za mu yi da ita ba, zanyi duk iya yi na in shawo kanta akan tasa su Abbu su fasa auran mu.

Murmushi nayi na ce "Hajiya zuwa fa nayi in miki sallama, shine kuma yanzu za ki tsare ni da tambayoyin ki, sai in ma yi zuciya in koma".

Hajiya ce ta ce "Ka ji ni da ja’irar yarinya, to koma mana, ba dole in tambaye ki ba, na ganki kwatsam ke kad’ai kuma nasan a Kadunan ana can ana ta shirye-shirye".

Shiru na mata taci gaba da maganganun ta, nasan ci gaba da tanka mata zai iya jawowa ta wargaza min shiri na, gwara in samu mu rabu da ita lafiya.

Ina gama cin abincin na kai plate d’in kitchen, ban dawo falo ba na wuce cikin d’aki don muyi waya da Dr.

Ido na ne yakai kan wayar Hajiyan Wagini, tashi nayi da sauri na sa ta a flight mode yadda in an kira za aji ta a kashe alhalin a kunne take, nasan za ta iya kiran Abbu ko Dadi taji dalilin zuwa na ko kuma su za su iya kiranta su tambaye ta ko na zo Waginin.

Waya na zauna muka sha da Dr kamar kar mu rabu, lallai na yadda ba abin da yakai soyayya dad’i musamman in ka had’u da wanda kuke so junan ku, sanar dani yayi yana hanya, idan ya k’arasa Kadunan zai kira ni, sallama muka yi dashi akan sai ya kira ni.

Yaya Khalil haka ya dawo ya sanar dasu cewa ban je gidan k’awa ta ba.

Haka aka ci gaba da kira na amma ba a samu na, wayar a kashe take, Ummu najin haka ta soma kuka tana cewa "Oh ni Aisha, Allah kasa yarinyar nan ba wani gurin ta tafi ba".

Abbu ne yaci gaba da lallashin Ummu akan ta daina kuka, a zuba ido a gani zuwa anjima, idan ban dawo ba sai a san matakin da za a d’auka.

Su kansu idan ka ga gansu, kasan suna cikin wani hali na tashin hankali.

Abu wasa-wasa sai gashi har dare ba a ganni ba, hakan yasa yaya Aminu wanda yazo gidan tun san da ya koma gida Anty Jiddah ta sanar dashi halin da ake ciki ya tawo gidan yace ko za a je a tambayi Dr ne ko yasan inda nake.

Abbu ne ya hana yaya Aminu zuwa, yace in aka yi hakan ba a kyauta ma Dr ba, tunda ba a da tabbacin ko yasan inda nake, kuma hakan zai iya jawo wata matsala, ni ai ba yarinya ba ce, a dakata a gani ko zan dawo.

Har dare ban dawo ba, shi kanshi Abbu ya rasa wace hanya zai bi ya shawo kan matsalar, gashi ya kasa d’aukar waya ya kira Dadi da Hajiyan Wagini ya fad’a masu halin da ake ciki, ganin dare yayi ne Abbu yasa kowa ya tafi ya kwanta, ko a ranar a nan yaya Aminu ya kwana, sai kiran Anty Jiddah yayi ya fad’a mata ba zai samu dawowa ba, a gidan su Ummu zai kwana.

Haka kowa a ranar yayi kwanan k’unci da fargaba, ba wanda yayi barcin kirki a cikin su.

Ummu kuwa da Abbu ba a san wanda yafi shiga tashin hankali ba, ba wanda ya rintsa a cikin su.

Dukkan su tunanin su yazo d’aya akan cewa na gudu ne ba ‘bata nayi ba, shi yasa Abbu bai samu k’arfin gwiwar kai report police station ba.


Washegari ne Abbu ya kira Dadi akan yana neman shi, wata ‘yar matsala ce ta taso.

Ba a d’au wani lokaci ba sai ga Dadi ya zo gidan.

Abbu ne yake sanar da Dadi ba a ganni ba, basa tunanin ‘bata nayi, sun fi tunanin guduwa nayi dan ra’ayin kaina.

Tun da Dadi yaji wannan labarin ya dinga ma Ummu da Abbu fad’a akan ya hakan ta faru.

Abbu na ganin babu wani dalili da zai ‘boye ma Dadi abin da yake faruwa tun da na riga na tona musu asiri, gwara ya fito ya fad’a mishi komai, hakan yasa bai ‘boye ma Dadi halin da ake ciki ba game da halin da muke ciki tsakani na da yaya Faruk da kuma Dr, har zuwa rashin gani na da ba ayi ba.

Abbu ne ya d’aura da cewa "yaya ina neman afuwar ka akan ‘boye maka halin da ake ciki da nayi, ina ganin na isa da Fatima da zan ba ta umarni tabi, ashe abin ba haka yake ba, soyayyar wani ta fini mahimmanci a gurin ta da har ta za’be shi akan bin umarni na, A yau da a ce ina da wata ‘ya macen ban da Fatima da na ba Faruk ita, ina rok’on alfarma a gurin ka yaya kar ka hana ni, ina so in nuna ma Fatima ni na haife ta ba ita ta haife ni ba, zan aura mata aure da Faruk a rananr da aka tsara ba tare da an fasa ba, sai dai in ta mutu da auran shi a kanta, zan nuna wa Fatima ni ba irin uban nan ba ne da zasu bi son ransu su faranta ma ‘ya’yan su akan abin da suke so" ya k’arasa maganar cikin takaici.

Dadi ne yaja gauron numfashi kana ya ce "Ibrahim ba ka kyauta min ba na ‘boye min halin da ake ciki na tsakanin Fatima da Faruk, dukkan su ‘ya’yan mu ne kuma ba za a tauye ma kowa hak’k’in shi dan mu faranta ma d’aya daga cikin su ba, ita soyayya Allah ne yake sa ta a zuciyar mutum, ba a tilasta wa d’an adam sai ya so wani, in Allah bai nufa yaso wanin ba zai ta’ba son shi ba duk kuwa da kusancin su, nasan Fatima ba ta kyauta ba da ta za’bi hanyar guduwa akan tana ganin shine maslaha a gare ta, da ni ta zo ta sama ta fad’a min halin da take ciki da abin bai kai ga haka ba, yanzu abin da yafi mahimmanci shine a samu a san inda Fatiman take, in yaso daga baya a samu mafita akan wannnan al’amarin.

Abbu cikin ‘bacin rai yace "yaya kayi hak’uri da abin da zance, ni dai da kaina ba zan sha wahalar neman Fatima ba, bayan nasan guduwa tayi, taje duk inda zata tun da tana ganin hakan shi yafi mata".

Ummu ce cikin kuka ta ce "Alhaji kayi hak’uri da abin da ya faru, yaro ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, menene amfanin neman yarinyar da ba za tayi wa iyayen ta biyayya ba, abin da kake ji yana faruwa ko ka kalla a talabijin shine yau ‘yar ciki na ta aikata, abin da bai ta’ba faruwa a dangin mu ba amma ta sanadiyyar yarinyar da na haifa sai gashi ta aikata".

Murmushi kawai Dadi yayi ya ce "Kar ki damu Aisha, komai zai zo da sauk’i insha Allah, ni zan koma, da yardar Allah za a ganta".

Sallama ya ma su Ummu yayin da suka jera da Abbu suna ci gaba da tattauna matsalar, Dadi ne yake ta ba Abbu baki akan ya d’auki komai da sauk’i, kar ‘bacin rai yasa ya d’auki mummunan mataki.

Yaya Faruk tun da ya koma Abuja ya ci gaba da ayyukan shi, sai dai matsalar da muke samu dashi na yawan fad’o mishi a rai, yana ganin komai ya kusa zuwa k’arshe tsakanin shi dani in har aka yi auren shi kenan, yasan wuyar ta ayi auran mu, yasan yadda zai yi ya shawo kaina in fad’a cikin zazzafar soyayyar shi, yana da hanyoyi da dama da zai bi da ni in kamu da son shi cikin sauk’i, da irin wannan tunanin yake jin sauk’i a ranshi.

Yau yana zaune a falon yaya Muhsin suna hira, yayin da Nana Khadijah ke zaune a d’aya daga cikin kujerun dake falo tana karanta wani hausa novel mai suna *SANADIN KADDARA* tattauna wa suke yi akan yadda bikin zai gudana, hankalin ta ya kasu kashi biyu, d’aya yana ga littafin da take karantawa, d’ayan yana ga tattaunawar da su yaya Faruk ke yi akan bikin shi, ba tasan me yasa in dai aka yi maganar bikin yaya Faruk take jin wani iri a ranta ba, ta rasa yadda za ta fassara wannan lamarin da yake damun ta, ba kuma wanda take ganin za ta iya fad’a ma wa dan kar a canza mata manufar ta, ita dai abin da ta sani shine yanzu sun yi sabo da yaya Faruk wanda ita kanta take mamaki, sai dai a yanzu jikin ta nayin sanyi in ta tuno da auran da zai yi, tasan dole ne ta ja jikin ta daga gareshi a dalilin auran da zai yi.

Yaya Faruk ne ya kira sunan ta "Khadijah!

Kiran sunan ta da yaya Faruk yayi shi ya katse mata tunanin da take yi.

"Na’am yaya Faruk" Nana ta amsa mishi cikin sanyin ta.

"Ina fatan normal, naji kin yi shiru ne ba ki ce komai ba".

Tsadadden Murmushi tayi kana ta ce "Ba komai yaya Faruk, novel d’in nan ne ya d’auke min hankali".

"Ok hakan na da kyau" shima ya fad’a yana murmushi.

Ta’be baki Mus’ab yaya ya ce "Kaima ai kasan wannan miskilar ba lallai ne kaji maganar ta ba, ko da yake naga ai taku tazo d’aya kuna hira, ko dan jirgin miskilancin tare ya d’ebo ku ya ajiye ku a airport d’aya ban sani ba".

Dariya yaya Faruk yayi wanda hakan ya k’ara fito da kyawun shi ya ce "Kai fa Mus’ab iskancin ka yawa gare shi, yanzu ina ruwan ka a cikin maganr mu, ko kai na tambaya".

Dariya shima Mus’ab yayi ya ce "Sorry Bregadier Faruk angon Fatima".

Murmushi kawai yaya Faruk yayi bai ce komai ba.

Wayar Mus’ab ce tayi k’ara alamar kira ya shigo.

Bayan ya gama amsa kiran ne ya kalli yaya Faruk ya ce "Ka ga ina da appointment da Birgedier Aminu na manta, shine ya kira ni yana jira na, bari in je in dawo, pls ka jira ni".

"Kawai dai ka same ni a Block d’ina tun da ban san time d’in da za ka dawo ba, idan muka gama hira da Khadija zan tafi" cewar yaya Faruk.

"Ba matsala, sai mun had’u a can kenan".

"Ok sai mun had’u" yaya Faruk ya amsa a tak’aice.

Muhsin ya juya kallon shi ga Nana Khadijah ya ce "In Maryam ta tashi daga bacci, kya fad’a mata na d’an fita".

"Sai ka dawo".

Nan suka yi musabaha da yaya Faruk ya fita daga falon.

Jefi-jefi suke yin hirar kasancewar su mara sa son surutu, lokaci d’aya kuma yaya Faruk na kara wayar shi a kunne da alama akwai wanda yake son kira bai samu ba.

Gajeren tsaki ya ja kafin ya ajiye wayar shi a kan jikin shi.

Shiru ne ya biyo baya kafin ya mik’e da niyar tafiya.

Sallama ya mata ya fara tafiya.

Kiran sunan shi da Nana tayi yasa shi juyowa.

Itama tashi tayi ta tako tazo kusa dashi.

Cikin marairaicewa ta ce "yaya Faruk what’s wrong".

Cikin basarwa ya ce "Me kika gani".

"Gani nayi yanayin ka ya canza a lokaci guda, kamar akwai abin da yake damun ka".

Lallausan murmushi yayi ya ce "No don’t mind Khadijah, ba wani abu bane, just ina ta trying d’in number Teemah ne ya k’i shiga, sai a ce a kashe take, ni kuma ban cika son takura wa mutane in ce ai kai mata waya za mu yi waya da ita".

Murmushi kawai tayi ta ce "Gaskiya amarya ba ta kyauta ma angon ta ba, tasan zai nema ta sai kuma ta kama ta kashe wayar" ta k’arasa maganar cikin zolaya.

"lallai Khadija kin ga gadon barci na, yanzu ni ki ke tsokana".

Dariya tayi ta ce "Sorry yaya Faruk, na ga Amaryar tamu ce za ta sa yayan mu a network".

Girgiza kai kawai yayi ya mata sallama ya tafi.

Yau kwana na biyu a Wagini, ina cikin d’aki ina waya da Dr.

Jin Hajiya ta shigo tana sababi yasa nayi saurin yi yi mishi sallama.

Cikin tsokana na ce "Hajiya wai ke da waye naji kina fad’a, wa ya ta’ba min ke".

Cikin fad’a Hajiya ta ce "Ban sani ba, dan jakar uban ki, me kika sa min a waya ta na kasa kiran mutane, gashi kwana biyu kenan bamu yi waya da ‘ya’ya na ba, nasan haka kawai ba za su k’i kirana ba, sai dai in da dalili".

Zagin da Hajiya ta min ne yasa na fara dariya.

Ran Hajiyan Wagini ne ya k’ara ‘baci jin dariyar da nake mata ta ce "Au ‘yar jakar uba dariya ma na baki ko, ba zaki fad’a min me kika yi ma wayar nake ganin wani d’an jirgi a saman wayar ba, nasan ba wanda zai min aika-aikar nan sai ke".

Kasa daure dariyar nayi saboda wani zagin da Hajiyan Wagini ta k’ara min.

Ganin dariyar da nake mata yasa taci gaba da sababi ta ce "Ki yi dariyar ki da kyau, zan rama ne, dan ni da iyayen ki zan had’a ki, kwanciyar hankalin ki shine ki gyara min waya ta, ai nasan Soja sai yayi hak’uri dake, ko da yake shi ba ragon namiji ba ne" tana gama fad’ar haka ta fita daga d’akin tana ci gaba da fad’an ta.

Ni kuwa cewa nayi "yaushe zan bar wayar ki a geneneral mode sanandin su Abbu su kira ki su tambaye ki, ki fad’a musu ina nan ko ke ki kira su".

Dadi tun da ya bar gidan su Abbu tunani ne ya addabe shi, yanzu abin da yafi damun shi shine halin da yaya Faruk zai shiga idan ya riski wannan labarin, ga kuma rashin gani na da ba ayi ba, ya zama dole ya sanar da yaya Faruk halin da ake ciki dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa, shi kanshi shaida ne da irin son da yaya Faruk yake yi min, ashe shi bai sani ba d’an shi son maso wani yake yi wanda yafi ciwo, da irin wannan tunanin yayi tayi har ya k’arasa gida.

Samun Momi yayi da Anisa suna ta hira akan bikin, jikin shi ne ya k’ara sanyin ganin yadda kowa yake maganar yadda bikin zai kasance.

Guri ya samu ya zauna yayin da Momi da Anisa suka mishi sannu da zuwa.

Momi ce ta tashi ta nufi kitchen ta d’akko coconut juice wanda yaji madarar peak a ciki, k’anshi flavour ne kawai yake tashi a ciki.

Tsiyaya mishi tayi a glass cup ta mik’a mishi.

Amsa yayi ya sakar mata murmushi duk da damuwar da yake ciki amma ba lallai ne ka gane hakan a fuskar shi ba, kad’an ya sha ya ajiye ya maida kallon sa ga Momi ya ce "Rukaiyya ina so muyi wata magana dake, ina so ki yi wa maganar kyakkyawan fahimta".

Jin haka ya sa ta tattara natsuwar ta ga Dadi dan jin mai zai fad’a mata.

Anisa ce ta mik’e da niyar fita daga falon, Abbu ne ya dakatar da ita akan ta zauna.

Dadi ne ya fara maganar da cewa "Rukaiyya kowani d’an adam da kike gani da k’addarar sa, Allah na iya jarabtar bayin sa ta hanyoyi da dama dan ya gwada imanin su yaga ko za su iya cinye jarabawar su, to hakan ce ta faru ga Faruk…".

Momi ba ta gama jin zancen ba ta katse Dadi da cewa "Me ya same shi Alhaji, pls ka fad’a min abin da ya samu Faruk d’in".

Dadi ne yaci gaba da cewa "Ba abin da ya sami lafiyar shi, sai dai wata jarrabawa da take niyar samun shi ko ma in ce ta same shi, nan Dadi ya sanar da Momi halin da ake ciki kamar yadda Abbu ya sanar dashi.

Ran Momi ne yayi masifar ‘baci da abin da nayi, ita a ganin ta wannan wani rainin hankali ne aka zo musu dashi, sai da biki ya kusa za a ce na gudu kuma akwai wanda nake so, shi yasa tun san da Faruk ya fad’a mata yana so na ta yi mamaki dan tasan akwai wanda Anisa tace mata muna soyayya, abin da yasa ta bar maganar ganin Faruk bai fad’a mata wata matsala daga gare ni ba, ashe kuwa matsalar tana nan za ta ‘bullo.

Cikin fad’a Momi ta ce "Alhaji lallai Fatima ta ci mutuncin mu, yanzu akan Faruk ta gudu dan ni ban kawo ‘bata tayi ba tun da ba kaza ba ce ita da za a ce a gida an zo an d’auke ta, duk yadda yake nuna mata so shine za ta saka mishi da haka a lokacin da bikin su bai wuce sati biyu ba, sakayyar da za ta mana kenan na irin son da muka nuna mata tamkar yarinyar da muka haifa da cikin mu haka muka d’auke ta, shine za ta nuna mana na butulci irin na d’an adam, me yasa tun farko ba ta fad’a bashi take so ba, da tuni ban bashi hak’uri ya hak’ura da ita ba, to tun da abin haka ne Anisa ma ta hak’ura da Khalil duk da shi na san bai da matsala, tun da k’anwar shi ta guji jinin ta itama me za tayi dashi".

Ganin yadda ran Momi ya ‘baci yasa Dadi ya mata shiru, sai da ta gama fad’an sannan yaci gaba da cewa "Rukaiyya a matsayin ki na babba fushi bai kamace ki ba duk da nasan ke aka ‘bata mawa, maganar Anisa ta rabu da Khalil bai taso ba tun da su ba ruwan su a ciki, in za a ga mai laifi to bai wuce Fatima ba, laifin ta da na gani shine guduwar da tayi amma dan ta ce ba ta son Faruk ba laifi bane duk da ta wani ‘bangaren in aka duba yaci a ce ta so shi ko dan son da yake mata da kuma alak’ar zumunci dake tsakanin su, sai dai shi so ba ya duba wannan, ni yanzu abin nafi buk’ata shine a ga ita Fatiman".

Momi ce tayi saurin katse shi da cewa "Anya Alhaji kana son Faruk kuwa, wato kai ba halin da d’an ka zai shiga ka ke tunani ba, kafi buk’atar dawowar Fatiman, yanzu duk yaudarar da yarinyar nan tayi ma Faruk duk ba abin duba wa bane".

Murmushi Dadi yayi jin Momi na tambayar shi wai anya yana son Faruk kuwa.

"Hajiya ina ganin tambayar ki ba ta buk’atar amsa na tambaya ta akan wai ina son Faruk kuwa, nasan za ki fi kowa sanin irin son da nake ma Faruk, kar ‘bacin rai yasa shaid’an yayi tasiri a zuciyar ki, duk wannan maganganun ba su ba ne maslaha a gare mu, sanar da Faruk shi yafi".

Yana gama fad’ar haka ya d’akko wayar shi ya kira layin Faruk d’in, cikin sa’a ya samu numbar shi.

Bayan ya d’auka ne Dadi ya umarce shi da yazo Kaduna yana neman shi, yaya Faruk ya amsa mishi da yana nan zuwa insha Allah.

Ita kuwa Anisa mamaki ne ya kamata da jin abin da na aikata, ba ta zaci zan iya aikata kwatankwacin abin da na aika ta ba, tuni ta fara tausaya ma halin da yaya Faruk zai shiga, ita shaida ce a irin son da yake min.

Itama ta k’udurce a ranta za ta rabu da yaya Khalil ko da Momi ba ta fad’i hakan ba duk kuwa da irin son da take mai saboda a dalilin k’anwar shi yayan ta zai shiga wani hali.

Dadi ne ya kalli Momi ya ce "Kin dai ji munyi waya da Faruk d’in zai zo, ban ce ke ko Anisa ku kira shi a waya ku fad’a mishi abin da yake faruwa ba" yana gama fad’ar haka ya nufi side d’in shi.

Momi cikin damuwa ta kalli Anisa ta ce "Anisa kin ji abin da Fatima tayi ko? amma kina gani Dadin ku bai ganin laifin ta, kema kina da laifin ki Anisa, nasan baza ki rasa sanin wani abu dake tsakanin Faruk da Fatiman amma ba ki fad’a min ba, da nasan matakin da zan d’auka da wuri, yanzu ai gashi har dake za a jefa d’an uwanki cikin wani hali" Momi ta k’arasa maganar cikin takaici.

Ita kanta Anisa jikin ta yayi sanyi, tana ganin ba amfanin ‘boye ma Momi komai tun da yanzu tasan halin da ake ciki, dan haka ta zayyane ma Momi komai na tsakanin yaya Faruk dani, da irin matsalar da shi yaya Faruk yake fuskanta a guri na akan Dr Sadik, da kuma damuwar da yake shiga akan haka.

Jin wannan labarin da Momi tayi ya k’ara sa mata ‘bacin rai akan wanda take ciki, nan Momi taci gaba da fad’an ta da irin matakin da za ta d’auka akan wannan al’amarin.
[7/3, 23:16] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*




Please Login or Register in order to submit comment