Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mansoor*
*Marubuciyar* (Munafukin miji)
💖💖💖

*Da*

*Memcy Ata*
*Marubuciyar* (Ni da yaya Farooq)💞💞💞

*Ina jin dad’in yadda kuke son wannan novel d’in*

*Ana tare*.🤝🏽




*QUESTION OF THE DAY*

Wani sahabi ne yake fad’in Magana tazo daidai da saukar wa a cikin Alkur’ani mai girma?





7&8

Murmushin mugunta yayi ya ce "by the count of three ku fara up & down"
K’irgawa ya fara yi da 1…2….kafin yakai 3 har mun fara.

Mun d’au kusan 15 min muna up & down amma yaya Faruk bai da alamar dakatar damu.

Juyawa nayi na kalli Anisa da ta dage ba ta ko tsayawa, zufa sai zubo mata take yi ga k’afar ta sai rawar awilo take yi saboda gajiya.

Duk da nima a gajiye nake amma hakan bai hana ni tausaya mata ba kasancewar yadda ba ta son purnishment.

Rawar da k’afar ta taci gaba da yi ne yasa na kasa danne dariyar da take ci na, fashewa da dariya nayi ba tare da nasan dariyar zata fito ba.

Mamaki ne ya kama yaya Faruk ganin dariyar da nayi amma bai ce min komai ba illah mik’ewar da yayi ya nufi inda chargers wire d’in mu suke ya zaro d’aya daga ciki ya nufi inda muke.

Anisa ce ta fara kuka tana cewa "yaya Faruk don Allah kayi hakuri kar ka dake mu baza mu sake ba"

Wuce ta yayi ya k’araso guri na ya zuba min d’aya a jiki, ina jin saukar bulalan na daka tsalle na hau kan kujera amma haka yaya Faruk ya biyo ni ya k’ara zuba min.

Rawar a sosa mata na fara yi domin ko ta ina sosa jiki na nake yi, ji nake yi kamar an zuba min k’aik’ayi a jiki na.

Rok’on shi na fara yi ina cewa "yaya dan girman Allah da darajar su momi da daddy da kuma darajar matar da zaka aura da kuma girman kakin sojan da kake sa wa kayi hakuri"
Duk da ba ko wani lokaci yaya Faruk ke dariya ba amma a lokacin sai da yayi dariya sannan a lokaci d’aya ya d’aure fuska kamar bashi ba ne yayi dariya.

Kallo na yayi kamar bazai yi magana ba can ya ce "uban wa kike wa dariya? ko kin ga mahaukaci ne a gurin nan"

"ni ba da kai nake yi ba, Anisa nake ma dariya" na fad’a da alamar tsoro.

1-sitter ya samu ya zauna ya d’aura k’afar shi d’aya akan d’aya yana fuskantar mu.

d’akin ya d’au shiru kamar ba mutane a ciki, sai da ya gama mulkin sa sannan ya kalle mu ya ce "zan tausaya muku na laifin da kuka yi, yanzu sai purnishment d’inku na surutun da kuka sa ni, saboda kun san surutu bai dame ni ba, ni ba irin ku bane in ta zuba kamar parrot"

kuka muka fara yi muna bashi hak’uri saboda yadda k’afar mu ta gaji amma ko alamar tausaya mana bai yi ba illa juyowa da yayi ya ce "kuyi kneel down & raise your hand up, ku rufe idon ku, by the count of 2 ku fara"

ai kafin ya fara k’irgawa muka yi kneel down, gwiwa ta kuwa ji nake kamar ba jiki na take ba saboda tsamin da tayi.

Haka muka d’aga hannun mu muka rufe idon mu, a raina kuwa ban san sau nawa na ma yaya Faruk Allah ya isa ba saboda duk yadda ka ke neman mugu in kazo gurin shi, zance ya k’are.

Duk da ido na a rufe yake hakan bai hana hawaye zubowa a ido na ba saboda rabon da a bamu irin wannan purnishment d’in ko a school har na manta.

Mun d’au kusan 7 min a haka sannan muka ji sallamar yaya Khaleel, wani dad’i ne ya kama ni saboda nasan Allah ya kawo mai ceton mu saboda shi yaya Khaleel duk ya fisu hak’uri da wasa don in muna hira dashi kamar wani mate d’in mu muka maida shi.

Yaya Faruk ne ya amsa mai sallamar da yayi, nufo inda yaya Faruk yake ya mik’a mishi hannu suka yi musabaha kana ya nemi kusa da kujerar da yake ya zauna

"yaya sannu da gida? Yaya Khaleel ya fad’a.

Ya amsa mai da "yawwa Khaleel, ya school d’in?

"School lafiya lau" sannan ya juya ya kalle mu wanda duk mun galabaita saboda izayar da yaya Fauk ya mana kana ya juyo da kallon shi ga yaya Faruk yaci gaba da cewa "yaya Faruk ina neman alfarma a gurinka ka tausaya ma sisters duk da ban san laifin da suka yi ba na tabbata ba za su sake ba, ko saboda Anisa yaya ba ta jurar purnishment"

Juyo wa yayi ya kalle shi yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai da ya gama shan k’amshin sa sannan ya ce "Anisa kawai ka sani da zaka ce ba ta son purnishment ko ita Fatima an fad’a maka ba ta gaji ba"
Da mamaki Yaya Kalil ya kalle shi amma bai ce mai komai ba.

"Stop" abin da yaya Faruk ya ce mana kenan.
Kamar jira muke yi muka sauke hannun mu yayin da muka fara kuka.

Ummu ce ta fito daga side d’inta ta nufo main parlour inda take jiyo kukan mu.

Guri ta samu ta zauna ta kalli yaya Faruk inda take cewa "babban yaya kai da k’annen naka ne? hala wani laifin su ka yi"

Ta juyo da kallon ta zuwa gare mu tana cewa "ku kuma ku rufe wa mutane baki, kun cika ma na gida da kukan ku"

Yaya Faruk ne ya sanar da ita abin da muka yi.

Mik’ewa tayi ta na ce wa "Anisa da Fatima ai kusan halin su d’aya, ga rawar kai da ya musu yawa, gwara da ka hukunta su, gobe ba za su sake ba" ta mik’e ta koma side d’in ta.

Kallon mu yayi da wannanan murmushin na shi da ba ka cika gane me yake nufi ba sannan ya ce "zaku iya tafiya amma ku sani bayan sallar isha’i zan maku tambaya a note book d’in ku, idan ku ka kasa amsa wa, hmmm ya girgiza kai, ya ce ba sai na fa’da muku ba, ku ‘bace min daga nan"

Tashi muka yi muka nufi d’aki, inda na mik’e da k’yar na shiga band’aki na d’auro alwala na shimfid’a sallaya kana na kalli Anisa wacce ta kwanta akan gado sai lumshe ido take yi alamar gajiya da kuma bacci da yake son d’aukar ta,
"Anisa" na kira sunan ta.

D’agowa tayi ta kalle ni ba tare da ta amsa ba illah idon ta da yayi ja.

Cikin tausaya wa na ce ‘ki daure ki tashi kiyi sallah kin ga ma an kusa sallar magrib"

Wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi tana cewa
"Fatima bazan iya tashi ba, k’afa ta ciwo take min, pls ki kira min yaya Khaleel ya nemo mai gyaran targad’e"

Duk da nima daure wa nake yi amma hakan bai hana ni yi dariya ba na ce "wane irin targad’e a na zaune k’alau, kawai tsabar up & down ne ya yi aiki a kan mu"

Da k’yar na samu ta tashi ta d’auro alwala ni kuma na ta da sallah, ban san nima k’afa ta na ciwo ba sai da nazo yin ruku’u da sujada nan na gane ban da wayau.

Bayan mun idar da sallah ne na d'akko ma na man zafi muka shafa a k’afar mu amma duk da haka ba mu daina jin ciwon k’afar ba.

Yaya Khaleel ne ya shigo yana mana dariya yana cewa "wasu yau sun sha hukunci, wannan ko a barrack ne ai sai haka" ya sake fashe wa da dariya.

Ganin yanayin da muke ciki yasa ya tsagaita da dariyar cikin tausaya wa ya ce "serious na tausaya muku amma ku ma kun san hali kuka k’i yin extra lesson bayan kun san yana gari, kuma ku ka dawo gida kuna gulmar su shi da yaya Aminu, pls ku dinga kiyaye abin da za a muku hukunci kun ji sisters"

Da ma bai san haushin shi nake ji ba, ya ce wai yaya Faruk ya k’yale mu saboda Anisa, ni na zama on my own kenan, ba mai tausaya min.

Hararar shi na dinga yi, in naga zamu had’a ido sai in wayance, ashe ya lura da abin da nake yi, don haka yayi murmushi ya ce

"Fateemah kenan! na san fushi kike yi da ni saboda na ce a tausaya muku saboda Anisa, ko da ba na gurin ku ka yi deciding d’in dawo wa gida, nasan ke kika kawo shawarar"

Shiru na mai saboda ni a yanzu abin da na fi buk’ata shine in ci abinci kuma in gasa k’afa ta da nake jin kamar ba a jiki na take ba.

Anisa ce ta kalli yaya Khalil cikin galabaita tace "yaya Khalil pls kaje kace iya talatu ta kawo mana ruwan zafi a bowl da tsumma mu gasa k’afar mu ta tawo mana da abinci"

Tausayin ta ne ya kama shi saboda yasan Fatima tafi ta dauriya da kuma tsiwa don haka ya mik’e ya nufi kitchen da kanshi ya d’aura ruwan a electric kettle sannan ya juyo ruwan a cikin d’an bowl da tsumma a hannun shi ya nufi d’akin.
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💕


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽




*Wannan shafin na ba ku shi ne kyauta ‘yan kainuwa Writers*
*Allah ya bar mu tare*🤝🏽


*Anty Fauza*💕💕

*Ummy On top*💝💝

*Batul Adam Jatko*💖💖

*Aisha Machika*💗💗

*Sameena Aleeyou*💘💘

*Jamila Sama’ila Yusuf*💜💜

*Aisha Sada machika*💛💛

*Mrs Mansoor*💚💚

*Mom Hanan*🧡🧡

*Jiddah Wali*(cool)💓💓

*Fauxia MB*💗💗

*Halima MK*🖤🖤

*Wanda basu ji sunan su ba, mu had’u a next page, kuma ina yin ku sosai*.


*Fatan alkhairi gare ku*

*Xarah Auwal*💔💔

*Fadyla ingawa*

*Amsar da ku ka bayar daidai ne na question of the day*
*Amsar ita ce Sayyidina Umar*
*Allah ya k’ara ilimi mai amfani*



TUNATARWA

Kar ka/ki raina matsayin wani saboda gaba.

Kar ka/ki duba wanda ya fi ka/ki wadata, ka/ki tuna ka/kin fi wani.

Kar ka/ki zamo cikin masu asarar rana guda ba tare da sunyi salatin Annabi (s.a.w) ba.

Yi k’ok’ari ka yak’i shaid’an ta hanyar karanta alqur’ani domin kariya ne a gare mu.

*Wannan 'yar nasiha ce a gare mu*👌🏼



9&10

Ko da yaya Khalil ya kawo mana ruwan, gasa k’afar mu muka yi muka k’ara d’aukar man zafi muka shafa kana muka hau gado dan mu kwanta mu wartsake gajiya kafin a kira magrib.

Kallon mu kawai yaya Khalil yayi ya fita da alama tausayin mu yake yi, side d’in Ummu ya nufa ya same ta tana kallon tauraron d’an adam.

Sallama yayi ya samu guri ya zauna a d’aya daga cikin kujerar dake girke a d’akin.
Amsa masa tayi da murmushi a fuskar ta tana kallon shi
"Khalil ya aka yi ne" Ummu ta fad’a.
ya amsa mata da
"Ba komai Ummu"
ya ci gaba da cewa "Ummu pls ki sa akai wa su sisters abinci su ci, k’afar su ciwo take yi ga Anisa sai kuka take yi tana cewa tayi targad’e’"
Dariya kawai Ummu tayi ta ce "wane irin targad’e, kawai dai ina jin k’afar su ce ta musu tsami, ai maganin su Kenan tun da su ba sa jin Magana, gobe ba za su sake ba".
Mik'e wa tayi tana cewa "bari in je da kaina in kai musu yau su auta sun sha hukunci, ta fita tana dariya". kitchen ta nufa ta d’akko abinci a food flask da kwalin extotic mai sanyi da kofi ta nufi d’akin.

Samun mu tayi har mun yi bacci, gefen gadon taje tana kiran sunan mu, da k’yar na bud’e ido saboda yadda na ji barcin bai sake ni ba.
Ummu ce ta kalle ni tace "ya kamata ku tashi ku ci abinci magrib ta gabato yanzu zaku ji an kira sallah"

Cikin shagwa’ba na ce "Ummu k’afa ta had yanzu ciwo take min ga Anisa ma har yau k’afar ta na mata ciwo"
Ummu ta kalli Anisa wanda har yanzu bacci take yi tace "Fatima tashe ta"
Duka na d’aka mata a jiki.
Cikin firgita ta tashi tana cewa "dan Allah yaya Faruk kayi hakuri ba za mu sake ba"
Mai zanyi in ba dariya ba, jin sautin dariya ta yasa ta tashi tana harara ta.

Ummu ce ta ce "Ku tashi ku ci abinci, yanzu ai gashi kun yi baccin dole, sai da nace ma Fatima tayi hak’uri ta dinga wannan extra lesson d’in amma shine tayi kunnen k’ashi da Magana ta, ku kayi shawara ku ka dawo gida gashi nan kun ja ma kan ku hukunci, ku dinga kiyaye abin da za ayi muku hukunci kun ga yanzu kun girma"

Amsa mata muka yi da "toh Ummu insha Allahu zamu kiyaye"

Sakkowa muka yi muka ci abinci, Ummu na k’ara yi mana nasiha.

Jin kiran sallar magrib ne yasa Ummu ta mik’e ta tafi side din ta, mu ma mik’e wa muka yi dan ba da farali.

Ana sallar isha’i muka d’akko abincin mu a kitchen mu ka shigo dashi d’aki, anan muka ci abincin.
Muna gama ci muka rufe k’ofar d’akin saboda kar mu had’u da yaya Faruk tun da yace in anyi sallar isha’i zai mana tambayoyi saboda mugunta.


K’ofa muka ji ana knocking, cikin mu an rasa mai k'arfin halin da zai je ya bud’e k’ofar.
Jin maganar yaya Khalil ce yasa Anisa ta mik’e taje ta bud’e k’ofar.
Shigowa yayi ya zauna a kujerar dressing mirror d’ina ya na kallon mu, can ya katse shirun da cewa ‘yaya Faruk yace ku fito da note book d’in ku yana sauri ne.
Kallon kallo muka dinga yi, Anisa kuwa har hawaye ya fara zubowa a idanun ta, ganin haka ne yasa yaya Khalil ya ce mata "haba Anisa miye abin kuka, ni nasan tambayoyin da zai muku baza ku kasa amsa wa ba, nasan sisters d’ina akwai k’ok’ari, ina so ku nuna mishi ku guraye ne".
Jin yadda yaya Khalil yake fasa mana kai yasa muka samu k’arfin gwiwar tashi muka je muka d’akko littattafan mu.

Yaya Khalil ne a gaba mu kuma muna bin bayan shi.
Samun shi muka yi zaune yana daddana waya, mun d’au kusan 5 min a zaune ba tare da ya ce mana komai ba, sai da ya gama miskilancin sa sannan ya juyo ya kalle mu ya ce "sai yanzu ku ka gadamar fitowa bayan kunsan ina sauri ne zan tafi gida"
Ganin neman wani hanyar yake nema da zai ci zalin mu yasa muka ce "kayi haku’ri yaya"
Bai amsa mana ba illa mik’o mana hannun shi yayi alamar mu bashi note book d’in.

Bud’e littafin yayi ya fara jefo mana tambayoyi, cikin ikon Allah muka amsa iya fahimtar mu.

A gaskiya nasan mun burge yaya Faruk duk da bai fito ya fad’a ba amma ya nuna a fuskar shi.

Ganin bai samu abin da zai ce mana ba ne ya fara borin kunya "Allah ya taimake ku kun amsa tambayoyin da na muku da yau sai kunyi kwanan zaune, dan jikin kune zai fad’a muku".
Ya na gama fad’ar haka ya mik’e ya d’au key d’in motar shi ya bar gidan.

Godiya muka yi ga Allah da ya ku’butar damu daga hukuncin yaya Faruk.

Bayan fitar yaya Faruk ne muka kafa zancen shi, yaya Khalil ne ya fara mana dariya yana cewa "yau Allah ya taimake ku sisters, da baku amsa question d’in nan ba ina jin yau da yaya faruk ya ta’ba lafiyar jikin ku amma Allah ya taimake ku kun amsa tambayar".

Cikin shagwa’ba nace "dama kaima yanzu yaya Khalil ba ka son mu, ashe so kake yi a dake mu, bari Abbu yazo sai na fad’a mai"

Dariya ya fara yi yana cewa "sorry ‘yan k’anne na, ni ai naku ne har kullum, wasa nake muku"
Nan hira ta ‘barke a tsakanin mu da yaya Khalil.

************************************************************
A can kuwa gidan su yaya Faruk kuwa, Momi ce da dadi zaune a falo suna hira, sallamar Yaya Faruk ce ta katse musu hirar da suke yi, momi ce ta amsa masa sallamar, zama yayi a k’asa yana cewa "wash na gaji! Momi da dadi sannun ku da hutawa"

"Yawwa Faruk" dadi ya amsa masa.
Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "daman ina neman ka Faruk, za muyi muhimmmiyar magana da kai.
Jin haka yasa ya maida hankalin shi gaba d’aya gurin dadi don jin mai zai ce masa
"Faruk a gaskiya bana jin dad’in zaman da kake yi ba iyali kusa da kai saboda shekarun ka ya kai a ce kana da yara 2 zuwa 3, ka kalli Aminu ka girme shi amma yaran shi biyu, nasan aure nufi ne na Allah amma kuma da sa kai, saboda haka kayi k’ok’ari ka fito da matar aure tun kan in yanke hukunci akan ka, na ga kai zaman bai dame ka ba, duk mutum kamalar sa ba ta gama cika sai ya ajiye iyali.
Momi ce ta amshi zancen da cewa "ni kaina Alhaji zaman Faruk ya ishe ni, a ce mutum ya isa aure amma shi abin bai dame shi ba, sau nawa ina kiran shi ina mishi Magana amma bai d’au zancen nawa da mahimmanci ba, gwara kai da ka mai Magana wata k’ila zai fi jin maganar ka"
Cikin ladabi Faruk yace "Momi da dadi kuyi hakuri insha Allahu na kusa fad’a muku wacce nake so, akwai wacce na dad’e nake so amma ita yarinyar ba ta sani ba, amma insha Allahu komai ya kusa zama daidai".
Momi ce ta katse shi cikin fad’a tace "zancen banza kenan, yaushe za ka zauna kana son yarinya ka k’i fad’a mata, in ban da abin ka yaushe har ka fad’a ma ita yarinyar tasan kana son ta har kuka fahimci juna"
Dadi ne ya katse ta da cewa "k’yale shi Hajiya, tun da yace a bashi lokaci, Allah yasa muji alheri"
Ta amsa mai da "shikenan Alhaji na bar zancen, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi".
Dadi ne ya kalle shi yace "yaushe hutun naka zai k’are ne"
Next week zan koma insha Allah saboda hutun da aka bani ya k’are" cewar Yaya Faruk.
Nan suka ci gaba da hirar su cikin nishad’i.



*HMM READERS A RAINA NACE DAMA AKWAI WADDA FARUK YAKE SO KUMA WACECE*?
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💝💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



*Ku ma ban manta da ku ba*

*Miss Ayusha*💝💝

*Ummien Fauzan*💚💚

*Maimuna matar Abdoulaye AM*💞

*Ummu nabil*💜💜

*Hauwa A Usman*🧡🧡

*Sa’adatu Alkali*💙💙

*Mrs Makama*💓💓

*Mai Awara*💕💕

*Momyn Arfat*🖤🖤

*Nasiba Isma'il gawo*💔💔

*Sophiee*💘💘

*Balkin Fulani*💛💛

*Ana mugun tare*




*Ina tare da ku*🤝🏽

*Sakina* (Tauraruwar mace group)
*Badiyya daga kano*
*Maman Abdullahi Adnan*
*Saudat*
*Hussaina* (facebook)

*Da sauran wanda ban san su ba, kuma ina tare da ku*
*Ina mik’a sak’on gaisuwa ta gare ku na yadda kuke son novel d’ina*




*QUESTION OF THE DAY*

Wani sahabi ne ya sadaukar da dukiyar shi da rak’uman shi a lokacin da manzon Allah (s.a.w) yake cewa "wa zai ba Allah rance, ya biya sa ranar tsayuwa?





11&12

Washe gari mun so mu makara kasancewar har yau ba mu wartsake gajiyar purnishment d’in da yaya Faruk ya sa mu ba. Yaya Khalil ne zai sauke mu a makaranta daga nan shi ma ya wuce School saboda yace akwai wani assignment da zasu yi submitting da safe.
A hanyar tafiyar mu, yaya Khalil ne ke ta mana nasiha akan mu dinga kiyaye abin da zamu dinga ja ana bamu purnishment ko a dake mu saboda yanzu mun girma.
Yaya Khalil ne ya kalli Anisa yana cewa "Anisa yau in zan dawo sai in tawo da mai gyaran targad’en dan na ga ma ‘kafar kamar tayi sauk’i"
Dariya muka yi gaba d’aya saboda mun san yaya Khalil tsokanar ta yake yi.
Cikin shagwa’ba tace "haba yaya Khalil! Har da kai ake tsokana ta, bari in na koma gida sai na fad’a ma momi saboda tace ya daina bamu irin wannan purnishment d’in…."

Yaya Khalil ne ya katse ta da cewa "A’ah sister, ka da ki fad’a ma momi, yaya Faruk yana yin hakan ne dan taimakon ku da inganta ku, ba za ku gane haka ba sai nan gaba, kuma lesson d’in waec da neco da kuke gani, yana da matuk’ar mahimmanci a lokacin jarabawa, mutane ne basu gane ba"
Amsa masa muka yi da "insha Allahu zamu kiyaye yaya Khalil"
A raina kuwa addu’a nake yi Allah in ya tashi bani miji ya ba ni irin yaya Khalil saboda saukin halin shi dan duk matar da ta samu mai hali irn na yaya Khalil ta ji dad’i ba irin yaya Faruk ba, in ban da miskilanci da mugunta ba abin da ya ajiye.
Har ya ajiye mu a school muna hira cikin farin ciki da nishad’i kamar kar mu rabu.



Yau ma kamar kullum, in dai aka tashi break a school, ko ni in je class d’in su Anisa ko ita tazo class d’in mu. Yau ma hakan take saboda ni ce yau naje class d’in su.
Samun ta nayi tana rubutu na zauna kusa da ita ina cewa "ke kuma me kike rubutawa ne tun d’azun gashi har an fita break baki gama ba"
Amsa min tayi da "malamin maths ne ya ba mu classwork yace muyi mishi submitting kafin ayi closing, kin san shi da sa purnishment kamar yaya Faruk, na ma kusa gama wa"
Kallon ta nayi cikin zolaya na ce "sister wata shawara na kawo mana, mai zai hana yau kar muyi lesson mu tafi gidan ku tun da nasan momi baza ta bari ya dake mu ba ko ya samu purnishment tun da kinga bayan lesson d’in school muna zuwa ran weekend, ba sai mu dinga d’an hutawa ba…."
Ban k’arasa Magana ta ba Anisa ta zaro ido tana cewa "in kin ganni a lahira kai ni a kayi, ba inda zani, kina gani har yanzu k’afa ta ba ta daina min ciwo ba"
Hararar ta nayi ina cewa "ke wani sa’in ba kiyi ba, kin cika tsoro, idan muna nuna muna tsoron shi haka zai dinga mana, kin ga gwara mu nuna mishi mun girma ba kamar yadda yake mana kallon yara ba"

Anisa tace "ni fa ba inda zani, in kin ga na k’ara guduwa daga extra lesson to anyi closing d’in lesson d’in ne kuma kina dai ji Ummu da yaya Khalil suka mana fad’a akan haka shine zaki ce mu tafi kuma ai gaskiyar yaya Faruk ne da yake cewa ba mu girma ba, ni kam ban girma ba"
Ai ban san lokacin da na fara dariya ba ina cewa "ke ce dai ba ki girma ba amma ni kam na girma, kina gani zamu yi graduation d’in gama secondary school, yanzu ai mun zama big girls" na ci gaba da dariya ta.

Anisa ce ta harare ni cikin wasa ta ce "ke matsalar ki ba kya raina abin abin dariya (A raina nace kamar Fauxia mb ta Kainuwa writers) yanzu miye abin dariya, ai duk cikin girman ne, da yaya Faruk ya zuba miki wire a jikinki ki kace yaya Faruk dan girman Allah kayi hakuri, dan darajar momi da dadi da kuma darajar matar da zaka aura da kuma darajar kakin da kake sa wa"

Dariya muka fara yi saboda ni sai a lokacin ne maganar ma ta ban dariya, cikin zolaya na ce ai gwara ni k’afa ta ba tayi rawar awilo ba kuma ni ba a tashe ni a barci na ce dan Allah yaya Faruk kayi hak’uri ba za mu sake ba"

Dariya muka sake fashewa da ita tare da tafawa yayin da Anisa ke cewa "in k’afar ki ba tayi rawar awilo ba amma ai kinyi a sosa mata san da ya zuba miki bulala"

dariya muka k’ara yi muna maida abin da ya faru jiya.

Aisha k'awar mu ce ta nufo inda muke tana cewa "kuna jin dad’in ku, wannan hira haka da dariya fa"
Murmushi nayi na ce "ko ke kika ji abin da ya faru sai kin yi dariya" nan na zayyane mata yanda muka yi da yaya Faruk, ita ma dariyar tayi inda muka ci gaba da hirar mu har aka buga k’ararrawa na koma wa class.



Tun da yaya Faruk ya dawo ba ni da sukuni domin a takure nake, d’an chat d’innan da nake yi ba dama sai dai in yi shi a ‘boye, gashi ni ba inda nake zuwa, in dai yana gidan mu to ni ina d’aki saboda kiyaye abin da zai tanka min, ga wata tsurfa da ya fito da ita, in dai yana gidan sai ya tashe ni na dafa mai abinci ko yace wanda aka yi ba shi yake marmari ba ko yasa ni had’a drink.
Wannan hutun yaya Faruk d’in ya zaman min bak’in hutu saboda ya hana ni sakat da jin dad’in rayuwa ta.


Yau Allah ya amsa addu’a ta saboda jiya muna hira a falo naji Abbu yana fad’a ma Ummu yau yaya Faruk zi koma Abuja, dad’in da naji bai misaltuwa saboda nasan zan samu sauk’i na takurawar da ya min.



Ina zaune a falo ina kalllan philliphine series film na (endless love), wani scene da aka nuno shi ya d’auki hankali na inda aka nuno jenny kwance a jikin johnny san da

Please Login or Register in order to submit comment