Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana son na rasashi yayi mgnr kamar zai zubar da kwalla "jaguwa ba kamar sauran mutane bane , gabad'aya alamuransa akwai lisssfi  ,yana da kaifin kwakwaluwa bazai bari mu rasa shi ba saboda yasan muna son shi "jabir nasan da haka nasan yana son mu duk duniya bashi da aminan da suka kai mu but bansan me yasa yayi irin wannan taurin kan ba ,nayi kokari fahimtar dashi nayi komai akan ya bar wannan aikin amman yaki ya kasa fahimtata jabir zuciyata na cike da tsoro yanzu idan wani abu ya sameshi  adalilin tango gote ya zanyi da rayuwata ? "Anas kana tsoro da tausayinsa with  reason nima zuciyata tana cikin damuwa amman abinda na lura dashi  yana sane so yake mu rasa shi inji cewar kamil wallahi idan wani abu ya sameshi bazan taba yafe masa ba yayi maganar yana goge hawaye "ba haka bane kamil  Anas ya fada shima hawaye ne cike da idanunshi "zai dawo   zai dawo anas ya dinga maimaitawa zai dawo da kafafunsa domin shi din ba mutun bane kamar sauran mutane mutun ne mai matukar amfani ga rayuwar mutane yayi handling din matsaloli a rayuwar data gabata ina da tabbacin zai dawo da kafafunsa suka rungume juna suna kuka ..

****
Alhaji tanko gote  zaune a cikin  tangamemen parlou'n sa daya ji kayan more rayuwar duniya tare da manya abokansa kowane hannunsa rike da glass cup  suna kurban ruwan  win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da'aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan  zagaye  yaje da flowers sannan  yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa  .

shewa ne ke tashi acikin parlou'n "mutunen  da zasu ce meye namu acikin lamuran   kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata    dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har  zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu,   maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati  "wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote   "muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so  acikin kasar nan da bamu samu ba  da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ?  "babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba'a so dole a dama damu  kuma muyi abinda muke so  "wannan gaskiya  ne ...

"waɗan kananun maganganun yasa  nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so  na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote   suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup  ya dauki  wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa  sannan  ya ɗauki wayar  ya soma magana kasa kasa   "ranka ya dade  aka fada  daga dayan bangaren na turo  da kudaden  yanzu haka yarona na bakin get din  estste " oooooo my  god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad "am sorry  sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali   "haka ne   kana da  fahimta dan   a daidai wannan lokacin ina tare da  shi wanda zai saka hannu   "to kagani sai ka  bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa .." shikenan  a gama karkaji komai  " zan bada umarnin a shigo da yaron  yanzu ya fada yana  canza magana "you have to understand that you should  know that what someone like us can do  in this land be left ,ya maida  wayar zuwa dayan kunnenshi  tare da shiga karamin parlou'nsa ya  bude window dining area  "nasani ranka ya dade  nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi" ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo  tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin "cewa  I will call you later  uhm alright "my dear  ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi "darling  har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade  kamar sauran lokuta karka  ɗauki lokaci mai tsawo  bana son ka  dade ka dawo da wuri   duk yau sati ne fa da dawowarka  "uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba   "really ?  ya gyada mata kai "idan zan dawo zan biya ta itly  "kai dan Allah tayi maganar a shagwa'be "dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal  ta soma tafiya tana farinciki  yana biye daita  abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka "hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb"akwai wani yaro  yana ....
"Okay sir gashi nan ma "yauwa ku barshi ya shigo "okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa ",zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara  ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin  d'aga wayar  gabansa yayi wani irin muguwar  faduwa  yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.

Saurin mik'ewa yayi yana kallon parlou'n kansa na juyawa a matukar zabure amaryarsa ta mike "what happened ?  "gabana ke fad'uwa da matsanancin karfi "gabanka ke faduwa ta maimaita tana kallonsa" ina jin kamar takun mutane "how is there tayi maganar tana kallon kofar parlou'n  tayi maganar a tsorace ganin haka yasa ya riko hannunta "colm down never mind  "what  do You mean never mind ?  tayi maganar a tsorace "don't leave the parlou "ban fahimceka ba  ? " Ina zuwa  yayi foring head d'inta kiss "i think  I will back don't leave the parlou   ya  juya ta riko hannunsa da sauri  "karki damu zan dawo yanzu ya sake rungumeta ya mannata mata kiss  ita dai a sanyaye ta bishi da kallo "meke faruwa ne haka daga gabansa na faduwa yace na tsaya anan na jirasa zai dawo  tafiya yake gabansa na faduwa ya biyo dogon coridor da zai kai  mutun wata kofa data fuskanci hagu ya fito a hankali yana dube dube har inda wata motar take parke yana dubawa gabansa na faduwa wanda duk sanda yaji haka  yasan akwai wani mummunar abu da zai samesa    cigaba da dube dube yayi  a hankali ya juyo yabi wani hanya stil bai ga kowa ba bai ga komai ba, ya tsaya yana waige waige hagu da  dama sannan ya sake juyawa ya nufi kofar daya biyo "Alhaji tanko gote.........."
yaji sauti daga bayansa cak ya tsaya tare da juyowa gabansa na wani irin dokawa a hankali Jaguwa yake daga kafafunsa "waye kai ? tambaya kake ko neman sani ? "duka ya fada cike da tsoro , jaguwa yayi murmushin  "colm don Tanko gote  zaka san komai cikin second daya yayi mgnr  haɗe da ciro bindigarsa daga maajinta  ya soma  gyarawa  yana kusanto inda tanko gote yake tsaye a matukar tsorace yake kallonsa  da bindigar hannunsa alama su shiga ciki yayi masa babu mutsu ya juya Jaguwa  na biye dashi har suka shiga parlou'nsa na uku ya tsaya " ba wani abu ne ya kawoka ba illa kudin da'aka ...
"Dakata kafin wannan kamar baka ganeni ba ?ya girgiza masa kai "Jaguwa yayi murmushin "daman mutane irinka basa iya gane mutane abinda yafi haka ma zaka iya saboda mutun azzalumi irinka ba lallai ne ya zamanto mara mantuwa ba well ba wannan ne abinda ya kawoni ba shiga ka fito dan zuwa yanzu ka fahimceni "sosai ai idan kudi ne zaka samu har sai kabari ni Dai ka barni da Raina da lafiyata "ban soma wannan aikin dan na dauki ran wani ba sai dai a rashin sani amman   kai wallahi  zan iya daukar naka  take jikin Tanko gote ya sake ɗaukar rawa ....

"   muje inda kudin suke jikinsa na rawa ya nufi wani daki suna shiga sanyi ac ya ratsasu buhu ne cike da kudade  daban daban na kasar  negeria  da kasashen ke tare ka ɗauki duk wanda yayi maka "Jaguwa yayi murmushin  yana shafa qirjinshi da hannu "ai gaba-daya zan wuce dasu dan haka   ka soma ɗauka  daya bayan daya "ka bari na bada umarni  a  kai maka  su cikin motarka  tana ina  "ance maka ni karamin kwaro ne karka bata min lokaci ka soma abinda ya kamata kafin na fasa maka kwakwaluwa .....

Darling's💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️09

.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe  ya cika zuciyar Alh tanko gote  mutumin daya shahara a cikin fadin duniya  da aikata masha'a bangaren neman mata  cin amana  ,makirci, son abun duniya  ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda  abun duniya  ,idan  kana son ka  kasance dan ta'adda  mai lasisi da  neman gindin zama acikin kasar nan  nemi  tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne  fayde zama dilan kwaya  da sauransu nemi tanko gote  duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............

Duk  wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon   shekaru yana aikatawa adalilin  connection din da yake da acikin yan siyasa   babu  wani mutun ko  ɗan fashin da makamin  daya taɓa kawowa  rayuwarsa farmaki  ,
hasalima yana jin  sign dinsu ajikinsa  kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi  yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa ,  jiki a matukar sanyaye  ya soma jan buhun  kudi  jaguwa na gefensa  "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki  wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... "

"Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin  da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga  yana dauko  buhun kudi   har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e  hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar  jaguwa .

Jaguwa ya manna  gun a gefen brain  d'insa  "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka  Alh tanko gote ya  kalleshi a  matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi  "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan  kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai  kar kwakwaluwarka tayi  maka  wanann banzan  tunani dan nasan  daraja da kimar  dan adam ba irinka ba wanɗa  yake  danne hakin dan Adam domin son  duniya , a  hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a  gaba-daya sansar  jikinsa yana tunanin "waye shi  wannan  ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani    har suka shigo parlou'n  zuciyarsa na cikin frigici  , yayinda har zuwa  wannan lokacin amaryarsa na tsaye  hankalinta a matukar tashe  tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa  yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama  kyarma ..

"kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki  ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni  gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa  "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan  , sai yadda kika so za'a yi dan  tanko gote  mijin tace ne agurinki  sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan  ya kamata ki san  ko waye wanda ke tsaye a gabanki  duk da idanunki a halin yanzu a makance suke  ,"sunana jaguwa  akaro na farko da wani  a duniya zai  san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "

" a wasu shekaru da suka gabata anyi  wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da   kane gudu  hudu  namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu  sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa  ya cigaba da magana  "abinda yasa na dan  baki  labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata  sai dai na barshi  da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba " idan mijinki  yayi  kuskuren ko gigin sako jami'an tsaro ciki aikina  domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan.....
da sauri tace" he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace    "shiga muje kou " Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda  Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya  "karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin  mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma  mutsu zaka min   yanzu na harbeka  na harbe  kaina muyi  mutuwar kasko ,babu mutsu  ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin  mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ....

Suna karasowa bakin get securities suka tsaida shi  warning  glass din bangaren Alh tanko gote yayi suna ganinsa suka shiga rigerigen kawo gaisuwa cike da girmamawa, daya daga cikinsu ya  bude tafkeken get din estate din jaguwa  ya fita  .......

Tafiya kaɗan jaguwa  yayi ya soma motsa lip's d'insa "nasan kana mamakin kwarewata kou? tanko gote  yayi saurin gyada  kanshi " karka yi mamaki duk acikin rashin imanin daka dasawa zuciyata ne , idan har baka tuba bisa ayyukan da kake shukawa a doron duniya ba, ka zuba ido zaka haɗu da wanda zai daukeka daga doron duniya gabad'aya ..
ya k'arasa maganar yana murmushin gefen baki  murmushin dake   kashe zuciyar yammata dan duk sanda yayi irin wannan  murmushin dole kaji ya shiga ranka sannan a take zaka rikice akanshi  ,yayinda shi agurinsa duk sanda yayi irin  murmushin to ya samu nasara ne akan aikinsa ,wayarsa ce ta soma babriting  ya   tura hannunsa d'aya cikin aljihun wandonsa ya ciro wayar  sunan Anas ya gani  yana yawo akan screen din wayar, maida wayar yayi  ya ajiye batare daya ɗauka ba sai da suka fita daga  area estate din sannan  jaguwa ya tsaida mota  a gefen titi  "fitar min a mota har yanzu  bazan hanaka kiran headquater na police ba ka kira  ........"
Kamar jira yake ya bashi umarni ya bude murfin motar jikinsa na rawa ya fita ya tsaya a gefen titi  jaguwa ya fixgi motarsa a guje ya barshi tsaye yana bin bayan motarsa da kallo   ....

Bangaren su Anas kuwa  sun shiga tashin hankali mara misaltuwa saboda ganin jaguwa yaki ɗaukar kiransu dan babu wanda bai yi amfani da layinsa ba amman jaguwa yaki ɗauka shi ana shi so yake  yayi surprise dinsu kusan fitowa suka yi daga cikin gidan suna shawagi a wajen unguwar kowane zuciyarsa cike da matsanancin tashin hankali jubi ne yace "kunga irin halin nasa ko?  "Ban san me yasa yake mana haka ba ana kiranshi yana kin ɗauka "karkace haka bakasan halin da yake ci ba a irin tsoron dake estate din ya cancanci fiyye da haka mu dai mu dai ya dawo lafiya shine kwanciyar hankalinmu inji cewar Anas wanda yayi magana hawaye na gangaro masa ....
ita kanta tanweer haka ta kasance zuciyarta na bugawa da karfin gaske  ga zazzafan zazzaɓi daya ziyarci  jikinta haka nan ta dinga jin wani iri ajikinta idanunta ta lumshe tare da kamkame jikinta guri daya zuwa yanzu zuciyarta cike take da kewar gida ..

Haka ma can gidan minister of health   Kuka sosai Hajiya zainab take  Alh Abubakar   shima kuka yake babu mai rarrashin wani ganin Alh Abubakar na goge hawaye yasa hajiya zainab ta saki wani gigitaccen kuka mai karfi tace "nashiga uku ni Zainab diyar tawa kwaya daya take hannu yan fashi da makami yau kusan kwana biyu Allah idan wani laifi nayi maka ka hukuntani ni kad'ai karka hukunta yarinyata dan batayi laifin  komai ba ,saurin toshe  bakinta Alh Abubakar yayi "haba zainab karkiyi sabo mana  kaddara ce kuma tana kan kowa  tanweer will be fine da yarda Allah lafiya zamu ganta ina iyakacin kokarina akan lamarin ta ko ina jami'an tsaron na kan bincike sannan nasa a tsananta addu'a bana jin tanweer na cikin damuwa kamar yadda muke ciki ,nasan killa suna bukatar wasu ƙarin  kudade ne  daga garemu yasa suka riketa a shirye nake da ko nawa zasu bukata zan mallaka musu komai dana mallaka akan tanweer dan Allah ki kwantar da hankalinki "wani kwantar da hankalinka  zanyi .."?
"Yan fashi da makami sun ɗauke min diyata kwaya daya tal yarinyata mafi soyuwa acikin raina ta yaya kake tunanin zan iya kwantar da hankalina ?
" waɗan nan  yan sanda dake rike da case din  basu san aikinsu ba basa komai kawai lamuran gabansu suke idan bazasu nemo min yarinyata ba ni na fita na  nemota a duk inda take,  gabad'aya ta gama fita haiyacinta sambatu kawai take zubawa  hawaye na gangarowa daga cikin kwayar idanunta "wayyohlly tanweer ko a wani hali kike ciki" ?"Allah kasa tana cikin koshin lafiya , Allah kasa basu taba min lafiyarta ba .."

Hajiya Zainab ta zabura daga zaunen da take  ta  mike tsaye  kamar an mintsineta jikinta na wani irin  rawa ,ta soma neman  police headquater ganin take kamar basa komai akan bincike wasu abubuwa take kamar zarariya ko mahaukaciya sabuwar kamu ..

"Sp me  ake ciki akan batun  'batan yarinyata har yanzu shiru  banga aikinku ba ?" idan har haka aikin police yake hakika bashi da wani amfani gareni  yau tsawon kwana biyu har yanzu babu wani tsayayyen magana akan batan yarinyata  "
"muna kan aiki ranki ya dade ya fadi haka yana cizan gefen lip's dinsa da tsotsa geyarsa  "dakata ni ba wannan na tambayeka ba Kawai inda yarinyata take nake son sani  tayi maganar wasu zafafan hawaye na sake wanke mata fuska "ranki ya dade hakuri dai zaki sake yi, babu wata hanya da zamu samu damar gano inda waɗan yan fashi suke sai  Kira daga yan fashi domin bukatar wani abu daga gareku  ta haka ne kawai  zamuyi saurin kamasu " Alh Abubakar dake tsaye a bayanta a tun sanda ta soma magana yayi gyaran murya ya amshi wayar hannunta yayi disconneting din kiran  "kiyi hakuri zainab tayi saurin zubewa ajikinsa tana kuka"yarinyata tanweer " "inshallahu za'a kamasu nan kusa ,
Dole akamosu sannan  dole a hukuntasu da hukunci mai tsanani domin  laifinsu daidai yake da wadan da  sukayi kisa..

****

Gudu jaguwa yake akan titi  ya yaga wata mota baka kiran marcende C class  na bin bayansa duk inda yabi sai motar tabi a karshe ya dauke bakin glass ya rufe kwayar idanunshi ya dauki hanyar da zata kai mutun aja ,gudu yake sosai har ya 'bacewa motar ya bi wata hanya mai ciyayi ya ja numfashi ya fesar jikinsa na bashi Alh tanko gote ya kira mahaikata, yanzu kam a hankali yake murza stearing motar yana sakin  murmushin cin nasara  Idanunshi ya ɗan lumshe ya ci-gaba da driving dukkanin alamu ya nuna yana cikin jin dadi ya gama da Tanko gote bai yi tunanin abun zai zo masa  cikin sauki ba sai gashi yayi nasara kara lumshe idanunshi yayi .....

yayinda sp yusif ke tsaye a cikin wani kango sanye da bakin suit tare da wasu daga cikin yaransa da suka biyosa aiki daman kuma ya rabasu kashi kashi ne kowanensu da bangaren daya ɗauka ,wayarsa ce  tayi ƙara ya ciro wayar daga aljihunsa cikin sauri yana duba screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya dauki kiran da sauri tare da mannawa a kunneshi "hello "
"Yes noted "
Inspector hasan dake fuskantar shi yace "how far ?
"We have to move immediatly "boss there won't be a problem there be danger today let us move ,let's move suka faɗa gaba-daya a hankali motar Jaguwa ke gudu ganin hanyar so silet ga duwatsu kaca kaca dole ko yana son yin gudu yabi a hankali yayinda yan-sanda ke la'be hagu da dama domin ƙoƙarin cafkarsa ..

A tsanake sp yusif ya fito daga maboyarsa ya sha gaban motar Jaguwa hade da tsaita bakin bindigarsa ga glass din motar Jaguwa slow  motar Jaguwa ta koma tafiya a hankali har yayi kusa da   sp cikin haka yaran sp dake boye hagu da dama suka bayyana suka saita bakin bindigarsu pistor  "crack and shut basu tsaya wata wata ba suka budewa motar wuta bisa umarnin da'aka basu harbi motar suke da iyakacin kwarewarsu har sai da suka tabbatar da sun yiwa glass din motar ratsatsa...

DARLING'S💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️10

...A hankali  sp  yusif ya sauke   bakin  bindigarsa  yana  haki  yana takowa a hankali  har ya karaso jikin  murfin motar jaguwa  ya ja ya  tsaya tare da d'aura  hannunsa ɗaya a  saman mota  "the wages of sin is death ......."
ya  furta haka yana duban inda  yaransa ke tsaye rike da bindiga   "yau  dai munyi nasara  kashe tantirin  ɗan fashin daya addabi  kasa da kasa   ,Allah na gode maka daka bani dama da ikon kawar dashi daga doron duniya , isar da gawarsa headquater  ma  wani  matakin d'aukaka ne  garemu ,na dade ina addu'a akan zuwan wannan rana sai gashi tazo mana  cikin sauki dole  mu  samu double promotion...... " ya karasa maganar yana kallon sararin samaniya zuciyarsa fes cike da matsanancin farincikin samun nasara .

   "ya sake buɗe  bakinsa da niyyar sake yin magana  yaji an daki  murfin   kofar motar  da karfin gaske   kofar ta buɗe wanda hakan yayi sanadiyyar da hannun  jaguwa ya bugu da murfin kofar dashi kanshi sp  yusif dake tsaye  yayi taga taga ya koma baya sannan ya tsaya bisa kafafunsa yana kallon motar  .

Mutuwar tsaye suka yi gabad'aya  suna kallonsa take  bindigar hannun sp yusif ta subuce  yayi saurin sake  ja da baya idanunshi na kan jaguwa dake ƙoƙarin fitowa daga cikin motar,  duk ilahirin jikinsu rawa yake har sp yusif wanda hankalinsa kusan yafi na sauran tashi dan yanayin bugawar zuciyarsa da yanayin tsoronsa sai ya baka mamaki tamkar ba jami'in tsaro ba  "

  cikin isa da izza jaguwa  yake takowa zuwa inda sp yusif yake tsaye , ya tsaya nisa kaɗan dashi wanda bai fi taku biyu su fuskanci juna ba  , idanunshi dake a lumshe  ya  ware su fesss  akan  sp  yusif yana ciza gefen  lip's d'insa na kasa,sp   yusif  ya kalli jaguwa  kamar zai yi kuka saboda gigita da ganinsa a raye da yayi , tunda yake bai taɓa ganin abinda ya d'aga masa hankali irin wannan ba , "bai taɓa ganin dan adam din da aka yiwa harbi irin wanda suka yiwa motar jaguwa ba amman ya rayu har ya samu damar fitowa  daga cikin motar cikin isa da izza ,tabbas yasan akwai wata a kasa ,wannan abu akwai tsarkakkiya acikinta     "

  Jaguwa  ya had'iye dariyar sp  yusif dake  neman kufce masa saboda gabad'aya ya gama karantar yadda sp yusif da yaransa suka tsorata dashi  ,dan gabadaya fuskokinsu ya sauya daga farinciki  zuwa matsanancin tsoro da firgici  kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tashin hankali mai tsanani ...

"waye  kai  sp yusif karaye  ?

Please Login or Register in order to submit comment