Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bare baren kallon da kikyi wa mutane Kmr zaki cinyesu ya sake bata umarni ta narke masa fuska  alamun baza tayi ba "ke wasa nake dake  ne ? nan take tayi kamar yadda ya umarceta ta shanye ruwan tasss ta rike cup din tana kallonsa ," kije ki ajiye cup din ki dawo,tana fita ya zaro kwalin sigari acikin aljihunsa ya kunna yana zuka a hankali har ta shigo a matukar tsorace take dubansa "danuwa daman kana shan sigari ne ?meye sabo aciki ? ai  duk suna cikin munanan dabi'una dana fada miki ko ma nace kadan daga ciki dan idan kikaji sauran ko kika gani bub zuciyarki zatayi ta buga "babu komai ina sonka a haka dan ni ko warin sigarin ma banji ba ta fada tana kokarin zama “bala’i ! Ya fada a kasan ranshi yana kallonta a kaskance abinda tanwer take mugun kyama shine ita wai ko warinsa bataji ba ?“nace ki zauna né ? ya fada a matukar fusace tayi sauri ta mike tsaye tana dubansa ya cigaba da abinda yake batare daya sake cewa komai ba ."

Bata  zauana ba  ta cigaba da tsayuwa tana dubansa  tana murmushi d'an duk abinda yayi mata bata ji zafi ko haushi acikin zuciyarta  ba bahasalima dadi taji dan tana mugun son kusancinta dashi  wani irin kallon soyayya take masa idanuwansa suna matukar mata kyau a duk sanda ta kallesu sai taji kamar ta sunbaceau amman babu hali  ya mike tsaye ya fito itama ta biyosa abaya sai ga ammi ta dawo "a'a yaushe kazo adnan ?Na  dan jima da zuwa ya fada yana shafa sumar kanshi ina kikaje? "nan kusa na shiga nayi barka  ne jikar gidan baba yaro ce ta haihu .ta shiga ciki  bangarenta hasera ta biyota da sauri tana yi mata rada shima dole yabiyota  bangarenta ta  zauna akan kujera me zaman mutun biyu suka gaisa ta tamvayesa aikinsa da abokan aikinsa duk yace mata suna lfy ta kira hasera "ki kawowa yayanki abinci mana  "aa ammi a koshe nake daman akwai wani aiki da zamu fita ne yana da matukar hatsari muna bukatar adduarki.
Aikawa nan take  ta shiga zubo masa sun dan ta'ba hira yace  "ammi ni zan wuce tô shikenan adnan allah yayiwa rayuwa albarka ke hasera kibi yayanki ya kaiki shopping din tunda baki da me kaiki dan allah ka sauke min hasera a wannan plaza din dake ayabo zata dan yi siyayyan kayan amafninta ne idan ma da hali ka tsaya har ta gama ka dawo min daita kaji dan alabarka ."

ya hade rai sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa sai dai bai amsa mata da zai kaita ba ko bazai kai ba  har sanda hasera ta shigo falon "dan allah ku tafi tare mana kaji yarona ai ba kullum né zaka dinga kaita ba  yau ne kawai ta fadi haka ne saboda ganin yadda ya hade rai ".aransa yace zamu fita tare amman babu inda zani daita a rabin hanya zan ajiyeta na qara gaba ".

Muryarsa a matukar hargitse yace "minti biyar na baki ki shirya idan ba haka ba sai dai ki nemi wanda zai kai ki ya fada yana shan kamshi tare da zira hannunsa daya cikin ajihinsa "kiyi maza ki shirya ki fito tun kafin ammi ta karasa maganar ta fada daki a wulakamce yabi bayanta da kallo sam sam bata da natsuwa da kamun kai wannan sai tanwer ita kuma dan taga ta samu kanshi shine take son juya zuciyarsa da rayuwarsa."

Minti biyar din ma bata gama cika ba ta fito da sauri kamar an korota yayi gaba yana sake yiwa ammi sallama kanta kawai ta girgiza wannan zuciya bata san ranar da zai daina ta ba abun zuciya da wanda bana zuciya ba duk fushin né agurinsa allah dai ya kawo maka sauki ta kalli haseera dake kokarin sanya baby shoe akafafunta "kiyi sauri fa kinsan halinsa zai iya wucewa ya barki ki dai san yadda zakiyi ki dan shawo kansa ku fahimci juna dan ina son ayi komai cikin kankanin lokaci a wuce gurin qarar hon din motarsa yasa ammi ta takaita maganarta "maza wuce gashi can ya fara  danna hon dinsa me hargitsa lissafi da sauri tayo waje ta bude murfin mota "kayi hakuri please na tsaya saka takalmi ne "wa ya tambayeki wannan shirmen sannan da zaki wani bude min mota nace ki shiga ne ?ke me yasa baki da natsuwa ne bare wani abu shi class?ranta yayi mugun mugun baci zuciyarta ta soma zafi da tuttukin bakinciki amman dai ta danne ta tsaya tana dubansa batare data shiga din ba ,shima kallonta yake yana son yaga wani abu ajikinta wanda zai dauki hankalinsa ko guda daya kawai ya aureta ya manta da wata tanwer a rayuwarsa amman sam ya kasa hango komai bare ya dauka zallar shirme ne ke tattare daita sai daya gama wulakantata sannan ya motsa bakinsa"shigowa !"
A ranta taja tsaki tana cewa duk ka gama iskancinka da wulakancinka zaka shigo hannu ne zaka gane baka da wayo sai kaga kudi kace kashi ne dan iskan me daurin kai da zafin zuciya kawai ta shiga ta zauna bata gama rufe murfin motar ba yaja da gudu tayi sauri ta qarasa rufewa tana dubansa kamar zatai kuka ."

Gudu kawai yake a natse akan titi batare daya waigo inda take zaune ba bare ya kalli fuskarta ta waigo a tsanake tana kallonsa da kallon  hannunsa daya dake kife yana motsawa a hankali ,taji kamar ta daura hannunta aka kyakkyawan hannunsa masu matukar haske da sheki  ,wani sanyi dadi ke ratsata hade da sanyi ac wanda ke sake tsokano da matsanancin soyayyrsa  dake daskare acikin zuciyarta ,hagu da dama shine kawai zuciyarta take muradi wani irin tuqi yake cikin salo me kashe wa duk wanda ake tukawa jiki .”
sai da sukayi rabin hanya taga ya tsaya a tsakiyar titi batare daya kashe motar ba sannan bai kalli inda take ba "maza sauka ki kama gabanki "
A matukar tsaro ce ta kallesa "bana da kudi ajikina fa tayi Kmr zatai kuka wani abu ya daga a gefensa ya ciro bandir din yan dubu day day na dubu dari ya daura mata akan cinyarta "ki sauka zaki samu wata motar da zata kai ki duk inda kike so kai tsaye dan ni bani da wannan lokacin "haba danuwna me yasa zaka min haka ?Sam bai kyautu ba da zaka barni anan abun sam babu dadi "Shiiiiiiii bance ki dameni da hauka ba just ki fita nace kuma karki qara kirana da danuwa kirani da sunan da kowa yake kirana dashi okay dan ni ba danuwanki bane ".

"Wai ma me yasa ka tsaneni baka sona haka ?,me na rasa ya adnan ?tayi masa tmbyr tana tsareshi da idanunta "amman daka soni da karka soni duk daya ne  aurena ne dai  babu fashi sai ka aureni kuma sai kayi rayuwar aure dani tamkar sauran ma'aurata "ai bazaki ta'ba samun wannan damar ba arayuwarki ,
oya dauki kudin nan kiyi out  yayi maganar a tsawa bata san sanda ta wawiro hand bag dinta ta fito ta koma gefen titi ta tsaya tana kallonsa yaja motarsa ya qara gaba da mugun gudu.”

Hankalinta yayi kololuwar tashi  da gatanta da komai arzikin ma da yake takama dashi byn mahaifinta ne silar samunsa da ba dan shi ba da yanzu killa ma bara suke yi akantiti gashi yace shi ba danuwanta bane , taji kamar ta kira mahaifinta ta fada masa wulakanci da yayi mata "amman kuma idan kika kira zaki lalata komai dan adnan ba mutunci garesa ba zai iya fadawa mahaifinki ido ido baya sonki alhalin shi bai san da wannan matsalar kinga kin kunnowa kanki huta gara ki share ki cigaba da hakuri da sannu komai zai daidaita tunda ammi tana son aurenki dashi ai ko baya só sai ya aureki dole ta numfasa kana ta soma kokarin tsaida mota wata mota “tsaya ta fada cikin harshen turanci mai mota ya  tsaya, ta fada mata inda zata " babban gurin siyayya dake kusa da nan zaka kai ni ya gyada mata kai ta shiga mai motar yaja ".

*****
Da misalin karfe biyar daidai na yammacin rana acikin shopright dake ikeja tayi musu kowannensu sanye da kananan kaya idan kagansu zaka d’auka shopping zasuyi ,daya bayan d’aya suka raba kawunansu bangare dabam dabam cikin salon kawar da hankalin mutane akansu ,kamil né zaune akan keken guragu yayinda anas ke tsaye abayansa yana turasa sai dai bada siffar bara ba dan sam shigar jikinsu batayi kama da wadan da suka zo neman taimako ba ,kowanne daga cikinsu kunnensa manne da abun jiyo sautin maganar jaguwa, haka zalika sauran jubi da jabir suna saman gurin suna baza idanu suka ta inda indoor zai shigo domin har zuwa wannan lokacin da suka rigada suka shigo suka fara bincikensu babu wata alama daya shigo gurin .”


Ahankali jaguwa ke hawowa saman lift hannunsa rike da wani had’adden karfe wanda marasa idanu ke amfani dashi ,idanunshi rufe cikin bakin glass me shegen kyau da tsada jikinsa sanye cikin kayan dark army green sai dai riga ta kasance me hula ce yayinda wando ma ya kasance kalar rigar jikinsa sai dai daga kasan wandon a tsukakken yake , jikinsa na wani irin fitar da kamshi turare flower ross .”
a natse yake komai nashi hankalin wasu daga cikin mutane dake gurin ya raja’a akansa most especially mata domin yayi matukar yin kyau sai dai fahimtar da sukayi makaho né yasa fuskarsu ta sauya ta nuna alamun tausayawa garesa ,ya dan waiga kasa inda yaga shigowar wasu fararen mutane su biyu suna magana da juna kamar ya juya ya sauko sai yaga kamar mutanen dake kallonsa zasu fahimci wani ba dan haka ya cigaba da kallonsu yana motsa lip’s dinsa a hankali domin hankaltal da yaransa kamar ance ya dago kansa idanunsa suka sauka akan sanyin idaniyansa ,soyayyarsa ,haukansa ,rayuwarsa tanwer ce ke saukowa sanye cikin doguwar riga hannunta rike da farar leda suna hada ido gabanta yayi wata irin mummunar faduwa shima faduwar gaba yaji ta riskeshi kwayar idaunta ta tsaida akanshi wanda yasashi jin wani abu na ratsa jiki da zuciyarsa take yaji komai ya sauya masa wasu abubuwa suka shiga yawo ajikinsa suna zaga jinin jikinsa gabadaya .”

So yayi ya dauke idanunshi daga kallonta saboda yanzu ba lokacinta bane idan yace zai biye mata komai zai wargaje masa amman ya tsinci kansa da kasa aiwatar da haka ‘wani irin kallo me daga hankali take binsa dashi tsigar jikinta na mikewa, Kallonsa take tun daga kan fuskarsa da kafafunsa dake rufe har zuwa yatsun hannunsa dake rufe cikin bakar safa babu wani abu daya nuna shine mutumin da ko baiyi amfani da ainihin fuskarsa idan ta gansa zuciyarta na fahimtar shine .”
saitin zuciyarsa tabi da kallo wanda hakan ya tabbatar mata da shi din ne tsaye a gabanta zuciyarta ta cigaba da dukan tara tara wanda yasata gaugauwan dauke idanunta daga kallon juna da suke shi kuwa har lokacin ya kasa dauke idanunshi akanta yana kallonta har ta sauka ta barshi zuciyarsa na wani irin dokawa da sauri ya biyota yana tsaidaita a hankali cikin sanyayyar murya batare da yayi amfani da sunanta ba só yake ya gano wani abu ba tayi mamaki jin ya tsaidaita ba .”

Ta ta juyo a natse aiko idanunta suka tsarke cikin nashi yana tsaye abayanta still rike da sanda naunayen numfashi ya sauke ita kuwa ganin rauninsa yasa ta sake had’e rai sosai tamkar bata ta’ba yin dariya ba ,muryarsa a tsarke yace “kamar naso na sanki sai dai na manta inda na sanki yayi mata tmbyr yana shafa sumar kanshi “wannan ba wacce kasani bace ko akwai taimakon da zan iya maka ?”kankance idanunshi yayi ya saka cikin nata qirjinsa na wani irin luguden bugu “okay ina ganin kamace “. baiyi mamaki ba dan a irin shigar da yayi ba lallai ta ganeshi ba, ya soma qakarin kusantota da niyyar fitar daita daga gurin dan kar hargitse ya faru tana ciki hankalinsa zai rabu gida biyu amman yaga ta qara taku ta matsa baya ita anata tasan muddin shine mutumin da zuciyarta ke dokawa akanshi yana gama qarasowa ba qaramin aikinsa bane ya had’eta da faffadan qirjinsa sake motsota yayi da sauri ta dakatar dashi “malam ka tsaya a iyakarka karka sake ka karaso inda nake adnan ko ka dauka bazan ganeka bane .”ta fada a matukar firgice.

step daya ya qara yana cewa waye kuma haka ?ya tamabayeta cikin wata irin murya “maganar wasa ta wuce ni nasan kai ne , ko wani irin canzawa zakayi hakan bazai sa na kasa ganeka ba kai ne dai adnan ahmed já…”Shiru tayi sakamakon karfen hannunsa daya saki a kasa kuma san dan katse mata maganarta yasa yayi hakan ,”ai kece kawai kakisan wannan.” tana gama jin abinda ya fada ta juya fuuuuuu tana rausaya tamkar wata bishiya
Bashi da yabi bayanta da kallo ba mutane dayawa sun bi bayanta da kallo sakamakon tafiyarta me d’aukar hankali nan take yaji wani kishi me tsanani ya caki kahon zuciyarta soyaytarta ta shiga masa kuwa acikin zuciya .”ahankali ya shiga daga kafafunsa domin biyota alokacin indoor ya shigo tare da yaransa shima kamar jaguwa da yaransa haka suka raba kawunansu ai kuwa nan take hankalinsa ya rabu gida biyu “.ya waiga yabi indoor da kallo sannan ya waiga hanyar da tanwer tabi da kallo har lokacin tafiya take na daukar hankali wanda ke sake kunno wutar soyayyarta…”

Manage please 🙏
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️43

...."Ahankali ya sake waigawa ya kalli bayan indoor dake tafiya ,a d'an rikice ya kamo lip's dinsa na qasa yana taunawa gumi na karyo masa bisa goshinsa at the same time yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fiyye da kaida ,baya jin zai iya kasadar rasa tanwer arayuwarsa sam bai so ya had'u daita ba ,da kuma yasan da zuwanta da babu abinda zai sa ya fito wannan aikin a yau, daya hakura da duk abinda za'a samu domin kuwa duk son da ya kewa aikinsa rayuwarta ta fiyye masa ."
Cikin tsananin tashin hankalin ya soma tafiya cikin sarsarfa yana magana kasa kasa "duk kuna jina ?suka had'a baki gurin amsawa da "eh!"To kusa ido sosai akan indoor da wad'ancan mutanen guda biyu na d'azu ."ya karya yabi hanyar da tanwer tabi tana kokarin karya wani layin , ta samu guri ta labe qirjinta na dokawa da matsanancin karfi dan ta lura kamar ya biyota ,dube duben nemanta yake amman babu ita babu alamunta ,daya bayan daya yake shiga gurin tsiyayyar amman stil bai ganta ba dan haka shima ya yanke shawara ya samu guri ya boye."

Leko da kanta tayi ta duba hagu da dama bata ganshi ba ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta fito ta cigaba da tafiyarta ,bai fi taku uku tayi ba taji saukar hannun mutun ajikinta da sauri ta juyo a matukar tsorace tana qokarin bud'e baki ta kurma ihu ta gansa tsaye dan haka tayi shiru tare da sauke ajiyar zuciya,ya zuba mata ido duk da ba asalin idanunsa bane amman sai data ga wasu abubuwa na fitowa daga cikinsu suna daure jijiyoyin jikinta ."
Ya d'auki second goma yana tsaye yana kallonta sannan ya kai hannunsa ya riko tsintsiyar hannuta cikin nashi ya nufi wata hanya da mutane basu kai kawo ya tsaya ya sake zuba mata ido, had'e fuskar tayi sosai tana cewa "wai meye haka ne ?"da sauri jaguwa ya girgiza mata kai "kinga ni bawani tashin hankali nake nema ba kawai ina bukatar ki bar nan kuma a yanzu ."

"saboda me kenan zan bar nan ? saboda banason wani abu ya ta'ba min lafiyrki "wacece ni da zaka
ce baka son wani abu ya ta'ba lafiyata ? ya lumshe idanunshi yana shafa goshinsa da hannunsa ya dauki second biyu a haka sannan ya dago kanshi "kinga malama ki maida hankalinki kiyi abinda nace kafin raina ya baci "tsaki taja da karfi ta cigaba da magana cikin tsananin fushi "kaga nifa banason wata matsla idan wani abu ya sameni meye damuwaarka ?"kamar yace mata babu amman ya kasa furta mata hakan ya cigaba da dubanta a tsanake . "kaga kaje dan Allah kayi abinda ya kawoka dan ni babu ruwana da abinda ya kawoka duk ma abinda ya kawoka nasan bai wuce ..."


cikin tsananin fushi yasa hannu zai buge mata baki ta kauce da sauri muryarsa cike da hassala yace "wannan bakin ina mutuwar sonshi amman sam bashi da mutunci amman zanyi maganinsa ne ."
wani irin kallo tayi masa wanda ya shagaltar dashi dan bai san sanda ya soma murza hannunta dake cikin bashi ba “wannan ikon duk na da ne a yanzu babu me maganin wannan bakin ta hanyar isa ko nuna iko sai wanda zan aura dan haka ka tsaya a matsayinka na wanda naso a ada ".tana gama fadar haka ta zame hannunta dake rike cikin nashi ta juya ,hannunsa taji ya riko kugunta gam ya hadeta da jikinsa sosai kmar zai hade bakinsu gurin daya "karya ne tanwer har yanzu ina cikin zuciyarki bama zaki iya saka wani mahaluki acikin zuciyarki ba wannan zuciyar tawa ce kuma ni kadai ". tanwer ta lumshe idanunta tana jin yadda soayyyarsa ke sake hud'a jiki da zuciyarta "wayyo allah adnan gbdy ka mamaye komai nawa amman duk da haka bazan ta'ba sadaukar maka da farincikina ba har sai ka saduda ka zubar da makaman yakinka kayi abinda nake so , cikin murya me cike da kasala ya cigaba da magana "dan allah tanwer kiyi abinda nake bukata".


hancinta ta hura masa kawai batare data amsa masa zatai ko bazatai ba sai dai alamunta ya nuna masa bazatai abinda yake bukata ba dan sai kokarin turesa take domin ta bar gurin dan haka ya jata zuwa wani madaidaicin plaza dake cikin shopright din wanda ake siyar da dafaffen abinci ya zaunar daita akan daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin , ya matsota sosai kamar zai shige jikinta yana shafa gefen fuskarta "kiji maganta ki zauna anan kada kiyi Kuskuren barin gurin nan duk runtsi duk wuya har na dawo ya furta cikin wani irin salo me kashe sansar jiki ,bata amsa ba ta dauke kanta daga kallonsa ta fuskanci masu siyar da abincin shi kuma ya juya cikin sauri ,bata juyo ta kallesa ba har ya fice daga gurin yana fita ya gyara abun kunnensa ta yadda kowannensu zai jiyosa "lokacin kutse yayi ." ya fada cikin zafin nama bayan fitarsa da minti biyar tanwer ta mike cike da tsinkewar zuciya tana jan tsaki ta fito sai dai batayi nisa ba opposite din plaza data fito ta shiga tana duba agogon mata qirjinta na cigaba da faduwa wanda ta danganta faruwar hakan da ganin jaguwa da tayi duk da a nata bata dauka operation yazo kasancewar shi kadai ta gani ."

kai tsaye indoor cikin inda aka tanada domin yin shoping ya shiga bayan ya karbi bakar jaka a hannun daya daga cikin yaransa aciki gurin ya hadu da mutanen daya zo domin su, hannu ya mika masu daya byn daya suka gaisa  sannan ya dan waiga hagu da dama dan a d'an tsorace yake amman fahimtar  babu wanda idanunsa ke kansu ya saki jikinsa  sosai ya bude jakar hannunsa ya ciro leda daya ta  coken ya mikawa mutun daya, ya kar'ba tare da ciro qaramin wuka a gaban aljihunsa ya tsaga   ledar ya dibi coken din kadan ya kai bakinsa domin tabbatar da me kyau ne ko akasin haka ."jinjina kai yayi alamun tayi  dan haka ya mika masa ya mayar inda ya cirota shi kuma   ya mika masa jakar dake dauke da makudan kudade ,shima indoor ya bude ya tabbatar da kudaden ne a ciki ya sake mika masa hannu sannan suka fito  atare indoor  yayi hannunsa na hagu yayinda fararen fata sukayi na dama ."

daga cikin abun jin magana  su suka ji muryar jaguwa yana cewa "duk ku ankare fa gasu nan da alamar sun gama kasuwancisu kada kuyi harbi har sai idan nace kuyi jakar dake hannunsu kawai muke bukata sannan muyi kokari jami'an tsoro suyi gaba dasu idan sunki su bayar ne kawai zan iya cewa ayi wani abu akai ."Indoor na tafiya kawai yaga kamar ana binsa abaya ya waiga bai ga kowa ba ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya sake rike jakar kudinsa da kyau  ya canza hanya, bangaren wadan can mutane suma anas ne da kamil har ma dasu jubi  ke biye dasu abaya duk inda suka bi suna biye dasu ."

tafiya kadan indoor yayi kawai yaga mutun ta gabansa tsaye yana kallonsa  jaguwa  bai tsaya wata wata ba   ya daura masa  bakin bindiga a goshinsa wata irin firgita yayi ya shiga zazzare idanunwa ya juya da niyyar guduwa nan ma yaga mutun biyu abayansa duk rike da bindiga ,nan take hankalin babban yaronsa wanda kuma ya kasance kani garesa ya tashi domin idanunshi na kan yayansa a bisa yadda suka tsara  atare ya waiga hagu da dama bai ga alamun polisawa ba hakan ya tabbatar masa da  'yan fashi ne aka musu cune.”
"Miko min jakar hannunka."Idan kai jami'in tsaro ne gara kawai ka danganani da hukuma ko kuma mu sasanta anan dan zamu iya gyarota ,girgiza masa kai jaguwa yayi "ko daya mu masu amsar rabonmu né kawai mu qara gaba bamu da wata halaqa da polisawa hasalima abokan gabarmu né "gaskiya bazan baku wannan jakar ba gara ma ku daina wannan sana'ar kuzo ku hada kai dani ni nan zansa rayuwarku ta canza ".bazan iya aikinka ba domin aiki ne dake gurbata rayuwar yayan al'umma bazan zama silar bata zukata ta hanyar siyar da abinda zai saka bushewar zuciyar ga ya’yan alumma ba kai ma ina baka shawarar ka daina domin kuwa gara alqallata akan taka.” sam maganarsa bai sa farinciki ya mamaye zuciyarsa ba sai ma duhu daya gilma a qirjinsa "ka bani jakar kudin ya sake maimaita maganarsa yana miko masa hannunsa .”

Atare daga inda yake a maboyarsa ya saki harsashi guda biyu  nan take jaguwa  ya juyo a matukar firgice sauran mutun biyu din  dake tare dashi suka zagayesa suna duba ta inda harbin ya fito  kanin indoor  ya nuna kansa domin su san ko waye   mutun  biyu   suka biyosa kamar  iska yabi wata hanya  anan ma boyewa yayi yana kallonsu .
gurin ne ya hargitse da hayaniyar mutane kowa ya fara neman takansa wanda hakan ya bawa indoor  damar  kwasa da mugun gudu rike da jakar hannunsa, jaguwa ya biyosa aguje shi  jakar kudin yake bukata daya ajiyeta  sannan yaga sun shiga hannun polisawa shi kenan sun gama dashi  babu wani binsa da zai yi dashi ."
acan dayan bangaren ma anas biye yake

Please Login or Register in order to submit comment