Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji zafin kalamansa amman kishinta daya nuna qarara yayi mata dadi kamar tayi masa dariya mai hade da kukan zafin furucinsa amman tsoronsa ya hanata ,yanayinsa kawai zaka kallo ya tabbatar maka da abinda ke dawainiya dashi gbdy Kishinsa ya fallasa abinda ke cikin zuciyarsa ,yana mugu mugun qaunarta amman tsabar miskilanci da jin kai ya hanashi fallasa muradinsa .”


“Tanwer I want to ask you a question tayi shiru tana kawar da fuskarta gefe ya kai hannunsa ya dawo da fuskarta garesa “why did you abused my sisters and my aunts ,Since when me and you meet each other which day did i abused you da zaki sako sister’s dina cikin magana?adnan ka kirani da …..”shiiiiii !
Yay saurin katseta qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske "abinda nake so dake wannan ya zamo shine karonki na farko kuma ya zamo na karshe da zaki sake kula wannan mutumin koda kuwa gaisuwa ce bana só idan .."
"Idan na sake kulasa fa me zakayi?" tayi masa tambayar cikin karfin hali tana kallon tsakiyar idanunshi at the same time kuma qirjinta na luguden bugu " wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa "tmbyta abinda zanyi kike ko kuma zaki Kibi  umarnina ?"bazanbi umarninka ba tunda ba aurena kayi ba ,baka aureni ba kaga ai bazaka hanani kula duk wanda raina yake so ba ,ko kai mijina ne ?ta sake jifa masa tambayar datasa zuciyarsa shiga tashin hankali ,magangunanta fa
sun doki zuciyarsa da kunnuwansa sosai sannan sun shiga kai kawo acikin kwakwaluwarsa sai yaji kamar ta sake kunno masa wutar kishinsa ne da yake ta kokarin dannewa acikin zuciyarsa ransa a matukar bace yace "kema a she kamar sauran mata kike da rashin mutunci ?kamar ta girgiza masa kanta alamun aa sai kuma ta fasa tunda tasan tayi rashin mutunci "ko da yake bai kamata nayi mamaki manyan maganganunji ba ,idan dai tsiwa da rashin kunya da rashin mutunci ne gidan nazo ko ba haka ba ?"
"Ban sani ba Karka sake kirana da wadan kalmomin bana.."Bata kai karshen maganarta ba ya dalle mata baki da dayan hanunsa da sauri ta dafe bakinta saboda azabar da taji ya ratsata nan take idanunta ya canza kala ta dan juya bayanta nan taga dr muyis tsaye ya kafesu da idanu yana Kallonsu yanayinsa
da alamun tashin hankali dukkanin alamu sun nuna yaji abinda ke tafiya ,daga can gefe kuma anas ta hango ya harde kafafunsa ya tallabe habarsa da hannunsa daya shima yana kallonsu ,numfashi ta sauke sannan ta dawo da kallonta garesa ta tsura masa idanunta cike da kwalla saboda har lokacin tana jin zafi a abakinta ."


Shi din ma kwayar Idanunshi suna kanta yana jin wani irin tuttukin bakinciki acikin ransa "ba laifinki bane tanwer samu kikayi nazo gurinki shiyasa kika samu damar yimin rashin kunya da wulakanci"ya girgiza kai yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa "I don't know that you are in responsible girl like this tanwer, kullum kina yaudarar kanki da kanki da sunan kina sona idan babu ni arayuwarki bazaki iya rayuwa ba amman kullum kina makale da wasu mazan kina shirmen banza dasu Alhamdulillahi for Almighty Allah who created me and you quickly show me the type and the kind of a girl you are ,sakarwa maza fuska, basu damar suga murmushinki a árha ,do you think that's life,wallahi what you're doing is a big shame for you ,my advice to you stop calling me or chart me again ,and I don't won't to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi "yana gama fadar haka ya sakar mata hannu da karfi yana jan tsaki sannan ya juya a matukar fusace ya soma tafiya cikin zafin rai kamar zai tashi sama ."


tsayuwa tayi agurin tamkar an dasata tana kallon every step of him wani irin tafarfasa zuciyarta keyi da sauri sauri tare da tsantsar nadama "me yasa tayi react irin haka ? me yasa tayi masa rashin kunya ?me yasa lokacin da yake maganarsa bata rabu dashi ta zuba masa ido ba tunda ta fahimci damuwa daita ne ya janyo haka ?"Why why tanwer!! jikinta ne ya kama rawa rawa taji kamar ta daura hannuwanta bisa kanta ta kurma ihun tare da kukan neman dauki amman haka nan ta tsinci kanta da kasa aiwatar da ko daya sai ma taji zuciyarta ta bushe tana kallonsa ya dafa kafad'ar anas cikin mawuyacin hali sannan ya zagaya ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna ."

Tayi tunanin anas zai karaso gareta ya tambayeta dalilin fushinsa ita kuma ta samu damar fahimtar dashi komai da matsayin dr muyis agurinta sannan ta nemi alfarmar ya shawo mata kanshi amman sai taga sabanin haka shima ya bude bangaren da yake jingine ya shige jaguwa ya figi motar da dan gudu suka nufi get ,dumi taji akan kuncinta ,ko bata duba ba tasan meye ya zubo akan kuncinta tana tsaye cikin wannan tashin hankali dr muyis ya karaso zai rike mata hannu ta goce da sauri dan ganinsa ma kara mata bakin ciki yayi tunda duk shine ya janyo mata wannan tashin hankalin da take ciki ,tana zaman zamanta tana neman hanyar da zai amince wa aurenta amman kuma ga abinda ya faru "meke faruwa tanwer ?wai waye shi wannan mutumi ne? "yau karo na uku kenan ina ganinsa tare dake please ki fada min waye shi ina da bukatar saninsa da sanin matsayinsa agurinki da har yake da karfin halin fada miki maganganun banza ?".bata ce masa uffan ba illa tsakin data ja sannan tabi gefensa ta karasa inda motarta take ya bi bayanta da kallo har sanda   ta bude gidan baya ta cilla hand bag dinta ta rufe ta bude mazaunin direba ta shiga ta zauna tare da kunna motar ta nufi get stil yabi bayan motarta da kallo kamar yayi kuka yaso ta tsaya tayi masa bayanin matsayinsa dan yasan ta inda zai dauki mataki ,”


Wani irin mugun gudu jaguwa yake yi akan titi har sai da anas ya waiga yana kallonsa "kayi parking a gefen titi please ka bari na karasa damu gida gudun da kake yi yayi yawa ,Iska mai zafi ya furzar batare da yace uffan ba ya cigaba da tuki can kuma ya soma magana "ni tanwer zata fadawa magana alhalin bata san abinda ya kai gurinta ba ?tasan me zan fada mata da naje gurinta tayi min wulakanci ? daman na fada maka soyayya karya ce ba gaskiya ba ". ya karasa maganar yana dukan stearing mota da karfi."kamar ya kwashe masa da dariya amman kuma sai tausayinsa ya mamaye zuciyarsa dan ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya da ruhinsa "ni zata wulakanta akan wani banza wallahi tayi na farko tayi na karshe dan sai ta sake ganina arayuwarta sannan tayi tunanin sake min wulakanci."
"Cool dwn my friend karka ce haka yana da kyau ka tsaya ku fahimci juna idan da hali ma ka bata umarni daina sauraron kowa "karta fasa ta cigaba da sauraran  kowani kato is not my business ko jikinta zata dauka ta bashi tayi bazan damu ba ,wai har da cemin idan ta sake kulashi me zan mata imagine anas wai ni tanwer take fadawa haka ?anas ya kawar da kansa gefe yana murmushin mugunta " wai aurenta nayi da zan hanata kula maza tunda ban aureta ba zata kula duk wanda take so well ta cigaba da kulasu ya fada cikin daga murya Ana's bai juyo ya kallesa ba saboda murmushin dake kwance a fuskarsa ,tanwer bata taba  burgesa ba kamar yau abinda ya kamata tayi kenan tun farko ta zauna tana lallabashi ."


Tafiya kawai yake akan titi batare da yasan ina zai nufa ba lokaci lokaci anas ke waigosa ya kalli yanaynsa agogon hannunsa ya kalla yaga karfe biyu har ta dan wuce ,yace " dan allah ka dawo haiyacinka ka dauki hanyar zuwa gida sai yawo kake yi da mutane ,jiki babu Kwari ya dauki titin unguwarsu cikin minti goma suka karaso jiki babu kwari ya fito ya shiga parlour sai dai kafin ya shiga ya boye abinda ke ransa baya tunanin zai bari su jubi su san halin da yake ciki dan sai suyi masa dariya, tsabar fadin rai da bakinciki bai kula kowa ba acikin gidan ya wuce dakinsa ya zube akan kujerar yana sauke naunayen ajiyar zuciya."
Kwalin sigari dake ajiye akan karamin table ya dauka ya zaro guda daya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuka yana fitar da hayaki ta hanci ta baki zuciyarsa na sake shiga rudani da tashin tashin hankali "Ni zaki wulakanta tanwer wallahi baki isa ba " anas daya shigo ya zauna kusa dashi yace "dan allah ka samu natsuwa bafa haka akeyi ba ,barni kawai anas dan dai ba a gabanka tayi ba nasan da sai ka wanke min ita da mahaukacin mari da zai sa ta dawo haiyacinta tasan tayi Kuskure ,yarinyar nan sam bata da mutunci ai kuwa ganin idanunta zata ga aikin marasa mutunci dan wallahi tayi kuskuren takowa gidan nan sai na ballata naga uban daya tsaya mata "Wallahi adnan kai ma har da laifinka yarnyar nan sam bata da laifi , wani irin kallo ya waiga yayi masa yana kashe sauran sigarin hannunsa ya dauki wani ya kunna ya kai bakinsa ."

"yes bata da laifi adnan tunda tabika ta sadaukar maka da komai nata ,ta soka fi sabililla bata kyamaceka ba me kuma ya rage ta maka ?mu ajiye maganar wasa ta fika gsky tunda baka aureta ba kuma bakace zaka aureta ba kaga baka da damar bata umarni akan wa ya kamata ta kula " tashi yayi bai ce masa komai ba ya dauki kwali sigari da farantin zuba toka ya shige bedroom dinsa cikin fushi tashi anas yayi ya biyosa da sauri yana masa magana "oh biyoni kayi ka cigaba da qara min damuwa akan wanda nake ciki ? "kai dai adnan bazaka canza ba bafa haka ake yi ba, sai anyi hakuri ni nasan zata kiraka ta rarrasheka cikin lumana ta baka hakuri duk da bata maka laifin komai ba "a wajen ka kika ganin bata min laifi ba amman ni a wajena jin abinda tamin nayi kamar na mutu
mace bata taba min abinda tay min ba kai kasani ."


"Nasani adnan amman dan allah kayi hakuri kaji maganata har yanzu tanwer yarinya ce sai ka kara hakuri daita sannan kayi kokari ka fada mata cewar kana sonta zaka ga sauyi na ban mamaki "sai na furta ina sonta zata daina kula maza ?yayi masa tambayar a fusace yana fesar da hayaki idanun shi sunyi jawur sun canza kala tsabar tashin hankali da shan sigari dan ya kusan tashi da kwali daya ,"no adnan ba haka nufi ba zata dai ...."kaga ya isa ya isa !! kama hanya ka wuce gida kawai muradin ranka na can tana jiranka ," Ana's bai san sanda dariya ta subuce masa ba ai kuwa ya shiga yi yana kallon jaguwa ,shi kuwa tsaki ya ja ya soma zariya a dakin still yana  bankawa cikinsa hayaki sai da anas yayi dariya mai isarsa sannan ya matso kusa dashi ya amshi sauran sigarin hannunsa ya dauki kwali ya bude ya duba sauran kara daya aciki "me ye haka adnan ?jaguwa ya tsaya tare da juya masa baya "karka sake shan sigari wanda ka sha yanzu ya isa haka, haba zaka kashe kanka ne akan mace just common mace fa ? yarinyar ma dakace baka sonta me yasa zaka damu kanka dan kaganta da wani "?.

Ya juyo a hankalin ya fuskancesa sosai zuciyarsa na karkarwa da zafi kamar ana diga masa wutan dalma, kamar yayi kuka yaji saboda maganarsa sai dai shima yasan haka ba me yuwa bane agurinsa ya bari anas yaga rauninsa akan tanwer ,a hankali ya motsa lip's dinsa ya soma magana cikin sanyi murya "gsky bai kamata na damu ba well daman bawai kishi bane kawai dai naji babu dadi ne ,ganin yadda wancan mutumin yayi kusa kusa daita kamar zai cinyeta amman daga yau inshaallahu bazan sake damuwa ba ko naganta dani .
"very gud abinda ya kamata kayi kenan tunda baka sonta bazaka aureta ka barta ta cigaba da rayuwarta cikin salama da kwanciyar hankali,ka barta ta kula duk wanda take so kuma a sanda taso ,ko cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka tunda kai bata da amfani agurinta?  "ya karasa maganar yana danne dariyarsa jaguwa yayi masa  wani rikitaccen kallo yana maimaita abinda ya fada a kasan ransa babu kalmar data nemi zautar dashi kamar "ko  cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka . ya lunshe rikitattun idanunshi yana jin zafi da ciwon maganar "Ana's me yasa zaka fada min irin wannan maganar "?Wacce magana  na fada maka ?saurin bude idanunshi yayi yana dubansa sakamakon jin abinda ya fada a she a fili yayi manager bai sani ba ,murmushi ne sosai akan fuskar anas dan shi abun nasa dariya yake bashi amman kuma babu halin yinta ."

jaguwa ya tsura masa ido kawai yana kallonsa tare da nazarinsa a hankali ya kai hannu yana shafa fuskar anas yana cigaba da kallon fuskarsa da yake kallon alamun dariya a tattare daita muryarsa a kasalance yace "Ana's dariya ko ? yay saurin girgiza masa kai alamun a'a "no karka ce min haka mana dariyar ne a fuskarka "dole yasa dariya ta bayyana a fuskar anas,jaguwa ya juya zai bar gurin yayi saurin riko hannunsa ya fixge hannunsa a fusace yana cewa "dole kayi min dariya tunda ga mahaukaci a gabanka ka samu ,please ka saurareni ba dariya bane ,bazan iya sauraron ka ba, zo dai ka wuce gida na sallameka wata dariya ta subucewa Ana's yana cewa "maganar tsara aiki fa ?an yafe maka kuma an sallameka bye ya fada yana zubewa akan gado ya kwanta flat yana fitar da numfashi sama sama ya runtse idanunshi sosai yana ciwo mai tsanani aransa anas bai yi magana dan yasan taurin kansa ba saurararsa zai yi ba dan haka ya dauki faranti zuba tukar sigari da kwalin ya fita zuwa falonsa ya ajiye karamin faranti ya fice da kwalin sai dai bai bar gidan gbdy ba ya samu guri ya zauna a falo cikinsu anas basu nuna masa komai ba aka cigaba da hira dashi ."


Bangaren tanwer kuwa da Kuka ta karaso gida ta bude murfin ta fito daga cikin mota bata tsaya rufewa ba ta shigo babban falon gidansu ta zauna a hannun kujera tana kuka kamar wata karamar yarinya kuka take sosai har mumy da masu aiki suka fito lokacin ita ruky tana daki tana sallah ganinta yasa masu aiki suka juya suka koma kitchen mum ta isa inda take tare da dafa kanta "me ya faru tanwer ? kuka ta cigaba batare data bata amsa ba "tanwer taso mu shiga ciki ki fada min me ya faru dake kike kuka haka ? hannunta mumy ta riko suka shiga dakinta ta zaunar daita a bakin gadonta a lokacin kukan nata ya fara tsayawa "me ya sameki haka kike wannan uban kuka ? duk yadda mumy tayi daita ta fada mata dalilin kukan taki ta fada mata duk da mumy ta fara zargin ita da adnan ne domin idan bashi bane babu abinda zai sa diyarta kuka irin haka "adnan ne ko !?.

Tayi shiru har sai da mumy ta sake maimata tambayarta sannan ta gyada mata kai tayi shiru tana nazarinta sannan ta numfasa ta soma rarrashinta tare da mata nasiha akan rayuwar duniya"kiyi hakuri tanwer rayuwar nan sai mutun ya jajirce mata ya koyi hakuri da juriya hade da dakiya akan duk wani abinda zai samesa karki manta komai qaddara ne rabonka bazai taba wuceka ba ,wallahi duk abinda kika ga bai zo hannunki ba to barabonki bane amman muddin rabonki ne kina zaune zai zo ya sameki , sai abu na gaba banason nasan abinda ya hadaku amman idan kin san kece mai laifi kiyi kokari kikirasa ki bashi hakuri amman idan kin san shine mai laifi ki rabu dashi idan ya huce zai nemiki idan yana sonki "tabbas nasihar mumynta ya shigeta sosai nan take ta yankewa zuciyarta zata jajurcewa rayuwa zata koyi hakuri zata koyi yadda zata danne damuwarta akan adnan sannan bazata sake furta masa tana son shi gara ta fadawa wani akansa
Tayi shiru tana tunanin abinda ya faru yau laifin waye acikin ita dashi .."?tayiwa kanta tmbyr tana kallon mumy dake zaune a gabanta kamar zata mata numfashi ."

"Ki kwanta ki dan huta ko zaki ci abinci ne akawo miki ?bana jin yunwa mumy ta fada a shagwabe,ban yarda ba dan nasan tun breakfast ne acikinki baki  ci komai ba ko ba haka?haka ne mumy amman a koshe nake ,saboda kun samu matsala da adnan ba ?mumy tayi maganr tana shafa fuskarta "no mumy ba haka bane kawai cikina ne a cushe ,yana daga cikin dabiyarki yanzu idan kin samu problem da adnan sai kiki cin abinci kefa likita ce kinfini sanin illarsa ,bari naje na kawo miki ko kadan ne kici kinji mamana ta gyada mata mai kawai ba dan tana jin yunwa ba sai dan kawai ta kwantar mata da hankali.
mumy ta mike tsaye tana sakar mata murmushi ta fice daga dakin bata jima da fita ba ta dawo hannunta rike da tire tanwe ta mike da sauri ta amsa tiren a hannunta "sannu mumy that's why I love more than anything ina sonki mamana ta fad'a tana ajiye tire "nima ina sonki kici abinci ina zuwa ta sake juyawa ta fita tanwer tayi shiru ta kasa bude abincin bare tayi tunanin ci gbdy  abinda ya faru tsakaninta da adnan    ya tsaya mata arai ta rasa waye mai laifi acikinsu dole ba dan tana so ba tabawa kanta laifi ,nice mai laifi tunda na kirasa sister dinsa da Aunty’s dinsa da useless alhalin shi misali ya bani
ta fada hawaye na zubo mata akan kuncinta ,kenan nice ya kamata na kira na bashi hakuri ?ta aikawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar .”

Jiki a sanyaye ta yunkura ta mike ta tashi tsaye tana goge hawayen dake tsiyaya daga cikin kwarnin idanunta ,ta dauki tiren abincin da mumy ta kawo mata ta fito zuwa parlour inda ta iske ruky zaune tana buga game a wayarta tana ganinta ta bar abinda take ta fuskanceta tana cewa “amaryar a gidan adnan yaushe kika dawo ?tanwer ta sakar mata murmushin yake tana boye damuwarta sannan tace “ban wani jima da dawowa ba akwai labari ne ?
“Sosai kuwa idan kin huta kizo kiji , amman dai yau kin dawo da wuri ,eh babu wani aiki dayawa ne ta bata amsa tana shigewa kitchen ,ruky tabi bayanta da kallo aranta tace “ko me ya sameta duk tayi wani iri da alamun ma kamar kuka tayi ?allah dai ka iya mana abinda bazamu iya ba, allah karka barmu da zabinmu ka zabamana abinda yafi alkhairi a rayuwarmu, tanwer ta ajiye tiren ta fito ta dauki handbag dinta ta koma dakinta .”


ta zauna a tsakiyar gadonta ta fito da wayarta tana kallo tana jin mummunar faduwar gaba dake tattare da tsinkewar zuciya mai tsanani wankakkiyar zuciyarta ce ke bata shawarar ta kirasa ta bashi hakuri yayinda wata zuciyar ke kwabarta tana tuna mata gargadinsa gareta “my advice to you stop call me or chart me again ,and I don't won't to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi nan take idanunta suka ciko da ruwan hawaye jikinta ya dauki zafi ta koma ta jingina bayanta da abun gado hawaye na bin gefen idanunta “me zanyi yanzu ? tayiwa kanta tmby zuciyarta na rawa sosai ta shiga tunanin yadda zata yi “me zai hana ki kira anas tunda kina da numbersa gyara zamanta tayi sosai ta soma neman layinsa kira daya ya dauka yana kiran sunanta .”

“Tanwer !
“Na’am anas ina yini ?
“Lafiya tanwer ya aiki da fama da jama’a ?alhamdulillah ta bashi amsa muryata a sanyaye ,
shiru ne ya biyo baya na kusan second biyar tana son tmbyrsa jaguwa tana jin tsoron ko yana kusa dashi tajawa kanta bala’i dashi karon kanshi jin tayi shiru yace “yaakayi tanwer ?,adnan fa ? tayi mgnr muryarta na rawa “yana dakinsa jin haka yasa ta sauke wani wahalallen numfashi da ajiyar zuciya atare ,me yake yi anas ?gskya ban sani ba ya dai kwanata yanzu ma nake son na koma dakin na tashesa dan bai yi sallah ba .”
“Okay daman na kira ne dan allah ka bashi hakuri akan abinda nayi masa nasan ya fad’a maka komai daya faru ,yayi hakuri kuskure ne bazan sake ba amman shima ka fad’a masa komai zai min bana son yayi min a gaban kowa gara yayi min daga ni sai shi ko kasheni zai yi yayi na yarda bazai dameni ba amman a bayyana nasi banaso Ana’s ta karasa maganar tana fashe masa da kuka .”

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke “karki damu tanwer inshaallahu zan fada masa sakonki , kema ki cigaba da hakuri da wannan rigimammen abokin nawa abinda kuma yayi kishi ne ba komai ba “wallahi zan iya rike alqurani nayi rantsuwa dashi babu komai acikin raina akan dr muyis ,ba tun yau ba munyi maganar dashi dr muyis a abokin aikina na daukesa shi dai yana sona amman ni sam sam babu soyayyarsa acikin zuciyata adnan kawai zuciyata ke só amman yadda yazo yayi min agaban dr muyis ya bani haushi shiyasa nayi masa abinda nayi amman dan allah ka bashi hakuri bana son nayi abinda zan bata masa rai ,adnan yasan yadda nake sonshi wallahi da wani abu ma idan ance yayi min bazai ba i love him so much please let him try to understand naso nazo a yanzu amman yayi min gargadi kuma na tsorata da gargadinsa ta karasa maganar tana sheshekan kuka tanwer don’t cry please and kiyi zamanki zan fada masa sakonki idan ya huce zan kiraki a waya na fada miki yadda mukayi dashi sai ki kirasa kuyi magana “.

tayi shiru tana tsaida kukanta can tace “Ana’s kana ganin kuwa adnan nasona kuma zai aureni?gsky ni dai a tawa fahimtar yana sonki kuma yana da muradin aurenki amman dole sai kinyi hakuri da adnan tanwer amman dan so adnan na sonki zuciyarsa ce ke yaudararsa amman jikina yana bani lokacin yayi da zaki mallaki zuciyarsa gbdy abinda yayi ma dazu cikin so ne tanwer idan bai sonki bazai yi kishinki ba ke dai ki kara hakuri ki kuma yi addua abinda yafi zama alkhairi a tsakaninki dashi allah ya tabbatar mana sannan ki daina kula wannan dr din
Sun dan jima suna waya yana fada mata adnan na sonta murmushi jin dadi ne ya bayyana akan fuskarta take taji kashi saba’in acikin damuwarta ta kau a karshe sukayi sallama ,”


*******


A hankali bacci ya dauke jaguwa daga kwanciyar da yayi duk da bacci yake amman hakan bai hana zuciyarsa suya ba har kusan karfe uku bai fito ba anas ya mike ya koma dakin ya dubosa stil bacci yake ya karasa inda akwatin kudi yake ya bude ya dauki daidai wanda zai bukata ya fita ya aiki sky yayi musu order

Please Login or Register in order to submit comment