Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cika alkwari ,wannan aikin alkwari ne karki damu zanje lafiya na dawo lafiya fatana Kiyi min adduar samun nasara ya zamo ni dana yi fita karshe ne zan samu nasarar kamashi kinga qarin girma daga dawowata zai samu ?.”
ta gyada masa kai kawai kamar zatayi kuka a ranta tace “da izinin allah bazaka ta’ba samun nasarar kamashi ba bare ka samu wani qarin girma na banza da wofi ya fahimci yanayinta ya sauya zai ma iya cewa yanayin daya gani tattare daita bai taba gani ba amman sai yayi tunanin ko saboda bata son ya fita ne yasa yanayinta ya sauya ya daga mata hannu kawai ya juya ta fita da sauri .”


ta runtse ido tana jin wani irin ciwo ajikinta “ya allah ya hayyu ya qayyum ka tsare min adnan ka kawo masa karshen wannan maseefa dake yawo acikin rayuwarsa ,ka yaye masa banason ya mutu cikin wannan maseefar shiyasa nayita kokarin ya bar sana’ar saboda gujewa wannan ranar ya Allah ga bawanka adnan ka tsare min shi idan kamashi shine silar shiriyarsa kasa ya shiga hannu a yanke masa hukunci ,ta karasa maganar tana zubar da hawaye masu zafi kwanciyar da ta kasa komawa kenan ta dauki wayarta zata kirasa taji halin da yake ciki tunani tayi kota kirasa da layinta ba lallai ya dauka ba saboda yanayin da suka rabu dashi tayi sauri ta shiga dakin mumy babu ko sallama allah yasa bata dakin tana bathroom ta dauki qaramar ta soma kiran layinsa ,kiran na shiga amman baa d’auka dan haka ta dawo falo sai dai tá kasa tsaye ta saka zaune ”


Gama jan table din keda wuya Anas, Kamil, Jubi, Jabir da suke tsaye cikin rudani suka zubama JAGUWA ido suna masa kallon mamaki sanadiyar gani wani murfin karfe daya bayyana me kama da abun masuburbud’an sanyi ,yasa yaransa suka bud’e bayan sun gama bud’e murfin sukayi tsaye suna kallo kofar sirri ko hanyar sirri zasuce wanda ke dauke da matakala bayyane a gabansu wannan shine karo na biyu da ya nuna musu abun mamaki, haka akaso kamasu a Abuja yace sudafashi sunayi sai gasu sun bace battt ,yauma gashi suna cikin rudani da tashin hankali ya sake zuwa musu da wani fik'iran nashi ,toma yaushe akayi wannan wurin wanda su suna gida tsawon shekara basu sani ba take Jaguwa ya basu umurnin kowannensu yaje store ya dauki katon na ruwan nestil ya shiga dashi .”


hakan kuwa sukayi d'aya bayan d'aya suka dinga takawa suna gama shiga wani mamakinne suka sake gani wani hadadden gida suka gani wanda babu abinda babu acikin sa harma yafi wanda suke ciki tsaruwa dakuna ne masu yauwa ga parlor yasha kayan more rayuwa komai akwai shi a wurin sukam sun gama sarewa da jaguwa shi din na daban ne Jaguwa na ganin su Anas sun gama shigewa ya lalubo wayarsa ya tura ma Tan sako kamar haka.”
“burinki ya cika yau ganin na shiga hannun hukuma sai ki zuba ruwa a k'asa kisha tanwer, hankalinki ya kwanta kisa a ranki Inuwa na rabu dake rabuwa ta har abada domin kuwa mutuwa ce gabana kinga idan na mutu bazaki sake ganina ba .”yana gama tura mata ya shiga yayi step biyu sannan ya janyo kofar bai kai ga rufewa ba ya janyo table din kusa yana sakin kofar table din na sauka akan kofar adaidai lokacin sifikar jami’an tsaro ya karade gidan “ku fito ku miko kanku cikin sauki kafin mu shiga mu sakar muku wuta .”


Duk da sun dan samu mafaka amman hankalinsu baya jikinsu yadda suke bin koina da kallo haka shima yake binsu da kallo bayan kamar mintuna shabiyar suka maida hankalisu garesa suna dubansa sai kuma yaga gbdy sun kwashe da dariya ban da anas d’an shi har lokacin zuciyarsa bata samu natsuwa ba yagansa a wajen gidan kawai yafi bukata baa kasan gidan ba d’an komai zai iya faruwa “yaransa suka shiga daga masa hannu suna sara masa “lallai gaba da gabanta ,gsky da gaske kai kadai ne fadera a kaf kasar nan ,kwarewarka na matukar burgemu, daman idan da kai ai babu wani fargaba ko tashin hankali,kai ne kwarin gwiwarmu ,haka ma sauran abokansa uku sun jinjina masa daman kuma
ya dade yana basu abun mamaki amman na yau dabam ne Kenan ya shiryawa zuwa wannan ranar “?
Abinda suka barwar ransu muddin yana raye zasuyi safe babu wani abu da zai samesu.”


Jaguwa ya gyara tsayuwarsa sosai yana fuskatarsu sai daya kallesu daya bayan daya batare da yace uffan ba su dai har lokacin kallonsa suke yi cke da matsanancin farinciki baiwar da allah yayi masa magana suke yi kasa kasa kowannensu na fadar yanayin daya shiga ya gyara murayarsa da yayi ne
ya katse su ya sake gyara tsayuwarsa yana tura hannuwansa duka acikin ajihunsa wondonsa muryarsa a sanyaye ya fara magana “ku daina murna domin har yanzu da sauran aiki a gabanmu domin kuwa bamu tsira ba .”anas ya sauke numfashi da ajiye zuciya zuciyarsa na rawa ya juya ya kalli Ana’s kullum maganrka mu ajiye wannan aiki mu ajiye aikinan bayan kasan komai ajiye wannan aikin bazai ajiyu ba kamar yadda kake fad’a.”


“Ajiye wannan aikin lallai yana bukatar nazari kamar yadda muka tsara komai kafin mu fara shima haka zamu tsara komai kafin mu barsa dan idan bamu kawo sauye sauye ba ko mun barsa dole zamu samu matsalar da’ake wa gudu faruwarta , yanzu kaga aiki da kwakwaluwa ko ?” acikinku babu wanda yayi tunanin wannan gidan ba aiki kawai zamu dinga yi ba kawo tsare tsare acikin aikin wanda idan matsala taso afkuwa akwai mafaka yanzu meye abunyi .”?


Tana tsaye tana cigaba da kai kawo taga alamun shigowar sako layinta da wani irin sauri ta qarasa inda wayar take jikinta a kasalance ta dauki wayar daga sama taga shigowar jaguwa jikinta na rawa ta soma karantawa Ji tayi jikinta da kafafunta sun dauki rawa suna barazanar kasa daukar ta ,lokaci daya zuciyarta ta nemi ta tarwatse ta dinga bin sako tana sake karantawa cikin tsananin kaduwa da tashin hankali bata son ta rashi “wata irin qara ta saki wanda gabadaya gidan ya dauka ta daura hannuwanta duka bisa kanta tana kiran “wayyo allah na shiga uku, shikenan adnan ya sadaukar da rayuwarsa a banza ,amman ba kansa cuta ba ni ya cuta .”

mumy ta dake daki tana amsa waya ta fito da sauri tana dafata “tanwer tanwer!! lafiyar ki kike kiran sunan adnan haka cikin tashin hankali what’s wrong with him”?” Mumy adnan zai mutu.” ta fada cikin mawuyacin hali jikinta na sake daukar zafi “taya akayi kikasan hakan “?batayi magana sai hawaye masu zafi dake tsiyaya akan kuncinta ta mika ma mumy wayarta dan bazata iya karanta mata sakonsa ba “shikenan ya cuci zuciyata mumy “.“me yasa kayi min haka ? me yasa ka cuci zuciyata adnan “.?

mumy ta zauna ta kamota ta rungumeta tsam ajikinta wacce gbdy ta rude ta fita haiyacinta mumy ta shiga shafa bayanta idanunta na kawo ruwa wata irin murya me hade da tashin hankali suka jiyo ana cewa “weldon abinda ya kamata kenan ya shiga hannun hukuma wannan shine burina shine adduar dana dade ina yi.” a matukar agigice tanwer ta dago daga jikin mumy tana duban dady dake tsaye a bakin kofar shigowa zuciyarta na kadawa Kmr ana kada qararrawa , lokaci guda dady ya cigaba da maganarsa hankalinsa kwamce “abinda na fada haka ne naji dadi kwarai da gaske da zai shiga hannun hukuma , a she daman yaudarar Ibrhim kikeyi ?
“Kika wani sake dashi a she har yanzu zuciyar na ga wannan tantirin ?”allah yasa a harbesa kowa ya huta wata irin zabura tayi tana girgizawa dady kai tamkar kadangariya tana cigaba da dubansa a matukar firgice “dady kana kuwa qaunata ?tayi maganar hawaye na turereniyar zubowa daga idanunta .”

“Dan girman allah kacewa hukuma su hada dani dady dan zan gwamaci mutuwa da wannan rayuwar , dan allah mumy kice Dady ya fada ma hukuma su hadani na mutu na huta yadda take maganar zaka fahimci tana cikin tashin hankali da firgici suna cikin wannan halin dady ya dauki remut ya kunna tv ya kai tashar labarai, nan take kuwa gidan jaguwa ya bayyana domin daukar kai tsaye ne akeyi ,tana kallo polisawa na basu umarnin su miko kansa amman shiru babu wanda ya fito acikinsu ai kuwa Ib da shugaban tawagar polisawa data sojoji suka bada umarnin harbi nan take sauran jami’an tsaron dake tsaye jiran umarni daga sama suka soma budewa gidan wuta wata razananniyar qara ta saki tare da zubewa kasa sunammiya.”


“Ayi hakuri da wannan sai Monday inshaallahu idan kuma na samu Sarari zaku iya gani kafin Monday na gode ku cigaba da hakuri dani dan allah abubuwa ne suke min yawa .”

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️45

.....Arikice mumy tayo kanta tana kiran sunanta "tanwer!tanwer!! amman Shiru bata motsa ba ta kai hannunta daidai saitin  hancinta taji bata sauke numfashi, tuni  ta sake rikicewa tare da fashewa da wani sabon kuka "tanwer karki min haka ,ki barni haka karki qara min wata damuwar akan wacce nake ciki , damuwarki  tana d,aga min hankali ,ki tausaya min ,kinsan ina sonki fiyye da komai a rayuwa ina son ganinki  cikin farinciki da kwanciyar hankali  shiyasa ma na amince miki da auri adnan ta qarasa maganar tana tattarota zuwa jikinta ta rungumeta tsam ta manna kanta a daidai qirjinta tana jijigata had'e da kiran sunanta adaidai wannan lokacin ruky da masu aikin gidan suka fito zuwa parlour'n  a rud".

Da sauri  ruky ta qaraso ta durkusa agaban mumy tana cewa "Lafiya mumy naga tanwer  haka kamar ma bata numfashi ?bata bata amsa ba dan bata san me zatace mata ba ,ita kanta bazata so ruky  tasan irin  nmj da diyarta ke kwakwar so kenan ba "mumy me ya sameta please ?"bata gama rufe baki ba mumy ta saki wani kuka me karfi "ki taimaka min ruky mu kaita hospital tana kokarin tashi ta gagara saka makon sakewar da jikin tanwer yayi, ruky tayi wuf ta  mike jikinta na rawa ta nufi hanyar kitchen karo suka ci da zulai ne aiki rike da goran ruwa dan ita tun fitowarsu   ta fahimci suma tan tayi ,da sauri ta kar'bi goran  ruwan ta dawo inda mumy take zaune rungume da tanwer wacce bata da alamun motsawa ,
ta bude goran ruwan ta tsiyaya  a tafin hannunta ta soma shafa mata ruwa a fuska tana kiran sunanta amman still  shiru ".

Hankali ruky ya tashi kwarai saboda alamarin tanwer ya fara damunta iya saninta  soyayyar adnan ne matsalarta kuma iyayenta sun amince mata tare da bata damar aurensa me kuma ya saura ?"to ma yanzu me ya faru da tai mummunar suma haka ?".
Dan ita kam ta kasa gane kanta ko adnan din ne kuma ya fasa aurenta  yasa ta shiga mummunar hali haka"?ruky tayiwa kanta tambayar da bata da me bata amsa tare da shiga rudani  sosai da tunani game da alamarin tanwer, yayinda shi kuwa dady har lokacin  yana nan tsaye yana dubansu cike da bakinciki mara musaltuwa batare da yace komai ba saboda takaici   amman kuma  shima din a matukar rikice yake baya dai son ya nuna ya shiga damuwa ne adalilin halin data shiga dan abun na tanwer ya wuce tunaninsa ."

Zufa ne ke keto ma mumy a gabadaya ilahirin jikinta yayinda zuciyarta ke tsananin bugawa gabadaya a rude take kallon dady dake tsaye har lokacin yana dubansu bashi da alamun nuna tausayawa gareta "abubakar ka taimakeni kar na rasa yarinyarta ,ka taimakeni mu kaita hospital domin ceto rayuwarta bazan gwamaci mutuwarta ba ka taimakeni dan allah "ta qarasa maganar cikin raunanniyar murya “naji zan taimakeki amman kafin nan sai kinyi min akwatin zaki tursasata ta cire wannan damuwar a ranta sannan ta tsaida zuciyarta akan Ibrahim ko wani mutumin kirki dabam .”ta gyada masa kai tana cewa '"naji nayi maka wannan akawarin zan ma bar kasar nan daita ni dai ta dawo haiyacinta shine muradina "auren ibrahim fa “? ta cigaba da girgiza masa kai "alamun a’a “.

“Daman yasa da wahala ta amince tafi bukatar farincikin diyarta dashi koma yace tafi qaunar tanwer dashi muryarsa na rawa da jikinsa ya soma qoqarin neman gurin zama yana me danne damuwarsa da tashin hankalin ganin halin da tilon diyarsa take ciki ya zauna ya cigaba da kallon abinda ke tafiya a gari,har wannan lokacin jami’an tsaro ne ke kan aiki ,inda jama’ar dake unguwar jaguwa suka cika kofar gidansa makil suna zanga zangar bazasu yarda a taba masa gida ba, hakan yasa polisawa suka kunna tiya gas tuni mutane suka fara darewa saboda zafi me hade da yaji dake shigar masu ido gefe guda kuma yan jarida ne ke faman tambayar mutane goma daaka fito dasu daga maboyar jaguwa ciki kuwa har da alhji tahir mahaifin Ibrahim.”

Cike da tsananin tashin hankali mumy ta kalli bakin tanwer dake fitar da wani kumfa fari sol bude ,ta bakinta da kyar "a karo na biyu abubakar kaci amanata wannan kalmar kawai take furtawa tana hawaye yadda take magana haka farin kumfa ke sake dalalowa abakin tanwer wanda ya dagawa dady hankali wannan karon kasa jurewa yayi ya mike a matukar tsorace bai san sanda ya zari keyn motarsa ya cicibi tanwer ya rungumeta ajikinsa ,shi da ya dauka abun wasa ne ,a rude sukayi waje daita ya nufi inda motarsa take pake tun kafin ya qaraso ya danna keyn hannunsa mumy ta bude masa gidan baya ya sakata ,bai tsaya jiran wani direba ba ya shiga mazaunin direba ya shiga ya zauna yana tada motar tare da danna hon da karfi .”


tun kafin ya qaraso bakin get aka wangale masa tafkeken get gidan ya fice da mugun gudu securities din bakin get suka bi bayan motar da kallo zuciyarsu cike da mamaki abinda yasa minister ya fita cikin tsananin tashin hankali haka ? fatan a sauka lafiya sukayi masa sannan suka maida get suka rufe ,
hospital da tanwer suka nufa kai tsaye emergency aka shiga daita gbdy kusan rabin abokan aikinta ne suka rufa akanta ana kokarin ceto ranta amman kusan minti talatin likitoci na kanta amman numfashi yaki dawowa hakan kuwa ya daga hankalin mumy da dady dan sai yanzu yaji nadamar abinda yayi domin shine silar faruwar komai da bai kunna tv ba da wata killa hankalinta bai tashi haka ba ,nan take jikinsa da hannunsa suka kama rawa balle mumy data kasa tsaye ta kasa zaune sai kai kawo take tana furta duk adduar datazo bakinta tausayin diyarta da halin da take ciki yasa ta kife kanta a bango tana kuka ."

Dady ne yazo  yana kokarin rarrashinta duk da yasan ba lallai ta fahimcesa ba wani irin nauyi da kunyar abinda yayi dazu ya kamashi shi kansa a halin yanzu yana bukatar yayi kuka ya fidda hawaye ko zai samu ya rage nauyin zuciyarsa mumy tun tana turesa har ta hakura ta fada jikinsa suka rungume juna yana rarrashinta daga bisani suka samu guri suka zauna jugun jugun suna jiran fitowar likitoci shiru wasu mintuna talatin tazo ta wuce lokacin har an kira sallahr laasar suka je sukayi alwala suka yi sallah tare da nemawa yarinyarsu sauki a gurin ubangiji allah madaukakin sarki ."

Suna zaune wayar mumy tayi qara ruky ta miko mata sunan ibrahim ta gani dan haka taki dauka dan yanzu haushi yake bata gani take kamar shine silar fadawar diyarta cikin fagarumin matsala tana mikawa ruky wayar kira ya shigo wayar dady ganin me kira ya daga da sauri suka gaisa anan yake fada masa cewa suna asibiti tanwer ce a emergency bai rufe bakinsa ba yaga an turota an nufi I.C.O daita da mugun sauri suka tashi atare suka shiga cikin suka samu tana sauke numfashi kadan kadan sai dai bacci take nan mumy ta zauna ta kife kanta da gadon da take kwance tana zubar da hawaye yayinda take tunanin jaguwa ko a wani hali yake ."?


Yadda jaguwa yayi shiru ya zuba masu rikitattun idanunshi da suka gama canza kala yana dubansu daya bayan daya domin jin abinda zasu ce ,haka suma suke kallonsa domin rasa abun cewa har sanda Ana’s ya zaro wayarsa da yaji motsinta ta hanyar bebriting tun kafin ya duba zuciyarsa ta bashi tabbacin me kiransa ai kuwa yana dubawa sunan my princess ya gani yana yawo a screen din wayar .”
JAGUWA ya dubesa cike da tashin hankali sai dai bai ce masa komai ba sai anas ne ya motsa labbansa a hankali maganarsa ta fito “hally ce !“.yana fadar haka yayi shiru “ka karka d’auka,idan wayar ta gama ringing ka kashe gabadaya .”

Ana’s ya d’an kallesa a rikice ya gyada masa kai alamun haka yake bukata ,babu yadda ya iya dole yayi kamar yadda ya umarcesa amman yaso yaji sautin muryarta bai sani ba ko shi zai zamo abinda zai ji karshe kafin mutuwa ta riskeshi ,jikinsa a matukar sanyaye ya zauna a saman hannun kujera idanunshi na qoqarin kawo ruwan hawaye, jaguwa ya ciro wayarsa ya soma neman layin ammi alokacin
Hally na zaune shiru tana tunanin abinda yasa anas yaki daukar wayarta har ma akarshe ya kashe wayar gabadaya,taji qarar ringin din wayar ammi ta dubi wayar dake yashe a kusa daita sunan yayanta ta gani ta dauki wayar da sauri ta mikawa ammi tana me tsura mata ido .”


Ammi ta karbi wayar daga hannunta ta danna koren maddani tare da sallama daga can bangaren jaguwa ya soma magana cikin raunanniyar muryarsa “ammi mun fita wani aiki ne wata killa mu dawo yau ko gobe ko kuma dai sai an ganmu muna tsananin bukatar adduarki “ta dan ja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana cewa “allah ya baku saa yasa kuyi nasara allah ya tsareku gabadaya” Ameen ya amsa tare da yin shiru yana sauke numfashi jin yadda yayi shiru tace “Anya kuwa bayan tafiyarku aiki babu wata matsala ?”babu komai ammi sai dai ina jin babu dadi ne araina ,”to a hakura mana da tafiyar “hakan bazai yiwu ba ammi yanzu haka ma muna cikin aiki sai dai fatan nasara “inshaallahu karkaji komai zakuyi nasara allah yayiwa rayuwarka albarka ,
Ameen ammi sai dai hally zata cigaba da zama agurinki har sanda zamu dawo “to shikenan yana gama jin abinda tace yay discounting din kiran ya sake fuskantarsu “.

Halima ta maida kallonta ga ammi dake zaune tana amsa waya suka hada ido daita taji gabanta ya shiga faduwa, take damuwa ta mamaye fuskarta ta dubi ammi tace “ammi me yaya yace miki ?”wai sun tafi aiki ne suna bukatar addua sannan ke zaki cigaba da zama anan har sanda zasu dawo “to ai na kira ya anas bai dauka ba byn bai ta’ba kin daukar wayata ba “yanzu me kikaji nace miki sun fita aiki “amman ammi ina jin ba tafiya wani aiki ne ya hana ya anas daukar wayata ba akwai abinda ke faruwa dashi tunda har yaya zai iya kiranki alhalin suna bakin aiki shi me yasa bazai dauki wayata ba ?.”ta fada muryarta a raunane kamar zatayi kuka .”


“ki kwantar da hankalinki karki yi wannan tunanin Kinsan yanayin aikinsu ya gaji haka inshaallahu lafiya zai dawo “duk sanda zasu aiki yana fada min kafin mu rabu me yasa yau bai fad’a min da kanshi ba sai yaya ne ya kira kuma me yasa bai dauki wayata ba ?”ta qarasa maganar tana hawaye ammi ta fuskanci rashin daukar wayarta da rashin fada mata zashi aiki ne yasata damuwa dan haka ta soma rarrashinta “inshaallahu babu wata matsala kiyi masu kyakkyawa fata .” ina masu kyakkyawa fata amman jikina yana bani akwai wani abu dabam .“haba halima me kuma jikinki zai baki kin dai tsargu ne kawai amman babu komai “allah ji nake kamar tafiyar me tsawo ce dayawa wallahi ni da zasu hakura da tafiyar nan su dawo zai fi min alkhairi .”

Tsab ammi ta gano manufar hally dan haka tayi murmushi “kiyi masu addua gamawa da aikin lafiya tayi shiru daga bisani tace to allah ya dawo dasu lafiya ta kwanta gefe wasu tsiraran hawaye na zubo mata ta gefe da gefen idanunta ,ammi ta gani akan fuskarta amman bata dai mata magana ba aranta tace “yaran zamani kenan kiriri suke nuna maitarsu a fili akan mazajensu .” jaguwa ya cigaba da sauraron su har lokacin babu wani daga cikinsu daya qoqarin cewa wani abu sai faman mulmula baki suke alamun suna son yin magana amman kwakwaluwarsu ta kasa aiwatar da komai .”


A hankali ya qarasa inda matattakala take cike da sand’a ya hau ya kasa kunnensa sosai sautin wata murya yaji yana magana “ba zamu bar nan ba sai mun kamashi dan haka Kuyi pata pata da gurin ta yadda harbi zai samesu a duk inda suka boye acikin gidan domin na lura suna son suyi wasa da hankalin hukuma ai kuwa kamar jiran umarni policewar dake rike da bindiga suke suka cigaba da harbin cikin gida wanda windows kam tuni an patattakasu har ana iya hango cikin gidan kuma hakan ne ma ya bawa jaguwa jiyo magana.”ya sauka a hankali ya koma inda anas suke ya janyosu suka yi wani bangare “ku tsaya anan ina ganin ni zan fita ni kad’ai da sauri ana’s ya mike tsaye jikinsa na kyarma yana girgiza kai yana kallon jaguwa da yanayinsa ya nuna alamun rashin tsoro wata irin damka yayiwa hannun JAGUWA da karfi yana cewa “babu inda zan bari kaje,wato kana son ka rigani mutuwa ko “?yadda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin rud’ani da tashin hankali.”


Kamo kafad’un ana’s jaguwa yayi ya zaunar dashi akan kujerar daya tashi yana qoqarin kwantar masa da hankali “please ana’s kayi qoqarin ka dinga rage wannan tsoron , idan ina hango tsoro acikin kwayar idanunka kana karyar min da gwiwa d’ago idanunshi yayi ya tsurawa JAGUWA yana kallonsa tabbas maganarsa haka ne a yanzu ma da yake kallonsa yaga jikinsa yayi sanyi runtse idanu anas yayi ya fara tunanin abinda zai faru idan jaguwa ya fita ”
“Har yanzu basu shigo ba suna haraban gidan ya kamata na hanzarta fita tun kafin su shigo“
kamil yace “no jaguwa zuciyata bata amince da fitarka kai kadai ba ko kuma nace bamu amince ka fita ka mika kanka ba ,wannan gaskiya ne kamil bamu yarda ba me yasa ma ka bari muka shigo .”?ai da an sani abi shawarar anas tun farko anyi bata kashin amman yanzu allah ya taimakemu mun samu mafaka me zai sa kuma mu maida kanmu da kanmu .”? ka dai sake wani tunani amman wannan sam sam bai yi ba inji cewar jabir .”


Wani sanyi dadi anas yaji ya mamaye zuciya da gangar jikinsa sakamakon goyon bayan da suka bashi ,jaguwa ya shafa sumar kansa da hannunsa daya, yayinda dayan hannun ke cikin na anas wanda yake dubansa cike da tausayawa, furzar da huci me zafi yayi ya zare hannunsa dake cikin na anas yana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba ya isa inda dining area yake ya tsaya cikin tsananin tunanin abinda zai yi bayansa suka bi da kallo ,ganin haka ya

Please Login or Register in order to submit comment