Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa tasan komai da yake ciki , amman tasan ko taki amincewa da shawarar nazafi me hali bazai fasa halinsa ba dan ba lallai idan ta fuskancesa  ya fahimceta ba gashi har mugun halinsa yasa nazifi zarginsa akan bashi ne ya kawo Ibrahim duniya ba, da'ace shine ya kawo shi duniya tabbas duk son kudi irinsa nasa dole ya hakura ya rungumi rayuwar d'ansa dan bazai cutar da gudan jininsa  ba wannan shine tmbyr da nazifi ya sha yi mata a tun sanda Ibrahim ya fara rashin lafiya ."

Cikin tsananin damuwa tace " wallahi shine mahaifinsa shine silar zuwansa duniya kawai dai haka rayuwarsa take yafi son kanshi akan kowa da komai, ta mike jiki a sanyaye ta shiga d'akinta a rikice Inda ta bar ib anan ta samesa kwance yayi shiru yana kallon sama d'akin tunanin tanweer yake yasan da lafiyarsa lau babu abinda zai zaunar dashi dole ta kowani hali ya dawo daita sai ga yadda Allah yayi dashi tashi ma baya iyawa bare akai ga magana duk wani kuzarinsa babu zuwa yanzu ya sadaukar da rayuwarsa  adduar mutuwa yakewa Kansa  ya huta da wannan rayuwar da yake ".

jin motsin shigowa d'akin yasa shi sauke idanunshi ya zubawa mata Idanunsa da suka rikid'e sukayi jazur , a kallon da yake mata ya fahimci bata cikin hankalinta da natsuwarta, ya cigaba da kallonta yana jiran yaji sautin muryarta ,itama kallonsa tayi dukkanin alamun sun nuna mata maganarta yake bukata ji, idanunta suka ciko da ruwan hawayen tausayinta dana yaronta ,ta zauna kusa dashi a bakin gado ta riko tafin hannunsa cikin nata hawayenta na diga  .take hankalinsa ya sake tashi jikinsa ya kama rawa kamar mazari ya soma motsi da bakinsa alamun yana cewa wani abu amman babu hali .
a hankali ta fashe da matsanacin kuka tana kallonsa "na cuceka d'ana ,hakika ban maka adalci ba ,me yasa na auri mahaifinka gashi da kaina na zamo silar cutar da rayuwar d'ana ? na boye maka Mugayen halaiyan mahaifinka amman lokaci yayi da zan fayyace maka waye shi " duk wannan maganar da take acikin ranta take shima hawaye ne ke gangaro masa yana jin zafi da radadin halin da yake ciki da zubar hawayen mahaifiyarsa sai da tayi kukanta me isarta sannan ta zare hannunta cikin nashi tana shafa sumar kanshi "bari na gyara maka kwanciya ka kwanta kayi bacci inshallahu jibi duk yadda zanyi sai na bar gidan nan da Kai, bazan zuba Ido rayuwarka ta tagyayara ba, ta gyara masa kwanciya ta lullu'besa da bargo ta shiga bayi bayan minti biyar ta fito yana kallonta ta d'auki hijab dinta ta saka ta tsaya akan daddumar sallarta tare da tayar da sallah isha'i . "
bayan  ta  idar  ta tashi ta fita zuwa  kitchen  babu kowa aciki kai tsaye ta shiga store din da kayan  abinci  yake , anan ta kira layin nazifi kira d'aya ya d'auka, ta fashe masa da kuka tana cewa"nazifi ka taimakeni tunda ka bar gidan nan na kasa samun natsuwa  ,hankalina yaki kwanciya Ina ji ne kamar zan rasa Ibrahim dan Allah kasan yadda zamu bar gidan nan da Ibrahim daga gobe jibin da kace yayi  min nisa dan bana son a bata lokaci dan a halin yanzu hankali yayi matukar tashi Ina ji ajikina kmr zan rasashi ne ,idan na rasa Ibrahim nima rayuwata tazo karshe zaka rasani ta k'arasa maganar tana kuka ".

" ki kwantar da hankalinki umma duk yadda kika ce haka za'a yi amman tafiya a goben akwai matsala saboda gbdy Shirin na jibi ne yanzu abinda za'a yi ki shiga d'akin ib ki soma had'a masa duk abinda kika san nashi ne me amfani inshallahu jibi zan zo da zarar dady ya bar gidan ,gobe idan zanzo zanzo da maganin bacci Koda zai zamo yana gida a jibi sai  kiyi masa amfani dashi , bama anan zamu bar Ibrahim ba kasar ma gbdy zai bari na gama shirya komai tunda daman passport dinsa da naki zaku iya fita a duk sanda tafiya ta taso ".
"na gode! na gode !! nazifi Allah yayiwa rayuwarka albarka , yadda ka tsaya min kaima Allah ya tsaya maka bazan ta'ba manta hallacinka ba na gode sosai ".babu komai umma ai "yiwa Kai ne ban d'auki ib a matsayin amini ba kamar dan'uwa na d'aukesa Kuma wanda nake jinsa har cikin raina, Ina qunar ib Kuma zan iya masa komai idan ta kama zan iya sadaukar masa da rayuwata Allah dai ya bamu sa'a ."Ameen nazifi sun d'auki sama da awa suna tautaunawa Kiran alhj Tahir ne ya shigo har sau biyu yasa tayi masa sallama tana cewa  "ka katse Kiran dady'nku na kirana ",to umma  sai goben kenan , ya fad'a tare da katse Kiran ta d'auki Kiran alhj Tahir.

yana jin sautinta ya soma magana cikin fushi da zafin zuciya "kina Ina ne?  sannan dawa kike waya haka tun dazu Ina kira busy busy ? "nida hjy zainab ne ,ta bashi amsa da hakan dan ta rasa me zata ce masa, ta godewa Allah ma  da sunan yazo bakinta , naunayen ajiyar zuciya ya sauke "to ki fito ina falo "tace to gani nan zuwa .
Ta fito ta iske shi hakince akan d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna akan kujerar dake fuskarta shi "me kuka tautauna da zainab din haka ? sai data zauna sannan ta fara magana "akan dai tanweer ne "
shiru yayi sannan ya gyara zama yana cewa " ko ta fad'a miki halin da'ake game da ma'aikatan nan dan yanzu na rasa gane kan lamarin nasu  ?"eh to tace dai tanweer din ta kirasu cikin tashi hankali"  a matukar firgice ya tashi daga rigin ginen da yayi ya zauna sosai yana dubanta a tsorace "uhm Ina jinki cigaba da bani labari sai data numfasa sannan ta cigaba" daga baya shima dan fashin ya kirasu tare da yi musu gargadi me karfi akan jami'an tsaro dake bibiyarsa idan suka cigaba da binsa zai kashe tanweer ta k'arasa maganar tana yin shiru.

"uhm to ita zainab din me tace ? Me kuwa zata ce ai tafi bukatar rayuwar diyarta nan dai tayita masa bayani kamar yadda hjy zainab tayi mata a wayarsu ta shekaran jiya ,jinjina Kai yayi kawai yana kallonta "Suma dai yanfashi nan da wasu kudin suka tambaya suka dawo musu da yarinyarsu cikin girma da arziki dan riketa da sukayi bashi da wani amfani hjy baseera tace" uhm "  yace "eh mana to meye amfanin riketa da sukayi  ?
duk abinda yace daga" eh! sai uhmmm take cewa a karshe ta tashi zata barsa "bari naje na kwanta. "tun yanzu ? ya fad'a yana duba agogon dake manne a falon. yanzu ne karfe goma tayi "eh yau duk ban zauna ba saboda masu shigowa duba jikin Ibrahim ko  baccin ranar da nake dan yi yau ban samu nayi ba , ko akwai abinda kake bukata ne? "eh idan zan samu bakin shayi nake so "me zai hana zaka samu mana. mikewa tayi ta shiga kitchen ,cikin kankanin lokaci ta had'a masa har zata fito wani tunani yazo mata ta fito ta shiga dakinta ta d'auki kwayar tablet din  da yake sa nazifi yana  bawa Ibrahim  ,ta fito ta markada ta zuba masa aciki shayinsa  ta soma  juya wa a hankali yadda bazai nuna ba "Kai ma kaji azabar da d'ana yake ji inshallahu kafin mu bar kasar Nan  sai karfin jikinka ya ragu mugu kawai  azalumi "
   ta fito ta ajiye masa akan center table ta janyo gabansa alokacin yana kallon labarai ya d'auka ya kur'bi kad'an ya ajiye .
ita Kuma ta wuce daki tana shigowa Ibrahim ya bud'e idanunshi dake lumshe , a natse ta k'arasa Inda yake kwance ta Kai bakinta daidai kunnensa "Ibrahim d'ana jibi idan Allah ya Kai mu zamu bar gidan nan da Kai zuwa kasar Egypt domin duba lafiyarka tana gama fad'ar haka ta cire bakinta ya kura mata Ido yana bukatar qarin bayani "nasan Karin bayani kake bukata zanyi maka amman sai mun bar gidan nan .idanunshi  ya shiga  juya mata alamun bazashi koina ba, idanunta suka ciko da ruwan hawaye "idan har ban bar gidan nan da Kai ba mahaifinka zai yi sanadiyyar ruguza rayuwarka , idan har kana son ka mike bisa kafafunka ka taimaki tanweer ta dawo garemu dole sai ka bar gidan nan kayi nisa da mahaifinka ,zan maka bayani komai kamar yadda na fada maka amman sai mu bar nan , idanunshi ya lumshe mata alamun ya gamsu daita .ranar sam hjy basera bata runtsa ba ta zauna tana shirya duk abinda tasan zasu bukata har  karfe d'aya saura sannan ta koma ta kwanta akan daddumar sallarta ."

****
Jaguwa ya gyara  tsayuwa   yana shafa  qirjinsa da hannu d'aya sannan  yana   jin  bayani  amminsa daki daki  akan matar data samo masa  ,"ammi ki bar maganar wata  hasera  a yanzu , zanyi k'okari na  kawo miki wacce zan aura ".ya fadi hakan ne ba dan zai Kai mata din ba sai dan ta rabashi da batun  wata hasera .
  a bangaren ammi ta katse shi da sauri  "lokaci ya kure maka bazan sake baka wata dama ba dan naga alamun zuciyarka bata shirya amsar soyayyar kowace mace ba ,gara ni na shirya maka  ga  hasera  nan ita  zuciyata ta zaba maka  Kuma ita zaka aura muddin Ina raye  idan Kuma bujirewa zabina   zakayi to sai ka sanar min ?   ". Shiru yayi
tare da lumshe idanunshi a tsayen da yake dan amminsa ta rigada ta gama d'aure shi da maganarta "kayi shiru ko bazaka bi zabina bane  nasani ? "
"Ban Isa ba ammi ,ban Isa naki bin zabinki ba amman ki canza min da wata ban da hasera"  ya fad'a yana Jin wani sabon tashin hankali ya kusanto rayuwarsa   "Amman  Kaine kace duk wacce  na zaba maka  baka da ja ?sun d'auki tsawon lokaci suna tautaunawa a karshe yace ta bar maganar idan ya shigo karshen sati zasu sake tautaunawa akai ".
Bayan ya gama waya da ammi ya  boye  number ya  kira mahaifin tanweer magana biyu yayi masa  ya katse Kiran  sannan ya kira  number baba yana sheida masa zai maida tanweer  gobe "bana ce maka karka kuskura ka  maida yarinyar nan ba ?
"wannan  yarinyar da kake  tare daita a gidanka  karka yarda ka rabu daita ko ka yarda  ta matsa a kusa da Kai kmr yadda na fad'a maka a watanni da suka gabata ,
abinda bakasani ba   ajikinta akwai taurari masu  haske da  karfin da zasuyi maka amfani  akan aikinka ka barta a karkashika  karka yarda ta bar karkashinka ".
"shiru  jaguwa yayi yana tunanin abinda yake ta fad'a masa kenan  kafin daga  baya ya soma magana a sanyaye "bazan iya cutar daita ba  sannan bazan iya amfani da taurarinta ba,  idan da hali na zauna a yadda nake.
na samu duk abinda nake nema batare danayi amfani da taurarin kowa ba..".
"Wannan yarinyar dabam ce km  ko ba yanzu ba  dole zaka   bukaci me irin taurarinta sai dai ba lallai ka samu  ba   dan haka ka barta  kayi amfani da taurarinta  ." bazan iya cigaba da zama da....."
"to ka aureta  domin ta kasance a karkashin ikonka abinda ake so dai ta zauna tare da Kai ".
"Aure  Kuma  baba ?"

Mmn sudais
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN domin sauraron littafaina a tuntubi channel dina ta hausa bakwai     .

🅿️ 21

"Eh  ! abinda  nake  nufi  Kenan  kuma  nake   bukata  ka  aikata,  muddin   wannan   yarinyar   bazata   kasance  karuwarka   ba  to  ya  zama   lallai  ka  aureta   Kuma  acikin tsakankanin wannan    lokacin  ".
Cikin   tsananin  firgici da  tsinkewar  zuciya  jaguwa  yace "  me   yasa   baba ? "mai yasa   baza'a bar   wannan   maganar ba  dan  Allah ? " ni  dai  gsky   a biyo  wata  hanyar   banda  wannan,  tanwer  tasan  koni  waye , tasan  sana'ata  fashi  ne , nayi   Imani   Koda na fada  mata  zan   aurenta  bazata  aureni  da   wannan  sana'ar ba ya k'arasa maganar tare da  yin shiru yana tunanin  zuci  "shi  dai  gaskiya  komai za'a yi  bazai  taba  auren  tanwer da wata manufar ba  ko cutar daita ba domin  yana  jinta  ajikinsa   tamkar   jininsa  ."

Shiru  ne  ya  biyo baya na wasu mintuna  kafin daga bisani baba ya  numfasa  kana ya soma magana  a dake "Hanya   daya   ce  zata  maye maka  wannan  gurbin , ka  nemi  mace   mai  irin  taurarinta  ka ajiyeta   akarkashin  ikonka  Koda  bazaka   aureta  ba ka dinga saduwa  daita  saduwa irin ta aure    idan   kayi  haka shikenan komai  zai cigaba da tafiyar  mana yadda   muke  so batare da wata matsala ba   ."
"shiru   jaguwa   yayi  yana kallon  zara  zaran  yatsun   kafafunsa  masu tsananin kyau da   sheki  yana  nazarin maganar  baba, nan  take  gumi ya  shiga  tsatsafo masa  a dukkanin   ilahirin  jikinsa, kwakwaluwarsa  ta  toshe  zuciyarsa  ta  cunkushe  guri daya , tunanin  da  yake ya tsaya cak  ya  Kasa  cigaba da tunanin  komai . sai  daya  dauki  minti  biyar   tsaye  batare da yasan madafar  dafawa  ba "amincewa  auren  tanwer  Ko  nemo  mai irin taurarinta ya ajiyeta akarkashin  ya dinga  aikata zina daita   "shi da yake neman yakice  zina  arayuwarsa sai ga baba  na kokarin  maidashi  ruwa tsundum.
"Ya amince  ne  ko kuma ya  fada masa a sake nemo wata mufutar ?  sautin  muryar  baba  ne ya dawo dashi cikin hankalinsa  ta Inda ya  cigaba  da  zayyano masa hujojinsa akan  bukatar auren tanwer da yake son yayi  Ko kuma  ya  shiga  gari ya nemo mace  me irin taurarinta  idan ba haka  ba  nan  gaba  kadan za'a  yi  galaba akansa  " .

duk abinda baba ya  fada  yasan  yana  da  huja  akan hakan kuma yasan ya fada ne domin ingata rayuwarsa daga sana'ar fashin da yake  but  shi  baya jin  zai iya  ajiye  tanwer a  matsayin karuwarsa  Ko aurenta domin samun  wani  biyan bukata  daga gareta  ". ya runtse idanunshi yana  mai  sake  gyara tsayuwarsa  yana  jujuya  maganganun baba  yana sake fadadasu  yana masu filla filla , gbdy  komai  ya  tsaya masa.
ya sake  neman natsuwarsa  ya rasa , ji yake Kamar zuciyarsa zata  buga   tsabar  shiga rud'ani  tunanin  matsalar dcp ,tanwer ,
Amminsa  , yanzu  Kuma ga matsalar baba da me zai ji?
"me ya kamata yayi ya samar ma  zuciyarsa salama ? yana jin kamar yace   babu abinda zai yi acikin umarnin baba wanda wannan shine  Karo na farko da zai sabawa umarninsa a tun tsawon lokacin  da suka dauka tare  dan bai taba cewa ga abinda zaiyi ya mutsanta  masa ba sai dai ya aiwatar . "
"tun  yanzu ka fara tunanin  shiga  gari  domin  nemo me irin taurarin  yarinyar nan ka ajiyeyata  a matsayin karuwarka  dan nasan bazaka taba aurenta ba tunda baka amince da auren  yarinyar nan ba  ."
Juya  maganar  baba yaketa faman yi acikin kwa kwaluwarsa , zuciyarsa ta dunkule guri daya  yana jin Kamar ya daura hannu akanshi ya saka ihu ko yaji saukin zafin da zuciyarsa ke masa sai daya sanyawa jikinsa jarumta sannan yace "wacce irin alama ce  zatasa na gane me irin taurarin tanwer ?
"Kenan kafin bukatar wata akan wannan yarinyar ?
"bazan iya cutar daita bane " ya fada yana furzar da iska mai zafi daga  bakinsa,  shiru baba yayi kafin daga bisani ya numfasa sannan  ya   cigaba da mgn "alamar da zaka gane me irin taurarinta , kana ganinta duk wata kafa ta gashi  dake kwance ajikinka zata mike, take wannan zoben dake hannunka zai yi baki, abu na gaba tsuntsun dake ajiye a gidanka zai bayyana akanta wannan shine alamar me irin taurarinta amman fa bai zama lallai ka samu ba."
"zan samu ....."  ina samun nasara akan komai dana saka gaba wannan Karon  ma  nasan zanyi nasara  da yarda Allah   "Ina  maka   fatan  alkhairi da fatan samun nasara  yana  gama fadar haka  yayi  disconnecting din Kiran , jaguwa ya cigaba da tsayuwa  agurun tare da lulu duniyar tunanin ."

bai dawo d'aki inda tanwer take  ba sai  wajen karfe d'aya da rabi na  dare lokacin tuni tanweer tayi bacci a kasa tare da kankame jikinta guri d'aya saboda karfin ac d'akin yayi mata yawa ,  ya   karasa ya tsugunna gabanta yana karewa jikinta kallo  yana   tunanin maganganun  baba , ganinta   yanzu kwance a gabansa  yaji kamar ya amince da maganarsa  sai dai take zuciyarsa ta dakatar da wannan tunanin  dan haka yayi  saurin kawar da  maganar ya tsaida kwayar  idanunshi akan  fuskarta da  tayi jawur alamun taci  kuka .
a hankali ya Kai hannunsa yana shafa  gefen  fuskarta cike da tausayawa  zafi yaji ya ratsa tafin hannunsa amman hakan bai hanashi Jin sanyi dadi a sansar jikinsa ba ,duk sanda zai kasance daita ya dinga jin irin  wannan  yanayin kenan   ,ba ko wani  irin yanayi bane illa kasala da tsananin sha'awarta  haka zai  dinga jin Kamar ana masa wanka da ruwan sanyi ."
Kallon fuskata ya cigaba dayi yana  shafawa  har zuwa kan tudun dukiyar fulaninta da suka dan bulluko  ta saman rigarta   wani irin  zirrrrr  yaji  a gbdy ilahirin jikinsa kafin kace me jijiyarsa ta shiga  harbawa da sauri sauri.

numfashi ya fesar yana jin kamar ya cire mata kayan jikinta  ya soma sarrafasu "a hankali ya Kai hannunwansa zai ɗauketa firgigib ta bud'e idanunta ta watsa masa runannun idanunta tana sake kamkame jikinta waje d'aya ya matso sosai kmr zai shige jikinta tare da Kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya kira sunanta  cikin sanyayyiyar  muryarshi mai tsananin kashe jiki da tsuma zuciya "tanweer ! 
Shiru  tayi taki amsawa "idan bazaki bari na d'aukeki  na kwantar  dake ba ki tashi kije ki kwanta  kar sanyi yayi miki illa " bata ce masa komai ba har sanda ta  mike ta  zauna shima ya matso kusa daita ya zauna yana shafa  wuyanta  zafi  ne  har lokacin  ya sake ratsa tafin hannunsa   yace " baki da lafiya ne  ? sai da ta d'auki second biyar sannan tace " eh !  Ina dan jin zazzabi ne ,"sannu ya fad'a yana sake  shafa gefen fuskarta "yauwa  ta fad'a a sanyaye tana mai tsura masa Ido  sai taga gbdy yanayinsa ya canza ba kamar da  da yake mata Komai da gadara ba  tausayinta ko tausayin Kansa ne ya maidashi haka bata sani ba ."

hakan ta dinga ji tausayinsa a ranta ya d'aukarwa Kansa muguwar rayuwa ,Allah ka shiryesa idan yana da rabon shiriya ta fad'a acikin ranta har karfe biyu ta buga jikinta da zuciyarta sunki saurara mata akanshi , tana son barin gidan tana tunanin matsayar soyayyarta agurinsa " Ina ma bashi da ta'bo komai da tabbas kowa zai tayata murna samun nagartaccen miji irinsa ya matso kusa daita sosai yana sake furta mata Sannu "nayi magana da mahaifinki  zamu  had'u dashi a gidan man royal stream gobe "  tana jinsa amman taki cewa uffan ,ya kamo yatsun hannunta cikin nasa  yana kallo farcenta masu kyau sai sheki suke  a natse  ya ɗauketa cak ya rungumeta tsam  ajikinsa yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta "zaki tafi gobe ki barni ?
ta lumshe masa idanunta alamun "eh! bai sake cewa komai ba haka bai  sauketa akoina ba sai a tsakiyar  gadonsa  ya kwantar daita  ya mata runfa da faffadan qirjinsa  ya canza wutar d'akin zuwa mara haske yana mai  lumshe  idanunshi."

numfashi me zafi ta fesar qirjinta na sama da kasa a hankali ta Kai hannunta tana shafa sajen dake kwance a  fuskarsa zuwa dogon  hancinsa "zan tafi na barka me zaka  bani wanda zan dinga tunawa da Kai ? ya bud'e idanunshi daya lumshe ya watsa cikin nata batare da yace mata Komai ba ,ya matso kusa daita sosai har tana Jin yadda qirjinsa ke bugawa fat fat kmr zai fasa qirjinsa ya fito, ya  kwanta gefenta yana kallonta  itama ta juyo  suna fuskantar juna.
ya kamo yatsun hannunta ya jefa cikin bakinsa yana tsotsa a hankali  yana cigaba da  kallon kyakkyawar fuskarta acikin haske da bai gama haskake d'akin ba.
kallon juna suke cikin yanayi na tsananin soyayyar juna  da buqatuwa da juna, sosai zuciyoyinsu  ke bugawa da sauri sauri  saboda yanayin da suke ji a sansar jikinsu "na tambayeka kayi shiru , shirunka na nufin baka bukatar na samu komai daga gareka ? ta fad'a tana shigewa  jikinsa still bai ce mata komai ba ya janyo bargo mai taushi ya lullubesu acikin bargon ma suna manne da juna Kamar zasuyiwa juna numfashi .
sosai ta shige  jikinsa "Adnan ......!
ta kira sunansa cikin kasalalliyar muryarta wani iri yaji a dalilin yadda ta Kira sunansa gbdy ta kashe masa jiki wani Abu yaji suna yawo a sansar jikinsa tun daga tsakiyar kansa har zuwa yatsun ka'fafunsa da kan jijiyarsa wanda bai taba ji akan kowacce mace ba sai akanta .
"Adnan kace min wani abu mana ka fada min abinda zaka bani  wanda zai dinga debe min kewarka  idan na tafi " still dai shirunsa ne ya biyo baya ta numfasa ", ni idan bazaka bani ba ka fad'a min abinda zan baka Wanda zaka dinga tunawa dani ,nayi alkwarin komai kace zanyi maka shi acikin a daren nan  ."

Lumshe idanunshi yayi  yana me sake  shigewa jikinta yayinda jijiyarsa Ke sake shiga cikin garari da kaiwa kololuwar bukata  da kyar ya fixgo magana  " bana  bukatar komai iya soyayyar da kika nuna min ma ta  Isa "To ni me yasa baka sona alhalin kasan Ina sonka ? dan Allah  Adnan ka soni  kuma  kar ka manta dani, dan ni Ina sonka da gaskiya ,ka rikeni aranka.
" ka rabani da abu me mahimmancin amman still zuciyata na sonka ban san wani irin so nake maka ba wallahi idan ka manta dani zan iya mutuwa  dan bazan juri zama a duniyar nan  babu Kai ba .
"wallahi Adnan tunda nake ban taba  gani  mutumin  da ya shiga zuciyata  farar daya   kamarka ba, Adnan  ka sace zuciyata da komai nawa  dan Allah Adnan  ka bani dama na shigo rayuwarka  domin na canzaka sannan na zama abokin  rayuwarka ."
Shi dai jaguwa  jinta  kawai yake yi har ta gama zubanta  shi bai ce kala ba "adnan  nasan kana jina ka shareni  "Dan Allah ka min  magana ko naji sanyi azuciyata  I love  you more than anything in this world  ba karamin dadin kalamanta  yaji ba sai dai yaki furta komai .
"don girman Allah  ad ....." a sukwane ya  toshe mata baki da bakinsa hannunsa Kuma ya hau shafa mata sansar jiki dashi  sai daya tsotse mata  baki tass sannan ya zare bakinsa yana cewa "bazan manta dake ba  arayuwata , zanyi k'okari na dinga tunaninki sau biyu a rana ya fad'a cike da zolaya yana jan karan hancinta  ".

"sau biyu kawai ?tayi mgnr a shagwa'be tana dukan qirjinsa ya kamkameta  tsam ajikinsa yana busa mata numfashinsa "shikenan  zan dinga tunaki akai akai , zanyi kewarki sosai .
dadin  maganarsa ta sake narkar mata  da zuciya , ta kai yatsun  hannunnta tana yawo dasu akan fuskarsa tana jin tmkr su hade su zama abu guda .
Yayinda shi kuma ya kai hannunsa qirjinta yana mata tafiyar  tsutsa yana ciza lips dinsa na kasa  "taya ma zan iya mantaki a rayuwata ?yayi maganar a kasan ransa" kin jiyar Dani dadin da ban ta'ba ji  ajikin kowacce mace ba ,Kuma nayi Imani  bazan sake ji ba in ba Ina tare dake ba"  ya kamkameta sosai ajikinsa kmr zai rabata gida biyu  yana shafa ta yana Jin wani maganadisu sonta na shigarsa, yaji sha'awarsa data tafi tana Shirin dawowa gashi bazai iya aikata komai daita ba .
ya birkitota saman qirjinsa ta kwanta a saman lafiyayyen qirjinsa tana sakin  numfashi "washhhh.. ! cike da  shagwa'ba tace  "ka  Aure ni please" shiru yayi yana faman shafa bayanta "please Adnan ka daina wannan sa'anar ka aureni sam sana'ar nan bata dace da Kai ba "naji zanyi tunani akansa" "batun auren fa ka fad'a min zaka aureni ko bazakayi ba ? "surayya !
ya kira sunanta muryarsa a kasalance  ta shige masa sosai batare data amsa ba, bata ta'ba jin wanda ya iya Kiran ainihin sunanta ba kamarsa "bazan iya abinda kike bukata ba a halin yanzu da zuciyata  take cikin garari da tashin hankali Kiran da kikaga na fita na amsa Kiran ammina ne wai ta samar min matar da

Please Login or Register in order to submit comment