Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san dame zai misaltashi  ba ."


"nima ina sonki tanwer   son da ban taba  tsammanin yiwa wani mahaluki irinsa ba ,ina jinki  ajinina  acikin bargona da tsokar jikina  bazan iya rayuwa babu ke ba but just give me time  ina bukatar lokaci zanyi wani abu akai ,wani irin sanyayyen dadi ke bin lungu da sako  na sansar jikinsa ,jinin jikinsa ya ninka gudu akan yadda yake yi ,a natse ya karasa gaban mirrow ya tsaya ya tokare hannunsa da jikin bango yana kallon kansa ta cikin mirrow , yatsan dayan hannunsa ya kai cikin bakinsa yana cizawa a hankali a hankali yana jin kamar yatsunta yake cizawa "ina son fararen fure ko zaka dauko min ?ina sonka adnan na yarda da kai na kuma amince da kai ,ya tuna lokacin daya kai kangon gida da bai yi tsammani zata iya rayuwa acikinsa ba amman da budar bakinta tace "me zai hana adnan ?wallahi zan zauna dan fiyye min kowani gida muddin da kai zan rayu acikinsa karka wani damu zan zauna ". ya sauke naunayen ajiyar zuciya a daidai lokacin da ana's ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya ya harde hannunwansa a qirji idanunsa akansa,jaguwa bai juyo ba sai ma kura masa ido da yayi ta cikin glas mirrow  yana kallonsa kafin daga baya ya juyo gbdy ya fuskanci anas  soyayyar tanwer na sake kanainayesa "yanzu me ka tsayar akan yarinyar nan tanwer?" I don't know what to say but is like bazan iya cigaba da rike wasu abubuwa ba zan dai yi shawara da zuciyata  nan kusa zan tsaida maka
yayi mgnr hannunsa na shafa faffadan qirjinsa  ,
gyada kansa kawai anas yayi tare da sauke boyayen  numfashi yace "please jaguwa ka hanzarta kayi abinda ya dace ka daina barazana da rayuwar yarinyar mutane " .

Ajiyar zuciya ya sauke tare da tsura masa ido yana jin yadda zuciyarsa ke mugu mugun bugawa ya kira sunansa "anas look at me babu wasa acikin kwayar idanuna idan bazan yi wani abu akai ba kai kasan waye  ne I won't lie to you ,zanyi wani abu akai amman ban sa yaushe bane , yau né gobe ko anjima né bansani ba ya karasa maganar tare da yin shiru ya cigaba da kallon anas ,dakin dakin ya dauki shiru bayan ya rungume hannunyensa  duka sannan ya janyo wayarsa da yaji tayi kara alamun shigowar sako ya shiga dubawa yana gamawa ya fesar da  iska mai zafi daga bakinsa sannan  ya soma magana a tsanake " satin nan  zamuyi aiki ma  alhji bello yanzu sakonsu ya shigo da inda zaayi aikin sai dai bana jin acikin mu biyar din nan akwai  wanda zashi zan tura sconpio  domin aikin zai fi dacewa da mutun daya ne ,nan  da 2 week kuma zamu shiga aikin akan masu safarar hodar iblis ,sannnan ina  saka rai mlm mudi zai turo mana sako yau ko gobe domin musan ta yadda zamu bibiyi alhji tajudenni da duk wasu masu irin sana'arsa ."

"suna dayawa fa kana ganin zamu iya dasu gbdy ?me yasa kayi wannnan tamabyar ?bansan dalilin ba amman haka nan nake  dan jin tsoro yin aikin ."shiru jaguwa yayi yana kallonsa up and down yana taba qirjinsa sannan yace "why anas?  akoda yaushe ina fad'a maka ka dinga  karfafa zuciyarka  ka cire tsoron a ranka babu abinda zai faru damu ,please  ka kwantar da hankalinka a yanzu nima na soma hango haske acikin maganarka zan  yi kokari na dawo kan hanya  kamar yadda kake bukata amman kafin lokacin akwai bukatar muyi komai cikin tsare....."
"ba tsoro bane adnan wallahi bana son hally ta rasani ne adalilin akin nan ni kaina  yanzu  na fara jin dadin iyalina  ka fahimceni kai kanka kasan aikinmu akwai hatsari, ada rayuwarmu kawai muke ko mutu ko mu rayu amman yanzu fa?"ina da hally acikin rayuwata kai ma kuma ina fatan nan kusa ka ajiye tanwer a gidanka  for how long zamu d'au...."qarar bude kofar dakin da suka ji  ne ya katsesa sky ne ya shigo hannnsa rike da farar takarda guda uku "boss ga sakon bayanai nan mlm mudi ya turo ta system gashi har na yi prit dinsa out ,okay sky ja  ajiye a can ya ajiye akan table ya juya."
"Am sky yayi saurin juyowa da sauri cike da respect ,
ka kawo min bakin shayi yanzu "okay boss ya fada tare da juyawa ya fice daga dakin .


Anas ya dan yi murmushi ya cigaba da magana "rayuwar yanzu data da ba daya bace agurina ina matukar son halima kamar yadda kasani banason na bar rayuwarta cikin kuncin da matsalolin rayuwa , cikin haka  sky ya sake yin knowking ya shigo hannunsa rike da farin glass cup mai dauke da ruwan coffee mai zafi  ya ajiye ya juya ,jaguwa na kokarin daukar cup din coffee wayar anas ta soma ringing dan haka ya dakata  yana son sauraron yaji daga ina wayar tace  .
  Ana's ya  zaro wayar  daga cikin aljihun gaban rigarsa yana kallon screen din wayar my princess wife ya gani  yana yawo daman da sunan da yayi saving kenan  ,ya lumshe idanunshi yana jin sanyi na ratsa sansar jikinsa ya dauka tare da rage sautin muryarsa "my princess ya kike ya jikin naki hope kin dan samu relief ?okay to shikenan my princess wife ki kular min da kanki gani nan dawo wa yanzu  ,
jaguwa ya maida hankalinsa sosai akansa "ina sonki sosai my princess wife bazan jima ba  muradin raina da wannan kalmar ya kawo karshen maganarsu ya katse wayar da murmushi akan fuskarsa."

"muradin ranka anas a kuma gabana ko  kunyata bakaji ba kamar ni ba surukinka bane ?wani kunya kuma adnan a zaune kalau ?ai maganar wata kunya ta kare kaga bari na wuce gida my princess wife bata da lafiya gashi har uku saura ya  juya , har ya  kusan bakin kofa ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar jaguwa data fito a hankali ,"gbdy maganganunka kunya suke bani anas,Karsu baka kunya adnan ka dai yi kokari Kaima   ka mallaki muradin ranka zai fiyye maka ya sa kai zai  fice daga dakin yana murmushin tsokana shima jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa  yace "ka shigo gobe da wuri please mu fara tsara abubuwa "okay ya fada tare da karasa ficewa.
Numfashi jaguwa ya sauke yana jin dadin yadda anas ke kulawa da kanwarsa gbdy rayuwarsa ma ta sauya ya daina shan giya yanzu iyakarsa sigari shima sai idan yaga yana sha ne .a hankali ya karasa ya dauki farar takardar da sky ya ajiye yana dubawa a tsanake yana kurban coffee at the same time kuma yana cizan lip's dinsa na kasa yana jin faduwar gaba  akan tanwer duk sanda ta fado masa sai yaji gabansa yayi mummunar faduwa gashi yanzu duk bayan sakonni take fado masa yaji kamar yaje gidansu ya ganta  amman bazai iya ba .

Hally kuwa tunda anas ya fada mata kalamansa masu sanyi taji ta sake nitso acikin soyayyarsa "kece muradin raina ta maimaita tana lunshe ido "nima kai ne muradina ,karfe hudu na yamma tai wanka tai kwaliyya kamar jiya sai dai kayan datasa ba irin na jiya bane dinki atamfa ne sai dai su din ma sun dan matseta daga kirji ta canza tasha zuwa zeeworld alokacin ana wani film din india mai kyau kuma na soyayya (sanam teri kasam ) daman itama mayar son kallon film din india ce karfe biyar yayi sallama taji matukar dadin dawowarsa ji tayi kamar ta tashi ta rungumeshi ajikinta bai shigo ba ya tsaya a bakin kofa .
Ta kallesa tace "Lafiya ka tsaya anan?"
Ya dan daga kafada "bazan shigo ba sai da kulawarki tayi murmushi tana mai tsaida idanunta akanshi "kulawa kuma tame "?ai ya kamata na samu ko yar runguma ne ayi min ko ba haka ba ?Tayi kasa da idanunta ta gyara zamanta babu alamun zata tashi "da gaske fa nake idan baki taso kin rungumeni ba alamar barka da dawo wa a haka zan ta tsayuwa bazan shigo ba gashi kuma na dauko yunwa ."

Jikinta a sanyaye ta tashi ta nufi inda yake tsaye yana aiko mata da kallon love sai dataje daf dashi sannan ta tsaya "to shikenan ka rufe idunka ya kuwa rufe a hankali ta karasa ta rungunesa tsam,shima ya hadeta acikin hannuwansa ya rungumeta ajikinsa yana shafa gadon bayanta "my princess wife nayi kewarki duk  abinda nake hotonki nake gani na tabbatar dana bari na kai Kmr jiya zaki sha mamaki domin zan iya ramewa."

Tayi murmushi "ramewa kuma ?"Wallahi zan iya ramewa domin kawai tunaninki nifa kin kara siyo min wata kima da daraja agareni sonki ya ninku a zuciyata fiyye da wanda banyi tsammani ba ina jinki a sahun macen da ko mutuwa idan ta rabu mu ita kanta tasan bata mana adalci ba ,ya dan zareta ajikinsa yana kallonta  itama shi din take kallo da kwayar idanunta  ya kai hannunsa yana shafa lip's dinta "ban taba jin bakinki ya fadi irin haka ba ina son nasan yadda kike jina acikin ranki ".Taja hannunsa zuwa kan table domin abincin rana datayi bata dauke shi ba yana cikin flak's "kace kana jin yunwa?"
"Eh ina jin yunwa amman kuma bazan ci abincin ba sai kin gaya min yadda kike jina acikin ranki "ka fiyye fitina yanzu  ya anas mai yasa ne ?"saboda na damu dake  ne kuma mutuwar sonki banason abinda zai nisantani dake my princess ya fada idanunshi na kanta ta danyi kasa da idanunta a hankali ta soma motsa lips dinta "ina... ina .." sai kuma kunya ta hanata furta abinda take son fada masa .

da murmushi ya sumbace kumatunta suka zauna bisa table "zanso ace muna rayuwarmu kullum atare batare dana fita zuwa koina ba amman ina hakan ba mai yuwa bane kullum cikin aiki muke ta dago ta kallesa daga zuba masa abincin da take "haka ai shine daidai ,abun haushi ma gobe akwai aikin da zamu fitar dani ta sake dagowa da murmushi a fuskarta "meye abun jin  haushi aciki dan zaka fita nemo mana halal?".nan take yanayinsa ya sauya zuciyarsa ta soma rawa  ,yayi shiru  yana kallonta cike da tausayawa "karka damu nasan na dan kewar juna da zamuyi ne wannan kuma na dan wani lokaci ne kawai ta ajiye abun zuba abinci ta kamo hannunsa  cikin nata ganin yanayinsa ya canza "haba mana ya anas ai baa acan zaka  kwana ba da ka wani canza Kmr idan ka fita goben bazaka dawo ba ?"

Yayi saurin girgiza mata kai "to ko na shirya goben muje tare ne ?ya harareta cikin tsigar wasa yana dawo da natsuwarsa "allah sai muje tare,shimkenan zan muje tare amman a zuciyata zan miki kyakkyawan riko ya fada yana shirin fara cin abinci ."Sarai ta gane ba zuwa zaiyi daita ba "ai kuwa idan bakaje dani ba bazamu kwana tare ba ya dago yana dariya "ai kuwa yarinya baki isa ba ai daga yanzu kullum tare zamu dinga kwana har na samu na isar da duk sakonnina gareki inda da rabo har baby ya samu ya shiga ,hararsa tayi tare da yin shiru ya bita da kallo "kinyi kyau sosai my princess wife kamar a India tayi murmushi gefen baki "ai duk kyau na ban kai matar jiya daka zage kana ta faman kallonta kana murmushi ta cikin wannan film din na jiya ya danyi dariya ya ajiye spoon a gefe ai yarinya tayi kokari ne ko ba haka ba ?".

Tayi shiru tana nazari maganar da zata fada masa amman kuma tayi shiru saboda ganin rashin dacewarta abinda zata fada masa da abinda tayi yake burgesa da jikin da yake kallo na mazan banza amman sai tace tayi kokari sosai ta kuma burgeni," yayi dan murmushi "da alama kin fara son kallon india ta dubi abincin dake gabansa "kaci abinci mana ya dauki spoon ya cigaba da cin abinci yayi shiru ta fahimcesa idan yana cin abinci baya magana irin dibiyar yayanta kenan yanzu ma tunda ya fara bai ce mata komai ba sai kallonta da yake kawai yana murmushi,"bayan ya kammala basu jima da zama ba aka kira sallahr magarib dan haka ya fita zuwa massalacin dake kasan unguwarsu daga nan kuma ya tsaya tare da wani mutumi wanda anan massalacin yasan sa malam bala bai dawo gida ba dai tara saura yana shigowa kuma kamar kullum ya rufe koina ya samu hally zaune a falo ya zauna kusa daita yana dubanta itama shi take kallo tana jin sallar soyayyarsa na fizgarta ta dan yi murmushi "ka shigo gida kenan .?"

"Eh ina kike son naje  my princess? shima ya mayar mata da tambayar bani inda zani daga gida sai aiki sai massalaci wani mutun mai suna malam bala yace na gaisheki mutumin yana da kirki sosai ,"ina amsawa  wata zan kaiki ki gaishe da iyalinsa kema dai kisan wasu acikin unguwar nan ta amsa da lallai kuwa da ka kyauta ni gida ma nake son zuwa gurin ammi nayi kewarta sosai aunty shafiq ma tunda suka zo da yaya sau daya bata sake zuwa ba wai bazata gane gidan ba "to bari inshaallahu duk zan kaiki cikin satin nan idan na samu lokaci ,ya  karasa mgnr yana kai hannunsa ya shafa gefen fuskarta zuwa wuyanta sannan ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta yayi mata magana cikin rada ,nan take ta fahimci manufarsa wata irin kunya ta rufeta gbdy ta rasa inda zata saka kanta  da dariya kema kina bukatar mikinki ."

"Nan take ta gitsine fuska "Aa ta fada saboda kada ya kara nata kunya "Kunya dai kunya dai ni na rasa wace irin kunya ce haka kike daita batayi magana ba illa mikewa datayi  da niyyar shiga daki dan ta shirya kafin shigowarsa .ya rike hannunta cikin kallonta "ina zuwa muna hira ?ta dawo ta zauna kusa dashi ya jawota jikknsa ya kwantar daita yana kallon fuskarta yace ina son mu dan yi kallo kafin mu kwanta ya kika gani ?".
"Tô kunna bari naje yanzu zan fito zan dan watsa ruwa ne a jikina bana son dare yayi sosai ban yi wanka ba "hakan yayi kyau ina jiran ki na siyo miki abun dadi ya fada yana sakar mata hannu ta tashi ta bar falon zuwa dakinta , a daren sunyi kallo sannan sun kwana cikin jin dadi fiyye da jiya yayinda bangaren oga jaguwa yayi  kuwa yayi kwanan wahala sakamakon tunanin abar qaunarsa da shaawarta tun lokacin da tace zata kirasa back yake dakon kiranta amman har karfe biyun dare daya kasa runtsawa shiru  bata kira shi ba ,sai ya dauki wayarsa da niyyar zai kirata sai mummunar zuciyarsa ta hanashi tare dayi masa gargadi mai karfi .

Ya janyo tautausan bargo ya lullube rabin jikinsa yana tunaninta , idan kwakwaluwarsa ta hasko masa bakinsu hade dana juna  sai yaji zirrr a sansar jikinsa idan ta hasko masa closing dinsu yana romancing dinta shima sai yaji tsigar jikinsa sun mike yar-yar  gbdy ya takure jikinsa guri daya yana jinta gbdy  ajikinsa numfashi ma da kyar ya dinga fitarwa ga wani faduwar gaba da yake ji akanta ranar dai bai wani samu isashensa bacci washegari kuwa bai tashi da wuri ba sai   gurin karfe goma shabiyu da rana  ya tashi  ya shiga wanka bai dade da fitowa  ba anas ya turo kofar dakinsa  ya shigo alokacin ya gama shirya kansa cikin wasu hadaddun  kananan kaya farar  riga da wando light blue yayin da takalmin dake rufe dakafafunsa ya zamo canvers ne  farare sol ya dan dago ya kallesa ta cikin mirrow murmushin gefen baki jaguwa ya sakar masa  "lover man har ka karaso ai na dauka sai irin biyun din zaka shigo ?"kai dai ka sani  dasa ido  kaima kayi kokari ka zama kamar din a  dinga misali da kai "haba dai Ana's ina zan iya abinda kake yi kawai  na zauna ina fadawa mace ina sonta ai kauyanci ne  da sharme wallahi jiya maganarka dariya tayita bani wai muradin raina  imagin ma wa yarinya karama kamar hally ya fada yana sake murmushi sannan ya dauki kwalbar turare ya feshe ilahirin jikinsa "zaka sa nayi maka mummunar addua akan soyayya fa ,"ka dade bakayi ba idan ma kayi na shiga damuwa kai  ne aciki muje ka rakani wata yar unguwa ya dauki agogon diamond fari sol  ya daura a tsintsiyar hannunsa ya fara tafiya "muje ko !"
Ya biyosa abaya suna taku a hankali suna zolayar junansu har suka karaso  babban falon gidan inda suka iske sauran abokansu zaune suna zukar tabar wiwi "zamu dan fita amman yanzu but bazamu dade ba zamu dawo kowannenku ya zauna a shiryensa akwai mahimmin aikin da zamu tautauna akansa yana gama fadar haka ya sa kai batare daya tsaya yaji abinda zasu fada ba anas ya biyo bayansa zuwa haraban gidan suka bar zuciyarsu da kunci da watsi Watsin inda zasu tsaki kamil yaja da karfi "kuna ganin lokaci bai yi ba da zamu fara aiwatar da nufinmu ba ?lokaci yayi mana wallahi idan nace muku closing dinsu yana min dadi nayiwa allah karya ka duba ko operation zamu fita hankalinsa na kan anas baya kowa gargadi mai karfi sai Ana's a komai sai ya nuna bambamci komai Ana's dai anas jubi ya fada cikin tsananin bacin rai "ku matso kuji suka matso a tare jabir yayi maganar sirri a tsakaninsu a tare suka kwashe da wata magaukaciyar  dariya "gasky wannan shawarar tayi daga yau zamu fara aiwatar da nufinmu shigowar eku ne ya katse masu maganarsu ya tsaya yana tambayarsu ko akwai abinda zasu bukata zai fita kowannensu yace bai bukatar komai dan haka ya juya ya fice ."

A hankali suke tafiya acikin mota suna cigaba da hira har suka karaso bakin get din hospital din  tanwer suka shigo kai tsaye cikin haraban hospital din kasancewar makeken get din a bude yake "me kuma zamuyi a hospital?kasa ido mana kaga ikon allah ,
"hope ba wani ne cikin yanuwa bashi da lafiya ba ?
idan wani ne me zai kawo mu nan bayan ga sadiq wata nazo gani ya karasa maganar yana kokarin  parking din motarsa a inda aka tanada domin ajiye motoci ya soma kokarin fitowa yana duba agogon dake daure a hannunsa daya  da rabi adaidai yana gama fitowa lokacin tanwer suka jero tare da doctor muyis da fadela abokiyar aikinta yayinda doctor muyis ke  faman yi mata naci da magiya ."
suka tsaya a bakin motar tanwer fadela na cewa "haba tanwer ki tausaya masa  mana ki dan samar masa gurbi azuciyarki ko babu yawa ne a soyayya baa son ka zurfafa kiyayya "barta kawai fadela só take ta kasheni , tanwer tayi murmushi "haba fadela  wallahi a halin yanzu  bazan iya wahalar da kowa a soyayya ba  ,kai kuma dr allah bazai sa na kashe mutun ba ."da wahalar da zuciyata da kike ai gara ki kasheni zan fi bukatar mutuwa akan wannan rayuwar ko ba haka fadela? "aa bazaa yi haka ba dr ta dai amince cikin sauki da dadin rai mu sha biki ba sai an kai ga haka ba ,ta fada tana juyawa ni zan wuce ana jirana naso ma muje tare da tanwer ne amman yanzu ina cewa muje zata fara dojewa ita dai ban san abinda mutane suka mata ba da bata son shiga cikinsu ? ta nufi gurin motarta tana magana ta bude ta shiga gidan baya ta zauna tanwer taji wani abu acikin maganar fadela wasu kuma sun bi iska  tayi murmushi  har fararen hakoranta suka bayyana tana kokarin sake cewa wani abu kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya harde hannayensa a qirjinsa  rikitattun idanunshi akanta yana kare mata kallo ,kasa magana tayi nan take kuma ta sanyawa jikinta natsuwa ta shiga hankalinta hatta murmushin dake  kwance akan fuskarta ta dauke qirjinta ya shiga bugawa da karfi tamkar zai fasa qirjinta ya fito waje cigaba da kallonta jaguwa yayi fuskar nan nashi babu annuri sam "ya kika yi shiru madam dina inshaallahu ki fadi min  abinda kike son nayi ki soni ,wallahi  ni magana dake ma kadai yanasani farinciki , bata kallesa ba ta furta "dan allah dr muyis kayi shiru na shiga rudani né fadela data shiga motarta kam batasan wainar daake toyawa ba sai dai ta dan leko ta side din da take zaune domin tayi musu sallama direbanta yaja suka wuce .
a hankali  jaguwa ya soma taku cikin isa da izza hannuwansa duka zube cikin aljihunsa yana kokarin karasowa inda take ai nan take zuciyarta ta shiga karkarwa ."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️38


......tafiya kawai yake fuskarshi babu annuri kana kallonsa zaka fahimci zallar 'bacin ran dake tattare dashi ,ran nan nashi yayi baki yayi kololuwar 'baci yana gama karasowa inda take tsaye bai kalli dr muyis ba ya kai kyakkyawa hannunsa ya rike tsintsiyar hannunta gam cikin nashi yana tsareta
da rikitattun idanunshi masu matukar firgitawa da hargitsawa mutun lissafi , a qalla ya dauki minti goma yana tsaye yana kallonta zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ,yana tunanin abinda ya kamata yay mata ,wata zuciyar ta bashi shawarar
ya hau dukanta yana yaryarfa mata maruka ko hakan zai sa yaji saukin zugin da zuciyarsa ke yi ,yayinda wata zuciyar ke gargadinsa ba dan jin tsoron abinda zai faru ba sai dan kasancewarta yarinya .
wasu minti goma suka shud’e yana tsaye yana kallon kyakkyawar fuskarsa , kafin daga baya ya jata zuwa gefe wanda tazaransu da dr muyis bai fi taku hudu ba kuma tana da tabbacin duk abinda jaguwa zai fada mata tabbas zai ji ,ita a tunaninta ma gurin da yayi parking din motarsa zai kai ta ko cikin motarsa sai taga sabanin haka, ganin zai soma magana cikin zafin rai tace “muje daga can ta nuna masa nesa da inda suke komai zai fada mata babu me ji ,amman da yake ransa a bace yake uwa uba kuma ga tsabar taurin kai sai cewa yayi “bazaa je
ba anan nayi niyyar magana banga uban daya isa yasa na kara taku daya daga nan ba tukun ma me kike yi tare da wannan mutumin ? qirjinta yayi mugun dokawa da matsanancin karfi har ta kasa bude bakinta,hakan ne ya bashi damar cigaba da magana "bakin san Idan mutane suna ganinki da maza kala dabam dabam ba zasu dauka kmr baki da kamun kai ne ba? “wallahi mutane zasu daukeki useless idan kika cigaba da kulaye kulayen maza “stil shiru tayi ta kasa magana duk da bakinta abinda yake son yi kenan ta tsaida shi daga abinda yake fad'a ."


hannunta dake cikin nashi ya sake matsewa sosai yana sake tambayarta cikin zafin rai "me yasa kika tsaya dashi ?"Ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "ban sani ba kai ne dai kake ganin kamar bani da kamun kai ,amman kowa agurin nan yasan ni wacece,sai abu na gaba ,adnan am not useless your sister’s your aunty’s I wont put your mother coz I use’s to respect mum, but your sisters are useless , your Aunty’s are useless even the children that you wont to born they wil be useless inshaallahu, in allah yaso ya yarda sune useless banice useless ba idan kaga dama karka kara zuwa inda nake ko yanzu ai ban kiraka ba kona kiraka ne da zaka fada min mgnr banza .”?
Shiru yay yana kallon karamin bakinta da take motsawa a hankali tamkar ba daga cikin zafafan magana ke fitowa ba yana jin wani irin zafi daga cikin kasan zuciyarsa idan yace bai ji zafi da ciwon maganarta ba yayiwa kansa karya "ita kuwa wani sanyi dadi ne mai tattare da farinciki ya lullubeta alokacin daya, duk da

Please Login or Register in order to submit comment