Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa gidan baya ya shiga yana  cewa "hope  kowannenku  yayi shiri  me  kyau? "  sosai  suka bashi amsa  motarsu na kokarin fita daga gidan Idanunsa  ya sauka  akan wani dattijo  zaune a gindin bishiyar dake gefen gidansa nan take yace wa eku "stop ! ".eku  ya tsaya   nan take mutumin ya mike tsaye yana kallon motocin  jaguwa masu shegen kyau da  daukar hankali da hannu ya yafito  me gadi  ya k'araso  da d'an saurinsa  ya   tsaya yana rusunwa  "wacan mutumin fa me yake yi  anan ? "wallahi oga gurinka yazo wai yana son ganinka tun jiya byn fitarka yazo nace baka nan shine dazu byn dawowarka sai gashi ya dawo  na  shiga domin nasar maka sky  yace Kuna meeting shine na dawo na sheida masa ya dawo Koda karshen sati ne amman yace lallai sai ya ganka ."

shiru  jaguwa yayi  yana nazari sannan ya dan Kalli Inda dattijon  mutumin yake tsaye cikin kod'ad'un kaya marasa fasali  yana cigaba da nazarinsa ,a hankali ya fito ya soma tafiya   har ya k'araso garesa , dattijon na ganinsa ya shiga rawar jikin "barka da fitowa ranka ya dade  "barkanmu  baba ya kwanan iyalin ?" Alhamdulillah duk muna Lafiya  ,
jaguwa ya kad'a Kai sannan yace  " baba fatan  dai lfy kake son ganina ?"dattijon ya marairaice murya  kmr zai yi kuka sannan ya fara mgn muryarsa na rawa gwanin tausayi "daman matsalace ke tafe dani gareka a wajen mutane na samu labarin irin taimakon da kake yiwa mutane ".  jaguwa na jin haka ya sauke numfashi yana dubansa a tsanake  " Ina Jinka baba wacce irin matsalar ce ?"daman akan yarona ne  shekararsa biyar kenan da kammala karatunsa  na  degree sai dai  yadda kasar nan tamu ta  dawo yasa  har yanzu yake gida zaune, duk Inda yaje apply din aiki sai ace sai ya biya kamin dubu dari biyar kudin office kafin a daukeshi  gashi  bashi da hanyar da zai samu kudin,  ni ya kamata na biya  masa ya samun aikin  to ni din ma babu dan na abinci ma da kyar muke samu, dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka  ka samo masa aiki ko Kuma  ka yarda ya kasance a karkashinka ya karasa maganar yana zubar da hawaye ."

jaguwa yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya "karkayi kuka baba    inshallahu zan yi iyakar kokarina  yanzu dai Ina kan hanya ne zani wani  aiki amman ka dawo zuwa  karshen sati da yaron   inshallahu matsalarka  tazo karshe dattijon ya soma k'okarin durkusawa jaguwa domin yi masa godiya, jaguwa  yay saurin sa duka hannuwansa ya taresa "haba baba karka min haka  mana " na gode  d'ana Allah ya albarkaci rayuwarka , Allah yasa ka gama da duniya lafiya ,Allah ya jikan iyayenka  idan sun rigamu gidan gsky, idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu Lafiya mai amfani na gode na gode  daman da gaske ana samun mutane irinka  ?karka damu baba ya k'arasa maganar yana tsaida dattijon bisa kafafunsa ya Ciro  dubu goma  a  aljihun wandonsa ya mika masa "ga wannan kayi kudin  mota  yana gama mikasa ya juya ya shiga mota suka bawa motacinsu wuta suka bar unguwar ,da sauri dattijon ya Ciro  wata rubabbiyar   wayarsa ya shiga neman  number d'ansa  domin yi masa albishiri  ."

******

Bangaren  minister of health  kuwa  gbdy  hankalinsa yaki kwanciya   kullum yana manne da hjy zainab yana rarrashi wacce kuka ya zame mata abincin ruhinta , yanzu ma zaune yake kusa daita  yana aikin daya  saba tare da babban  amininsa alhj Tahir  dake k'okarin shawo kanta   "kada kiyi fushi  da hukuncin  Allah  zainab  wannan  abu daya faru gbdy bai mana dadi ba sai dai  bawa  baya wuce qaddararsa  Allah ya rigada ya  qaddaro surayya zata fad'a cikin wannan tashin hankali bamu Isa mu canza mata qaddararta ba,  fatan mu  dai Allah yasa bata cikin tsanani cikin muryar kuka tace "na kasa  jurewa   dady  dake hk take kiransa kmr yadda Ib ke kiransa "  yau  da mutuwa tanweer tayi na binneta da  zan fi samun natsuwar zuciya  amman Ina raye tanweer  tana hannun  'yan fashin da ko labarinsu ba'a samu ba , taya kuke tunanin hankalina zai kwanta ?".  Suma kiramu muji me suke  bukata daga garemu sunki  ta k'arasa maganar tana kallon saman falon hawaye masu zafin gaske na gangaro mata wanda zafinsu da rad'ad'insu ya wuce tunanin mai karatu .
"wannan haka ne  amman duk da haka  addua zamu  taru muyi allah ya bayyanata cikin koshin lfy "amen ta furta a kasan makoshi tana cewa ya jikin Ib kuwa?   kullum Ina sa ranar zanzo na dubasa   mutanen dake shige da fice agidan nan  zuwa jaje ke hanani  fita ammn inshallahu zan samu lokaci na  leko na dubashi  .
"to jikinsa dai da sauki zamu ce Allah dai ya iya mana  da iyawarsa dan rayuwar Ibrahim na daf da fuskantar matsala da Kuma qalubalin rayuwa ya kasa jurewa rashin tanweer  "Allah  sarki ib yana qaunar  tanweer  kmr yadda yake qaunar rayuwarsa  inshallahu zata dawo har ma suyi aure  ta k'arasa maganar tana sake matso ruwan  hawaye sun dade suna tautauna wa akarshe  minister ya  kira  cp  yaji halin da'a ake ciki  ,byn  cp   ya d'auki Kiran  suka gaisa "wai ya ake ciki ne da batun yarinyata  shirun fa yayi yawa zuciyata ta fara tsinkewa Ina Jin kamar Allah ya d'auki raina  na huta ? na kasa jurewa rashin diyata da rashin kwanciyar hankalin matata ".naunayen ajiyar zuciya cp  ya sauke sannan ya fara magana a natse"mun baza mutanen mu  cikin   gari    yanzu haka mun  fara  samun improvement akan lamarin   "to alhamdulillah   Allah ya taimaka   yasa aga  yarinyata  cikin koshin lfy "karka damu inshallahu komai yazo karshe ka kara mana lokaci kad'an "na gode na gode "  sukayi  sallama minister ya  fuskanci  hjy zainab tare da yi mata albashiri da abinda cp ya fad'a masa  nan take farinciki ya mamaye zuciyarta  shi kuwa alhj Tahir  cikinsa ne  ya duri ruwa gabansa ya  shiga  fad'uwa hankalinsa yayi kololuwar  tashi .
babu shiri yayi musu sallama   ya  shiga motarsa direbansa ya ja suka  kama hanyar zuwa gida ,yasan ya taro wa kanshi  match tunda yayi sanadin da'aka d'auke tanweer  wayarsa ya Ciro yanata  Kiran number jaguwa  ana ce masa akashe  take har ya k'araso gida bai samesa ba ,  ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa  yasan muddin  su jaguwa sukazo  hannu   kashinsa ya  bushe domin asirinsa ya tono ."

fitowa yayi da sauri daga cikin motar bai tsaya jiran direbansa ya fito ya bude masa ba  kmr zai tuntsura ya shiga cikin gidansa gumi na karyo masa ta koina a sansar jikinsa  kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya rage kayan jikinsa ya shiga zariya  yana neman mafuta , yana tsaye hjy baseera ta shigo tana binsa da kallon mamaki dan ta kwana biyu bata gansa cikin yanayi irin haka ba  "wai Lafiya ka shigo kamar wani kububuwa me km ya faru ? tsaki yaja   yace "babu  komai . "To daga Ina kake yanzu "?. daga  gidan minister nake ya bata amsa yana fifita da hannunsa dan wani irin  azababben zafi yake  ji ta koina    tana Jin  haka na gane komai   ta  kama  gabanta  zata fita ya d'auki remut din ac yana kokarin  qara karfinta tare da cewa  "ya kuma zaki wuce ki barni ga dan iska kin samu  kin tmbyeni na baki amsa kawai zaki juya ki kama gabanki  "oh to ni me  zanyi  maka ?"   zata sake magana ya d'aga mata hannu"jeki kawai bananason jin komai tunda babu abinda zakiyi shasha kawai  ya  fad'a a matukar fusace  yana juya mata baya.
tabe baki tayi a ranta tace  "ai Kai ne Sha Sha ,mutumin banza kawai  da bai san ciwon kanshi ba aurenka ko hasara duk a tunaninka ban San halin da kake ciki bane  byn na san komai  a juri zuwa rafi dai wata rana tulun zai fashe  juya tayi ta barshi tsaye  yaji da damuwarsa .ta nufi gurin  d'anta ta bashi maganin karfin jiki  dan ta sha alwashin bazata sake yarda da tsarin mijinta  ba   hk kawai  ta rasa tilon d'anta a banza, gbdy magungunan da yasa  nazifi ya rubuta masa an siyo sai dai bata bashi ya sha ba  wasu dabam ta bashi  jikin ne dai nashi yaki daidai saboda an rigada an karya masa garkuwar jiki " .

*******

Sannu a hankali motarsu  jaguwa   ta d'auki  titin airport  suna  gama  Isa kowace  mota  ta samu guri  ta  tsaya a Inda jaguwa  yayi  umarni tare da saka fuskokin roba , motar  da  jaguwa yake ciki  ne kawai  ta  Kai cikin  mutane sosai. shiru yayi yana nazari da karewa gurin  kallon da  tarin mutane dake bin mutane  ko suna bukatar canza kudi .facing cap dinsa ya cire ya juya ta baya ya cire glass din  dake manne da idanunshi ya makala a goshinsa   bayan kamar minti   talatin  ya  ciza lip's dinsa na kasa da karfi  ya  fito  rike da bindigarsa  ak 47  yana gama  fitowa  ya fara sakin  harbi kamar ruwa  domin  Kore  mutane dake safa da marwa agurin , kafin  kace me mutane sun rud'e tare da neman gurin 'buya  bayan kmr minti biyar sai ga anas shima  ya fito had'e da   harbi   nan  ma sauran  mutanen da  suka rage suka  tarwatse ya tsaya yana huci "iam  bally  the deadly one, mutun ya kama kanshi idan baya son ya bukunci lahira ."ya fad'a yana sauke numfashi .

jubi ya fito ya saita bindigarsa wani lungu Inda ya hango wasu mutane suna likensu  sai dai  bai  yi harbi ba bisa umarni  jaguwa dake duk suna Jin  maganarsa  sakamakon connecting din da yayi da wayoyinsu  ya sauke numfashi yana cewa  "as you can  see am gentle man to the core , I don't take what's beyond my capacity disprit  that iam not the one to be taking for granted , go and ask those how have done such before ya k'arasa maganar yana numfasawa  tare da gyara  tsayuwarsa eku remo ya k'araso ya tsaya gefen jaguwa rike da bindigarsa yana cewa ""Jaguwa ne da kanshi  d'an   mutuwa  Kuma mutuwa  ta dade da kar'basa  amatsayin d'anta  so everyone should run for his life "yana gama fad'ar haka ya koma gurin tsayuwarsa ya had'e da sauran  yan'uwansa suka tsaita bakin bindiga ."

Shiru jaguwa yayi ya  fuskanci office din da aka kwatanta masa jubi ya matso kusa dashi  yana cewa  " jaguwa let's move to his office  jaguwa yace "da alamun bai nan jikina ya bani  amman Kuma wannan lokacin anamdi ya bamu "to mu juya mana mu koma  girgiza masa Kai yayi yana ciza lips dinsa na kasa "to ko zamu shiga office office ne muyi operation  ?"no ya bashi amsa atakaice "okay ya fad'a yana gyara bindigarsa .gbdy gurin ya d'auki shiru  ciki kuwa har da jami'an tsaro dake aiki agurin kowa nason rayuwarsa dan da ganinsu an san ba kananun yan fashi bane ."

Loakaci zuwa lokaci yake duba agogo dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Bayan  kamar minti talatin sai ga wata  mota   fara sol  ta  shigo  gurin. tun da suka shigo tsoro ya kama na cikin motar  sakamakon ganin gurin shiru babu motsin mutane  jaguwa ya gyra bluetooth din dake manne da kunnensa  "eku  ga mutumin da muka zo dominsa nan ya shigo  "okay   boss I will do my duty .cike da matsanacin tsoro   direban motar yaja burki yana k'okarin juyawa  sakamakon ganinsu take eku  ya harbi tayar motar .
tsayawar motar ke da wuya yaga  mutane sun zagaye motar  kamar almara sai ga jaguwa ya  bayyana a tsakiyarsu  direban yayi saurin kife kanshi akan stearing motar yana rawar jiki , jubi ya bude murfin site din baya Inda alhj  aminu ke zaune    ya fito dashi  yayi cilli dashi  gaban jaguwa ya tsaita kanshi da bakin bindiga  "where's the money jikin mutumin na rawa yace "it's inside the car ya fad'a yana nuna motar "cheek !  inji cewar jaguwa".Anas  da kamil suka nufi motar suka duba can byn  second biyu anas yace "comform it's there "okay fine ,move move kamil ya fad'a yana ture alhj aminu " face the grand if you do nonsense i will kill you ,nan take alhji aminu yay sujjada gbdy ilahirin jikinsa na kyarma .

Suka jefa jakar kudin byn motarsu  jaguwa ya shiga byn mota sauran dake shirin shiga  sai ga jiniyar motacin police suna harbi ,ai nan take qarar  harbi ya karad'e gurin police na harbi Suma suna yi  kowa ya shiga mota har sun fara ja  ya saura  kamil  ne bai samu damar shiga ba  ya biyo motar aguje yayinda sauran yan'
uwansa ke harbin yansanda suna Kiran sunansa "km run kayi gudu mana  suna miko masa hannu shi kuwa gudu yake da iyakar karfinsa yana k'okarin Isa ga motar gabad'aya suka mika masa hannuwansu suka  had'a baki "zo kamil zo  gamu maza mana kamil ka kara  gudu  suka fad'a hankalinsu a tashe .ganin   halin da ake ciki  yasa  hankalin jaguwa yayi matukar tashi nan fa ya shiga bud'ewa police wuta daf da kamil zai shiga mota wani police yayi nasarar harbinsa a kafa wata razananniyar qara ya saki ya durkushe kasa cikin azaban ciwo tare da rike kafarsa  "...

Mmn sudas💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️14

.....Cike   da  zafin  rai  da zafin  zuciya  jaguwa   ya  soma   k'okarin   fitowa daga  cikin  motar  yana gyara   bindigar   hannunsa   nan  fa hankalinsu   anas  yayi  kololuwar   tashi , anas  ya rud'e    yay   saurin dakatar  dashi  ta hanyar Kai   hannunsa  qirjinsa  "karka   fita  jaguwa , kaucewa  yayi  yana cewa    "ku   wuce  kawai   zanji   da  komai "dan  Allah   jaguwa  karkayi wannan  kasadar ".  bai  sake    saurararsa   ba ya  soma  harbi  gumi  na  karyo   masa  ,  hakan  yasa   da   sauri  kowannensu   ya  cigaba   harbi  da  iyakacin kwarewarsa ."
da  mugun   gudu   jaguwa  ya  isa inda  kamil   yake  durkushe  rike   da  kafarsa  yana  cewa "km    bani hannunka " ,  cikin  tsananin  tashi hankali   kamil  ya d'ago kai  sai dai bashi  da kuzarin da  zai mika masa hannunsa  " nace  ka bani hannunka ya  sake  mika  masa hannu  shima  kamil ya mika  masa  ya  rike  hannunsa  gam cikin nashi   yana cewa "taho  km   ka  mike dan allah karka  bari mu  rasaka  "  kamil  ya fara   k'okarin  mikewa adaidai  lokacin da sky ya  juya   kan  mota  zuwa  inda   suke   tare da yi musu tsakani da  police officer's ,  cikin   azama  jaguwa yace " maza   mike  km  da taimako  allah  jaguwa ya shigar  da  kamil  cikin  mota  ai  kuwa  shigarsu motar keda wuya suka figi  motar  aguje  nan motocin   'yansanda suka  biyosu  da   mugun gudu  suna  harbi   suna danna  jiniya ,  haka suma bangaren   jaguwa    harbinsu suke  ,   gudu sosai motacin  jaguwa  sukayi   har suka  yiwa police  nisa  a karshe suka  daina  hangosu ."

a matukar  wahale suka k'araso  gida  jaguwa  yay  saurin fitowa daga cikin mota   ya  k'arasa  da sauri  ya  bud'e  kofar shiga cikin ainihin falon gidan , su  jubi  suka  kamo  kamil  suna tafiya  dashi a hankali kafafunsa babu takalmi dan tuni sun cire masa tun acikin mota ,Kai  tsaye suka  nufi hanyar  falon   jaguwa  na mussaman dashi    suna  masa sannu,  a hankali suka kwantar dashi akan wani k'aramin  madaidai  gado wanda daman an tanadesa domin irin haka  ,kamil  ya runtse idanunshi saboda azabar ciwo , cike da hanzari jaguwa ya nufi Inda first aid box dinsa  yake ya d'auko  ya  dawo da sauri , eku ya janyo masa kujera  ya zauna  a gaban kamil yana masa sannu  ."

jin  motsin  shigowar motocinsu  da  maganar  wasu  daga cikin yaransa   sama  sama  yasa tanweer  lalla'bowa babu takalmi  a ka'fafunta tai hanyar  babban   falon   gidan    tana  bin bango tana  qarasowa bakin kofar falon ta tsaya  a hankali ta bud'e kofar ta shiga  bata   ga  kowa  a falon ba,  kasa  kasa  take jiyo  magangansu  , kawai   ta nufi   wani  dogon  korido  Inda  take  zaton daga  nan sautinsu yake fitowa  , a hankali  ta tsinci kanta acikinsu   kowannensu cikin tsananin tashin hankali , jaguwa  zaune a gaban kamil   cike  da tausayawa  yana k'okarin  cire   masa   harsashi . binsa tayi  da kallon mamaki  qirjinta na wani irin bugawa da matsanacin karfi shafa  idanunta   tai  hade da runtsesu  na second biyu sannan ta bud'e tana sake  sauke idanunta akanshi wanda zuwa   lokacin har yay nasarar  ciro bulet   din  yana kallo sannan  ya  saka acikin  farantin  silver dake rike a hannun jubi, yayinda sauran ke zaune cikin  tsananin tashin hankali gbdy idanunsu ya rufe babu wanda hankalinsa ya Kai Inda take tsaye ."

naunaye ajiyar zuciya  suka sauke lokacin  da jaguwa ya  cire wa kamil bulet  ita Kuwa tanweer zuciyarta ta shiga rawa had'e da tsinkewa  ."me zata  gani  yau ? daman likita ne shi  ko kuwa mafarki  take  ?   yes  wannan ba  mafarki take ba shine tagani  zaune  ya cire  bulet a kafar abokinsa, kasa tayi da idanunta tana kallon bayansa nan  idanunta ya  hango  bindiga pestol  soke a abayan wandon  jaguwa  ,nan   take ta  sake fita  daga  haiyacinta "bindiga ....! ta furta a kasan ranta " me   Kuma yake  yi  da bindiga ? ya  Allah karka sa  abinda  zuciyata ke hasashe  akansa ya zama gaskiya dan bai cancanci haka ba " wani kuka ya kufce mata   ta juya da sauri tana  shesheka   wanda  hakan  yasa  gbdy suka   d'ago suka ganta tana sarsarfa  , cike da matsanacin firgici   suka  tsura ma jaguwa   Ido    dan  jin abinda zai ce  bai yi magana ba haka zalika bai  nuna alamun  damuwa atattare dashi   ba , ya  mike  tsaye yana
furzar da numfashi tare da yiwa kamil sannu" ka kwanta ka huta kafin  akawo maka abinci ya gyada masa Kai  yana cewa" na gode abokina Ina alfahari da Kai ,nima haka   ."

jubi  ya dube jaguwa  yana cewa  "wallahi ban  ta'ba   shiga tashin hankali  ba irin na  wannan  lokacin na tsorata  matuka   na sadaukar zamu rasa  kamil  "ba  kai kad'ai ba inji cewar anas  tafiya  jaguwa  ya  fara a hankali   suka  biyosa   a baya  har gurin   shakatawarsa    "da'ace  sunyi nasara akanmu   zamu  iya rasa rayukanmu gbdy". sai lokacin jaguwa ya motsa lip's dinsa   "ina ai sai dai idan  tawa ta kare sannan zaku iya shiga  wannan  hali  amman muddin Ina tsaye akan kafafuna babu wanda zai yi  nasara  bare har mu rasa rayuka "  ya  karasa maganar  tare da  tsayawa  cak ya  rike  karfen  runfar dake  kafe acikin   gurin  shakatawar , "hakika Nima na karaya  inji cewar jabir  " Karku  ta'ba rungumar  Karaya arayuwarku duk halin da zamu shiga karku karaya saboda    rashin samun nasara  ba namu bane ,a duk lokacin da naga Kun Karaya  sai  naga kamar tun asalin ku din ba jaruman gaske bane, sannan baku ne jarum da mukayi gasar mutuwa dasu  ba  ."

murmushi sukayi gbdy suna sauke numfashi  "uhm wannan fa ba kamar gasar mutuwa bace  ,gasar mutuwa kowa yasan  mun saida rayukanmu ne dan biyan bukatarmu  wannan fa ?"bayan sai da rai har da  tozarci  zamu  janyowa  gangar  jikinmu  idan muka tsinci kanmu a hannun jami'an tsaro ".anas ya karasa maganar yana  dafa kafad'ar  jaguwa  "yanzu dai barkanmu  allah  ya k'ara karemu  ." ameen  jaguwa  ya fad'a acikin zuciyarsa.   "ka zauna    kana bukatar  hutu, jaguwa   ya  zauna  akan d'aya daga cikin kujerun gurin yana lumshe idanunshi " me za'a  kawo maka ka d'an sha ? ya  girgiza  masa  Kai  alamun bai   bukatar komai , zama  anas yayi kamar yadda sauran abokansa sukayi  yana cewa  "ya za'a yi da wannan  yarinyar ta rigada taga komai , koma nace  taji wasu abubuwa akanmu ? ,yana  d'aya daga cikin abinda yasa kaga  banason yarinyar nan agidan nan "."me taji ?."Ko me mu kace ?yay masa  tambayar a dan kufule " idan Kuma taji taji kenan shikenan daman abinda  take bukatar sani kenan  tasan su waye mu " ya k'arasa maganar yana jan  dogon tsaki tare da  jin bakinciki  da takaici, haka nan Kuma ya tsinci Kansa da Jin fad'uwar gaba mai tsanani ".

Koda tanweer ta koma d'aki  ta kasa  tsaye ta kasa zaune sai zariya take  acikin d'akin  ita kad'ai, ta saka wancan ta kwance , kwakwaluwarta ta shiga tunani mai zurfi, babu abinda zuciyarta bata kisama mata ba akansu , abu uku  zuciyarta ta tsayu akansa  shi din  dan fashin ne  ko Kuma jami'in sirri ,ko  likita ,  idan ba haka ba me yake yi da bindiga ajikinsa ?  ta kasa hakuri dan  haka ta sake fitowa tai hanyar boys quarter nan fa hankalinta ya sake tashi ganin yadda yaran jaguwa  ke fitowa  da manya  bindigu suna adanawa a maboyarsu ,mutuwar tsaye tayi har sanda suka kwashe komai  suka  d'auki  katuwar jakar kudin da suka shigo dashi  suka nufi hanyar Inda jaguwa yake tare da abokansa suna tautaunawa ,  cike da matsanacin tsoro ta biyo bayansu  a tare suka k'araso ta ra'be jikin wata bishiya kasancewar yaran jaguwa  suna   gabanta yasa jaguwa da abokansa kasa ganinta ."

sky ya ajiye jakar  kudin a gaban jaguwa yana cewa  "boss ga kudin operation din ". operation ? ta furta a kasan ranta zuciyarta  na tsananta bugu kamar zai fasa  qirjinta ya fito waje , tayita  tunanin abinda  manufar operation yake nufi  acikin ranta .
a natse Jaguwa ya d'ago idanunshi  yana ciza lips dinsa na kasa  sai daya d'auki minti biyar sannan ya gyada Kai , yay musu alamun su wuce suka soma k'okarin juyawa  tana ganin haka tayi baya  da sauri ta  la'be dan karsu ganta , gbdy kwakwaluwarta
ta gama tabbatar mata da manufar operation fashi ne ".barin wannan bishiyar tayi ta dawo kusa dasu sosai ta sake makalewa a wata bishiyar ta kasa kunne daga Inda take  boye take jiyo duk abinda suke  cewa  "mun gama da operation din  yau  yanzu dai  a  kasa  kudin   gida  uku nasan inamdi na  nan zuwa  komai dare ya amshi  kasonsa dan bashi da hakuri kmr alhj Tahir  yake "kamar alhj Tahir ta maimaita sunan ?tunanin Inda tasan sunan take gbdy ta kasa tuno Inda ta ta'ba Jin sunan amman tabbas kwakwaluwarta na hasko mata tasan sunan Kuma  na kusa da jikinta ne ".
ko gama rufe baki   jaguwa bai yi  ba sai ga inamdi da eku remo , inamdi ya mikawa jaguwa  da abokansa hannu suka gaisa shi Kuma eku ya juya ya kama gabansa .
guri jaguwa ya nuna masa da hannunsa , ya zauna yana cewa "sannuku Kun sha da kyar lokacin dana ga police sun harbi d'aya daga cikinku naji tsoro matuka, hankalina yayi matukar tashi "sa'anar  armrobber's   akwai dadi akwai saida rai  ,bancin kwarewa irin naka da yanzu kuna hannun police.
"inna lilli wa inna lillahi rajiun" tanweer ta shiga furtawa  tana maimaiwa tasa hannunta duka ta rufe  bakinta dan   kar sautin kukanta ya fito "ya dai  tabbata su din 'barayi ne ........?  " wannan shine dalilin da yasa ya fad'a mata  da tasan shi ko waye shi  da bata kamu da soyayyarsa ba ?wayyohhhly Allah nah ! "wayyohhhly Allah   Adnan me yasa? " me yasa ka zabi wannan sa'anar ?  jikinta banda rawa babu abinda yake  tana kallo  aka kasafta kudin aka bawa inamdi  nasa kason ya ciro  wata karamar jaka a aljihunsa  ya shiga  d'aukar bandir   din daloli yana  zubawa cikin  jakar  har ya gama ya mike  ya sake mimika musu hannu sukayi sallama ya  wuce cikin sauri ."

A hankali ta dinga d'aga ka'fafunta tana takowa  zuwa Inda suke zaune , jaguwa ne  ya d'ago   idanunshi suka  sauka akanta,  cikin  tsananin tashin hankali da damuwa mara misaltuwa  yake kallonta   ,bakinta na rawa ta soma magana cikin firgici  "daman 'yan  fashi ne ku  ?".ta fad'a tana kallonsu d'aya byn d'aya .a rud'e abokan jaguwa suka  had'a baki gurin cewa" no  mu ba 'yan fashi bane armrobber's ne" jaguwa ya mike a natse cike da bakinciki taji sirrinsu  yayinda gbdy  abokansa  suka rud'e  da  ganinta har suka  kasa bambamce tsakanin abinda tace da amsar da suka bata , fuskarsa a murtuke  tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya  kallesu d'aya bayan d'aya  kana ya soma mgn  "babu bambamci  da abinda

Please Login or Register in order to submit comment