Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Ido  sai dai hannunsu bai ka ga jikinta ba  suka hanata ta'ba kowacce mota a daidai lokacin su anas suka fito suka tsaya suna dubanta .

xagi ba kalar da tanweer  bata musu  ba da hausa da turanci Amman Babu Wanda ya kulata haushi ya isheta ta bar gurin mota ta nufi bakin get nan ma babu hali dan me gadi yaki bude mata get duk Inda tasan zata bi ta fita daga gidan babu hali ta shiga maseefa tana cewa " sai na bar gidan Kuma Babu wanda ya Isa ya hanani fita idan na bar gidan sai na sa ankamaku anyi muku hukunci me radadi,wallahi  da Kun San Koni wacece a garin nan da baku tsaya bin umarnin wannan ba Kun  hanani fita ba, ta juya ta Kalli Inda jaguwa yake tsaye jikin motarsa Idanunsa na kanta yana cigaba da kallon bakin tsiwa  "zan nuna muku ko ni wace acikin garin nan tare da juya masa baya.
"Kashi Amman na tausaya miki wannna shi ake kira da power less" juyowa tayi cikin fushi ta Kalli Inda yake idanunta ya sauka akanshi.
yana nan  tsaye sai dai zuwa wannan lokacin   ya harde  hannuwansa a qirji  yana mata murmushin mugunta fuuuu ta nufosa cikin tsananin  fushi da zuciya   tace "zan nuna maka wannnan power din kasa Ido ka gani"tayi  mgnr tana nunashi da yatsa  "me  zaki  iyayi ?ba abinda zaki iya yi min ,ki daina takama da wannan dan matsayin da mahaifinki yake dashi dan baki da wani power da zaki iya min koma" .

ba bata lokaci ta cukumi wuyansa "zaka ga abinda zanyi ".
Yaransa suka bishi da kallo haka ma abokansa me gadi kam saurin kawar idanunshi yayi kamar bai ga abinda ke faruwa ba  ran jaguwa yayi mugun 'baci sai dai bai ce mata Komai ba har sanda ta hau fad'a da maseefa  da zaginsa da fada masa bakaken maganganun ,sai da tayi mai isarta sannan ta  sakar masa wuya ta dukurshe ta zube kasa ta  runtse idanunta  wasu hawaye masu zafi suka zubo mata .
shi kuwa ya matsa gefenta ya tsura mata Ido ransa na quna kafin daga baya ya canza kallon zuwa natsana yayi taku biyu zuwa Inda take durkushe  dafe da goshinta "sorry tanweer bazaki iya komai ba sai da kiyita ihu kina kuka kina zagina
just like a baby ,the great tanweer, kyakkyawar matashiya mai ji da
kudi  yanzu ta zamo abar tausayi  agidan nan , gidan nan fa  ba yadda kike tunani bane dan ba  haka kawai yake ba ko mahaifinki da karfin masu karfin garin nan zasu zo  basu Isa su shigo ba, Ina tabbatar miki muddin kika bar gidan to nine na fitar dake amman rashin kunyarki da ihunki bazasu fitar dake ba cikin sauki ba  ."

wani mugun kallo take masa tabbas da zata samu bindiga a halin yanzu  da zata hakura da son da take masa
ta harbesa ta huta, hakan ne  ma zai zame mata sauki a rayuwarta dan tasan muddin bai duniya zata hakura dashi , "amman bari na gwada miki karfina ai kina son fita ko?tayi shiru taki cewa komai sai hawaye dake zuba "Ammar  bude mata get tuni
taga get ya bude "how dare you? ta fada tare da k'arasawa gurin me gadi ta d'aukeshi da mari "Kai har ka Isa na maka mgn Kaki bin umarnina  kasan kuwa waye ubana a garin nan?  "ubana shine minister of health na garin nan waye shi wannan daya ajiyeku ban da tantiri   ?jaguwa ya matso gabanta ya mika mata roban ruwan faro me sanyi  ",Sha ruwa sanyi  tanweer  kiyi aiki da kwakwaluwa " me yasa mahaifinki zai d'auki mataki akansu ?"anan basu san kowa ba sai  sani , babu dokar kowa da zai yi aiki sai nawa ,gidan nan gidana ne mahaifinki bashi da wani matsayin bashi da power haka kema , shi wannan matsayin ko power  din ki bari sai kin koma gidanku dan anan babu Wanda zaiyi respect dinki babu Wanda zai ga girmanki  sannan babu Wanda zai bi umarninki sai nawa , nawa  za'a bi   kin san me yasa ?Yayi kusa kusa daita "kowa yasan matsayina, dan fashi ne  dake sata wa kasa da kasa the CEO of  armrobber's, armrobber's din daya yi suna da girma a fad'in Africa gbdya kowa yasan jaguwa wato Adnan amad gwoza  anan wa yasan matsayin tanweer har ta bada umarni abi har ta kafa doka abi a zauna ?ke ba kowa bace sai diyar common minister of health da iya garin nan da wasu tsirarun garuruwa  akansansa
sannan mutumin dake zaman banza
a offishinsa da suna yana aiki wa alumma mutumin da  maci   amana kasar ne  , bai San komai ba sai shaye shaye da  neman matan banza da bata rayuwar mutune  wannan shine cikakken  halin mahaifinki da kike takama dashi ,bari kiji da zai fito da boyayyen  halinsa fili babu mutun d'aya da zai ga girmansa  hatta ke kanki sai kin tsaneshi ,wallahi idan baki yi amfani da tunaninki kin kiyayeni ba kin daina  zagina ba zan nuna miki asalin waye jaguwa, zan fito miki da true colour dina, zan yaga miki rashin mutunci ,zan mayar dake baiwa a gidan amadadin bautar da nake miki  , sannan ki zamo daya daga cikin karuwaina nayi duk yadda nake so dake idan bukatata taso nayi ko sau nawa nake so yana gama fad'ar haka ya juya   abunsa ."
ran  tanweer yayi mata zafi ta dinga Jin zuciyarta kamar wuta magangunsa suka tsaya mata arai ta kasa motsi, ta bishi da Ido  kawai
tana kallonsa  ,lokaci  na farko kenan da'aka  fad'a  mata bakaken maganganun da suka daga mata hankali Km akan masoyinta data fi qauna akan komai,sosai  taji mgnr sun tokare mata zuciya Kuma ta kasa Koda motsi balle ta bud'e baki ta zagesa ko ta fad'a masa bakar mgn. shiru tayi tana mamakin abinda ya fad'a akan mahaifinta karyata hakan zuciyarta tayi sai dai Kuma ta rasa dalilin da zuciyarta ke wasi wasi akan maganarsa ."

Shi kanshi jaguwa yayi mamakinta Yana jiran yaji ta balbalesa da masifa da balai akan furuncinsa sai yaji shiru don haka byn ya dan yi nisa kad'an sai ya juyo yaga me takeyi, har yanzu tana zaune tana kallonsa yaga wani bacin rai atattare daita wanda bai ta'ba gani ba tayi sanyi sosai bazai iya karantar meye a kwakwaluwarta ba tuni yaji hankalinsa yayi matukar tashi Anya bai fadi magana dayawa ba kuwa  akan dad dinta ? "Shi kansa yasan ya fadi abinda bai dace ya fad'a ba , jikinsa ne yayi sanyi ya Isa d'akinsa yana tunani   hankalinsa ya tashi dan arayuwarsa baya qaunar ya batawa wani bare ita da yake jin duk saukar numfashinsa yana sauka da tunaninta ne ,yadda yaga yanayinta yasan ya ta'ba zuciyarta" me yasa na fadi abinda na fada "karka damu is a very good respond to her akan furucin bakinta km ya kamata   tasan kadan daga cikin halin mahaifinta .
" amman Kuma karya zamo da gaske zata shirya daukar fansa akanka ? tsaki yaja dan me zakaji tsoro ko ka manta ko kai waye ? Yayi shiru na dan tsawon lokaci sannan yace "babu abinda zata iya  ya kwanta akan kujerar kushin ya janyo pillow kujerar ya rungume a qirjinsa yace"tanweer you can't do anything coz na zamo wani bangare na rayuwarki ."

Tanweer  ta koma d'akinta ta kwanta lamo akan kayan da tayi kaca kaca dashi  sai dai tsabar zafin zuciya ta jima tana tunani wani lokaci hawaye ya zubo mata ta tsinci kanta cikin kewa ta dinga Jin kamar bata da kowa da komai a duniya a tattare daita haka ta yini kwance agurin ta Kulla wannan ta kwance har dare jaguwa yasa aka yi order abinci kala kala wanda yasan take so, ya nufo d'akinta Yana  bud'ewa yaga wani duhu ya kunna wutar d'akin ya sameta kwance cikin yanayi mai ban tausayi ya matsa gareta ya tabata "tanweer "!
ya kira sunanta ai kamar wanda ya dana mata shoking din wuta tayi saurin  mikewa  ta buge masa hannunsa "ka kyaleni ka rabu dani kaji dadi burinka ya cika kasani cikin wani hali ,ka rabani da kowa nawa,kasani cikin damuwa  hawaye ya zubo mata "ka rabani da masoyina ka rabani da dady ka rabani da komai hatta matsayina da mutuncina ka rabani dashi kana Jin wai Kai wani
ne  shiyasa ka dauki kanka a wata  tsiya to bari na fad'a maka sai dai idan ban bar gidan nan a raye ba amman wallahi sai na ......" shiiiiii ki Daina wahalar da kanki coz you can't do anything  ".
  dukkaninsu sukayi shiru suna kallon juna a zahirin gsky  bai so ya fad'a mata abinda ya fad'a ba amman tunda ya fad'a babu abinda zai goge hakan, muryarsa can kasa yace"ga abinci kici ki km  huce  dan nasan baki ne babu abinda zaki iya yi ya mike ya juya yana cewa "ki tabbatar kin gyara d'akin ko ki  kwana cikin datti ".  kifi abincin tayi a kasa "baza'a ci abinci ba, gbdy ta zubar dashi tabisa  da fad'a da tsawa bai kulata ba ya wuce ya tafi a wannan daren dukkaninsu babu  wanda ya runtsa kowa da abinda ke ranshi ke sakawa  jaguwa  da bacci ya gagara ya tashi ya shiga d'akin anas kusan kwana sukayi suna Hira sai dai bai yarda ya Sako mgnr tanweer ba yayinda Zahra tayita Kiran wayarsa bai  d'auka ba , wannan abu yayi mugu mugun d'aga hankalin zahra ta kwana da matsanacin fushi da bacin rai a zuciyarta  da sake d'aukar burikan mugunta  akan tanweer haka ma washegari bata hakura ba tayita kiransa bai d'auka ba shi kuwa duk kiranta  yana gani   amman yaki d'auka  dan bai ga abinda zaiyi da kiranta ba ya cigaba da harkokin gabansa ."
A daidai wannan lokacin kuwa Zahra na can cikin tsananin tashin hankali tsaye cikin bakake kaya kunneta manne da waya  cikin yanayi na tashin hankali take waya da blessing  "matsalata daya yanzu arayuwa shine Adnan ."
"Na fada miki zaki samu Adnan zaki auresa ta kowani hali duk Wanda zai shiga tsakaninki dashi karshensa mutuwa ,mutuwace makomarsa dan haka ki kwantar da hankalinki mu gama da next target dinmu ki natsu karki rusa mana plan idan aikin boka yaki akwai makirci bare zai ci zan sake kaiki wani guri Ina tabbatar miki  duk abinda yake takama dashi da asiri baya cinsa sai mun rusa, mun ruguza komai nashi yaji baya qaunar ganin kowa sai ke ."
"Shine abinda nafi qauna blessing ya zo da kanshi ko bai rokoeni soyayya ba ni dai yazo blessing  bazan iya rayuwa babu Adnan ba "ki daina kaskanrar da kanki  kina da komai da duk wani cikakken nmj zai soki akanshi kece kika fi dacewa da cancata dashi ba wacan  tsinanniyar yarinyar ba, ya soki ya qaunaceki amman saboda rashin hankali da tunani me kyau irin nasa  ya rasa Inda zai ajiye soyayyarsa sai gurin...." "excuse me  blessing don't ever call him mad  karki sake zaginsa idan kina cewa bashi da hankali da tunani ni Kuma da nake so  shi fa ?don't don't try to insult him "am sorry kit  Zahra ta katse Kiran batare da ta jira taji me blassing  zata sake cewa ba ."

*******
Alhj tahir dake zaune yana jiran  zuwn nazifi yace "ya'akayi son  Kai nake jira anyi nasarar samun alluran kuwa da kwayoyin ?"kayi hakuri karka ga kamar Ina cutar da abokinka wallahi rashin tashinsa shine zaman Lafiya da kwanciyar hankalina sai da nazifi ya zauna akan kujera sannan yace "karka ji komai dady an samu da yarda Allah Kuma zai yi aiki ajikinsa sosai  fiyye dana baya dan wannan maganin  bincike ya nuna idan anyiwa mutun sau goma zai iya mutuwa dady ya matso gabansa "kar dai ya mutu amman Kuma idan mutuwar zata zame min hutu Allah ya bada ikon tafiya  "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nazifi ya furta a ransa  qirjinsa na bugawa da matsanacin karfi a sukwane nazifi ya jingina bayansa da abun kujera "dady nifa Ina ganin daga wannan maganin da zan kaiwa mumy bazan sake kawo komai ba nagaji da wannan aiki zuciyata ta kasa samun natsuwa kullum zuciyata na fad'a min Ina cutar da aminina, ruhina yaki samun salama wallahi bana iya runtsawa  dama nasan dalilin da yasa kake son kassara rayuwar Ib Kuma nasan cewar ba cutarwa bace a rayuwarsa wallahi zan tsaya sai Inda karfina ya kare sannan  zan tsaya naga komai ya tafi daidai ."
"kai dan Allah gafara can Sha Sha  dady yayi hanzarin katseshi ta hanyar fad'ar haka "Ashe baka da hankali Taya kake tunanin zan fada maka dalilina  ?  karfi da  matsayin  da  Ibrahim yake dashi acikin garin nan  ne farkon jegon komai ,  muddin na bari ya tashi bisa kafafunsa  komai zai iya faruwa  dani, kasani Kai ma  ko ka manta matsayinsa ne?bama haka ba Ibrahim nada karfin da zai iya komai akan cikar nawa burin  dan haka 
nazifi bazan barshi ya tashi ba Kuma bazan   fada maka dalilina ba dan ko na fad'a maka bazaka  fahimta ba ka dai qara min lokaci ka cigaba da aikin nan  karshensa ma yazo ".
nazifi ya furza da wani huci Yana tsinewa alhj Tahir a zuciyarsa ya mike tare da yi masa sallama har ya kusan Kaiwa bakin kofa yaji muryar alhj Tahir "karka kuskura ka fadawa kowa wannan shiri dan bazan fad'a maka abinda zai biyo baya ba sai dai kawai ka tsinci kanka cikin tsaka me wuya abinda bazan so faruwarsa ba kenan  dan har yanzu kana nan a matsayin d'ana" . gyada Kai kawai nazifi yayi ya fice .

Hajiya baseera zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga nazifi ya shigo hannunsa rike da leda wanda da gani kasan na asibiti ne  dan a zahiri ake iya ganin abinda ke ciki  ,hjy baseera  na ganinsa ta saki  fuska duk da zuciyarta cunkushe take da damuwar rashina lfyr Ibrahim ,
sosai  tayi farincikin ganinsa tana qaunarsa tamkar yadda take qaunar Ib .ya dan rusuna  cike da girmamawa ya gaisheta "Ina yi mumy ?"lafiya lau son ya fama da jama'a da  kokari Kuma ?
"alhamdulillah mun godewa Allah ya  Ib da jiki ? alhamdulillah Lafiya na ta samuwa  ta nuna masa gurin zama da hannunta "ka zauna son "ya samu guri ya zauna yana cewa daga bangaren dady nake gbdy lamarinsa babu sauki a yadda yake kokarin son kassara rayuwar Ib,wallahi mumy abun na matukar bani mamaki haka nan sai na zauna Ina tunanin Anya kuwa mahaifinsa ne da yayi  silar zuwansa duniya ?"mahaifinsa ne nazifi kama daina tantama shi mutun da son abun duniya ke sama da farincikin iyalinsa ".
runtse idanuwanshi yayi "dady na bukatar rayuwar Ib domin kuwa wadan nan  magungunan da yake bukata a dinga bashi da allurai daidai suke da mutuwarsa dan  watan wata rana za'a wayi gari babu shi ."
"Da naji wannan mummunar labari zanfi bukatar  na bar gidan nan dashi sai dai ban san yadda zan bar gidan dashi ba  batare da sanin mahaifinsa ba". ta k'arasa maganar cike da damuwa .
  shiru suka yi na second biyar  sannan  nazifi  ya cigaba da  magana a tsanake "karki  damu mumy daga yau  kisa a  ranki Ibrahim zai dawo rayuwa kamar yadda  sauran mutanen suke yi "zan d'auki nauyin ib bama garin nan  ba kasar ma  zan bari dashi gabad'aya Cikin dakiyar zuciya hjy baseera tace "wannan hukuncin naka yayi daidai Kuma na gamsu dari bisa dari dashi  wallahi , dan haka babu abinda zance maka  sai godiya ,yadda kake son ka nisanta tsakanin Ibrahim da mahaifinsa ta k'arasa maganar tana Kuka sosai  tmkr wacce aka Aiko mata da sakon mutuwar ta ko akace  mutuwa Ibrahim zaiyi ".
"lamarin alhj Tahir akwai ban tsoro da rashin tausayi da Imani "sosai kuwa  yanzu dai a sirrance zamuyi komai ta yadda bazai fargaba  "Allah ya d'aura mu akansa Allah ya kawar da tunaninsa akanmu "Ameen mumy ni zan wuce  duk abinda ake ciki zan kiraki a waya. "To na gode na gode sosai Allah yayiwa rayuwa  albarka ya mike ya fice ."yana jinina girman alamrin dady ,gbdy ya gama ganosa  Kuma yana tare da kwararrun  hujojin da zai sa jami'an tsaro su tunhumeshi   dashi idan bukatar haka ya taso , idan ta kama ya tsaya gaban alqali zai tsaya ya bada sheida domin kuwa mutumi kirki  ake karewa  da rufawa asiri irinsu dady kuwa sai dai a fallasasu duniya tayi Allah wadai dashi ."

***""
Da misalin karfe goma   na daren ranar litini  jaguwa   ya shigo d'akin jikinsa sanye da kayan shan iska farare sol  yayinda hannunsa ke  rike  da farar leda dake d'auke da roban takeway guda biyu  wayam ya ga d'akin babu ita babu alamun ta  jiki a sanyaye  ya ajiye ledar hannunsa ya karasa ya zauna abakin gado a tunaninsa wanka take  shiru har minti biyar ta wuce bata fito ba ya kira sunanta yana duba agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa still shiru ya Kara five  minute  bai ji motsin saukar ruwa ba ya mike tsam  ya Isa  bakin kofar bayi yayi knowking still babu respond Kara knowking yayi no answer a hankali yaji zuciyarsa ta buga da sauri ya  d'aura hannunsa kan handle din kofar  ya murd'a   yaji murfin a bud'e  ya sanya kanshi cikin  ya leka wayam ya gani nan  ma  babu ita yayi mamaki Inda  taje ya fito a rud'e yana duba sauran dakunan gidan nan ma shiru babu ita ..
Wata  uwar ashar ya saki ya wuce su anas ya  fito zuwa haraban gidan da sauri da mugun sauri yanzu kam jikinsa ya fara bashi akwai matsala yana tafiya anas ,jubi,jabir ,har ma da kamil dake dingisa  kafarsa suka biyosa suna Kiran sunansa amman bai juyo ba sai faman dube dube yake yana Kiran me gadinsa da sauri ya k'araso ya rusuna cike da girmamawa "ka budewa  yarinyar nan  kofa ne ?me gadi ya girgiza masa Kai alamun a'a , cikin fushi ya  d'auke shi da mari "ka bud'e baki kamin magana zaka wani girgiza min Kai kamar kadangare "a'a sir ban budewa kowa get ba tun safe ma babu wanda ya fita daga gidan nan bayan Kai  ".
ya Salam ya furta yana rike kugunsa da hannu d'aya ya shiga sintiri a haraban gidan  ya bar me gadi dafe
da quncinsa "gidan ubanwa ta shiga ?wallahi idan banganta ba sai naci ubanka ya fad'a a fusace yana juyowa tare da  nuna me gadi da yatsansa gbdy abokansa suka k'araso garesa alokacin d'aya anas ya dafa shi "wai meke damunka ne "ban sani ba duk banga amfaninku  ba ace Kuna zaune tanweer ta fito baku sheida min ba "
"ta fito taje Ina ?"tun byn sallahr isha'i  muke zaune a falo  bana tunanin ta fito zo muje mu sake dubata tana ciki  may be ko tana bathroom ne ya kamo hannun jaguwa ,ya fixge a fusace "bata nan na duba koina  bata nan bata cikin gidan nan  wallahi idan banganta ba duk sai na kasheku d'aya bayan d'aya cikin kankanin lokaci gabad'ayansu suka shiga tashin hankali anas ya basu umarnin nemota   duk suka raba kansu suna nemanta shi kuwa  jaguwa tuni ya dawo tamkar wani zarare   shi kad'ai yasan irin tashin hankali dayake ciki "Ina tabi tunda me gadi yace bai bud'ewa kowa get ba ?ya d'aga Idanunsa da suka rikid'e suka canza kala zuwa katangar gidan da sauri ya girgiza Kanshi "muddin ta tsallaka katangar nan  lallai zata mutu idan Bata mutu ba zata  nakkasa gashi  bayan gidan  babu wasu gidaje sai kango .
ya fito a gigice anas da jubi suka biyosa suna cewa "Ina zaka ? "dan Allah ka natsu  bazata iya tsallaka katangar nan ba , bai tsaya sauraronsu ba dan kwata kwata hankalinsa bai jikinsa  Kai tsaye bayan  gidan ya nufa yana haska gurin da wayarsa yana Kiran sunanta babu  ita babu alamunta ya  juyo
a harzuke yana masu wani irin kallo mai d'auke da rashin mutunci suna kallo ya dungule hannunsa, gbdynsu suka yi matukar tsorata shi kuwa anas byn tsoro har da kallon mamaki yake masa sai dai ya kasa ce masa komai wani irin kallo jaguwa ya cigaba da yi musu da  jajayen idanunshi .."
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️18

....Anas ya Kalli jaguwa yaga gbdy yanayinsa ya sauya ,
dukkanin wani jijiya dake Kansa sun gama fitowa sunyi rud'u rud'u babu abinda qirjinsa yake sai d'agawa sama da kasa kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa .ya d'aga hannunsa sama zai naushi jabir dake tsaye kusa dashi yayi saurin matsawa baya, ya sauke hannunsa ya naushi iska kana ya zagayesu ya wuce cikin tsananin fushi, suka biyo bayansa suna fad'a masa tautausan kalamai masu sanyi "kayi wa Allah ka samu natsuwa inshallahu za'a ganta " bai kulasu ba ya shiga gidan kmar mayunwanci zaki yana haki ya rike kugunsa da hannu d'aya yayinda d'ayan hannunsa ke rike da goshinsa yana shafawa saboda saran da yake masa .anas da sauran mutanen dake zaune acikin gidan suka cigaba da duba ciki da wajen gidan ko Allah zai sa su ganta har Inda suka duba da farko sun sake dubawa babu ita babu alamunta, gabad'ayansu a matukar tsorace suke dan sun san muddin ba'a ganta ba sun zama abun zargi agurinsa me gadi yafi kowa shiga rud'ani , jikinsa banda rawa babu abinda yake ,da zarar zasu had'a Idanu da jaguwa zai yi saurin kawar da fuskarsa yana salati .

Tsayawa jaguwa yayi cak qirjinsa na wani irin luguden bugawa da matsanacin karfin gaske, ya tsaida idanunshi daidai Inda durom din ruwa yake wanda suke zuba shara acikinsa, haka nan yake Jin fad'uwar gaba me tsanani a yanzu da Idanunsa suka sauka akansa ,ahankali ya soma taku domin k'arasawa gurin , taku uku yayi sai ga anas ya k'araso da sauri "jaguwa !" ya kira sunansa cak ya tsaya yana sauraronsa dan a tunaninsa zai ce masa an ganta "munata wahalar da kanmu muje a duba cctv camera Ina da tabbacin zamu san inda take ."
wani irin juyowa jaguwa yayi da sauri tare da yiwa anas kallon second d'aya sannan da sauri ya soma tafiya cikin sauri kamar zai tashi sama ya nufi d'akin da camera yake , anas ne kad'ai ya biyosa daman Kuma daga shi sai anas ne suke shiga bangaren suna shiga d'akin anas ya kunna cctv camera bayan ya kunna yayi rewarning sai ga hotunan mutanen dake zaune a gidan ya soma bayyana .
a hankali suke kallo har zuwa sanda tanweer ta fito tana sand'a har ta fita zuwa haraban gidan har zata nufi get sai Kuma ta fasa ta Isa jikin window me gadi ta la'be tana dube dube da neman mafaka , cike da tsoro ta waigo bayanta nan taga alamun fitowar aliyu wanda shi sam hankalinsa bai je gurinta ba ganinsa yasa cikin sauri tasa hannunta ta bud'e durom din ruwa ta shiga.

wani irin naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke da karfin gaske sannan ya juya da sauri yana cewa "daman zuciyata da jikina sun bani naje na duba cikin durom din a she tana cikin ". ya Allah kasa wani abu bai sameta ba tafiya yake cikin sauri kamar zai tashi sama anas na biye dashi a falo suka wuce sauran abokansa da yaransa suma suna ganin haka suka biyousu cikin sarsarfa ya k'araso gurin ya bud'e duron din sai gata durkushe ta rufe bakinta da hannunta d'aya dan kar kukanta ya fito , gashi ta dungule jikinta guri d'aya tana haki bai san sanda yasa hannuwansa duka ya kamo kafad'unta ya fito daita waje ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke wahalalle numfashi . fuskata ya manna adaidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfin gaske , ita Kuwa haushi da bakinciki ne suka had'e mata a lokaci daya, ita da take ganin wa'adin zamanta ya kare a gidan dan har ta hango barinta gidan a yau din nan sai gashi ya rusa mata Komai .

a hankali ta d'auke kanta a daidai saitin zuciyarsa ta cusa cikin qirjinsa ta rushe da

Please Login or Register in order to submit comment