Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata amfani daita gurin lallabata "kace Baka bukatar cikin Ko"?
Shiru yayi na tsawon minti goma kana a hankali ya fesar da numfashi  ya kwantar da murya "ba wai bana son cikin bane matsala zai zame mana arayuwa bare ke da kike matsayin  mace  "ni dai gsky Ina son kayana "a hankali ya d'aura tafin hannunsa a goshinsa ya dafe tare da lumshe idanunshi cike da kulawa yace "nima Ina son abuna amman kiyi hakuri acire zamu samu wasu nan gaba.
"Da gaske kake ?"
Yayi shiru yana cigaba da cizan lips dinsa .
A hankali ta Kira sunansa "Adnan !"a hankali ya motsa lips dinsa "na'am tan ."ka tabbatar zamu samu wasu ? da kyar ya fixgo mgn "eh idan kika bi umarnina kika cire ba ya k'arasa maganar yana shafa sumar kanshi "tunda muka rabu ban kara samu sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nake kullum cikin damuwar soyayyarka nake da zazzabin cikin nan bana wani cin abincin kirki gashi Kowa ya gane halin da nake ciki a gida ".
"oh my god tanwer me yasa kikayi haka me yasa kika bari suka sani ?
"saboda ina qaunarka ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka ..
Qirjinsa yayi masa nauyi tausayinta ya lullubesa duk da bai son yawon surutu amman haka yayi shiru yana biye mata "gsky banso kika sanar dasu ba "to yazanyi da rayuwata dole ce . ya dunkule hannunsa sosai yaji ya Shiga damuwa" ina sonka Adnan Allah idan bakayi wani abu ba tunanika zai kasheni  "
ki daina yawon tunanina .
tace "bazai Yiwu ba yanzu ma Na fara idan kaga na rage tunaninka to ina gidanka ne "
"Ki rage yawon tunsni yana kisa ,dan Allah kiyi kokari kije asibiti gobe acire cikin nan sannan su rubuta miki magani. "nifa bazan zubar ba .
Ki yi abinda nace shine  kwanciyar hankalina  sun dade suna magana akan ciki duk yadda yayi daita  taki  amince masa   da zata  cire cikin,  wanda ita a zuciyarta   tuni ma  ta yarda  kuma ta amince ma zuciyarta zata  cire ta hutawa ranta tunda shima bai so amman bazata yarda ta bari yasan zata cire ba sai ta d'aga masa hankali.
"ki kwanta ki huta zan  Kiraki  zuwa  gobe amman ki tabbatar kin amincewa ranki zaki cire "
Tace "to !
"karkiyi tunani komai kinji "
  ta sake cewa " to ! ta fad'a tana  jin zafi aranta  saboda gbdy ta gano rashin sonta da bai mata sai  tana jinshi  ya katse Kira ."

zuciyarta ta  kasa  samu natsuwar  tunanin daya gargade shi ta cigaba da yi, bata da burin da wuce ta mallakesa a matsayin mijin aurenta , tunani kala kala tayi ta saka wancan ta  kwance har ta shigo    tunanin rayuwar da sukayi  agidansa a farkon zuwanta  suna lullube dashi cikin bargo d'aya babu kaya ajikinsu tana makale a gefensa  yayinda hannunta d'aya Ke Saman faffadan qirjinsa shi kuma yana shafa  sansar jikinta tare da sarrafa albarkatun  qirjinta nan take  tsigar jikinta  suka tai  mikewa  ,ta dinga jinsa ajikinta a hankali  jikinta ya kama kyarma  ta kankame jikinta guri daya tana jin kamar jijiyarsa na shiga jikinta ,yayinda taji tafukan hannunsa na yawo sansar  jikinta da wannan tunanin bacci barawo ya dauketa ."

Washegari da misalin karfe biyar da rabi ta farka had'e da yin mika , jiki a sanyaye ta sauko daga kan gadonta     tashiga bathroom tayi alwala  ta fito ta gabatar da Sallah byn ta Idar bata tashi  ba ta kwanta akan sallaya  tana azkar  tana  kuka har ta gama ta kama addua "rabbi Inni Lima Anzalta Ilaiya min khairin  faqeer ta dade kwance tana tunani da fargaban zafin cire ciki ahankali baci ya dauketa sai gurin karfe goma ta farka ta mike tare da nade dadduma Sallah ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta  shirya  ta  nufi d'akin mumy anan  ta samu  mumy har dasu uncle bashir   byn ta gaishesu ta gaishe da mumy sannan  ta roketa  tare  da bata hakurin damuwar da ta sakata jiya, sannan Kuma  ta  tabbatar mata Da ta amince  a cire cikin .
nan take mumy taji ta warke daga ciwonta ta ji jikinta ya dawo normal damuwa ta bar gangar jikinta sai faman saka mata albarka take "inshaallah sai Allah ya yaye Miki abinda kike ji akan dan iskan mutumin nan ,
Allah ya yaye miki gbdy suka amsa da" ameen".
cike da farinciki suka dauketa zuwa babba asibitin kudi batare da bata lokaci ba suka Samu ganin likita suka fad'a masa taimakon da zai musu ,dake yasan minister bai tsaya  bata musu lokaci ba yayi mata gwaje gwaje dan ya gano cikin  Ko na wata Nawa ne dan yasan me za'a mata ganin karamin ne yace "za'a Iya bata kwaya tasha  amman fur dady yace a'a  ayi mata abortion Kawai zaifi samun natsuwa , dan haka batare da bata lokaci ba aka Shiga daita Wani d'aki .
ta sha wahala sosai Kamar zata mutu  har aka  gama kuka take tana Kiran "wayyo Allah zan mutu  nurse ta d'auki sama da minti talatin tana aikinta  bayan an gama nurse   ta fito ta barta ta dan huta .
byn kmr awa d'aya ta fito tana d'aga kafa da kyar tana jin jikinta kmr ba nata ba sai dai ta daina jin nauyin da jikinta yayi mata  amman   kallo  d'aya zaka mata ka tausaya mata dan  taji jiki sosai  , duk tayi wuri wuri Kamar wacce tayi shekara tana ciwo.
  sai dai ciwon bai kai zafin rashin son da jaguwa yake mata ba office din doctor  ta shiga inda ta iske su dady zaman jiranta doctor  ya  rubuta mata magugunan da zasu taimaka mata sannan suka dawo gida .
Kai tsaye d'akinta suka nufa daita suka kwantar daita akan gado suka zagayeta suna mata Sannu  "doctor yace abata ruwan zafi ta sha kafin ta sha magani inji cewar uncle Jamil.
  mumy najin haka  ta mike da sauri  ta fita ta shiga kitchen da Kanta ta dafa mata ruwan zafi ta juyo a cup ta dawo d'akin "Tashi ki sha kinji tanwer dina ,tan ta soma k'okarin mikewa uncle bashir ya taimaka mata  ta zauna  tana fidda zazzafan numfashi ya janyo pillow ya saka mata abayanta ya jinginata yana mata "Sannu!"
Mumy ta mika mata cup din ruwan zafi tana sake mata "Sannu"! tanweer ta gyada mata kai Kawai dan ita kad'ai tasan ciwon da zuciyarta ke mata .
a hankali ta dinga kurban ruwan zafin ,kadan ta sha tana k'okarin mikawa mumy cup, ta miko mata magani ta karba ta sha da kyar ta mika mata cup ta koma ta kwanta lamo had'e da kunna wayarta dan tun safe a kashe take ta tura karkashin pillow   .
Ko minti biyar batayi da kunna  wayar  ba,ta soma babriting alamun ana Kira  ta lalubo tana  duba screen din wayar  number jaguwa ne dan haka ta maida wayar inda ta dauko batare data dauka ba ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafin gaske wanda take jin zafinsu har cikin jikinta .
"ya kiranta yanzu saboda yana bukatar ta zubar da ciki amman ita kira nawa tayi masa bai d'auka ba ?"tana jin Kira na sake shigowa wayar amman taki d'auka "ciwon abun taji sosai bata san meye matsala arayuwarta ba sai da qaddara ta  hadasu ,wani Kiran ne ya shigo aranta tace "duk ka gama kiranka  bazan dauka ba   sai na ganar da kai kuskurenka .
Ahankali duk suka watse suka barta a d'aki ranar yini sukai cikin farinciki bini bini sun shigo dakin dubata har dady yayinda wuni jaguwa yayi yana Kiran number tanwer amman taki d'auka a karshe ma ta kashe wayar  gbdy."
Haka yayita damunta da kira acikin kwanan biyu ya hanata sakat da batun zubar da ciki ita kuma taki yarda ta fad'a masa ta zubar tun su mumy basu fahimci mai Kiran ba har suka zo suka fahimta haushi kamar ya kashesu ganin tana sauraronsa.

Bayan kwana biyu su uncle Jamil suka fara Shirin komawa uncle bashir yace zai wuce da tanwer dan ta kara samun natsuwa ko hankalinta zai bar mutumin da take so "ki shirya kinji tanwer muje Katsina.
uncle Jamil ya gyara zama yace gaskiya gara ka tafi daita dan ni Zan iya Mata Dukan mutuwa idan naga tana nacin wancan banzan mutumin," kai dai kayi hakuri komai qaddara ce fa ni dai idan zata bini zan wuce daita.
dady yace "kuyi hakuri bazata koina ba ta cigaba da zama tare damu shine kwanciyar hankalina Ku cigaba da yi mata addua.
Allah ya tsare mana zuria inji cewar mumy  uncle bashir yace ", inshaallah da sannu zata manta komai hawaye suka cika mata Ido bata Jin zata manta da Adnan, yayi mata tabon da bazata manta dashi ba ta yunkura zata tashi tana kuka sai kuma ta kasa tashi dan haka ta rarrafa jikin dad dinta ta kudundune ajikinsa ta rushe da kuka nan da nan ta Karya masa zuciya to daman Shi akwai sanyi da tsananin jin tausayi mutun bare tanwer dinsa daya fi qauna akan komai , idanuwansa suka cika taf da ruwan hawaye a hankali ya d'aura hannunsa a Saman Kanta muryarsa na rawa yake cewa "da zan iya tanwer da na Karbi number yaron nan na aura miki Shi ,wallahi Ke  abar tausayi CE amman bazan Iya ba, bazan iya wannan Imani ba ."

"Please dad ....."Sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganar
Ahankali ya janyota yace"dubeni mamana da kyar ta dubesa hawaye na zuba "ki daina kuka yana daga min hankali ,baki dace kiyi soyayya da irin wadan nan mutane ba ,bare har ta kai ga aure jikinki bai dace dasu ba rayuwarsa rayuwar wulakacin CE "dady Allah zai daina wannan rayuwar "bazai daina ba ".
ta zuba masa Ido ta kasa cewa komai ta kankame Shi tana kuka washegari haka su uncle Jamil suka tafi sukar barsu cikin Wani yanayi kafin rana ta fadi duk sun isa gidajensu .
Sati biyu Kenan jaguwa na Kiran layin tanwer kwata kwaya bata d'auka ta danne zuciyarta ta cigaba da abubuwan gabanta a karshe ma ta koma bakin aikinta .

*******"
Fitowar nazifi Kenan daga  d'akin  tiyata yaga  wasu  mutane su   biyu  a bakin kofar office  dinsa  suna k'okarin  bud'e kofar office din , gabansa ne  ya fadi .
wani irin bugawa had'e  da tsalle zuciyar nazifi  yayi  har ya haifar  masa da tsayawar  numfashi haka  nan  yaji bai yarda  dasu ba nan take  Kuma maganganun  alhj Tahir suka shiga dawo masa  suna masa kuwa acikin kwaluwarsa  da kunnuwansa  "kwana  biyu kawai na baka matata da dana su dawo  Idan ba haka zan sa adaddatsa min kai  sannan na aika ka lahira "ai Ko bai sa an daddatsa   shi ba yasan   zai iya sawa a nemishi a rasa na har abada take tsoron haka   yake nema yi masa  barazanar da  tarwatsa masa kwakwaluwa da zuciyarsa, kallonsu yake yana tunanin abunyi .
yaje police station da sheidu daya tattara  sai  dai gbdy bai ga wanda ya dace ya mikawa  sheidun ba, dan akan idanunsa yaga anyi rashin adalci  muraran " wani mashayi ne ya buge wata mata  da tsohon ciki  ta mutu har lahira shine aka kamo mutumin aka  kawoshi office din yansanda   aka nufi office din wani ma'akaci dashi , alokacin  da shi kuma yake k'okarin shiga office din , abinda  ya d'aga masa hankali  bai wuce  yadda police din Ke k'okari son su  gyarota  Kawai  ya kama  gabansa "
Kamar nawa zan bayar yallabai a kashe maganar ?"ka bada  million dari  "million dari  yallabai ?"eh muddin kana son akashe case din Kamar bayi ba domin duk wanda yasan da wannan batun sai an bashi kudi "gaskiya ni bani da wadan nan kudadade "a she kuwa zaka gidan yari".
cike da sanyin jiki ya juya ya bar station din zuciyarsa cike da bakinciki ya koma gida ranar kasa bacci yayi bai ya suka kare ba amman jikinsa na bashi zaa gyarota .
Naunayyen ajiyar zuciya nazifi ya sauke   yana k'okarin  juyawa domin tsiratar  da rayuwarsa dan yasan idan sun kashesa sun kashe banza  yaji an buga  masa wata hadadiyar tsawa tare da cewa "ga mutumin da mukazo nema  karka kuskura ka  kara  taku  d'aya ."
" nan take jikinsa ya kama rawa" ya  zubar da abinda  ke   rike a hannunsa ya falla da mugun  gudu, aiko kamar  jira suke  suka biyosa  aguje.
gudu yake  suna  binsa   domin  k'okarin kamasa amman ina tazararsu da nisa gudu yayi sosai  yana haki  yana neman inda zai boye kuma har lokacin suna biye dashi akan titi wannan karon har da garbi yana gocewa mutane sai kallonsu suke yana
K'okarin shiga wani super market domin buya  yayi   tuntube da gangar jikin mutun nan take  ya zube a jikinsa yana haki yana furta "ka taimakeni  dan Allah kasheni  zasuyi zasu kasheni  yana gama fadar  haka numfashinsa ya dauke  su kuma mutanen na ganin haka suka juya suka koma da  gudun kar asirinsu  ya tono dan basu san matsayin mutumin ba .

Nazifi   bai sake sanin inda yake ba sai farkawa yayi ya gansa a wani hadadden daki hannunsa daure da drip a hankali ya karasa bud'e idanunsa yana kallon d'akin ya zabura ya mike ya cire drip yana k'okarin durowa daga saman gadon, sallama yaji Da k'okarin  shigowa  d'akin shiru yayi tare da bin kofar da kallo ganin mutumin daya fad'a jikinsa ne ya sauke ajiyar zuciya .
"Sannu Ko ,ya ka cire drip din tun bai kare ba ?"numfasawa yayi wallahi rashin samun natsuwar zuciya ne dan ban san a hannun da nake ba ya fada yana maida drip din.
ya gyada  masa yana duban wanda suka shigo tare "dan Allah Kawo masa abinci "okay yallabai !"ya fad'a tare da juyawa cikin kankanin lokaci ya dawo d'akin hannunsa rike da food flake da plet da spoon ya ajiye ya zuba masa abincin a plet ya saka masa spoon ya  mika ma  nazifi ya karba.
da hannun daya ya fara ci ya karasa inda fridge yake ya d'auko masa maltina mai sanyi ya bud'e ya ajiye masa ya samu guri ya tsaya yana dubansu .
A hankali nazifi ya d'ago yace "na gode fa ranka ya dade "karka damu me kayiwa wadan can mutane suka biyoka suna neman rayuwarka ?"naunayyen ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye spoon din hannunsa a natse ya shiga Koro masa komai dayasani har zuwa sanda aka fara farautan ransa mutumin ya gyada kai Kawai sannan ya soma magana a natse "ka natsu ka kwantar da hankalinka zaka cigaba da zama anan har na tsawon sati zansan abun yi da fatan bakada iyali ?
"girgiza masa kai yayi alamun bai da"okay !ya fad'a tare da mikewa suka bar d'akin ."

****
Tanweer na zaune a falo tare dasu rukayya suna kallon zeeworld Kiran jaguwa ya shigo ta mike tsam ta koma d'akinta ta d'auka tana d'auka yace "dan iskanci me yasa kika d'aukar wayata kwana da kwanaki ?
"abinda yasa kake d'aukar tawa wayar kwanaki shi ya hanani d'auka   .
"okay haka ma zakice? tace "eh!
Idan na bari kika haifi cikin nan mahaifiyata janyowa abun kunya ,wannan abu zai sata jin kunya ".
ai babu abun kunyar daya wuce satar da kakeyi aboye batasani ba wallahi sai tafin jin kunya idan ankamaka akan wannan cikin dan hakan ni dai bazan zubar ba sai kaje kajira ranar da Zan haifa maka danka Ko yarka ka Samu dan aike Ko magajin fashin ba sai kayi training yayan wasu ..."
"Enough tanwer  ki maida hankalinki jikinki kinsan irin maganar da zaki dinga fad'a min "bangane na maida hankalina ba gsky ce na fada kaima kuma ka sani ."dan nawa ne zai yi fashi ?"to meye aiki har ma sai yafika tunda magajinka ma fiyinka ".
Shiru yay kanshi na Kasa Kamar yana gabanta cikin sanyin murya yace"ni dai ki zubar Kawai idan Kuma kikaki zubarwa ..."
"Me zakayi "?
"Nace Mai zakayi idan naki zubarwa ?babu abinda zaka iya yi Kuma ciki baza'a zubar ba kayi abinda zaka yi ina jira   ta k'arasa maganar tana jan tsaki tana gama fadar haka tai disconnecting din Kiran ...."
Shiru yayi rike da wayar a kunnensa yana jin zafi da ciwon abinda tayi masa, babu abinda yafi masa ciwo Kamar tsakin da tai masa .

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️25

zama   jaguwa  ya  cigaba   da  yi  rike  da  waya   zuciyarsa  na zafi da  farfasa  a qalla  ya kusan minti  goma  yana  tunanin maganganunta,"  bai  san me yasa  zai  damu  kansa  akan cikin  ba , cikin  ma  da bashi da  tabbacin  tana d'auke dashi .
wani   dogon   tsaki  yaja  yana   sake  kiran  layinta , babu 'bata  lokaci   ta   d'auka  qirjinta na bugawa  fat  fat "Ke ni zakiwa wulakacin ? "
shiru  tayi  taki  ce masa komai  sai  dai  zuciyarta  ke wani irin  bugawa da sauri sauri .
"har  kin  isa   ki dinga  farfad'a min  magana son  ranki  ?"
ya sake tmbyrta tare da jan  tsaki "har  ma  da  kashe min waya ? "shiru  tayi  still  cikin  tsananin  tashin  hankali tana tunanin  abinda  zata sake fad'a masa  wanda  zai sake d'aga masa  hankali  sai dai bata kai ga tattara  abinda zata  fada  masa ba  ta  tsikayi  muryarsa na dukan   dodon  kunnenta.
"dan  kinga ina lalla'baki  shine zaki d'auka ko ina  jin  tsoron ki haifi cikin ne ? "to  kar  allah yasa ki cire cikin ai cikin ba ajikina  yake  ba  idan akwai shi kenan  dan  haka  ko ki cire ko Karki  cire ruwanki sannan  matsalarki ce  bata Adnan  .
ba Adnan za'a dinga kwatance dashi ba , sannan ba shi zai rasa mai aurensa ba . aurenki  ne dai bazan  yi ba  kije ki nemi abokin rayuwarki  dan ni  tuni na amince da  zabin mahaifiyata aikin  banza Kawai  ki jira  ki gani  idan  zan sake  nemanki".
ya k'arasa maganar yana jan dogon  tsaki sannan ya katse Kiran  yana fidda wani wahalallen numfashi ,yasa hannunsa  d'aya ya dafe goshinsa yana  jin  zafi  da ciwo a ransa, shiru yay na  second goma  qirjinsa  da  gangar jikinsa na  rawa   gbdy  sai   yaji  kimai ya tsaya  masa  guri  daya  ya shiga tunanin abinda yayi mata  a ganin zuciyarsa   bai  kyauta mata  ba daya farfad'a mata son  ranshi  dan  bata  cancaci  ya fad'a  mata  magangun daya fad'a mata ba ,ita din wata aba ce mai daraja da  kima a  rayuwarsa. amman daya  tuna irin maganganun  data  fad'a masa da irin mugun fatan da tai masa a mintunan da suka gabata  sai  ya  dawo  haiyacinsa ,  komai ya dawo  masa daidai, qirjinsa da gangar jikinsa da suka d'auki rawa  suka  daidaita  yaga  mai ma yayi mata ai bai mata komai ba  . "

Bangaren  tanwer  kuwa maganganunsa sun  daki Kunnuwanta  sosai sannan sun wuce  har  cikin zuciyarta, gbdy ya  kunno  mata  wutar  damuwar da take dannewa  acikin  zuciyarta  ,Kawai sai ji  hawaye yazo idanunta  ya fara zuba  akan  kuncinta, a hankali ta fara  rare kuka mara sauti qirjinta na zafi  "Allah ka gani ba wai  nayi  masa haka dan  na wulakatanshi bane , "na yi dan na raunata zuciyarsa,na yine  ko zai saduda ya zubar da makamansa ya  canza rayuwarsa  darajan  tace  bata zubar ba suyi aure  ,ashe  wata sabuwar maseefa  ta jefa kanta ciki tayi maganar a fili tana sheshekan kuka  "wayyo Allah  ka d'auki raina  na  huta  da wannan rayuwar  da nake " wani  zafi take a kahon zuciyarta sam ba taji kashi  daya na son da take masa ya  rugu  sai ma qaruwa da son shi yayi acikin zuciyarta , tana  sonshi    muddin zai aureta zatai  confuse din  iyayenta  akwai  hanyoyi  da dama da idan ta bullo dasu dolensu  su  hakura su rungumi  nata qaddarar su aura mata shi amman shi kuji abinda yake fad'a  mata har ma ya amince da zabin mahaifiyarsa ita ko  oho  zama  tayi ta  cigaba da rera  kukanta tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin  sanin  madafa ."

tana  cikin  wannan halin  rukayya ta shigo d'akin ganin idanun  tanwer   na  zubar da ruwan   hawaye yasa ta karasa shigowa  d'akin da sauri  tana cewa "lafiya  tanwer menene Kuma ?"
Rukayya ta samu guri gefenta ta zauna ta riko hannuwanta duka  cikin  nata  tana dubanta cike da tausayawa , runtse idanunta tanweer  tayi sai ga wasu hawayen  sharrrrrr."
"wallahi ina cikin damuwa  rukayya ,ina cikin tashin hankali  na rasa  yadda  zanyi da wannan rayuwar da nake  ciki , komai ya canza  min rukayya  ina ma rayuwata ta baya  zama dawo  , "ina ma ban dawo kasar nan ba"..
Rukayya  ta numfasa tace" haka ne  kina cikin  damuwa da jarabawar  rayuwa  tanwer  amman  kiyi  hakuri da sannu komai zai  daidaita ,"sannan   kiyi kokari ki  rage damuwar nan duk  da  tasan komai dake faruwa  daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
" ki kara  imani  da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake  bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne  kawai dai  Allah  ya bamu Ikon cinye jarabawarmu  rukayya   ta  fadi  haka ne dan takaita maganar .
"nima ina son na rage tunanin  Adnan acikin zuciyata  amman na rasa dalili da tunaninsa  kullum sai gaba  yake , wallahi ina  masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi  ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi  ba sai  ranar dana ji an shafa fatihan  aurensa ta k'arasa maganar tana  mai  runtse idanunta."

"Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa "? tanweer ta gyada mata kai alamun "eh! "gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi  addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi  .
Tanweer ta gyara zama  tana kallonta "na  fahimceki yar'uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki "to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace  "na gode rukayya inshallahu zan daina .
." Ki  kwantar  da hankalinki  kinji dan Allah karki  sake daga hankalinki  akansa Ki  fara  nemi zabin Allah kiyi k'okari kiyi  istahara domin neman  zabin  Allah "rukayya ko ya min  wani irin adduar  istaharar da zanyi".?
"zan koya miki , mu nemi zabin Allah  bamu  sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku  idan babu idan  kinyi zaki ga komai ya tafi daidai   amman Karki  yarda  ki bari  wani yayi miki  kiyi  da kanki ,zaki iya yi kullum  idan  zaki kwanta raka biyu zaki yi  sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki  hatta wannan radadin da kike ji akanshi  zaki rage jinsa ."
Jiki a sanyaye   tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta  amsa ta fara rubuta mata adduar "Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as'aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta'alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi."inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure "na gode rukayya inshallahu zanyi  ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta'ba sanin zama da mutun guri d'aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k'okarin  kawar mata da  dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau  ."
Da misalin karfe goma na dare kowa  ya  shige  d'akinsa  tanweer  ta shiga bathroom dinta tayi  alwala ta fito ta

Please Login or Register in order to submit comment