Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanya dogon hijab dinta tare da  shimfida sallaya tayi sallahrta raka biyu sannan ta gabatar da adduar istaharar da rukayya ta rubuta mata sannan ta nemi guri ta kwanta  akan  katifa  zuciyarta cike da tunanin Adnan  kala kala a hankali wani bacci mai ni'imal ya d'auketa ." 

Dare  ya  raba bacci yaki  zama cikin  kwayar   idanun jaguwa  saboda zafi biyu  sun  had'e masa takura masa akan auren  hasera  da amminsa  take so ga Kuma takaicin kin zubar da cikin da tanwer tayi uwa uba tsakin data had'a mashi dashi har yanzu abun nayi masa zafi a zuciya  idan ya tuna kalamanta ya kanji kamar ya mutu wai shi ne zai haifi magajin fashi ?"
Idanunshi suka cika da hawaye amman ya danne .
haka ya wayi gari da rashin  bacci shiyasa da  gari ya waye yake ta  jin kasala ajikinsa.
Shigowar  Anas  yasa ya dan ji dama  ya  dan mike ya zauna rigingine dan yasan dole zai dawo dashi daidai "mutumina ina  fatan dai lafiya ba wata matsalar bace ?"
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke yace "matsaloli ne ba matsala Kawai ba, sai dai fatan samun sauki daga Allah .
"ammi ta matsa lallai sai an saka ranar aurena da haseera  karshen watan  nan  da zara an gama bikin Shafik  kenan ,ga matsalar yarinyar nan wai  ni tanwer zata wa haka ina bata umarni tana wani butsarewa wai har da cewa bazata cire ciki ba zata haifa ko na kar'ba ko ta Kawo wa ammi," ni ba kaiwa ammi  ne ma yafi damuna ba wai ta haifar min wanda zai gajeni a fashi ba sai nayi training yayan wasu ba ,wallahi wannan abu yayi min ciwo ko ance mata wannan sana'ar muna yinta ne dn  dadin rai ?"
"Kana ji ko muyi magana ta fahimtar juna  Allah  kuma  yasa ka saurarrni ,Jaguwa ya kara matsoshi sosai"me zai hana Anas ka fad'a komai zan saurara dan mafuta yake  nema tun kafin komai ya kwabe masa  ."

"Abinda kakewa yarinyar nan Sam bai da kyau , duk fa kai ka jawo abinda ta fad'a maka ba wai wulakanci tayi maka ba ,sai abu na gaba adnan Kana yiwa yarinyar nan wani so na dabam haka  itama  tana sonka sosai fiyye da komai irin son da zata iya rabuwa da Kowa nata dan ta rayu da kai  hasalima soyayyar da take  maka ne yasa ta kasa zubar da cikinka ba wai ina takura maka  akan  kana son yarinyar  nan bane ,sai dai   ina son ka sani  har abada bazaka daina sonta ba , itama  haka . zanyi farinciki idan ka sauke komai ka rungumeta ka aureta , nasan muddin  iyayenka sukaje  neman aurenta  zata yarda ta zubar da cikin duk da shima zubar da cikin babban laifi ne .
Jaguwa ya numfasa tausayin kansa dana tanwer ya rufesa tabbas shima ya fara jin wani abu akanta a yanzu ma babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai hotunanta , yayi saurin ya bud'e idanunshi da suka kada "kayi hakuri wannan shawarar taka ba abar d'auka bace yanzu agurina kasan komai nawa Koda zanyi aure bazan Iya aurar mace sama da daya ba ," kaga Kenan bazan iya bin zabin Kowa ba sai na mahaifiyata dan haka maganar auren tanwer ma bata taso ba  ka bani wata shawarar yadda zanyi ta cire cikin nan dan ko bata samu hanyar kaiwa mahaifiyata ba ta cuceni muddin ta bari dana Ko y'ata sukazo duniya  ta wannan hanyar ."
"Komai fa muqaddari ne  daga Allah amman ka sake lallabata ka gani may be zata yarda  "babu irin abinda ban mata ba anas  babu irin  rarrashin da ban mata ba  ingaya maka yarinyar nan taki d'an Karan taurin kai gareta ,anas yayi murmshi yace "zanice ta tarar da muje kai daita duk abu daya kenan " sun dade suna magana akan cikin tanweer a karshe ya tsaida shawarar zai nemota da kanshi ya kaita acire mata cikin ya huta da damuwar dake damun zuciyarsa."

******
Tunda yaran alhj Tahir suka Kawo masa labarin rashin nasarar da suka samu gurin kashe nazifi ya kasa samun sukuni, ranar a zaune ya kwana saboda tsananin tashin hankali addua yake Allah yasa ba hannun Jamin tsaro nazifi  ya shiga ba .
haka ya raya daren batare daya runtsa ba haka washegari tsumayi yake yaji ta inda za'a aiko masa da sammaci amman shiru kake ji ,haka yayi kwana biyu adaddafe duk ya zube Kamar wanda yayi shekara yana ciwo  baya Iya  zuwa  koina ganin har lokaci babu wani sammaci daga hukumar yansanda ya dan kwantar da hankalinsa .
Yau ta kama jumma'a   alhj Tahir yaje massalacin sallar jumma'a kai tsaye daga massalacin gidansa ya nufo shi direbansa Sai dai kafin ya karaso get din gidansa wata mota marcende tasha gaban motarsa take direbansa ya tsaya cak cikin tsananin tashin hankali .
wasu mutane masu siffar karfi da bai san ko suwaye ba fuskokinsu rufe da bakin face mark sukai attacking dinsu. duniya juyi juyi yau shi akayi attack shi da yake  turawa mutane fataken dare yau Shi aka turowa ,hankalinsa bai wani tashi ba a tunaninsa kudi sukazo nema sai dai yadda suka karaso tamkar zakuna suka hau bud'e kofar inda yake zaune a gidan baya suna cewa "fito muje shine yasa cikinsa ya turu ruwa "ya fito suje ina ?"yayiwa kanshi tmbyr a kasan ransa ,amman a zahiri cewa yayi "nasan kudi ne ya Kawo gani ga gidana can tafiyar mintuna kadan zai kai mu muje zan baku duk abinda kuke bukata ni dai ku barni da raina."

"ba kudi ya kawomu gurinka ba cewa akayi muzo da kai Idan kaki biyo mu mu d'auki ranka" nan take jikin alhj Tahir ya d'auki kyarma kmr mazari yana zare Ido gaba da gabanta kenan, bai tsaya bata musu lokaci ba ya fito yana gyara babban rigarsa suka tasa keyarsa gaba har gurin matarsu suka saka shi a gidan baya mutun biyu suka sakashi a tsakiyar suka bar gurin aguje.. suna barin gurin direbansa ya fito tare da daura hannuwansa duka saman kanshi yana kururuwa neman d'auki ya bi bayansu sai dai akin banza yayi dan babu wanda ya fito ,daman kuma haka unguwar take duk abinda zai samu mutun da wuya ataimaka masa kuwarka banza barinsa ma haka ."

*****

9:am daidai motar jaguwa ta karaso bakin get din  asibitin tanwer , yayi parking nesa kad'an da asibiti  yana zaune sai ga  direbanta yazo da wata  hadadiyar mota Kirar  land cruiser jeep sai sheki take .
tun daga nesa ya tsura mata Ido fuskarta a had'e tamkar bata ta'ba  murmushi ba sai dai yanayinta kamar zatayi kuka tayi masa kyau aini yaushe rabon ya sanyata akwayar idanunshi .
 driver ya sa kai zuwa cikin hospital din shima ya biyo bayansu , direba bai tsaya akoina ba sai a daidai hanyar da zata Kaita office dinta  yayi parking ya fito da sauri  ya bud'e mata gidan baya .
A hankali ta yunkura ta fito tana jin wani faduwar gaba ......"
ta tsaya shiru tana bin haraban gurin da kallo kafin daga bisani ta soma d'aga kafafunta zuwa ciki yayinda driver ya Shiga motar ya tayar ya soma k'okarin barin gurin .

Tana tafiya tana sake jin faduwar gaba tare da jin motsin tafiya a bayanta ta tsaya cak ta juyo bayanta a natse wayam babu Kowa sai ita kad'ai sai mutanen Dake kai Kawo ta gabanta ta cigaba da tafiya adaidai bakin corridor da zai Kaita office dinta suka hadu da doctor muyis cike da fara'a ta tsaya suka gaisa yana k'okarin janta da magana ta wuce ganin fara'a a fuskarta yau yasa shi jin sanyi aranshi dan haka yabiyota abaya  har ta karaso bakin kofar office dinta bata daina jin faduwar gaba ta tsaya tana k'okarin   bud'e  jakarta ta ciro key  Dr muyis ya amshi jakar hannunta dan ta Samu damar  bud'e kofar a tare suka  Shiga ya maida kofar ya rufe batare da yasa key ba .
Ya ajiye Jakarta akan makeken table din dake office din ta  zagaya ta zauna shima ya samu guri ya zauna suna fuskatar juna office din ya dauki shiru na minti goma sannan ya fara magana zuciyarsa na rawa dan fargaba. "jiya  dr Safina bata fad'a miki sakona bane ?" sai da tayi jim sannan tace "sakon me Kenan ?tayi mgnr batare da ta d'ago ba. ya gyara zama yana sakar mata murmushin sai lokacin ta d'ago ta dubeshi suka had'a Ido
"ya'akayi Dr muyis ?"yace "babu komai Kawai so nake muyi hira "ta sauke numfashi tana cewa "Ai yanzu ba lokacin hira bane lokaci ne na aiki zai fi kyau ka kama gabanka kaje kayi aikin gabanka" ta maida Kanta ta sunkuyar tare da numfasawa.

"nasan kin fahimci wani abu akaina , ta sake d'ago ta dubansa tace "ban fahimci komai ba idan akwai wani abu ka sanar min ina da tarin ayyuka a gabana ya sauke numfashi yace "nasan kin fahimci yadda nake sonki Ko?"ta numfasa sai dai bata ce uffan ba "wallahi ina sonki tanweer kuma da aure ta runtse idanunta tausayinsa ya kamata tayi sauri ta bud'e idanunta a sanyaye take cewa" kayi hakuri kayi addua Allah ya sauya maka wata dan ni zuciyata tayi nisa a soyayyar waninka inshaallah nan kusa za'a shafa fatiha
"inshaallahu Ke rabona ce bata Wani ba ba kuma zan hakura ba har sai an shafa fatiha wanda nake fatan da ni ne "to wannan kuma yana ga Allah domin shi Ke shirya yadda yaso amman dai ina maka fatan samun wacce ta fini domin Ko da zan zamo mallakinka gangar jikina Kawai zaka rayu dashi amman zuciyata baza ka taba galaba akanta ba ".
Ya gyara zama yana kallonta "shikenan na fahimceki amman fa bana jin zan hakura dake ki bani dama mu dinga zantawa koda kuwa a office ne kafin nasamu matsayin zuwa gida .
ta kallesa sai ma ya bata dariya  "kaje ka nemi mata tun kafin a fara kiranka da gwaro dan nasan shekarunka sun kai hamsi ta k'arasa maganar tana murmushi "ki bari na rasa wacce nake so tukun na sai na rufe ido na kwashi Ko wacece inyi maneji "no karkayi haka ai ita rayuwa .."
turo kofar office din akayi tare da  shigowa  ya katse mata maganarta aka   maida kofar  office din aka  rufe garam cikin zafin nama da zafin zuciya .
a natse ta d'ago zuciyarta cike da mamaki rashin neman izini da ba'a yi ba kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya soke duka hannuwansa ciki aljihun wandonsa ta gaba ,ya balain kafeta da rikitattun idanunshi   yana jifanta da mugun kallo ,
yayinda take  zuciyarta ya soma  bugun tara tara ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa ta sunkuyar da Kanta Kasa sannan ta cigaba da duba file din data fara aiki akansa sai dai gbdy komai nata ya  tsaya  dan batayi tsammanin ganinsa ba ji tayi kmr an zari wani abu ajikinta " me ya Kawo Shi gurinta ?" tayiwa Kanta tmbyr da babu mai bata amsa sai Shi .
Dr muyis ya juyo a hankali ganin Kowa ye ya shigo babu neman izini ,shima sai da gabansa yayi mugun bugu da karfi ganin ingarma nmj tsaye sai dai cikin kamala yake sanye cikin bakaken kaya har facing cap dinsa da takalmin kafafunsa da agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa , ya juyo a hankali ya dubi tanwer fuskarsa da alamar tmbya "dr muyis nayi bako  ka dan  bamu guri ".
"okay my tanwer zan dawo
zuwa anjima mukarasa mgnrmu ya mike tsaye tare da juyawa ya mikawa jaguwa hannu amman kememe  yaki  bashi hannu illa kallon hadarin kaji da yayi masa yana yatsina face, dr muyis yayi mamaki active dinsa zuciyarsa  cike da damuwa ya d'aga kafadunsa ya bud'e kofa ya fita  .
kusan minti biyar shi  bai fita ba sannan shi  bai karaso inda take ba, dan haka  ta mike tsaye da zumar bar masa office din  idan ya gaji yasan inda dare yayi masa ta gefensa tabi zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa daya  ya dawo daita ya tsayar daita a gabansa batare daya ce mata komai ba ya tsura mata rikitattun Idanunshi masu bugar mata da zuciya ....."
wani yanayi mai tsarkakiya da wuyar fassarawa ya ziyarci gangar jikin duka masoyan guda biyu a bangaren tanwer tsantsar soyayyar da qaunar jaguwa ne yake bin dukkan ilahirin sansar jikinta ,ji take Kamar ta mutu ta huta akan wahalar da take sha akansa . "
Shim abinda yake ji Kenan a sansar jikinsa  ji yake Kamar ya zarta dukkan maza sa'a  a duniya data makance akanshi, sun shiga wata duniya wanda ma'abota so da shauki ne  suka san zakinta a hankali yake Jin qaunarta na sake huda zuciyarsa yayi taku biyu ya had'eta da qirjinsa yana fidda wani wahalallen numfashi.."
saurin dauke numfashi tayi tana so shi kamr ranta ita Kanta tana mamakin zazzafan soyayyar da take ma jaguwa mai tafiyar da dukkan wani motsi  da bugun zuciyarta da numfashinta .
yadda soyayya Ke walagigi da zuciyar tanwer haka ne yake faruwa da zuciyar jaguwa a sukwane ya motsa lips dinsa ",waye wancan mutumin daya tasaki gaba kamar zan ciyeki "? ya k'arasa maganar cikin zafin rai ."
Shiru ya biyo bayan tambayarsa dan bata jin zata iya bashi amsa idan tace lallai sai ta bud'e bakinta to kuka ne zai biyo baya ta juya a hankali zatabi ta gefensa hannunsa ya kai ya rike tsintsyar hannuta gam ya karasa gaban table dinta ya d'auki handbag dinta ya makala mata a kafad'a  ya soma tafiya daita har ya fito daga cikin office din  magnata  take  son yi amma  bakinta ya kasa furta komai   illa jikinta dake wani irin rawa sakamakon had'uwar da jikinsu yayi , bai tsaya a koina daita ba Sai a inda yayi parking din motarsa ya bud'e mata gidan gaba  ya Sanyata ya rufe ya zagaya ya Shiga ya tada motar  ya bar haraban hospital din."

Sosai yake gudu akan titi  batare daya Kalli inda take ba ,itama bata Kalli inda yake ba idanunta na kallon gefen titi ,dan cija lips dinsa yayi yaso tayi masa mgn  amman yaga ta sharesa saboda taurin kai irin nata dan haka bai yi mgn ba  shima ya yatsina fuskar ya cigaba da tukinsa sunyi tafiya mai nisa still bata juyo tace masa ina  zai Kaita ba har ya karaso bakin get din gidansa yayi hon aka bud'e masa get ya shiga da motarsa ya k'arasa inda aka tanada domin ajiye motoci yayi parking sannan ya kashe motar ya bud'e bangaren da yake a hankali ya fito ya zagayo side dinta ya bud'e mata kofa ya tsaya yana kallonta muryarsa a kasalance  yace "fito !
"Na fito nayi me ?" sai lokacin tayi mgnr cikin karfin hali da dakiyar zuciya .
"Bansani ba kuma Karki kara bani irin wannan amsar Oya  fito" .ya fad'a yana zabga mata  harara kin fitowa  tayi ta makale  handbag dinta ta  cigaba da zama tana girgiza masa jiki tana yatsina fuskar .
on-expecting taji ya sunkuceta ya fito daita ya shiga cikin gida daita  suna shiga babban falon gida ya sauketa  yana cewa "daman abinda kike so Kenan jikina ya hadu da jikinki gashi nan  nayi miki abinda kike so ."
Ta kallesa idanunta cike da bacin rai  ta rasa me yasa yake mata haka "ki samu guri ki zauna doctor na zuwa ta duba min lafiyarki idan aka dubaki  baki dauke da ciki sai kinga yadda zanyi dake a gidan nan  duk sai na fanshe d'aga min hankalin da wahalar dani da kikayi".
still dai bata ce uffan ba sai tagumin  da tayi cike da zullumi abinda zai mata .

Byn minti shabiyar sai ga doctor tayi sallama ya bata umarmin shigowa ta shigo suka gaisa da jaguwa Kawai dan ita tanwer Ko kallon inda take batayi ba .
ya mike tsam  ya k'arasa inda tan take zaune cikin tashin hankali  ya riko hannunta cikin nashi batare daya ce Mata komai ba ya fara tafiya doctor na biye dasu Abaya  yana mata bayani abinda yake bukata tayi masa  har cikin bedroom dinsa  suka shiga ya zaunar da tan sannan yaja ya tsaya tare da rike kugunsa da hannun daya yayinda dayan hannunsa Ke qirjinsa yana shafawa a hankali .
Doctor  ta ajiye kayan aikinta  ta kalli tanwer sannan ta mika mata wata karamar roba "ki shiga bathroom kiyi fisari aciki ki Kawo". kin amsa tayi sai da jaguwa ya maka mata harara sannan ta amsa ta nufi bayi bata jima ba ta fito ta mikawa doctor roba ta samu guri ta zauna tana mamakin karfin halinsa da rashin tsoronsa .

Doctor ta gama duba fitsarinta  ta d'ago ahankali tace "bata dauke da komai idanunshi ya zuba mata yana mata kallon tsab cike da bacin rai take hantar cikinta ya soma kadawa dan irin kallon da yake mata babu sausauci  irin wanda za'a  iya wa mutun dukan mutuwa ne muryarsa can kasa "yace ni zaki yaudara ? " sanya kwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye tayi  cikin  nasa muryarta can kasa tace "bagane yaudara ba dan d'aukar ciki na d'auki cikinka na tsawon wata biyu kuma naji ciwon rabani da d'ana Ko y'ata da akayi domin bansani ba Ko iya abinda zai zama rabona  Kenan, abinda ma baka sani ba  cikin yanbiyu ne ta k'arasa maganar tana zubar da ruwan hawaye "wallahi cikinka ya zauna ajikina bani da zabin da wuce ciresa shiyasa nayi , wannan likita ce ka d'auketa  dani   muje hospital dinsu  tayi min scan tabbas zata gane ciki ya zauna a mahaifa haka zalika zata gane a min abortion , me ye amfanin bani da ciki nace ina dashi ?"
Likita najinta ta cigaba da had'a kayan aikinta "me yasa baki fad'a min gsky ba cewar  kin zubar kika  dinga wahalar dani har da mun mummunar addua ?"bata ce komai ba illa kukan da take sosai , doctor tace "yallabai ni zan wuce ".okay zaki Iya tafiya ki tura min account number dinki "to na gode Sosai tasa kai ta wuce ..
Ya tsura mata Ido yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta qirjinta shi yafi komai daga masa hankali dan riga da siket ne sanyi ajikinta rigar ta dan matseta daga sama Sai mayafi baki data yafa akafadanta fargaban da take ciki yasa bata juyo ta rufe gaban rigar ba Cike da natsuwa yake tahowa inda take zaune ,saurin juyar da Kanta gefe tayi Kamar bata San ya karaso  gurin ba ,ya matso ta sosai Kamar zai shige jikinta  "yanzu kina kuka ne dan na d'aukoki  Ko kuwa dan kin cire cikin da zai zame mana damuwa arayuwarmu ne"? "duka !"ta fuskanceshi sosai sannan ta cigaba "Kukan duka nake yi  dan ina son abuna ".
ya kwabe baki yana mata wani kallon kasan Ido aranshi yace ina ai lalacewata bata kai na barwa zuriata dan gaba da fatiha ba amman zahiri cewa yayi "tunda kina bukatar haifar min da Ko 'ya ki shirya Ko a yanzu sai na sake miki wani cikin "a mutukar firgice ta tsareshi da Idanunta  "yes idan kina bukata sai na baki wani  baby ".ya k'arasa maganar yana shafa saman kafarta da tafin kafarsa wani irin abu taji ya tsarga jijiyoyin kafafunta da sauri ta janye kafafunta tana girgiza masa kai alamun" a'a .!
Ya d'aga kafadansa
"shikenan tunda baki so ya fad'a yana zare mayafinta had'e da ajiyewa a gefe ya durkusa a gabanta yana   shafa wuyanta  zuwa saman qirjinta wani irin zirrrrrr ........"taji a gbdy ilahirin jikinta hankalinsa  ya tashi mutuka  sha'awarsa ta motsa  tundun dukiyar fulaninta  sai sheki suke  suna sake kuno masa wutar shaawarta tun daga wuyanta ya fara shafata yana cewa "sam wannan shigar batayi ba tanweer Kalli tundun qirjinki  a fili a haka ne kika yarda wancan Katon banzan  ya sanyaki  gaba duk ya gama kare musu kallo wama yasani Koya taba duk da shaukin da take jin yana zirayar sansar jikinta hakan bai hanata bare masa  baki ta fara kuka ba "Allah ya sani qirjina a rufe yake alokacin bai ga komai ba bare ma ya kai hannunsa jikina ni din ma  ba irin wadan nan matan bane , ina kare kima da darajata .
" na sauraresa Kawai dan na kwantar masa da hankali saboda na Lura yana mutuwar so .... "shiiiiiiii .."ya d'aura lips dinsa akan nata  Suna fuskantar juna tare da shakar numfashin  juna gbdy suna jin bugun zuciyoyin junasu haka zalika suna jin yadda numfashinsu Ke gauraye da juna wanda yake sake hadda musu bugun zuciya  "
"Ban tmby ko yake miki ba amman kisani ina da masefaffen  Kishi bana  son Kowa yayi miki  mgn bare kallon surar jikinki , daga yanzu ki dinga suturta jikinki kina shiri Kamar matar aure idan kikayi haka babu wanda zai kalleki bare ma yayi  miki mgn .
"duk wanda ya kalleki haka hakika ya cuci wanda zai aureki  a bayyane yake mgn batare daya sani ba "kayi hakuri Allah ba da wata manufa na kulasa ba sai lokacin ya dawo haiyacinsa ya fahimci a fili yayi mgnr  "shiiiiii" ya sake furtawa yana  rufe mata baki da lips dinsa a hankali yake lasar bakinta zuwa qirjinta  a karshe ya zarce da kising dinta Wani irin kissing dinta yake kmr mayunwacin zaki tun tana jurewa har ta kasa ta fara mayar masa da martani ganin  dukurso  bazata kai su ba ya janyota suka fad'a saman gado dan itama lokacin babu abinda zata Iya tabukawa Kanta dan jikinta ba karamin mutuwa yayi ba ya kwantar daita ya haye Samanta ya cigaba da sarrafa bakinta a hankali taji yana rabata da kayan jikinta , nan take ta dawo hankalinta dan bazata taba manta wahalar data sha gurin cire ciki ba  ,ta zuba masa Ido  tana jin Wani zallar bacin rai na ratsa lungu da sako na gangar jikin a hankali Kuma hawaye ke bin kuncinta ta ina zata fara irin wannan rayuwar da yake bukata daita ,yayi mata ciki ya nemi ya wulakantata yanzu kuma yana k'okarin morar jikinta ta ina zata fara irin wannan rayuwar kaskanci ?"
"wallahi bazata Iya abinda yake da muradi ba "yanzu na sake tabbatarwa kaina da baka qaunata Adnan kai tsaye kake nuna min manufarka akaina jikina kake so idan ka gama mora na dawo abar wulakantawa agurinka  wallahi bazan yarda da irin wannan rayuwar rashin mutunci da rashin  sanin ciwon kan ba ta furta a fili tana dukan qirjinsa da dukkan hannunwanta.
a natse ya bud'e idanunshi da suka rikide ya zuba mata "wato  tunaninta Kenan yana son ya sake kusantarta ne ,wallahi har cikin zuciyarsa bashi da muradin sake keta mata haddi ,ga mata nan burjiki a gari da wanda suka fita da wadan da tafi idan yana so har gida za'a Kawo masa.
shi ne dai yanzu bai raayinsu Ko Zahra da yana raayi Zai dawo daita rayuwarsa sbd kullum garin Allah ya waye sai ta kirashi baya d'auka yanzu ma abinda yasa ya taba jikinta Kawai rage zafi zai yi daita dan wani irin sha'awa ce ta taso masa ya manta when last yaji haka.
a halin yanzu baya Jin shaawar kowace mace sai ita A hankali ta soma k'okarin mikewa ta hanyar kai hannunta qirjinsa har tayi nasarar zamewa ta sauko daga sama gadon tana mayar da kayanta har ta gama sakawa bai ce uhmmm bare uhmm yana zaune yana kallonta tasa hannu ta d'auki Jakarta ta juyo da sauri ya duro daga saman gadon ya fizgota nan take ta zube  saman faffadan qirjinsa  sakamakon fizgota da yayi ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yana busa mata numfashinsa .
nan take  qirjinta ya shiga dukan uku uku tayi yunkurin barin qirjinsa taji ya sake rungumeta very tayt idanunshi a lumshe kamar yadda nata suke dukkaninsu suna jiyo bugun zuciyar juna dake bugawa fiyye

Please Login or Register in order to submit comment