Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba .”


anas ya biyosa da sauri yana cewa “ina ganin bazan samu fitar gobe ba ,ku tafi kawai allah ya tsare ku inshaAllah idan zaa fita wani lokacin idan muna da Rai zani ,amma ni zan zauna a gida zan muku addua “what ?jaguwa ya fada a kasan ransa zuciyarsa na zafi ya juyo ya kallesa kawai sannan ya juya a fusace ya shiga mota ya bar gidan qirjinsa na wani irin bugawa dan sai yaji abinda tanwer tayi masa shafan mai ne akan nashi ,aiko sharesa da sukayi nashi yafi masa zafi akan tanwer ,Ana’s ya juya ya koma ciki yana jin damuwa aransa “lafiya kuwa ?hankalina yayi matukar tashi meke faruwa ne ?”babu komai my princess ya kamota jikinsa yayi mata kyakkyawan runguma yana shafata domin son mantar daita abinda taso fahimta .”
Wannan yanayin ya wuce ace babu komai nafa san waye yayana nasan halinsa ,na taso na ganku tare ne nasan ba haka kuke tafiyar da rayuarku ba ,dan allah kuyi hakuri da juna koma akan meye idan wani abu ya shiga tsakaninku zan shiga damuwa sosai ”nace miki babu komai ke yanzu kina tunanin akwai abinda zai shiga tsakaninmu ?ta girgiza masa kai “to ki yarda babu komai ya fad’a yana shafa bayanta .
Wani irin gudu jaguwa yake yi akan titi cikin tsananin tashin hankali “anas !!!! Kawai yake furtawa a fili yana shafa sumar kanshi “Ko daya anas dina ban wulakantaka ba ,ko ina yi bazan iya maka ba ,kai ruhina ne ,zuciyata ce bazan juri rashinka ba ,bazan juri fushin nan ba, duk motar daga irin gudun da yake falfalawa sai tayi gefe ta bashi hanya da taimakon allah ya karaso gida ya zauna akan kujerar kushin yana jin wani azababben ciwon kai .”


Wani hadadden gidan sama ne da hawansa ya kai goma ,Maganar adadin daku nan dake cikin wannnan gidan ba azai lissafu ba ,daya daga cikin dakin mutane guda shida ne acikinsu sai dai mutun uku ne kawai a zaune sanye da bakaken kaya ,
yayinda mutun daya dake cikin wadan da suke tsaye ke yaga farar takarda yana cewa “wannnan takardar babu abinda zata mana bayanan wannna file din ne kawai zai mana amfani sun dauki lokaci suna tautaunawa akan gurbatacciyar kasuwancinsu kafin daga karshe nabel ya dubi alhj tajudenni “ya batun yaran nan kuwa sun nemeka sun baka hakuri ?ya girgiza kai alamun” a’a ! nabel ya gyada kai “amman sai da nayi masu gargadi kamar zasu yi aiki dashi ashe aikin banza nayi “ina fad’a maka taurin kansu ya wuce tunaninka “. Ina bukatar bayanan kowanne acikin wadan nan mutane guda biyar din inji wanda ya fara magana da farko wato Ahmed abba “.
“Idan muka bibiyesu hakan zai sa su qara suna a idanun duniya ,ba kuma zai yiwu ace kmarmu mun buga qasar mutuwa dasu ba inji cewar dahir “ai kuwa gara a tashesu aiki a share babinsu na daina jin duriyarsu acikin duniyar nan shine kawai kwanciyar hankalina kullum da tunanin wadan nan mutane nake kwana nake tashi most especially mutun biyu din nan jaguwa da amininsa lallai sai na daina jin bugun numfashinsu hankalina zai kwanta ruhina ya samu salama ya qarashe mgnr cikin tsananin tashin hankali ai kuwa hankalin kowa dake gurin ya tashi
“ai kuwa bazamu barsu ba lallai sai mun ga gazawarsu takowa ni hali nabel ya fada tare da daukar glss cup dake cike da tacaccen ruwan giya ya kai bakinsa .”

tunda suka fara maganarsu akan jaguwa tanko gote na zaune bai ce uffan ba sai yanzu “nifa ina ganin kamr aikin sirri suke wa gwanati , dan ban ta’ba ganin yan taadan da suka gagari kasa da kasa ba sai su ,ko a labari ban ta’ba jin masu irin sanarsu sun dauki shekaru me tsawo suna wannan aikin ba batare da anfarmakesu ba an musu kissan gilla ba , bugu da qari kafafunsu nada tsawo akwai asiri ajikinsu ,ai naso na jnyosu cikin mu amman sam yaran nan suka ki yarda, kunsan kuwa idan babu wata a kasa basuki amsar tayin alqalarmu ba ,gashi fashin su basayiwa masu adalci sai marasa adalci da azzalumai suke yiwa duk kuma inda masu laifi suke sai nemo sun masu hukunci sannna sun hadasu da jami’an tsaro,ku duba mutane guda biyar din daake zargi da kisan honorable ai sune silar shigarsu hannu nifa a nawa mu manta dasu muyi lamuran gabanmu kar muna zaman zamanmamu mu janyowa kanmu balai ba fadawa hannun hukuma bane matsalar zubewar mutunci idon duniya shine abinda zamu duba dan ta hukuma me sauki ne “.
Ya karashe maganr yana dubansu daya byn daya .”
“Abinda ya kamata muyi bincike akansu ba wai janye hukuncinmu ba ni nan zan yi bincike akansu ku bani kwana daya kacal inji nabel ya fada yana daga musu yatsansa daya “wallahi muddin nayi bincike banganosu cikin masu binciken sirri ba lallai ni nan zanyi ajalinsu daya bayan daya…””


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️42

......a hankali kan jaguwa ya dinga sarawa da karfi tamkar ana buga masa guduma, zamewa yayi kasa sosai gumi na tsatsafo masa har akan karan hancinsa ,labbansa ya motsa magana ta fito cikin wani irin yanayi na tashin hankali "oh my goodness wai meke shirin faruwa dani né ?tanwer tana qoqarin juya min baya haka shima anas "why anas kai fa nawa ne na har abada ban cancaci kayi min haka ba ?."
Gabadaya idanunshi sun kad'a sunyi jazur tamkar garwashin wuta , zuciyarsa na masa wani irin zafi ya dinga jin kamar ya fixgota daga qirjinsa ya fito daita waje ya huta , cikin tsananin damuwa ya zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya shiga app ya tsurawa cikin wayar kwayar idanunshi anas ya gani zaune kusa da hally hankalinsa kwance babu wani alamun damuwa atattare dashi .
"Shikenan bai damu dani ba ?"bai damu da kowani hali zan shiga ba rayuwarsa kawai yake ? yayiwa kansa tmbyr da bashi da me bashi amsarta,mikewa yayi cike da sanyin jiki ya bar d'akin ya wuce direct hanyar d'akin da suke ajiye kayan shaye shayensu bai qarasa ba eku dake zaune ya hangosa dan haka da sauri ya taso ya biyosa yana tambayarsa "boss akwai abinda kake bukata ne ?."

Ya tsaya cak batare daya juyo ba yace "wiwi nake so , okay boss an gama ,"kayi min babban nad'i kamar guda goma yayi maganar tamkar wanda ya sha ruwan barasa ,eku yayi shiru yana d'an dubansa sai dai bai ga alamun a buge yake ba ,koda yake shi daman baya shan ruwan barasa iyakarsa wine non alcohol ko wiwi da taba baya wuce wadan nan abubuwan "shikenan boss ka koma ciki zan kawo maka yanzu , kamata ma yayi ka kirani ba wai dan wannan bukatar ka fito da kanka ba ."
Jaguwa bai ce uffan ba ya juyo ya fuskancesa "shiga kayi abinda nake bukata ka bani kawai” babu musu eku ya shiga cikin d'akin ,cikin kankanin lokaci ya nad'o masa tabar wiwi babban nadi kamar yadda ya bukata "muje na kai maka boss wannan karon bai ce masa qala ba sai ma ya kai hannunsa ya d'auki guda d,aya ya kai bakinsa eku yayi saurin miko masa abun kunnawa ."

ya kunna cikin kwarewa ya soma zuka yana daga kafafunsa a hankali yana fitar da hayaki bai tsaya akoina ba sai falonsa dake had'e da bedroom dinsa ya zauna akan daya daga cikin kujerun dake falon tare da d'an zamowa yana fitar da hayaki ta hanci ta baki ,eku ya ajiye masa faratin wiwi akan table ya juya tare da rufo masa kofar."
" ko cikakken minti biyar ba'ayi ba ya gama da guda hud'u nan da nan kwayar idanunshi suka sake rikidewa ya soma skiping na maye nan da nan idanunshi suka fara hango masa tanwer dinsa acikin idanunshi cikin shigar kananan kaya wondo iya cinyarta da wata yar karamar riga da tsayinta bata wuce kasan dukiyar fulataninta ba, yayinda cibiyarta ke bayyane a ganinsa , tana sakar masa tsadadden murmushi ,wata irin zabura yayi ya mike tsaye yana sake ware idanunshi da suke lumshe irin na masu zukar wiwi ".


"Tanwer kin had'u sosai gskiya qirarki ta had'u sosai ,ya za'ayi ki bar adnan ya samu kwanciyar hankali da sukuni? ai sam qirarki bazata bar zuciyata ta huta da tunaninki ba bare tarin qaunar da nake miki ta raqu ,komai naki yayi min sosai ,
haka nake son mace kamar yadda kike , zan iya 'bata tsawon rayuwata kawai ina kallonki, tunanina babu wata halitta me kyawun halitta kamar naki ,hatta taurarin da suke sararin samaniya nasan suna jinjinawa halittar qirararki ,ina sonki tanwer lallai sai yanzu na fahimci sirrin dake tattare dake ina kewarki cike da soyayyarki dan allah karki barni haka bazan iya jura ba kamar yadda kika jurewa soyayyata."

" kamanin surarta ne kawai ke yawo acikin tunaninsa, tsukakken kugunta wanda ke d'auke da faffad'an mazaunai masu rikitarwa da birkita lissafi yaga ta juya masa rikicewa yayi ya rungumo a iska amman shi gani yake kamar itace ajikinsa yana sarrafa sansar jikinta , ya sake kai sigari bakinsa ya zuka da iyakacin karfinsa" ina jin tsoro tanwer bazan iya jura ba ,bazan iya rayuwa babu ke ba ,kice soyayyata,kece haukana ,kece rayuwata dan allah karki barni "
kansa ne ya cigaba da sarawa amman bai daina zukar hayakin wiwi ba daman kuma haka yake yi a duk sanda ransa ya 'baci idan yana son ya huce har ya samu bacci dole sai ya sha wiwi over amman wannan lokacin bai yi tasiri ba domin har 2 na dare bai samu barci ba sai tunanin da yake ta qaruwa a cikin kwakwaluwarsa da zuciyarsa."

A yanzu tunanin tanwer shine worst da yafi komai d'aga masa hankali don yana jin muddin bata amince ta auresa ba zai iya rasa rayuwarsa ,acikin mayen tunaninsa ya soma canzawa ya dinga magana da zuciyarsa "me yasa zaka zama haka adnan bayan kai din jarumi ne ba'a ta'ba kasaka a komai ba ? "baa ta'ba ganin rauninka a komai ba me yasa zaka bari aga rauninka akan mace macen ma da kake da tabbacin tana sonka ?"ka shareta kawai ka cigaba da rayuwarka ya qarasa maganar hade da zubewa kasa alokacin da karfe hud'u ta buga wani naunayen bacci yayi awon gba dashi ."

Yadda yake kallon anas ta cikin app haka shima anas din lokaci zuwa lokaci yake dubashi ta app yana kallonsa gbdy yaga halin damuwar da yake ciki, hankalinsa yayi matukar tashi amman yaki nunawa dan kar hally ta fahimta ta shiga damuwa ,dan haka ya sake janyota jikinsa yayi mata kyakkyawan runguma bacci bai daukesa ba sai daya sake dubawa yaganshi kwance bai motsi ya fahimci bacci yayi sannan shima ya kwanta da zumar gobe da sassafe zai tashi yaje ya gansa ya kuma bashi hakuri komai ya wuce dan yasan muddin bashine ya bashi hakuri ba ba zai daina wannan fushin na babu gaira babu dalili ba."

Jaguwa bai tashi ba sai kusan karfe takwas ya mike ya nufi bedroom dinsa yana layi saboda mayen baccin dake idanunshi kai tsaye bathroom ya shiga yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah ya haye gadonsa tare da lullube ilahirin jikinsa da bargo me taushi ya koma bacci wani bacci ne me nauyi ya daukesa bai tashi ba sai gurin 1:00 dot shima kiran sallah daaka kwlla a masalacin unguwarsu ne ya farkardashi ya sauko daga kan bed dinsa bathroom ya shiga yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa daure da white towel ya tsaya gaban mirrow yana kallon qirjinsa da murdaddun hannuwansa ya kai hannu ya shafa qirjinsa sannan ya sauke numfashi "ni din ba irin nmjin da mace zatace bata so bane ko daina so bare macen dana juya rayuwarta daga duniyar kasa zuwa sama jannati da shaukina”ina tanwer bazaki iya rayuwa babu ni ba kamar yadda nima bazan iya rayuwa babu ke ba .”


Naunayen ajiyar zuciya ya sauke ya dauki lotion din da yake shafawa ya shafa ajikinsa zuciyarsa na ayyana masa abubuwa "tunda ita tace ta daina sonka bazata aureka da sana'arka ba ka auri haseera zabin mahaifiyarka ita ai bazata gujeka ba daman kuma ta tabbatar maka da zata aureka a duk yanayin da zaka kasance ka koma gareta kawai
Ka bar tan na zuwa wani lokaci .”
“Wankakkiyar zuciyarsa tace “da wannan haukan zaka auri hasera? ka dai canza shawara karkaje fushin zuciya ya kaika ya baro “?ka koma gurinta kawai ba sai ka mata jarabawa ba dakakiyar kwakwaluwarsa ta bashi karfin gwiwa da hakan .”

tsaf ya shirya cikin kananan kaya ya feshe ilahirin jikinsa da turare me sanyin kamshi yana sake bawa kanshi kwarin gwiwa ya dauki cum ya taje sumar kanshi da kasumbar dake kwance a kyakkyawar fuskarsa ,ya fito zuwa falonsa inda ya iske an gyara tsaf idanunsa ya sauka akan table babu farantin jiya na tabar wiwi sai wani faranti dabam murmushi yayi dan yasan wannan aikin anas ne dan shi sam bai iya gyaran komai ba kuma baya yarda wani cikin yaransa yayi masa sai anas daman kuma tun fil azul shine me qokarin gyara komai ."
"Anas kenan bai san sanda murmushi ya subuce masa ba da sauri ya hade fuskarsa sakamakon jin qarar bud'e dakin yasan bai wuce Ana's ba shi din ne kuwa ya shigo shima kyakkyawan shirinsa ya raba ta gefenshi ya fita daga dakin ran anas yay matukar ‘bace ganin sharesa da yayi amman hakan bai hanashi daukar plet din abinci ya biyosa dashi ba ."

Tsaye a bakin fridge ya iske shi ya dauki fresh milk da cake yana ci duk da shi din ba me son zaki bane amman haka ya dinga turawa cikinsa anas ya ajiye plet din hannunsa akan center table adaidai lokacin da jaguwa ya samu guri ya zauna tare da daukar remut ya kunna tv a natse anas ya qaraso inda yake ya mika masa tafin hannunsa "assalamu alaikum .” da kamar ba zai amsa ba sai kuma ya mika masa nashi hannu bayan sun gaisa anas ya kasa sakar masa hannu ya cigaba da dubansa kamar ranar ya fara ganinsa .
"ya kake fatan kana cikin koshin lafiya ? jaguwa yayi masa banza kamar bai jishi ba "a ransa yace ina fa zanyi wata koshin lafiya byn an hada kai da kai ana neman haifar min da damuwa ,”allah yasa mu dace ya kuma bamu ikon zama da juna lafiya da amana kasan idan kana tarayya da mutun sai ana hakuri ,
idan wanda kake tare dashi yayi ba daidai ba ka fad'a masa gsky tunda kana zaune dashi ne tsakaninka da allah ,karka ce zaka zuba ido kana kallonsa bazaka masa magana ba ,ni kasani kasan halina adnan bana kwanciya da kowa araina duk kuma wanda yace yana sonka to yana sonka ."


"Ban iya son mutun ba anas kai ma ka sani amman yadda kayi min jiya kamar ka buga wani abu ne haka naji har yasa jikina yayi sanyi “jaguwa ya fada cikin mawuyacin hali yana ciza lip’s dinsa da karfi .
“Nima haka ne adnan ina bugan jiki qirjina akanka iyayena dangina kowa nawa yasanka kafin su bar duniya ,kai kasan you're so special to me ,abinda kayi min banji dadi ba ,”nima ai haka ne banji dadi ba ka wulakantani ka fada min magana me zafi ka tafi ka barni cikin zafin radadi "?
"Ya zan maka adnan ? kona tsaya bazaka saurareni ba ,mintuna nawa na dauka a gidan kafin na wuce ? ko ka dakatar dani kana kallonfa na bar dakina,koda yake gani kake kamar bazan iya rayuwa ba idan babu kai wanda ba haka bane kawai allah ne ya jarabceni da qaunarka acikin abokai na cireka daya tilo wanda zan bugi qirji ince wannan shine aminina amman sai kake son ka daukeni kamar ban san me nakeyi ba wanda ban san dalilinka ba ina jure kowani wulakaci da cin fuska amman idan yayi yawa sai na dakatar da mutun domin shine kawai zai sa na samu sausauci dan banason wulakanci kai kuma abincin ruhinka kenan kaga kana wulakata mutun gashi baka son gaskiya ni kuma muddin muna tare da kai zan fada maka gsky ko zata maka dadi ko zata maka ciwo amman sai na fada maka idan ya bata maka rai muyi zage zage amman banda zargi abokina ya karasa maganar yana dubansa Kamar zai zubar da kwalla ".

"Ka gama abinda ya kawoka ".?jaguwa ya fada yana dubansa zuciyarsa na karkarwa.”
"Eh!
"To sakar min hannu haka nan dan ka wani rike min hannu zakasa jijiyon hanuna suyi week ,sannan ka tashi ka wuce tunda kai kace bazaka fita aiki ba mu kuma shirin fitar da zamuyi yau muke yi kaga tunda bazaka ba ai ya kamata ka barmu ko ?.ya share wacan maganar da anas shima anas din yadda yayi masa haka yayi yace "bakace komai ba akan maganar da nayi yanzu ? "me zance maka kayi duk abinda ya fiyye maka idan ka shirya rabuwa damu ne bismillah "?"banason wulakanci adnan wai kana tunani zan mutu ne idan na barka da kake wasu abubuwa?” bari na fada maka zan iya rayuwa babu kai “dana mallaka maka abinda zai rike kai da rayuwar taka ba “? Eh naji koma me zakace ina sonta da ganin kimarta sbd ta mallaka min dukkanin farincikin dana rasa". jaguwa ya kallesa a dage yana tabe lips dinsa ."
Sannan murmushi ya sube masa "dan iskan abokina zaka rabu dani akan mace kenan ?ni bance haka ba ni dai bana son rigima komai ya wuce kai ne ka bani haushi yasa nace maka bazan je koina ba ,Ina fatan komai ya wuce yanzu zumuncinmu ya kai har aljanna don Allah idan kayi ba daidai ba ka dinga natsuwa a fada maka gsky “Naji inshaallahu komai ya wuce har abada amma don Allah kai ma ka daina bin bayan tanwer bana jin dadi ,yarinya nason ta dinga juya ni kai kuma kana side dinta kai da zakayi side dina mu taru mu yaketa ".

"Ai gskiyar kenan da baka so nifa banga laifin yarinyar nan ba kuma bazakasa naga laifinta ba
dan gskyar dake ranta ta fad’a ,"ai sai tayita fama da gskyarta takamarta ina sonta ba taje na hakura daita "au kana sonta ne a she ?"Bansani ba dan rainin hankali kawai kaga ni yanzu zabin uwata zanbi zan ma fi jin dadinta , nan da mintuna talatin ma gidan ammi zanje zaka fita operation ko ka fasa ?" Me zai hana masoyi kai kasan kai ne kwarin gwiwa ta hira ce ta balle a tsakaninsu kafin daga bisani jaguwa ya mike tsaye shima ya mike “ka tsaya ka duba system zakaga yadda muka shirya komai y akan tsari amman dai ka sake dubawa abinda kaga bai yi ba ka gyara bari naje bazan dade ba zan dawo yasa kai ya fice “.
“Okay zan duba idan na gama zan koma gida nayi sallama da madam saboda halin rayuwa zamu sake ganin juna ko kuma tafiyar kenan ?kai fa matsalar ka kenan sai ana jin dadi ka wani sako zance mutuwa murmushi Ana’s yayi yana karyar masa da kai tare da nuna shi da dan yatsantsa daya,ba dole na fadi haka ba tunda muna aikin sai da rai .



A hankali suka fito tare daga cikin bangaren jaguwa anas ya nufi inda system yake shi kuma ya fito zuwa haraban  gidan kai tsaye inda jerin motocinsa suke ya nufa yana kokarin shiga mota eku ya qaraso da sauri da hannu ya dakatar dashi baya son zashi gurin ammimsa ajashi, ya shiga motarsa Range Rover black colour yaja ya fito daga cikin haraban gidansa   ya tsaya a kofar gida batare daya kashe motarsa ba ya sallami masu zuwa amsar kudin taimako a duk safiyar duniya ,cike da farinciki suke saka masa albarka yaja motarsa yayi gaba ,a natse yake tuqi zuciyarsa na tunanin tanwer amman sai yayi sauri kawar daita ya sako wani tunani dabam a haka har ya qaraso kofar gidansu yayi parking ya fito yana taku a hankali tamkar baya son taka kasa  nan ma dai mutane sukai masa casaaa yan maula ya tura hannu cikin ajihunsa ya zaro bandir din kudi ya mimika masu sannan ya shiga gidansu bakinsa dauke da sallama  yayi mamakin da yaji baa amsa ba dan da wahala ka shigo gidan kana sallama ammi bata jiyo ta amsa ba ."

Yana kokarin kutsa kai cikin falon ammi hasera ta fito da sauri hannunta rike da plet  tana cin soyayyar kaza sauran kadan ta fada jikinsa yayi saurin ja da baya  yana kakkabe jikinsa murmushi ya bayyana akan fuskarsa  "a'a danuwana sannu da zuwa haka nan ya tsinci kanshi da jin haushin ta tamkar ba dan ita yazo gidan ga , yaja tsaki batare daya amsa ba , ta kada kafadanta alamun bata damu ba ta cigaba da yagar kazarta shi kuwa yayi matukar hade fuska  yana sake jin damuwa yaji komai ya sauya masa ba karamar yadda yazo da niyyar zai karbeta ba ,yadda ma take cin kazar ma kamar wata mayunwaciya "ina ammi ? yayi tmbyr a can kasan makoshi tare da juya wa ya nufi  part dinsa na gidan   "me kace ? ta biyosa da plet tana tmbyrsa "mara kwakwaluwa kawai yanzu zakice bakiji me nace ba da zaki min wata irin tmby ?".ya fada a zafafe yana cigaba da tafiya ."

"Allah ya baka hakuri ai banji abinda kace bane shiyasa da zaka wani ce min mara kwakwaluwa ."ya waigo inda take a bayansa ya kalleta a natse ,gata dai Kmr goggagiya amman sam villager ce ko magana bata iya ba komai  da hauka take yi ,to daman yaushe zaa hada  mutumin  da yazo daga maiduguri da wanda yake rayuwa a lagos ?".ita kwakwaluwa bata aiki yadda ya kamata idan ana dankara mata nama dan allah malama ki ajiye kazar nan haka kin wani rungume kaza Kmr baki taba ci ba yasa kafa ya buge plet din hannunta  ya shige part dinsa  shiru tayi tana kallon kazarta a kasa  ba tace masa komai ba dan  ta fahimci rigima yake ji dashi ta zuba wa kazarta  ido tana kallo ."Ta dauki lokaci tana kallon kazar kamar ta dauka amman ta guji  ta disga kanta ta hakura   tabiyosa dakin ta samu guri ta zauna tana fuskantarshi tare da sha gala da kallonsa atsawa ce yace "ke !.

"Tayi firgigib ta dawo haiyacinta “naam  danuwa ta amsa da hakan batare data nuna damuwar da ke din daya kirata dashi ba ita da zai dinga shiga tsabgarta koda zagi ne ai zataji dadi ,"kawo min  ruwan sha a cup".  ta mike ta juya da sauri yabi tafiyarta da kallo sam babu natsuwa kamar tanwer ya lumshe rikitattun idanushi “Anya kuwa zan iya karbarta na hakura da tanwer “ ? Yana wannan tunanin taje ta kawo masa ta mika masa ya bude idanunshi da kyar yace "sha !
Ta bisa da kallon mamaki dan ita bata bukatar wani ruwa "ki sha ki samu natsuwar  wannan

Please Login or Register in order to submit comment