Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zira hannunwansa duka cikin wondonsa ya cigaba da tafiya still suna biye dashi har ya shiga wani d’aki basu daina binsa ba har anas ,hakan yasa yaransa ma suka biyo bayansu cike da tsananin tashin hankali.”
Ya tsaya cak ajikin bango yana kokarin saita kanshi bayan kamar second biyar sannan ya soma magana muryarsa can kasa kasa “Tabbas na gama nazari da duk wani tunanina akanmu sai dai banga mafuta ba ,daman na shigo damu nan ne domin boye sannan mu san yadda zamu tsara fitar da kanmu kafin su riskemu akwai wata boyayyar hanya ta nan amman magudanar ruwa ne ,da iya mu biyar din nan ne nasan zamu iya ficewa tunda mun ta’ba yin haka a can baya amman wadan nan dake tare damu acikinsu babu wanda nake tunanin ya iya iyo.”ya qarasa maganar tare da yin shiru yana fuskantarsu.”

Babu wanda yayi magana acikinsu suka cigaba da sauraronsa ya dan numfasa sannan ya cigaba da mgn “idan gabadayanmu muka kasance anan hakan zai iya janyo mana asarar rayuka dayawa ciki kuwa har dani ,a yanzu ne fa muke cikin wani yanayi me matukar wahala da hatsari dan haka gabadayanku ina bukatar kuyi hakuri ku zauna anan ni zan fita, idan na riski mutuwa daman ni din me kararren kwana ne, idan kuma ina da sauran rayuwa zan dawo gareku mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka faro yana gama fadar haka yayi wuf ya fice acikin dakin tare da janyo kofar dakin wacce bata da maraba da magnet kofar bata kai ga rufewa ba anas yasa hannunsa kofar ta tsaya cak bayansa yabi da kallo kamar ya zubar da hawaye sai daya daina hangosa sannan ya koma ciki dakin cikin tsananin tsinkewar zuciya ya zauna yana dafe goshinsa yana fidda numfashi sama sama .”



JAGUWA ya qarasa a hankali ya haye matattakala har lokacin basu shigo bangaren da kofar kasa take ba sannan basu daina harbe harbe ba , bangarensu jabir kuwa gabadayansu zama sukayi tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa ,
zuciyarsu tunanin jaguwa kawai take ,suna tsananin qaunarsa musamman ganin yadda shima yake matukar qaunarsu sun san da ana yiwa mutun numfashi tabbas da zai musu ,jaguwa ya samu nasarar fitowa cikin sauri ya maida kofar ya rufe kamar yadda take ya janyo table ya maida shi ya bar gurin da sauri zuwa wani bangaren .”


Alamarin polisawa da sojoji da dss kuwa sun shigo cikin gidan sun bincike gidan jaguwa sama da kasa amman babu su babu alamun su , suka sake bincikar me gadi shi kuma ya sake tabbatar masu da lallai suna cikin gidan alokacin daya sheida masu, kuma acikinsu babu mutun daya daya fita nan da nan hankalinsu ya tashi suka fara tunanin ta ina zasu fara Ib yafi kowa shiga rud’ani da tunanin ina suka yi “? to ko ‘bacewa sukayi “? ya tambayi kansa “Lallai hakan zata iya kasancewa tunda akwai tsari me karfi a tattare dasu duk wannan tunanin da yake yana yi ne yana tafiya yana dube dube bai ankara ba yaji yayi karo da mutun yana kokarin fitowa daga wata kwana .”Shiru yayi tun daga kafafunsa ya d’auki kallonsa har zuwa boyayyar fuskarsa sannan ya saita shi da bindigarsa yana kallonsa dafe da kafadar hannunsa daya, ga kuma jini na tsiyaya, zuiyarsa ce ta soma rawa ganin irin zane mutumin daya gani d’azu a office din tanwer , fuskarsa ce kawai ta bambata da wancan mutumin ,bai tsaya wata wata ba yace “you are under arrest “.

“Na nawa kuma sp bayan gani agabanka ka kama ni mana ya fada a dake yana sakar masa murmushin gefen baki wani sabon tashin hankali da mamaki ya mamaye zuciyar Ib “kana mamaki ko to ka daina mamaki naga damar ka kamani ne shiyasa ka ganni agabanka domin ina son mu buga wata yar qaramar wasa a tsakanina da kai.” sp T. Ibrhim ya sake saita kansa da bakin bindiga kamar yadda polisawa kan yi “ka d’auka zan kamu ne cikin sauki kamar yadda ka saba kama mutane ? jaguwa bazai kamu a hannun qaramin ma’akaci sirri irinka ba aikina kuma rayuwata ce babu wanda ya isa ya dakatar dani akanshi sai dai idan bana numfashi a duniya muje gani sai lokacin da waadina ya cika ka tafi dani duk inda zaka kai ni a madadin ma ka samu qarin girma fad’uwa zaka samu daga wannan lokacin zamu fara buga wasan sp .”

“shi wannan wasan baza’a kai ga bugasa ba zaka bakunci lahira , ya dauke bakin bindiga akansa ya saita daidai saitin zuciyarsa dake harbawa da sauri sauri sakamakon abu biyu da suka hade masa alokaci daya wannan tashin hankali dana tanwer dinsa,har Ib zai harbesa sai kuma ya tuna baa bashi umarnin harbinsa ba dan haka ransa amatukar’bace ya cigaba da magana “da’ace an bani umarnin harbeka da tun yanzu anan na cika aiki kaga wasan yazo karshe kenan .”
“jaguwa yayi wani murmushin gefe baki “ good job sp ka gwada harbina mana kaga me zai faru “?.yayi maganar yana matsosa cike da kwarin gwiwa da sauri Ib yaja baya cike da firgici mutun kamar aljani.”suna cikin wannan halin sai ga wasu daga cikin jami’an tsaro ganin ib yasa suka qaraso da sauri suna cewa ka samu nasarar gani ko gawar mutun daya ne acikinsu .”?

“ban samu nasarar ganin gawa ba amman na samu nasarar kama mutun daya wanda nake kyautata zaton shine babbansu .”yayi mgnr alokacin da suka hallara “na dai yarda ka ganni zaka fad’a masu baka samu narasa kamani ba ”jaguwa ya fada. yana huci yana sake rike hannunsa dake tsiyayar jini yana masa zugi ”wata tazananniyar tsawa sojojin dake cikinsu suka buga masa da karfi “enough ka dade kana bawa jami’an tsaro wahala yau dubanka ya cika kwararre interligent police officer yayi nasarar kamaka daman kuma shi kadai ne zai iya da professional criminal like you .”


Gabadaya jami’an tsaro suka zagayesa suna huci tamkar mayunwata suna tamabayrsa sauran abokan aikinsu a tsawa ce, sun matukar firgitashi amman hakan bai sa ya nuna ajikinsa ba “ka sanar damu ina sauran abokan taadanceka suke ?“a yanzu ni kadai ne kowa yayi ta kanshi .”Ib ya dago kanshi yana kallonsa “tunda ka shigo hannu su kansu bazasu tsare ba muddin suna cikin kasar nan azabar dazaa gana maka kadai ta isa tasa ka nemosu a duk inda suke “na gwamaci mutuwa dana nemosu daya daga cikin sojojin dake tsaye agurin ya daga hannunsa zai wanka masa Mari jaguwa yayi saurin gocewa ai kuwa yasa bakin bindiga ya buga gwiwarsa kafin kace me gwiwarsa tayi kasa cikin tsananin azaba .”
Ib ya bada umarnin a shigo da yan jarida ya nufi ciki ya bar wasu jami’an tsaro tare da Jaguwa babu inda bai shiga acikin gidan ba yan jarida na biye dashi suna haskawa kai tsaye tare da haska fuskar jaguwa wanda zuwa lokacin an daba masa handcuff a duka hannuwansa har part din baya suka shiga suna dubawa “I thought bayan gidan nan na zagaye da jami’an tsaro?” haka ne sir !.”


“Ina mamakin inda sauran gang dinsa suka boye ,ku raba kwananku kuyi bincike me kyau lallai suna cikin gidan nan duk kuma wanda yayi kokarin tserewa ku harbe kansa da sauri wanda ib ya bawa umarni ya juya ya fice daga part din daidai gurin makeken table din dake part din baya ya tsaya komai na cikin falon ya hargitse sakamakon harsashin da suka sakarwa gidan ,yayiwa table din kuri da idanunshi yana dubansa yana qoqarin janye table din “qarar wayarsa ta dawo dashi dagawar da yake qoqarin yi ya dauki kiran “yes sir mun samu nasarar kama mutun daya Kmr yadda kake gani ana haskawa,yaki fadi inda sauran suke kuma an tabbatar mana suna cikin gidan gabadaya alokacin da muka shigo sir .”yana wa me gidansa bayani yana cigaba da jan table yayinda sauran inspectors ke bincika wasu bangaren.”

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️45

.....Arikice mumy tayo kanta tana kiran sunanta "tanwer!tanwer!! amman Shiru bata motsa ba ta kai hannunta daidai saitin  hancinta taji bata sauke numfashi, tuni  ta sake rikicewa tare da fashewa da wani sabon kuka "tanwer karki min haka ,ki barni haka karki qara min wata damuwar akan wacce nake ciki , damuwarki  tana d,aga min hankali ,ki tausaya min ,kinsan ina sonki fiyye da komai a rayuwa ina son ganinki  cikin farinciki da kwanciyar hankali  shiyasa ma na amince miki da auri adnan ta qarasa maganar tana tattarota zuwa jikinta ta rungumeta tsam ta manna kanta a daidai qirjinta tana jijigata had'e da kiran sunanta adaidai wannan lokacin ruky da masu aikin gidan suka fito zuwa parlour'n  a rud".

Da sauri  ruky ta qaraso ta durkusa agaban mumy tana cewa "Lafiya mumy naga tanwer  haka kamar ma bata numfashi ?bata bata amsa ba dan bata san me zatace mata ba ,ita kanta bazata so ruky  tasan irin  nmj da diyarta ke kwakwar so kenan ba "mumy me ya sameta please ?"bata gama rufe baki ba mumy ta saki wani kuka me karfi "ki taimaka min ruky mu kaita hospital tana kokarin tashi ta gagara saka makon sakewar da jikin tanwer yayi, ruky tayi wuf ta  mike jikinta na rawa ta nufi hanyar kitchen karo suka ci da zulai ne aiki rike da goran ruwa dan ita tun fitowarsu   ta fahimci suma tan tayi ,da sauri ta kar'bi goran  ruwan ta dawo inda mumy take zaune rungume da tanwer wacce bata da alamun motsawa ,
ta bude goran ruwan ta tsiyaya  a tafin hannunta ta soma shafa mata ruwa a fuska tana kiran sunanta amman still  shiru ".

Hankali ruky ya tashi kwarai saboda alamarin tanwer ya fara damunta iya saninta  soyayyar adnan ne matsalarta kuma iyayenta sun amince mata tare da bata damar aurensa me kuma ya saura ?"to ma yanzu me ya faru da tai mummunar suma haka ?".
Dan ita kam ta kasa gane kanta ko adnan din ne kuma ya fasa aurenta  yasa ta shiga mummunar hali haka"?ruky tayiwa kanta tambayar da bata da me bata amsa tare da shiga rudani  sosai da tunani game da alamarin tanwer, yayinda shi kuwa dady har lokacin  yana nan tsaye yana dubansu cike da bakinciki mara musaltuwa batare da yace komai ba saboda takaici   amman kuma  shima din a matukar rikice yake baya dai son ya nuna ya shiga damuwa ne adalilin halin data shiga dan abun na tanwer ya wuce tunaninsa ."

Zufa ne ke keto ma mumy a gabadaya ilahirin jikinta yayinda zuciyarta ke tsananin bugawa gabadaya a rude take kallon dady dake tsaye har lokacin yana dubansu bashi da alamun nuna tausayawa gareta "abubakar ka taimakeni kar na rasa yarinyarta ,ka taimakeni mu kaita hospital domin ceto rayuwarta bazan gwamaci mutuwarta ba ka taimakeni dan allah "ta qarasa maganar cikin raunanniyar murya “naji zan taimakeki amman kafin nan sai kinyi min akwatin zaki tursasata ta cire wannan damuwar a ranta sannan ta tsaida zuciyarta akan Ibrahim ko wani mutumin kirki dabam .”ta gyada masa kai tana cewa '"naji nayi maka wannan akawarin zan ma bar kasar nan daita ni dai ta dawo haiyacinta shine muradina "auren ibrahim fa “? ta cigaba da girgiza masa kai "alamun a’a “.

“Daman yasa da wahala ta amince tafi bukatar farincikin diyarta dashi koma yace tafi qaunar tanwer dashi muryarsa na rawa da jikinsa ya soma qoqarin neman gurin zama yana me danne damuwarsa da tashin hankalin ganin halin da tilon diyarsa take ciki ya zauna ya cigaba da kallon abinda ke tafiya a gari,har wannan lokacin jami’an tsaro ne ke kan aiki ,inda jama’ar dake unguwar jaguwa suka cika kofar gidansa makil suna zanga zangar bazasu yarda a taba masa gida ba, hakan yasa polisawa suka kunna tiya gas tuni mutane suka fara darewa saboda zafi me hade da yaji dake shigar masu ido gefe guda kuma yan jarida ne ke faman tambayar mutane goma daaka fito dasu daga maboyar jaguwa ciki kuwa har da alhji tahir mahaifin Ibrahim.”

Cike da tsananin tashin hankali mumy ta kalli bakin tanwer dake fitar da wani kumfa fari sol bude ,ta bakinta da kyar "a karo na biyu abubakar kaci amanata wannan kalmar kawai take furtawa tana hawaye yadda take magana haka farin kumfa ke sake dalalowa abakin tanwer wanda ya dagawa dady hankali wannan karon kasa jurewa yayi ya mike a matukar tsorace bai san sanda ya zari keyn motarsa ya cicibi tanwer ya rungumeta ajikinsa ,shi da ya dauka abun wasa ne ,a rude sukayi waje daita ya nufi inda motarsa take pake tun kafin ya qaraso ya danna keyn hannunsa mumy ta bude masa gidan baya ya sakata ,bai tsaya jiran wani direba ba ya shiga mazaunin direba ya shiga ya zauna yana tada motar tare da danna hon da karfi .”


tun kafin ya qaraso bakin get aka wangale masa tafkeken get gidan ya fice da mugun gudu securities din bakin get suka bi bayan motar da kallo zuciyarsu cike da mamaki abinda yasa minister ya fita cikin tsananin tashin hankali haka ? fatan a sauka lafiya sukayi masa sannan suka maida get suka rufe ,
hospital da tanwer suka nufa kai tsaye emergency aka shiga daita gbdy kusan rabin abokan aikinta ne suka rufa akanta ana kokarin ceto ranta amman kusan minti talatin likitoci na kanta amman numfashi yaki dawowa hakan kuwa ya daga hankalin mumy da dady dan sai yanzu yaji nadamar abinda yayi domin shine silar faruwar komai da bai kunna tv ba da wata killa hankalinta bai tashi haka ba ,nan take jikinsa da hannunsa suka kama rawa balle mumy data kasa tsaye ta kasa zaune sai kai kawo take tana furta duk adduar datazo bakinta tausayin diyarta da halin da take ciki yasa ta kife kanta a bango tana kuka ."

Dady ne yazo  yana kokarin rarrashinta duk da yasan ba lallai ta fahimcesa ba wani irin nauyi da kunyar abinda yayi dazu ya kamashi shi kansa a halin yanzu yana bukatar yayi kuka ya fidda hawaye ko zai samu ya rage nauyin zuciyarsa mumy tun tana turesa har ta hakura ta fada jikinsa suka rungume juna yana rarrashinta daga bisani suka samu guri suka zauna jugun jugun suna jiran fitowar likitoci shiru wasu mintuna talatin tazo ta wuce lokacin har an kira sallahr laasar suka je sukayi alwala suka yi sallah tare da nemawa yarinyarsu sauki a gurin ubangiji allah madaukakin sarki ."

Suna zaune wayar mumy tayi qara ruky ta miko mata sunan ibrahim ta gani dan haka taki dauka dan yanzu haushi yake bata gani take kamar shine silar fadawar diyarta cikin fagarumin matsala tana mikawa ruky wayar kira ya shigo wayar dady ganin me kira ya daga da sauri suka gaisa anan yake fada masa cewa suna asibiti tanwer ce a emergency bai rufe bakinsa ba yaga an turota an nufi I.C.O daita da mugun sauri suka tashi atare suka shiga cikin suka samu tana sauke numfashi kadan kadan sai dai bacci take nan mumy ta zauna ta kife kanta da gadon da take kwance tana zubar da hawaye yayinda take tunanin jaguwa ko a wani hali yake ."?


Yadda jaguwa yayi shiru ya zuba masu rikitattun idanunshi da suka gama canza kala yana dubansu daya bayan daya domin jin abinda zasu ce ,haka suma suke kallonsa domin rasa abun cewa har sanda Ana’s ya zaro wayarsa da yaji motsinta ta hanyar bebriting tun kafin ya duba zuciyarsa ta bashi tabbacin me kiransa ai kuwa yana dubawa sunan my princess ya gani yana yawo a screen din wayar .”
JAGUWA ya dubesa cike da tashin hankali sai dai bai ce masa komai ba sai anas ne ya motsa labbansa a hankali maganarsa ta fito “hally ce !“.yana fadar haka yayi shiru “ka karka d’auka,idan wayar ta gama ringing ka kashe gabadaya .”

Ana’s ya d’an kallesa a rikice ya gyada masa kai alamun haka yake bukata ,babu yadda ya iya dole yayi kamar yadda ya umarcesa amman yaso yaji sautin muryarta bai sani ba ko shi zai zamo abinda zai ji karshe kafin mutuwa ta riskeshi ,jikinsa a matukar sanyaye ya zauna a saman hannun kujera idanunshi na qoqarin kawo ruwan hawaye, jaguwa ya ciro wayarsa ya soma neman layin ammi alokacin
Hally na zaune shiru tana tunanin abinda yasa anas yaki daukar wayarta har ma akarshe ya kashe wayar gabadaya,taji qarar ringin din wayar ammi ta dubi wayar dake yashe a kusa daita sunan yayanta ta gani ta dauki wayar da sauri ta mikawa ammi tana me tsura mata ido .”


Ammi ta karbi wayar daga hannunta ta danna koren maddani tare da sallama daga can bangaren jaguwa ya soma magana cikin raunanniyar muryarsa “ammi mun fita wani aiki ne wata killa mu dawo yau ko gobe ko kuma dai sai an ganmu muna tsananin bukatar adduarki “ta dan ja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana cewa “allah ya baku saa yasa kuyi nasara allah ya tsareku gabadaya” Ameen ya amsa tare da yin shiru yana sauke numfashi jin yadda yayi shiru tace “Anya kuwa bayan tafiyarku aiki babu wata matsala ?”babu komai ammi sai dai ina jin babu dadi ne araina ,”to a hakura mana da tafiyar “hakan bazai yiwu ba ammi yanzu haka ma muna cikin aiki sai dai fatan nasara “inshaallahu karkaji komai zakuyi nasara allah yayiwa rayuwarka albarka ,
Ameen ammi sai dai hally zata cigaba da zama agurinki har sanda zamu dawo “to shikenan yana gama jin abinda tace yay discounting din kiran ya sake fuskantarsu “.

Halima ta maida kallonta ga ammi dake zaune tana amsa waya suka hada ido daita taji gabanta ya shiga faduwa, take damuwa ta mamaye fuskarta ta dubi ammi tace “ammi me yaya yace miki ?”wai sun tafi aiki ne suna bukatar addua sannan ke zaki cigaba da zama anan har sanda zasu dawo “to ai na kira ya anas bai dauka ba byn bai ta’ba kin daukar wayata ba “yanzu me kikaji nace miki sun fita aiki “amman ammi ina jin ba tafiya wani aiki ne ya hana ya anas daukar wayata ba akwai abinda ke faruwa dashi tunda har yaya zai iya kiranki alhalin suna bakin aiki shi me yasa bazai dauki wayata ba ?.”ta fada muryarta a raunane kamar zatayi kuka .”


“ki kwantar da hankalinki karki yi wannan tunanin Kinsan yanayin aikinsu ya gaji haka inshaallahu lafiya zai dawo “duk sanda zasu aiki yana fada min kafin mu rabu me yasa yau bai fad’a min da kanshi ba sai yaya ne ya kira kuma me yasa bai dauki wayata ba ?”ta qarasa maganar tana hawaye ammi ta fuskanci rashin daukar wayarta da rashin fada mata zashi aiki ne yasata damuwa dan haka ta soma rarrashinta “inshaallahu babu wata matsala kiyi masu kyakkyawa fata .” ina masu kyakkyawa fata amman jikina yana bani akwai wani abu dabam .“haba halima me kuma jikinki zai baki kin dai tsargu ne kawai amman babu komai “allah ji nake kamar tafiyar me tsawo ce dayawa wallahi ni da zasu hakura da tafiyar nan su dawo zai fi min alkhairi .”

Tsab ammi ta gano manufar hally dan haka tayi murmushi “kiyi masu addua gamawa da aikin lafiya tayi shiru daga bisani tace to allah ya dawo dasu lafiya ta kwanta gefe wasu tsiraran hawaye na zubo mata ta gefe da gefen idanunta ,ammi ta gani akan fuskarta amman bata dai mata magana ba aranta tace “yaran zamani kenan kiriri suke nuna maitarsu a fili akan mazajensu .” jaguwa ya cigaba da sauraron su har lokacin babu wani daga cikinsu daya qoqarin cewa wani abu sai faman mulmula baki suke alamun suna son yin magana amman kwakwaluwarsu ta kasa aiwatar da komai .”


A hankali ya qarasa inda matattakala take cike da sand’a ya hau ya kasa kunnensa sosai sautin wata murya yaji yana magana “ba zamu bar nan ba sai mun kamashi dan haka Kuyi pata pata da gurin ta yadda harbi zai samesu a duk inda suka boye acikin gidan domin na lura suna son suyi wasa da hankalin hukuma ai kuwa kamar jiran umarni policewar dake rike da bindiga suke suka cigaba da harbin cikin gida wanda windows kam tuni an patattakasu har ana iya hango cikin gidan kuma hakan ne ma ya bawa jaguwa jiyo magana.”ya sauka a hankali ya koma inda anas suke ya janyosu suka yi wani bangare “ku tsaya anan ina ganin ni zan fita ni kad’ai da sauri ana’s ya mike tsaye jikinsa na kyarma yana girgiza kai yana kallon jaguwa da yanayinsa ya nuna alamun rashin tsoro wata irin damka yayiwa hannun JAGUWA da karfi yana cewa “babu inda zan bari kaje,wato kana son ka rigani mutuwa ko “?yadda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin rud’ani da tashin hankali.”


Kamo kafad’un ana’s jaguwa yayi ya zaunar dashi akan kujerar daya tashi yana qoqarin kwantar masa da hankali “please ana’s kayi qoqarin ka dinga rage wannan tsoron , idan ina hango tsoro acikin kwayar idanunka kana karyar min da gwiwa d’ago idanunshi yayi ya tsurawa JAGUWA yana kallonsa tabbas maganarsa haka ne a yanzu ma da yake kallonsa yaga jikinsa yayi sanyi runtse idanu anas yayi ya fara tunanin abinda zai faru idan jaguwa ya fita ”
“Har yanzu basu shigo ba suna haraban gidan ya kamata na hanzarta fita tun kafin su shigo“
kamil yace “no jaguwa zuciyata bata amince da fitarka kai kadai ba ko kuma nace bamu amince ka fita ka mika kanka ba ,wannan gaskiya ne kamil bamu yarda ba me yasa ma ka bari muka shigo .”?ai da an sani abi shawarar anas tun farko anyi bata kashin amman yanzu allah ya taimakemu mun samu mafaka me zai sa kuma mu maida kanmu da kanmu .”? ka dai sake wani tunani amman wannan sam sam bai yi ba inji cewar jabir .”


Wani sanyi dadi anas yaji ya mamaye zuciya da gangar jikinsa sakamakon goyon bayan da suka bashi ,jaguwa ya shafa sumar kansa da hannunsa daya, yayinda dayan hannun ke cikin na anas wanda yake dubansa cike da tausayawa, furzar da huci me zafi yayi ya zare hannunsa dake cikin na anas yana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba ya isa inda dining area yake ya tsaya cikin tsananin tunanin abinda zai yi bayansa suka bi da kallo ,ganin haka ya zira hannunwansa duka cikin wondonsa ya cigaba da tafiya still suna biye dashi har ya shiga wani d’aki basu daina binsa ba har anas ,hakan yasa yaransa ma suka biyo bayansu cike da tsananin tashin hankali.”
Ya tsaya cak ajikin bango yana kokarin saita kanshi bayan kamar second biyar sannan ya soma magana muryarsa can kasa kasa “Tabbas na gama nazari da duk wani tunanina akanmu sai dai banga mafuta ba ,daman na shigo damu nan ne domin boye sannan mu san yadda zamu tsara fitar da kanmu kafin su riskemu akwai wata boyayyar hanya ta nan amman magudanar ruwa ne ,da iya mu biyar din nan ne nasan zamu iya ficewa tunda mun ta’ba yin haka a can baya amman wadan nan dake tare damu acikinsu babu wanda nake tunanin ya iya iyo.”ya qarasa maganar tare da yin shiru yana fuskantarsu.”

Babu

Please Login or Register in order to submit comment